Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe suna suka samu zuwa barka shima din su Yaya da su Hajiya sukabi da zasu barka mamanmu ita ke zuwa tana Ma jariri wanka wanda yaci sunan Baba Mallam
Suna zaune Jaririn na Hannun Hanne Amina ta karkato tana Fadin"Wlh bakinsa Sak na uwar ne..!
Hanne ta Zunkuleta tana Fadin"Ba Ruwana Amina..kada taji.!
Amina na Danne Dariyanta ta Dago tana Fadin"Mamanmu kalli jaririn nan yana karami bakinsa babba..!
Hamida da Hanne da suka san mganar suka yi tsumu tsumi.
Hajiya Uwa ce tace"Banda abunki Amina ai jariri ne yana girma zai Sauya..!
Mamanmu tace"Mai sunan mallam fa Shamsiya ce Sak..Kila sai nan gaba zamu ga Jafaru..!
Akayi Dariya Shamsiyan na gefe batace komai Amina nata Dariya sai da suka fito zasu tafi Hamida ta jawota Tana fadin"Amina wlh ki bari ba kyau kushe hallitar Allah..!
Hanne tace"Kuma bata san me zata haifa ba!
Amina ta toshe kunnenta tayi gaba Tana Fadin"Nagode da wa"azi Malama Hamida da malama Hanne..!
Kyaleta sukayi ganin bazataji ba Washegari sun so su koma Mamanmu tahanasu tunda ya Jafar din yace ba suna ba Taro an dai yanka Raguna Mallam yaje yayi barka da kansa.
Ranar kwatsam sun je makaranta sai ga Zainab tazo da karamar waya Tecno mai memory,Tsohuwar ta Anty ta ce aka bata akwai Memory aciki ita Amina waya ba Damunta tayi ba Shiyasa bata Damu ba
Acikin yan ajinsu akwai masu waya Ranar an tashi Break Taji Zainab na ma wata Saratun ajinsu mganar ta Turamata Sabbin Wakoki
Tana Daga sit dinsu tana karatun Wani Littafin da Zainab ta aro mata mai suna Yar Jagora.
Duk da kunnenta baya wajen taji Sunan Radau acikin kanta.
Saratu ta kalli Zainab tana Fadin"Ni ban da wasu wakoki Zainab..Sai dai ina da Sabbin wakokin AMINU buba Da yayi kwanan in kina so sai na Tura miki..!
Kamar a mafarki taji ankira sunan ta Taba jin sunan ta kuma Haddace sunan acikin kanta.
Da Zumudi a Murnan Zainab tace"Yauwa don Allah sakamin..Ina son wakokinsa..!
Daga sama kawai suka ga Amina Sanda ta Dafa Saratu tana Fadin"Wani Aminu Buban..?
Da mamaki suke Binta da kallo kafin Zainab tace"Mawaki ne mai Tashe Amina..!
Ido ta zaro kafin tace"Da gaake..?kina da Hotonsa..?
Zainab cikin mamaki tace"Hotonsa kuma..?a"a ni bani dashi wakokinsa kawai nakeji shima a wayar ya Kamal nasansu..!
Saratu ce tace"Yayata nadashi in kina son ganinsa ki bari gobe zan turo miki..!
Da sauri Amina tace"Yauwa don Allah ki turomin akwai wani dana sani ne in so nagani ko shi ne..!
Da mganarta suka yarda da ita Washegari kuwa suna zuwa makaranta Saratu tace ma Amina ta Turo Hoton a wayarta Vivo Lokacin da Amina ta ga Hoton sai da Gabanta ya Fadi.
Yana Sanye cikin Riga da wando Ja da Fari Wandon Ja ne Rigar ciki Fara sai Jaker dinsa ja Takalmin kafarsa Booth ne fari haka ma Facing cap din Kansa Ja ne mai Kalan Fari yayi Tsayuwar matasan wannan zamanin Fararan Hakoransa mai Wushirya duka suna waje a kasan Hoton an sanya A.A BUBA..!
Sai alokacin Amina ta tuna yana ta Nanata mata bata sanshi ba..?Ashe cele ne shi to ita ina zata sanshi..?
Ba waka suke ji ba ballatana kallo.
Saratu ta karbi Wayarta tana kallon Amina Zainab isa ce tace"Shine..?
Sai ta samu kanta da girgirza kanta Saratu tace"Kila suna ne yazo Daya..Shi wannan Aminu Aliyu Buba sunansa mawaki ne mai tashe yadda naji ana Fada bai Dade ba sunansa yayi Fice..!
Amina na jinsu batace komai ba Zainab ce ta karba tana ganin Hoton kafin tace"Kyakyawa dashi kamar Bafullatani..!
Saratu tace"Ance Bafulatanin Yola ne..Karatu ya kawosa kano..ya fada Harkan waka..!
Amina ita Daga Lokacin batama jinsu Tana chan Tana Mirmishi Lalle Amina mai Sa"a ce yau ga Wanda Duniya ta sani ya Taba cewa tana Burgesa anya in ta Fadama Mutane zasu yarda da ita..?
Taso gaban irin su Sa"adatu ne ta tabbata sai Haushi ya kashesu ita Kadai kawai in ta Tuna A.A Buba ranta sai yayi Fari kanta ya kara Girma Ho..Sai ita Amina Aminene Manya kasa..!





*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki duk inda kike*


*🅿️16*

*Yola..*
BAYAN WANI LOKACI..!

Kwata kwata bai ji kiran sunansa da take yi ba sai da ta Daddage ta Dirkamai Duka a gadon bayansa kana ya dawo cikin Hayyacinsa Dago Shanyayyun Idanuwansa yayi ya zube akanta cikin kosawa yace"Haba Nenne..!
Haba..!
Ya ke fada yana sosa bayansa Hannu ta kai zata kara Dukansa ya mike Tsaye da Sauri yana Fadin"Haba mana Nenne..!
Wannan ai cin zali ne..!
Tana Hararansa tace"Awa na nawa a Tsaye akan ka ina ta mgana baka ji ba..?
Anya Aminu wani abu baya Damunka..?
Tun shekaranjiya da ka iso nake ganinka cikin Zurfin Tunani ko Mtsalan wajen aikin naku ne..?
Bayansa yake sosawa kafin yace"Shine Zaki Saki karfin da Allah yayi miki ki Dake ne..?
Haka ake yi Nenne..?
Kunnensa take neman taja ya matsa yana Dariya yace"Tsaya..Tsaya..Wlh hannunki kamar na maza saboda zafi..Nenne akwai karfi..!
Kinsan mu Jikinmj mai Laushi ne Nenne zata yi kisan kai..!
Yana yi yana Dariya itama Dariyan take Farar mace ce,kamar sa sai dai itama bata da wani Tsawo kamarsa Suna da Diban kama ta Hasken Fatarsa ba wata babba bace domin Iyakarta wajen Shekaru arba"in da wani abu.
Ganin ya shagala yana Dariya yasa ta Shamacesa ta Murdo Wuyansa yar kara ya saki yana Fadin"Wayyo Allah..Jama"a
Haba Nenne zaki karyamin wuya ne..?
Cikin Fada tace"Ka maidani kakar ka ko Aminu..?
Ga Breakfast dinka chan tun dazu har yayi sanyi kana zaune tunda ka zauna sai faman Tunani kake yi..!
Da sauri yace"To naji Sake ni in miki Bayani..!
Sakinsa tayi kafin ya juyo Kafadanta ya Dafa yana Fadin"To banda abunki Nenne duk duniya wa nake dashi bayan ke..?kece uwata kece Ubana, kuma kece kakata..Dole nayi wasa dake..!
Mirmishi ta saki kafin taja Hancinsa tana Fadin"Nima bani da kowa sai kai..Kasani ko..?
Yana yar dariya yace"Sai kuma Sabuwar suruka in na kawo miki..!
Baki ta washe gabadaya tana Fadin"Aminu da gaske kake..?
Innalillahi a ina take..?
Ganin yadda ta Rude ne yasa yace mata"Nenne..Haba..Nace in na samo miki Suruka bawai na riga na samu bane..!
Duka taso Dirkamai ya Zura da gudu zuwa Bangaransa yana Dariya itama Dariyan take Lokaci Daya tana Fadin"Zaka zo ka sameni karyan Tsiya kake..!
A tsakiyar kayattacen Dakinsa ya Tsaya Kafafuwansa ya Nitse kan Tattausan Cafet din Daya malale Falon,Hannunsa Duka ya saka saman kansa yana Birkita gashin kan nasa meke Faruwa dashi..?
Yarinya karama taki barin Tunaninsa Tun sanda ya baro Dutse ko da rana Daya bai iya mantawa da ita ba a dukkan abunda yake yi Tunaninta da yanayinta da mganarta suna Gilma masa ya Dauka da gaske mganarta da Tsiwarta ke Burgesa sai dai yanzu da Lokaci ya tafi abun bai sauya ba.
Duk Yanmata hadaddun Da suke Rubibi akansa bai ga wacce ta kasa barin Tunaninsa ba Irin Amina Yazo Yola gida ne domin ya Huta na kwana Biyu ammh tunda yazo bai da aiki sai Tunani ko yaso ya kaucema abun ya kasa bai kara Tabbatar da ba iya Burgesa yarinyar take yi ba Harda wani abu Dayake jansa wanda bai gama Sanin koma Miye ba,sai da yazo gida.
Abu Daya ya sani zai Nemota kusa dashi Domin ya samu Tabbacin Burgesa take yi ko kuma wani abu ne Daban wanda baisani ba.
Da wannan Tunanin ya karisa samam makeken Gadon Dake dakin ya Dauko Farar wayarsa Kirar Samsumg.
Nura yaronsa ya Doka ma kira da Sanyin Safiya sai da ma ya Kira ya Duba Lokaci 10:00am na Safe tun motsa jikin Daya fita ya Dawo ya shiga Dakin Nenne suka gaisa yazo Falo ya zauna ya shiga Tunani Tunanin yarinya karama wacce Bai taba Tsamannin zai taba Haduwa da ita ba.
Sai da yayi ma Nura Kira Biyu sannan ya Daga kiran cikin Alamun barci yace"Oga Lafiya kuwa..?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Bansani ba..Dillah mallam ka wartsake..Wani aiki zan saka ka..!
Da sauri Nura yace"Afuwan Oga ina Sauraranka..!
Sai da ya gyara Tsayuwa kafin yace"Yarinyar da muka Hadu da ita kwanaki..Nake son kafin nan da zuwa Dare in ji komai akanta in nace komai ina Nufin komai..!
Cikin Mamaki Nura Dagachan bangaran yace"Wata yarinya kenan Oga..!?

Cikin Bacin rai yace"Bansan yawan Tambaya kasani Nura..!
Shuru yayi mai domin bai gane wata yarinya ba Yanmatan ai suna da yawa ganin yayi shuru yasa yace"Ina yarinyar nan da muka hadu da ita a Dutse..Oh..Ba Dutse ba yama sunan garin da mukaje Shooting din wakar nan Last Month..!
Nura yace"Munje Hadejiya da Gumel sai Jigawa wanne Daga ciki..?

Aminu yace"Inaga Gumel ne in da muka Tsaya Shago siyan kati har naci karo da wata yarinya wata baka mai ido mai mgana tana da Tsiwa haka..!
Baki Nura ya Hamgame yana jin Ogansa mamaki duk ya cikasa Cikin mamaki yace"Wannan yarinyar Oga..?
Karama ce fa..!
Da sauri yace"Ina Ruwanka..Do as i say..in bazakayi ba zan kira T..!
Da Sauri yace"Zan yi..Zan yi..!
Bai jira cewarsa ba ya Datse kiran yana Fadin"Nura yana da matsala...!
Haka ya fada kafin yayi Cilli da wayar saman gado ya taka cikin Sassarfa ya Shiga Tiolet din Dake Cikin Bedroom din.

Aminu Aliyu Buba Haifaffan garin Yola ne Bafullatani ne ta bangaran uwa dana Uba,mahaifinsa da Mahaifiyarsa hatsarin mota sukayi suka rasu tun yana da shekara Goma aduniya kuma shi kadai suka Haifa karamar kanwarsa tun kafin ayayeta Ciwon kyanda ya zama ajalinta.
Sai Rikonsa ya koma Hannun kakarsa wacce ta Haifi Mahaifiyarsa,mahaifiyarsa tana da Tarin kannen da yayyi wadanda suke Uba Daya tunda alokacin matan babansu Hudu Aisha itace Wacce suka Fito Ciki Daya ita da mahaifiyarsa kuma Allah ya Doramata Kaunar Aminu tun sanda aka Haifesa yana karamin sa yana da kyau da kwarjini irin nasu na yara.
Sadaukarwan da Aisha tayi ma Aminu mai girmane wanda baki bazai iya Fadi ba saboda shi tayi aure aure har Hudu baata zauna ba Saboda duk inda Tayi aure sai tace da Aminu xata tafi wanda yake kamar kani gareta yana da Jikin girma yasa ya kamota ita kuma gata Daman bata da tsawo.
Yawancin Rayuwarsu a Yola sukayi an gaji da Mgana an kyale Aisha Domin tace matukar ba zata zauna da Aminu ba sai dai ta Hakura da aure da Kuruciyarta ta zauna agida tana kula da Aminu ta zamemai uwa da uba da yar"uwa shima komai ya samu itace Dalilinsa ta samu Sunan Nenne sunan Daya Bita kowa dashi yake Kiranta.
Kakkaninshi suka taimakamai yayi karati har matakin Secondary Nenne iyakarta Diploma bata cigaba ba Lokacin shiga Jami"a sai Aminu ya nuna kano yake son tafiya ba gaddama aka kai mai Cuku cuku ya tafi Tunda bayan ma haka Mahaifinsa Alhaji Buba ya mutu ya barmai Tarin kaddarori gidaje da Filaye.
Zuwansa kano ne mafarin fara wakarsa ammh bai taba Tsammanin ba Haduwarsa da wani abokinsa Oscar shima mawaki ne,Dakinsu Daya shima anan Buk din yake karatu Cikin ikon Allah kuma yana da Rabo acikin Harka cikin Lokaci sunansa ya fita bai samu matsala da kowa ba sai Nenne itace ta nuna tafi son ya maida Hankali a karatu ammh itama sai da yaja Ra"ayinta ta amince.
Kafin ya gama Jami"a Sunansa ya fita waka ta karbesa kuma ya samu Alherai da ita ba adadi yanzu haka yana cikin mawakan da Yan Film suke Damawa dashi Tun shekaru Biyu da suka gabata yana kasuwancin shigo da Motoci da karafuna Da kudin gadon Daya gada sannan yana da Shagon sai da gwala gwalai anan garin kano.
Yayi gida anan kano nashi na kanshi yaso ya Dauko Nenne su dawo Alhaji Babba yahana yace ba inda zai kaita Shiyasa ya gina mata gida kato shi da ita Ya Daukota suna zaune tare daga ita sai yan aiki da ya"yan yan"uwan tunda Duka auran duk da tayi bata zauna ba ballatana ta Haihu Aminu ne komai nata shima itace Duka Duniyarsa babu abunda bai ijiye mata na jin Dadin Rayuwa ba Domin komai ya Zama a wannan Duniyar itace Kan gaba.
Yafi zama a kano saboda Harkokinsa,Sai kuma garuruwan da suke zuwa in zasu shooting din waka Aminu baya shaye shaye kuma baya Harkan mata sai abunda ba"a rasa ba Matashi ne dan kimamin shekara 30 aduniya ne mai ji da kuruciya da kudi Yanmata sun na kawo masa hari ammh bai taba maida kai ba Nenne ma ta matsamai yayi aure ita da Alhaji Babba ammh suma baya maida kai sai yace Lokaci ne bai yi ba Yana so yayi aure saboda Farincikin Nenne sai dai bai sa nan kusa ba Domin bai Taba jin wata mace aransa ba yasan suna sonshi ne saboda suna da kuma Kudi ammh Haduwarsa da Amina komai ya Sauya yasani yarinya ce ammh kuma Rayuwarta Cikin Burgewa Bata da damuwar komai ashekarunta kudi ko suna basu da Muhimmanci awajenta

Har ya fito wanka Tunanin bai bar kansa ba yana son jin komai akanta Saboda yaga ta ina zai fara yana son ya kara ganinta nan kusa komawa Gumel ya kamasa Duk da wannan ne Lokaci na farko daya taba zuwa garin
Agurguje ya shirya cikin manyan kaya cikin gari zai shiga ya gaida Alhaji Babba kuma in ya je da kananun kaya Daga shi har Hajja sai sun tasomai Shiyasa yayi shigar Farar shadda riga da wando da Hula.
Daga Dakinsa kai Tsaye Dakin Nenne ya Nufa ya isketa tana gyara adon wata Sarkarta,bataji ma shigowarsa ba sai Hannunsa dataji ya saka ya karbi Sarkan yana Fadin"muga Abun da Nenneta take yi da bataji shigowata ba..!
Sai Lokacon ta Dago tana kallonsa Cikin Farimciki tace"Masha Allah..Ka ganka kuwa..?kamar bakai ba..Hala gidan Alhaji babba zaka je ko..?
Kai ya gyada mata yana Kokarin gyara mata sarkar lokaci Daya yana Fadin'Kina son sarkan nan Nenne..!
Hannu ta mikamai Tana Fadin"Sosai..Bani kayana kagani sakashi zan yi..!
Bai musa ba ya zagaya ta bayanta ya saka mata yana Fadin"Ko zaki shirya muje tare ne..?
Kai ta girgiza kafin tace"Ina da Bakuwa..Hajiya Iklima ta kirani tacemin zata zo kada mu fita tazo bata sameni ba..!
Dan baki ya tabe kafin yace"Ok..Bari na wuce ni..Sai an juma zan dawo domin zanshiga cikin gari mu gaisa da Friends dina mun kwana Biyu bamu Hadu ba..!
Kai ta gyadamai kafin tace"Shikenan kada kayi Dare..Sannan ina Fatan ka Karya..?
Da sauri ya gyada mata kai Saboda baya son ta takuramai kuma bayajin cin komai Dukawa yayi ya Sumbaci kuncinta kafin ya Fice da Sauri Ta Bisa da gudu tana Fadin"Aminu zan ci maka mutumci da Dabi"ar nan fa..!
Tana jinsa yana Dariya yana Fadin"Haba Nenne watarana fa Madina zamu koma Dole mu koyi gaisuwan Larabawa..!
Mirmishi take ita kadai Burinta ya gama cika Saura abu Daya Aminu ya samu matar aure ta gari taga ya"yansa shine Babban Muradinta.
Ranar Wuni yayi zirga Zirga achan gidan kakanin nashi ma Chaa akayi mai kan mganar auran kansa Kadai yake shafawa yana fadin Lokaci ne bai yi ba ko abokansa na nan Yola suna ta mai tsiya domin su kam daga masu yara sai masu kokarin Karin ta Biyu.
Bai shigo gidan ba sai bayan Isha"i shima sai da Nenne ta kirasa haka take Koda ya girma tana Tsaye kan Tarbiyasa ko yana kano Dare nayi zata Kira taji inda yake tana tsoron Gurbacewar Tarbiyan Matasan zamani akan Aminunta
Tare sukayi Dinner shi da ita da Wasu yan Biyu Hassana da Husaina ya"yan kawartace Hajiya Iklima ta bar mata su kwana Biyu tunda suna Hutun makaranta Daman suna zuwa Aminu ya saba da yaran suna da shiga rai su suka Daukemai Hankali ya manta da Batun kiran Nura sai da yaga Kiransa wajeb karfe Tara na Dare sannan ya Tuna.
Sabewa yayi ya koma Dakinsa baya so Nenne ta Fahimci komai yasanta yasan Zuciyarta yanzu sai ta Girmama abun Fiye da yadda yayi tsammani kiran ya katse sai kara kiran Nuran yayi yana Dagawa yace"Nura kada ka sanar dani sabanin abunda na saka ka..!
Ajiyar zuciya Nura ya sauke kafin yace"Tun bayan da muka gama waya Na shirya na tafi Gumel Oga..Ban sha wahala sosai ba Saboda gidansu yarinya ba Boyayyen gida bane..Gida ne da ko kai na Fadama sunan zaka san sunan..!
Cikin Mamaki Aminu yace"Wani suna kenan..?
Kai Tsaye Nura yace"yarinyar tana Daga cikin Ahalin babban Malamin nan Sheick Yunus Abdulrahaman bazanga..!
Aminu yace"Sheik Yunus Abdurrahaman Bazanga..?
Nura ya gyada kai kamar yana ganinsa kafin yace"Eh shi Oga...!
Aminu ya jinjina kai ai ba wanda baisan Mallam bazanga ba in baka sanshi a Fuska ido da ido ba kasanshi a Talabijin ko ajaridu ko kuma awajen wani Taro na Malaman sunna.
Cikin Kosawa yace"Ina jinka..yarsa ce ko Jikarsa..?

Nura yace"Shine bansani ba..Ban samu Cikakken bayanin Dangantar Mahaifinta da shi Mallam bazanga ba..Sai dai an bani Tabbacin kamar D'a yake garesa gidajensu suna jikin juna ne nan bayan inda muka hadu da yarinyar sannan Mahaifinta ne kan Duka kasuwancin Mallam din..Sannan iyalansu a Hade suke komai Tare suke Hatta Ragamar aurar dasu Mallam din ke gudanar da komai wasu suna Tunanin kanin sa ne wasu kuma suna Tunanin Shine Babbar D'ansa..!
Aminu yace"Naji wannan ita yarinyar fa..?me ka sani akanta..?

Nura yace"sunanta Amina Sa"idu Yarinya ce karama Tana aji Dayan babban Sakandiri yanzu a makaranta tana zuwa Hadda da Islamiya,Dokar gidan gaskiya yadda na samu Labari gidan Tarbiya ne basa fita Daga makaranta sai gida sannan basa Tadi da Samari ko auransu ana Tunanin auran Hadi ne sannan iyakarsu Sakandiri ake aurar dasu, su goma sha Daya ne agidansu itace Karama awajen Mahaifiyarta sannan matan babanta biyu..!
Aminu ya sauke Numfashi kafin yace"Yanzu ba yadda zan yi na kara ganinta..?
Nura yace"Ba mafita. domin ko makaramta Mota ke kai su ya dawo dasu..Mai bani Labarin ma yayi matukar mamakin Da nace masa mun ganta ya Tabbatrmin da Ahalin gida basa zuwa ko"ina..!
Aminu ya sauke Numfashi kafin yace"Ya zama Dole na Hadu da ita..Gobe zan shigo kano..ka shirya zamu koma Gumel..!

Daga haka ya Datse kiran ya bar Nura bakinsa Bude meke Damun AA.buba ne..?
Wannam yarinya zai kare mawa duk matsayinsa..?Tsaki yaja acikin ransa yana kunkunin yadda Aminun yasa shi zuwa gumel ayau din nan Allah yasa Bawani sha wahala ba Tunda ba Boyayyen gida bane, shagon da suka fara haduwa ya fara isa Daya tambayesa ya tabbatarmai shima bai santa ba wani ne a kusa Dayaji Mganar da sunanta da yanayinta yace ya santa kanwar abokin kaninsa ne Shamsu ya"yan gidan Bazanga ne a bakinsa ya samu Duka Labaran Daya zo ya Fesa ma Aminu dawowarsa kenan ko Hutawa bai yi ba..

Indai ko Oga son yarinyar yake ya kwafsa yar yarinya yar cikinsa bakomai Cikinta sai rashin kunya.
Aminu kuwa yana ji aransa ya zama Dole ya koma ya sake ganin Amina Saibyanzu ya kara tabbatar ma kansa bata sanshi ba gidan Malamai ba"a wani samun sakewa ballatana Har taji waka ko tasab sunanshi.
Yana ji ajikinsa kamar akwai wani abu mai girma Tsakaninsa da yarinyar bazai gane haka ba sai yaje ya kara ganinta ya kara tabbatar da abunda yake ji akanta.

********

*BAYAN SATI DAYA..!*
Gumel...!

"Wlh in na yarda Allah Tsinan..Kin manta jiya ma da muka dawo agidanku na sauka kenan yau gidannmu zaki sauka yarinya..!

Amina ta fada tana Faman Jan hijabin Hanne Hamida na gefe tana musu Dariya dukkansu kayan makaranta ne ajikinsu da Uban jakunkuna Hanne Fadi take"Sakeni Amina..Nace ne bazani ba..?
Amina tace"In sake ki ki shige gida..?naki wayon..?Hamida karbe jakarta..
Hamida ta warce Jakar makarantar Hanne Tana Dariya ya Zeenatu tazo shigewa gida da Katuwar jakarta Sabe a Hannu ta bisu da kallo kafin ta Tabe baki tana Fadin"Miye haka..?
Kudai bazaku bar yarinta ba..Kuna girma kullum kuna cin kasa..!
Baki Amina Ta tura batayi mgana ba Hamida ce tace"Ba ruwana Amina ce..!
Karamin Tsaki taja ta shige gida Abunta ya Abida ce Daga nesa ta hangosu kusan itace Karshen sauka Daga Motar,yau a waje idi ya saukesu motar ba Lafiya Dakyar ta kawo su gida gareji yace zai kaita shiyasa ya Saukesu anan waje su Sa"adatu tuni sun shige gida abunsu su Ya Akilu ne ke wajen jikin Motan.
Abida ta kalli Zubairu tana Fadin"Kalli yaran chan..?
Akilu yace"Bari na Tarkatasu su shige gida..!
Yafada yana Daukan Sanda ya fara Tafiya yana Fadin"Ya shamsu..Eh gasu nan suna wasan banza a waje..!
Kamar sun ga Shamsu da gaske suka Zura aguje su kuma suka kwashe musu Dadariya Abida ta shige get din gidansu ita da Zubairu Akilu yabi bayansu,su Amina suka Tsaya suna maida Numfashi Amina tace"Wlh Ya Akilun nan mugun dan saka ido ne..!
Hamida tace"So yake ya zama makwafin ya shamsu tunda shi ya gama..!
Akwai son yayi Displine..!
Amina tace"Barni dashi Watarana zamu yi mganinsa ne..!
Hanne tace"Badai kararara zaki sakamai ba irin na ya Shamsu..!?

Atare suka Saka Dariya Tuna abunda ya Faru wanchan satin Amina ta samo kaikayi a makarantar Islamiyansu taji su mariya na Fadin abun na saka kaikayi ta tsinko ta Dinga tusama Mutane Cikin Hijabi a ajinsu suna ta Soshe soshe,Shine ta sakama Shamsu Saboda ya Rankwashesu ita da Hanne basu gama Rubutu da wuri ba har aka tashi sun bata musu Lokaci shine suka Fakaicesa da Daddare Amina taja Hanne sukaje suka Watsamai akan Katifarsa da Safe suna Daki sukaji Hajiya na Fadin shamsu wani abu ya Sameshi jiya da Daddare kwana yayi susa da wanka sai da mallam ya dinga mai addu"a.
Sai da Amina ta kwanta Saboda Dariya Hamida ma bata sani ba Labari Hanne ta bata.
Amina na Dariya tace"Ai mallam Auwal ya saka an sare Ganyen mai kaikayin..!
Hamida tace"Ina Fatan kada ya Shamsu yaji Wlh sai na Lahira yafiki jin Dadin Amina..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"To in ma yaji wlh ke kika fada!
Hamida tace"Ni kuma..?
Amina ta Bude baki zatayi mgana keman Idonta ya Fada kansa yana Tsaye Daga Kofar gidansu bai yadda sun kariso da Motarsu ba Tana baya Nura ke ciki yana kallon Ikon Allah
Sun fi awa Daya suna wajen nan agaban idonsu Motan makaranta tazo ta Sauke su Amina suka Firfito.
Ko alama bata manta dashi ba gani su Hamida sukayi hankalinta ya koma Chan gabansu yasa suka juya suna kallonsa yana Tsaye sanye Cikin Riga da wamdo bakake sai ya Dora Farar Jaket ya saka F.cap ya Rufe Fuskarsa sai dai ya Janyeta kadan.
Amina cikin mamaki tace"Laaa..Kai ne..!?

Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Nine..Amina kina Burgeni..!
Fadin haka da yayi yasa ta washe baki ta fara takawa gabansa shima ya tako suka Tsaya daidai kofar gidansu Amina Hamida da Hanne suka saki baki suna kallonsu.
Amina Hannu ta Fara tafawa tana Fadin"Kai..Daman ina neman ka..?Ashe kai mawaki ne bansani ba..?
Ido ya zaro yana kallonta kafin yace"A ina kikaji..!?

Kai Tsaye Amina tace"A wayar wata yar ajinmu mana..naji suna mgana suka ambaci mai irin sunanka nace anunamin Hotonka kuma Wlh kai ne..Yauwa daman ina ta so na Fada ma su hanne don Allah ba kai kace ina Burgeka ba..?
Kallonta kawai yake yi yanjin wani Farinciki sai da ya ganta ya kara ganin yarintarta tana mgana ko Tsayawa ta kasa yi.
Kai ya gyada mata yana kallonta juyawa tayi ta riko hannun Hanne da Hamida ta kawo gabanshi tana Fadin"Yauwa don Allah sake fada musu..Kila su yarda..!
Tafada tana wani juya ido Dariya abun ya basa cikin gyara Tsayuwarsa yace"Amina Kina Burgenii..Wani ya Taba Fada miki u are so Beautifull..!
Amina taji wani Sanyi acikin ranta Cikin Alhafari ta kalli su Hanne da mamaki ya sa suka kasa mgana tace"Kun ji ko..?ai in na Fada muku sai kuce Karya nake..Nima fa ina Burge mutane
Kunga wannan babban mawaki ne yana tare dasu Umar.m sharif..!
Dasu Ani nihu kasan su ko kilama abokan ka ne..?
Take Fada tana kallonsa Cikin Dariyarta Kai ya gyada mata Cikin Dariyarta yace"Ai Ani nuhu abokina ne..yama ce yana gaisheki..!
Ido ta zaro kafin tace"Da gaske.?
Ya sanni ne..?
Yana Danne Dariyansa yace"Sosai ai yasan Amina..Amina ta Gumel abakin Aminu..!
Amina ta Dafe kirji Murna Duk ya Cikata Hanne taja gefen Hijabinta tana Fadin"AMINA kada wani ya fito fa ya ganmu fa.?
Hamida kuwa uwar tsoro sai waige take yi kafin tace"Amina kin sanshi ne..?
Hijabinta ta Fizge kafin tace"Dillah..ku na sanshi fa..Shagon chan muka hadu kwanaki da mamanmu ta aikeni..!
Har yace ina Burgesa ko..?
Tafada tana wani juya ido Kai ya gyada yana kallonsu Hamida kafin yace"Sosaima
gaskiya kuma Laifin ku ne da baku taba Fada mata ita din abar Burgewa bace!
Amina ta washe baki kafin tace"Kun ji ko..?yauwa gayamusu..Ni da suke cemin ina naga abun burgewa
Sai ma na gundiri mutane da Halina..!
Tafada tana bata Fuska da Sauri yace"Kada ki damu..Ni kina Burgeni..!
Hamida taga Amina ta Zake da yawa hannunta ta Fincika tana Fadin"Amina kada wani ya ganmu fa..?
Hanne tace"Bawan Allah don Allah ka tafi jidalin Amina ne kawai..In wani cikin yan gidanmu ya ganmu Dakai yau mun shiga uku..!
Amina ta kwace hanmunta tana Fadin"Dillah sai me..?iyaka duka ne kuma baya kisa..!
Hanne tace"Baba Mallam kinsan baya nan bamu da maceci sai Allah Amina..!
Wa kika taba ganin ya tsaya da wani..?ko su ya Abida kin taba gani..?
Amina ki shiga Hankalinki..!
Sai kuma tayi shuru ta tsaya tana kallon Hanne kafin tace"Kuma fa hakane..muje..bawan Allah sai an juma..Yauwa don Allah ka kara

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment