Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka Duka suka Dumbuza Ledojon suka Zura aguje Sai alokacin su ya Zeenatu suka juyo suna kiransu Zeenatu ta rike baki tana Fadin"Ya Umaima su Amina ne ko..?
Kai ta gyada batayi mgana bata son Hayaniya saboda ciwonta.
Badiya yar ajinsu ya Abida tace"Aminar gidanku ko"ina sai ta nuna Hali..!
Sai ga Abida ta shigo tana Fadin"in na rike su Amina sai nayi musu dukan Tsiya..!
Ya Zeenatu tace"Ki hadasu da ya Nazeem ne yaci ubansu..!
Kyafci tayi tana Fadin"Ku bar badawa hakanan..bari agama Walima sai mu fara Shirya na malaman mu ki hada musu da abun Rabon duka Zeenatu..!
Suka amsa mata kafin ta fice Chan ta hango su Amina akarshe suma cin abunsu hankali kwance suna Dariya kai kawai ta girgiza domin tasan in tayi mgama zasu Raba Hali ne gaban Mutane.
Mariya ce tazo gabansu tana Fadin"Kunci kun barsa ne naga har da Sata..?ana ci hannu baka Hannu kwarya..!
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Mariya in baki bar nan ba na Rantse na mike bazaki ji da Dadi ba..!
Mariya ta saka musi Dariya tana Fadin"Kudai ku ci kawai..!
Harda gwalo Amina tace"in ban dagi bakin yarinyar chan ba ba sunana Amina ba..!
Zafira na Tura Donut bakinta tace"Daga gani irin yan Shisshigin nan ne..!
Amina tace"Kamar kin sani..Tusa kai ba kwarjini..kamar mayya..!
Har Malaman da zatayi Wa"azin tazo suna chan baya suna Ciye ciye,Daya Daga Cikin matar wani abokin Baba Malam ne Sheik Ahmad Hadeja Ta iya Wa"azi sosai kawar Hajiya Babba ce ta na hallarta Dukkan wani Mahadara na mata sannan Har programme tana yi agidan Radio da Tv akan mata ta kuma yin Wa"azin aure irin wannan in gayyaceta Motace ta Lalace musu ahanya Anan garin Gumel din suke zaune.
Nan ta fara Lacra kan hakkokim mata akan Mijinta kafin ta gangaro kam Hakokin miji kan matarsa sannan ta bada Shawarwari sosai da kuma Mgugunar karin Ni"ima bangaran isalama domin Taimakom mata Hamida ta taba Amina tana Fadin"Ku Tsaya ku Saurara Wlh mgangunta akwai amfani aciki..!
Amina ta saki Tsaki kafin tace"Dilla mu kyalemu ta ina zai amfane mu..?ko kina cikin Amaran ne Hamida?
Hamida tace"A"a abun ba bakar mgana..Ko don gaba nake nufi..!
Zafira tace"Gaskiyan Hamida mu ma nan da Shekara Biyu muma amaran ne..!
Amina ta saki Tsaki kafin tace"Sai ku jira Lokacin..Me kuke ci na baka na zuba..?
Ba wanda ya tankata ita kanta Hanne ta maida Hankalinta kan malamar ganin haka yasa Amina ta maida Hanlinta itama Sai tabe baki take yi Domin ita bama wani fahimta take yi ba.
Shida saura Mintuna aka gama Wa"azin bayan an gama su ya Abida suka fara rabon su Jakunkuna da Karamin Frame na Ayatul kursiyi da su ya Aisha zata raba Daga bangaransu.
Sai ya Zeenatu da ita da kawayenta suna ta Rabonsu Turaran tsinke da Memo na ya Zulaihat su Sa"adatu kuma suna ta Rabon Turaran Wuta na Rushi,da su Sabulun Salo harda Fallen Atamfa,acikin Wata Katuwar Leda da mafitai na zamani.
Bangaran Haj.Nasara ma su na ta Raba Kananun Kofuna da Kuma Mug na shan Tea abun sai wanda ya gani.
Kowanne sai da su Amina suka Dauka ba"a sani ba Har da su Sa"adatu Amina tace"Da kudin Baba Mallam akayi sai mun dauka..!
Hamida na Dariya tace"Amina kina da Karfin Hali..!
Amina ta balla mata Harara,sukayi Dariya kafin ma atashi suka Gudu gida Saboda kada asasu wani aiki kamar kuwa sun sani ana ta Cigiyansu su taimaka a kimtsa wajen aka nemesu aka rasa sai su Ya Abida suka Bige da aiki chan aka barsu a makaranta bayan sun gama Sallaman malamansu maza Hajiya kuma ta Sallami Malama Hafsah da tazo tayi Wa"azin mata.
Duk a kasa suka koma gida su Ya Nazeem suna masallaci wajen Karatun Baba Malam.
Sai Bayan mangariba su ya Abida suka Dawo amaran kaf suna Shashen Hajiya Babba nan Zasu kwana Har sai gobe bayan Daurin auran za"a kai kowacce shashen Mahaifiyarta na karshe,Shine Falon Baba Mallam inda shi da Aba da kuma su ya Danmalam manya inda za'ayi musu Nasiha Tare da mazajen nasu sannan kowacce a Damkata Hannun mijinta.
Su Amina ko Abincin Dare basu ci ba suna ta cin kayan Fulawa Hamida tace"Kada ya danne mana zuciya mu kasa tashi..!
Amina tace"Dillah zuwa gobe da Safe ya Sabbabe..!
Sai da suka cinye kusan duka Sauran suka bama yara har suka koma suka kwanta suna Hira Daganan sai barci.

******

Anty Amarya na Falon Shashenta Cike da baki,Wayarta Dake hannunta ta Fara kuka tana Dubawa sai da gabanta ya Fadi agogon bangon Dake Dakinta ta Duba 12am na dare ta wuce Acikin Dakin akwai wadanda sukayi barci akwai wadanda basuyi ba.
Sulalewa tayi ta nufi Bedroom dinta nan ma cike da Mutane Dayan Dakin ta Nufa taga Sakina na ciki ita Sarood sai kawai ta Juya ta Fice Daga Shashen Har wata yayar Anty Amarya tana Fadin"Marliya ina zaki da wannan Tsohon Daran. ?Sha biyu fa ta gota..!
Ta fice tana Fadin"Yanzu zan dawo Ya Salamatu..!
Kitchen dinsu tana jin hayaniya su Lami suna aikin Miya zasu soya da Daran nan na abinci gobe nan zasu kwana ganin haka yasa tayi kamar zata je shashen Baba Mallan sai ta Shige lungun Dake tsakanin Shashen nasa da Bangaran Dakunan mazan gidan.

Jikinta na Rawa ta Daga kiran har ta katse sake kira akayi Cikin Makale murya tace"Miye haka DAYYABA..?
Kinsan fa gidan cike yake da Mutane..!
Shuru tayi na dan Lokaci da alamun Tana Sauraran mai mganar ne Daga Chan bangaran
Kafin na ga ta saki wata Kayattaciyar Dariya kafin tace"Daman nace sai an gama wannan Hatsaniyar zan kiraki muyi mgana..Balarabiyar banza..?tasha gabana har ta sakani Fargaba..Tuni nayi mganinta Daman na Fadamiki bayan Sakina ba macen da zata Kafu a gidan Umar bayan ita. wannan Burina ne in ban samu mallaka Malam ba..Zan samu Damar mallakan abunda yake Takama Dashi Dagashi har Hajiya Babban atafin hannuna suke Dayyaba..!
Shuru ya sake biyo baya kafin chan kuma ta kara Sakin Dariya tana Fadin"Kema saura kiris...Ki kara Hakuri kawai..SA"IDU ma matsalata ce Dayyaba..Shiyasa na Hada hannu Dake ni Burina bazai cika ba sai Sa"idu ya bar mallan..Kema naki Burin bazai cika ba MAtukar HADIZA na Numfashi acikin gidan Sa"idu zamu yi mgana..Hanya Dayace...Kawai da zai sa komai ya Dawo hannunmu.
Zamu yi mgana in Hankula suka kwanta..!

Kamar Motsi taji abayanta da Sauri ta katse wayar ta leka Shamsu ne ya Fito yayi alwala ya koma Dakinsu sai da ya Dade da shiga sannan ta fito inda Allah ya Taimaketa An kashe gen Duhu yayi sosai yasa ta Lallaba tana Waige waige ta shige shashenta Lokaci Daya tana Sauke Numfashi.
Sako ta Turama Lambar data kirata.

*Kada ki sake kirana..Sai ni na Kiraki da kaina..*




*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

_Ina matukar godiya ga Tarin masoyan labarin Aminene ikon Allah..Nagode matuka Baiwar ba tawa bace ta Allah ce godiyar kuma zuwa garesa ne Allah ya bar zumunci nagode matuka da Alherinku gareni musamman Halima yusuf Besty Alherin Allah ya cigaba da Bibiyanki har gaban Abada_


*🅿️13*


Karfe Daya da Rabi na Ranar jumma"a 1:30pm aka Daura auran su ya Zulaihat a babban masallacin Gidan Baba Mallam bayan an idar da Sallar jumma"a masallacin Daman Kaf anguwan da Zagayenta shine babban masallaci,Shiyasa bayan karattukan Addini da akeyi da kuma Duka Sallolin khamsin Salawatu ana Sallar Jumma"a acikinsa.
Kamar yadda kowa ya sani ne al"adan gidan Baba Mallam Ranar jumma"a yake Daura auran ya"yansa To hakan ce ta kasance ayau din ma ana idar da Sallar jumma"a Daman kowa yasan da Daurin auran anguwan ta cika ta batse da manyan mutane kama Daga manya malamai Daliban Baba mallam,Angaye da duka Tawagan abokansu, abokansu ya Jafar da Sauran Mutanen anguwa da kuma Jama"a da basa Wuce sha"anin Babban malami irin Baba Mallam.
Bayan an gama Daura auran Gabadaya Tawagan angayen da abokansu da su ya jafar da su ya Danmalam dashi da abokinsa kwara Daya Tal Daya gayatta wanda ko bai gayyaceshi ba zai zo tunda sun zama Daya tare sukayi makaranta Tundaga matakin primary anan Gumel kafin aiki ya maida mahaifinsa Dutse,suka koma chan cikin ikon Allah kuma sai suka Sake hadewa a Dutse a Wata Bording school ta maza Inda suka Dora matakin Secondary Dinsu.

Aliyu Ahmad Gumel yanzu haka Lacture ne a School of Nursing Dutse acikin makarantar ma yake zaune da Matarsa mai suna Aliya da ya"yansu Hudu sai mahaifiyarsa dake tare da Iyalinsa mahaifinsa ya Dade da Rasuwa shine kadai amini kuma aboki ga D'anmalam wanda Tare ma suka zo da Iyalin nasa tana cikin gida wajensu Sakina,Kawaye ne ita da Sakina Tunda in dai suka zo garin suna zuwa Dutse wajensu sannan Aliyun yaje Madina shi da Aliya ashekarar da suka je Hajji sai suka Rankaya gabadaya suka isa makka suka Sauke Farali.
Gabadayansu cikin gari suka tafi wani kayattacen Waje inda sukayi Reception wanda Danmallam ya Dauki nauyin komai ya hana su Hajiya yin wani abincin Daurin auran Mallam ne kadai da Aba basu awajen,Suna chan gida sallaman baki mutanen bazanga da kuma yan gusai da ana gama Daurin auran suka juya

Ammh Tundaga kan su Zubairu har ma da Mutanen gari da abokan arzuka suna wajen Sun ci abinci sannan sai aka gaggaisa aka Dauki Hotuna Saboda Tarihi.
Gabadaya Iyalan Baba Mallam Fararan Shadda suka Sanya Sai illah D'anmallam da ya Nazir ne suka saka Shadda mai Ruwan kasa Babban Riga da Hula Aikin hannu kuma iri Daya wannan aikin Baba Sa"idu ne shi ya Dimka musu su Hudu Cikon su Baba Mallan ne wanda ya Dora Rawaninsa kan Hularsa mai sakar yan Maiduguri wato Zanna Bukar.
Angwayen kuma kowani Tawaga da nasu irin Tsarin Shigar Cikin Burgewa basu wani Dauki Lokaci ba Misalin Biyu da Rabi na Rana Motocinsu suka Fara Dawowa Kofar gidan Baba Mallam,Saboda Daukan Amran kamar yadda ka"idan take mata na cikin gida Ana ta Haraman Hada abubuwan Daya Dace kada a manta da wani abun
Amaren Shashen Hajiya Babba suka kwana kuma ba"a fito dasu ba sai da aka Daura aure dukkansu sun saka Shadda Fara mai aikin Gold sannan hijabinsu har kasa mai Ruwam Gold ne da Takalmansu,ayayinda su Hajiya kuma Shaddar su mai Ruwan kasa ce suma Dukkansu har da su Mamanmu Da yaya a ka"idan Biki su kayansu iri Dayane Baba Mallam ya hana Sauya kala sannan Tundaga kan su Amina har kan su Abida shaddarsu Kalan Sararin Samaniya ce Kuma Dinkin su Duka iri Dayane da kalan aikin zaren mai ruwan zuma suma Duka Hijabinsu mai ruwan zuma Tunda saka gyale sai da su gani wajen wasu Tundaga kan na gaba dasu har iyanzu ba wani wanda har ya gama zamansa yayi aure yasan yadda ake saka Mayafi wannan Tarbiyan Baba Mallam ce Hijabinki har kasa da Safa Nikab ne bai saka musu Dole ba wacce tayi Ra"ayi ta saka abunta
Hatta masu auran suma sun yi shaddarsu sai dai kowacce kalan ta ta Dinka.
Sai bayan an gama Daura auran Angwayen sun tafi cin abinci mallam da Aba sun gama sallaman baki wajen yadan Ragu da maza kana Hajiya Babba da Hajiya uwa suka taso Amaran zuwa gidan Baba Sa"idu domin suyi sallama kowace na Lullube Cikin Hijabi tana kuka yara irinsu Amina da basa jin mgana suna Bin bayansu rii,su ya Abida kuma suna Shashen Haj.Nasara nan suka Sauke kawayen Amaran in sun zo Duk su ba wani gayya suke yi ba yawanci Duk yan islamiyan su ne sai yan Hadda ko yan makarantar Bokonsu sai Daidai kowa ya sani su kansu sun isa gayya a sha"aninsu.
Dakin Mamanmu aka fara kai su bata wani Tsaya ba suma Dayake gidan yana Cike ne,addu"a kadai ta yi musu da Nasihan Hakuri kafin tace a kai su Dakin Yaya.
Hajiya Babba tace"zamu bar miki Zulaihat ku kebe a matsayinki na Uwa gareta..!
Mamanmu Dariya tayi kafin tace"A"a Hajiya..Ni Uwar Amina ce inda yau auranta akeyi bama sai kin ce mu kebe ba..Ammh Ai Zulaihat Diyar yaya ce ku mika mata ita Dakinta ta kara mata Fada ita da Sauran yan"uwanta..!
Ana ta Dariya Kowa wannan karamcin na Mamanmu yasa take da kima a idon kowa Musamman Mutanen Gusai Dangin Aba,ba musu aka Kwashesu sai Dakin Yaya tayi musu Nasiha matuka tare da Fatan Alheri Suna ta kuka banda Sadiya kanta dai na kasa.
Amina da Hanne da Zafira da Hamida suna Dakin Domin duk inda aka saka Kafa nan suke saukewa sai ana Tafiya su rika jama su ya Aisha Hijabi suna leken Fuskarsu ba wanda ma yake Lura dasu.
Zafira tayi ma Amina Rada tana Fadin"Wanchan fa naga bata kukan Rabuwa da gida ne..?
Amina ta kalli Sadiya kafin tace"Diyar Anty Amarya ce..Yayar Sa"adatu..Ai bazatayi kuka ba yar na gada ce..!
Zafira tace"Tab wai ina ma Sa"adatun ne yau duk ban ganta ba..?
Amina tace"Tana Shashensu mana .Ki bari zamu ganta ai duka za"a kaisu..!
Zafira tace"Yauwa sai na kara ganin Balarabiyar nan..!
Amina tayi Dariya tana Fadin"Basabam ba..bakauyiya..!
Ita dai Dariya tayi Hamida da Hanne suna gefe suna jin duk nasihan da ake mu su ya Zulaihat Banda Amina da Hankalinta ba bashi a wajen.
Basu wani jima ba Saboda Baba Mallan yace karfe uku kowacce zata mika Gidan Mijinta Gabadaya Har dasu Mamanmu da Yaya da su ya Jalela da Mutanen gusai aka Dumguma gidan Baba Mallam Dakin Hajiya Nasara suka yada Amaran itama Amtsayinta na uwa zatayi musu Fada da Nasiha,alokacin ne ya Zulfa ta hango su Amina Cikin mamaki ta tabo Jawahir tana Fadin"Jawa kalli yaran nan..?
Ta kallesu kafin tace"Baki gansu ba..?ai tun dazu suna kugu da manya ko su Abida basa wajen nan sai su nayi mgana Hajiya tace a rabu dasu..!
Zulfa tace"Amina ta na wani juya ido..Kamar wata babba..!
Jawahir tace"Ko an koresu sai Amina ta Rika Labe kamar baki santa ba..?
Zulfa tace"Allah ya shirya..!
Jawahir tace"Ameen. !
Su bama su san suna yi ba suna chan suna ta Gulmar wata Kanwar Haj.Nasara da take da kiba katuwa ce Amina na Danne Dariyanta kasa kasa tace"Chabdijam..Wayaga Him..Buhun Masara..!
Tana kallonsu suna Dariya kasa kasa Sai ta kallesu sai su kauda kai ganin hakane yasa suka koma Daga kofar Shigowa suna Dariya nan ma basu Dade ba suka fita zuwa bangaran Anty Amarya,chan suka iske Danginta Na Duste har da yayin angon Sadiya wadanda zasu tafi da Amarya sun zo su Sakina an ci wani Leshi mai Tsada an kashe Dauri Sarood ma ta saka Leshi iri Daya dana Sakina mai Ruwan Maroon da Kwalliyar blue gabadaya Cikin Dakin nan sai da ta Haskawa kowa yadda tayi wani kyau kamar ka ijiyeta kayi ta kallonta Masha Allah.
Zafira tace"Tsarki ya Tabbata ga Allah..Amina kinga kyau..!
Amina tace"Gaskiya kayan sun mata kyau..Ji Anty Sakina da ta saka Wlh kamar akuya..!
Tafada tana Dariya Hamida ta Zungureta tana Fadin"Kiyi a hankali Tana kallonmu kada ta gane..!
Amina na Danne Dariyanta tace"Kalleta..Sai kiba take karawa ga Gajarta kamar akifeta da kwarya..!
Hamida tace"Amina ki bari..ba kyau kushe Hallitar Allah fa..!
Amina ta balla mata Harara Tana Fadin"Anki a barin kabarinki Daya Dani ne..?nifa Hamida kin isheni Wlh badama ayi abu sai ki ce Amina kamar Ni kadai ce uwar Laifi..!
Hanne tace"Mu dai don Allah kada ku fara wannan Fadan..!
Amina tace"Gayamata ta Daina ambaton sunana..In ba Haka ba taga Tijara ganin idonta Wlh..!
Hamida ta tabe baki kafin tace"Daga Fadin gaskiya..?
Kuma da kike mganar Tijara.?har akwai Sauran Tijaranki da ban gani bane Amina..!
Amina ta Hura Hanci kafin tace"Tab..ai baki ga komai ba Hamida..!
Hanne ta raba Fadan da Fadin"Ku ga Sa"adatu chan..!
Jin haka suka koma inda ta Nuna musu Daga bakin Kitchen din Anty Amarya suna ta Fito da kwalaye suna Tarawa anan Tsakiyar Falon itama Less ne ajikinta,mai Ruwan kasa Iri Daya dana Jikin Sabeeha ta gansu yasa ta zo ta wuce ta gabansu Amina ta kalleta kamar taga kashi kafin ta Mele baki tace"
Aikin mur in ji tusa..!
Zafira tace"Ita bata saka irin kayan ku ba..!
Hanne tace"Ko Anty Amarya ai bata saka irin nasu Hajiya ba..Itafa komai nata Dabam take yi ita da ya"yanta Baki ga yawancin Danginsu da less ba kila su nasu ankon kenan..!
Zafira tace"Hala Baba Malam bazai yi Fada bane..?
Hanne tace"Ina ma zai Lura yana Fama da Jama"a..Kuma kinsan Hajiya ba ruwamta da wannan..Daman Anty Amaryan ne akwai kai kara da ance kace..!
Amina na jinsu kafin tace"Ko Uban me zasu saka Wlh basu fimu ba..!
Hamida tace"Infa..Bama zasu Fimu ba Wlh..!
Anty Amarya suke kallo da take ta Dafa Duka kawunan Amaran tana ta musu Nasiha da saka albarka.
Basu jima ba suka fito bayan sun bar Sadiya anan Shashen itama Ikram shashen Haj.Nasara aka maidata Su ya Abida basa nan wai sun tafi gidan ya Jafar Ya Uzairu ya tuka su zasu Dauko wasu kayan Amaran Dake chan gidan
Ya Aisha da ya Zulaihat Shashen Hajiya Babba aka maidasu,Sannan Hajiya ta fice zuwa Babban Store din gidan Inda su ya jafar da ya Nasir ke jiranta aka Bude aka Fara Fito da Buhun hunan Shinkafa taci da na Tuwo sai garan kayan abinci bangaran su Taliya da Sauransu sai manyan Bombi na su kayan fulawa da Akayi ma kowaccensu.
Harda da manshanu sai da aka saka ma kowacce Dukkansu garansu kowacce abu Biyu ne wani uku,Harda da su kuka Kubewa yaji,Fulawa da Sauransu kayan Kamshi Hajiya Babba ta saka su Baba Lami sun Dakasu kowacce an Dibar mata har da kayan Miya Tattasai Bushashe Tumatiri na angwangwani aka Siyan musu.
Sun Raba kayan gida Hudu kowacce aka kwashe mata Daya su ya Shamsu ke Fita dasu suna Lodawa a Motocin angwayen.
Hajiya Babba ta koma Shashenta ta Fito da wasu kayan Kitchen da zannuwan gado masu kyau na Saudiya,guda Biyu Daya na Aisha Daya na Zulaihat kayan Kitchen dim Biyu aka Raba duk da an siya musu wasu wannan karin ne saboda kayan aiki basa kadan,Bangaran Anty Amarya ma suna ta fito da kwalaye ita harda Nakiya suka kara ma Sadiya sai bangaran Haj.Nasara itama Danginta suna ta fitowa da wasu kayan Sai ga su ya Abida daman Tururuka suka Dauko na Ruwa da na Turaran Daki,Na Aisha da Zulaihat ne ta riga ta bama nasu sadiya ta bama iyayensu mata.
Kowacce Angwayen sun zo da Danginsu guda Biyu da zasu tafi da Amarya Ya Aisha Mata uku suka zo Daga barayin mijinta Daga kaduna ya Zulaihat kuma mace Daya,Sai ya Sadiya ita gasunan da yawa tunda Abun gidane Ya ikram kuma algaita Tuni ya Cika kunnin Mutane Tawagayan ya"yan Sarki manyan uku suka zo tafiya da ita.
Anriga an gama Loda Duka kayan Daga bangaran Duka Motocin guda Daya,Daya Kaduna Daya Jigawa Daya Dutse Daya kuma nan Gumel
Cikin gida ma duk an gama Shiryawa Ya Rage saura Falon Malam Dashi da Aba sai Sauran manya yayyi irin su ya Danmallam da su ya Jafar Daga Falon Baba Mallam shi zai fito da kansa ya Mika kowacce Motar da zata sadata da gidan Mijinta bayan ya mata Fatan Alheri.
Su Amina sun kasa sun Tsare a Kofar Shashen Anty Amarya suna Hiransu Sama sama,Jidda ce ta fito ta gansu Cikin mamaki tace"Ku kuma lafiyanku kuke tsaye anan..?
Hanne ce tace"Bakomai muna son ganim Tafiyar Amare ne..!
Jidda Tayi Dariya kafin tace"Ai Daga kan su Abida sai ku Duka Mallam ya Hadeku mu aurar daku rana Daya..Wannan fa ban gane ta ba..?
Ta fada tana nuna Zafira Wannan karon Hamida ce tace"Daga Gusai take Diyar kanwar Aba ce..!
Jidda tace"Goggo Husai..?
Hamida tace"A"a Mamata..!
Jidda ta gyada kai kafin tace"Allah Sarki naji ma ance goggon na kwance Zazzabi ya Rufeta ko..!
Hamida tace"Eh Tun jiya da yammah Shiyasa ma baki ganta tare da su Yaya ba..!
Jidda tace"Allah ya sauwake in an wuce da Amaran zan shiga na gaisheta..!
Daga haka ta koma ciki,Hanne ta Tabo Amina tana Fadin"Baki ce komai ba..!
Amina tace"Yan mganar basa kusa..ai duk cikin ya"yan Anty Amarya ina girmama ya Jidda ba ruwanta..Mara kirkin sai Sa"adatu itama ya Sadiya ba baya ba akwai gulma..!
Dariya suka saka Zafira tace"Wai ni ban gane wacece matar Ya Danmallam din ba..!
Hanne tace"Anty Sakina..?gatanan mai Less iri Daya dana Anty Sarood..Gajera..!
Zafira tace"Naga wata Doguwa Fara kusa da ita..!
Hanne tace"Ba ita ba wannan Anty Aliya ce matar abokin Ya D'anmallan ne ya Aliyu..!
Amina tace"Ke don Allah..?oh na tuna ko wanman abokin nasa mai zuwa gaida su Hajiya wani Dogo baki haka..!
Hanne tace"Shifa matarsa ce Dazu suka zo da safe ai kinsa kawar Anty Sakinan ne. !
Amina tace"Ke kam matar abokai..!
Dole su zama kawaye kuma Halinsu yazo Daya itama sai kiga tana maka kallon kashi kashi..!
Hamida zatayi mgana kenan sai ga Kanwar Haj.Nasara ta fito mai kiban nan tana Tafe jikinta na rawa waya ce a kunnenta ta fito tana mgana sai Goran Ruwa Dake hannunta.
Mai su Amina zasu ba Dariya ba gwara su Hamida suna Rufe bakinsu kada taji ammh Amina Da karfi take Hamida ta Daketa tana Fadin"Dillah Amina kiyi a hankali kada taji..!
Amina na Dariya tace"Jar uba kalli Wuyanta..Timama kenan..?Wlh ko Buhun Dawa albarka Markadi..!
Daidai sanda Matar ta Juyo tana kallonsu daman tun dazu da suka shigo taga suma mata Dariya yanzu ta fito tana waya tana jin Dariyansu.
Tana juyowa suka shanye Dariyansu ta Harari Amina kafin tace"ke wa kike cema buhun dawa..?
Amina ta zaro ido ta kasa mgana Tana Danne Dariyanta.
Hamida tayi Saurin cewa"Ba Dake muke ba..!
Da Sauri Amina tace"Ai buhun dawar ce.!naga kin ma fi buhun masara ..Dankari..!
Matar ta Zaro ido kafin tace"Ni..?
Amina na Dariya tace"Ku kalli Duwawunta asama Hanne..!
Matar ta nufosu gadangadan tana Fadin"Kaga min yan iskan yara marasa Tarbiya..!
Kafin kace me sun Zura a Sittin Amina ce kan gaba sai hanyar waje suka Nufa suna Dariya Ta riga ta saki jikinta Tana kuma Gudu tana waigen su Hanne Dake bayanta sai ji tayi Ta buge Mutum agabanta Da kuma karar Faduwar wani abu wanda ya bada Sauti Tus...chas..!
Baya tayi da Sauri bayanta ya Bugu da Goshin Hanne Dake bayanta Sauran Kadan su Fadi Hamida ta Rikesu tana Fadin"Zaku fadi fa..!
Sai alokacin Hamida ta ga wanda Amina taci karo dashi ta kuma Lura da yadda Haraban Gidan ya Cika da maza bayansu ya Jafar har da wasu bakin Fuska ma.
Salati ta saka ranta Jikinta ba inda bai Rawa hanne kuwa datagama Fahimta baya ta koma tana Kifta ido kamar wacce tayi karya
Amina kuwa Tsoro ne ya kamata sanda ta Dago ido ta ga Ya D'anmallan agabanta Fuskar nan tasa ba Annuri ko Kadan Cikin Shigarsa wacce ta kara Fitomai da kyansa da Zatinsa Lokaci Daya da kwarjinsa.
Shikadai ne bata iya Hada ido dashi bazata iya jure kallonsa ba Tunda suka Hada ido taji gabadaya bakinta ya Mutu gabbanta sun saki ta yi Saurin Sadda kanta kasa tana Bin waayarsa Tadata watse akasa kenan lokacin data ci karo dashi Tayi sanadiyar Faduwar wayar.
Kamar wacce aka kai kasa haka ta durkushe ta fara Tattara wayar tana Fadin"Bansani bane..Kayi hakuri..!
Su Hanne suka saki baki suna kallonta Hankulan mutanen Dake wajen ya Dawo kansu har su ya Shamsu sun matso da ya Nazeem kallonta yake tana Tatarra wayar tayi Daidai yace"Amina ce ko..?
Wlh Yaya kaci Ubanta yarinyar nan sam bata da Hankali..!
Bata kara mgana ba sai da ta Tattaro wayar ta Mike bata yarda ta Kallesa ba ta mika mai wayar kanta na kasa.
D'anmallam Cikin Takaici yake kallonta ya kasa karban Wayar wai meyasa yarinyar nan bata da natsuwa ne..?ji yadda ta kwaso gudu kamar wata ballagaza kamar wata Namiji..?
Ganin yaki karba yasa Abokinsa Aliyu Dake Gefensa ya saka Hannu ya karbi Watsatsiyar Wayar yana Fadin"Ba kyau gudu acikin gida..!
Yafada yana kallon Amina acikin Ransa yana Tunamin ko kanwar Danmallan ne to bai santa ba.
Sai da yayi mgana ne Amina ta Dago suka Hada ido da Aliyu sai alokacin tasan ba Ya Da'nmallam ya karbi Wayar tasa ba.
Gabadaya taji ta muzanta ne ganin da Maza awajen yasa ta Ja kafafunta zata wuce su hanne kuwa suna gefe sun Rakube kamar wasu marayu.
Ba zato kawai taji wani Dogon Hannu mai Laushi ya Riko Duka Kafadunta da karfi ya Dawo da ita gabansa Cikin Mutuwar jiki ta Dago manyan Idanuwanta ta Sauke a nasa da suka Fara Sauya Launi saboda bacin rai.
Ya Jafar suna chan nesa suna Hira da wasu abokansu su ya Nazeem ne ke kusa ya Nazir kuma yana chan gefe saman manyan Darduman da suka shimfida a Haraban gidan yana kallon meke Faruwa ammh bai maida Hankali ba Chart suke da Hidaya matarsa Tana Fadamai Hayaniya ya Isheta sai yake tambayanta tana ina..?tace tana Bedroom din Hajiya inda ta Sauka shi bai ma tsaya lura da abunda ke Faruwa ba.
Kamar mayen karfe haka suka Tsaya suna kallon Juna shi yana mata kallon Haushi da Takaichi ne ita kuma ta kasa Sauke idanuwanta ji take kowani gabobinta suna yin Sanyi kamar yana Hukuntasu duk Rashin kunyarta yau sai da aka ga Tsoro a cikin Idonta Lokaci Daya

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment