Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai dai ita Kaddaran Allah Daman Dayace komai Tsalle Tsallen bawa bai isa ya Gujemata ba, Aminu gusai ya Rasu Lokacin da Jinyarsa ta karar da komai ya Rasu ya bar Matarsa Hajiya Hadiza da Yarsa Husai da Sa'idu ko kafin Rasuwarsa ya kara Jadaddama Malam Sa'idu nasa ne har Abada wannan karamcin na Aminu Malam har ya koma ga Allah bazai manta ba.
Yaso ya Dauko Husai da Hajiya Hadiza ya Rikesu sai yan"uwan Aminu suke roko alfarman ya bar musu Rikonsu sai ya kyale musu Tunda karamcimsu garesa mai girma ne Gidan yayan Aminu Hajiya Hadizan ta koma da zama ita da Husai ba kyashi ba Hasaada riko na Tsakani ga Allah Sa"idu Lokacin yana makarantar kwana ta Hassan gwarzo Dake kano Aminu ya rasu sai da ya Dawo yaje yayima iyayensa gaisuwa Kowa bashi yake tsausayi ba Domim cewa ake Aminu yayi ma Sa"idu gata Domin Uba irin Malam abun Alfaharin kowani Cikakken D'a ne.
Tun Rasuwar Aminu Garin Gusai ya Fita kan Malam Yunusa batare da Shawara da kowa ba ya Fara Binciken yadda zai tashi Daga garin Dayake Tunamai da adalin Amini kamar Aminu,Ba Dadewa ya samu Cikakken bayani kan garin Gumel da yadda Suke da amfanin gona da Sauran Cigaba ba Dadewa ya mallaki Fili a wannan anguwan ta Zango ya Fara Gina iya adadin ida zasu zauna.
Sannan ya samar da Katon Fili Domim Kiwo yayi alkawarin Sa"idu sai ya zama wani abu sannan yana da Burin Cikamai wannan Burin nasa.
Dawowar Malam Yunusa garin Gumel baima Hajiya Hadiza Dadi ba Saboda ta Saba da Hajiya Babba sosai sannan Husai ta Saba da su Umar ammh bata da yarda zatayi tun anan din ma ba Wahala take ciki Yan"uwan Aminu ba suna Rike dasu tsakani ga Allah Duk da itama Duka na gida ne
Shekarun da suka Shude masu yawa ne sannan sun zo da Nasarori da Dadama da kuma akasinsu Sa"idu ya gama Secondary ya Fada Jami"ar garin Dutse yana karantar agric abunda ya Shafi noma da kiwo Ko alokacin Gidan gonar Baba Mallam Dake kusa dasu Sa"idu ke da Ahakin kula dasu Haka Allah ya yisa Zama Cikin Dabbobi sune ke sakashi Nishadi sannam Agarin ba wanda yasan Sa"idu ba yaron Malam bane Sannan kowa Dauka yake Shine Babba sannan su Umar Duka kannensa ne,Malam bai yi kasa a gwiwa ba anan din ma ya Cigaba da Karantar wa Ya Hakura da neman ilimi ya Zauma yana karantar da Duka Dalibin Dayazo wajensa neman ilimi Sannan bai da ina zuwa Da"awa ba duk inda za"a je dashi ake zuwa.
Zuwa Lokacin Malam ya Kara auran yar nan garin Jigawa ce Hajiya Nasara ita yar Masu kudi ce sannan zuwa Lokacin Gidan Malam ya fara Cika da Ya"ya kamar yadda yake fata sannan bai manta da Hajiya Hadiza da Husai ba da Lokaci bayan Lokaci suna zuwa suma suna zuwa sannan babu abunda suka nema suka rasa na bangaran Rayuwa.

*******

*Bayan shekaru Talatin..*

Cigaba da Nasaran Rayuwa da Rashi da Samu ba wanda Baba Malam bai gani ba ya Samu Nasara ya Daukaka bama Nageria ba Duniya gabadaya ta Shaida Iliminsa da Sadaukarwansa kan kasarsa zuwa Lokacin hatta Kasar Saudiya tasan da zamamsa yasan Manyan Mutane masu Saurata da masu Dukiya yasan manya malamai kala kala ta Dalili Jajircewansa da kuma Dattakonsa zuwa Lokacin baisan adadin Daliban Daya rike ya karantar ba kuma ya Taimaka musu suka zama wani abu baisani ba Sai Dai Burinsa ya Cika ya amfanar da iliminsa ga al"umar kasarsa kamar yadda yake Fata.
Yayi rashin Amini kamar Alhaji Aminu sannan kuma sunyi Rashin Hajiya Hadiza Cancer ce ta kasheta sannan sun aurar da Husai Tana Jordan da zama ita da Mijinta da iyalanta wanda ya kasance amsader ne mai Wakiltan Nageria Akasar sannan kuma Burinsa ya Cika Sa'idu ya zama wani Jigo..Jigon Dayake alfahari dashi har yau har gobe Sa"idu yayi karatu har matakin Master akan abunda ya Shafi sanin Noma da kiwo sannan baisan adadin Kwasakwasan Daya Hallata kan Abunda ya shafi abunda yake so ba Sannan Bayan haka shi ya bama Baba Malam Shawaran Siyan wani Katon Fili a Farkon gari Dake Hadeja Road Inda suka Samar da Katuwar Gidan Gona babu abunda babu,na kiwo awajen katon Fili ne mai kama da alkarya Guda Abaya iya Dabbobi ne yanzu kuwa da aka Cigaba Har da Kaji da Talo Talo komai fa babu abunda babu Sannan kuma an Fadada abun har da Offices acikin wajen sannan akwai ma"aikata masu kula da wajen da masu Dawainiyar Kwashe kwaiyayan in Kaji sun saka sannan Baban Gidan Gona ne da kaf garin Gumel ba Kamarsa da kewaye.
*GIDAN GONAR BAZANGA..!
babu wanda baisan da zamansa ba Sannan Sa"idu shi ke da alhakin Kula da komai na Dukiyar Baba Malam,Sannan bangaran Gonakinsa Sa"idu ke da Ahalin kula da komai Daga Daukan masu Noma biyan su Cire amfani gona Fitar da zakka Komai na Hannunsa ne Baba Malam abu Dayane ke gabansa yakan Koyar da Dalibai Kadan Daga abunda ya Sani ammh Gabadaya alhakin Kula da Dukiyarsa da Komai yana Wuyan Sa"idu ne,Tare suka wahala sannan Kusan kula da komai dukiyar ta habaka Jajircewan Sa"idu ne.
sannan har zuwa wannan Lokacin Sunan Sa"idu ne gaba abakin Malam kafin ya"yansa
Baba Mallam yayi ma Sa"idu Auren Farko da Hadiza Haifaffiyar garin nan Gumel ce sai dai marainiya ce bata uwa bata da Uba ba wani Cikakken Dangi Labarinta yaji ya Tsausayamata Tana daga Cikin marayun da suke samun Tallafi Daga Kungiyarsu na Ahalus sunna Sa"idu tunda yake bai Taba Saba mganar Mallam ba Gabadaya Rayuwarsa ta kare ne a Yimasa Biyayya Da Hannu Bibbiyu ya Karbi Hadiza,Bayan Baba Malam ya gina mai Filin Dake kusa Dashi Daman Tunda ya siyeshi da Sunan Sa"idun ya siya Halak malak.

Shekararsu Biyar da aure Har sun samu karuwar ya"ya Biyu Jafar ne Babba ne sai Jadwa sai kuma tazo tayi Jaleela daganan ne ya kara aure da Balaraba yar"uwansa ce Daga Gusai Daga Dangin Babansa suka auramai ita tazo suka Hade kai da mamanmu suma zaman Lafiya da juna.
Sannan Daga gefe Dayama Malam ya kara aure da Marliya Itace yarinya Cikin matansa ita yar Garin Dutse ce sannan itama kakanta Malami ne sun gaji arziki da malamanta itama yazo ya Hadata Cikin matansa ta shiga Zazzaga ya"ya Kamar yadda gidan Baba Malam ya Cika da Wadatar ya"ya Haka Gidan Baba Sa"idu Wanda suna ne da su Umar suka sakamai kuma ya bisa,Shi Allah ya basa Haihuwar akai akai ba kamar Mahaifinsa ba da su Biyu kadai ya Haifa ba,
Sannan sunan Sa"idu ba arayuwar Malam ba kaf a Duka ahali da Zuru"arsa wannan Kauna Tsakanin BABA MALAM da BABA SA"IDU daga allah ne Kaunace da Duk hassada da Kyashinka sai kabarsu sun Hade sun zama abu Daya da har har gobe Baba Mallam Sa"idu ne agabansa Duk kuwa  ya"yansa sun Girma ammh bakin sai sai ya ambaci Sa"idu kafin su kamar yadda shima Baba Sa"idun duka Rayuwarsa baida wani abin Dubawa Wanda ya zamemai Madubi Wanda shi yake kallo amtsayin komai Daya Taka na Rayuwa sannan yana Mai kauna Kaunar dako Mahaifinsa Daya kawosa Duniya baya masa kwantankwancin kaunar Dayake ma Baba Mallam..Ita Kaunar junansu Daga Indallahine.








*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*🅿️06*

Ayanzu kimanin Matan Auren Baba Malam Hudu Cif ya riga ya Rufe kofar Sannan da albarkan Ya"ya Guda Ashirin Daga duka jerin Dakunan matan nasa.
Hajiya Babba keda shida Daga bangaranta Bayan Umar da Nazir sai da aka Auro Hajiya Uwa kafin ta sake Haihuwan Nasir,Daga sai Aisha sai Abida sai karamarsu ta baya baya ce Ta karshe kuma Auta Hannatu.
Sai Hajiya Uwa Dake da guda Biyar itama Babban shine Nazeem,Su.Nasir sun Girmemasa saboda sai da suka Dawo Gumel ta dan Dadewa ta Haifeshi,Sai Uzairu,Nazifa da Umaimatu sai Shamsu Ta aurar da Nazifa wacce ke garin Abuja ita da ya"yanta Umaimatu ma Saboda bata da Lafiya ne ammh a ka"idan Gidan Mallam bakya wuce sha takwas yake aurar Dake mazan yaransa ne ke Karatu mai Zurfi.
Sai Anty Nasara itama ya"yanta Biyar Fatima ce babba sai Akila sai Ikram,Akilu da Zubairu sune yaran Matasa Sai Anty Amarya ita kuma Tana da yara Hudu Jidda ce Babba saimai bi mata Sadiya sai Sa"adatu karamarsu kuma Sabeehatu.
Hajiya Babba ta gama aurar da Duka Mazan ya"yanta Umar Shine Babba yana Madina,Shi Tun farko bai yi Rayuwarsa anan ba Yana gama Secondary Shcool Dinsa Baba Malam ya Turasa Madina Wajen Abokinsa da Sukayi Karatu Tare A madina Kattab,Wanda yanzu yake kasuwancinsa achan Madina Balarabe ne Asalin Haifaffan Garin Ma"aiki wato Madina achan yayi Degree dinsa na Farko kan Islamis Studies sannan yayi maaster dinsa kan Qur"an and Islamic Studies Domin Shi Umar irin Mahaifinsa ne Tarin Baiwa da kuma Daukan karatu ko wani iri ne shima achan haka ya Fita Zakka cikin Sa"aninsa,Shima kamar Mahaifinsa ne sun rike sa achan yana Musu koyarwa Sannan Tuni ya Samu Lasisin zama achan kasar Madina yayi aure Da Sakina Diyar yayar Anty Amarya Data riketa a Hannunta Bayan Mahaifinta ya rasu Shekaru Biyar kenan ammh bata taba ko bari ba sannan da Farko anan Gumel din ta fara zama Sai da ya Samar mata Lasisin zama achan kasar kana yazo ya Dauketa.
Umar shima mai arziki ne sai dai komai ya samu na Iyayansa ne da yan"uwansa sannan da yima Addinin Allah Hidima,Shi ya rika aiko da kudi aka Gina wannan Masallacin sannan aka Sabunta gidansu da kuma Gidan Baba Sa"idu.
Sannan ginin gidansa kuma baya nan aka Fara har aka gama Duka Alhakin Kula da komai Baba Sa"idu ne Dayazame musu wani jigo kuma babban yaya shi yake Turomawa Shi kuma sai ya Wakilta Jafar da Nasir Saboda shima akwai wasu ayuukan agabansa,Umar bai cika zuwa ba sai dai Waya in ma yazo ya Dade karshen Shekara ne in kuma ta kama yazo din yakan zo yayi kwana uku hudu ya koma Gabadaya Rayuwarsa a Madina ce achan ya Farota kuma achan zai karisa Domin har gidan zama ya mallaka anan kusa da Jami"ar Musulunci na Madina afarko acikin Jerin Gidajen Malamai na Cikin makarantar ya fara zama sai dai Umar mai Kokari ne Tuni yayi Fafutuka ya mallaki nasshi Da Taimakon Uban Dayake Dashi achan Wato AbuKattab.
Sai Nazir wanda shine Dan Boko ne Yayi Duka Karatunsa Har matakin Master yanzu yana Lagos yana aiki da Hukumar Tattara Haraji na Kasa Wato (FIRS) Federal inland Revenue Service,Yana da Matar aure Daya mai Suna Hedaya da ya"yansu Biyu Matarsa itama yar Boko ce yar gidan masu kudi ce Babanta ya rike Alkalin alkalai na kasa gabadaya Shiyasa Rayuwarsa kamar ba D'an Malam ba Cikin Boko da wayewa shi da ya"yansa Yana zuwa gaida iyayansa ammh matarsa bata cika zuwa Gumel ba sai ya zama Dole.
Sai Nazir Da ke matsayin Likitan yara yana aiki a anan asibitin gwannati na Garin Gumel bai jima da Aure ba Lokaci Daya sukayi Aure da Jafar din Baba Sa"idu shima yayi karatu Abunda ya shafi harkan Tattalin arzikin kasa ya karanta sannan yazo yana aiki da Wani kamfani na Sarrafa Takin zamani gefe Daya yana Taimakama Baba Sa"idu kan Harkan gidan gona.
Aisha da Abida basu yi aure ba sai Hannatu,Aisha tana daga cikin wadanda za"a aurar dasu wannan Shekarar sai Dakin Hajiya Uwa Nazem yana Abu zaria inda yake Masters dinsa Shi da Uzairu dake matakin Degree dinsa Nazifa tayi aure Umaimatu na nan sai Shamsu dake Gabda kamallah Secondary School alokacin..
Sai Dakin Anty Nasara Fatima Tayi aure ta nan a garin Dutse sai Akila Dake aure a Katsina cikin Masaurata,sai Ikram wacce itama Tana cikin amaran da za"a aurar dasu alokacin Sai Akilu da Zubairu dake matakin SS1 amakaranta Dayake basu da nisa Haihuwan nasu kusa kusa ne..
Sai Anty Amarya,itama Jidda na gidan Auranta anan Kano,sai Sadiya da itama tana cikin Amaran wannan Lokacin Sai Sa"adatu Sa'ar Hannatu ne Sai Sabeehatu yar kimanin Shekaru goma da wani abu.
Bazan ce gidan Baba Malam ba"a zaman Kishi ba A"a ana kishi sosai da Takun Saka ammh cikin Ilimi da Hikima Baba Malam Tsaye yake kan gidansa da tarbiyan ya"yansa sannan Hajiya Babba ta Dauki wannan Girman Daya bata Duk matar da zai aura sai ya sanar da ita ta bi shi tayi mai Biyayya kamar yadda zatayi ma Hajiya Babba.
Tsakanin Hajiya Babba da Hajiya Uwani sun fi Shiri hatta ya"yansu ma sun fi Jituwa Duk da ya"yan gidan Gabadaya ahade suke basu da Rabuwan kai sannan Anty Nasara ta Ware kanta Daga ita Sai ya"yanta yayinda itama Anty Amarya ta ware kanta duk da Anty Nasara taso su Hada kansu kamar yadda su Hajiya sukayi sai Anty Amarya taki bada Dama ta Nuna kowa nashi ta Fisheshi.
In ma akwai wacce Kishinta ke Bayyana afili Anty Amarya ce tana Takama ita Amarya ce sannan haka Allah yayo ta in bata yinka bata iya Boye maka don kaji Dadi ko acikin ya"yan gidan ba da kowa take yi ba,Shiyasa kowa yasan inda ya Ijiyeta Duk da Aurattaya ya shiga Tsakaninta da Hajiya Babba basa Shiga Harkan Juna Hajiya ta kama kanta Ta ja Girmanta Dole Anty Amarya take bata wannam Girman a matsayinta na Uwargidan Malam kuma uwa ga Mamyan ya"yansa.
Auran Umar da Sakina Rana Tsakane Domin ba wanda yayi Zato ko Tsammani Sai dai kuma Daya Furta ko Hajiya Babba bata kushe Zabinsa ba ammh Ranta taso ya nemi Daga waje ne,ita kuma Har acikin Ranta taso Cikin Manyan ya"yan Baba Sa"idu ne sai kuma hakan ta Faru ko Mallam bata Furtamai ba batasan Shima aransa yaso hakan ba Har yau har gobe auratayya Tsakanin ya"yansa da na Baba Sa"idu bai Shiga ba Duk da yana da Burin haka sai dai bai yima ya"yansa Maza Auran Dole Samin Halin Rayuwa kada azo a Samu matsala Sai dai shi yake kokarin Zabama Matan Inda ya Dace dasu Tunda su tundaga matakin Haihuwansu har girmansu suna Under Contorl ne kuma Har yau har gobe ya"yansa suna Alhafari da Zabinsa sannan inda yakai suna Alfahari dasu Saboda sun Samu Wadattacen ilimi da Tarbiya.

A Gidan Baba Sa"idu ma akwai Mata guda Biyu Hadiza da yara ke Kiranta Yaya sai Baralaba da yaran ke kiranta Mamanmu Saboda Gabadaya yaran danatan da ba natan ba Duka Dayane a wajenta itace komai nasu ita Yaya kamar yar kallo ce acikin Gidan
Yaya nada ya"ya bakwai ne Jafar ne Babba sai Jadwa sai Jaleela sai Jamela sai Jawahir sannan Amina sai Jawaad Dakin Mamanmu kuma ya"yanta biyar Zulfa ce Babba sai Fatima Zahra sai Zulahait sai Zeenatu sai karamarsu Hamida.
jadwa tana auran Yaron Goggo Husai kanwar Baba Sa"idu Dake chan Jordan tana chan itama sai  Jaleela Dake auran Abokin aikin Ya Nazir wanda Sun zo Tare ne ya ganta yayi ma Malam mgana Akayi Bincike aka gano na gari ne aka bashi Tana chan Lagos din da zama Duk da shi ma Dan Jahar kano ne.
Sai jamila Dake  Gombe Tana auran wani Contoroller ne ma"aikacin Costume ne,Sai Jawahir Data Tafi Gusai Tana auran yaron wan Baban Baba Sa"idu ita auran gida tayi tana chan gusai ba kasafai suke zuwa gida ba Malam ya hana sai da wani Dalili mai karfi.
Sai Zulfa itama tana Zaria Tana auren wani Lecture ne Awajenta ma su Nazeem suke zaune Tunda suna Cikin Jerin Gidajen malama ne na Abu zaria,sai Zahra Dake parthorcourt Tana auran wani Mai kwangilan Titin Sama ne sai Zulahait da wannan Lokacin ne za"a aurar da ita sai Zeena mai bi mata sai Hamida wanda Tsakaninta da Amina Wata Uku ne
Amina ce aka fara Haihuwa sannan Hamida,Rayuwar Gidan Baba Sa"idu Kamar Rayuwar gidan Baba Malam ce Domin komai Tare suke Gudanarwa sannan Gabadaya Doka da Tarbiyan Lokaci Daya take aiki bama Haka ba Baba Sa"idu Tarbiyan Malam ne ko shi baya Tsallake mganarsa Ballatana Iyalansa.
baza'ace Duka gidajen yaran basa Samun Sakewa ba A"a sai dai ba irin Sakewar nan ta ya"yan da suka Samu gata mai yawa ba suna cikim jerin ya"ya masu samun komai na Rayuwa cima mai kyau Sutura mai kyau komai Tare Baba Malam ke gudanarwa ba Nuna bambamci Gabadaya makaranta Daya suke yi manyansu da yaransu in Sallah Tayi kaya iri Dayame kuma Duka Mallam zai bada Umarnin Asiya Baka Taba Nuna wani bambamci Tsakanin ya"yan Gidansa dana Baba Sa"idu.
Suna Samun ilimi sosai Da Tarbiya Mata basa Rike waya sai agidan mijinki Wani Daga cikin su tun kan su Jadwa ba wacce tataba Tsayawa da wani Namiji a waje Da sunan Zence sai wanda zaki aura zaku gana afalon Baba Malam ko Falon Baba Sa"idu ba inda suke zuwa Daga makaranta Sai gida shima mota ce kai kaisu ta Dawo dasu basa ma Fita Ballatana Har wani ya Taresu su Rayuwarsu tana cikin Gida ne sannan Gidan Baba Malam da Baba Sa"idu ba"a Kallo basu ma da kayan kallo Saboda gidan Mahaddata ne ba"a Saka Musu abunda Zai Dauke musu Hankali.
Sannan akwai girmamana na gaba Dakai ba Rashin kunya Yaro ko kwana Daya ya baka Dole ka Kirasa Yaya kuma ka Girmamasa Dole kuma in yayi maka Hukunci ka karbeshi Haka suka Taso Tundaga Tushen manyansu har kawo yanzu suna girmama juna da ganin Darajan juna.
Ba"a taba Haihuwar Mara kunya Mara jin mgana irin Amina ba,Tunda aka Haifeta tazo Duniya ba wanda ya Huta da Fitinarta da Jidalinta ita Kadai ta Fara Rashin kunya da kin girmama na gaba da ita tun Tana karama sannan ita kadai ta fara yin abu gaban Kanta Amina ba irin Sauran yara bane Duk wannan Hallayar nata yarinya ce mai Shiga Rai Aba yana Matukar Kaunarta Ballatana Datake bala'in kama da Yaya Hadiza sanda sukayi aure ba sonta yake yi ba ammh Hakurinta Sadaukarwanta Nasabanta Kirkinta yasa Ta samu Matsayi mai girma acikin Ransa tana da Kimar da Har Abada wata mace bazata kamota aransa ba.
Ba shi kadai ba ya zamo Hatta Baba Malam yana Kaunar Amina Saboda Baba Sa"idu yayi mai kara ya saka sunan Mahaifiyarsa yasa tun Amina na karamarta ta fara Bude ido da Kaunar Baba Malam gareta Har girmanta kuma wannan Kaunar shi yajamata Bakin jini wajen Ya"yan Anty Amarya da suke ganin Baba Malam na Fifita Amina akan Ya"yansa
Tun Tasowarta tare sukayi wasan kasa da Hanne da Hamida da kuma Sa"adatu daman Tun alokacin ba",a Shiri kafin agama wasa ayi Dambe fin sau Biyar wannan Kiyayyar tasu ba ta yau bane Ta Dade a zukatan junansu Sannan Kaunar Junansu Tsakanin Hamida da Hanne Daga Allah ne Duk kuwa da Amina ta fisu Baudewar Hali Ammh suna Tare da ita kowani Jidali ta Debe suna Daukansa ya koma kansa..
In nace Amina ta gagari kowa Zaku yarda..?duka ko Fada baya mata komai Domin in duka nasa yaro ya Natsu da ba haka ba sai dai bata Jin ko Daya ba wanda ya isa ya hanata abunda tayi niyya Duka baya Damunta Domin ya Zame mata Jiki Aba tun baya Damuwa da Lamarinta Har ya fara yana Tunanin kada watarana Ta fita zakkan da zata sakamai wani Cutar da zai kaisa kasa ganin Tun tana da kananun Shekarun Idanuwanta a Tsaye suke basu da Ladabi ballatana su Rankwafa.
Goggo Husai taso ya bata Amina Tatafi Da ita Saboda Duka ya"yanta Manya maza ne macenta Dayane kuma Tayi aure Baba Sa"idu ya Hanata Saboda yana Tunanin anan ma Amina ya aka kaya ballatana taje Cikin Jajayen Fata hakanan yaji gwara Tana gabansu da wata uwa Duniya Malam ma bai amince ba yace Amina zata Sauya Har yau har gobe yana ganin yarinta ne ke Damunta.
Baba Malam bai manta da gida ba Yana Zuwa bazanga kaima yan"uwansa da suke Rage ziyara suma suna zuwa sannan Duk Shekara achan yake Fidda Zakka Sannan Har alokacin ana Nomamai Gonakinsa Daya gada wajen Mahaifinaa sannan bai daina yawon Da"awa ba yana cikin Malaman Kungiyar Sunna alokacin ba garin da basa zuwa Da"awa ko kuma wani Taimako in wani abu ya taso bai da matsala Baba Sa"idu na kan komai zai kuma Kula da komai kamar yadda ya Sani.
Hajiya Babba itace Uwa bada Mama ga Baba Sa"idu ko ya"yanta sun sani in Abu ya Shafi. Baba Sa"idu Hajiya bata Zaune bata Tsaye gabadaya ya"yansa matsayin kaka suke kallonta Tasha Fadi Sa'idu babban yaro na ne Balle da bata Kiran sunan Umar sai dai tacemai D'an mallan sunan Daya bisa Har yau bamai kiran sunansa sai Yaya D'an Malam in ya nuna jin Haushinsa sai tayi Dariya Har ce mata ya Taba yi Hajiya meyasa ni bakya Kiran sunana..?ammh kuma kina Kiran sunan Baba Sa"idu..!
Dariya take alokacin sai tace"Sa"idu babban yaro na ne..Dashi na Fara sanin Soyayya ya"ya Shiyasa bana masa alkunya..!
Tabbas bata masa alkunya Wani mtsalan nasa Baba Mallam saidai yaji sa bakin Hajiya akwai Fahimtar juna da Shakuwa Tsakaninsu hakama Hajiyar ko wani abu ne saita Dauki Waya ta Kirasa Sa"idu in ka dawo kazo ina nemanka..Ko ya"yanta basu isa su san Tsakanin Hajiya da Baba Sa"idu ba,ita din Uwace garesa bada Mama ko Baba Mallam wani Lokacin sai yace suna mai Wariya da yan Ubanci fa Shi Kanshi yasani Haihuwan Sa"idu ne kadai basu yi ba ammh Suna mai kauna irin wacce ko ya"yan Cikinsu basu yimawa.
Shi kanshi Baba Sa"idu haka yake jinsu Ammh Duk da Haka baai yada Danginsa na Gusai ba suna zuwa shima yana zuwa ballatana Har gaban Abada bazasu Daina Labarin kima da Dattakon Baba Malam ba..!
Koda Yaushe suka zo ko Sa"idu yazo Sai sun Fadamai ya yi ma Baba Malam Biyayyah Shi din Uba ne Cikin Dubu sai antona Gaskiya suka Fada In yana Kallon Alkhairan Baba Mallam zuwa garesa sai yaga yafi kowani Da Sa"an Uba awannan Duniya Soyayyar da ko su Umar basu Sameta ba Sa"idu Shi kadai ne Mallam bai Taba Hadasa da wani ba kowa ya san da wannan ba ga ya"yan nasa ba har ga Matan nashi.

Wannan kenan ..!

******
Tare suka Fito Daga massalaci Dayake bayan an idar da Sallar Isha"i Baba Malam yakan dan yi jan Hankali kan masu wasa da Sallah na Tsawon Mintina Ashirin kafin su tashi Sun Dade acikin masallacin shi da Baba Sa"idu kafin su fito Daga Masallacin Kai tsaye Falon Baba Mallam suka shiga
Baba Malam na zama Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon lokaci Daya yana gyara zaman alkyyaban Jikinsa Cikin Nazarin Baba Sa"idu Daya Duka gabansa kamar me neman gafara yace"Sa"idu da wata mtsala ce..!
Baba Sa"idu ya Dago yana kallon Baba Mallam kafin ya maida kansa kasa yana Fadin"Eh Malam...Kun yi mgana da D'an Malam cikin kwanakin nan kuwa..?
Baba Malam na Cire gilashin Dake Idanuwansa yace"Eh mun yi mgana Dashi yace suna tafe cikin Satinan..Sai dai bamu yi wata mgana ba..Ammh in ban Manta ba har alokacin yace min Baba Malam Baba Sa'idu bai ce maka komai ba..?Tun da naji haka nasan Yan"uwan juna sun yi abun da suka saba..Nasan da wani abu Saboda haka ina jinka wani Laifi ya aikata yau kuma ya Labe abayanka..!
Ya fada yana Kayattacen Mirmishi Baba Sa"idu na sosa kansa shima yana Dariya Baba Malam yana da Saurin gano Mutun yasan indai aka Fara wannan Zagayen Zagayen wani abu ne ya Faru asan Sa"idu Dabam ne a wajensa Dashi yaran suke kamun kafa in suka aikata wani abun ko kuma suna son suyi wani abun da  suna Tsoron yima Mallam mgana Kai Tsaye.
Baba Mallam ya kara Muskutawa yana Fadin"Uhm ina jinka...Meya faru ko ya fasa zuwa Bikin kennan nasa ne..?
Da Sauri Baba Sa"idu yace"A"a yana nan tafe..yau ma yace ma Jirgin kayansu ya taso zuwa gobe zai kariso nan..!
Baba Malam ya gyada kai yana kallon Baba Sa"idu wanda kansa ke kasa Kafin yace"Dama..Dama yace na Fada maka ne..Abukattab ya basa auran yarsa Sarood shi kuma bazai iya masa Musu ba ya karba..!
Baba Mallam bai Sauya Fuska illah Cewa da yayi"Ina ce ba an Daura auran Jiya ba..,?
Da mamaki Baba Sa"idu ke kallonsa kafin ya jinjina kai bai basa Zarafin mgana yace"Abokina bai Rufeni ba kamar yadda kuka Rufeni..Bai Fadamai bane ammh bai Daura masa aure Yarsa ba sai da Izinina..!
Baba Sa"idu ya washe baki yana Fadin"Allah kara girma Baba..!
Dariya yayi kafin yace"In kunyi waya ka Fadamai nasan komai..Kuma har munyi mgana da Kattab da ita zai zo Gida Taga Dangi..Wannan Abu ne mai kyau kuma Sunnar ma"aiki ne Sallalahu alaihi wasallam,Sannan kuma Kattab ya wuce wannan a wajena ballatana Wajen Umar..Ina Farincikin Shigowar Zuru"arsa Cikin Zuru"ata Allah ya Zaunar dasu Lafiya..!
Baba Sa"idu nata amsawa da Ameen Baba Mallam ya cigaba da Fadin"Ya mganar

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment