Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karyan nan zaki haifarmin da Gaba cikin Gidana kuma in hakan ta faru Uwani zaki sha mamakin hukuncin da zan yanke akanki Wlh..!

Gabanta ya fadi taya ya komai zai kwace mata Burinta bai cika ba yasa ta kwantar dakai tana ta basa Hakuri sai da taga ya Hakura sannan ta Sauke Numfashi ta koma ta zauna tana kokuwa da bacin ran dake taso mata..!
Ba domin ta kasa galaba akansa ba da Tuni Mama ta samo mata kan mallam ya zama sai yarda tayi dashi sai dai ina ta gaji da kashe kudi akansa ta Hakura Allah yana tare dashi kuma ya kare bawansa wani abu bai isa ya Cutar dashi ba sai dai ko in ya so..!
Ganin yadan sauko har suna Hira yasa ta Sako mganar dake cin ranta"Mallam ya mganar Amina da Danmallam ne..!?
Naji bakace komai ba haryanzu..?
Kai tsaye yace mata"Har gobe sunanan a matsayin miji da mata..wani abu kike son sani kuma..?!
Ya kalleta cikin son Tabbatar da abunda yake Tunanin take son ji game da lamarin.
Da sauri ta sauya mganarta da cewa"Maallam mganar tarewa fa..?ai tunda angama mai wahalar itama sai yayi mata Visa da Shedar zama achan kamar yadda yayi ma Sakina ya Tafi da matarsa ni aganina zai fi mallam..!
Ya dade bai yi mgana ba har ta Fidda rai kafin taji ya sauke numfashi Lokaci Daya yana fadin"Bazan yi haka ba..zan bama Mamana daman da bana ma kowacensu..Bazata tare a matsayin matar Umaru ba sai ta gama makaranta ma"ana in sunyi Candy in Hadata da yan"uwanta in aurar dasu..!
Hajiya uwani da Farimciki ya cika sai ta kanne cikin wani yanayi tace"Nan da shekara nawa kenan Mallam..?
Kai Tsaye yace"Hajiya tace alissafi Shekara Daya da wani abu in bai kai Biyu bama..!
Ranta Fari tas kafin Lokacin nata Burin ya cika wato ma ta kwantar da Hankalinta Amina bata cikin Tsarinta yanzu tunda mijin ma baisan da ita ba kuma tarewar ma ba yanzu ba hakan ya Bala"in yi mata Dadi har sai da Fuskarta ta Nuna cikin dan yanayinta tace"Gaskiya kuma fa hakane..Ko Sa"idu kada yaga anyi mata Rashin Adalci..!
Wani banzan kallo yayi mata Kafin yace"ko Sa"idu ina da iko da Kansa ballatana abunda ya Haifa..Ko cutar dashi zanyi bazai taba mgana ba..Ballatana ba wannan Tsakani na dashi.Kauna ce da Biyayya Tsakanin Uba da abunda ya Haifa..Kada ma na Sake jin wannan mganar Sa"idu namin Biyayyar da ko ya"yan dana Haifa basa min yana wahala dani da Dukiyata batare da na yankamai albashi ba gayamin cikin Tarin mazan da na Haifa akwai wanda ya zauna Dani yake wahala dani kamar Sa"idu..?
Kai ta girgiza ta kasa mgana Miyan bakinta ya kafe cikin Dattakonsa yace"To ki saka aranki Sa"idu Shakikana ne..Kafin na same su shi na Sama kuma ina masa kwatakwacin kaunar da Uba zai yima abunda ya Haifa..Ki saka wannan aranki..!

Daga haka bai jira cewarta ba ya mike  Dauke da Littafinsa ya Nufi Cikin Bedroom dinsa yana Fadin"Ni na shiga ciki sai kin shigo..!
Da kallon Takaici ta bisa kamar tatashi ta Makesa haka take ji Sa"idu rai Daya ya hana Burinta cika agabanta Mallam ke fadin yafi yemai ya"yan daya haifa Dariya tayi acikin Ranta Saboda itace silar rashin zaman Umar da Nazir agaban Ubansu ballatana su taimakamai bata so su sha gaban ya"yanta Yanzu kuwa Burinta yana gabda cika Nazeem ya kusa gama makaranta sannan Tsumi da Tanadi ya karanta wato Economics sannan yayi Degrre dinsa na Biyu kan abunda ya shafi Kasuwanci yana Dawowa zata san yadda zatayi Sa"idu ya matsa ya bama mai waje wajensa ya kasance shine kan duka Dukiyar Mallam din Kafin Uzairu shima ya gama yazo su hada hannu hango kanta Take shekara Biyar masu zuwa ita Amtsayin Hajiya babba..Ya"yanta ne masu gidan ita ce mai Bada Umarni da mgana da yawun mallam wannan Tunanin yasa ta farinciki ta tashi Cikin Takunta ta nufi Bedroom din mallan tana cigaba da Tsara wasu abubuwan acikin ranta..!

Amina kuwa sai washegari Hajiya ta ganta saboda sanda ta shigo gabadayansu sun yi barci Ya Abida ce kadai idonta Biyu tana karatu hanne ma ta Dade da yin barci.
Da safe ko gida bata koma ba kayan Hanne ta saka da hijabinta na Hadda Tunda guda Biyu hannen gareta.
Suka tafi Hadda Hamida bata je ba bata da Lafiya ciwon mara Ya zeenatu ke fadama da Amina taga bata ga Hamidan ba..!
Sai da yammah da suka Dawo Amina ta Dawo gida ita Da hanne suka Duba Hamida taji sauki ma,Hanne bata jima ba tayi musu sallama ta wuce gida Mamanmu daman jiran Amina take yi taji ya ake ciki tun Safe Aanty Amarya ta Kirata taji Labari mai Dadi ba wani bayani shiyasa Hanne na Tafiya taja Amina kuryan Dakinta Tana Fadin"Ya kuka yi da Mallam din..?

Amina ta Sadda kanta kasa kafin tace"Mammanmu na kasa..Bazan iya kallon Baba mallam nace bana son jininsa ba..Bai kamata na rama Tarin Alherinsa da sharri ba..Sannan in Aba yaji Wlh sai ya kusa kasheni agidanan..!

Ta karishe kamar tayi kuka ba Domin mamanmu ta kai zuciyarta nesa ba da sai ta kaima Amina Duka yadda Wani Takaicinta ya kamata ammh duk da Haka sai da ta Tureta tana Fadin"To Shikenan tunda kin kasa..sai kije..Sakina ta gasaki don Ubanki..bakuma zaki taba Daraja ba Tunda baya Sonki..Kuma matar Cushe bata Daraja .!

Yadda ta Zageta ta kuma Tureta yasa tasan ranta ya baci da Sauri ta riko Hannayenta tana fadin"Ba haka bane mamanmu..Wlh na kasa ne bazan yi kallon Baba mallam nace mai bana son auran nan ba..!
Mamanmu da kanta har ya fara ciwo Saboda takaici tace"Shikenan na fita Acikin mganar nan..Ba ruwana daman yancinki zan kwatan miki..!
Amina taji kanar tayi kuka kafin tace"To ke kije mana ki fadamai mamanmu..!
Hararanta tayi kafin tace"Saboda ni ce nake son rabuwa da shi ko..?ba inda zani ke kika sani ni sakamar min hannu Ke ji chan ki karata Wlh Amarya da Sakina bazasu barki ki zauna Lafiya ba.!

Amina tace"Tab..Sai dai ni ce bazan bar su zauna Lafiya ba Mamanmu..!
Ta razana gabanta na Fadi tace"Bangane ba..?
Amina tayi dariya kafin tace"To ai ba Tsoronsu nake ji ba..mamanmu ai Amina nake kirarina badai ta Mutum ba sai ta Allah su din banza!
Basu isa suyimin Abunda Allah bai min ba..!
Ta dade tana kallon Amina sai taga kamar Shagube tayi mata shiyasa cikin son tabbatarwa tace"ko kin fara son Danmllan din ne..?
Ta fada cikin Hararanta Amina ta Zaro Ido kafin tace"Ni..?Allah ya kyauta..ni Aminu kadai nake so..!
Ta Karishe Fada cikin wani yanayi Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Na Dauka kin fara son shi ne nace Ke kika sani..Domin Danmallam dai ya fara Tsufa auran wuri ne bai yi da kuma Haihuwar da bai samu ba..Kadan ne Aba din ku fa ya Girmesa..

Amina ta zaro idanuwanta suna shekk tace"Kai Mamanmu ko Aba fa bai Tsufa ba ballatana ya Danmllam..!
Mamanmu tace"Eyee..Kina son shi kenan Tunda ke baki ga tsufansa ba..?
Tafada tana Dungure mata kai Amina ta Dafe wajen tana fadin"Allah ya Tsari Amina..wannan ne zan so..Ya taba fa cemin banda natsuwa kuma ni wai kazama ce..!
Ta fada kamar alokacin yake fada mata Takaicin abun na Dawo mata Mamanmu ta kwace hannunta tana Fadin"ni sakeni..Kekika sani..Ba ina neman hanyar kwatan miki yanci ba kina bani kunya ba..Na barki dashi..Kin dai ji kazama yake ce miki Allah kadai yasan kuma wata kalma zai kara Jifanki dashi in ya ganki agidansa an riga an Tusamai ke..!
Amina ta Tura baki kafin tace"Sai na rama wlh..!
Mamanmu ta kalleta cikin Tunanin mafita ko mgana batayi ba ta Tura Kofar Tiolet din Dakinta tana Fadin"An kira sallah..!

Amina fita tayi ranta yadan yi sanyi ganin kamar mamanmu ta Dauki Zafi da Farko ammh Taji Dadi taga Daga baya ta saki ranta ajiyar rai ta sauke Tana jin kaso mafi yawa daga cikin Damuwarta suna yayewa Samun uwa irin Mamannu is a Bleessing..!
Mamanmu kuwa har Aba ya Dawo ta kasa samun wata mafita tana ganin ta bangaran Amina ba nasara Dole zata Jaraba ta bangaran Sa"idu ta Latsa ta gani ko zata ga Jini..!
Shiyasa koda ya dawo tayi wanka ta Shirya cikin riga da zani na Atamfa Hamida ta saka ta gyara Shashen nasa Dazu dataji Saukin jikinta Kayan abincinsa kuma tun kafin ya Dawo akai kai komai ciki.
Sanda ta fito duk suna Tsakar gida kan Tabarma suna Hira an kunna Gen akwai haske shiyasa basu shiga sun kwanta ba..!
Ganin bata ga Jawad ba yasa ta kalli Zeenatu Dake fama da karatu tace"Ina Jawaad..?
Hamida ce tace"Aba na shigowa ya makale masa..!
Mamanmu kamar ta saki Tsaki yaron nan zai zame mata ciwon ido sai ta rabashi da Uban taga ya zai yi shege kawai..!
Mirmishi ta saki kafin tace"Ni ina Dakin Abban ku. Ku kwanta da wuri ke Zeenatu saboda makaranta Gobe..!
Da toh suka amsa mata har ta wuce suka cigaba da Hiransu Amina da Hamida suke ta uban gaddama sai da Zeenatu ta Daka musu Tsawa tace sun dameta.!

Koda ta shiga Shashen Aba ta iskesa zaune shi da Jawaad suna cin Tuwom Shimkafa Miyar shuwakan data Girka Dazu da yammah Saboda Aba din Ranta ya kara baci ganinsa Dare Dare kan cinyar sa yana bashi Tuwon abaki Dakyar ta iya shigowa cikin Dakin tana kokuwa da yanayinta..!
Kan kujera ta zauna Tana fadin"Sannu da zuwa..Ka shigo ina wanka..!
Da yauwa ya amsa mata yana fadin"Haka yaran suka ce..!
Kafin ya cigaba da cin Tuwonsa yana Tambayan ko Jawad ya koshi ya Dagamai kai alamun eh Mamanmu tace"Daman Gulma ce irinta Jawad..Bai dade da gama cin nasa ba .!
Aba yace"Kinsan yaro..Ballatana ko abaya Jawad dani yake cin abinci ko da riga yaci nasa ne..!
Takaici bai barta tayi mgana ba Tana kallonsa har ya gama cin abimcin tatashi ta Dauki Faranti ta Fito dashi Ta mikama Amina tana fadin"Saka shi a Kitchen Amina..!
Da Sauri ta zo ta karba ita kuma ta koma ciki ta ga Jawaad ya gyara zama kan cinyarsa yasa ranta ya kara baci ta kalli Jawad tana Fadin"Jawad tashi kaje dakina ka kwanta..!
Tunda tun bayan rasuwar yay wani Lokacin in ya saka Rigima wajen Aba yake kwana ita kuma bazata iya Daukan wannan ba ta gama da Uwarsa kuma shi yazo ya rika sakata Damuwa ba..!
Aikuwa make Kafada yayi alamun bazai je ba Aba ya kalleta yana Fadin"Kyalesa in yayi barci sai ki kaisa..!
Takaici bai kara sa tayi mgana ba ta koma kan Daya daga cikin kujerun falon ta lafe ta maida hankalinta kan Tibin Dake falon cikin tashan Larabawa tana ji Aba ya maida hankalinsa kan jawaad yana Biyamai karatun da sukayi yau a makaranta Tun tana jinsu tana Gumduma ma Jawaad zaki aranta har ta fara barci Sama sama taji Aba na Kiran sunanta ta Bude ido tana kallonsa cikin Mamaki yace"wai har kin yi barci..?
Har jawad yayi barci na mika shi wajen Zeenatu nace yayi Fitsari kafin ya kwanta..!
Mikewa zaune tayi Dakyau tana sosa idonta kafin tace"bansan sanda barcin ya kwasheni bane..!
Kai ya gyada kafin ya wuce ciki yana Fadin"Bari nayi wanka..!
Da toh ta Bisa kafin tatashi tabi bayansa Yana shiga wankan ta Fitomai da jallabiya da gajeran wando ta koma ta zauna tana jiran fitowarsa Daya fito ya ganta sai da yayi mamaki cikin mamakin yace"Baki kwanta ba..?
Kai Tsaye tace"Eh ina son mgana Dakai ne..!
Bai damu ba yace"Bari nayi shafa"i da wuturi ke kin yi ko.?
Da sauri tace"Eh saboda bata so yace sai tayi alhalin ba Damunta yayi ba Khamsul salatin ma dole take yinsu.
Sai da ya saka Jallabiyan ya Shimfida Darduma ya tada salla har ya idar tana zaune ganin haka yasa bai Tsawaita addu"a ba ya juyo yana kallonta kafin yace"Ina Sauraranki..!
Gyara zama tayi tana Tattaro Jarumta da wani Kalan Tsausayi tace"Abban Jawad daman kam mganar Amina ce..!
Cikin dan Fargaba yace"Amina..?me Aminan ta sake yi kuma..?
Da sauri tace"Kwantar da Hankalinka batayi komai ba..Kawai ni ke son mgana Dakai kam Auran da mallam ya hada Tsakaninta da Danmallam na wajem Hajiya..!
Kallonta yake yi ko Kiftawa bai yi ba cikin mamakinta yace"Ina jinki..Sai me ya faru kuma..?
Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Tsakani ga Allah Abbansu baka ganin an kwari yarinyar nan..?
Cikin kosawa yace"Ina jinki..jeki kai Tsaye kan mganarki..!
Mamanmu bata Lura da yanayin kallonta da yake yi ba ta cigaba da Fadin"To gani nayi shi ba sa"anta ba In fa aka duba ya kusa haihuwanta in da auran kauye yayi..Ina Amina zata kai shi..?Sannan ga tarin Kishiyoyi har Biyu Abbansu a shekarun Amina batasan Dubarun zama da Kishiya ba,Shiyasa naga bari nayi maka mgana gaskiya aduba wannan al"amarin..!

Kallonta yake yi yana kokuwa da bacin Ransa kafin cikin Kaushin Murya yace"Ita Aminar ne tace miki bata son Dubarun zama da kishiyoyi ba..?To don Ubanta agidan nan Tsakanin mata Biyu ta taso..Gidan Baba Mallam kuma Hudu garesa reras gayamin wani karatu ne ya Ragemata bayan na wadannan gidajen..?
Sai mamanmu ta Daburce cikin Inda inda ta fara fadin"Ai kasan yarinya ce..Allah na Tuba ko hamida girman jiki ne..Ammh sai wannan shekaran ne suka shiga sha shida fa..Ina zata kai Umar..?
Akwai zalunci gaskiya..!
Kai Tsaye yace"Naji an zalunceta..Yanzu me kike so ayi..!?

Ta zata ya yarda da mganarta ne yasa Cikin Fara"a tace"Yauwa..Mallam kawai zaka je ka fadamawa baka son wannan Hadin na tabbata zai saka Danmallam ya saketa..!

"KE BALARABA..!

Aba ya Daka mata Tsawa da sai da ta Tsorata cikin Bacin rai mai Tsanani yace"Ita Aminar ne ta aiko ki kizo ki Fadamin naje na samu Mallam na Fadamai bata son auran Umar..?Tana so ya saketa..?
Mamanmu Sai taji ta kasa mgana Mikewa yayi cikim bacin rai yana Fadin"Dake nake mgana..!
Cikin kwantar da Murya tace"ba yadda ka Dauka bane..Wlh basu dac..!

"daman waya ce sun dace..!

Ya katseta cikin Tsawa kafin ya Cigaba da fadin" A yanayin Rayuwar Umar Kwata kwata Amina bata Dace dashi ba..Ita din ba ajinsa bane..Kinsan waye Umar kuwa..?Kyakyawan Asali Ubansa Malami ne, da ba iya Nageria ba kasashen Duniya sun san da zamansa Umaru nada shaidar Degree guda Biyu akan abunda ya shafi Qur"ani da Hadisai Balaraba tashin Madina karatun Madina garin ma"aiiki Kinsan adadin iliminsa..?Koyarwa yake a Babbar Jami"ar Musulunci ta Madina Shine kike fadin an zalunci Amina domin an aura mata Mutum nagari mai kamala da nagarta..Mai Sanyi mai biyayya da gudun mgana Shine kike fadin an zalunceta..?To bari kiji ba ita aka cuta ba Shi aka Cuta..Shi aka Tauye Balaraba ammh bai Bude baki yayi mgana basai ku..!?to ni Ubanta banda Sanadin Ubansa da ko Filin jirgin sama bazan taba Tsallakewa ba..!

Ya karishe fada cikin bayyana bacin ransa har jijiyon kansa na mikewa.
Mamanmu kuma ta Daskare Rashin Sukuni ya shigeta tasan ba Nasara wannan gabar bata ci nasara ba sai dai bata sare ba cikin Lallashi tace"Kayi hakuri abun bai kai harda gori ba..!
Dakatar da ita yayi yana fadin"Ko ni Sa"idu ban isa Mallam yayi Umarni akaina na Tsallake ba ballatana abunda na Haifa ki Fadamin gaskiya Aminar ce ta aiko ki ko..?
Mamanmu ranta ya gama baci shiyasa tace"Yarinya ta fadi Ra"ayinta ne Abbansu kada kaga Laifinta..!

Bai jira cewarta ba Fuuu ya fice yana kwala Kiran Sunan Amina Tun daga Cikin Dakin har ya fito Tsakar gidan Mamanmu ta rufamai baya gabanta na Fadi.
Amina da suke hira da Hamida da taji kiran Aba sai da gabanta ya fadi kuma sai suka ganshi agabansu kwatsam cikin Tsoro ta mike tana fadin"Gani Aba..!
Yadda idanuwanta sukayi ne saboda Tsoro sai ya ganta kamar Hadiza Shiyasa sai ya Sauke Murya yana Fadin"Zo nan..!
Lokaci daya ya juya ya Raba gefen Mamanmu ya koma Falonsa Amina ta koma Daki gabanta na Fadi ta Dauko Hijabinta ta saka tabi bayansu Hamida da Zeenatu sukayi Tsuru Tsuru suna Tunanin me ya faru kuma..!
Dukkansu a tsaye ta gansu Aba da Mamanmu sai ta kara Rikicewa yasa ta Zube gabansa cikin Rawan baki tace"Gani Aba..!
Cikin rawan murya sai yaji Fushinsa ya Sauka sai yaji Tsausayinta komawa yayi ya zauna yana Sauke Numfashi kafin yace"Amina..Ni waye a wajenki..?
Sai da ta kallesa sannan tace"Kai Baba na ne..Mahaifina..!
Cikin Jinjina kai cikin wani irin Sauti yace"Indai ni mahaifinki ne Amina..Ki sani ko bayan raina kika bijirema Auran Jinin Baba Mallam ban yafe miki ba Amina..!

Ba Amina kadai ba hatta Mamanmu ta firgita cikin wani yanayi Amina ta Dago ta na kallon Aba cikin Taruwan Hawaye aidanuwanta.
Ganin haka yasa ya Daga mata kai yana Fadin"Eh haka nace..Ban yafe miki ba Amina..Sannan zan sallama ki acikin ya"yana..Bazan jure ganin Abunda na Haifa ya Bijirema Mutumin da ya zama gata na ba..Mutumin da ya Lullube Rayuwata da Duka Alheransa..ki Tuna da wannan..!
Da haka ya mike ya shige ciki ya bar su nan Amina ta kalli mamanmu sai hawaye sharr.
Mamanmu tayi saurin cewa"Tashi kije zamu yi mgana da safe..!
Ba musu ta mike ta fice bayan ta share hawayenta tana fita su hamida suka fara Tambayanta Lafiya Mirmishin Daya fi kuka ciwo tayi kafin tace"Bakomai..!
Daga haka ta shige daki kokarin Daidaita kanta take yi domin tayi alkwarin daina bayyana rauninta kan wasu abubuwan..!
Ko washegari kasa ce mata komai tayi mamanmu ta tuna yadda suka kwana Aba bai kalleta ba tasan kwabarta tayi Ruwa da Safe ta Fadama Madina komai ita kuma tace bama zai sabu ba auran nan  bazai Daure ba koda ya Tabbata din.!
Amina kuma ko hanne bata fadamata abunda Aba ya fadamata ba,sai dai ta Dauki nauyin mganar acikin ranta tana jin kamar abu ne mai wahala.!

Haka Rayuwar ta cigaba da Tafiya su Zeenatu suna cigaba da Jarabawarsu sun gama Weac sun fara Neco gefe Daya kuma ana cigaba ana cigaba da Shirin Bikinsu wanda Baba mallam yace nan da wani Lokaci za"ayi Auran nasu kamar yadda Tsarin yake..!







*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*



*🅿️27*

A kwana atashi ba wuya a wajen Allah gashi har kwanaki sun wuce an shiga sattitika sannan an shiga wattani Tunda su ya zeena sun kamallah Jarabawar fita babban Sakandiri sai kuma mganar auransu ne ya taso gadan gadan kamar yadda kowa ya sani ne Mallam baya aurar da ya"yansa sai kin sauke Qur"ani da Haddan sauran Littafai Sannan Bisa ka"ida Makaratanr Haddarsu zata Shirya Walimar sallama data Bada kyatttuka kamar yadda aka saba.

To wannan karon bata Sauya zani ba shiryen shiryen ke gudana Tunda nan da Sati uku Baba mallam yace za"a Daura auran a mika amaran a Dakunansu Ya zenatu kaduna za"a kaita ita kuma Ya Abida porthercourt inda Mijinta ke aiki.
Ta kowani bangare shiri ke gudana Sai dai shirin yafi girma a bangaran gidan Baba Mallam kamar yadda aka sani Hajiya Babba ke da Alhalin komai a hannunta hatta kayan Daki sun gama komai Na Abida Ya Zahra ke da Alhakin siyan komai Tunda ita ke poethercourt ita hajiya ta turama kudi ta siya manyan kayan achan Kananun da sukayi saura ne aka siyesu anan,na Zeenatu ma ya jidda Dake kano aka barma komai ita tayi siyayyan komai ranar Jere kadai take jira babu abunda bata siya ba kamar Yadda Hajiyan ta tsara komai,Dayake Aisha ta bar kaduna aiki ya maida mijinta Abuja.

Tunda aka Tsaida Lokaci ya Abida da ya zeenatu suke ta rama atsaye sai wuya da ido kowa yasan sun fi Damuwa akan sauran da aka aurar duk sun yi sanyi barin ma ya Abida dake da Zakewa ammh yanzu ta koma Ruwan sanyi,Ko su Amina sai sun gaji da Tsokanarta sun kyaleta bata ma bi ta kansu kamar baya ballatana ya Zeenatu daman bata cika sakar musu ba Sai dai tafi ma ya Zulaihat sakewa da Mutane da Sakin Fuska..!
Ana biki Saura kwana goma Hajiya tace aje ayi jere kaduna Na Abida sai ana gobe Daurin aure Haj.Uwani zata tafi ita da ya Aisha su hadu da su Zahra su yi jeran kafin Amarya ta kariso..!
Masu tafiya jeran ya zeenatu Anty Amarya ce sai Haj.Nasara sai matan Ya Nasir da ya Jafar shamsiya da Fadila suka tafi kano suka kwana Daya daman already kayan dakin sun isa kaduna Washegari suka wuce suka ma Zeenatu jere a gidanta mai kyau da tsari,Anan gidan suka kwana Har da Jidda sai da Safe suka shigo Motar Haya zuwa Gumel ya Jidda ta hau ta kano..!
Tuni shiryen shiryen ya cigaba da Tafiya ta kowani bangare Amina ta fi kowa Murna ganin Ya zeenatu zata tafi ta bar musu daki daga ita sai Hamida in taga hanne na Damuwa Dakin Hajiya bakowa sai ita kadai Dariya Amina ke mata tana fadin"Ke fa banza ce..Bama kiji Dadi ba Daga ke sai Hajiya ki sha Shagalinki.!
Sai hanne tace"Kadaici zai dameni Amina..!
Sai Amina tace"Sai ki dawo gidanmu da zama ko Hamida..?
Sai Hamida ta gyada kai hanne baki take turawa tace"Uhmm kema waya sani ko daga nasu Bikin sai naki Amina..!
Aranar da Hanne ta fadi haka sai da suka kwana Amina bata mata mgana ba Tana Fushi da ita Sai da Hajiya ta shiga mganar tayi Sasanci Ta kalli Hanne tace"Ki bata Hakuri hanne..Ko ni ce mamah haka zam miki Fa..Ai sai naga kamar kin gaji dani ne kin kosa na tafi..!
Jin haka yasa Amina ta Sassauta Fushinta tace"Hajiya hakane fa..Kamar ta gaji dani..Ni ba inda Zani ina nan tare daku ko Hajiya..?
Ta fada idonta na tara maikon Ruwa Hajiya na Danne Dariyan tace"Da yardan Allah ma kuwa..!
Da sauri Amina tace"Yauwa Hajiya..Mun shirya..!
Tafada tana kallon Hanne har da bata Hannu suka kulla Hajiya na Dariya ita da Hamida harda ya Abida Dake falon acikin ranta tana auna yadda zama zai gudana Tsakanin sanyi da Miskilanci da Dattako da kuma Masifa da Jidali da Rashin kunya awaje daya Lalle akwai kallo kuwa..!
Su Amina wannan karon kansu yayi girma saboda su,su Abida suka sanya akan abunda za"asu raba wajen Walima su ka fara Bude Hanci suna Daga kai suma sun girma ba yara bane Tunda ana sakasu a sha"ani ba yan aiki aka maida su ba kamar baya..!
Tare dasu akayi Donot da Samosa da Dublan din da za"a raba agidan su ya Jafar suka hadu da su Anty Shamsiya,Sai kuma abincin da za"ayi aranar,waina kuma Gida za"ayita Mamanmu zasu yi da bakin gusai in sun iso Hajiya kuma ita tayi abun Rabo na Amare mug din shan Tea da Maficai da kofuna sai Jaka mai kyau Haj.Uwani tayi Key holder na Rabo Haj.Nasara kuma tayi robobi masu Murfi Dauke da yaji aciki Anty Amarya tayi Turaran wuta,Ta shiga Bikin sosai bata koma baya ba komai da ita ake yi har Amina na gulma Saboda Sakina take wannan Shigewar har sa"adatu wannan karon bata ware kanta ba Haka Anty Amarya tace mata Kada ta ware cikin yan"uwanta duk tsiya suna Tare bata mgana da Amina itama bata mata sai dai su yi mgana da Hamida ko Hannatu..!
Bangaran Kayan da amare zaku saka Baba mallan ya bama Hajiya Komai a hannunta an dinka musu kala uku uku Less Daya amtafofi Biyu masu kyau da Tsada sai Dogayen Riguna bakake guda biyu sai aka Dinka musu Hijabai Farare har kasa na walima sannan kuma ta Dinka ma su Amina Atamfa da Hijabi fari sai kuma su Matan Baba Maallam din suma Atamfa ce iri Daya harda Mamanmu na Fitan Biki kamar yadda aka saba Allah Sarki ba yaya da komai tare ake yi musu..!
Biki ya rage saura kwana uku Ranar agidan ya jafar suka wuni har Dare suna yin meatpie din da za"a saka a Takeway,a kasa suka tako zuwa gida Tunda duk ba mazan gidan ya Shamsu yana Dutse ya jafar kuma basu dawo ba Akilu ne da Zubairu kuma Baba mallam ya hana su Daukan Mota!
A kofar gidan Baba Mallam suka hangi ya jafar da ya Nasir da Aba awaje suna mgana sai wani mutum basu ganesa ba,Gabadayansu gidan Aba suka shige,Har da Sa"adatu su ya Zeenatu ne agaba su Amina na baya sai da suka shige gidan sannan Amina ta jawo Hannun Hanne suka koma baya zatayi mgana kenan ta Rufemata baki sai da suka Shige korido kana ta Saki bakinta cikin mamaki Hanne tace"Menene wai..?
Amina ta Tabe baki kafin tace"Ke baki ga sa"adatun nan bane..?
Sai wani shigemana take yi yanzu..?

Hanne tace"To ina ruwanmu..Daman mu bamu gujeta ba itace ta janye jiki Damu Tunda yanzu kuma ta Dawo shikenan..!
Hararanta Amina ke yi har ta gama mgana kafin tace"Sai gamu marasa zuciya sai mu biye mata..?Kune naga kuna mata Dariya ni ko kallo bata isheni ba wato taga yanzu mu ba yara bane muma mun girma Dole ta shigemana..Ni gaskiya ku sallameta in kuna son na rika Binku keda Hamida..!
Ta fada har tana yarfa Hannu,Hanne tace"Ko bakomai ai yar"uwarmu ce Amina..Naka ai sai naka..!
Amina tayi karamin Tsaki kafin tace"Yar"uwarki dai ni ban hada komai da ita ba .!
Hanne ta rike baki tace"Ehye..?in dai

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment