Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya D'anmalam din bazan iya Tuna kamaninsa ba gaskiya..!
Hanne tace"Kinsan bai cika yawan zuwa ba..?in yazo ma shi kadai kwana Biyu yake ya koma in kuma Zai zo da ita sai karshen shekara kuma suna Gidansu Dake nan Kano Road sai dai in sunzo gaida su Hajiya kuma Har gidanku yana shiga gaida Yaya Hajiya tace Dan Dakinta ne sosai..!
Amina ta mike itama tana Fadin"Ke ni ban taba ganinsa ba..Kina da Hotonsa .?
Hanne tayi Dariya tana Fadin"Sha Kurumimki naji Hajiya na Fadin nan da wata Daya suna na nan zuwa Saboda Mganar auran su ya Aisha..!
Amina ta kwalalo ido kafin tace"Kice muna da shan Biki..!
Hanne tace"Wlh kuma har dasu ya Sadiya ma za"a Hada fa...kilama Har dasu Ya Zeenatu..!
Amina tayi wata Dariya kafin tace"Allah yasa hardasu..su tafi su barmana Gidan dagani sai Hamida muci uban juna..!
Dariya suka saka Gabadaya Harta Tafawa suna cigaba da Hiransu Salla sukayi Tunda suna da alwala Sai da suka idar kana suka fita Falo ba kowa suna Falon Baba Malam Kichen din Hajiya Hanne ta shigo ta Dibo musu Doya da miyar Stew nan falo suka Fito suna ci suna Hira da Dariya Daga ganinsu kasan kaunar da suke ma juna Daga Allah ne.
Sai wajen 9:30am na Dare su Ya Aisha da Ya Abida suka shigo Ya Aisha Daki ta wuce ita bata cika mgana ba Ya Abida ce ta kallesu tana Fadin"Meyasa baku je Dinner ba..!
Amina ce tace"Mun yi namu mu kadai..!
Kai ta kada kafin tace"Sannu Shafaffu da mai..To Baba na kiranku..!
Amina Rada take ma Hanne tana Fadin"Mijin Ya Abida zai sha Gulma..!
Hanne na Matse Dariyanta Ya Abida ta Zaro ido tana Fadin"Amina me kike cemata akunne gulmata ko..?
Da Sauri Amina tace"Labarin wata yarinya mai Bala"in saka ido nake bata..yar ajinmu a islamiya..ko Hanne..?
Hanne ta Daga kai da Sauri Abida Wucewa tayi tana Fadin"Sai na Daki bakin yarinya yanzu nan..!
Amina ta Rakata da Daga Lefe tana Shigewa suka kyakyalce da Dariya
Saida suka gama Hanne ta kwashe komai takai Kitchen Amina tace"Dauko Hijabina na tafi gida Hanne..!
Hanne tace"Kiran baban fa..?
Tace"In mun fito sai na shige gida..!
Hanne tace"Nazata nan zaki kwana..!
Kafada Amina ta Daga kafin tace"Anki din..Ina fa Kirge nice na kwana Na karshe..Malama kece fa da kwana..!
Hanne tace"Dillah zan kwana nima gobe..!
Amina tace"Yauwa sai na baki ma Labarin wannan litaffin..!
Da Sauri Hanne ta Danne bakinta tana Nuna mata Dakin dasu Ya Abida suke Amina Tayi Dariya Kafin tace"Sai me..?Allah yasa ma suji..!
Hanne dai wucewa tayi ta barta Tasan wacece Amina bata da tsoro komai zai Faru sai da ya faru ita zata saka a uku.
Hijabinta ta Dauko mata itama ta Dauko nata tana Fadin"Muje na Rakaki..!
Fita sukayi Daga Dakin suna Tafe suna Hira Amina na Zagin malamar hausansu har tana kwaikwayon mganarta Dukkansu Jss3 suke sai dai Amina Ita da Sa"adatu suna A ne yayinda Hamida da Hanne ke ajin B.
Suna tafe har Shashen Baba Maallan Amina tasan inda suka zo yasa ta Bude baki Daga Kofar Falon ta kwarara Sallama.
Hajiya Dake Cikin Falon gefen Baba Mallam Dake zaune kan kujera yana Duba wani Littafi tace"Ga Mamar taka nan ta iso..Kaji Doguwar sallama kamar ta Kirki..!
Tafada Cikin Zolaya yana Duken yace"Ta kirkin ce mana Zainabu...Mamana Harda yarinta ajikinta da ta kara girma ta mallaki Hankalinta sai dai Labari..!
Kai kawai ta Kada tana Hangen abunda ba Haka ba kan Aminar ita ta amsa Sallamar ta Amina Hanne na Shirin Shiga ta riketa tana Fadin"mu shigo baba cikin harshen larabci
Shi kanshi sai da ya Murmusa ya Dago Fuskarsa Daya cika da Farin gemu Cikin Dattakonsa yace"Na"am...!
Baisan meyasa ba Ko Muryan yarinya yaji sai yaji wani Dadi yana mata kauna wanda ko cikin ya"yansa sai an Tona Amina haka Allah yayi ta mai Farinjini ne Malam yana sonta Saboda Allah da kwazonta Duk da take bata maida hankali Kokari gareta yana ganin makamceceniyar kwakwalwarta Data D'an malam awajensa da itace kadai yake Dogon Mgana da Larabci bata kakare ba Tana Jin Labarci Fiye da yadda kowa ke Tunani kuma Bayan Baba Malam ko Baba Sa"idu baisan wannan baiwar nata ba..
Sannan ko makaranta sun sani tana da Jawo Jidali ammh itace Over roll acikin ajinsu har mamaki ake yi masu Hassada da ita na Fadin Cuta akeyi Amina jidalinta baya barinta gane Karatu shiyasa Sa"adatu ke Kishi da ita matuka basa Shiri ko a islamiya da hadda Itace Zakka kamar yadda ta Fita Zakka acikin gida Daga waje ba,sannan Amina Zakka ce sai kowa Tunani yake sa"a take ci Saboda ba"a Taba ganin tabama karatu Muhimmanci ba nan kuwa basu sani ba Tana da baiwa sau Daya zata ga Abu Ta kuma karantshi ta gane shi kuma ya Zauna Bisa kanta Har Abada.








_Naji Dadin yadda kuka karbi Labarin nan kamar yadda kuka saba karban Duka Labaraina Naji dadi nagode matuka Allah ya bar zumunci nayi alkawarin bazan baku kunya ba_






*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty) Alherin Allah ya kai miki adukkan inda kike*

_Intelligent writer's asso_


*🅿️03*


Kai tsaye suka shiga Kayattacen Falon Dauke da wata sabuwar Sallama,Suna Shiga Kamshin Turaran da Duk wanda yasan Baba malam yasan wannan kamshinsa ne wani Turare ne mai kamshi mai Sanya natsuwa Turaren mai Tsada ne dan Kasar Saudi mai suna Arab Saboda yawan amfani da Turaran yasa Duk inda Malan ke yawan zama kamshin ya kama wajen,Kamar yadda Kamshin ya kama Falon Dayake ma mallakinsa.
Kayattacen Falo ne wanda yaji kayan More Rayuwa na alatu Falon babba ne mai Dauke da Royal Chair da Tattausan Cafet na kamfanin Italiayan.
Sannan Daga gefe chan wata Kofa ce data fita Haraban gidan akwai wani Falo shi na ganawa da bakin Baba Mallam ne,Sannan Daga cikin Falon akwai Kofifin Bedroom Guda Biyu sai Daga shashen Yammah akwai wani Cabet na glass mai girma da Fadi kafe ajikin Bango wanda yake Shake da Littafan addini Kala kala nau"i nau"i Dabam Dabam Sannan Daga gefensa wani katon Tebur ne mai Dauke shima Da Tarin Littafai ba masaka Tsinke,sai Kujera Guda Daya wajen zaman mallam ne in zai yi Nazarin wani Littafi kamar yadda ya saba koda yaushe.
Sai katon Talabijin mai kama da Kamar Mutum yana waje ne saboda Girmansa,Sunna Tv ne ke tashi Acikinta Dauke da Muryan Sheik Haruna Kabir Gombe yana kwararo Wa"azi Cikin Barkwancinsa.
Cikin Lokaci kadan Amina ta gama Nazarin Falon Kafin idanuwanta su sauka kan Mafi Daraja a wajenta,Wanda shi kadai ne bata iya kallonsa Kai Tsaye shi kadai take shakka Da bata iya Hada ido dashi shi kadai ne yasan Wasu abubuwa Game da ita Saboda yana janta ajiki Wanda ko Aba dinsu bai kaisa saninta ba.
Cikin Farimciki gabadaya Fararan Hakoranta suna Waje ne ita ce kan Gaba Hanne na binta abaya zuwa Inda Baba malam ke zaune Saman Daya Daga Cikin Kujerun Falon Hajiya Babba na gefensa Zaune..
Kamar yadda take Farimciki da ganinsa haka shima ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa mai Dauke da Farin gashi Daya Lullube gemunsa Dattijo ne mai Kima mai Daraja mai Dattako masanin Addinin Musulunci Dana Zamani SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA kenan Shehin Malami na bangaran Addinin Musulunci da na Sunna Gabadaya ba iya garin Gumel ba Kasa gabaki Daya susan da zamansa yana da kyakyawan alaqa wajen Sauran Malamai sannan kowa na girmamasa Malami ne mai Tsoron Allah da Sanin ya kamata ba Malamin Siyasa ba kuma ba mai ci da addini ba ba ga Jama"ar gari ba Hatta ga iyalan Dake Zagaye dasu sun san karamci da Dattakon Sheik Yunus bazanga.
A kama baya kama da duka ya"yansa Domin shi Fari ne sannan yana da Cikar Fuska da zati Duka ya"yansa sun fi kama da matansa Daya Dayane Cikin Jerin ya"yansa ke kama dashi Shuiyasa har acikin Ransa UMAR NA dabam ne..
Akallah a shekaru bazai gaza 78 aduniya ko ya D'ara ma sai dai yanayin Hutu da jin dadi sun boye shekarunsa yana Sanye da Jallabiya Mai ruwan Madara ya Cire Rawanin kansa,Farin gashin kansa da Rabi da kwata ya koma Fari sai kyali kyalin baki,Wanda Saboda Cire Rawaninsa kansa ya bayyana Fuskarsa Sanye da wani Sirrin Farin Gilashi mai karamai karfin gani Jaridar Rariya ce ta Ranar a Hannunta yana karantawa sanda su Amina sukayi Sallama.
Tun kafin ta karisa Tace Cikin Muryanta"Baba...!
Yana kokarin gyara zaman Gilashinsa yacce"Mamana..Sai yau nake ganinki..?
Yafada yana kallonta Cike da wata Kauna da Allah kadai yasan adadinta
Daidai kafafunsa ta zauna tana Fadin"Baba nazo shekaran jiya kana da baki Hajiya bata fada maka ba..?
Tafada tana kallon Hajiya datayi Saurin Cewa"Na fadamai fa Maamah..Mallam na Fadamaka zuwanta ko..?
Yana Dariya ya dafa kanta yana Fadin"Tafadamin Tsokanarki nake Yanzu Sa"idu ya tashi nake Bidarki sai Hajiya tacemin kina ma Cikin gidan nan nace shikenan Tunda Wajen hannatu kikazo ba wajena ba .!.
Yafada Cikin Mirmishinsa na koda yaushe,Amina ta rike baki Tana yar Dariya Hanne Dake gefenta ta Duka Tana gaida Baba mallam ya amsa yana kallonta kafin yace"Ke kika Rikemin Mamana ko Hannatu..?
Hanne kanta na kasa tace"Baba nima yau ba zuwa na bane..Laifi tayi Ya Jafar yace zai daketa sai ta gudo wajena..!
Baba Mallam yace"Laifi..?ba na Hana su Jafaru tabamin Uwata ba..?na fada musu komai zatayi duka baya gyara Tarbiya Nasiha ne kawai mafita ballatana Duka Duka Mamana nawa take..?nan gaba sai kun yi mamakinta..!
Yafada yana kallon Amina da Ta dan Daga idanuwanta Sama kafin tace"Baba bafa Laifi nayi ba..Gidan kawata naje ta bani kudina..Baba Ranta fa tayi fa tace yau zata bani a makaranta kuma taki zuwa makaranta yau fa Baba ina Laifi Domin na Bita na amso kudina..!
Baba Mallam na yar Dariya yace"Baki da Laifi Mamana..Daman ai kyan alkwari Cikawa..!
Amina tace"Yauwa Baba..nasan Dama kai ne kadai zaka Fahimceni..!
Hajiya na Dariya tace"Daman ai Mallam baya kware miki baya..!
Malam yace"Wa kika Taba ganin ya kware ma Uwarsa baya Zainabu..?duk dan kwarai yana neman albarka ne..!
Hajiya Dariya kadai tayi batayi mgana ba Amina ce ta Zunguri Hanne Tana Fadin"Tashi muje..!
Tafada a Hankali Baba Malam Dake kallinsu tace"Ina zaku..?
Hanne tace"Gida zataje Baba..Zan Rakata ne..!
Agogon Dake manne adakin ya Daga ido ya kallah Goma Saura Kadan kafin ya Dawo da Kallonsa kan su yana Fadin"Dare yayi Mamana yau ba ki kwanciyarki wajen Hannatun taki..!
Amina tace"Baba itafa ke da kwana agidanmu ni na kwana na karshe ko Hajiya..?
Hajiya na Dariya tace"Kwarai kasan abun nasu Team team ne..!
Baba maallam ya gyada kai yana Fadin"To..to hakane..To ke Hanne yanzu Zagayowarki ne kenan..?
Hanne tace"Sai gobe in mun Dawo daga Hadda zan kwana Baba..!
Hajiya ya kallah yana Fadin"Yayi kyau..Hajiya bani Wayar nan Dake kusa Dake..!
Ba musu ta mikamai Wata Lafiyayyiyar waya Fara Samsumg ce,Ya karba yana fadin"ku zauna bari na Kira shamsu yazo ya rakaki Amina Dare yayi..!
Alokacin da aka ambaci Shamsu sai da suka Kalli Juna ita da Hanne Amina ta Kada ido aranta tace"Mugu.com kenan..!
Ammh Afili bazata iya mgana ba, bata ma Baba Malam gaddama Hanne kuwa ai tasan Halin ya Shamsu Duk gidanan yafi kowa mugunta Da Dukan Mutane ko bakamai komai ba.
Baba Malam yana Kokarin Kiran Shamsu Kira ya shigo wayarsa Cikin Mamaki ya kalli Hajiya yana Fadin"Sa"idu ke kirana Hajiya..!
Sunan da aka ambata yasa Amina ta Dago tana kallon Baba Malam
Hajiya kuma cewa Tayi"Kila mamah ake Cigiya..!
Ba musu ya Dauka da Cikakkiyar Sallamarsa kamar ko yaushe Sa"idu Daga chan bangaran yana Zaune afalonsa gefensa Mamammu ce Cikin Girmamawa yace"Allah yasa ban katse maka wani abu ba Baba..!
Baba Malam yace"A"a Sa"idu ina fatan Dai Lafiya..?naga baka Dade da fita ba..!
Aba ya Dukar dakai kamar yana Gaban Malam yace"Daman Maman yara nan ne tasa na kira wai ko Amina tazo nan gidan..!
Mallam yayi Mirmishi Kafin yace"Gata ma kusa dani Sa"idu..Ammh yansu zan saka Shamsu zai Rakota..!
Da Sauri yace"Tayi kwanciyarta nan mana Baba..!
Baba Malam yace"Tace ba ita ke da kwana ba Hannatu ce..Kasan mamar tawa yar Ra"ayi ce..!
Aba yar Dariya kawai yayi domin ya Daina mamakin Kaunar Dake Tsakanin Baba Malam da Amina abaya ya Dauka Domin tana da Sunan Mahafiyarsa ne sai Daga baya ya Gane Kaunace kawai Daga Allah..
Sallama sukayi da juna yana Datse Kiran ya Dago yana kallon Mamanmu Dake gefensa Cikin Basarwa yace"Kin ji tana chan yanzu..Shamsu zai Rakota..!
Daga haka ya cigaba da cin Abincinsa Domin Alkawari yayi ya Daina bari Lamarin Amina na Tadamai Hankali yanzu ma Mamansu ce ta matsa sai ya Kira Malam din yaji ko ta na chan
Tun bayan shigowarsa Duka yaran sun zo sun gaishesa banda Amina yasan bata gidan in tana nan itama Zatazo ta gaishesa.
Mamanmu Tayi Mirmishi kafin tace"Daman Nasam ai bata wuce Gidan Malam din..Nace ka Kira ne Saboda na Kore Bacin ran Dake Kan Fuskarka kan Amina din..!
Bai ce komai ba har ta Fidda rai da zai kara mgana sai chan taji yace"Uhm..Nifa ban Damu ba kawai dai naga ya kamata ko bata Fadama kowa zata fita ba..Ke mai karenta baki isa ta Fadamiki ga ta zuwa ba?..!ko don ita ta saba yin gaban kanta da yin abunda taga Dama..!
Mamanmu ta Bude zatayi mgana ya Daga mata Hannu yana Fadin"Ki kyaleni don Allah..Yau na dawo agajiyae bana son sabon bacin rai..!
Yadda ya fada din tasan Har ransa haka yake nufin yasa ta Hadiye mganarta ta koma gefe tana Sauke Numfashi.
Shi kuma bai kara kallon Inda take ba ya Cigaba da cin Abincinsa Kamar acikin Ransa bai da Damuwa nan kuwa Tsoro ne da Fargaban wani abu kuma man Gaba Amina zata jawomai.

Achan gidan Baba Malam kuwa Shamsu ya Kira yace yazo yana son ganinsa ba Dadewa sai ga Matashin Saurayin ya shigo,Dogo ne mai Kaurin Jiki Kadan yana da Haske ba sosai ba Yana Shigowa ya Duka ya gaida Malam da Hajiya Suka amsa mai Cikin Sakewa Hanne ta gaisheshi ya amsa yana Hararanta Tunda ya gansu yasan Su suka saka aka tadosa Amina kuwa kanta na gefe aranta tace"Yasin bazan gaishe shi ba..!
Tafada Har tana Murguda baki Baba Mallam ya kalli Shamsu yana Fadin"Me kake yi sanda na Kira ka Alarammah..!?
Daman haka yake kiransa Saboda Mahaddacin Qur"ani ne sosai.
Kansa na kasa tace"Ina k'arama zubairu da Akilu karatu ne Baba..!
Dan Mirmishi yayi kafin yace"Dakyau Alarammah..To kafin ka koma ka cigaba da Biya musu karatun Ina so ka Raka Mamana gida sai ka Tabbatar da ta shiga gida sannan ka dawo..!
Kai ya gyada aransa yana fadin sai ya Daki bakin yarinyar nan ko gaisheshi batayi ba sannan ga Jiranta datasaka yau sukayi a makaranta tatafi gantalinta ga kuma Tasosa da ta sa akayi Duk sai ya famshe ajikinta.
Baba Malam ganin yayi shuru bai ce komai ba yasa yace"Kana jina ko..?
Kai ya jinjina yana Fadin"Naji Baba..!
Amina ya kallah yana Fadin"Tashi kuje Mamana..Sai da safe kenan ko..?
Mikewa tayi tana Gyara Hijabin Jikinta Tana Fadin"Baba sai da safe..Hajiya sai gobe..!
Tare suka amsa mata da Fatan Allah ya kaimu Baba Malam ya kalli Hanne yana Fadin"Rakata mana Hannatu..!
Tanajin Haka ta Mike suka Fice Shamsu ya Rigasu gaba suna Fitowa suka gansa yana Tsaye yana Jiransu Fuskarsa ta Hade kamar bai taba Dariya ba.
Hanne ta makale bayan Amina tana Fadin"Ya shamsu..Wlh Fuskarsa ba Rahma..!
Amina tace"Dillah sai me..?mala"ikan Mutuwa ne..!
Kwas...!
Bata sani ba kawai sai ji tayi wani Rankwashi ya Ratsa kanta Bata gama Dawo Hayyacinta ba taji an ja kunnenta an murde Cikin muryansa yace"Wato ba mala"ikan mutuwa bane ko..?zaki gane baki da wayau..!
Yafada yana kara sakar mata rankwashi kanta da Dafe da hannu Daya tana Fadin"Occh..Ya shamsu kunni na..?
Da bakinsa yace"Shiii..Yana kallon Falon Baba Malam,Hanne ta fara baya Baya tana Murza ido Amina ya Sakarma Kunni yana Fadin"Oya wuce muce..Wannan na Farkon na Jiran da kika sa mukayi yau a School ne..Akwai na Kin gaisheni da kuma Tasoni da kika Saka Baba Malam yayi..Wuce muje..!
Yafada yana Tura kanta gaba Ta wuce tana Dafa kanta Cikin kunkuni take Fadin"Allah ya isa na mugu..!
Shamsu da karfin ji kamar maciji Kallonta yayi yana Fadin"Me naji kince Allah ya isa Amina..?
Da Sauri tace"A"ah fa..Cewa nayi Allah yayi maka albarka..!
Mirmishi yayi yasan Allah ya isa tamai ammh Tunda ta nuna Tsoronsa yasa ya kyaleta Hanne ya kallah da Sauri ta Juya zata koma ya Kira ta ta dawo Kafin tayi mgana ya Tasa keyarta zuwa gaba yana Fadin"Ina zaki..?kema wuce muje..Duk tare kuke daman sai Hali yazo Daya ake aBota..!
Har yana gwara kansu,Kafin yakai su kofar gidansu Amina sun Sha Rankwashi kamar kansu zai Cire Daman ai ya iya Rankwashi baya Dukan Bulala Murdan kunni Rankwashi da Iza keya a kofar Gidan ya Tsaya ya Tura get din yana Fadin"Oya to a shige..!
Amina ta shige tana Hararansa ta kasan ido,Hanne tayi Saurin cewa"Ni gida zan koma..!
Hararanta yayi yana Fadin"Ina..!nan zaki kwana tunda kika zo shiga.!
Ya Tunkudata ya Rufe get din ya Juya yatafi Amina ta kalli Hanne tana Sosa kanta tace"Wlh Gidanku Duk mugaye ne Hanne..!
Allah ya isa bamu yafe ba..!
Hanne na Sosa kanta tace"Kaina Zafi yake ya iya rankwashi fa Amina..!
Amina tace"Insha Allah sai ya samu mai mai mafinyinsa..!
Hanne Dariya abun ya bata Amina Tayi gaba Tana Fadin"Alqur"an ban yafe ba Har kabarinsa na Balbali da Wuta..!
Hanne sai kanne Dariyanta take har suka iso Tsakar gida ko"ina Shuru sai Hasken Inji Dayake an kunna Tun Dazu Hanne tace"Kowa yayi barci Amina..Da ma agida mukayo kwanciyarmu..!
Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bafa nayi niyyar kwanan bane..!
Daga haka ta wuce Dakinsu Hanne tabiBayansu.
Aba Dake bakin Kofarsa ya Sauke ajiyar rai kafin ya Fito Kai Tsaye Kofar Gidan yaje ya Rufe da Kwado kafin ya Dawo yana Dudduba Tsakar gidan,Shi ya Rufe Kofar Kitchen din kafin ya Shige Dakinsa ya Rufe Yau Mamanmu keda shi yasa Tun dazu Yaya ta shige Ciki ita da Jawaad.
Hanne da Amina sukayi mukus da sukaji Motsi Amina na mata Rada akunne tace"Aba ne ya fito..!
Hanne ta gyada kai basu wani motsi ba sai da sukaji Shigarsa Dakinsa Sannan Ya Zeena tayi barci ita da Hamida Ya Zulaihat ne batayi ba tana Karatu Saboda suna gabda fara Jarabawar Fita.
Ta Dago ido ta kallesu Hanne tayi Saurin gaisheta ta amsa kafin ta maida kanta tana Cigaba da Karatunta Amina ta karisa wajen gadonta tana Fadim"Ji Hamida tayi barci..Hanne tasheta..Yasin da ita zamu Hirar nan..!
Ba Musu Hanne ta Daketa sai gata tatashi Hanne tace"Tashi mu yi hira..!
Hamida tayi Tsaki kafin tace"Uban Hiran gobe fa muna da Hadda kun sani..!
Amina na Kwabe kayan ta tace"Hanne kizo ki Saka wannan Rigar..Ke Hamida Sarkin karatu Badai kin iya Haddar ba..?Hanna ma ta iya ba shikenan ba..!
Hamida na Hamma tace"Ke fa Amina..?
Amina na Dariya tace"bala"i ai ni na manta inda nike ma..Kamar Cikin Suratun Khafi ne ko..?nifa inaga Tun Sati Hudu daya wuce Malan Amadu bai karbi Haddata ba ni Tunda Ranar nan ban kara Bi ta kansa ba..!
Hamida da hanne suka kalli Juna kafin Hamida tace"Kinsan Bulala goma ce..!
Amina na Hawa kan gadonta tace"Shine me..?yayi ya gama na Kakkabe jikina..!
Tafada tana Dariya Hanne Zatayi mgana Amina Taja Bargo Tana Fadin"Malama Hanne ki adana wannan wa"azin naki zuwa gaba wajen Amina bamai amfani bane..!
Suna jin haka suka kyaleta Hanne ta Cire kayanta a Tiolet ta Sako Rigar Barci akwai Gado wanda ba kowa kai Saman na Ya Zeena Daman nan take kwana in tazo ta Haye tana Fadin"Uncle T ya baku Assigment Amina..!
Amina tayi Tsaki kafin tace"Kila ya basu ni ina na sanin musu.!
Au kice Uncle Gajere yana Tafiya kamar Dan kaciya..!.
Sai Tasa Dariya Zulaihat ta Dago Dagachan kafin tace"Amina Dare ne fa..?sannan Tsakaninki ga Allah Uncle T din ne mai Tafiya kamar dan kaciya..?
Da Sauri Hamida tace"Ya zulaihat kalli yadda Duk Unity ake Fadin kyansa da ajinsa..Ammh Amina Tsinarsa take..!
Amina Dariyanta ta Rage tana Fadin"Ku Anty Sara mai Warin maza..!
Don Allah kuna jin warin in tazo kusa da ku..?
Hamida da Hanne suka kalli juna ya Zulaihat kuwa cewa tayi"Hamida Kashe mana Hasken Dakin nan nagama karatun..!
To ai tasan Tunda Amina ta shigo to ta Daina Fahimtar komai kenan.
Hamida ta mike ta Sauka tatafi Rage Hasken Dakin Hanne ce tace"Amina kiji Tsoron Allah duk Unity wa yakai Anty Sara gayu da kamshi..!
Zulaihat ta tabe baki tana Fadin"To a ina ma tasan kalan warin maza Hannatu..!
Amina tace"Tabdijam..To wlh warin kashi take duk wannan Uban Turaran datake sawa da kaje kusa da ita kake ji..Wai baku taba ji ba..?ku Tsaya Harda Warin bakin Sir Gumel ma baku Taba ji ba..?
Gabadaya Salati suka saka Ba Hamida Data Kulle Kofarsu ba Hatta Zulaihat Datace"Amina Sharrin naki Harda Principal..!
Bakinta ta Danne tana Dariya Hamida Da tadawo zata kwanta tace"Kibar mganar nan Amina kada kije ki Fadeta a makaranta ya koma kunnensu..!
Amina tace"Sai me..?karshenta kenan Suppention Amina Saidu ta samu freedom ni daman suji Wlh a koreni Gabadaya..!
Ba wanda ya kara tankata ita kadai ta Cigaba da mgana sanin Halinta Duk mganar data Fada har ranta take Nufin haka din.
Zulaihait ne ta gaji tace"Ki kama mana Bakin ki anan wajen Amina ko in na taso kika ga yadda zan yi wurgi waje Haba..Muna so muyi barci kina Hanamu..!
Tafada Cikin bacin rai Amina ta Tura baki cikin kunkuni tace"Mutum dai ya Kusa aure ya bar mu mu shakata..!
Tana jinta batace mata koma ba Indai ta Biye ma Amina sai Su Aba sun fito sun jisu Domin bakinta bazai yi Shuru ba.

Washegari tun Safe kamar abun arziki suna Idar da Sallar asuba Sukayi azkar Hamida da Hanne suka zauna Zulaihat na Biya musu karatu Ya Zeenatu na Kitchen tana Soya musu Dankali Amina ta Fita Tsakar gidan Dakin Mamanmu ta fara shiga bata Ciki Tana Dakin Aba sai ta wuce Dakin Yaya ta sameta kan Darduma tana Karatun Qur"ani yadda Amina Tayi sallama ta Shigo aranta Tana Fatan Daman Amina ta zauna haka sai dai ina tana Shigowa taci karo da Jawaad dake barci nan kusa da Yaya ta Daga hannu ta Dagamai Duka tana Fadin"Wana kama yanzu..?
Ta Tashi yana Sosa inda ta Dakesa Wuyansa ta Chakuma kamar wani Babba tana Fadin"Wa kake ma Dariya Jiya..?
Yasan Halinta yasa da Sauri yace"Bafa Dake nake ba..yi hakuri ya Amina..!
Fayau Fayau ta Fallamai mari tana Fadin"Daman na Fada maka na fika jidali..Yanzu sai nayi wirgi dakai sai ka Bugu iya Buguwa!
Dakatawa da Karatun tayi ta Dago Tana kallonta kafin tace"To sake sa kafin kiyi wurgi dashi..Fitarmin Daga Daki..!
Ta Fada Cikin Bacin rai Amina ta kama Hanya tana kunkuni Lokaci Daya Tana Fadin"Yaro yayi ta iskaci ba"a gani..Sai ace baza"a Dakesa ba..Kwarankwatsa na gansa sai na bugesa..!
Tana jinta tana Fada Har ta Fice Daga Dakin kai ta kada tana Kokarin Cigaba da Karatunta sai gashi ta Leko Tana Dagama Jawaad Hannu Tana Fadin"Zaka sani ne yaro bar ganin Yaya..!
Ta dago Cikin Bacin rai tace"Amina..!
Da Sauri tace"Ina kwana Yaya..Daman nazo gaisheki ne..!
Ko Sake kallonta batayi ta kalli Jawaad tana Fadin"Wuce kaje ka Tube kaya na saka ruwa a Kittle a Tiolet kayi wanka dashi..lokaci na Tafiya..!
Ba Musu ya wuce ita kuma Amina ta wuce aranta tace"Nidai na Fita Hakki na gaisheta..!
Daganan Falon Aba ta je tana ta Sallama kafin taji ya amsa mata kamar ta Allah haka ta shiga kanta na kasa yana zaune kan kujera yana Duba Wasu Takardu ya Dago yana kallonta Da Sauri tace"Aba ina kwana..?mamanmu na ciki..?
Yana Nazarinta yace"Ita kikazo nema..?tana ciki tana barci..!
Da Sauri tace"A"a nazo gaishe ku ne Aba..Sannan na tambayeka..Wai ni na saka maka Hawan jini Aba..?
Kai Tsayen yake kallonta kamar yadda Itama ta Sauke masa Dara Daran Idanuwanta wandanda yake kallonsu kamar na Hadiza Lokacin tana kamarta.
Ita kadai ce acikin ya"yansa take iya Kalllnsa ido Cikin ido ta Fita zakka Tabbas ko acikin Ransa Amina Dabam take har Tunani yake daman Hausawa sunce Maraji aciki yayan Mutun sai kaga kafi sonsa To shima Hakanne sai dai yana kokarin Danne komai sannan yana ganin kamar Kaunar Dayake ma Amina tasamo Asali ne Tun Kaunar Daya ke ma Mahaifiyarta har yau gobe Hadiza In soyayyarta ta Motsamai sai yaji wani Abu acikin Kirjinsa mai Nauyi game da ita.
Saurin Dauke kansa yayi daga kallonsa ita kuwa ganin haka yasa tace"Kayi Shuru Aba bakace komai ba..?
Sai da ya Daidaita natsuwarsa kafin yace"Waye ya fadamiki haka..?
Kai Taaye tace"Waye zai fada..Yaya ce Aba..!
Kai ya dan jinjina kafin yace"A"a bake bace..Ciwo na Daga Allah ne da kuma Girma kinsan ai nafara Tsufa..!
Yafada yana kallomta Itama kallonsa take Tana so taga tsufan Dayace ya Fara,Yana da Tarin Baiwa da Zati in ka kallesa shi ba Fari bane sai dai yana da Haske Daga Zaunen Dayake zaka gane yana da Tsawo da Dan Jiki Sannan akaron Farko zaka san a Tsaye yake Bakin Zamafare kodaga yanayin mganarsa da Zamfaranci.
ALHAJI SA"IDU AMINU GUSAI kenan Ba Rago bane mutun ne Jajirtattace wanda ba abu kadan ke saka aga Rauninsa ba sannan mai Neman na kansa wanda baisan Lalaci ba mai Ra"ayi da Tsari da kuma tsauri kadan acikin Rayuwarsa.
Ashekarunsa in

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment