Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu dawo..
Suna wajen sai gasu Haj.Nasara da Hajiya babba da goggo yakura sun fito dasu,kafin su ma mazan ne suka fara fitowa su ya uzairu da su ya Nasir ya Danmallanm da abokinsa Daga baya suka fito baba mallam da Aba sune ke rike da Amaran zuwa motocinsu Ba yau aka saba biki agidan ba ammh wannan na Dabam ne kamar yadda amaren suke na Dabam haka suke ta kuka kamar ransu zai fita Zeenatu da Abida.
Ana fito dasu suka kyalla ido suka hango su Amina suka kwace daga rikon Baba mallam suka nufesu Abida ta Rukunkume hanne tana kuka Zeenatu ta rumgume Amina da Hamida tana kuka duk da sun girmesu sune sakon su na kusa dasu akwai shakuwa sosai a Tsskaninsu.
Amina bata taba tsammanin zata yi kuka domin su ya Abida zasu tafi gidan mijinsu ba ammh yadda suke kuka suna rike su ne da kuma yadda Hamida da hanne ke kuka sai Amina ta fara Tsausayin kanta tana Tunanin in da gaske ne ta auri ya Danmallam kenan watarana itama zata iya Tsintar kanta cikin wannan yanayin sun bala"in bata Tsausayin da batasan sadda ta fara kuka ba takamkame Zeenatu suna kuka ita da Hamida ganin haka yasa Abida da Hanne suka zo suka hade suka yi Rumfa suna ta kuka kamar anyi mutuwa sai kallo ya koma garesu hajiya bata awajen ta koma cikin gida Haj.Nasara ne sai dangin mamanmu dana Aba na gusai.
Baba mallam tsaye kawai yayi bai ce komai ba ya jafar ne ya fara fada shi da ya Nasir suna fadin iskanci banza kukan uban me suka hadu suna ma mutane..!
Baba mallam ya kallessu yana Fadin"Ku kyalesu suyi kukan rabuwa da kannensu da gidansu..Gida fa ba kamarsa kuma aure ai yakin mata ne ko domin ku din maza ne shiyasa baku san wannan Raunin ba..!

Jin haka yasa sukayi shuru ya Danmallam bai ma san abunda ke faruwa ba suna haraban gida azatonsa amaren sum mika Aba kuma an kirasa a waya ya kebe agefe.
Haj.Nasara ne ta kalli Baba mallam tana Fadin"Maallam Uku tayi fa..Tafiyace kuma agabansu..!
Goggo yakura tace"Abidar kuma Angon yace jirgin karfe hudu zasu bi zuwa chan kuma ta Dutse zasu tashi..!
Baba mallam bai ce komai ba ya juya yana fadin"Ina Umaru..?
Ya Jafar yace"Yana daga cikin gida mallam..!
Kai Tsaye yace"Kiramin shi..!
Ba musu ya juya ya shiga ya kirasa sun ma hadu dasu ne zasu fito ya fadamai kiran mallan din sun fito kenan sai ga su Sakina da Sadiya da Tawagan yan"uwansu sun fito su ga Tafiyar amaran.
Daman Aliyu ya rako zai koma sai ga Kiran mallam sai ya isa wajensa yana zuwa Mallan ya dafa kafadarsa yana Fadin"Ka ga matarka da kannenka chan sun hade kai suna ta kuka. taimakeni ka lallasomin su kafi su Jafar sanyi su yanzu sai su ce zasu kai musu hannu..!
Inda mallam ya nuna mai yabi da kallo Takaici ya kumesa su din yara ne da zasu zauna suna ma mutane kuka kamar wasu marasa hankali sai karin wani takaicin wai matarsa shi fa har ga Allah ya Dauka Sakina ce da farko sai da ya kalli wajen yaga su hanne ne Tunanin sa ya basa wannan kazaman yarinyar ce bazai iyama mallam gaddama ba yasa ya kada kai yana Fadin"Shikenan mallam..!

Ko kafin ma ya isa garesu su ya Zulaihat sun isa suna faman lallashinsu su saki juna Sakina na gefe ta kame tana kallon kowa Daya bayan Daya sai ta ga Danmallam ya isa wajen yana mgana batajin me yake fadi,Ranta ya baci kishi ya Rufemata ido ganin Amina awajen badai ita yaje yana Lallashi ba..!
Sadiya ce tace"Ya sakina ga ya danmallam chan yana Lallashi..!
Bata tankata ba ta wuce fuu sai da ta isa wajen ne sannan taTsinkayi mganarsa yana fadin"Haka kurum zaku zo kuna ma mutane kukan banza..?
Kukan jin dadi kuke yi ko na menene..?Ko kuma an dake ku ne..Dillah ku sake su bana son Sakarci..!
Cikin Kiftawan ido suka Saki junansu suna Cigaba da gunjin kuka Daya bayan Daya ya kallesu kafin yace"Kowacce ta kama bakinta kafin nayi kasa kasa daku..!
Bai gama rufe baki ba suka yi shuru suna ajiyar rai Amina da Hanne suna rike da hannun juna kansu na kasa Amaran ya kallah sun yi Dama dama da Hijabinsu da hawaye da majina kafin yace"ku kuma ku wuce ku shiga mota..!
Da sauri ya Nazifa tace"Bari mu rikesu..!
Haj.Nasara na Dariyan su Amina tace"Danmallam da ka roki mallam ya bari su je koda kai Zeenatu ne zasu ji Dadi..!
Ko amsata bai bata ba illah su Amina Daya kalla cikin Taushinsa yace"Haj.Ba inda zasu je me zasu je suyi kuka..?Kowaccen ku ta koma cikin gida kuma ku cigaba da kukan ku gani Tunda anyi mutuwa ne..!

Sum sum suka mike hanya maimakon su koma gidan Baba mallam sai suka koma gidan Aba ko motsin kirki sun kasa Baba mallam baya wajen ya koma Falonsa shi da Aba
Sakina ranta yayi Dadi ganin ba mgana mai Dadi Umar ke fadama su Amina ba sai ta saki Fuskarta.
Su Haj.Nasara suka ssaka amaran Amota tare da rakiyan yan gusai da yayyinsu da kannensu suna kuka kamar ransu zai fita suka mika hanya sai Fatan Allah ya Kiyaye su.
Kafin La"asar kofar gidan ya zama wayam ba Jama"a Danmallam gidansa ya koma ya Huta Aliyu kuma ya koma Dutse dazu.
Hankula basu kwanta ba sai da Amare suka natsu adakinsu Jidda na Tare da Ya zeenatu a Kaduna sai gobe zata koma kano hakama Abida sai Dare suka sauka su Anty Amarya sun gama gyara komai gidan Zahra suka koma zasu kwana sai gobe zasu dawo..!
Su Amina kuwa ba wamda ya kara ganinsu har aka kwana suna Dakin yaya chan suka yada Zangonsu ammh fa duk sun yi sanyi ba ya zeenatu ba Abida gida yayi shuru sai su kadai kuma aranar ma su zafira suka koma harda ya Jamila,sauran baki ma suna ta wucewa tunda an gama Biki sai kuma Taro ya tashi.
Su Anty Amarya da wuri suka iso wajen La"asar,suka yada zango Shashen Hajiya suna fadamata karan Dangin mallam tunda uban yaron dan bazanga ne kuma matsayin kawu uban yaron yake ga mallam..!
Hajiya Babba ta kudira abu aranta sai dai batace ma kowa komai ba ta bari sai angama Hayaniyar biki sannan zata Furta abunda ta yanke.
Sai ranar Lahadi gidan ya watse harta yaran sun koma gidajen auransu,Ranar Hajiya keda shashen Baba mallam bayan sallar isha"i Mallam da Aba sun dawo shashen mallam din kamar yadda suka saba suna Hira.
Sai ga Hajiya ta shigo Cikin mayafinta yanzu shashen nata ita kadai ce Hanne ta mata yaji tana tare da su Amima agidan Sa"idu.
Lokacin da tayi sallama ta shigo gabadaya suka dago suna amsa mata Mallam ya tareta da Mirmishi yana Fadin"Zainabu abu mai Tagwayen suna..Uwargida sarautar mata..!
Yar dariya tayi batace komai ba Aba ne yace"Kuma Amarya ba..!
Baba mallam yace"A"a uwargidan dai Ni da zainabu ai mun tsufa kodon baka san tsufan ta..!
Aba na Dariya yace"Allah ya kara girma mallam..!
Hajiya na zama gefen mallam tace"Ameen kyalesa Sa"idu..Marliya ce Amarya barni in rike Tsufana..!
Aba yace"Haka za"ayi Hajiya..An watse taro lfiya yau ina sauri ana jirana na fita ban leka mun gaisa da ban gajiya.ba..Angode Hajiya Allah ya kara girma..!
Hajiya tace"Ameen bakomai..Tunda naga ban ganka ba nace uzuri ya rikeka..Ina yaran nan..?Hanne ma tamin yaji wai shashena ba Dadi ba kowa..!
Baba mallam yace"Daman ni na sani..Ranar da Abida tatashi..Sa"idu da Balaraba zasu ja Hannatu..!
Hajiya tace"ba ruwansu mamarkace da Hamida suka jata..!
Mallam na Dariya yace"To shikenan ku kyalesu ke hajiya kiyi zamanki ke kadai tunda kin zama giwar mata ki aurar da naki ki hada har da wanda ba naki ba..Allah ya kara girma da Lafiya Hajiya..!

Tana Mirmishi ta amsa Ameen kafin Aba yamike yana fadin"bari na shiga gida..!
Hajiya ta kallesa tana Fadin"koma ka zauna Sa"idu mgana nake so muyi..!
Ba musu ya koma ya zauna Baba mallan yace"Tunda na ganki daman nasan akwai mgana..!
Hajiya tace"Ina Danmallam..?
Bai shigo wajenka ba..?
Baba mallam yace""Yau kwata kwata ban gansa ba bai shigo anguwan tamu ba..yadai kirani da Safe ya gaisheni..!
Aba yace"Yaje gidan gona yau..Tare mukayi La"asar dashi ma..!
Hajiya ta fito da wayarta tana Fadin"Bari na kirasa.!
Daga Aba har Mallam ba wanda yayi mgana har ta Kira Danmallam bayan sun gaisa tace yazo gida shashen mallam gata nan tana jiransa.
Daganan ta datse kiran Mallam ya koma ya kishingida jikin kujera daman da yaga Yadda Hajiya ta shigo yasan yau Rigima take ji kuma ga Duk alamu kawaicinta ne ya kare kan Umar yau zai sha Fada..!

Tunda ya Dawo daga gidan gona bai kara Fita ba yana gida,Cikin Dakinsa Sakina kuma tana falo tare dasu Sa"adatu da suka zo mata yini,Sallar mangariba ce ta fitar dashi sai da ya Tsaya yayi sallar isha"i a Hanya sannan ya shigo gidan sai kuma yaga su Sa"adatu basu tafi ba ya farama Sakina Fadan meyasa sukayi Dare Cikin Basar da mganrsa tace"Nan zasu kwana fa..!
Kallon bacin rai yayi mata kafin ya kalli Sa"adatun datayi Fiki Fiki da ido yace"Ke mallan yasan kun zo nan zaku kwana..?
Kai ta gyada alamun A"a Harara ya sakar mata kafin ya wuce cikin Dakinsa Uzairu yaso ya kira yazo ya kaisu gida sai gobe yaso ya leka chan din sai ga Kiran Hajiya gabansa sai da ya fadi ba kasafai Hajiya ke kiransa ba yasan akwai wani babban Dalili kuma tace afalon Mallam.
Ko zama bai yi ba ya fito ransa bace Daman shi da Sakinan haka suka zo kowa na Harkan gabansa ya riga ya Dauke mata Tunda ya Lura bai isa da ita ba,Yayi alkwarin wlh bazai koma da ita ba nan zata zauna bashi da kudi bazai matsa ma kansa ba kuma ta nuna tafi son zaman nan din tabbas zata gane bata da wayau..!
Yadda taga ya fito yana cika yana batsewa sai da ta sha jinin jikinta da Sauri tace"Bari na kira Anty ko cikin mazan nan wani yazo ya kaisu..In kuma Idi na nan shikenan..!
Ko kallonta bai yi ba ya fice yana cema Sa"adatu"Dauko Hijabanki mu tafi..!
Daman ita da Sabeeha ne suna Shirye tunda yayi mgana basu ga ta zama ba suka mike tama kasa bin bayansu Saboda mamaki tabe baki tayi aranta tace sai kuma kayita yi ni dai na Riga da na nazo..!
Tsawon mintuna Talatin sannan ya shigo Falon a waje ya ijiye motarsa ya Sauke su Sa"adatu suka nufi Cikin gida yadda ya iske Aba da Mallam ga Hajiya yasa yaji kafafunsa sunyi sanyi Jikinsa ya basa wani Laifi ya aikata Domin Hajiya ko mallam ko Aba suke da Alhakin Zartar da kowani Hukunci..!
Gefe ya zauna bayan yayi sallama kansa na kasa ya gaishesu suka amsa mai Cikin Sakewa har mallam na mai Tsiyan"Umaru na kusa daina ganeka..Ka koma sak Balarabe..!

Ballatana daman shigar Jallabiyace ajikinsa mai Kalan ruwan madara kansa ba Hula gashin kansa ya bayyana..!
Kansa na kasa bai ce komai ba Aba ne yace"Ai yama koma Balaraben Mallam harta Harshensa ya koma nasu..!
Mallam na Dariya yace"Na bar ma Kattab.ni nan ya"yana sun isheni..!
Hajiya na jinsu batace komai ba Sai da ya Dago yana fadin"Hajiya gani nazo..Allah yasa Lafiya..!
Hajiya tace"Eh na ganka..!
Mallam mganar tarewar Amina ne dakace nan da wata shekarar ina so ka ijeta gefe..Ba shawara bace mallam Umarni ne amatsayina ta mahaifiyar Danmallam...Zai tafi da matarsa chan inda yake aiki..!
Daga Mallam har Aba da Danmallam baki suka saki suna kallon Hajiya wacce Daga yanayin mganarta zakasan ba wasa aciki.
Danmallam gabansa ke fadi Hajiya zata Takaitasa ina zai kai wannan yarinyar a yanzu kuma..?
Mallam ne ya katseta da Fadin"Meyasa abaya kika yarda da hakan yanzu kuma kika ce ba haka ba..?
Kai Tsaye Hajiya tace"Kada ku matsa sai kun ji Dalilina don Allah..Bazan Fadama kowa ba..abaya na yarda da hakan ne saboda ina ganin shine Daidai ammh Shekaranjiya na Fahimci munyi kuskure Mallan..anyi mai Wahalar an Daura aure To me zamu jira..!Biki ai ba Dole bane..Saboda haka in zai koma ya tafi da matarsa shine mganata..!
Aba ya bude baki yace"Hajiya hakan kamar ba adalci bane..Shi ai bai yi shirin haka ba..Ta yaya Lokaci daya kuma atakuramai..?
Hajiya ta karkace kai tace"Sa"idu ina da Dalilina..Ni ba shiri nake so yayi ba..Ko ya shirya ko bai shirya ba Insha Allahu da Mamah zai tafi in har na isa Dashi..!
Tafada tana kokarin mikewa da Sauri Mallam yace"Koma ki zauna Zainabu..Muyi mgana..!
Ba musu ta zauna Umar ya kallah yaga kansa na kasa sai zufa yake yi sai ya bashi Tsausayi bai da Hayaniya sam mai Biyayya ne da bin Umarni.
Yasan bazai taba musa mata ba har abada.
Cikin Salama ya kalli Hajiya na wani Lokaci kafin ya koma ya kalli Danmallan lokaci Daya yana Fadin"Umaru kaji abunda mahaifiyarka tace..Kuma bakace komai ba..!?

Sai da ya Hadiye wani miyau mai zafi kafin yace"Mallam bani da tacewa..Duk abunda Hajiya tace shi za"ayi..!
Baba mallan yace"Kana da inda zaka ijiyeta in ka tafi da ita ne..?Ko kuwa zamanta achan bata da takardan zama ba Takura bane..?
Sai da ya Dade bai yi mgana shi kuma Mallam Dubara yayimai su samu su lallaba Hajiya yasan da matsala rana Tsaka ya tafi da Amina gari ba kusa ba kuma ba kasarsa ba sannan abu Lokaci Daya ba shiri..!
Yasa yacemai haka domin ya samu ya kwaci kansa yana so Hajiya tabi komai a sannu sai dai baya so taga kamar yaki Sauraranta da kuma bata goyon baya..
Cikin Dattakonsa yace"Muna Sauraranka..bakace komai ba..!
Hajiya tace"Mallam basai mun jirasa ba..Koda bashi da inda zai ijiyeta sai ya tafi da ita ai ba'a Daji yake kwana ba..!
Da sauri mallam yace"A"a ba"a haka..Ki bari yayi mgana kada ki manta kasar dayake aiki ba Kasar sa bace nan din dai nan ne Kasarsa..!
Dole tayi shuru shi kuwa ya kasa mgana Aba ma haka Domin hajiya Fuska ta Hade ba Fara"a ballatana su ga wani Rahma tana so ne ta Nuna ma Sakina da Amarya Danmallam ya zauna acikinta na wata tara..!

Cikin karfin Hali ya fara mgana yana Fadin"In da son samu ne mallam.Hajiya ta bari in na koma sai na Fara cikun cukun sama mata takardan zama a kasar..sannan da wajen zamanta gidan da nike ciki karami ne Ni da Sakina da Sarood ma maallam maneji mukeyi yayi mana kadan gidana na nan yafisa girma Wlh Tallahi na rantse da Allah in na Tafi da ita zamu Takura mallam..Sai dai bazan iya bijirema Umarnin Hajiya ba..Sai ta fara shiri Jafar zai zo ya kaita ayi mata passport saboda Visa Nan da kwana Hudu nake so na koma..!
Daga Aba har mallam Tsausayinsa ya Rufesu Umar mutum ne mai Ladabi da Gudun bacin ran iyayensa,Hajiya kuwa bata Damu ba illah kada kai datayi tace"Ko ya ya ne dai tunda da inda zata zauna kamar sauran ka tafi da ita..Ka tafi da ita nace UMAR..!

Sai da ya dago kansa jin ta kira sunansa cikin wani yanayi yace"Shikenan Hajiya yadda kikace haka za"ayi..!
Sai kuma ya bata Tsausayi ammh in ta Tuna mganar sakina da yan"uwanta sai ranta ya baci so take ta gani ko zata bar mata mijin ne kamar yadda tace.
Yasa bata damu ba sai ta saki Fuska kafin tace"Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen cikin sanyinsa.
Maallam yayi mirmishin su na manya kafin yace"Hajiya..Hajiya manya..Kiyi hakuri zan yi wata mgana ni ba Umarni zan baki kamar yadda kika bama Umaru ba Alfarma zan tayasa riko tunda shi ba"a bashi Dama ba Sa"idu kuma bazai iya tsalleke mganarki ba shima ammh ni ai ina da Damar mgana ko ba haka ba..?
Kai Tsaye tace"Ina jinka..!
Maallam ya gyara zama yana Fadin"Daman zan ce ki yi hakuri don Allah duk da bamu san meyasa kika kawo wannan mgnarnan ba..Maimakon ya tafi da ita cikin Takura Zainabu me zai hana ta tare anan gidansa Dake nan Allah barshi in ya koma ya gama Dukkan shirinsa nima ina goyon bayan yazo ya tafi da ita inda yake aiki Tunda an riga an yi mai Wahalar..!
Hajiya tayi shuru kafin tayi mgana Mallam ya rigata da fadin"Alfarma mukace..Don Allah ayi hakuri ayi mana..!
Yafada cikin sigan lallashi Sai Hajiya tayi Laushi Cikin Dan kauda kai tace"Na amince ammh nima ina da Sharadina..!
Mallam yace"Bakomai tunda kin amince shikenan muna sauraranki..!
Hajiya tacigaba da fadin"Na amince da mganarka..Sai dai Abu Daya nake so in ya tafi bazai Dauki Lokaci ba .In ya Dade sosai wata Biyar ko Shida..Sannan Mamah zata tare agidansa goben in Allah ya kaimu bana son bata Lokaci..!
Mallam yace"Gobe kuma..?anya gaggawa ba aikin shedan bane..?
Da sauri tace"Haka kuma wani Jinkirin matsala ne mallam..!
Ganin yadda ta Cije ne yasa yace"Ammh kinsan nace sai ta yi Jarabawar gama sakandiri ko..?
Hajiya tace"Zata rubuta a Ss2 din ba shikenan ba..!
Mallam yace"Shikenan..mungode..!
Kafin ya maida kallonsa kan Umar yana fadin"kaji mahaifiyarka..na roketa alfarma kuma tayi mana sannan kaji itama sharadinta ko..?
Kansa na kasa yace"Naji mallam..na amince Allah ya shige mana gaba..!
Mallam yace"Ameen cikin gidan naka Dakuna nawa ne..?
Yace"Uku ne sai falo da Kitchen..!
Sakina na cikin Daya da Sarood tazo nace ta bata Daya sai nawa..!
Mallam zai yi mgana Hajiya ta Rigasa da Fadin"Zata zauna anaka Dakin..Mganar jere kuma ba bukata Tunda kowaccensu ba ita ta saka kayan gidan ba..Bana kowaccensu bane..Sai dai ka sani zaka samar ma Amina nata Muhallin anan domin ayi mata Jerenta kamar ko wacce ya' acikin gidanan..!
Mallam bai ce komai ba sai Danmallam ne yace"Insha Allahu Hajiya..!
Ko Aba ya kasa mgana Ganin haka yasa Mallam ya sallami Danmallam yayi musu sallama ya fice Aba ma ya Mike jikinsa sanyaye yayi musu sallama Hajiya ta kallesa tana Fadin"Sa"idu ka sanar ma Balaraba da ita Mamah..Da safe zan shigo insha Allahu gobe agidan mijinta zata kwana..!
Bai da tacewa ya amsa mata da toh ya ficen bayan fitansa mallam bai tada mganar ba domin yasan tana da Dalilinta sha"anin mata sai abarsu.
Aba haka yajema mamanmu da mganar sai ta sakamai kukan nawa Amina take da hajiya zata mata haka bai Saurareta ba ya Kira Amina ya Fadamata Sakon Hajiya ranar su uku kwana sukayi kuka kamar anyi mutuwa kukan sabo da kuma Rabuwa da Amina.
Adaran Mamanmu ta kira Anty Amarya ta fadamata ta Zunduma ashariya tace mamanmu tasan yadda za"ayi Amina ta Bijirema Tarewarta aikuwa da Safe ta kira Amina ta sata adaki tana kuka tana fadin za"a cutar da ita kowace sai da ta gama makaranta aka mata aure banda ita ta Rika Tusa mata mganganu da sai da Amina taga haka din ne ita za"a kwareta an cutar da ita mamanmu tace taje ta samu hajiya ta fashe mata da kuka tace batason tarewan tasan zasu kyaleta Amina ta yarda da hakan domin bata hasko ma kanta ta zama matar aure ba yanzu Haka ta Zurma Hijabi Fuska kozai kozai tasha kuka ko su Hanne basu san ta fita ba
Sai dai tana shiga gidan ta baro shashen Mallam kenan dan lungun Dake tsakanin shashensa da na Anty Amarya taji tashin murya sama sama Abunda yasa taja ta Tsaya sunanta taji ana ambata..!

"Dayyaba..In har AMINA tatare a matsayin Matar UMAR..na sabama Sakina alkawarinta..Alhalin na mata Rantsuwan in har ina Raye auran Amina da Umar haka zai kare a gantale ba Fa"ida..Ammh yanzu komai zai lalacemin in har yarinyar nan ta tare agidan nan Kashin mu ya gama Bushewa Fitar da ita shine babban aiki..!






*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*🅿️29*

"Gaban Amina ya fadi ras jin Sunanta da mganar da ke tashi akanta Labe ba Dabi"anta bane ammh sai ta kasa yin gaba sai ta ja ta tsaya ta kara kasa kunnenta tana sauraran muryan Anty Amarya Tar tana mgana cikin bacin rai da takaici.

"In ya kulata din fa Dayyaba..?Kada ki manta Namiji ne ko bai kulata domin yana sonta ba na tabbata zai iya kulata watarana saboda Hajiya da mallam..Ayadda yarinyar nan ke da Tasiri a wajensu matukar tatare agidan Umar Tauraruwar Sakina zai koma baya ne..Ni kuma nayi alkawarin matukar ina Raye Sakina ce kadai Mowa agidan Umar..Kuma sai na tabbatar da na cika mata wannan alkawarin Indai bata Haihu da Umar ba alkawari nayi ba wata macen data isa tazo ta Haihu..Ita kadai ce Tauraruwa kuma Sarauniya..!

Amina mamaki ya kara cikata gani take abun kamar amafarki,so take ta Tabbatar da zarginta yasa ta Leka lungun bayanta take hangowa dayake ta Juya bayane tana mgana ta waya,Sai dai ko daga barci tatashi Ko ta baya ko ta gaba zata shaida Duka matan baba mallam ba ta murya ba Daga yanayinta ko kaffara ba zatayi ba Anty Amarya ce sannan gaa ma Muryanta nan na fitowa duk da Bada karfi sossi take mganar ba..!
Baki ta rike tana kara mamakinta Sanda taji tana Fadin"Na bar komai a hannunki..Don Allah ki san yadda zaki yi kada Tariyar ta Amina ta tabbata..In har auransu Kuskure ne to kada ma wannan ya zama kuskure Dayyaba..In ya zama Kuskure zamu yi shekaru kafin mu iya gyarashi..!
Kiyi gaggawan yin wani abu..!

Amina taji kanta ya sara abaya tasan Anty Amarya ta Tsaneta,Ammah bata taba tsammanin Tsanar nata yakai haka ba meyasa bata son ta Tare a gidan ya Danmallam...?Wata zuciya tace Saboda Sakina mana Tunda Diyartace to ammh da wa take waya..?Waye take cema yayi mata kokarin kada Tariyanta ya tabbata..?Ta shiga Rudi Kwakwalwarta ta toshe ta kasa Tunani Abu daya ta kama Anty Amarya bata so ta tare saboda Sakina
Abun kamar almara sai taji kuncin Dake zuciyarta ya yaye Daga rashin son Tarewar zuwa son ta tare din ba son ya Danmallam take ba har Abada Aminu ne aranta Sai dai zata taren sai Taga yadda Anty Amaryan da Sakinan zasu yi da ita munafukam banza Har itace zasu ma Burauba to sai ta taren Uban daya Fasa sai ya Hanata..
jidalinta kadai ya ishesu daga Sakinar har Mijin nata basu isheta kallo ba
Maimakon ta wuce shashen Hajiya Babba kamar yadda Mamanmu ta Tsara mata sai kawai ta fasa ta kada kai ta juya zuwa Haraban gidan tana Tafe tana auna maganganun Anty Amarya tana Tunanin adanginsu wacece Dayyaba..?Ta gama Tunaninta kaf bata ganota ba to wacece take cewa ta bar komai a hannunta..?
Tana wannan Tunanin ta kusa cin karo da Akilu ya fito daga Falon Mallam Sanye da Uniform ajikinsa sai da ta gansa ma ta tuna yau Monday suna da makaranta.
Shekeke yake kallonta ganin ta Dauke kai zata wuce yace"Ke Amina bazaki makaranta bane..!?
Mamaki ya bata suna da son Girma shi da Zubairu gwara ma Akilun ya basu shekara Daya da wani abu Zubairu fa saurin girma yayi Hajiya tace tsakaninsu ko wata Biyar bai kai ba An riga sakashi makaranta Shiyasa ya Tsere musu da aji Daya ammh sai su rika nuna abu kamar sun wani basu Shekaru barin ma Akilun nan dan Rainin Hammata ne..!
Kasa kasa ta juyo tana kallonsa da Kumburarrun idanuwanta kafin kai Tsaye tace"Eh..!
Kallonta yake cikin bude ido yace"Eh fa kikace..To saboda mene ko baki da Lafiya ne..?
Amina ta gaji da yadda ya wani Tsareta da tambayoyi kamar Ubanta Cikin Kufuluwa tace"Bansani ba..!
Baki ya rike yana fadin"Amina ni ma kike cema baki sani ba don Uwarki..?Ni sa"anki ne..?
Daman shi abu kadan zagi kamar ba Jinin Mallam ba
Amina ta Bude manyan idanuwanta kafin tace"Wlh badai uwata ba..!
Ya Zaburo Cikin bacin rai yana Fadin"Sai tawa uwar kenan..!
Ta matsa da Sauri tana kunkumi tace"Ai uwa bata fi uwa ba Ehe..!
Akilu Duka yake son ya kaimata Bai ji Fitowar Mallam ba sai mganarsa.

"kai Akilu kaniyarka nace..!
Matar yayan naka zaka Daka dayake baka da kunya ko..?

Dukkansu suka juya Baba mallam ne Cikin Akyabbansa da Rawani Tsaye kofar Falonsa yana kallonsu Bai ji Mganarsu ba Fitowarsa kenan Daga Daki yaji Akilu na fadin shi Sa"anta ne yana Lekowa yaga zai kai mata hannu.
Akilu na ganin Baba Mallam ya Rankwafa yana fadin"Allah ya kara girma Baba..!
Amina kuwa gaisheshi tayi ya amsa yana fadin"Mamana Daga ina da Safan nan..?
Amina ta sharara karya da cewa"Nazo gaida Hajiya ne..!
Baba maallam ya Murmusa yana kallonta kafim yace"Yar gidan Hajiya..To kin gaishetan ne..?
Amina kanta na kasa ta Daga kai Baba mallam Akilu ya kallah yana Fadin"Bana son na kara ganin wannan Sakarcin..In har zaka Daketa ashe zaka sa ka hannu ka Daki Umaru ko..?
Akilu ya Dago kansa yana kallon Mallam kafin ya juya yana kallon Amina da kanta ya fashe ta Hura Hanci tana Juya ido shifa tun sanda aka Daura auran Amina da ya Danmallam yake Tsausayamai ko shi da yake yaro daidai da ita bazai iya da Amina ba ballatana ya Danmallam wanda bai da Hayaniya mai sanyi ne shi.Ai Tsab zata jazamai hawan jini in kuma ta Hadu da Sauran ciwo Tsab zata Karisa shi Lokacinsa bai yi ba.
Dukar da kansa yayi yana Fadin"Ayi hakuri

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment