Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa Kikace baki hada komai da Sa"adatu ba nima baki Hada dani ba Domin Uban mu daya da ita..!
Amina tace"Ke dabam ita dabam..In kuma kin Dauka hakanne to haka din ne..Ni fa Hanne basai kin min gorin Sa"adatu yar"uwarki bace ni kuma bare ce.!
Hanne ta saki baki kafin tace"Yaushe nace miki bare Amina..?

Cikin kufuluwa tace"Bansani ba..!
Tazo zata wuce fuu Hanne tace"Da kike mganar yar"uwata ce..To in dai baki karbi gaskyan Sa"adatu yar"uwarki bace ita din kanwa take gareki..!
Sai alokacin Amina ta waigo Cikin wani kallo tace"Kanwata ta gidan uban wa..?
Kai Tsaye hanne tace"Kanwar MIJINKI ce..Kanwar ya Danmallam ne ai shi bai isa yace ba kanwarsa bace..!
Amina taji kamar ta Tsinke hanne da Mari sai kawai taja Tsaki mai girma kafin tace"Sai dai kanwar Ubana bata Miji ba..!
Daga haka ta wuce afusace ta bar Hanne na rakata da Dariya Tayi Tsaki yafi sau goma in ta Tuna da Abunda Hanne tace shiyasa suna shiga Dakin mamanmu taga Sa"adatu kwance kan kujera ta Fara sakin tsaki tana Fadin"Ni fa bana son shisshigi..Abaya an nuna kai da banza duk Daya sai yanzu kuma azo ama wani Haba Haba dakai..Munafunci ne bana so..Kowa yayi ta kansa..!

Take fada tana Hararan gefe ya Abida na Dakin kuma tasan da Sa"adatu take itama Sa"an tasan da ita take yi ammh bata nuna ba Tunda abun nan ya Faru na wattanin baya Anty Amarya tace mata ko musu ta sake yi da Amina sai ta sani ammh yarda ta Tsani Amina ko Hanya bata Kaunar ta hadasu sannan karin bakincikinta da taji labarin auran dake tsakaninta da ya Danmallam Haba ai ba"a duba ba ba Sa"anta bane sannan Anty Sakina tafi karfin ta Hada Miji da Amina don ma Anty Amarya ta kwabeta da kame bakinta da kanta cikin mganar ne da yau sai Amina ta raina kanta maimakon haka sai ta nuna kamar ma bataji ba ya Abida ce ta tanka Tunda tasan Halin Amina cikin Fada tace"Amina ki mana shuru..Wlh bazaki Fara mana jidalinki da Daddaran ba..In kuma kika ki wlh bar ganin na yi sanyi yanzu sai mu Taru mu nada miki na jaki..!
Amina ta Hura hanci kafin tace"Mu ta kanmu kowa yayi ta kansa..Dariya ba fa so ba mai hali bai bari ba.!

Cikin waka take fada tana nuna Sa"adatu da baki ya Abida sai ta kasa mgana gashi mamanmu bata Dakin tana Tsakar gida wajen su hanne.
Amina cigaba da wakarta tayi tana fadin"Takun yayi..Wasu sun saki Reshe sun kama ganye...Warrrr..!
Sai ta watsa ma Sa"adatu hannu data juyo tana kallonta sai ta Daga mata ido ta Juya kafin ta fice ganin ya Abida ta Biyota ta gudu ta fice tana Dariyan Shakiyanci Ya Abida ta kada kai kafin tace"Kai Amina sai fatan Allah ya shirya. ya Danmallam zai sha fama..Sa"a kiyi hakuri kin ji ko..!
Sa"adatu tayi wani munafukin Mirmishi kafin tace"Bakomai ya Abida..Amina yar"uwata ce kuma haka take..Kinga tunda musan Halinta sai muci mganin da zama da ita kamar yadda su hanne sukayi..!
Ya Abida tace"Yauwa Sa"adatu na..!
Dariya kawAi tayi tana son ya Abida bata da Damuwa sam kaf cikin ya"yan Hajiya Babba da Hanne ne basa shiri itaama Saboda Amina ne..!
Abida aranta tana Tunanin ina Amina ta iya wakar nan su da ba waka suke ji a agidan ba,Abunda bata sani ba a wayar kawarta Zainab Amina tasa wakar Warr.
Agidan zasu kwana shiyasa suka Firfito waje ana Hira baki sai gobe zasu fara sauka ya Aisha ma gobe zata iso ita da ya Jamila da ya zulfa"u duk agoben zasu iso ya Jadwa ne bazata zo ba jamila da Jawahir ne kadai zasu zo har ya jalila bazata samu zuwa ba abun yayi kusa kusa da Rasuwar Yaya da suka zo Baba mallam ne ma yace duk suyi zamansu sai nasu Hannatu saboda kada Zirga zirgan tayi yawa .!

******

Baba maallam na gaban Makeken Dorowansa na Littafai Dake falonsa Sanye yake da Jallabiya Mai ruwan zuma kansa ba Hula fufuransa ta bayyana sai Farin gilashinn da ke karamai karfin gani Falon akwai hasken Wutan gen ko"ina tar,kansa na chan kasa yana so ya Dauko wani Littafi Anty Amarya ta shigo Falon cikin kwalliyarta Ita ke da Shashen ayau din dazu ta iso taga yana Tare da su ya jafar da su Aba sai ta koma sai da Tara ta wuce goma saura sannan ta Dawo domin ta tabbatar da zuwa Lokacin Mallam din shi kadai ne..!
Har ta kariso bayansa bai sani ba sai da ya Dauko Littafin ya Juyo sannan yaci karo da ita bai nuna Razana ba illah kallonta da yayi yana Fadin"Da girmanki marliya sai ki shigo ba sallama..?
Ido ta Juyamai Kafin tace"Nayi baka ji bane..ina nan na Tsaya ina karema Mijina kallo sai yanzu na Lura ashe ashe Mallam ya Tsufa bansani ba..!
Ta karishe fada cikin yar Dariya Shima Dariyan yayi kafin ya wuce gaba tabiyosa abaya cikin Sanyinsa yace"Sanda aka bani auranki Farin gashi bai gama cika kaina ba marliya..Kuma ahaka kika gani kikace kina sona ko ba haka ba..?
Ya fada yana zama kan Daya cikin kujerun falon mai zaman Mutum Daya tana Dariya ta zauna ahannun kujeran tana fadin"Ah..Ni yaushe nace ina sonka..?Kuma ka rufeni da rawaninka bansan haka farin gashi ya Cika kanka ba..!
Tafada tana jan gashin nasa yar Dariya yayi kafin yace"Ai lokacin bai kai haka cika ba..Bayan na aureki ne kika Ida Tsufar dani Marliya..!
Yafada yana kallomta Baki ta Rike tana Dariya tace"Mallam!.
Saurin tareta yayi da fadin"Dole na fadi haka..Naga yau Amaryan tawa Gori take ji da tsokana..!
Dariya take yi tana fadin"Kodai ka Tsufar dani mallam?
Mirmishi ya saki kafin yace"Ko nan da shekara ashirin muka kara tare..Mallam dinki zai cigaba da kallon yarintarki Marliya..!
Sai kanta ya fashe ta fara Mirmishi Ta sani duk cikin matansa tafi kowaccensu Kuruciya kuma Tsakani ga Allah sai kana da kuruciya ake Damawa Dakai.
Bata samu zarafin mgana ba wayarsa Dake saman Center table din Dake falon ta Dauki Kidan Larabawa Gabadaya hankalinsu ya koma kan inda wayar take cikin Daidaita Natsuwarsa yace"Hanzarta mikomin kada ta katse..!
Da azama tatashi ta Daukomai sai dai ganin sunan mai kiran yasa nan da nan Ranta ya baci ABU NA..!
Hajiya ce wannan Keda sunan tun auranta da Maallam ta sanshi dashi abu na kamar wani yaro mtseewa tsaki taja acikin Ranta kafin ta mikamai wayar yana Fadin"wake kirana..?
Sai da ta koma Kujeran dake gefensa kafin tace"Ina ga Hajiya ce..!
Tafada tana Daidaita yanayinta Abu Daya ke batamata rai sufa da sunayensu yayi Saving a wayarsa ammh ita Hajiya kai Tsaye yake nuna ita din ta Dambace komai zai yi kafin ya aiwatar dashi ita da Sa"idu sai sun fara Tabbatar dashi sannan..!
Tana jinsa Daya karbi wayar yana Fadin"Hajiyar ce ma ba musu ba..!
Kiran ya katse sai yabi bayan kiran tana jin sandda Hajiyar ta Dauka da Sallama ya amsa yana Fadin"Hajiya..!
Bata ji me tace ba sai dai taji yace"Kizo shashena ki sameni daman nima ina son mgana Dake..!
Daga haka bata san me tace ba yace yana Jiranta ta katse kiran
Sai da ya gama sannan ya Dago yana kallon Anty Amarya kafin yace"Amarya..Amarya..!
Dan juya ido tayi kafin ta dan Tura baki na Shagwaba Mirmishi yayi kafin yace"Yanzu dai kimin hakuri adana duk wannan amarcin naki zuwa anjuma..Ina so na gana da Hajiya na minti talatin in ba Damuwa..!
Yake tayi kafin ta mike cikim basarwa tace"ba damuwa..in kun gama sai ka Taboni..!
Cikin jin Dadi yace"Shikenan Allah yayi miki albarka..!
Aciki ta amsa ta fice tana kunkuni ahanya suka Hadu da Hajiya tasha Lullubinta suka gaisa ta wuce Anty Amarya ta bita da kallo tana Fadin"Tsofai tsofai dake bazaki hakura da miji kibar ma yara irin mu ba Mtsewww Jaraba..!

Take fada har ta fada shashenta Hajiya batama san tanayi ba Falon Mallam ta karisa sukayi mgana kan Kayan garan Amaran ne da Tsarin da za"a cire musu sai abincin Bikin da na yan Daurin auran,Baba Mallam yace su bar abincin Daurin aure Mallam Hamza ya Dauki nauyin mutane bayan Daurin aure zasu je suyi Reception abincin gara kuma yace a Diba kamar yadda tsarin yake..!
Bayan sun gama mganar Hajiya ta mike zata tafi tunda ba ita keda Mallam din ba shi ya Tsaidata da Fadin"Zainabu kunyi mgana da Da'nki kuwa..?
Tana Daga Tsayen tace"Sa'idu..?
Yar dariyq yayi kafin yace"Sa"idu..Sa"idu..Ke da Sa"idu bansan wanda yafi wani kaunar wani ba..Nan fa muke mgana dashi gani ni Ubansa ammh sai ya tsallakeni komai nace sai yace Mallam kuyi mgana da Hajiya yadda tace haka zaa"ayi..Anya Zainabu baki kwacemin Sa"idu ba..!
Hajiya na Dariya tace"Ni ban kwacesa ba..Ammh ai kowa yasan Sa"idu na Zainabu ne..Kayi hakuri dai da aron da nake baka..!
Mallam yace"Ai na ma gode..Tunda ana bani aronsa!
Dukkansu dariya sukayi kafin tace"Nazir kake mgana..?Mun yi mgana dashi dazu yace sai Ranar Daurin aure zai zo..matarsa kuma yace saboda aiki yara kuma ga makaranta..!
Baba Mallam yace"Bama shi ba..Ai shi nasam zan samu labarinsa awajenki..Umaru fa nake mgana..!
Hajiya ta tabe baki tace"Sai kace min Danka. kanin Sa"idu sai nafi ganewa..!
Mirmishi yayi kafin yace"Zauna muyi mgana nasan kema bai kiraki ba..!
Hajiya ta zauna gefen Mallam tace"Jiya ya Kirani mun gaisa Daganan bai ce min komai ba badai wata matsala bane ko..?
Mallam ya Sauke Numfashi kafin yace"To matsala ne kan matansa..!
Hajiya tace"Topha me ya faru..?
Mallam yace"To ni ma bansan Farkon abun ba..Yadda dai Abu kattab ya Kirani ya fadamin kan zuwa wannan Sha"anin ne..!
Hajiya cikin mamaki tace"Daman ba Danmallam din ya kiraka ya Fadamin ba..?
Mallam yace"Kema kinsan bazai Fadamin ba..Sa"idu ya Kira sukayi mgana nima yanzu bayan fitansu Abu kattab din ya Kirani mukayi mgana..Kan zuwa Sha"anin nan ne yace yaso yazo shi kadai saboda zirga zirga da kashe kudi kuma ko wata biyar basu yi da komawa ba,gashi ba wasu kudi a hannunsa sai yace zai taho shi kadai sai Sakina tace zata zo ita zata Biya ma kanta kudin jirgi,To bayan haka ita Saratun daman yace tayi hakuri ta zauna har su dawo ga karatunta tunda tana hada Degree dinta anan Jami"ar musulunci to bai kuma sani ba ko Sakinar ce ta Zugata har ta amimce sai ta fara mai boren itama sai ta taho shine yace duka su hakura bazai zo da ko daya ba Sukayi ta Hayaniya yayi musu yaji yaje ya kwana acikin makaranta shine ita Saratun taje ta Fadama Abu Kattab din shi kuma ya Nemo Umaru yayi musu Sulhu ya kuma bama Umaru Umarni Daya Taho da Sakina Ita kuma Saratun ta zauna ta jirasa har su dawo Tunda tataba zuwa kinji Abunda ya Faru..Kuma dazu fa mun yi mgana dashi bai ce min komai ba yadai cemin zai taso gobe zai kwana ajidda Daga jidda zai shigo Jirgi zuwa Kano..!
Hajiya tace"Allah ya kyauta..!
Mallam yace"Amin fa.bana so Kattab yaga kamar na nuna Umaru dana ne..Da sai nace itama Sakina ta zauna ban ga abunda zata zo yi ba..!
Hajiya tace"Barta tazo ba ruwanka..Inkana da iko da Mijinta ita fa..?
Cikin Dattakonsa yace"Ko bata tashi agidana ba..Kamar ya"yana Haka na Dauki matan ya"yana Saboda haka na isa da su gabadayansu ballatana ahannuna tatashi na kuma aurama Umaru ita..!
Hajiya ta mike tana Fadin"Gwara da baka ce ba..Allah ya sauke su lafiya..!
Ya amsa da Ameen daganan sukayi sallama ta fice ya bita da kallo bai tana ganin mace mai kawaici da kauda kai iron Hajiya ba to sai marigayiya matar Sa"idu su kan suna da kauda kai kan abunda suka Haifa yasan Hajiya bata taba saka baki kan Umaru da sakina ba,ko abaya ballatana yanzu..!
Anty Amarya ya Kira yace ta shigo Ya sallami Hajiya ba jimawa sai gata ta Dawo ta kara sabunta kwalliyanta yayi ta kallonta yana yaba mata kanta nakara Fashewa.!

*****

Tun washegari bakin nesa suka fara isowa yan Gusai ne farko su ya Jawahir har da Zafira akazo duk da ba"azo da mamanta ba ta Makalema Ya Jawahir sai da ta saka baki aka barta tazo suka Hade dasu Amina sai Ihu da Murnan ganin juna Tunda su ko sha"ani ake yi sai dai su mamanmu su je su kan bamai barin su.
Bayan sun iso ba Dadewa sai ga ya Zulfa"u ta iso ita da Uzairu yana shirin kamallah karatunsa gabadaya na Degree Ya Nazeem dai yace shima sai ya gama Project dinsa zai dawo ya Aisha ma ta iso ita da ya Sadiya da suka Dawo da ga America ciki ma gareta su Sa"adatu haka suka ozare jiki daga su Amina an ga Yar"uwa.
Amina tace daman munafukace su hanne dai basa mgana Amina ce ta iya wannan jidalin.
Ranar laraba su ya Jamila suka iso da ya Nazifa da ya Fatima sai ya Akila da ya ikram dake kusa ya Zulahait sai wajen yammah ta iso Daga jigawa gida ya cika da baki sai Hada hadar Biki akeyi.
Da daddare misalin karfe 9pm na dare su ya Danmallam suka sauka su Amina bama su sani ba sai da Sabeeha tazo kiran Ya Sa"adiya Dake nan gidan Aba wajen su ya Zulaihat tazo ga Anty Sakina sun iso.
Ya zulaihat na wajen tace"Daman da ita zai zo..?
Ya Jawahir tace"Ni har shi na Dauka bazai samu zuwa ba..Tunda har goggo Husai ma ita da Ya Jadwa bazasu samu zuwa ba..!
Ya Jamila ta kada baki tace"Ya za"ayi kuce bazai zai zo ba..kuma kunsan zai zo komai rintsi shine fa Babba..!
Amina da su hanne na wajen Amina tana jin sun iso bata kara mgana ba ta Hade ranta ganin hanne da Hamida na kallon ta suna kuskus zafira dai na gefe bata son abunda suke fada ba.
Ya zulfa ce ta Kalli Amina kafin tace"Ki tashi ki chakare Aminene..Miji ya sauka fa..!
Amina taji ta muzanta ta fara Fiki Fiki da ido sai suka saka mata Dariya Gabadayansu har suna Tafawa kawai sai tatashi Fuu ta fice Daga Dakin daman suna Dakin yaya ne gabadayansu su hanne suka rufa mata baya jawahir tabi Amina da kallo kafin tace"Amina sai dai Allah ya tarota..!
Basu kuma hadu da Sakinar ba sai Washegari wajen walima suka Ganta,Su Dayake basu zo da wuri ba,sai da suka gama Hada komai na Rabon,da wainar da akayi da abinci almajirai sukayi gaba dashi su kuma ya Uzairi ya Dauko kayan rabo a Mota..!
Atamfansu ta ankon su ya Aisha suka saka da sabbin Hijaban da Hajiya ta Dimkamusu,Su sukayi rabo ita da Hamida,Hanne da Zafira sai Sa"adatu data gayyato su mariya yan ajinsu Amina taso ta tada fada su hanne suka taushe ta akayi komai aka gama An bama ya Zeenatu kyaitan murya da Tajwud sai kuma ya Abida na Tsafta da Sanin Hadisi.
Sai nasihan aure da mallanm Datti Shugaba yayi musu Amina bata ma san Sakina na wajen ba taje tana Raba musu Takeway din da suka saka Nama da Meatpie domin kajin gidan gona sun sha wuka.
Da ta bata sai taki karba sai da Sabeha ta karban mata,Amina sai alokacin ta kalleta ta wani Kalleta Sakai sakai itama kuwa ta rama ta wuceta aranta tana fadin"yi sabgrki in yi tawa..Baki gabana..!
Ita kuma sakina tana mamakin girman Amina taga ta kara tsawo ba kamar rasuwar nan ba.
Karfe shida da wani abu aka tashi Walimar ammh su sai dare suka baro makaranta sai da suka daidaita komai sauran kayan rabon da abincin Daya ragu suka bama Sauran Daliban makarantar.!
Da suka Dawo amaran suna gidan ya Jafar su suma chan suka wuce suka kwana sai da safe suka Dawo gida sukayi wanka suka saka atamfarsu Sabuwa suka koma gidan suna ganin Shiryawan Amare bayan sallar Jumma"a za"a Daura auran..!
Hajiya Shashenta ya cika da baki yan"uwanta daga maiduguri sun so sannan Dangin mallam yan bazanga sun iso tun jiya,Soyayyan Naman kajin da aka soya tun jiya tace ma Haj.Masara ta ijiye a wajenta tana so ta bama baki sai taje Shashen ta Karbo Tunda duk ba yaran sai Haj.Nasara tace ta kaima Anty Amarya Ajiya data ga Baki sun cika Shashenta.
Gashi Anty Amarya sun tafi porthercourt ita da  ya Aisha da yagana kanwarta sai Haj.Uwani Tun safe suka bi Jirgi Wayar Anty Amaryan ta Kira sai tace mata ta Tambayi Sadiya ita tabama ajiya tace in Hajiyar tazo abata..!
Saboda Jama"a da hayaniyar Biki yasa Har Hajiya ta shiga Shashen Anty Amarya ba wanda ya Lura da ita Danginta cike da Daki duk da bata nan,Sakina ce a tsakiyarsu an yi mata Rumfa tana fadin"Ai baku sani ba..Da naga yarinyar sokuwa ce yasa na Zugata nace mata saboda yayi amaryane yaki zuwa da ita Nageria kunsan Larabawa da kishi..Daman kuma tamai Bore lokacin da na Fadama ta Mgamar auransa da Amina..Koni fa bai fadamin ba dana Turkesa sai cemin yayi ai yasan naji da muka zo gaisuwa da abun ya bani haushi sai na Hadamai famfo wajenta ita kuma ta hau kai ta Dinga Bore Wlh duk Sanyinsa sai da ta kaisa bango..Naso ne ta kuresa ya Saki wawiyar banza..!

Gabadaya suka saka Dariya wata acikin yan"uwansu na Dutse tace"Dakyau..Sakina cikin Ruwan sanyi tayi waje ta baki waje..!
Sakina tace"Wlh ai bana nuna mata ina Kishi da ita..Nuna mata nake yi mun zama Daya sakaryan ta yarda..Cikin sauki nake hadamata Tarko tana fadawa..!
Ya Sadiya na wajen tace"kinsan larabawa ba wayau wani Lokaci kuma basu san kishi ba..!
Sakina tace"Basu san komai ba..Sai son miji!
Dariya suka saka gabadaya sai Sadiya tace"Sai ma Amina tatare ku zama ku Uku sai Show din yafi kyau..!
sakinaa tace"Ai bama zata taren ba..kinsan Allah na yarda dakaina yadda aka Daura auran nan haka zata kare anan agaban iyayanta Daga karshe har su gaji su raba auran ni bata gabana..nafi karfin na Hada miji da wannan kwailar Allah ya Tsareni..!
Suka saka Dariya wata mai zakin murya tace"sai dai ki bar mata Mijin..!
Sakina tace"Kwarai da Dai in Rab'u da abu ta sanshi..Gwara na bar mata gabadaya..!
Idonsu ya rufe basu ga Hajiya Tsaye agabansu ba sai da tagama jin komai sannan ta kara Rafka sallama suka juyo suna kallomta arazane sai ta nuna musu su yara ne cikin Haba Habanta tace"Shigowata kenan ina ta sallama shuru..!
Da sauri Sadiya tace"Bamu ji ba Hajiya..!
Sai tace"Kuna nan baku je kun Debo abinci ba..Sadiya ina sakon da Amarya ta bar miki ki bani..!
Da sauri ta mike tana fadin"Yana Daki Hajiya bari na miko miki..!
Gabadaya sun yi tsuru tsuru barin ma Sakina da kanta ke kasa Hajiya ta kalleta Cikin takaici tace"Sakina baki je wajen kannen naki ba ashe..?
Cikin Daburcewa tace"suna ina ne Hajiya..?
Tace "Suna gidan su Jafaru..Kuje keda su Sadiya ku taho dasu an kusa Daurin auran kunsan kuma da an Daura za"a wuce dasu..!
Jin haka yasa ta mike jiki na Rawa tana Fadin"Yanzu kuwa hajiya..!
Sai ga Sadiya da Botikin nama ta mikama Hajiya ta karba tayi godiya ta fice sai da ta fita wata cikin kannen Anty Amarya tace"Allah yasa Hajiya bata jimu ba..!
Sadiya tace"Inaga bata ji ba gaskiya..
Sai alokacin Sakina ta iya Sauke Numfashi.
Abunda basu sani ba Duka mganganunsu Hajiya taji su sannan mgnganinsu sune silar Faruwan wani abun da basu mutane da yawa basu taba zato ba..!
Har takai shashenta abun na cin ranta ta kuma Kudirci kafin a gama Bikin nan sai ta nuna ma Sakina ita din banza sai dai kuwa in zata bar ma Amina Danmallam ne ammh Zama Daram in ji mai Naguda..!








*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*🅿️28*

Karfe biyu da rabi na rana aka Dauran auran su ya zeena bayan an idar da sallar jumma"a ana Daura auran Hajiya ta kira ya Fatima awaya tace su taho dasu Abidan malam zai yi sallama dasu zasu tafI kada Dare yayi ga yanayin Tsaron kasar tamu daya riga ya lalace sai fatan Allah yabamu zaman lafiya.
Gabadayansu suna gidan ya jafar har su Amina,tunda amaran suka ji an daura auran suka fara kuka su ya Jamila na musu Dariya suna fadin muma hakanan akayi mana kuma gashi mun zauna..!
Amina ce harda wakar"Su sukace suna so..Da basu ce suna so ba..Da ba"a basu shi ba..!
Ya Abida na kuka cikin Hijabinta ta Leko Tana hararan Amina Lokaci Daya tana fadin"Kema yarinya kwana nawa ne..?Keda ma zaki bar kasar bar ma wasu dariya..!
Tana fadin haka sai bakin Amina ya Mutu ta yamutsa fuska kafin ta Tura baki tace"Tab..Wlh in na je Allah ya Tsinan..!
Ya nazifa na wajen tace"Kin je ma kin gama zuwa yarinya..!
Amina ta kara Hade rai tana faman kunkuni aka saka mata Dariya gabadaya har da su Hamida daganan ta Hade rai bata kara mgana ba har suka shirya komai suka Tattara kayan amaran da suka cire waje Daya su Amina suka bamawa suka fara yin gaba su Uzairu zai zo da Mota ya Daukesu sauran kuma suka taka da kafarsu tunda ba wani nisa.
Koda suka iso kofar gidan ba Jama"a sosai,Amina ita hankalinta ma baya ma wajen kallon jama"ar wajen duk Rashin kunyarta bata juran kallon Taron maza.
Bata ma Lura da ya Danmallam Dake bakin wata bakar mota ba Shi da abokinsa Aliyu suna mgana su Hanne ne suka ganshi,Hamida Dake kusa da Amina ta tabota tana nuna mata barayin da suke Lokaci daya tana Fadin"Amina kalli mijinki..!
Amina tabi inda Hamida take nuna mata da kallo,Suna dagachan nesa ne ba lalle su gansu ba,dukkansu suna Tsaye jikin Motar ne Danmallan yana Sanye cikin Shadda kalan Sararin Samaniya Dinki riga da wando tazarce anyi Dinkin zamani na matasa masu ji da kansu sai hula zanna bukar Zaran yanayin aikin shaddan Jikinsa kafarsa cikin Bakin Rufaffan Takalmi na Fatar damisa sai bakin agogon Fata Dake tsitsiyan hannunsa na Hagu bashi ke mganar ba Aliyu Dake kusa dashi yake saurareshi shi key din Mota ne ke hannunsa yake kadawa Lokaci bayan Lokaci yana Sassauta yanayin Fuskarsa.
Sai da gaban Amina ya fadi da Sauri ta kauda kai ta sani ita bata isa tace Ya Danmallam ya dace da ita ba Tazaran Dake Tsakaninsu mai girma ce,kana kallonsa zaka hango Tsantsan kamala Dattako da sannin addini sannan uwa uba kwarjinin da Haiba ta mutumin da yasan addini sosai da sanin ya kamata sannan da yana kyau, kyau irin na fatan kowacce mace zabinta ya kasance haka..!
Bata son mgana saboda ranta ya riga ya baci shiyasa taja karamin Tsaki ta kauda kanta sai ma ta kara Sauri ta shige gidan bata son wata mgana ammh Hanne da Hamida sai suka saka Dariya har suna Tafawa Allah yasa Zafira na baya tare da yan garinsu.
Hamida ta kara riko gefen Hijabinta tana Fadin"Amina ki kallesa mana..Kai wlh ya Danmallan yayi kyau matuka..!
Amina ta Juyo a Fusace daidai sanda suka shiga get din gidan Baba mallam tace"Ba mijina ba..A"a ubana ne..Nace sai dai Ubana Hamida haba..Kin Dameni..!
Hamida da hannu suka kalli juna suna kunshe Dariya Hanne tace"Mijinki ne..Kuma ko bakomai ya Danmallan yana matsayin Uba ne agareki..!
Amina ta kalleta shekeke kafin tace"Allah..?Aiban yi mamaki ba..Kowa ya ganni yasan auran son zuciya yayi da yar cikinsa..!
Hamida da Hanne suka zaro ido Hanne tace"Amina kin ma kanki karya..Kaf gidanan ko ya Nazir bai kama kafar ya Danmallam akomai ba wlh..Baki magodema Allah ba kin Samu miji Kamar sa bama..!
Cikin Hargowa Amina tace"Ban gode ba..Domin bani nayi tallar kaina ba..Da kike mganar duk gidanan ba kmarsa to ni ina ruwana..Kinsan dai ina da Aminu..Kudi kyau nasaba ga yarinta bai isa ya nuna mai ba..!
Sai kawai ta saka musu kuka abunda basu taba gani ba in ta Tuna da Aminu bata iya Boye rauninta har Abada bazata taba mantawa dashi ba ko wani Hali yake ciki yanzu Allah masani..!
Jikinsu yayi sanyi suka kasa mgana ganin su zafira suna kokarin shigowa ne yasa ta juya ta fara tafiya suka mara mata baya Hanne na Fadin"Allah baki Hakuri Amina..Ammh aragama yayana ko Saboda ni..!
Amina ta Daga murya tana Fadin"Saboda ke..?ai ke din ba Mutumcinki nake gani ba Hanne..Ki kyaleni kada ki Tunzurani na yi miki Tijaran da zaki ji Haushina..!

Hamida tace"Hanne abar mganar..!
Daga haka suka kyaleta har shashen Hajiya sun shiga ba Dadewa sai ga Amaran da yan gusai,ba kamar wanchan karon ba Amina wannan karon batayi ra"ayi ba shiyasa da su Hanne suka ce tazo su raka amaran Nasiha Shashan su Haj.uwani da Nasara da gidan Aba Amina tace sai sun dawo ita ba inda zata jin haka sai suma jikinsu yayi sanyi suka ki binsu Zafirace dataga sunki zuwa sai ta Bisu.
Basu fito ba sai da Zafira tazo tana Fada musu amare zasu tafi ssannan suka fito Lokacin ma suna Falon Mallam ana musu nasiha da bankwana sai fito da kayan abinci su Ya Akilu suke motocin amaran suna kwasa suna sakawa acikin Booth ya Zeenatu Tawagar angoyen ta suna shirye harda mace Daya wacce zata tafi da amarya suka zo ya Abida dai tafi gata tunda su Anty Amarya na chan sai gobe

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment