Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Villah mu Bude Hanci wai waya ga Amina Aminene a Villa Jar Uba akwai Daga kai..!
Yadda ta karkacen ne yasa Dole har ya Zeenatu sai da Dara tana Fadin"Ke ai Tun get din farko Sojojin Villa zasu Wurgoki waje..!
Amina tace"Tab kaji ya Zeenan nan..Mune fa kalan masu kudi kalan yan gayu..!
Take Fada tana wani Fari Zeenatu na Dariya tace"Aifa kalan masu kudi a bushe kirji gandas Amina kamar kin shafi kasan kabari Ko Hanne fa ta Fara Nanna banda ke suna chan makale a kirji kamar na maza..!
Amina ta Chuno baki itama abun na Damunta kafin tace"Wlh nima abun ya isheni kaf yan ajinmu baki ga nasu ba Tumbul tumbul..Ni don Allah ko Hamida zata san min nata ne..?
Kalli nata kamar Lemu sun yi Bulbul dasu..!
Salati Zeenatu ta saka Hamida kuwa har da cin Tuntube wajen Fita ya Zeenatu tabi bayanta tana Fadin"Mamanmu ki fito..kiji Abunda Diyarki ke fadi..!
Da gangan ta koresu suna fita ta Dauko Katin tana kallo acikin Haban Sikat din ta Boye shi ta fara maida kayan tana kwalama Hamida kira.

"Hamida.Haba mana Hamidas..Zan yi miki zaman Daki na sati Daya zan tayaki gyaran gado..Yaya Hamida..Anty Hamidassassas..!
Take fada Hamida na jinta tayi mata banza Daga Tsakar gidan tace"Bafa zan tayaki ba ki gyara da kanki..!
Kamar Amina tayi kuka tace"Shikenan Baza"a ma ace Antyn ba Hamidan ba..Hamidu din..!
Ba Hamida ba Hatta Yaya Dake Dakinta tana jinsu sai da ta Dara Mamanmu na cikin Bedroom dinta ko ta jisu ma bata fito ba Jawaad ne ke wasa ya kyakyalce da Dariya yana Fadin"Ita kuma Aminuu ba..!
Zeenatu da Hamida suka saki Dariyan Amina na ciki na jinsu taji sunan Daya ambata yasa ta Daga Murya tana Fadin"Jawaad ina wasa dakai ko..?
Wlh in na kamaka sai na yi kasa kasa Dakai..!
Tagumi tayi tana maimaita sunan Aninu acikin ranta Tsikar jikinta sai da ya tashi wani yanayi ta shiga da batasan Dalili ba.
Sai ta gama gyara kayanta Tsab har Hamida data shigo sai da tace"Yau wata rana Amina anyi abun kai..!
Tana Hararanta tace"Yau jumma"a munafus aga ban gyara ba..!
Dariya take mata Lokacin data fita alwalar mangariba ta shiga Dakin Mamanmu tana Tiolet din Cikin Dakinta yasa ta Dauki wayarta ta Sake a Sikat sai dakoma Daki tayi sallar mangariba Lokacin Yaya da Mamanmu da su Hamidi sun fito baranda kamar yadda suka saba suna Hira ta Lallaba ta shige Dakin mamanmu har cikin Makewayi ta kuma Sakama Kofar key.
Kan abun bahaya ta zauna ta fito da waya da katin Duk yadda Tsoro ya Cikata kalaman Aminu na yana jiranta Cike da yakini yasa ta kwashe Daya Cikin Lambobin ta Doka mai Kira.
Sai da ta shiga har taji an Dauka sannan wata zuciya tace"Amina me kika aikata..?
Da sauri ta kashe sai dai ta makara Tunda yace ta kirasa yaji ajikinsa zata kira din yana ganin bakuwar Lamba yasan itace.
Karar wayar yayi daidai da Daukewar Nunfashi Amina kafin gabanta ya koma ya Fadi Dam..!
Ta rude yasa batasan ta Danna Dauka ba sai da taji muryansa yana Fadin"Hello Amina..
Nasan kece..Daman ina da yakinin zaki kirani..!
Fitar muryansa kamar wani Sinadiri ne ajikin Amina hakanan taji kamar komai yana kwance mata wannan Tsoron kuma yana Fita Daga cikin kanta.
Bata sani ba wannan wayar itace mafarin Kaddaranta Itace mafarin FITA ZAKKAN da tayi acikin Yan"uwanta da Danginta..!


Yanzu muka shiga labarin da sauran mgana agaba..!




*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*




*🅿️18*

In wata Kaddara zata sameka Sanadin wani abu to baka da tsumi ballatana Dubara sannan Tsoro bashi da muhalli a wannan bangaran to kamar hakane ya faru da Amina inda ta san Sanadin Aminu zanen kaddaranta zai bayyana da tasani zatayi zatace Daman Tun farko komai bai faru ba.
Amina bata taba tsintar kanta ahalin data tsinci kanta ba Yarinya ce mai son yabamata a nuna mata so da Muhimmanci zuciyarta karamace ba bu kowa acikinta shiyasa cikin Sauki Aminu ya samu Dama mai yawa akan Amina.
Tun fara wayarsu ta farko abun bai Tsaya ba sai ya cigaba duk sanda Amina ta samu dama zata Dauke wayar mamanmu ta shige Tiolet dinta ko na Tsakar gida,flashing take mai yana gani kome yake yi zai ijiyeshi ya Kirata su sha Hira cikin abunda bai gaza sati Biyu ba, suka yi wani irin Shakuwa ta ban mamaki ko shakka babu Aminu ya samu Matsugunni azuciyan Amina tana sonshi tana kuma Tsausayamai saboda Maraya ne.
Komai take aboye take yinshi bata taba yarda a Fahimci Halin data ke ciki Daman chan bata da tsoro sai da soyayyar Aminu yasa AMina ta koyi Munafunci da nuku nuku ko bata fito Fili ta Fada ba,kowa yasan tana cikin Walwala da Farimciki ba wanda yayi Tunanin wani abu daman ita Amina akullum cikin Jidali take da Tsiwa sai Chanzawar bai wani damu kowa ba Hatta dasu Hanne da suke tare da juna koda yaushe.
Kafin lokaci yaja Amina ta gama sanin komai na Aminu duk halin Dayake ciki in sukayi waya sai ya Fadamata Amina ta zama kamar wata bangonsa yana Tunanin ranar Daya rasata baisan ina Rayuwa zata kaisa ba komai nata yana Burgesa komai tayi a wajensa mai kyau ne.
Abokan aikinsa ba wanda baisan sunanta abaki ba Musamman ma Oscar,da Nura koda yaushe suna waya sai yace"Minata kinga Oscar ko..?
Yau bai barni na Huta ba. !
Minata kinga Nura ko..?
Yana sani yawan mgana...!
Komai nsshi itace"Minata kinji me Nenne tace..?
Wai bazata yarda na Daukeki zuwa kano ba Tare zaku zauna ayola kin yarda..?Ira iran irin wadanan zantukan Amina ta gama Haddacesu acikin kanta indai akan Aminu ne.
Taki bari su kara haduwa wannan Tsoron bai saketa tana aikata abunda ko su ya Jadwa zamansu ba wacce tayi Tsaurin idonta sai dai ina Zuciyarta bazata iya bata ma Aminu ba Daya matsa ta amincemai yazo ya ganta Ranar Jumma"a da basu da Ismilya Daman sun yi mgana jiya da Daddare zasu hadu in da suka Hadu Na Karshe Alayin Gaban gidansu bayan La"asar.
Haka kuwa akayi Tana idar da Sallar La"asar tace ma Mamanmu zata shiga wajen hanne ba wanda ya tankata sanin basu da Shamaki da gidan Baba Mallam
Mazan duk suna masallaci suna Karatu ta sabe ta tafi koda taje har ya iso yana Jiranta,Ranar sun sha Hira Amina ta kara sanin Aminu sosai ta kuma gama yarda ma kanta itama In bashi bazata iya auran kowa ba Ko alokacin yayi yayi ta bari ya Turo a tambayan mai Izini Amina ta nuna ba yanzu ba tana tsoro ko Ss2 Bata kai ba ta Tura Saurayi gida ai su ya Jafar sai su kusa kasheta da ranta Tana Tunanin da Sauran Lokaci bata sani ba Daga ita har Aminun wannan Tunanin nasu shine ya bada kofar shigowar wannan kaddaransu kaddaran da zata Haramta musu juna har Abada kila da bai bi mganarta ba da Kaddaran tajasu zuwa gurbi ko matsayin da suke Fata
Abu kamar wasa karamar mgana ta zama Baba Soyayya mai karfi ce Tsakamin Amina da Aminu agida ba wanda ya sani duk bayan sati uku yake zuwa ya ganta ta fita da Niyar zuwa gidansu Hanne sai su hadu alayin gaban gidansu wani Lokacin Nikab take sakawa saboda kaucema Idon Mutane wani irin so Aminu yake mata so mai zafin da komai zai iya yi kan Amina Yaso ta bashi dama ya Hidintamata ammh kuma taki yarda bata yi Tsaurin idon da zata karbi wani abu Daga wajensa ba Ranar da Dubunta ta Cika sai ta Mutu ta Dawo Saboda duka tasani akwai wannan Ranar watarana zata zo sai dai bata san yaushe ne ba ammh Tabbas akwai Ranar kin Dillanci.
Zuwa Lokacin ba wanda Aminu bai sani ba agidansu Amina da gidan Baba Mallam ba,su ya Jafar kuwa har ya Haddace Labarinsu da su Sa"adatu da basa ga maciji Hanne da Hamida kuwa Koda yaushe suna waya rabi Duk Labarinsu ne Ya riga ya sani Hamida da Hanne sune gaban goshin Amina sannan kaunar Dake tsakaninta da Mamanmu kaunace da Allah ne kadai yasan Girmanta.
Nenne kuwa koda yaushe suna mgana da Amina in yazo ko kuma in yaje Yola Nenne tana ganin abun kamar wasa sai kuma karamar mgana ta zama Ita dai jikinta bai bata ba tana ganin wannan hanyar da Aminu ya Biyo anya mai bullewa ce kuwa..?
Tana Tsorom watan Watarana komai yazo ya Rikice tasha cemai"Aminu Anya bazaka Daina Biyema yarinyar nan ba..!?
Kafita Hankali fa kai babba ne kana ganin wannan Soyayyar taku ta Boye ba wanda ya sani agidansu watarana in aka sani bazata Haifar maka da matsala ba..!
In ta fadi haka Dariya kadai yake mata yace"Haba Nenne..Bafa komai mai Wahalar Meena ce..In tana sona ko Duniya zata hade bamai rabani da ita so kada ki damu babu abunda zai faru..!
Kallonsa take yi bata cewa komai ba ganin idonsa ya Rufe ammh ajikinta Tana jin kamar zuwa gaba wannan zai zame ma Aminu kabule babba ma kuwa da bazai iya yin komai alokacin ba..!

Babu wanda ya taba Lura da Halin da Amina ke ciki sai dai an fara Lura da ta na yawan Shiga bandaki ta Dade bata fito ba,Ranar Bandakin waje ta shiga tafi minti Talatin bata fito ba Da Daddare ne duk suna Tsakar gida abaranda suna shan Iska Aba ya Dawo yana Shashensa Yaya tatafi wajensa Mamanmu ce da ya Zeenatu da Hamida sai jawad Dayayi barci kan katuwar Tabarman da suka baza anan Baranda abincin Dare suka gama ci su ka koma Hirar Anty sakina da Tayi barin yan Biyu,Achan madina din ance ta Zubar da jini sosai sai tafi sati a asibiti achan Anty Amarya taso taje Baba Mallam ya hana yace akwai mahaifityar Sarood da ita kanta Sarood din suna kula da Sakinar sai dai ance Danmallam din zai zo akwai mganin Hausan da zai tafin ma Sakinar dashi.
Duk Amina na cikin Bayin Tsakar gida tana jinsu suna waya da Aminu ya katse yace ta jirashi ya amsa wani kiran bata so ta fita kuma ya Sake kira ta shiga uku duk da wayar asilent take sakata kuma da sun gama waya take Goge Lambar tasa data Riga ta Haddaceta akanta.
Tana nan Tsaye tsabar sakama rai bata Damu da inda take wajen Najasa bane,Hankalinta kwance take shigowa suyi wayarsu domin nan din ne kadai mafita inda Hankalin wani bazai zo kanta da wuri ba.
Karaf taji Hamida na Fadin"Wai ina Amina ne..?
Mamanmu tace"Ba ta na cikin Dakin ku ba..!
Ya zeenatu na kishingide tace"Ina jin fa bata fito ba..Naga Daukan butatanta da shiganta Bayi indai ba yanzu ta fito ba to tana ciki..!
Hamida tace"Kai meke damun Amina ne..?
Kwanakin nan bata da aiki sai shiga bayi..Kuma sai ta Dauki Lokaci kafin take fitowa ko Basir ne ya kamata..!?
Mamanmu tayi shuru kafin tace"Nima na Lura mgana ce kadai ban yi ba..!
Ya Zeenatu tace"Ko basir din ne mamanmu..?
Kinsan fa tana saka yawan kashi..!
Mamanmu tace"Bari ta fito muji dai..Ammh yawan shiga bayin Amina bana Lafiya bane..!
Duk Amina na jinsu sai jikinta ya Saki Yanzu wani amsa zata basu..!
Bata gama Tunani ba Aminu ya sake kira sai ta manta da su mamanmu ta Dauka suka cigaba da Hirarsu.
Bata da Tsammani taji Muryan Hamida gabda kofar Bayin tana Fadin"Amina..Amina..!
Mamanmu shuru fa bata amsa ba..!
Jin haka yasa Mamanmu ta mike tana gyara Daurin zaninta Lokaci Daya tana Fadin"Zeenatu ba Lafiya..Gayama Aba dinku da yaya na shiga uku ni Balaraba..!
Take fada Cikin Rudewa Tunaninta Allah yasa ba masai Amina ta Fada ba basu sani ba
Zeenatun ta Rude itama ta kwashi Sauri zuwa Shashen Aba ta Fadamai jin haka yasa Amina tayi Saurin katse wayar jikinta ya fara rawa saboda Sauri yasa sai taa danne wayar ta kasheta Gabadaya ta Turata Cikin Wandonta Hamida na shirin Turo kofar Makewayin Amina tayi Zaraf ta fito har tana Bangaje Amina.
Sai Hamida ta saki baki tana kallon Amina datayi wani Fiki Fiki da ido.
Daidai Lokacin da Mamanmu ta Kariso tana Fadin"Jijjiga Kofar makewayin Hamida a bude take..Ami..!
Bata karisa ba ta ci karo da Amina Tsaye Cikin Sauke Numfashi tace"Alhamdulillahi..Wlh gabana ya Sare na zata kin fada masai ne..!
Da sauri Amina tace"Masai kuma mamanmu..!?
Tace"Yo eh mana..Wajen awanki Daya fa da shigarki bayi baki fito ba..ni har na saka Zeenatu ta Kira babanku da Yaya..!
Amina bata samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Aba yana Fadin"Balaraba meke faruwa ne..?
Sukaji Muryansa sai Amina ta Rude da Sauri ta matsa jikin Mamanmu tana Wurga ido.
Hannunta ta jawo zuwa Tsakar gida Hamida ta biyo bayansu Lokacin da Yaya ke fadin"Me ya samu Aminan..?
Zeenatu tace ta shiga makewayi tun dazu bata fito ba..!
Badai wanda ta shiga tun kafin Aba dinsu ya shigo bane ko..?
Hamida tace"Shine..Yaya mu mun zata ko ta suma ne ma abayin..!
Aba ya kalli Amina na Tsawon Lokaci yana Nazarinta yadda take Fiki Fiki da idonta ajikinsa yaji bai yarda da ita ba.
Cikin kaushinsa ya Kira sunanta "Amina..!
Sai da gabanta ya fadi da Sauri ta amsa"Na"am Aba..!
Kai Tsaye yace"Me kike yi a bandaki har na tsawon wani Lokaci..?
Kan Amina na kasa tana kokuwa da Fargabanta tace"Bakomai Aba..
Ya zeenatu tace"In baki da lafiya ne ki Fada a nema miki mgani..Wlh Aba kusan koda yaushe Amina cikin shiga Bayi take kuma sai fa an manta da ita take fitowa..!
Kallonta kawai yake yi yana kara nazarinta Hamida tace"Ni fa na Fara Tunanin ko Aljanu sun shafe ta ne..!
Har fa bayin Dakin Mamanmu tana shiga ni Ranar ma da ta shiga na shigo sai na rika jin mganarta kasa kasa har da Dariya fa..Aba..?
Kiris ya Rage Amina ta bata Dafe Kirji ba ta shiga uku Yaushe Hamida ta ji haka bata mata mgana ba..
Mamanmu ce tace"Mun shige su..Kuma shine baki Fadamin ba..?
Hamida tace"na manta ne mamanmu..Ammh Tabbas Amina bata da Lafiya..!
Kamar an Dasa Yaya da Aba haka suke bin Amina da kallo Mamanmu tana Salallami tana Fadin"Allah ya kaimu gobe zan shiga wajen Malam da kaina na Fada mishi Babansu kada fa ayi Shuru karamar mgana sai kaga ta zama Babba..!
Ya zeenatu tace"Mamanmu gama Turaran Hayakin nan da Baba mallam ya bada kika taba Turarama ya Zulaihat da suka taba Bigeta a makaranta..?
Yana cikin Dirowarki ki Turara mata yanzu agani in ma sune zasu bayyana..!
Mamanmu tace"Yanzu kuwa Zeenatu..!
Aba ne yayi gyaran Murya kafin yace"Ba fa wani Aljanun Dake Damunta..Ki tambayeta ko wani Cutar ne dabam..!
Jin haka yasa da Sauri Amina tace"Aba basir ne..Zafi nake ji in naje yin bayan gida sai yaki fita..!
Yadda ta fadi mganar yasa Dole ma ayarda Yaya ce tace"Ararrabi zaki sha yana mganin basir sosai..!
Aba ya juya yana fadin"Ku jika ku bata ta sha in bai yi ba zan ma Nasiru mgana sai ya kaita taga Likita nan General..!
Daga haka ya shige Falonsa,yaya kuma ta koma Daki ta Dauko Daddaken Ararrabinta da bata Rabo dashi ta Jikama Amina aruwa kadan ta bama Mamanmu hade da Sauran na Ledan tana Fadin"Tasha wannan yanzu..Gobe da safe ko atea ko koko sai ta kara sha insha Allah cikin zai saketa tayi bayan gidanta Lafiya lau..!
Mamanmu ta karba tana Godiya ita ta tasa Amina sai d ta Shanye duka tas tana yamutsan baki Saboda Bauri bata Damu ba Hankalinta ya kwanta Tunda ta isa barka asirinta bai Toni ba.
Tundaga Ranar Amina ta Rage shiga Makewayi tana waya Aminun, sai da aka kwana Biyu ta nemesa ta Fadamai Halin daake cikin Cikin Damuwa yace"Meena ki bar ni nazo naga Aba ko mallam..nagaji da wannan kumbikunbiyan..Da gaske nake yi ina sonki kuma auranki zan yi..!
Amina sai ta marairaice tana Fadin"Ba yanzu ba Amin..Aba ko mallam baazasu taba Sauraranka ba
Ko fa Ss2 ban shiga ba kuma aka"idan gidanmu sai kin kusa gama Candy ake Fara mganar auranki yanzu kana gani ko su ya Zeena bamu ji komai ba Har yanzu kuma basa su wuce shekarar nan mai zuwa ba ka Kara Hakuri akwai sauran Lokaci..sannan Zamu Rage waya na kwana Biyu..Gudun Faruwan wani abu wanda bazai mana Dadi ba..
Zan nemeka in na samu Dama..!
Bazai iya mata gaddama ba Saboda yana sonta kuma baya so ya sakata acikin matsala.
Atsukin Taji ance ya Danmallan yazo abakin Hanne sai dai kwana Biyu yayi ya koma Allah kuma yasa basu hadu ba,Don ko gidansu bai shigo ba,Tadai ji su Yaya nata jajanta Lamarin suna Fadin yace Sakina tasha Wahala sosai yaso ma ya taho da ita Mallam ne ya Hana shiyasa
Anyi haka da kwana Hudu Labari yazo kan ya Zulaihat itama ta zame a bandaki Ta fadi itama tayi barin Cikinta,Tana asibiti washegari kuma Yaya da Hajiya Babba da Hajiya Uwa Mallam yasa Idi yakaisu kano inda mijinta ke aiki nan suka koma sukaje suka Dubata ya Zulaihat taso ta dawo gida sai ta samu Lafiya Baba mallan yace maza Tunda uwar mijinta na nan da kanwarsa sun isa su kula da ita tana ji tana gani su Hajiya suka Dawo Gumel suka barta.
Sauran yan'uwa kuma sai a waya suka mata sannu da jiki har da su Amina da suka gama nacin abarsu suje Mallam yace ba wanda zai taka bama su ba,har su ya Abida Dake gaba dasu jin haka yasa kowacce ta maida maitanta.
Amina sun cigaba da mgana da Aminu sai dai tana shiga Bandakin waje koda yaushe,Domin haka Mamanmh ta Dinga Dura mata mganin Basir Asibiti kuwa sai da Aba ya Tambayeta ta warke ko kuwa sai sun je asibitin tace ta warke shiyasa sai ta sauya Taku.
Sai dare yayi in suna Tsarkar gida da an fara Hira sai ta fara hammar karya tace barci take ji ta shige Dakin Mamanmu chan kurya ta Kirasa da kuma taji motsi ta kashe wayar ta Boye ta Lafe kamar mai barci ba wanda ya Taba Fahimtar wani abu na Faruwa.
Idon Amina ya Bude tasan menene Dadin Soyayya,Domin karance karancen datakeyi sun kara taimaka mata sosai,Bayan su Hamida ba wanda yasan Amina na karatun Littafan Hausa su kuma Aminansu ne bazasu taba fada ba,Sai dai koda yaushe suna mata Fadan ta Daina Abunda take yi ita kuma sai tace ina Ruwansu..!
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah gashi har su Amina suna shirun Fara Jarabawar third Semester dinsu ns shiga SS2,alokacin kuma sun kwarari wajen wata bakwai tare da Aminu aboye batare da kowa ya sani ba.
Sai dai akwai ranar da asirinta ya kusa Tonuwa Aminu yazo tayi karyan Tana gidan su Hanne Fitanta kuma ba Dadewa sai ga Hanne tazo nemanta Hamida tace ai yanzu Aminar ta fita zuwa wajenta.
Hanne ta kalli Hamida cikin mamaki kafin tace"To bata je ba don ban ganta ba..!
Cikin mamaki Hamida tace"Wasa kike ko..?
Kusan fa duk jumma"a Aminar wajenki take kai har mangariba fa Hanne..!
Hanne ta zaro ido kafin tace"Ni..?
Yaushe rabon da naga Amina. ?ranar ne fa shima ana kiran sallar mangariba ta shigo sallah kadai tayi na Rakota gida..!
Hamida ta koma ta zauna tana waige waige kafin tace"To wlh Amina na fita kuma tace wajen ki take zuwa
Yanzu ma fa bata Dade da fita ba..!
Hanne tace"To abun mamaki ina Amina take zuwa..?
Hamida tace"Wlh bansani ba mu jira ta Dawo mu tambayeta..!
Wasa wasa Amina har bayan mangariba bata Dawo ba Hanne da Hamida sun fara shiga Damuwa har gida Hanne ta koma ta tambayi ya Abida ko Amina ta shigo tace bata ganta ba.
Ta sake dawowa ta Fadama Hamida,suka Rude suna wannan Tarardadin sai ga su ya Jafar sun shigo Sai suka kara Tsurewa kada su Farga ba Amina inda Allah ya Taimakesu har suka fita basu Lura ba Aminan ba,Suna Fita ba Dadewa sai ga Amina suna Daga cikin Daki sukaji ya Zeenatu na mata mgana tace Daga gidansu Hanne take
Ya zeenatu ta harareta kafin tace"Hannen ai kina fita ta shigo..?
Ko wata hannen dai ba wannan taki ba..?
Amina sai ta fara Kifta ido kafin tace"Dakin su ta barni na kwanta bansan yammh tayi ba sai yanzu..!
Ko kara kallonta batayi ba Jikinta asanyaye ta karisa Dakinsu kaifafun idanuwan Hanne da Hamida na kanta Hannunta take Boyewa Cikim Hijabinta kada su ga Zoben azurfan da Aminu ya bata yau batasan me zata ce musu ba.
Ganin yadda suka Zuba mata ido ne yasa tace"Wai lafiya..?
Wannan kallon kamar naci bashin ku..!
Tafada Cikin Hararansu Adole sai ta barsa da mganar dake ransu.
Hanne ce ta mike tana Fadin"Amina ina kika je..?
Amina tace"Ina kuwa..?
Ina zuwa akace kinzo gidanmu naga bazan iya dawowa ba na shiga Dakin ku na kwanta..!
Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka koma suna kallon Amina datake wani Kifta ido alamun ba gaskiya.
Hamida tace"Yanzu Hanne ta koma gida..Ya Abida tace baki zo ba..!
Amina ta saki karamin Tsaki Lokaci Daya tana Cire Hijabin jikinta take fadin"Bata ganni ba ko Hajiya batasan na shigo ba..!
Ruwanku ku yarda ko kar ku yarda..Ku Tsayama Zargina kukeyi na tafi yawon banza ko me..?
Hanne tace"Bata kawo nan ba..Muna gujemiki matsala ne..
Kinsan Fita zuwa waje ba Tarbiyanmu bane Amina kada ki Fara Halin da kike Dade baki yi ba..!
Amina ta Zabga ma Hanne Tana Fadin"Bangane ba..?
Kinga Hanne don Allah ki kyaleni bama son Hayaniya..!
Daga haka tayi saurin Fita Daga Dakin kafin su ganota Dakin Mamanmu ta Fada tana Kiranta.
"mamanmu Mamanmu..Na dawo..!
Tana fita Hanne ta kalli Hamida kafin tayi mgana Hamida ta Rigata da Fadon"Karya take yi wlh..Acikin idanuwamta naga Karya Hanne..!
Hanne tace"Nima nasan haka
To ina taje batasan Fadamana..!
Hamida tace"Wayasanin mata..?
Kila gidansu wannan Zainab isan taje aro Littafin Hausa kinsan Amina..!
Hanne tace"Ai ba Littafi a hannunta..!
Hamida tace"Zai iya yuyuwa bata samun bane..Ina zata Daya wuce nan..?
Hanne tace"Hakane..!
Daga haka suka bar mganar ammh kamar acikin sun kasa yarda da cewa Amina gidansu Zainab taje sun santa in ma chan taje zata gayamusu ammh abun mamaki yau Amina bata son Hada ido dasu suna Zargin akwai wani Sabon Al"amari game da Amina sai kuma basu san komenene ba..!
Tunda Amina taga sun Fahimceta sai tace Aminu ya Dakata da zuwa gidan su Hannen Data ke Fakewa dashi an ganota yasa sai ya kwana Biyu bai zo ba sai su yi mgana ta waya.
Watarana Ranar da ta zama mafarin bakaken Ranaku acikin Rayuwar Amina da bazata taba mantawa dasu ba.
Ranar da suka gama Jarabawarsu ta Karshe wajen kwana Uku basu yi mgana da Juna ba tasan yana chan Hankalinsa atashe jinta shuru ita kuma bata samu damar Daukar wayar ba akwanakin Mamanmu na Makale da wayarta bata samun Daman Dauka duk hanyar da zata bi tabi bata samu Dama ba.
Sai Ranar da Daddare Allah ya taimaketa Mamanmu ta ijiye wayar saman Mirror dinta Tana Dakin Aba tana gyaramai yau ita ke dashi.
Bata Kira ba sai da taji Dawowar Aba da kuma Kai da kawon Mamanmu ashashen nasa sai da taji tsit alamun Tagama Zirga zirgan sannan ta shige Kuryan Dakin Mamanmu ta Kirasa yana ganin kiran ya biyo baya Tana Dauka ya Sauke Numfashi yana Fadin"Da baki kirani ba yau Meenata..gobe sai dai ki ganni agidanku..!
Tasan zai aika shiyasa ta fara bashi Hakuri suna cikin mgana taji kamar Muryan Ya Zeenatu tana mgana da Sauri ta katse wayar,ta koma ta Lafe kamar mai barci sai dai abun da ya bata Haushi Falon Mamanmu Ya Zeenatun suka Dawo ita da Hamida suna Hira maimakon da da suke Falon Yaya ashe kanta ke ciwo ta kwanta Shiyasa suka barta ta Huta.
Sanin in bata Lallashi Aminu ba zai ballo mata ruwa yasa tatashi ta Fito Falo tana mika kamar mai barci.
Cikin Muryan barci tace"kun dameni ina barci Hamida..!
Ya Zeenatu tace"Sai ki sauya Daki malama..!
Bata ma Tsaya ba ta Tura baki tana Fadin"Na koma Dakinmu ni da Dakin uwata an koreni..!
Tana jin Hamida na mgana bata tankata ba ta koma Dakinsu sam Tunanin ta Rufe kofa bai kawo mata ba ta Haye kan gado ta kira Aminu daman yana Jira ya Kirata suka cigaba da mgana Korafi yake mata kan ya gaji zai zo yaga Aba ko mallan ita kuma tana kokarin numamai Lokacin bai yi ba.
Sam ta manta a inda take hankalinta ya Riga yayi gaba bata ji shigowar Kowa ba bataji motsin ba ko Tafiya kawai sai jin wata Gigitaciyar tsawar Muryan Aba ta karade Kunnuwanta Cikin kaushinsa yace"Amina..Amina Dawa kike mgana awaya..?
Ba Amina kadai Hanjin Cikinta suka yamutse ba har da Aminu Dake Sauranta ya Rude domin Baya son Amina ta shiga matsala..yana ji ya kara Daka mata Tsawar yana Kara Fadin"Nace da Uban wa kike waya da Tsakar Daran nan Amina..?
Tsawar da har Yaya sai da tadata ita Daga barci Mamanmu Zani a hannu Ita dasu Hamida suna Rigen rigen shigowa Dakin.
Bayan ya shigo gida ne ya manta bai kulle gida ba yasa ya kara Fita ya kan yi Dube Dubensa atsakar gida kafin ya kwanta in sun manta da wani abu ya Kaudashi yana jin Hiransu Hamida bai leka Falon Mamanmu ba sai dai har ya

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment