Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tadan kwanta Sama Sama taji Zeenatu na Fadin"Mamanmu..Mamanmu..!
Bude ido tayi tana Fadin"Zennatu meyasa kika tasheni..?nasan barcin yammah bai da dakyau..Kaina ke Saramin..!
Da sauri Zeenatu tace"Daman nasan baki ji ba.Yaya yau ranta ya baci gashi chan tana kuka tana Dukan Amina..!
Ai bata gama ba ta ingize Zeenatu ta Diro Daga kan gado Dankwali a Hannunta Zaninta na neman Faduwa ta Fice da gudu Zeenatu ta Bita da kallo ta Girgiza kai.
Tana fitowa ta isa ga Amina ta Rumgumeta tana ganinta ta riketa tana kuka take fadin"Mamanmu don Allah ki fadama Yaya bana bin maza Wlh ban bi maza gidan su yar Ajinmu naje Zainab isa kudina naje amsowa na iske sun yi tafiya ba kudi a hannunsa saina tako akafa mamanmu ammh kiji fa abunda yaya ke..!
Bata karisa ba ta Rufe mata baki Cikin Rauni tace"Basai kin fada ba..Nasanki Amineene..bazaki fara Halin da bana ki ba..
Share Hawayen Daina kuka matukar mamanki na Raye baki ba hawaye har Abada..!
Tafada tana share mata kwallah Cikin kauna Yaya kada kai tayi ta bi hanyar Dakinta tana Fadin"ki Rika samun waje acikin ranki kina fadama Amina gaskiya..Ko tana so ko bata so Ta fita zakka acikin gidan nan..!
Daga haka ta bankade labule ta shige Dakinta Mamanmu bata Damu ba mikewa tayi tana Dago Aminan Lokaci Daya tana Fadin"Hamida Dauki Jakar Amina ki kaimata Wajen Dirowarta..Ke Zeena zubo mata abincinta a filet ki hado mata da Ruwa da Zobo yanzu adakina..!
Zulaihat dake gabanta ta kallah kafin tace"Matsa ki bani waje..!
Zulaihat ta kalleta kafin tace"Mamanmu..!
Rai bace ta balla mata Harara tana Fadin"Ki yi wanke wanke..Gobe Aminan tayi..ku kuma kuyi abunda na sakaku..!
Daga haka ta shige Dakinta Dauke da Amina Dake kuka kamar ta maidata Ciki Hamida ta ja Jakar makarantar Amina zuwa Dakinsu Dirowansu kusa da juna ne Domin gadon su ma ahade yake ita tana Sama ne Amina na kasa saman gadonta ta ijiye mata ta Fice ta koma bakin Famfom ta Cigaba da wankinta ita kuma Zeenatu ta shiga Kitchen ta Bude Cooler ta Dibo Taliyar da Kifin Dake ciki ta Bude Fridge ta Dauko Ruwa da Zobo ta Fito zuwa Dakin Mamanmu.
Ita kuma Zulaihat ranta bace ta Fara Fito da kwanukan da aka bata akichen Zuwa bakin Famfo.
Hamida Dake Dauraye kayanta Tace"ki barshi Anty Zulaihat in na gama shanya zan wanke!
Kai tsaye tace"Yauwa.Daman duk Ranar da Amina ta kwaso jidalinta yafi Shafarki..!
Daga haka ta wuce Bata bi takan Hamidan Dake Dariya ba tana Fadin"Amina ce Anty Zulai..Wlh ko Aba baya iyawa da jidalinta ko Ya Jafar gajiya yake..!
Take fada tana Dariya shanyan kayanta tayi tazo ta fara Jika kwanukan sai ga Amina ta fito Daga dakin mamanmu kallonta tayi itama ta kalleta kai tsaye tace"Gobe da Safe har zuwa rana zan yi wanke wanke..Zan rama miki kada kice kin Dauki Jidalin Amina..!
Tafada tana Share bakinta Daya kumbura Hamida kai kawai ta kada Amina ce sai tayi mgana.
Ta fara wanke wanke sai gata tafito jikinta Riga ce doguwa na Atamfa sai Hular Dake kanta Kayan makarantarta ne ke Hannun ta Zata wanke saboda gobe Asabar suna Hadda Tun Safe sai yammah,haddar tasu daya take da islamiyan shiyasa ana tashi Uku da Rabi ayi sallah aci abinci a shiga islamiya itama Madaratul Umar Bin kallab din mallakin Baba mallam ce snnan gabadaya malaman makarantar ya"yansa ne da Dalibansa har ya jafar yana koyawar ajin manya Wato Jss1 da ajin matan aure ya Nasir da ya Uzairu da ya Nazim Duka suna koyarwa anan,Sai dai yanzu Ya Nazim da ya Uzairu suna Makarantar jami"a sai sun dawo Hutu suke zuwa Yaya shamsu ne shima Dukka da kananun shekarunsu Kansa na ja yayi Sauka da Hadda ga Sauran Littafai kai duk ya"yan mallam haka suke akwai kwanya kuma ance duk Kwanyarsu basu kai Babban DA'N MALAM ba dake jami"ar madina yana koyawar chan yake zaune da iyalansa sai karshen shekara suke zuwa gida sai dai Sakonsa akai akai yana zuwa ga mahaifansa.
Har ta fara wankinta ta gama bata cema Hamida komai ba itama batace mata ba Tana idar wa kenan tana Shanya Sallamarsu Ya Jafar da da Ya Nasir ta karade gidan da Sauri Amina ta juya tana kallonsu Fes suka Hada ido hudu da Ya Jafar wata uwar Harara ya Zuba mata yana fadin"Gama Shanya..Ki Tsaya a inda kike ki kama kunninki..!
Nasir Dake gefensa yace"in kin gama kama kunnin ki hada da Tsallon Kwado..Yau zaki gane iskancinki kadan ne Amina..!
Daga haka suka wuce lokacin suna amsa gaisuwan Hamida Jawaad dake bayansu ta kallah yana mata Gwalo yaro dan shekaru goma.!
Amina Rai ta bata a fili ta Furta.."Azzalumai Biyu kenan..Allah ya Hadasu abota kamar yadda Muguntarsu tazo Daya..!
Hamida ta kallah wacce ta zuba mata ido Hararanta tayi da karfi Tana Fadin"Bana son gulma Hamida..!
Kanta ta kauda tana Dariya gama Shanyar tayi ta koma bakin kofar gida ta Coge taki yin abunda akace sai taji motsi sai ta yi kamar ta Duka ta kama kunni sai taga basu bane sai ta Mike Dakin yaya suka fara shiga.
Tana chan tana Hararan Hamida suka Fito Da sauri ta Duka ta Daga hannunta Sama Jafar ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kada kiyi..Kiga yadda zan yi dake agidan nan..!
Nasir kuwa wayarsa yake latsawa hannanunsa Daya Dauke da Littafan Karatu na addini Dakin mamanmu sukayi sallama suka shige Amina ta bisu da Harara afili ta Furta"Duka ai baya kisa..!












*Janafty*
*15/07/2022**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*SADAUKARWA:ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*

_Wannan Labarin Jinjina ce gareki *SUMAIYYA ABDULKADIR TAKORI*(Takorinmu) Allah ya raya miki zuru"a ya tabbatar da aminci da zaman Lafiya agidan auranki_

*🅿️02*

Hamida na wanke wankenta Ammh Rabin Hankalinta na kan Amina ganin yadda ta koma ta zauna Dirshan a kasa Tana wani cin mgani kamar babu abunda ma ya Dameta yadda take zaune kamar tana zaune acikin Daki ne cikin Natsuwarta.
Abu daya ke bama Hamida mamaki bama ita ba kowa da kowa Dake gidan nan yana mamakin yadda Amina bata jin tsoron Ya Jafar da Ya Nasir wadanda kaf gidajen sune manya kuma su ke hukunci da kuma Daidatuwar Tarbiyansu bama su ba na Sama dasu su ya Zeena suna Tsoronsu da basu girmansu banda Amina Har yau har gobe bata taba ganin Wannan Tsoron da Shakkarta acikin Idanuwanta ba.
Tagama wanke wanken kenan taji an fara kiran sallah Daga masallacin gidan Mallam Daidai da fitowar Zeena Daga Dakinsu kanta ba Dankwali sai akayi rashin Sa"a Lokacin Ya Jafar da Ya Nasir suka fito Daga Dakin Mamanmu tana Biye dasu abaya.
Bata da yadda zatayi sun riga sun ganta Ya Jafar ya Duka yana Saka Takalminsa mai igiya Hamida Ta kalli Amina Dake zaunenta tace cikin Rada..'Ke Amina ga su nan fa sun fito..!
Daga ido tayi ta kallesu kafin ta mike Tsugunne ta daga hannunta sama kamar gaske.
Ya Nasir ne ya kalli Zeena Dake kokarin komawa Daki Cikin Muryansa mai Cike da Iko yace"Wacece nan take yawo ba Dankwali..?
Ba yadda Zeena zatayi Dole ta juyo tana Fadin"Nice ina yini Ya Nasir..!
Harara yayi mata kafin yace"Dillah wuce ki saka Dankwalin ki..Kuna manya kuda su Hamida zasu yi ku musu Fada..!
Bata ko kara mgana ba ta shigo Dakinsu Daman Dakin Mamanmu zata shiga ta Dauko littafinta jiya ta manta Dashi,bata zata har alokacin basu tafi ba Shiyasa ta fito haka.
Tana Shiga Dakin Zulaihat data mike Tana Tatattara Littafanta tace"Kema kin samu Rabonki kenan..!
Zeena bata iya mgana ba Umh kawai tace ta Dauki Damkwalin Abaya ta saka lokaci Daya tana Tura kofar Bandakin Dake Daknsu ta shige Tare da Rufowa Zulaihat ta Bita da kallo Lokaci Daya.
Achan waje kuma Nasir ne ya kalli Hamida yana Fadin"wai sau nawa zan ce kudaina zama bakin Famfo nan da mangariba..?baku gujema Lafiyarku ko .?
Kanta na kasa tace"Ai nama gama yanzu zan tashi ina wanke wajen ne..!
Mamanmu ta kalleta tana Fadin"Wato Zulaihat ke ta bar ma aikin kenan..?gobe kuwa sai tayi shi..!
Tafada Daidai Lokacin Data hango Amina da Sauri tace"Amina wa ya sakaki kama kunni da mangariban nan...?
Jafar kai tsaye yace"Nine mamanmu..Zata fadamin inda ta Biya bayan an tashe su daga makaranta..!
Mamanmu ta Bude baki zatayi mgana ya Rigata da Fadin"Don Allah Mamanmu kada ki saka baki..Bazan Daketa ba in har ta bani amsar Tambayana..!
Mamanmu tace"Kada ku maida Amina Jaka mana..Jikinta fa ya Saba Da dukanku..!
Bai Saurareta ba ya Nufi Aminar Nasir ne ya tsaya yana Fadin"Wake ja Mamanmu..?yarinya Daya Tal zata zame ma kowa ciwon kai..!
Mamanmu tace"Sai addu"a..nidai kada ku tabamin D'iya..Nasan ku da Duka kamar kun Hada kauna..!
Yana jinta yar Dariya kawai yayi Hamida kam data gama kwashe komai ta maida Kitchen Dakin Yaya ta shige ta sameta Har ta Kabbarta Sallah Cikin kurya ta shige ta samu Jawaad na saka Jallabiya da Sauri yana Fadin"Ya Hamida Don Allah su Ya jafar na nan..?
Hararansa tayi kafin tace"Bansani ba..Sai ka fita kagani..!
Dariya yake yi kafin ya Fice ta bishi da kwafa tana Fadin"Zaka Dawo zakasan wanda kake ma Dariya..!
Daga haka ta shige Tiolet din Dake Cikin kuryan Dakin na Yaya.

Jafar gaban Amina ya Tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa abun na bashi mamaki ba kowa ke iya Hada ido dashi ba Saboda kwarjininsa da yadda kannensa ke tsoronsa  ko Jadwa Datake Daga shi sai ita bai jin tana kallonso ido Cikin Ido.
Kai Tsaye Cikin Kakkausar Muryansa yace"Da aka tashe ku makaranta ina kika Tsaya..?ko nace ina kikaje..?
Amina kai tsaye tace"Gidan yar ajinmu Zainab isa..!
Da mamaki yace"Yaya ta aikeki ko mamanmu..?ko Aba..?
Itama Cikin dan mamakin ta Waro Idanuwanta kafin tace"Kudina naje amsowa..!
Tafada tana Dan Tura baki Hannu yasa ba tsammani ya bige bakin yana Fadin"Watarana sai na rabaki da Hakoranki na gaba..!
Nasir Dake bayansa yace"An fa Tada sallah Jafar..!
Jin haka yasa ya ja kunnenta Har sai da tayi kara Cikin Fada yace"Kije kiyi sallah ki jirani kafin na wuce zan dawo ban yarda da mganarki ba..!
Sannan ya saketa gefe ta koma tana Sosa kunnenta Nasir ma sai da ya bata Rankwashi mai Zafi sannan suka Fice Sai ga Jawaad ya Fito ya Bisu abaya da Gudu yana ma Amina gwalo,Tana Dafe da kanta Dataji zafin har Tsakar kanta tace"Yaro in na kama ka sai na Lahira yafi  ka jin Dadi..Na fika Jidali da Fitina..!
Tafada kafin ta mike tana Kakkabe Jikinta nan bakin famfon ta karisa ta Bude ta fara alwala sai da ta gama kana ta shige Dakin Mamanmu ta isketa kan Darduma tana Lazimi..!
Kai Tsaye Amina ta wuce uwar Dakinta tana Fadin"Mamanmu na Dauki Hijabinki Cikin Wardrope dinki..nawa suna Dakinmu kuma bana son shiga..!
Tafada Muryanta Cikin yar shagwaba Tana Daga zaunen kan Darduma ta Daga mata kai Ciki ta shige ta Bude makeken Wardrope din ta Bude barayin Gogaggun Hijaban Mamanmu ta Dauko guda Daya ta fito tana zuwa Mamanmu ta matsa gefen Darduman Datayi sallar duk da Shinfidadden Cafet din italiyan din Daya malalen Falon
Tana cikin Sallar mamanmu ta Fice kuma Tana da tabbacin Dakin Yaya zataje domin duk bayan mgariba da isha"i adakin take yinsa suna Hira da Tattauna wasu abubuwa Kamar ba Kishiyoyi ba..
Tana Idar da Sallar ko dan addu"a bata Tsaya yi ba ta mike Zaraf kamar an tsunguleta mganar Ya Jafar take Tunawa Dayace zai dawo duk da tasan da Wahala ya dawo yau sai gobe saboda akwai wa"azin da Baba mallam ke yi kowani bayan Sallar mangriba zuwa Isha"i sannan in an gama zasu Rufe da Sallar Isha"i kuma Tana da Tabbacin Aba ma ya dawo suna masallacin Tare in ma sun fito daga waje zasu gaisa ya wuce gidansa ina ma wannan mayyar matar tasa zata barsa ita Har mamakinta take yadda take mutuwar son Ya Jafar ko ina abun so a wajen wanda ya maida mugunta Dabi"arsa.
Baki ta Tabe bata tsaya Cire Hijabin Jikinta ba ta Fice Takalmin mamanmu na Yawom Tsakar gida ta Zura ya ma mata yawa sosai karamar kafarta ta Zurma aciki batason shiga Dakin su ne Saboda hamida tasan su Ya zeenatu ba lalle su bi ta kanta ba ammu Hamida gani taake tafi kowa Shigar mata Hanci da Dunkunkune in ta koma Dakin Hamida tayi mgana sai ta tankata kuma Hakan kamar wani Lasisi ne ta siyo ma kanta Fada Wajen Aba Shiyasa ta zabi Tafiya gidansu Hanna tayi zamanta sai Dare yayi Lokacin Hamidan ta kwanta sai ta Dawo.
Batare data Fadama kowa ba,kamar yadda ta Saba yin komai gaban kanta ta saka kai ta fice Daga gidan kuma Har ta fice bata Hadu da kowa ba,Awajen ma ba kowa Saboda an shiga masallaci Wajen yayi Haske Saboda an kunna Generator massllaci ba wuta suma ana Dawowa sallah su Ya shamsu zasu tada na cikin gidan Mallam babba ne mai bama Duka gidan da gidansu wuta taji dai ana ta Fada D'an malam Dake madina ya aiko da kudi aka siya har ma gyaran gidajen da aka sabunta musu wattanin baya duk shi yake turo ma dasu Ya Jafar kudi su kuma suna aiwatar da umarninsa.
Tasamu nasaran shiga gidan kanta Tsaye saboda Buba megadi shima yana masallaci wannan Dokar Baba Malam ne,ba hujja kana jin ana Kiran Sallah ka fake da wani aiki ya zama Dole kowa ya bar komai ya tafi kiran Allah
Gidan Baba Malam ya wuce yadda zan kwakwatanta muku Babban gida ne mai Dauke da Haraba mai girma Dauke da Motoci guda biyar hudu suna Bayyane Daya kuma an Lullubeta da Tamfol Tadade ahaka in ba mai mallakin Motan ya Diro garin ba bamai da ikon hawanta Duk da bai Saka Dokar haka ba,Sai Dayar bakar prado din ta mallam ce in fita ta kamasa Dayar 306 iri daya guda Biyu Daya ta Ya Jafar ce Daya ta Nasir,Sai wata benz baka ta Aba ce,Sai babbar Macapolo ta Jigilan makaranta ne.
Haraban gidan na Zagaye da Fulawowi masu kyau da yarari.
Daga Cikin gidan kuma Flat Biyar ne ajere na Farkon na Baba Malam ne grefensa akwai Dakuna kamar guda Biyar saboda mazan gidan Falt din Dake bayansa kuma Shashen Hajiya Babba ce Uwargidan Mallam sai shashen mai bi mata Hajiya uwa Daga nata sai na Anty Nasara na Anty Amarya shine na karshen wanda Daga gefensa kuma wani katon Kitchen ne da Store mai Dauke da Kimai na Bukatar mace na girki Kowacce tana da nata ashashenta ammh Gudun Fitina yasa aka Fitar da na waje inda duk wacce keda girki Zata Fita ita da yara da masu aiki suyi komai Tare Dokar gidan ce da Tsarin komai Bisa Tarbiya da Sunna Baba mallam Sharahararran malami ne Daba iya Nigeria ko Gumel ba Har Kasheshen Larabawa an san dashi.
A Babban Falon Dake shashensa ake Taruwa Matan da yaran maza da mata aci abinci sannan Ashashen sa ne kadai akwai Talabijin shima kuma In suna wajen sai Tashar Karatu sai wa"azi in ba kaga an Sauya sai in Dare ya Tsala yana so ya kalli Labarai Sun saba ya Zame musu jiki Duk wanda ya kwana da tashi agidan Mallam ina ka Fito karatu ina zaka ne..Me kace Aya ce mai na maida maka Hadisine ba iya Iyalan gidan ba Har damu da muka Hade dasu muma Dokarsa muke bi Domin har yau har Gobe in ba"a Fada maka ba Mutanen gari Dauka Suke mu jikokin Mallam ne BABA SA"IDU ne babban yaron Malam..!
Kai tsaye shashen Hajiya Babba ta wuce Domin nan ne Dakin su Hanne Auta take ga Hajiya,Bata Tsaya sallama ba ta Tura kofar shashen da Karfi Tana Kiran sunan Hannan.
"Hanne...Hanne..Hanne..!
Take Fada lokaci Daya tana Wulka manya Idanuwanta Cikin kayattacen Falon na Hajiya Dayaji komai na More Rayuwa.
Sai dai mamaikon taga Hanne sai taci karo da Hararan Ya Aisha Dake Zaune kan Darduma tana karatun pass Q domin suna gabda fara WAEC da NECO, Bata katse Karatun nata ba ammh Amina tasan Hararan ko ta macece Yasa ta Daga Hannunta tana Fadin"Yi Hakutri Ya Aisha..sallamu Alaikum..!
Tafada kai Tsaye tana kara Wurga ido wajen neman Hanne.
Abida Dake zaune kan kujera Tana Karatun Qur'ani
Wacce Tunda taji Bangazan kofa Da kira tasan sai Amina itace kadai bata da natsuwa Kaf acikin ya"yan gidansu da gidan Baba Sa"idun.
Itama Hararan ta jefa mata kafin tace"A tsakiyar falon ake sallama Amina..?
Sai alokacin Amina ta ganta aranta ta Furta"Uwar sa'ido..!
Afili kuma sai ta Dan Rasauya ido kafin tace"Sallama fa sunanta sallama Ya Abida..!
Abida daman ai tasan bazata koma ba Kafiya ce da ita kamar kafura.
Bude mata ido tayi tana Fadin"Au bazaki koma bakin kofa ki sake wata ba kenan..?
Amina ta Bude baki tace"Ah gaskiya..!
Cikin kunkuni tace"Haka kurum..Tab...
Abida tace"Me kikace..?
Kallonta tayi da manya Idanuwanta kafin tace"Nifa ban ce komai ba..!
Abida Kai ta Rausaya a cikin Idanuwan Amina akwai wani kaifin da indan ta kalleka sai kaji gwiwanka yayi sanyi..!
Da hannu ta nuna mata tana Fadin"Hanne tana Dakinmu tana Guga..!
Ai bata gama Rufe baki ba Amina ta Kwashi gudu tana kara kiran sunan Hanne Wacce sai Lokacin taji kiran da Sauri ta kashe Iron din Daman Hijabin haddarsu na gobe take gogewa ko mafarki take yi tasan Sautin Kiran Amina Dabam yake kuma akowa da Hannatu yake Kiranta Aminene ce kadai ke kiranta da Hanne.
Akofar Dakin sukaci karo Dakin Dake kusa da Bedroom din Hajiya sai wani Wanda suke Saukar baki Dangin Hajiya in sun zo nesa dana Hajiya.
Kusan karo sukayi da juna Wanda yasa Hanne tayi baya tana Fadin"AMINA gani nan fa..!
Tsayawa sukayi suna kallon Juna kafin Amina Taja hannunta su koma Cikin Dakin Tana Fadin"Hajiya fa..!?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Amina tabi Dakin da kallo ta Sauke ganinta kan Hijabin da Hanne ke gogewa tace"Dadina Dake kina da Zafin Nama Hanne..ni fa ban ji ma Hijabin nawa awanke yake ballatana akai ga gugansa..!
Hanne Dukawa tayi ta kunna Soket ta Cigaba da Guganta ita kuma Amina kan Karamin gadon Hanne ta Zauna Babban na Ya Abida da ya Aisha ne
Hanne bata damu ba tace"ai ke babba ce..Amina kike ni kuma Hannatu..!
Amina Tayi dariya tana Fadin"dillar Sarkin Tsoro..Ki Saki jiki ki amsa sunanki Hannatu Yusus Abdurraham Bazanga kowa shakkarki zai yi..!
Hanne na Guganta bata Dago ba tace"Uhmm..Meya fito dake Daga gida da Daran nan..?nasan da Dalili..!
Amina ta Tabe baki tana Kwabe Hijabin Jikinta Lokaci Daya tana Fadin'"Ke da kika sani..Yau fa Har Yaya sai da ta Dakeni Hanne su Ya Zeenatu suka min gami wajen su ya Jafar harda fadamin in ya Dawo sai na Sani..!
Hanne na Duken ta Dago kanta tana kallon Amina Kafin tace"Kan Tafiyarki yawon da kika saba in an tashi makaranta ko..?nima fa ana tashi nazo ajinku bakya nan..!
Gajiya akayi da jiranki Ya shamsu yace mu taho gida..!
Amina ta Zabga mata Harara tana Fadin"Ni daman bance ku jirani ba..Nasan Hanya..!
Hanne tace'Koma miye dai baki kyauta ba..Amina don Allah ki daina Wasu abubuwan kai tsaye ko ni in kika fadama zakije wani wajen.ko Hamida haka zata faru..?
Amina ta Juya idanuwanta kafin tace"Hanne..Hanne..Ki kyaleni don Allah kada ki batamin rai bazaki iya da Jidali na ba..!
Hanne bata Kara mgana ba itama Aminan haka Sai da ta juya taja Littafin Data gani kan gadon Hanne Ta Fara Budewa kafin ta Dago Tana Fadin"Hanne akwai Kwazo..Kin yi aikin Malamin Lissafin nan..!
Hanne na Nimken karshe a Hijabinta tace"Ba Dole ba kada ma na manta kinsan mugu ne wlh ya Rantse Bulala goma ga duk wanda bai yi ba..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Kan bala"i..Wai haka yace..?
Hanne ta kashe Soket din ta Mike Dauke da Hijabin tana Fadin"Ajinmu ba..Bansani ba ko ku bai Fada muku ba..Ammh nasan komai tare yake mana ba bambamci..!
Amina tace"Oho ni fa sanda ya shigo ina chan ina Karatun littafin da Ziyada ta daukomim adakin Antyta Garin Kallon Ruwa kin ji Dadinsa Hanne..!
Hanne ta tsaya kyam tana kallon Amina kafin tace"Amina Daman baki Daina wannan karance karancen nan ba..?kinsan fa in aka sani bazaki ji Dadi ba..!
Amina tayi tsaki tana Fadin"To sai me..?ke zaki fada..?ke ni kyaleni Sai fa nayi kema zan koya miki Allah da dadi..!
Hanne tace"Allah ya Tsareni..!
Amina ta tsuntsire da Dariya tana ganin Hanne ta Bude babban Wadrope din Dake Dakin gefen inda kayanta yake ta sakashi Kana ta Rufo Tana kallon Amina kafin tace"ki Tafi da littafin gida ki kwafe kada muje Ranar Monday Uncle Gaddafi ya Dakeki kinsan Halinsa..!
Amina tace"Dillah Rabu dashi..Duka na Kisa ne..?da yana Kisa da babu Burbushin Amina aduniya kuma ya Dade bai yi Dukan ba Alqur"an bazan yi ba..!
Hanne ta kada kafin tace"Ammh in kika kiyye taba Lafiyarki fa Amina..?
Amina tayi kamar bataji ta ba ganin Haka yasa Hanne ta karisa gabanta Tana Fadin"In ya jafar ya dawo fa..?
Amina na Dariya tace"Ke bazai dawo ba kema kinsani..Yaushe mai wannan Dakalin bakin zata barsa..!
Hanne na Rufe baki tana Fadin"Ke Amina Anty Shamsiyan ne mai Dakalin baki..?
Amina na Dariya Harda Buga Kafa tace"Eh mana baki taba Lura ba..Sai ma in tana mgana..Sweetheart..!
Amina ta fada tana kwaikwayonta Dayasa sai da Hanne ta Duka saboda Dariya Kafin ta Dago ji kake Tas sun Kashe da juna Cikin Nishadi Tare suke Zube kan gadon Amina nama Hanne Rada akunne dayasa ta kara Saka Dariya tana Tureta Lokaci Daya Tana Fadin"Ba ruwana..Ba ruwana Amina..Bazan iya Da jidalinki ba kinsani..!
Amina bata Damu ba Chanza Fuska tayi tana Fadin"Kin Tuna sadda Muna aji uku a islamiya kullum Karatunta Dayane..Anjadada.Kalli Leben nata jadaddaad..!
Dariya sai da tasaka Hanne Hawaye Saboda yadda Amina ke yi da baki kamar Tsohuwa zatace isuhu..!
Cikinta ta Dafe tana Fadin"Ki barni haka Amina kada ki kullarmin da ciki da Dariya..!
Dariyan suke gabadayansu Basu san da shigowar Hajiya ba sai dai sukaji mganarta Daga sama.

"Dariyan me kukeyi haka ne..?
Da Sauri suka jiyo suna kallonta Hajiya Babba tana sanye da Doguwar rigar Shadda ajikinta Mace ce Doguwa ga kiba,Akallah ta bama Shekaru hamsin baya sai dai Hutu sun Lullube shekarunta Da ka ganta Kaga su Hanne da Ya Aisha Saboda suna Kama da ita sosai.

Amina ce ta mike zaune tana Fadin"Hajiya ina yini..?
Hajiya na Daga kofar Dakin tace"Lafiya lau Mamah..Sai yau nake ganinki..?
Amina na Dariya batace komai ba Bata iya maidama Hajiya mgana Saboda Kirkinta,Mamah take ce mata Saboda sunan Mahaifiyar Baba Malam Amina kec dashi basa Kiran Sunanta ita tace Mamah shi yace Mamana..!
Hanne ce tayi zaraf tace"Yau ma Laifi Tayi Hajiya..!
Hajiya ta kada kai tana Fadin"Ohh maamah duk baki ji nasihata ba ko..?Don Allah ki natau ki dinga jin mgana Bana son wannan Korafin Kowa yace ke Babanki Sa"idu kullum Mganarki yake yi hakama iyayenki mata Don Allah Mamah ki rika jin mgana ki zama kamar kowacce y"a acikin Gidanan..!
Zaku Dauka yadda Amina tayi shuru Tana jin Fadan ne nan kuwa bata ma Fahimta Domin indai wannan Nasihan ne ta Haddacesu Daga bakin Hajiya da Baba Malam
Ammh Cikin Dan kada ido tace"Shikenan Hajiya..!
Kallon Hanne tayi kafin tace"Ku tashi kuyi sallar isha"i gashi chan ana Kira..Ku fito muje falon Malam mu ci Abinci..!
Da Sauri Amina tace"Hajiya zamu ci namu anan..!
Saboda in akwai abunda ta Tsana wannan al"adar ta gidan mallam Akwai Wadanda bata son Haduwa Dasu acikin gidan nan.
Hajiya ta juyawa tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ba ruwana ku da Babanku..!
Sai da Hajiya ta fice ne Hanne tace"Meyasa indai kikazo gidanan bakya son zuwa Falon Baba cin Abinci..?
Amina tace"Ba wani dalili..Kawai bana son ganin matar nan ne..!
Hanne tace"Wai Anty Amarya..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Itafa Bata da Mutumci Ni tun Ranar da Fada ya hadani da Sa'adatu ta Shigar mata Har tana Fadin meyasa ta Hada kashi da irin Tsiya kamata..?na tsaneta Daga ita har ya"yanta kinsan ko a makaranta bana mgana Dasu..kuma ina jiran Watarana yarinya ta shigar min Harka na Sauke mata Hayakin kaina..!
Hanne ta mike tana Fadin"Amina baki da mantuwa..!
Amina tace"Bana manta wanda yayimin Alheri..Da wanda yayimin Sharri..Kina wani abu kamar kuma jin Dadin zama da ita kuke..Saboda Baba malan ne take Rage wasu abubuwan ammh da badomin haka ba Allah kadai yasan iskancin da zatayi..!
Hanne tace"Ni ina ruwana da ita..Iyaka in mun hadu na gaisheta ko Shashenta bana zuwa sai ta kama..Sa"adatu ma ta Dade batamin mgana kinsani Saboda ke..!
Amina tace"Share banza..Itace akasa mu muyin gaba badai ta Mutum ba sai Allah..!
Hanne na Dariya tace"Kinsan fa Diyar yayarta Ya Dan mallam ke aure ko..?
Amina ta yamutsa Fuska tace"Haka naji shiko Duk yanmatan Duniya sai ita .?
Hanne tace"Kowa haka yake fadi..in kinga ya"yan masu Sarauta da masu kudi da malamai yadda suka rika kawo ya"yansu wajen Baba ammh Duk yaki sai kawai Rana Tsaka yace Anty Sakina yake so..Kinsan tare tatashi wajenta dasu ya Jidda !
Amina tace"Eh mana na Tuna lokacin duk da bamu da wayau tafi kowa iskanci kamar gidan Ubanta..Nifa inaga Tun da akayi auran ban kara ganinta ba Duk zuwan da sukeyi har su tafi bama Haduwa har shi

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment