Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mallam baza"a kara ba..!
Yaji Dadin haka nan da nan ya saki Fuskarsa yana fadin"Ko kai fa..?Allah yayi muku albarka..!
Ya amsa da Ameen ya mike yana kallon Amina Data fakaici idon mallam ta Zabgamai gwalo Rai ya bata yana Kada mata ido ita kuma tana wani Juyamai ido.
Sai da ya shige Dakinsu sannan Mallam ya kalli Amina yana Fadin"Ina Sa"idu..?
Yana gida ko ya fita ne..Au ga motarsa ma ashe yana gida kenan..!
Amina tace"Eh yana gida mallam
Mallam yace"Yauwa in kin je gida kice mai ina son ganinsa saboda da wuri zan fita!
Amina tace"Mallam tafiya zakayi..?
Mallam yace"Zaria zani Cikin makarantar ABU akwai wani Taro da aka gayyaceni a Depatment din Islamis Studies shine Uzairu zai kaini yau nakeson mu dawo bana so muyi Dare..!
Cikin Sanyinta tace"Allah ya Kiyaye hanya..!
Ya amsa da Ameen uwata Daganan tamai sallama ta wuce ya bita da kallon Tsausayi har yau bai daina jin yanayin kamar bai kyauta ma Amina ba,Hajiya tataso da wannan mganar kuma bazai iya musa mata Ba bataba ja da mganarsa ba yasanta sarai tana da Dalili ammh Tunda bata Fadamai ba bazai matsamata sai yaji ba Jiya yayi istikara akan al"amarin kuma yaga Hasken Amina Tatare agidan Umaru zasu rakasu da addu"an zama Lafiya da Zuru"a Dayyaba..!
Amina Jikinta a sanyaye ta shiga gida ba Kowa a tsakar gidan Har Falon Aba a kulle alamun bai fito ba Sai ta wuce Dakin Mamanmu.
Bata afalo sai ta kutsa kai Uwar Dakinta Kamar yadda ta saba kai Tsaye hankalinta baya tare da ita Shiyasa har bata jin shigowar Amina ba,kalma Daya Amina ta jita Cikin kunnenta.

"Kada ki damu bani nace ba..Ki kwantar da Hankali......!

"Mamanmu..!

Gabanta ya fadi dam jin muryan Amina abayanta Jikinta sai ya fara rawa ckin rawan jiki ta juyo tana kallon Amina Dake kallonta Cikin mamakin ganin yadda take rawan Jiki ga Zufa na keto mata ta saman goshinta.
Cikin Fargaba da wani irin Tsoro tace"A..A..mina yaushe kika shigo..?
Amina tace"Yanzu na shigo mamanmu..!
Tana jin sadda ta Sauke ajiyar zuciya Da sai da ta kalleta,Cikin mamakin ganin yadda tayi Firgai Firgai kamar wacce tayi karya agaban Sarki.
Hannun Amina ta riko Daya jike da Zufa ta zaunar da ita gefen gado tana Fadin"Kin gayama Hajiyar abunda nace..?
Amina ta samu kanta da kasa Fadama mamanmu komai da Farko ta shigo da Niyyar Fadamata har wayar dataji Anty Amarya nayi ammh yanzu sai ta kasa Haka kurum kamar an Rufe mata baki an sauya mata mgana taji ta tana fadin"Eh na fada mata..!
Tana ganin sadda ta washe baki tana Fadin"Yauwa to me tace..?
Amina gabanta ne ya fadi bata so zargi ya shiga ranta Kodai kodai mamanmu ce suke mgama da Anty Amarya Da sauri tace A"a mamanmu ba muguwa bace ba mamanmu bace ba ita bace watace ta Dabam ita Tana yin komai Saboda Farincikina ne.
Da sauri ta Kauda wannan Tunanin da Fadin"Tace na koma gida gatanan zuwa..!
Mamanmu tayi shuru tana Tunanin anya Hajiya zata janye mganar ta kuwa..?
Duk da Mallam da Safen nan Amarya tace ya Tarasu ya fada musu Tariyar Amina ayau dinnan
Ganin kallon da Amina ke mata yasa Ta fashe da kukan makirci tana Fadin"Amina duk abunda kikaga inayi Saboda ke ne .Ina so na ga Rayuwarki ta Inganta kamar ta kowa Amina..Danmallam bai dace dake ba..Matansa Biyu Amina ina zaki iya Kishi da mata Biyu mace ma irin Sakina..Uwarta Kinsani na sani bata Kaunarmu Amina zasu yi komai Saboda su ga bayanki ni kuma na Shirya Saboda ingata Rayuwarki Sai inda Karfina ya kare,na gwammace na rasa komai Ciki kuwa har da Rabuwa da Aba dinku Saboda ke Amina..!
Ran Amina ya cika da Tsausayin Mamanmu aranta take jin mamanmu bazata taba Cutar da su ba,da sauri ta Rike Mamanmu tana fadin"A"a mamanmu kada kice haka fa..Insha Allahu saki bazai kara shiga Tsakaninki da Aba ba..Ki daina Fadar haka don Allah bana jin Dadi..!
Mamanmu tana Jan hanci tace"Tun jiya muke tsiya dashi Nidai nace ban yarda ki tare ba sai kin gama makaranta kamar kowacce ya haba..Ai wannan rashin adalci ne shima Maallam din bai Duba ba Gaskiya..Ni bazan yarda ba na Fadamai sai dai koma miye ya faru din..!
Amina tayi saurin cewa"A"a Mallam bazai taba kaini inda za"a cutar dani ba..Shi da Hajiya suma bangarena Jikina ne Mamanmu kamar yadda kike sona haka suke kaunata don Allah na Rokeki kada ki saka baki ran Aba ya baci don Allah..!
Mamanmu na kara matsan kwallah tace"Ni daman ban ce basa kaunarki ba..Bama ke ba Duka Ya"yanmu damu kanmu suna kaunarmu nace ne su Dubaki don Allah kin yi kankanta da Daukan wannan auran..!
Nidai in kina so nayi shuru kada nayi mgana koda Hajiya tazo Aba dinku ya kiraki ko yayi mgana ki Taimakeni ki Fadamai Bakisan wannan Tarewar da auran gabadaya in kuma kika kasa Fada ni zan Tubure nace ban yarda ba Duk da yace in nayi mgana zai yanke igiyar auranmu ban damu ba Zan iya yin komai Saboda ke Amina..!
Amina Sai kuka itama jin kalaman mamanmu Cikin kuka tace"Naji zan fada..Don Allah mamanmu kada kiyi mgana Ran Aba ya baci..na rasa yaya alokacin da bansan Dadinta awajena ba..Kema kuma bana so na rasaki..In kika tafi kikabar gidam nan ina zamu..?Wazai Rikemu..!?
Ni da Hamida zamu lalace mamanmu..!
Da Sauri ta Rumgume Amina Tana Mirmishin nasara kafin cikim karyewan murya take fadin"Bana so a Gurgunta miki Rayuwa ne Amina..!
Haka take fada tana jan majina karshenta dai Amina ce ta share hawayenta tana Cigaba da bama Mamanmu baki har tayi shuru kafin ta kalleta tana Fadin"Tashi kije Dakin ku..Abun karyawanku na Kitchen bari naje Nagani ko Jawad yagama Shirin Tafiya makaranta..!
Daga haka ta mike ta fice tana Dariyan Nasara duk karya ta Fadama Amina tun DAran jiya datayi mganar da Aba bata kara cemai komai ba Shima bai ce mata ba ita shegiya ce da zata bata goma ko Daya bata gyaru ba Saboda Amina ta Samu Sakin Farko ta Tabbata Sa"idu zai iya Sakinta Saboda mallam da Hajiya duk da ta samo kansa din ammh gwara ta Kiyaye in har Makircinta bai yi ba zatace ma Madina ta Kira malaminsu arufe bakin Hajiya da mallam din kan mganar Tarewar kowa ya Huta..!
Amina ma Dakinsu ta koma ta Iske Hamida da Hanne kozai kozAi ba Fara"a kallonsu tayi kafin tace"Miye haka kowacce ido kamar Nama..kunyi wani Figai figai kamar Kajin da aka Tsoma acikin Ruwan zafi..!?

Yake Kadai Hanne tayi mata batayi mgana ba Amina ta Cire Hijabin Jikinta tana Fadin"Mamanmu tace abun karyawan mu na Kitchen Hamida tashi ki Dauko mana..!
Hanne ta Dago daga kwancen Datake tana kallon Amina cikin mamakin kamar ba itace ta kwana kuka ba.
Cikin Dashewar murya tace"An fasa kai ki gidan ya danmallam din ne..?
Amina tace"A"a me kika gani..?
Hanne tace"Naga kin saki jikin ki ne..!
Amina tayi wani Mirmishi, Mirmisshin da ya bama su Hamida mamaki Kafin tace"Ya zan yi Hanne..?
In ba saki Jikina ba za"a fasa ne..?
Daga auran har Komai da komai da suka Faru bani na Tsarama kaina ba Allah ne..bakomai shima wannan din kaddartace..Abu Daya ne zai dameni zan Rabu daku..Bazan iya Rayuwa baku ba zamu daina zuwa makaranta tare zamu daina kwana tare zamu daina Fada zamu daina cin abinci tare zamu daina zuwa Hadda Tare zan koma ni kadai..Wlh in na Tuna haka sai naji kamar zan yi hauka..!
Kawai sai ta saka musu kuka bata so ta Fadamusu abunda taji haka kurum Taji bazata iya fadama kowa ba,suma kansu Abunda ke sakasu kuka kenan suka mike dukkansu suka Rumgumota suna ta kuka suma kukan kewarta suke Amina Bangaran jikinsu ne in Tayi nisa da su zasu shiga uku ne.
Suna wannan kukan sukaji Sallamar Hajiya shiyasa suka Tagaita Falon Aba mamanmu ta shigar da ita sun Dade suna mgana kafin su fito Aba fita yayi yayinda Hajiya ta kalli Mamanmu tana Fadin"Balaraba ina yaran nan suke ne..?
Daman Tun da tazo tana Dakinta Hankalinta yaki kwanciya balle dataga sun dade suna mgana da Aba su ka kuma gama ya fita bai ce mata komai ita fatan ta yasa Hajiya tana Rusa mganar tariyan ne
Shiyasa cikin Damuwa tace"Suna ciki Hajiya..Karki so ki ga yadda suka Tada Hankalinsu hamida da hanne..!
Hajiya tayi Dariyansu na manya ta wuce tana Fadin"Sakarci ne..ai ba Mutuwa zatayi ba..banda abunsu ai suna Tare da ita koda yaushe tunda tana kusa..!
Mamanmu ta Daskare tana Bin bayan Hajiya da kallo me take nufi..,?
Kasa shi ga Dakin tayi sai da taji Hajiya na kiranta sannan ta shiga Dakin taga Amina zaune gaban Hajiya Hamida da Hanne na gefe suna Sharan kwallah.
Cikin Dariya tace"Tayani Lallashin ya"yan nan naki balaraba sun tasani suna min kuka..!
Mamanmu tace"Nima Hajiya da zan samu mai lallashina ina so..Kukan ma ai na yi shi Hajiya..!
Hajiya tace"Balaraba hakuri zaku yi nasan zaku ji mganar Daga sama ko..?to me zamu jira..?,an gama mai Wahalar zaman me zatayi...
Zaman bai da Fa"ida Tunda yana da Gida anan sai ta tare abunta sai Hankalin mu yafi kwanciya..!
Mamanmu ta ji kamar Kafafunta sun kasa Daukanta Dakyar tace"Hajiya Karatun Amina fa..?
Hajiya tace"zata cigaba da zuwa Duka makarantrta..Zata dai zana Jarabwar Fita a wannan shekaran tare dasu Akilu Saboda yadda muke so in Danmallam ya koma ba Dadewa zai zo ya tafi da ita..!
Mamanmu ta zaro ido tana fadin"Madina Hajiya..?
mirmishi tayi kafin tace"Insha Allahu..!
Ai sai mamanmu ta koma ta zauna akasa Dabas tana fadin"Allah Sarki Amina..!
Sai ta fara jan Hanci Hajiya na Dariya ta Mike tana Fadin"Haba balaraba da girmanki keda yara zasu yi kiyi musi Fada..? Bafa komai tana kusa kafin su tafi..Hsmida da hanne kuyi hakuri kubar kuka In Mijinta ya koma zaku rika zuwa ku tayata zama makaranta kuma Dagachan zasu rika zuwa kuma Tare baku Rabun baa Tukunnah..!
Hanne ta washe baki kafin tace"Da Gaske Kike Hajiya..!?
Kai ta gyada mata tana Fadin"Har da mallam ma munyi mganar.. bai dai ce komai bane..
dukkansu sai Dariya Hajiya ta kalli Amina tana Fadin"Mamah kin amince zaki Tare agidan Mijinki ko.?
Amina kanta na kasa ta Daga kanta mamanmu har tana Murnan Amina zata ce bataso sai tasha mamakinta Hajiya taji Dadi ta Dafa kanta tana Saka mata albarka kafin tace ma su hanne"Ku taimaka ku hadama Amina kayanta Waje daya tun daga Littafan makarantar ta da komai har kayan sawanta nan da Sati daya mallam zai mata Sabbin dinkuna.
Ta Tsefe kanta Ku rakatanan nan gidan Magajiya ayi mata Kitso mai kyau da kunshi duka suna yi agidan kun ji ko..!
Da toh suka amsa mata Kafin ta kalli mamanmu Dake Zufa tace"Balaraba zan wuce..Sai zuwa anjuma inaga Sai Dare zaku kaita..!
Mamanmu ta Mike dakyar tana Fadin"To Hajiya Allah yasa hakan yafi zama Alheri bari ni na Tsefe ma ta kanta na wanke mata su hanne sai su hada kayan..!
Hajiya tayi Dariya kafin tace"Ameen ai Amina Diyarkice Balaraba nasan zaki mata komai..!
Daga haka ta fice mamanmu ta Rakata bata Dawo Cikin gidan ba Daga Haraban ta Tsaya bayan Tafiyar Hajiya ta Danna ma Madina kira.
Kamar tana jiranta ta Daga kiran tana Fadin""Ya ya an dace..?
Mamanmu tace"Ba Nasara madina..!
Dagachan bangaran Anty Amarya ta Laila ashar kafin tace"Basu isa ba..Karyansu..!
Mamanmu tace"ki kira mallam..Shawara ta a Danne bakinsu ammh in ba Haka ba kwabar mu na Shirin yin ruwa..Yanzu Hajiya ta bar gidan nan..!
Nan ta shiga bata Labarin duk abunda ya Faru.
Anty Amarya tace"Wannan Shegiyar yarinya makira ce Dayyaba..Zata zame mana ciwon ido..!
Mamanmu tace"Uhm..Nima ina ta mamakinta sai mun gama mgana ta yarda sai daga baya ta sauya..!
Amarya tace"Tsaya Tsaya..Baki Fahimci wani abu ba..Kodai ta ganoki ne..?
Mamanmu tace"Kai a"a gaskiya bana jin haka..Sai dai tsoron Aba dinsu da kuma kunyar su Hajiya..!
Anty Amarya tace"bari na Kira mallam..!
Daga haka ta katse kiran Tana kokarin kiran mallam din ne Sakina ta Shigo Cikin Bedroom din nata a yarkace agyale a Hannu Cikin Numfashi take Fadin"Anty kin ji abunda naji..Wai yarinyar nan zata tare yau.Yanzu Umar ke fadamin Anty har yana cemin zata zauna adakinsa kinji fa..!

Tafada cikin wani yanayi Anty Amarya sai ta fasa abunda tayi niyya ta maida wayarta saman madubi ta kama Sakina ta Zaunar gefen gadonta tana fadin"Kwantar da Hankalinki..muma da Safe mallam din ke Fadamana ba Kulle kullen kowa bane sai Hajiya babba..matar nan ta Zame min ciwon ido wlh..!
Sai Sakina ta saka kuka tana Fadin"Ni dai wlh Anty in dai yarinyar nan ta tare agidanan bazan koma ba..ai wannan ci baya ne..Taya zan hada miji da Amina haba Anty..!
Cikin sigar Lallashi take fadin"Haba Sakina bani nace kiyi hakuri ba..Bazata tare ba na Fadamiki..!
Sakina tace"Haba Anty..Kince auran haka zai kare gashi kuma ana Fadin zan zauna waje daya da ita..!
Amatsayin kishiyoyi Haba don Allah wannan ai Tsabar ci baya ne..!
Anty Amarya ranta ya baci ta mike tana Fadin"To shikenan kiyi yarda kika ga dama Tunda baki ga Kokarin da nike yi akanki ba..,!
Daga haka ta Dauki wayar ta ta fice Daga Dakin Sakina tatashi ta Fita tana kuka har Falo tana Fadin"Anty Wlh in har yarinyar nan ta tare agidan nan bazan zauna ba sai dai na koma Dutse..!
Anty Amarya ta juyo tana fadin"In ma ta taren sai me..?
Ba Madina zaku koma ba.zan san abunda zan yi in kuka koma sai dai taji Shuru daga ita har iyayen nasa..!
Sakina ta Rushe da kuka ta fadi kasan Cafet tana fadin"Anty Umar yayi Rantsuwan bazai koma Dani Madina ba..Nan zamu zauna har sai yaje ya Dawo..!
Anty ta Zaro ido tana fadin"Mun shiga uku..!
Sai ta koma ta zauna tana fadin"Meya faru yace haka..?
Sakina tace"Saboda rigiman da mukayi na zuwa wannan bikin Tunda yace bazani ba na matsa shikenan ashe yayi bakam da niyyar in nazo bazam koma ba..,!

Anty Amarya ta yi Tsaki kafin tace"Ai Sakarcim ki ne Sakina..Baki yi Shawara Dani ba kika aiwatar da abunda kikaga dama..Kin kuma sani Tunda ya Rantse bazai tafi dake ba din..Kin manta kun taba yin haka Farkon Tafiyarku..!
Sakina ta kara Fashewa da kuka ta Tuna Lokacin farkon auran su ne da ya tafi da ita Hajiya bata da lafiya zai zo Dubata tace sai tazo yace in tazo nan zai barta sai ya sake Dawowa ta zata Fade yake sai da suka zo ya tafi ya barta Sai da tayi wata Takwas sannan yazo suka koma shima sai da Mallam ya kirasa yamai fada bai da Saurin Fushi ammh in ya Zuciya Bashi da kyau..!
Tana ta kuka Anty Amarya ta mata bazan karshenta ma tashi tayi ta shige Dakinta ta Kulle ta barta anan  Mallam tayi ta kira bai Dauki wayarsa ba kila yana cikin wani aiki ne ranta ya baci ga kukan sakina gashi kuma ta raasa mafita yasa ta fita Falo tana Fadin"Sakina wlh in baki min shuru ba sai naci Ubanki..!
Tsit Sakina tayi tasan ran Anty ya baci Cikin Fusata tace"Duk uban wa yaja in bake ba..Ki rika yin abu gaban kanki ba Shawara sai ki koma Chan Dutse ni bazaki zauna anan ki kasheni ba ina ji da kaina nima..!
Kara jan Tsaki tayi tana juyawa ta koma Ciki Sakina ta rakata da Fadin"kiyi hakuri Anty..!
Umar baisan ta fito ba yana gama Fada mata mganar Tarewan Amina ta Zaro mayafi Ko kudi bata Dauko ba Allah yasa Pos dinta akwai yan Chaji da mai adaidaita ya mata Tijara.




*Ina cigiyar wani Tsohon Littafi na MAMAN KAUSAR mai suna WATA SHARI"AR wanda ya samu Comp Doc dinsa yamin mgana ta wannan lambar 09069067488*



*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK1*


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*Kar'shen Littafi na D'aya*

Dole Mamanmu ta cire komai aranta kada a ganota bayan fitan Hajiya ita tayi ma Amina Tsifa ta wanke mata kanta tas,su hamida kuma suka Hada ma Amina kayanta waje daya kamar yadda Hajiya tace suna yi suna hawaye domin sun san zasu yi kewar Amina kewa mai yawa,Wadanda ba"a wanke ba Mamanmu tace su bar mata zata wanke kafin su dawo daga gidan Kitso,Su ukun suka tafi Raka Amina wacce suka kasa gane yanayin data ke Ciki Fuskarta ba fara"a kuma ba Damuwa sosai Kadahan kadahan
Bayan fitansu Mamanmu ta kwaso sauran kayan Amina ta wanke ta shanya bata so tayi wani abunda za"a Fahimci Ainihin Fuskarta,Bayan fitansu Ta kira Jafar awaya tana kuka tana Fadamai yayi ma Aba mgana a bari Amina ta karisa karatunta ammh Jafar ya nuna mata mganar Baba mallam ce Aba ya kirasa ya fadamai shima ya yarda da hakan Amina ai Jidalinta sai ita barinta ma ai wani Damuwar ne duk da yaga ta Rage wani abun ammh gara a kaita gidan Mijinta kila in tana da Rabon hankali Tayi,ganin ba Nasara yasa ta maida akalan Kiranta kan goggo Husai itama dai da Farko taso ta bi bayan mamanmu sai da ta Kira Aba sukayi mgana ya Fadamata komai sannan ta Fahimta ta Kira mamanmu tana kara bata Hakuri ita a tunaninta tana Tsausayin Amine ne batasan so take a hana Tarewar Amina ayah din nan ba sai dai Bakin Alkalami ya riga ya bushe..!
Duka yaran nan kaf sai da ta Kirasu tana kuka tana fada musu Rayuwar Amina na cikin wani hali su Jadwa sun yi Na"am da mganar mamanmu Amina tayi kankanta ba zata iya zaman kishi da Sakina ba sai dai ya zasu yi? su basu isa suce wani abu ba..Mganar Hajiya da Baba mallam ko Aba bai tsallaketa ba, ballatana su da Fatan Alheri kawai suka bi kanwar tasu Domin awannan gabar basu da abunda zasu iya yi.
Ganin duka ba sa"a sai ta Kira Kanin Baban Aba na gusai. baba Salihu tana kuka take fadamai abunda ke Faruwa shima Hakurin ya bata ya nuna mata Amina ta isa aure har ta gota sannan gatan da Mallam yayi ma Sa"idu ko su Dangin ubansa basu yi masa ba..Saboda haka Sa"idu Mai yima mallam Biyayyah ne su kuma bazasu taba Katsaladan kan abunda ya Shafe su ba Tun Aminu nada rai Mallam ke amsa sunan Uba ga Sa"idu ballatana da kasa ta shafe idonsa ko su yan"uwansa Suna Alfahari da Mallam bama Sa"idu kadai ba Saboda haka tayi hakuri ai mallam din ya Kirasa sun yi mgana kuma yayi Na"am da mganar tunda an Daura auran tarewar shine mafi Alheri.

Mamanmu ta rasa mafita ko"ina taje ba Sa"a sai alokacin ta kara yardan ma kanta Mallam Ya riga yayi nisa mai Tardosa sai ya Shirya.
Shiyasa ta yanke shawaran kiran Anty Amarya ta fadamata kokarin da tayi ba asamu mafita da sannan taji ya sukayi da mallam din kuma bata Dauki waya ba,Ita kadai agida abun Duniya duk ya Isheta ko girki ta kasa yi Jawad ne kadai yaje makaranta Hamida da Amina basu je ba da Hanne suna chan gidan Kitso Mamanmu kanta Sara mata yake yi domin har ta fara Hango yadda abubuwa zasu lalace da yadda Madina zata Dauki lamarin ta santa Sarai taki Daukan wayanta ne zatace Batayi mata kokari ba,Data san yadda ta kasa zama shiga nan fitan nan da tayi mata uzuri ta tabbata in ta Zake da yawa auran nata daya Rage igiya Biyu Sa"idu zai iya Tsinketa ta shiga uku..!

*****"

Bayan wani Lokaci sai ga Anty Amarya ta sake fitowa daga cikin Dakinta Fuskar nan duk a jagule Sakina ta kallah wacce ke kuka tana yi tana faman toshe bakinta kada kukan ya fito ammh kallo daya zakayi mata ka fahimci yadda ta Yarkace lokaci daya.
Wani katon tsaki ta kara saki tana kallon sakina Lokaci daya tana Fadin"Kukan me zaki dameni dashi Sakina..?Yau duk kwabewar komai ta Sanadinki ne sanadin shegen kafiyanki da Taurin kanki.!
Ayadda take mgana daga gani ranta ya gama baci Sakina ta gama Saki da lamarin tasan bata da wata mafita sai Anty Amarya yasa cikin karyewar murya tace"Kiyi hakuri Anty..Wlh ban zata abubuwa zasu lalace mana haka ba..!
Anty Amarya tayi kwafa tana Sake Duba wayarta kafin ta fara Zagaye Falon Tana sakin tsaki ita kadai Lokaci bayan Lokaci tana kara Duba wayarta kafin ta kalli Sakina tana Fadin"Kin isheni da wannan koke koken naki..in har bazaki yi min shuru naji da abu daya ba to.. ki tashi ki koma inda kika fito ko kuma ki hau Mota ki koma Dutse Bazan iya da iskancinki ba..!
Sakina ta kalli yadda idanuwan Anty Amarya suka Yi jajir tsabar tashin Hankali sai jikinta ya karayin sanyi Domin tasan duk abunda take yi saboda ita take yi da sauri ta share Hawayenta ta na kara sunkuyar da kanta cikin muryan wacce tasha kuka tace"Na bari Anty nabi Allah na Bki.Bana so na koma gidan Umar..Bazan iya hada zama da wannan yarinyar ba..Sannan in na Koma Dutse wajen wa zan zauna..?,Sannan so kike makiya su yi mana Dariya Anty..?
Anty Amarya ta harareta kafin tace"Sun dade basu yi ba koma me ya faru ai ke kikaja..Sakina bakya jin shawara..Sannan kin raina kokarina a kanki to zan tsame hannuna ga ki ga Umar din sai naga abunda za"a fasa din..!
Da sauri Sakina tace"Don Allah ki yafemin Anty bazam kara ba..!
Anty Amarya ta kalleta tana Saussauta bacin ranta domin ji take kamar ta kamata tayi ta duka ko zata wuce haushinta Sakina batajin mgana ta lalata komai Ayadda tasan Halin Mallam bazai yi mgana ya Saba ba..Ta bangaran hajiya ne taso suyi Amfani da Amina su samu nasara ita din ma Shegiyar yarinyar ta zame musu ciwon ido Shawaran Dayyaba tabi ta kira mallam domin ya Rufemata bakinsu Sai dai bai Dauki kiranta ba kuma bai kira ba ranta yana bace ne sannan ga Sakina da mganganunta na banza yadda kanta ke sarawa ji take kamar tayi ta kurma Ihu lokaci Daya abubuwa sun lalace mata kuma ta kasa samun Mafita..!
Sakina ce ta katseta da Fadin"Kin ji Anty Ki yi hakuri don Allah..!
Sai alokacin ta sauke numfashi Tana Fadin"Naji zan hakura..Ammh da sharadin bazaki sake aikata wani abu ba sai kin nemi shawarata..Sannan ki Rage kafiya da Taurin kai in kikace haka zaki cigaba da yi Bazaki taba cimma nasara ba sakina komai da kika gani dan taku ne..Sannan sannu sannu ai kwana nesa ne watarana Burin mu zai cika..!
Kai ta gyada mata tana Fadin"Insha Allahu Anty yanzu menene mafita..?

Ta bude baki ta bata amsa kenan wayarta ta Dauki kara tana Dubawa taga Mallam ne ai hannu kawai ta Dagama Sakina ta wuce Dakinta tana amsa wayar.
Cikin Damuwa ta fara mgana daidai Sanda ta shigo Cikin Dakinta"Mallam ina ta kiranka baka Dauka ba..!
Hankalina ya tashi ina cikin matsala..!
Dagachan bangaran wata kakkausan murya wacce ba Tausasawa acikinta Sake take kawai irin na manyan mutanen masu katuwar murya mara Tsari mai ban tsoro naji yace"Hajiya Madina ina kan wani aiki ne..Lafiya akwai damuwa ne..?
Cikin sauri tace"Sosai ma mallam..Kan shegiyar yarinyar nan ne da ka taba yima Dayyaba aiki ya fada kanta..wacce na Fadamaka Malam ya aura ma Umar ita..To itace zencen tarewarta ya taso yau yau Mallam ka taimakamin nayi iya bakin kokarina ta bangarena ba Nasara. !
Wata dariya ya saki mai Ban tsoro kafin yace"Ai daman na Fada muku..Tunda ta Tsallako aikin da ba nata ba a kawar da ita shine masalaha..Nasani ne watan watarana sai ta shigo Tsarinmu Tsundum..!
Anty amarya tace"Yanzu duk ba wannan ba..Yanzu bakin mallam da Hajiya zaka Rufemin in mganar tarewar ta sha ruwa sai muyi mganar Turata inda uwarta taje mallam ko Dayyaba ta amince ko bata Amince ba..Bana ragama duk wanda yace zai shiga Tsakanina da Burina..!

Dariyan ya kara saki kafin yace"ki bani minti goma zan kara kiranki..!
Kit ya Datse kiran sai ta koma ta zauna gefen gado tana share zufan goshinta Dayyaba ta cuceta tun farko taso ta bari su kawar da Amina tace a kyaleta ita din bazata zame musu matsala ba sai gashi yanzu Ta zame mata ciwon ido bata fatan Amina ta Tare agidan Umar tana hango Tarin abubuwan da bazata so faruwarsu ba nan gaba..
Abunda bata sani ba Bakin Alkalami ya Riga ya bushe..Da sun sani..Dama ace suna Tara sani da Allah da basu bar Amina ba..Domin watarana itace Sillar bankadaran sirrikansu..!
Itace kuma zata Shiga Tsakaninsu da cikar Duka Burikansu..!
Tana zaune tana faman Tunanin mafita Minti goma na cika Mallam ya Sake kiranta Hannunta na rawa ta Dauka bai bari ma ta fara mgana ba ya Fara mgana cikin Sauri da karfi yana Fadin"Kin makara Madina..Kin manta na Fadamiki Mallam yunusa yafi karfinki..?Na fada miki bayan ke acikin matansa akwai wacce taso ta mallakesa bai samu ba itama an fadamata Allah yana Tsare bawansa Mijinku yana da Tsari mutum ne mai Ibada da addini aljanun mu bazasu iya Tunkaransa ba..!
Da sauri Anty Amarya ta katseshi da Fadib"Hajiya fa..?
Sai da yayi jim kafin yace"Bazan iya Tankwara zuciyarta Lokaci daya ba Madina itama bazaune take ba..Sannan Lokaci ya kure miki..Nagani Dole yarinyar ta tare..Na hango wani Duhu sannan

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment