Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa ba wanda ya damu ammh su Ya Jafar sun Tsargu ballema da suka ga yadda Baba Mallam ke ta Annushuwa kuma yana gaba gaba kan komai ko auransu Zulaihat bashi ya bada ba su ya Danmallam ne suka Zama Waliyansu..!
Basu gama mamaki ba sai da Liman yace"Allah ya gafartama Mallam an gama Raba Goron da Dabinon har yayi saura ma..!
Baba Mallam ya Jinjina kai kafin ya karkace ya zaro Bandir din kudi Sabbi yan Dubu Dubu ya ijiye gaban Liman Cikin Dattakonsa yace"Walicci zakamin Mallam Muhammad..?
Cikin mamaki yace"Waliccin wane kuma Allah gafarta mallam..?
Baba Mallan sai da ya kara Fara"ar Fuskarsa kafin yace"Waliccin Umarun Faruku zakamin aure zan kara masa ayau din nan acikin wannan masallacin..!
Liman yace"To..To..Masha Allah ai babu Laifi Allah gafartama Mallam sai Waliyan ita yarinyan su matso afara siga..!
Baba Mallam ya Murmusa kafin yace"Nine Waliyan Amarya..Ga Sauran yan"uwanta nan..!
Ya nuna su ya jafar da suke zaune mamakin kalaman Baba Mallam ya cika su.
Cikin karin mamaki Liman yace"Au kace Abun duk na gida ne..To masha Allahu..Ba bu laifi sai mu fara gabatar da siga ya sunan Amaryan..?
Sai da Baba Mallam ya gyara zama kafin yace"Sunanta AMINA..AMINA SA"IDU..!
Jafar da Nasir suka kalli juna kafin su juya suna kallon Baba Mallam Shamsu kuwa Kunni ya saki yana jin abun kamar almara..!
Liman ya washe baki yana Fadin"To..To..Masha Allahu wannan abu yayi kyau..Allah yasa a kulla alheri..!
Zamu fara gabatar da siga..Ladan ya Ciremana Lasifika..!
Da Sauri Baba Mallan yace"A"a abarta Liman..!
Liman cikin mamaki yace"Dokarka ce Allah gafarta Mallam ba"a Daura kowani aure cikin Lasifika..!
Baba Mallam cikin Annuri yace"Na yau kadai na Sauke Dokar liman..So nake naji Sautin Tattabatuwar auran Uwata da Umaru so nake na ji Sosai acikin kunnuwana Liman..!
Liman bai yi gaddama yace abar Lasifika,cikin Abunda bai fi mintina goma sha Biyar ba aka gabatar da siga aka kuma Tabbatar da Daurin auran AMINATU SA"IDU GUSAI da angonta Mijinta UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA akan Sadaki Naira Dubu Dari Cif..!
Adaidai Sanda Muryan Ladan ta Karade Lasifikan yana kara Jaddada Daurin auran Amina da Umar din Akan Sadakin da uban Amarya kuma Uban ango ya Biya Mallam Yunus Abdurrahaman bazanga..!
Awannan gabar Alkawarin Allah ne ya cika..!
Zanen kaddara ya tabbata..!
Auran ya Dauru.!
"fallasa wasu sirruka ne..!
Dalilin wannan auran za"a rasa rai..!
Fuskokin wasu amintattu zata bayyana..!
Zuciyoyin wadanda basu taba Tsammani ba zata girgiza..!
Abunda basu taba zato ba ya faru alokacin da basu shiryama hakan ba..!
Wasu sun makara..Saboda Alkalamin ya riga daya Bushe ko sunzo kafin Lokacin Allah bazai sauya wannan kaddaran ba SABODA RUBUTTACIYA CE..!
Daurin auran daya Faru a kunnuwan mutane Dadama da suka cika da Dimbin mamaki wadanda da basu yarda ba Sa"idu ba dan Mallam bane yau suka kara yarda da mganar wasu Mutanen yadda Baba Mallan ke Hannu da Mutane kawai zaka Fahimci yana cikin Farimcikin da bai Taba tsintar kansa aciki ba shi ya Hana Jafar ko Nasir cewa wani abu suma sai sukabi ayarin yan gaisawa da Mutane suna faman amsa Fatan Alherai daga kowani bangare..!
Baba Mallam Dakyar ya samu ya Fito daga masallaci su Jafar ya kallah yana Fadin"Ku scigaba gda amsan Fatan Alheri jama"a bari nayi wata waya..!
Daga haka yayi nesa da Masallacin ya Fiddo wayarsa ya Kira Danmallam..!
Tana gabda Katsewa ya Daga Kiran Cikin Mutuwar Jikin da Baba Mallam ya Saukarmai Tun Safe daya Kirasa yana Fadamai zai aura masa Kazamar yarinyar nan..!
Cikin Farimciki Baba Mallam yace"Umaru..!
Dagachan bangaram Muryansa a shake yace"Na"am Baba..!
Bai jira cewarsa ba ko yanayinsa ba yace"Yanzu nan aka Daura auranka Da Uwata..Ayanzu din nan AMINA ta zama Amanarka Umaru..daidai da Rana Daya in kaci Amanarta ko ka Dannen Hakkinta Allah na kallonka sanna amatsayina na Mahaifinka ban YAFE maka ba Umar daidai da Rana Daya in ka Zalunci AMINA.!
ya karishe Fada Cikin kaushin Murya
Gabadaya sai yaji kamar Duniyar na Juyawa dashi wannan shine gaba kura baya Damisa..!
Baba Mallam bai Damu da amsar ba ya Cigaba da Fadin"Ina Alfahari dakai..Yau ka cikamin Burina Umar..albarkata da addu"an Allah ya baka Zuru"ata tagari bazata yanke Daga bakina ba..Ina Rokon Allah yasa Amina ce Sillar Arzikinka da Daukanka..Ina ji ajikina Uwata ce Farincikinka watarana ko bana Raye alokacin nasan zaka Tuna dani Umar..!
Jin Mallam kawai yake ta ina wannan kwailar yarinya zata zama Farincikinsa watarana..?
An dai hadasa da aiki Yarinya kazama ga rashin Natsuwa da Taurin kai da rashin ji yana zaman zamansa Mallan ya Debo masa aiki Sai dai shi Yaro ne mai Biyayya har abada baya Fatan Ranar da zai Sabama Iyayansa..!
Shiyasa Cikin karfin hali yace"Nagode Baba..Allah ya kara girma..Insha Allahu zaka sameni mai biyayya..!
Baba Mallam cikin jin dadi yace"Nasani..nasan bazaka watsamin kasa a ido ba..Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen Daganan sukayi sallama bayan ya tambayi jikin Aba yace da Sauki sannan suka rabu da juna da cewar shi Danmallan din zai kira wayar Baba Sa"idun Baba mallam yace ya Kirasa Jafar ya Tahomai da wayarsa da Safe..!
Abunda kowa bai sani ba Tun Da Asuban nan da Danmallam ya Kira Baba Mallam yaji aransa wannan mafitan ne Allah ya nuna masa.
Bai yi shawara da kowa ba kafin ya tafi asibiti wajen Aba ya kirasa suka Tattauna Komai Daga farko har karshe sai da ya Fadamai duk abunda ya Faru kwanaki da na jiya Daddare da kalaman Baba Sa"idu da Rokonsa garesa ya kuma Roki Danmallam Daya auri Amina ba domin Umarni ba sai domin daman Yana da Burin Hada Dansa ko yarsa da Ahalin Sa"idu..!
Umar bai iya cewa A"a ba..Mallam ya wuce gaddama garesa Cikin wani yanayi ya amsa masa da cewa Ya amince wannan kalaman nasa su suka Tabbatar da Kaddaransa da Amina Kaddaran zama amtsayin miji da Mata..!

****

Cikin wadanda Daurin Auran Amina da Danmallam ya shiga kunnensu yaya na ciki ita da Hajiya da Mamanmu kai kaf wadanda ke gidan sun ji hadda Amina uwar gayyar Domin tatashi alokacin Hamida ta taimaka mata tayi wanka tayi alwala tana Rama Salolinta ta idar kenan tana Zaune Saman Darduma alokacin ma Tunanin Aminu take da Tunanin Halin Dayake ciki.
Kamar mafarki Taji muryan Ladanin nan yana bayyana sunanta da na Ya Danmallam amtsayin mijinta da aka Daurama taaure yanzu nan.
Ta Rude kanta kamar ya Kulle domin bata gane komai ba Sama sama take jin Muryan Mamanmu Daga Tsakar gida inda suka zauna tun bayan Dawowarsu daga asibitu tana Fadin"Kunji Abunda naji kuwa..?
Kamar Naji ana Fadin an Daura ma Amina aure da Danmallam..ku Saurara,kuji..!
Suma sun ji din sai dai sun kara kasa,kunni Saboda su gasgata,Hajiya kuwa tun jinta na Farko ta tabbatar da Duk abunda taji gaskiya ne..Mallan ne fa tasani Daman shurunsa Zai iya zama koma menene..!
To duk abunda akeyi a masallacin kamar agidansu akeyi saboda lasifukun masallacin akwai kara sosai,Radau suka sake jin wannan al"amarin Daya basu matukar mamaki Yaya Dake Dakinta Tana zaune ne sai da ta mike yayinda ya Zeena ta kwalalo ido tana Fadin"Wlh Mamanmu da gaske ne..Amina ce..!
Hamida da Hanne suka kalli juna Cikin mamaki kafin Hanne ta Rumtuma Dakinsu Hamida tana Fadin"Amina..Amiaa..Kin ji an Daura miki aure da ya Danmallam yanzu a masallaci..?
Kallonta Amina takeyi da manyan Idanuwanta da suka Zama wani irin Cikin wani yanayi tace"Naji..Naji Hanne..ammh bangane komai ba wani Danmallam din..?
Ni Umar naji an ce fa..?
Tafada cikin wani yanayi Hamida ce da ta shigo cikin wani yanayi tace"Shine Umar din Amina..Yayansu Hanne..Mijin Anty Sakina da Anty Sarood wanda ke zaune a madina..!
Cak Numfashi Amina ya Tsaya ta Fara Kokuwa dashi bata samu zarafin mgana ba taji muryan Yaya tana Fadin"Hajiya kinsani..?meyasa kikabari Mallan yayi haka..?
Amina bata dace da kamilalle irin Umar ba..Bata dace dashi ba sam..bai kamata kuyi haka ba..!
Sai kuka,acikin ranta kuma wani Sasaauci taji Tana ganin kamar Addu"anta na Shekaru ne Allah ya amsa sai dai Tana jin Tsoro tana jin tsoron An Hada Kamili kamar Umar da Amina kada ta zama mai sonkai kada taso yarta Shiyasa tayi mgana..!
Hajiya kuwa tana zaune sai Mirmishi take saki Annushuwa ta bayyana acikin ranta kafin tace"Sun Dace Hadiza..Duk abunda kikaga Mallam ya yanke mai kyau ne..Naki addu"a ne Allah yasa Alheri muka kulla..Allah yasa su aminan juna ne..!
Da karfi Mamanmu ta amsa da Ameen tana sharan kwallah tace"Yaya Amina fa y'arki ce..Tayaya zaki rika Fadin mgana mara kyau akanta ya zataji in taji abunda kike fada!
Tana mgana tana sharan kwallah..!
Amina Daga cikin Dakinsu Hawaye suka kwanyomata tace"Naji..Naji Mamanmu naji..Gaskiya ta Fada ban dace ba..Ban dace ba..!
Batasan Lokacin da wani kuka ya kwace mata ba Lokaci Daya tana Fadin"Wlh bansani ba..Bansan wannan kaddaran ke Bibiyata ba da Ban fara son ka ba Aminu..Wlh bansani ba..!
Taausayinta ya kama Hanne da Hamida suka karisa gareta suka Rumgumeta suma sai kuka Riris kamar anyi mutuwa..!
Zuwa Lokacin Wannan Daurin auran mai Cike da Bazata da mamaki ya kama Yaduwa a gidajen nan guda Biyu Anty Amarya sai da tayi suman Wucin gadi bata kara gasgata mganar ba sai Da shamsu ya shigo ya kara Tabbatar musu agabansu akayi ita da Hajiya Nasara,Haj.uwa na shashenta bata fito ba Duk da tasan abunda ya Faru domin taji..!
Alokacin da Kowacce take kiran ya"yanta masu aure na nesa tana Fada musu Anty Amarya bata cikin natsuwa ballatana ta iya kiran wani ta Fadamai awannan gabar abubuwan sun bala'in shammatanta
Abunda kowa bai sani ba alokacin Baba Mallam na cikin Falomsa na Shashensa tare da baki Daga Yola..!
Yana gama wayar nan da Umar Motoci biyu suka gyara parking kofar Gidansu kuma wajensa suka zo ya karbesu hannu Biyu ya kuma Saukesu afalonsa zuwa Lokacin mutane sun fara watsewa..!
Jikinsa yayi sanyi da yaji kamar yayi gaggawa AMINU ne saurayin Amina da iyayansa sun zo neman auran Amina da kuma ban Hakurin abubuwan da suka faru..
Ashe ashe jiya da dadaddre Aminu Daga Gumel yola ya wuce Allah ne ya kaisa Lafiya yaje gaban Baba Alhaji ya Fadamai komai yana kuka da Rokon suje Gumel suba ma iyayan Amina Hakuri su bashi auranta sai dai abunda bai sani ba sun makara..!
Mallam yaga Dattakon Alhaji Baba yaji matukar kunya alokacin Dayake Fadamasu Amina ta haramta ga Aminu yanzu taron chan na waje na Daurin auranta ne..!
Yana ganin wanda aka kira da Aminu ya tashi ya fita yana Rangaji hawaye Sunaa zuba Daga idonsa.
Sai yaji jikinsa yayi sanyi yaa ji aransa kodai yayi gaggaawa ne..?
Aminu Dakyar ya kai kansa Bakin Motocinsu da suka zo dashi Wayarsa ya Dauko biyu biyu yake gani da haka ya Kira Nenne..!
Tana ganin kiransa gabanta ya Fadi Daman kiran nasa take jira tana Dauka tace"Aminu ya ake ciki..?
Cikin karyewar murya yace"Na rasata Nenne..Nasara MEENATA..
Na makara Nenne an Daura mata aure da wani bani ba..!
Yana gama fadin haka ya Datse kiran ya Sulale nan kasa Dirshen ya Hada kansa da gwiwa yana kuka kukan Rabuwa da masoyi Rabuwa ta Har Abada..!
Nenne Dake cikin gidansu na Yola gidan Alhaji Baba yayyinta da kannenta sun zagayeta suna tambayata Lafiya Cikin fitar Hawaye ta kalli Mahaifiyarsu tace"Hajjo ya rasata..Aminu ya rasa Amina....an daura mata aure da wani kafin su isa..!
Gabadaya suka hada baki wajen fadin"Innalillahi wani"inna ilaihirraju'un..!
Sun sani Aminu zai samu matsala Kaddaran ta riga fata duk wani ahalin gidannan yasan yadda Aminu yake kuka yana rokon Alhaji Baba yaje yane masa auran Amina..
Ya Aminu zai yi..?
Bakin Alkali ya riga ya bushe..!
Zanen kaddaransa bata Amina bace..Kila na watace chan Dabam
Inda ya sani..Dama..Dama ace bai Hadu da Amina ba..Dama ace komai daya faru mafarki ne..!






*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

_Wannan shafin jinjina ce da godiya gareku masoyana a duk inda kuke masu Sharhi da masu fatan Alheri musamman yan Group dina na TA FITA ZAKKA COMMENTS SECTION da ku yan JANAF NOVELLA Tare da duka sauran gidajen marubuta da ake yin sharhin wannan Littafin nagani kuma na yaba naji dadi Allah ya bar zumunci gaisuwa ta musamman zuwa gare ku yan wattppdians kuma kuna kokari sosai nagode Allah ya bar zumunci.._


*🅿️22*

Zuwa dare duk wanda ya kamata yaji Labarin Auran Amina da Danmallam yaji,kowa mamaki kamasa yake yi in yaji Domin agabadaya da Dubawa ta mahanga ta Dan adam Amina bata Dace da Rayuwar Danmallam ba sai dai Ina Allah shi ke Tsara dukkan Lamuran sannan kuma ya zartar ya riga ya Dora alkalamin kuma ya Bushe akan Amina da Umarun dan bazanga..!
Aba yana asibiti ya jafar ya kirasa ya sanar dashi maimakon ya shiga bakinciki da takaici kamar yadda ransa ya darsu da Tunanin Baba Mallan yayi gaggawa domin Amina bata dace da Rayuwa irin ta kamili Natsattse Irin danmallam ba sai kuma sai yaji kamar zuciyarsa tayi son kai yaga kamar ita diyar tasa irin Mijin Daya dace da ita kenan baisan Lokacin Daya Daidaici gabas ba ya Fadi yayi sujudul Shukur ga Allah ya Dago yana Hawayen Farincikin da bai taba Zaton Daga jiya zuwa Dazu zai iya Fuskarta haka ba yadai ce zai aurar da Amina ammh acikin ransa yanajin kamar bai kyautu ba yana ji kamar wani al"amari zai faru ashe wannan al"amarin ne mai Daraja tuni kimar Baba Mallam ta kara Hauhawa acikin Zuciyarsa ya tabbata ko mahaifinsa Aminu gusai na Raye iyakar kaunar da zai bayyana masa kenan..!
Bangaran Amina kuma tun Lokacin Dataji labari data fara kukan nan bata Daina ba,Har Hajiya Babba da mamanmu sai da suka taru akanta suna ta bata baki bayan sun Fatattaki su Hamida Dake tayata kuka,Agabansu sai tayi kamar taji Duka Nasihansu ta daina Abu Daya ke mata yawo Aminu ta kasa gane wannan wata irin kaddarace da zata Raba ta da masoyinta ta kaita inda Har Abada baza"a taba sonta ba..Wannan wata irin kaddarace haka take ta Tambayan kanta..!
Hajiya Babba na tafiya Amina ta cigaba da gunjin kukanta har ta su Hamida sun daina sun koma suna Lallashinta,Ammh taki daina kuka Mamanmu kuma gajiya tayi ta rabu da ita ya Zeena ce ke kitchen tana samar da abunda zasu ci da wanda za"a kaima Aba Dake chan Asibiti suna Tunanin yasan abunda ke faruwa Tunda Baba Mallam baya Zartar da wani abu sai da saninsa shi da Hajiya Babba basu san wannan karon duka bai nemesu ba shi kadai dagashi sai Allah Daya barma Zabi bayaso yayi mgana da wani ko wata su ce ba haka ba shi yasa wannan karon ko Hajiya babba batasan me ya yanke ba Sai Daga baya..!
Tun Mganar da Yaya tayi ma Hajiya Babba ta koma Daki ko motsinta ba wanda ya sake ji,Sai Lokacin da iskancin kukan Amina ya isheta sannan ta fito ba wanda yaji Shigowarta illah Dundun data Dirkama Amina agadon bayanta wacce ke zaune kasa ta Hade kai da Gwiwa tana gunjin kuka alwala ta Dauro Dakyar shima sai da Hanne da Hamida sukayi ta magiya shine ita batayi sallar ba ta koma tana kuka..!
Dukkansu sai karan Dukan sukaji Amina ta bankare baya wannan Hannu shi kadai ne bata saba dashi ba Hannun Yaya ne..!

Cikin bacin rai ta kalli Amina tana Fadin"Ai bake bace da kuka ba Amina..Umaru ne da kuka domin shi aka Gurbanta ma Rayuwa..Mutum kamili kamarsa an Hadasa da wacce bata Dace dashi ba Amina kamar ki ace kin san Namiji..?Daman nasan wannan Firiritan nan naki watarana sai yakai ga haka har kina mana wani kukan banza to wlh ki kama bakin ki ko na sake Dana miki Dukan da sai kin Raina kanki Sakarya wawiya mara Tunani kawai..!
Ta karishe Fada Cikin Huci Amina na kuka tana Fadin"Wlh bana bin Maza..Ni ba yar iska bace..!
Yaya tace"Shi Jafarun zai miki karya ne..?yaron da yace ya ganki Rumgume dashi Ubanki ne shi..?wlh in bakin ki bai Mutu ba,zaki sha wahala ke baki ji kunya da Tsausayin kanki ba..?Mahaifnki nachan kwance asibiti taa Dalilinki Tir da Halinki Amina Tir wlh..!
Tafada Tana nuna ta da Hannu Cikin wani yanayi Hanne ce ta Dukar dakai Cikin wani yanayi tana Fadin"Don Allah yaya kiyi hakuri..Nasan Wacece Amina sai dai in kuskure akayi wlh bazata aikata abunda akace ba..!
Yaya bata samu bakin mgana ba Mamanmu Data Daga Labule tun dazu Tana jin yaya tace"Hanne ku kyalesu..Duk abunda zasu fada sun Dade basu fada ba..Abu Daya na sani Amina ba Haka take ba..Amina bazata Watsar da Tarbiyanta ba..Akwai abunda ba Daidai ba..!
Yaya tayi mirmishin Takaici kafin ta Juyo tana kallon Mamanmu Cikin Sanyin Muryanta tace"Yaushe ne Ranar da Amina zatayi kuskure ki nuna mata tayi ba Daidai ba..?
Yaushe ne Ranar da zaki bi bayam gaskiya ba bayan Amina ba..?
Mamanmu tace"Sai Ranar da na Tabbatar da gaskiyan kuke fada yaya..Ammh ayanzu har gaban Abada bazan bar Tsagin Amina ba..Amina Diyatace da nake mata soyayyar da ko ya'yan dana Haifa da cikina ban musu shi ba,Har abada bazan Daina Fadin kunyi kuskure Amina ba haka take ba..!
Yaya Batace komai ba kawai ta girgiza ta raba ta gefen mamanmu ta fice Mamanmu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan su Hamida tana Fadin"Ku bata baki..Bari akawo abinci taci tasha mgani..!
Daga haka ta saki Labulen Dakin ta koma to a wannan gabar sai kukan Aminan ya tsaya cak kamar an Dauke ruwa Zuciyarta ta Bushe bata jira Lallashin kowa ba ta Gyara zama Daga zaune ta tada sallah domin jikinta har yanzu atsame yake bata iya Tsayuwa waje daya ta Gudanar da sallar ba..!
Wajen karfe Tara na Dare sai ga Ya Jafar da ya Nasir sun zo Amina na Daki taji Ya Jafar na fadin"Ina ita mara kunyar Aminar .?
Yaya Data Fito daga Daki tana gyara zaman Hijabin jikinta Da zasu tafi asibiti tace"Tana ciki..Tun dazu da taji Labarin abunda ya faru take kuka..!
Yaya Jafar sai da ya Lailaya ashar kafin yace"Yar iskace bata Daku bane..Ai wannan auran Baba mallam ya Daurasa ne ba domin ya dace ba wlh..!
Ya Nasir yace"Uhmm.Ni kuma ina ganin Daidai ne Jafar..Amina sai irin su ya Danmallan ne daidai dasu..!
Ya Jafar yace"Kamanta ne shi fa ba irin mu bane bai da Hayaniya bai kuma kaimu Zafi ba..!
Ya Nasir yace"Duk na yarda..Ammh kuma ya fimu Shekaru sannan cikin Ruwan sanyu yake Ladabtar da Mutum..Wlh ina ji ajikina Wannan al"amarin ba Tsarin Mallam bane Tsarin Daga Allah ne..Abu ne da Hasashe ko Tunanin mu bai taba kawo ba yanzu muka gama mgana da Ya Nazir shima haka yace..!
Ya Jafar yace"Nima ya Kirani yana Tambayana sai dai ina mamakin waya fadamai..?
Ya Nasir yace"Tab to har su Nazeem Dake Zaria sun ji Labari..Ya Danmallan din ne ban da masaniya ko ya sani..?
Mamanmu na zaune saman Tabarma cikin baranda tace"Nima yaran nan sai kirana suke Zulahait dai tace min Aisha ta Kirata ta fadamata itama tace Abida ta sanar da ita da wayar Hajiya..Suma mamaki suke suna son ji ko gaskiya ne nace musu gaskiya ne..!
Ya jafar yayi ajiyar rai kafin yace"Dawa dawa zamu koma asibitin..?
Mamanmu tace"Da yaya zaku je ni bazani ba zan zauna wajen Amina..!
Ya zeenatu tayi karaf tace"Ya Jafar don Allah zani..!
Tana rufe baki Hamida da Hanne suka Fito suna Fadin"Muma zamu don Allah..!
Sai da ya Hararesu kana yace"Bazaku ba..gobe da safanan za"a sallamesa..!
Mamanmu ce tace"Kaje dasu don Allah Jafar..Oh na manta ina mai ciwon kunni..?
Ya jafar yace"Yayi sauki sosai kin ma Tunamin ban karbi mganin da Baba Mallam yace nazo na karba ba..bari mu dawo..kuzo mu tafi Dare yayi kuma bana son rawan jiki yarinya ta natsu..!
Ba musu suka shiga Taitayinsu Ya Zeenatu ce ta Dauko kwandon data Zuba abinci yaya daman da hijabinta Jawad na gefenta sai su Hamida sallama suka ma mamanmu suka Fice,ya zeenatu da Hamida Motar Ya Nasir suka shiga ashe matarsa na gaba Anty Fadila da ita za"aje..!
Yaya kuma da Hanne suna Motar ya Jafar
Koda sukaje Aba yaji Sauki sosai sun samesa yana cin kayan marmari ga Ferfesun kayan ciki ne,da suka tambayesa wa ya kawo masa..?
Yace Hajiya Babba da Hajiya uwani yanzu suka fita Idi Direba ya kawosu ya riga ya koshi shiyasa suka ijiye abunda suka zo dashi Aba ya amsa gaisuwan Hamida da Hanne ya Kallesu Cikin kulawa yana Fadin"Ina Amina..?
Hamida tace"Tana gida Baba..!
Daman ta sani Amina na ransa ita din yarinya ce mai shiga rai kaunar da iyayanta Biyu suke mata Allah ne kadai yasanta sai dai baza su bayyanata ba Saboda kawaici da kuma Tunanin ba ita kadai suka Haifa ba
Daganan bai kara mgana ba Jawad yaja kan jikinsa yana Tambayansa ya makaranta yana bashi amsa basu Dade da zuwa ba sai ga Baba mallam ya shigo Cikin shigar Alkyabbansa da Rawaninsan nan suka Ramkwafa suna gaishesa ya amsa cikin Sakin Fuska yana kallon Su Nasir kafin yace"Ashe nan kuka zo..?
Kan Nasir na kasa yace"Eh Baba..Na kawo Fadila ne ganin bata zo ba..!
Yana zama saman kujeran Dake gefen gadon Aba da Ya jafar ya tashi ya bashi yace Lokaci daya"Yayi kyau..Kun kyauta Allah yayi muku albarka..!
Su hamida ya kallah ita da Hanne kafin yace"Naga zara ban ga wata ba..Ina mamana..?
Wannan karon Hanne tace"Tana gida Ita da Mamanmu Baba..!
Kai ya gyada kafin yace"In ta warware zamu daidaito ni da uwata insha Allahu..!
Ba wanda yayi mgana sai Su ya Jafar ne suka Murmusa kawai,Baba Sa"idu ya kallah yana Fadin"Kai ai ka warke tunda naga har kana iya Daukan Jawaad..!
Baba Sa"idu yace"Da sauki Baba..nacema ce su sallame ni yau sukace sai da safe in Likita yazo..!
Baba Mallam yace"Gwara ka kara samun karfin jikin ka kafin ka koma gida..!
Ganin suna gaisawa da Aba yasa su ya jafar sukayi shirin tafiya sai alokacin Baba Mallam ya kalli yaya yana Fadin"Hadiza bana son ganin wannan Damuwar afuskarki Daga gani kin ta kuka..Sa"idu ne babban banza shi ga inda ya kawomu ke kuma kina chan kina kuka har wata Cuta ta kamaki ta Miki illah ina amfaninta..?Ina ce Amina ce Matsalarku..?to ta fita Daga Hannunku ta koma karkashin ikon Umaru sai ku daina Damuwa..Ina ce ba Shikenan ba..?
Yafada yana kallon Aba da kunya yasa ya Sunkuyar da kansa Yaya kuwa kanta na kasa batayi mgana ba har sukayi musu sallama suka fice suka bar Baba Mallam anan da Jawad daya makale ma Aba yaki tafiya Baba Mallam yace a kyalesa in zai taho zasu taho tare. !

******

Tun bayan Fitarsu daga gidan ta Mike ta Leka Amina abinci ta Debomata Farar Shinkafa da Miya Kadan Amina taci don ma Mamanmu tana bata baki Tana Hadawa da Lallashinta Fadi take yi"Ki daina damun kanki ni nasan babu abunda kika aikata..Kuma mganar auran in baki so batare da kowa ya sani ba zan kira shi Danmallan din na Rokesa ya Sauwake miki..Ina Zaki iya da Sakina..?Matansa fa Biyu Kina yarinya Dake duka duka Shekarunki nawa Amina..?Sha Shidda fa Ko sha bakwai din Baki cika ba Har yanzu..Gaskiya akwai kwa ruwa acikin Hukuncin Mallam..!
Take fada cikin bayyana bacin ranta Amina kallonta kawai take batayi mgana ba to me zatace..?Tayi mgana ai bai da amfani komai ya riga ya kare ta rasa Aminu ta gama rasa komai Mganar Rabuwa da Ya Danmallam kuma bata isa ba har gaban Abada bazata watsama Baba Mallam kasa a ido ba kamar yadda bazata watsama Mamanmu ba uwa uba gasu Aba da yaya bata Fatan wani abu ya kara Giftawa,Ta riga ta sani Kaddara ta,kaita wani bingiren da Har yanzu ta kasa dora kanta a inda kaddaran ta jata ta kaita in tana tunawa ma sai wani Rauni da Faduwar gaba su Lulleta waje ne da har Abada zatayi Daraja ba ta sani..!
Har mamanmu ta gama bata tana ta Mita panadol ta bata tasha sai kuma ta shafa mata man zafi ajikinta Da Amina taji Dadinsa kwarai hawaye take yi da kukan zucci acikin ranta tana kara Ninka kaunar dake yi ma Mamanmu tana Fadin dama dama ana Sauya wani abu da Tuni ita Amina ta Dade da Sauya Yaya da Mamanmu amtsayin uwa..!
Amina bata sani ba Allah yana Boyemana wani abun ne kafin mu sani saboda kila alokacin in ya bayyana mana bamu da karfin gwiwan da zuciyan da zamu iya Dauka..!
Boyayyin Fuskokin wani Lokacin Alheri ne garemu kila sanda zasu bayyana Mun Tsaya da kafafunmu Raunin da zai bayyana garemu kadan ne..!
Sai da ta tabbatar da barci ya fara Daukan Amina kana ta bar dakin Dakinta ta koma bata Dangana ako"ina ba sai Cikin Bedroom dinta tana shigowa wayarta Dake kan gadonta ta sake Daukan kuwwa alamun kira ya shigo Da hanzari ta karisa ta Dauki Wayar sunan wacce ke kiran yasa bata Tsaya bata Lokaci ba ta Daga Daman ta sani zata kirata itama din Jiran kiran nata take yin bayan Tabbattuwaar abunda basu taba Tsammani ba..!

"Dayyaba Da saninki komai nawa ya Rushe..Dayyaba da saninki akamin wannan yankar bayan..Da Saninki kika bari yarinyar da ta Ratso cikin gabar aikina alokacin danake Hasashen ina gabda cin nasara..Na sani hakan zata faru shiyasa nake ta Kiranki

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment