Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naga Haske guda Biyu na wata da kuma kananun Taurari Madina sai dai acikin hasken Duhu ya mamaye ganina ban fahimci wani abu ba..!
Anty Amarya taji kamar tayi Fitsari Saboda Tsoro Cikin rawan murya tace"Menene Mafita mallam kaina ya Kulle..?
Mallam yace"Muna kan Bincikenmu ne Madina..ammh Zata tare tabbas..Sai dai zan kara Lalata Tunanin yarinyar wajen kara yawan Tsiwarta da rashin Da"a ga shi Mijin..Sannan na saka tashin Hankalin a Tsakaninsu yadda zaman bazai Dade ba zai lalace na fada miki Aiki Daya muka taba yi kan Shi yaron ya kamasa yanzu haka aljanunmu baza su iya Tunkararsa ba,Yana da Tsari sannan iyayansa Biyu suna Tsaye a kansa ne Shiyasa aikin namu zak fi karfi kan yarinya da dama Tun farko mun samu nasara akanta Sarrafa Tunaninta bazai mana Wahala ba..Kada ki yi wani yunkuri..Zata tare tabbas in kika hana Faruwar haka Madina wani kullin zai Lalace kuma Faruwar haka tamkar Rugujewar Duka aikin ki ne ki kiyaye..!
Kit Kawai taji Anty Amarya Cikinta taji yana Faman juya mata Innalillahi kawai take fadi afili in Har asirin data Binne ya bayyana ta shiga uku ta Lalace Cikinta ne yayi wani yi kara Kuuuu..Data saki waya ma bata sani ba,Ta kwashi gudu zuwa Tiolet kafin ya Zubo mata tana hawa kan sit din Kikaji Zuu..Zuuu..Sai kuma zufa ta koma ta jingina da bango tana ajiyar zuciya Yadda take jin kanta kamar zai Rabe gida Biyu..!
Mafita take nema ido Rufe kafin komai ya kwace mata ta Dade kan masai din tana zawo zawon tsoro da Firgita kafin ta Dauraye jikinta ta fito Tana ji ana kiran wayarta sai da ta Fito ta Duba Dayyaba ce Tsaki taja Domin duk itace silar lalacewar komai nata in da ta amince sun Kauda Amina da yanzu wata mganar ake yi ba wannan ba,Ta fara Tunanin ko Dayyaba ta na so ta juya mata baya ne saboda ita ta samu cikar nata Burin eh mana ko bata samu duka ta fara Hawa matakin nasara Yaya ta bar gidan Duniya ya'yanta sun dawo karkashinta sa"idu yanzu nata ne ita kadai ai kadan ya rage mata ta cika Burinta ita kuma yanzu abubuwa sun fara Lalace mata daga wannan sai wannan kuma duk sanadin wannan shegiyar yarinyar da shiyasa bata taba kaunarta ba..!
Gefen gadon ta koma ta zauna tayi Tagumi hannu Biyu tana Tunanin mafita ta Dauki tsawon Lokaci ahaka batasan sakina ta shigo ba sai da taji Muryanta saman kanta sannan ta Dawo Hayyacinta yadda idanuwanta suka Fada ne Lokaci Daya yasa Jikin Sakina ya kara yin sanyi cikin Damuwa tace"Anty na jiki shuru ne tun dazu shiyasa na shigo naga ko Lafiya..Na sameki cikin Tunani ina ta mgana baki jini ba..!?

Anty Amarya ta kasa mgana Sakina ta Kurama ido na wani Lokaci kafin tayi Zaraf ta mike tana Fadin"Ke wani ya ganki sanda zaki shigo..?
Da sauri ta Girgizakai ajiyar rai ta Sauke kafin tace"Tashi tashi maza mu tafi..!
Sakina tace"ina kenan Anty..?
Tana kokarin Daukan Hijabinta Cikin Wardrope dinta tace"Gidanki zan maidake sakina..Dole zaki koma Domin chan din ne ya Dace Dake..!
Sakina ta saki baki kafin tace"Yanzu sai naje nayi zaman kishi da wannan yarinyar..?Haba Anty kin manta kin Fadamin hakan bazai faru ba indai kina Numfashi..!
Anty Amarya da ranta ya gama baci ta Juyo tana Fadin"Ke sakina kada ki koma don Ubanki..In kin koma kinci Ubanki nace..to gani da Numfashina Amina zata tare agidan da na gama Tsara ke kadai zaki dinga juyi acikinsa..Wannan karon ba kamar Zuwan wannan balarabiyar nan bane..Wannan mganar ta girmama Hajiya da Mallam ne kuma kinsan babu mai ja da su..ki zauna kina ji kima gani Amina zata tare ta samu Ciki ta Haihu ni dake mun zama yan kallo,ke ba auran ba,ba kuma miji ba Sannan ni kuma kin jamin raini sannan kin saka mafarkina na mallakan gidanan ya tashi a banza Sakina Kada kije ki koma ki zauna ni Dake mu Taru mu rushe gabadaya..!

Ta karishe Fada cikin wani yanayi Lokaci Daya tana komawa ta zauna gefen gado tana jijjiga kafa kamar ta Rufe Sakina da Duka haka take ji.
Sakina ta fashe da kuka kishi da Bakincikinta sun cika mata Kirji Cikin Wani yanayi tace"Haba Anty wannan yarinyar fa..?Wlh bazan iya jure zaman waje daya da ita ba..Dama zaki rokar min Umar ne ya amimce ya koma da ni Madina shikenan sai na Biki mu tafi..!
Anty Amarya ta mata kallon Tara saura kwata kafin ta mike tana Fadin"Kinga in zaki tafi ki zo mu tafi..In bazaki jeba shikenan mu koma mu nade hannu mu zama yan kallo..Wahalarmu tatashi a Tutar babu..!
Anty bata kara bi ta kanta ba ta Fice Daga Dakin kada ta cigaba da zama Sakina ta cikamata ido ta kaimata Duka Tana zaune afalo tana jiran taga Sakina zata fito ko kuwa kasa Zata watsa mata a ido sai gata ta fito Idanuwanan sun kumbura saboda kuka Anty Amarya tayi Mirmishin Nasara kafin ta Mike tana Fadin"Muje na maidake..Karaya ba Halin Madina bane..Ita Nasara insha Allahu Tamu ce Sakina..Kafin su kaita zasu tarar dake agidan Mijinki..Ita ai aro muka bata nan da wani Lokaci zata zama tarihi..!
Sakina sai taji ta samu natsuwa Daki Anty Amarya ta koma ta Dauko wayarta ta Karamar jakarta ta saka Sakina gaba suka fice daga gidan ba wanda ya gansu,Mallam kuma shashensa a kulle kila ya fita adaidaita suka samu suka hau zuwa kofar arewa..!
Buga get din sukayi megadi yazo ya Bude musu bayan yaga sune,Sakina na kan gaba Anty na bayanta suka Shiga Falon gidan da sallama ba kowa Tsit kamar ba Mutum acikin gidan
Anty Amarya tabi Falon da kallo kafin ta kalli Sakina tace"Naji gidan tsit..Ko ya fita ne..?
Sakina ta zare mayafin Jikinta tana Fadin"Bana jin ya fita..ga motarsa chan a haraban gida..a dakinsa na barosa koda na fito Dazun..!
Anty Amarya ta samu Daya Daga Cikin kujerun falon ta zauna tana Fadin"Shiga kicemai nazo ina son mgana dashi..!
Sakina ba Musu ta Nufi Dakinsa Knooking ta farayi taji gyaran Muryansa kafin ta Tura kai ta shiga Dakin komai nashi Baki da Fari ne makeken gado da wardrope sai Cafet sai Madubi,Yana kwance kan gado yayi kwwnciyar Ringigine yana kallon p.o.p din Rufin Dakin yayi matashi da Hannayensa bai da Riga Dogon Wando ne baki ajikinsa Gabadaya Kirjinsa yana waje inda Gashi suka kwanta Luf.
Idanuwansa suna Rufene kamar mai barci sanda ta shigo Dakin yana jinta ammh bai Motsa ba saboda Halin Dayake ciki baya Bukatar hayaniyar kowa akansa yana jin sanda ta Fita bai yi kokarin hanata ba saboda ba shi da kwarin gwiwan Daukan kokenta na banza shi kanshi inda zai yi kukan Dayaji Dadi Ransa gabadaya a jagule yake tsammanin abunda bakayi Tsammani ba baida Dadi sam.
Gefensa ta zauna tana Fadin"Habibi Anty na Falo tana son mgana Dakai..!
Kamar bazai yi mgana ba ta kafeshi da ido tana kallomsa yadda taga kamar yadan Fada mata a fuskarsa da Wuyansa.
Ji kawai tayi yace"Karata kika mata sakina..?
Yafada cikin Sanyim muryansa kamar koyaushe,Da sauri tace"A..a..!
"A"a ko Eh..!
Ya fada Lokaci Daya yana Bude Idanuwansa kuma ya tashi Zaune yana kallonta sai taji ta Daburce ta kasa kallonsa idonta na kasa tana wasa da Zoben hannunta.
Bai kara ce mata komai ba ya Zuro Santala santalan kafafunsa suka nutse saman Italian Cafet din Dake Dakin ya Mike Tsaye yana Fadin"Kije gani nan zuwa..!
Ba Musu ta mike ta fice Daman ta Kosa ta Fita Kwarjininsa yafi na koyaushe bata so ya Tsareta da wannan kallonsa da yake sakawa ka kasamai gaddama ko Karya.
Wajen Anty Amarya ta koma tana Fadin"Gashi nan zuwa Anty Don Allah kiyimai mganar tafiyata..!
Anty zatayi mgana kenan Kamshin Turaransa ya sanar da su zuwansa Falon suka Dago suna kallonsa atare Jallabiya ya sanyo saman wando jikinsa Fara Tas da ita,Anty Amarya ta kalli Sakina tana fadin"Koma kasa ki zauna mara kunya..!
Ba musu ta sulale a kasa shima saman Cafet din ya zauna yana gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin yadda yanayinsa yayi wani iri duk da daman bamai gane yanayinsa koda yaushe haka yake.
Kansa na kasa Anty Amarya tace"Ina gida dazu sai ga Sakina tazomin da kuka..ni Hankalima ma har ya tashi na Zata matsala kuka samu..Sai Daga baya take Fadamin wai ka Fadamata Amina Zata tare yau shine tazomin tana min kuka kaji wani Sakarci Umar..?
Kansa na kasa shidai bai ce mata komai ba Sakina ce ta Dago tana kallonta ta Rakata da Harara kafin ta Dauke kanta ta maida kan Umar tana Fadin"Tana fadamin haka ban yi mata da wasa ba nayi mata Fata Fata..Nace wannan ai Sakarci ne..Mallam ya Fadamana da Safe zemcen Tarewar kuma in banda abun Sakina Amina ai kanwa take gareta keda zaki kwantar da Hankalinki ki jata ajiki ki Riketa amana kamar yadda kike rike Sarood ai kece babba Kece zaki samar da zaman Lafiya agidan Mijinki ammh baki dunga wannan Sakarcin ba..Gatanan Dukanta ne kadai ban yi ba sai ta fara kuka tana bani Hakuri nace bani zata bama Hakuri ba sai zata zo ta baka hakuri nace mata me zai dameta ai bata tashi Hankalinta Lokacin auranka da Sarood ba sai kan Amina ta gida ku zaku hade kai ma a matsayinku na yan gida Daya haba Sakina..
In kaji yadda na dinga mata fada sai kace na Sauraramata ta gane kuskusranta Daman kishi ne na hallitar mata ya Rufemata ido..Shine data gayamin bakasan ta fito ba na Daukota kafa da kafa nazo baka Hakuri..Dom Allah Umar kayi hakuri ka kuma Cigaba da Hakuri Nauyi ne ya karu a Kanka sai ka kara Hakuri kasan mu mata sai a hankali Wani Lokaci ana taromu ne muna karkacewa..!
Ta karishe fada tana yar Dariya kansa na kasa yana Sauraranta aransa kuma Dariya kawai yake yi wai ta mata Fada Sakinar ce zatayi ma Fada daman baisan yadda batason damuwarta bane sai dai ko ba domin Sakina ba Anty Amarya Matar Uba take garesa zai bata girmanta yasa ya jinjina kai yana Fadin"Bakomai Anty komai ya wuce..!
Anty Tace"Yauwa nagode..Allah ya Zaunar daku lafiya ya kade Fitina..!
Da ameen ya amsa kasa kasa Sakina ke Zungurin kafarta yasa ta gyara Zama tana fadin"Sannan naji wata mgana Umar..Sakina tace min kace baza ta bika ba madina ba yanzu..?

Sai alokacin ya Dago kansa ya Kalli Sakina kafin yace"Eh Anty..Bata fada miki yadda mukayi da ita bane..?
Anty Amarya tace"Ta fadamin nayi ta Fada kamar zan ari baki..Wlh bansani bane dasani ba zata zo ba don Ubanta Sakarci ke Damunta..Don mai garinku bashi Hakuri yanzu agabana..!
Tafada tana Dungurin kan Sakina wacce ta rankwafa tana Fadin"Kayi hakuri..!
Kallonta yake yi bai yi mgana ba yana Rokon Allah kada kafin ya koma Sakina ta Cikashi taga dayan kalansa Taga bacin ransa.
Ganin yayi shuru yasa Anty Amarya tace"Ta baka Hakuri Umar don Allah ka yafemata in ka tashi komawa sai ta Bika ku koma tare..!
Umar ya Dago kansa kafin yace"Anty mi batamin komai bafa..Mgana Dayace na riga na Rantse bazata Bini ba..Nan din Datake so nan zata Zauna Insha Allahu..!
Sakina ta kalli Anty Amarya itama ta kalleta Cikin Takaicinta alamun ta kara Rokonsa tayi mata bata sani ba Duk yana kallonta aransa yace zaki gane baki da wayau ne sakina..!
Anty Amarya tace"Kadai yi hakuri..In ba kudin Visar ne ni zan Biyamata sai ku tafi taren kaji..!
Kai Tsaye yace"Chan din in ta taka ta koma to bada yawuna ba Anty..nima ban rasa kudin da zan Biyamata ba kawai Ra"ayina ne bazata Bini ba..Ita ta sani nayi Rantsuwa kuma akanta bazan yi kaffara ba Wlh anan zata zauna sai sanda naje na dawo..!
Sai dukkansu suka kasa mgana Anty Amarya ta mike tana Fadin"Shikenan gwara kayi mata haka ko zatayi hankali..Ni bari na tafi.Allah ya kyauta..!
Ya mike Tsaye yana fadin"Ameen Anty Idi ne ya kawo ku..?
Anty Amarya tace"A daidaita muka zo..Idi kila sun fita da mallam ne..!
Da Sauri yace"To bari nazo na kaiki gida..!
Da Sauri tace"A"a ka bar shi kawai Nagode..!
Daga haka ta kalli Sakina ta Harareta Kafin ta fice Umar ya fita ya Rakata har waje ta samu adaidaita ya biya mata Drop suka wuce.
Daganan bai koma gidan ba takawa yayi da Kafafunsa zuwa masallacin Dake gaban gidansa Uku da wani abu Lokacin La"asar ta kusa cikin masallacin ya shiga ya zauna yana Faman Tunanin ta ina zai fara zama da yarinyar nan gabadaya Bata dace da Rayuwarsa ba ga Sakina ita kuma kamar wata karamar yarinya ta fara rashin jin mganarsa Lallabatan Dayake yi yasa ta fara Tunanin ya sakar mata ne tarika abunda taga dama..!

*****

8:30pm

Misalin karfe  Takwas na Dare Hajiya Babba da Hajiya Uwani suka shigo gidan Sa"idu domin tafiya da Amina wacce tunda suka dawo daga gidan Kitso gabda mangariba,Anyi ma Amina Kitso mai kyau da kunshi ja da baki,salla kawai sukayi ko abinci basu ci ba ya Jafar da ya Nasir suka Shigo Daga masallaci suke suka Kira Amina Dakin yaya ba abunda basu Fadamata ba, ba Lallashi bane Fada ne da Umarni ya jafar ya Jaddadamata bar ganin zata koma chan da zama Wlh Tallahi ya rantse ya kara rantsewa intayi wani abun da ta saba na iskancinta Har chan zai taka ya mata Dukan Tsiyan ya Nasir ma yayi nashi Fadan shidai fadi yake kada Allah yasa tayi hankali Tagani wuya ce zai sa tayi hankali Tunda suka fara mata Fada take ta kuka kamar ranta zai fita,Basu Dade ba suka yi ma mamanmu sallama suka tafi Shikenan fa Amina ta cigaba da kuka su Hanne ma suka kama ko abimci sum kasa ci,Duk da suna jin yunwa Dakyar mamanmu ta matsa Amina tayi wanka ta shirya cikin Less din Bikin su ya Abida riga da sikat da Hijabi Fuskarnan duk ta Kode saboda kuka.
Sanda Hajiya suka shigo sai Amina ta Kara gasgasa cewa da gaske fa Wani Sabon Shafin Rayuwar ya kara Bude mata batare data shirya ba,Barin ma d Su ka shigo da su Ya Akilu suka Dauki kayan Amina ghana Must go uku Duka an cika harda Takalman makarantarta da Jakarta komai nata dai an hada mata Hajiya tace su kai Falon Mallam Amina ta waiga taga wajen Dirowarta wayan ba komai kawai sai ta sulale kasa tana ta kuka Mamanmu kuwa baya ta juya tana Sharan Hawaye makirci da kuma rashin mafita

Hamida da Hanne kuka suke kamar ransu zai fita Harda Jawad ma kukan yake yana rike Amina yana fadin"Ya Amina ina zaki je kina ta kuka..?
Hajiya dai bata ce musu komai ba Hajiya Uwani ce tace"Kai kubar kukan nan hakanam mana Balaraba har da kema..?
Keda zaki lallashesu..Kudaina kuka ku taso muje ku raka Amina Dakinta..!
Hajiya tace"A"a Mallam ya Kira Danmallam shi zai zo ya Dauki matarsa su tafi..!
Sai su ka kara saka kuka Haj.Uwani na Dariya tace"To kuyi hakuri Bayan kwana Biyu sai kuje ku wunin awajenta ko..!?
Wayar Hajiya ce ake kira yasa ta Daga tana Fadin"Kun gani mallam ne ma..!
Da sallama ta Daga Kiran Mallam ya amsa Dagachan bangaran yana Fadin"Hajiya kuna ina ne..?Ga Umaru tundazu yazo yana jiranku..!
Hajiya tace"Gamunan yaran ne ke ta koke kokensu..!
Mallam yayi Mirmishi kafin yace"Ku taho dasu dukkansu mu lallashesu hajiya..Ba su ba har ni zan yi matukar kewar Mamana..!
Daga haka ya katse kiran Hajiya ta kalli Mamanmu tana Fadin"Balaraba Hakuri zaki yi..Dauko Mayafinki ki mika Diyar taki Falon malam..Haj.Uwani Taimaka ki Lallaso su hannatu mallan yace muje gabadayanmu..!
Mamanmu na Sharam kwallah ta Sako Hijabinta ta riko Amina Dake kuka Hajiya uwani kuma ta Lallaso su hanne suka mike suka fito tare Hajiya Babba na gaba Tare da Mamanmu da Amina dake kuka cikin Hijabinta su Hanne da Hajiya uwa na baya Har da Jawad shima yana Hawaye har falom Baba mallam Dake cike dasu Aba sai su ya Jafar da Ya Danmallam
Yadda Aka shigo da Amina na kuka ko Aba sai da anbun ya tabasa Danmallam kuwa aransa yasan ya shiga uku Kwalin panadol zai siya kafin ya koma domin shi da ciwon kai Salamu alaikum sun kulla abota

Gaban Aba da Mallam suka Direta Hajiya tace"Gata nan ka mika amanarta Hannun Da"nka..In yaci Amanar Amina Ka fadamai Bazan taba YAFEMAI BA..!

Tafada cikin son tabbatar da mganar Danmallam kansa na kasa bai ce komai ba Aba ne zai yi mgana Hajiya ta katse shi da Fadin"Kayi mata fatan Alheri Sa"idu!
Shiyasa ya kasa mgana Amina ya kallah yadda take kuka ya tabasa sai kawai ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Amina..Allah ya albarka ci auramku..Nima na Fada kuma zan kara Fara koda Sau Daya in kika Sabama ma Umar gashi nan Amina BAZAN TABA YAFE MIKI ba..!

Cak kukanta ya tsaya kowa kuma Aba yake kallo shi kuma ya kara kausasa Muryansa yace"In kika basa Wahala Amina keda Allah..In kika Bijirema Umarninsa Keda Allah..In kika Zame masa Damuwa keda Allah Amina..ki zama Haske garesa sai Allah ya Haskaka lamuranki..Allah ya baku zaman lafiya..!
Yana gama Fadin haka ya mike da Sauri ya fice yana Boye kwallarsa Jawaad yabi bayansa yana kiran sunansa Mamanmu tabisa da kallon Takaici tasan waya tuna yaya ce..Kai Wannan soyayyar dai ko bayan rai ma Ana mararinta.
Baba mallam yayi shuru bai yi mgana ba sai da Hajiya tace"Kaifa Mallam me zakace..?
Maallam cikin wani yanayi ya mike yana gyara Rawaninsa yace"Umaru taso..!
Ba Musu Danmallan da Jikinsa ya Mutu ya mike sanye da shadda Jikinsa Riga da wando Mai ruwan kasa Dinkin Tazarce,ya isa gaban Mallam yana kokarin Dukawa ya saka Hannuwansa ya Rikosa suka karisa gaban Amima ya Duka da kansa ya Dagota yana Fadin"Taso taso..Taso Uwata..!
Ba musu ta mike kanta na cikin Hijabi ya Hada hannunta dana ya Danmallam Dukkansu sai da sukaji wani Dum a Atsakiyar kansu.
Su Hajiya ya kallah yana fadin"Ku zu mu yi musu rakiya..Ina marliya da Nasaratu suke..?
Hajiya zatayi mgana keman sai gasu sun shigo kai Tsaye Mallam yayi gaba Yana tsakiya Amina da Umar suna gefensa ya hade hannayensu waje daya yana fadin"Ku biyoni..!
Ba musu suka bisa a baya Hamida da Hanne suna ta kuka har Haraban gidan Wajem Motar ya Danmallam
Ya jafar ya Bude gaban motar Mallam ya kalli Dammalam yana fadin"Taimaka mata ta zauna mana..!
Sannan ya sake su ba musu Umar ya Taimakama Amina ta shiga Mota ta zauna yana rike da hannunta sai alokacim Mallam yace"Kaga yadda ka rike hannunta tundaga Falona har nan waje...?
Sannan ka taimaka mata ta shiga motarka..!?
To ina so ko ba Raina Umaru kada ka saki Hannun Amina..Da Dadi ba Dadi ka Zama mai Tallafa mata ka zama Ubanta,yayanta,Mijinta Uwarta da yan"uwanta bango mai Bangon Alheri Umaru..!
Kansa na kasa yace"Insha Allahu Mallam..!
Mallam ya kalli Amina yana fadin"Mamana kiyi masa Biyayyah..In kikamai gaddama bazan ji Dadi ba..Allah ya zaunar daku lafiya kuje..Addu"armu da alBarkanmu na Tare daku har abada..!

Shima Hawayen ne suka cika idonsa yasa ya Juya Amina taga ana shirin Rufo mota da ita ga su hanne tana kallo suna kuka ita kadai zata tafi kenan ai sai gani akayi ta wuntsilo Har sai da Danmallan ya riketa Saura kadan ta Fadi kasa hanne ta Tunkara ta Rumgumeta ta fashe da kuka sai Hamida ma ta kara mata Rumfa suka Durkushe suna wani kuka mai Shiga ran mai Saurare Baba mallam Dagachan ya tsaya yana Fadin"Hajiya ku rike su hannatu..Kai kuma Umar rike hannun matarka kuje..!
Daga haka ya juya ya koma Falonsa Hajiya Uwani da Haj.Nasara suka kama su Hamida sai Amina ta koma Wajen mamanmu ta fada Jikinta sai kuka ko ya jafar sarkin zafi bai yi mgana ba ya Danmallam dai na gefe yana kallon ikon Allah yara kamar masu aljanu

Hajiya ta bambare Amina Daga jikin Mamanmu ta Tura ta Mota ta Rufe tana Fadin"Ku tafi UMAR..!
Sai yau ya taba jin ta kira sunansa ya kalleta ta kallesa sai kawai ta juya tana Fadin"Allah ya baku zuru"a tagari..!
Da Mirmishi saman bakinsa yace"Ameen Hajiyata..!
Anty Amarya ji tayi kamar ta Kurma Ihu agaban idonsu ya shiga bangaran Direba ya Tada Motar Amina na kallonsu Hanne da Hamida suna kuka ta mika hannu ta Glass tana kallonsu sai taji kamar zata shide Tunda suka taso basu taba Rabuwa da juna ba sai yau batasan haka Hamida da Hanne suka zama jinin jikinta ba sai yau da taga Rabuwa da su Kirkiri.
Sanda Megadi ya Bude get suka sulala waje ya dauki hanyar gidansa sai Amina ta Juya baya bata ga Hanne ba,Ba Hamida sai ta Juya tana kallon ya Danmallam Dake Driving hankalinsa baya wajenta,Kenan ya Tabbata shine mijinta..!
Gidansa zasu koma..?
Ina Aminu..?
Shikenan ta rasashi..!?
Ta tun yasha Fada mata in bai aureta ba zai lalace..!
Yau zata je ta kwana in da ba hanne ba Hamida ba mamanmu..!
Kawai sai taji Duniyar tayi mata Tsit ta kama kanta ta girgixa kafin ta Daddage iya karfin muryanta ta Saki wani irin kuka..!
Lokaci daya tana Fadin"Wayyo Allah na na shiga uku..Bazan iya ba..Don Allah ka maidani gida..!
Ihun data saki yasa har sun hau kwalta Kansa ne ya sara ya saki Sitiyarin ya Dafe kansa kawai sai Motar ta kwacemai ta fara yawo saman Titi ya manta sam Tuki yake yi ihun Amina da kukanta sun Shiga kunnensa sun Haukata Tunaninsa Hayaniya nadaga cikin Abunda yafi Tsana arayuwarsa...!


*Alhamdulillah anan na kawo karshen Littafi na daya da Labarina na ta fita zaka,Nagode ma Allah domin baiwarsa ce kuma ikon sa ne bazan Tsawaita mgana ta ba kun riga kusan yanzu aka fara wasan akwai tarin abubuwan da zasu faru a kashi na Biyu na cigaban wannan labarin a baya naso nayi sa Cmpt dinsa Hardcopy ne ammh Sakamakon Rikon Wasu masoyana yasa na amince zan yi sa Softcopy ammh da Sharadin in kun siya Over 150 a paid group sannan bazan fara posting ba sai nan da Sati Daya zuwa sama in na gama Hutun dana Dauka ga masu son su Fara payment din su zasu Biya N500 Via 0552179550 Jamila umar Gt bank sai a Tura Shedar biya ta wannan lambar 09069067488, masu Turo kati kuma sai ku Dauki hoton katin ku Turo kai Tsaye ta wannan lambar 09069067488,Mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223 sai na jiku ina gaida masoyana a ko"ina afadin Duniyar nan wanda na sani da wanda ban sani ba..Sannan ina mika jinjinata ga Groups din da suka yi sharhi kan wannan labarin da masu sharing dinsa da yan Wattpadian dina Allah ya saka da Alheri Allah ya bar zumunci Maassalam*











*Janafty*
*20/09/2022*

AMEENA HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on 07014979567 WhatsApp ONLY

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment