Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muna chan..!
Mallam yace"Dakyau haka ake so..Allah ya zaunar daku lafiya..Sai ka zama jajirtattacen adalin zama da macen Fiye da Daya sai Adali Umar..Bana jinka nasan bazaka taba aikata wani abu mara kyau ba..Sannan itama Diyar Kattab din indai Halin Mahaifinta ta Biyo Har Abada bazakayi nadama ba..!
Baba Sa"idu yace"Allah ya sa...!
Kansa na kasa shidai bai ce komai ba basu Damu ba Sanin Halinsa Shuru Shuru bai da Hayaniya.
Baba Malam ne ya kalli Baba Sa"idu yana Fadin"Sa"idu ka tafi wajen aika..Nima anjuma kadan zani Gidan Sarki Tun jiya Sakon sa ya isoni yana son ganina..Umar kuma ya shiga Cikin Gida ya gaida iyayensa zuwa anjuma sai mu zauna gabadaya domin a gabatar da Bakuwar data shigo Cikinmu Gabadaya..!
Baba Sa'idu ya jinjina kai yana ma Malam Allah ya kiyaye Hanya.
Tare sukayi mai Sallama suka Fice shida Baba Sa"idu sun Dade aharaban gidan suna jingine jikin Motar Baba Sa"idun suna mgana kafada na gugan kafada Malam na daga cikin Falonsa yana Hangesu ta Wandow Falon Lokaci Daya ya saki kayattacen Mirmishi.
In ka gansu kamar wasu yaya da kaninsa uwa daya uba Daya ya Tabbata abunda bazai iya Fadamai bane yake Sanar da Sa"idu Akwai Shakuwa da Fahimta a Tsakaninsu Yana Daukansa kamar kaninsa Shima yana Daukansa kamar yaya kuma Uba agaresa
Sun dan jima suna mgana kan yana Fadamai bai Tsara Karin aure yanzu ba, sai dai kana naka Allah na nashi ne Baba Sa"idu na ta bashi Wasu Shawarwarin kafin suyi sallama ya Shiga Mota ya wuce Gidan gona yayinda Shi kuma ya Fara takawa yabar Filin Haraban gidan zuwa Shashen Hajiya ammh Kuma Ransa da da Kallonsa na Shashen Anty Amarya yana Tunanin ko Sakina ta Daina kukan..?ya manta Rabonsa Daya ga taci wani abu sai ruwa kawai..!











*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima Yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*


*🅿️09*

Cikin Tafiyarsa ta natsuwa ya karisa Shashen Hajiya babba kamar yadda yake a ka"idarsa sai ya fara isa shashen Mallam sun gaisa sannan sai ya shiga cikin gidan Daya bayan Daya ya Bisu ya gaishesu.
Hajiya na cikin Dakinta har alokacin Daya shigo Aisha ce da Hanne har Lokacin afalon yana Shigowa Cikin Sallamarsa da Muryansa mai Zaki da Sanyi a koyaushe,Lokaci daya da kamshin Turaransa na Arab yayi musu Sallama..!
Gabadayansu suka mike Cikin Fara"a da Murnan ganinsa domin sun Dade basu gansa ba Tun Karshen wanchan Shekara sanda yazo Lokacin Duba Hajiya ce Datayi ta Fama da Kafa suna makaramta basu gansa ba kuma Kwana Biyu yayi ya koma.
Hannayensa duka Sanye Cikin Aljihun wandonsa ya Kariso Tsakiyar Falon gabadayansu har suna Hada baki wajen gaisheshi da yanayin Natsuwarsa ya kallesu yana amsa gaisuwarsu yana kara ganin girmansu acikin Idanuwansa.
Kai Tsaye yace"Hannatu Aisha meyasa baku je makaranta ba..?
Da Sauri Aisha tace"La yaya bana Fada maka ba..!
Sai Alokacin ya tuna da Sauri yace"ohm.Sorry na manta..Allah ya bada sa"a..!
Suka amsa da Ameen gabadayansu sai kuma yayi shuru yana kara nazarin Falon kamar me neman wani abu basu Damu ba Sanin Halinsa Sannan babu wani Shakuwa sosai a Tsakaninsu Tunda shi Babba ne sannan Lokacin da suka taso baya kasar yana Madina so zamansa Dasu bashi da yawa ammh duk da Haka yana da Kwarjini da baiwar da kowa ke girmamasa,ba Duka yake yi ba ba kuma Fada ba,Shi ina ma ya zauna ballatana yayi Hukuncin ..?in yazo kuma bai wani Dadewa yake komawa sai dai AllAh ya riga ya bashi wannan girman kuma ya Dauka kamar yadda In mallam yayi mgana bamai Musamai haka shima mgana Daya zai yi Cikin kwanciyar Hankali da Salama kowa zai shiga Taitayinsa bawai bashi da Sakewa bane, bai da yawan wasa da Dariya sannan bai da mgana ballatana Hayaniya yana da Matukar Sanyi Sosai a lamuransa.
Kamar ma ya manta daasu acikin Falon Saboda yadda yayi Shuru bai kara mgana ba sai chan ya kalli Aisha kafin yace"Ina bakuwar ku.?
Da Sauri tace"Na kaita Dakinmu na nuna mata Tiolet tana ciki na barta Tun dazu..!
Kai ya gyada kadan kafin yace"Ina Hajiya..?

Wannan karon Hanne ce ta nuna mai Dakinta tana Fadin"Tana ciki Yaya..!
Bai tsaya kara mgana ba ya Kama Hanyar zuwa Dakin Hajiya Cikin Natsuwarsa kannensa suka Bisa da kallon Sha"awa Duk cikin gidan nan ba kamarsa Sai dai abiyo bayansa.
Sai da suka Tabbatar da ya shiga Dakin Hajiya sannan Hanne ta Juyo Tana Fadin"Ya Aisha kinga yadda Ya D'anmalam ya kara kyau kuwa..?Wlh nima ina son naje Madinar nan Watarana..!
Aisha tana jinta batace mata komai ba illah ta Cigaba da Duba Littafin Dake Hannunta Hanne bata Damu ba Sanin Halin Aishan itama din mai Sanyi ce.
Hajiya na Tsaka da kasafin Turaranta Taji Sallamarsa Cikin Sanyi da Haiba Lokaci daya da Kamshin Turaransa mai Sanyaya Zuciya batasan Lokacin data saki Mirmishi ba Cikin Farinciki ta amsa sallamar tasa tana jaye kayan gabanta Lokaci Daya tana mai maraba.
"Maraba..Maraba..Maraba da Danmallam maraba da bakin madina Bakin Larabawa..!
Sai alokacin hakoransa kadan suka Fito yana Mirmishi gaban Hajiya ya Duka kansa na kasa yace"D'anmallam dai Hajiya..?Har yaushe ne zaki Fara Kirana da Umar ne..?Alhalin Baba Sa"idu Sa"idun sa kike kiransa Hajiya..!
Hajiya na Dariyan Farincikin ganin Yaronta ta kauda mganar da cewa"Masha Allah..Danmallan me kuke ci a Madinar ne.?gabadaya ka Sauya ka koma kamar Balaraben chan..!
Kai kawai ya gyada yana Shafa Gemunsa kafin yace"Hajiya bakomai..Sai nasaran addu"an ku gareni..!
Hajiya tace"Hakane..Allah ya kara Tsareka Allah ya Dafa maka Allah ya albarkaci Rayuwarka..!
Ya amsa da Ameen kafin ya Dago yana Fadin"Hajiya baki ce Allah ya bani Zuru"a ta gari ba..!
Hararansa tayi kafin tace"Ko ban Fada ba..Ina maka wannan addu"ar D'anmallam..!
Daman yasan haka zatace yadda Hajiya ke kunyarsa ko Ita Bafullatanane sai haka Tambayan kowa da kowa yayi tace duk suna Lafiya,Shuru ya biyo baya shi bai ce mata ba itama yasan bazatace ba Hajiya nada wannan Halin bata matsa ma Mutum akan abunda tasan Dole zata saani Shiyasa bata ce masa komai kan Sarood ba shima bai ce mata ba.
Kansa na kasa yana Duke ita kuma tana Cigaba da Zuba Turaranta Ganin Yaki zama kuma yaki tashi yasa ta kallesa tana Fadin'Ka zauna mana..Kada Tsugunnen ya gajiyar Dakai..!
Kai ya girgiza kafin yace"Hajiya Ina da gajiya ajikina..So nake na shiga na gaisa da su Hajiya uwa..Kafin naje nayi wanka na Huta..!
Kai ta gyada kafin tace"Hakan ma ya kamata..Mallam ya fitan ne..?
Kansa na kasa yace"Bai riga ya fitan ba ammhh yace yanzu zai fitan..Muna ma nan Haraba ni da Baba Sa"idu yanzu ya wuce gidan gona..!
Hajiya tace"Sa'idun Zainabu da Malam..ya shigo mun gaisa tun zuwansa..!
Bai yi mgana ba ita kuma ta kallesa tana Fadin"Dame zaka Karya..?nasa dai yaran sun yi maka Sinasir da waina..Bansan kuma me zamu ba wannan bakuwar ba kasan ku achan ba irin Cimar mu bane naku..!
Sai alokacin ya Dago kafin yace"Da kuli Hajiya..?
Kai ta gyadamai tana yar Dariya shima Mirmishin yayi yana Fadin"Yaushe Rabona da waina da kuli Hajiya..?Naji dadi sosai su dafamin ruwan Tea da na"a na"a,su hadomin da waina din ita kuma Sarood su hada mata Tea su soya mata Kwai is ok..!
Hajiya bata wani Damu ba tace"Shikenan.Ammh a Shashen mallam zaka Huta..?ko yanzu zaku isa gidan naku..?
Da Sauri yace"Sai Dare hajiya..Dakin su Shamsu zan yi wanka na Huta zuwa an juma..!
Hajiya tace"Na manta ne da na saka su Akilu sun gyara maka Dakinsu Nazem ka Zauna aciki..!
Kai ya kada kafin yace"Bakomai Hajiya nan din ma ya isa..!
Hajiya tace"Ai shikenan..!
Yana kallonta Kafin yace"Hajiya Turare kika fara saidawa..?
Hajiya tace"A"a Goggonku Yakura ta aikomin dashi shine nake rabawa zan aikama sauran iyayanka Sauran kuma na matan Sa"idu ne..!
Danmallam ya Murmusa kafin yace"Su yaya suna Lafiya..!
Hajiya tace"Duka suna Lafiya..!
Daganan sukayi shuru hirar ta kare ya Dade kafin ya tashi ya mata sallama ya Fice,Bayan ya fito su Hanne sun zata zai nemi Sarood sai dai bai ce musu komai ba ya Fice bayan Fitarsa Hajiya ta leko tace Hanne ta Dafa Ruwan Tea ta soya kwai ita kuma Aisha taje wajen Shamsu ta karbi key din Dakin Su Nazem ta dan gyarama Danmallam ya samu wajen da zai karya ya Huta.
Dukkansu da toh suka amsa Aisha tatashi ta saka Hijabi ta Fice,Hanne kuma ta shiga Kitchen.
Daga Dakin Hajiya Shashen Hajiya Uwa ya isa Tana ganinsa Cikin Fara'arta ta fara mai maraba itama Dukawa yayi yana gaisheta ta amsa tana Fadin"Umaru basai ka jira mu zo sannu da zuwa ba..!
Kansa na kasa bai ce komai ba tayi Dariya ya tambayeta yaran tace kowa Lafiya sai ga Umaima ta fito ta gaisheshi ya amsa yana kallon Hajiya uwa kafin yace"jikinta ya daina tashi ko..?
Hajiya Uwa tace"To ya dai yi Sauki Umaru..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kara afuwa..Nazo mata da wasu manganuna in na Huta zan kawo mata ta fara amfani dashi mu gani..!
Hajiya Uwa ta fara mai godiya yana amsawa Har ya fice tana Rakasa da addu"an haka take ita tana da Kirki kamar Hajiya take.
Daganan sai bangaran Haj.Nasara itama ta karbesa sosai suka gaisa da Tambayan bayan Rabuwa Ikram ya gani tazo ta gaisheshi ya amsa yana kallonta ganin ta girma har zai tambayeta meyasa bataje makaranta ba sai ya tuna da mganar Aisha sai ya Fasa Yana Shirin Fita ne Take tambayansa ko da ba Sakinar suka zo bane..?
Cikin Haibarsa yace"Tare muke da ita..Tana bangaran Anty Amarya..!
Baki ta tabe batace komai ba yayi mata Sallama ya fice yana fita tace Ikram ta shiga Kitchen ta Dafamai Tea da soya kwai,Saboda Umar Domin in yazo garin ba wacce bata kokarin kyautatamai kamar yadda zata kyautatama Malam.
Kai Tsaye Daganan sai Shashen Anty Amarya ita kam koda ya Shiga bata Falon Sa"adatu kadai ya gani Tana Kwance saman kujera ko Sallamarsa ma bataji ba sai dai ta gansa saman kanta Cikin Muryansa yana Fadin"Ke baki jin sallama ne..?

Kamar ta kifa haka ta sauko daga kan Kujeran tana Raba ido Cikin Kifta ido Tace"Sannu da zuwa ya D'anmallam..!
Bai amsa mata illah Falon Dayake bi da kallo kafin yace"Ina Anty..?
Da Sauri ta mike tana Fadin"Tana Dakinta ita da Ya Sakina..!
Baima ce ta Kirata ba yaga ta wuce sai bai kirata ba Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa ya kurama waje Daya ido kamar mai nazari.
Sa"adatu sai da tayi knooking Domin Tun isowar Sakinar tana kuka suka Kule Cikin Daki ita da Anty basu Fito ba,Kuma sun kulle kofar Daga ciki Anty Amarya da Ranta ke bace domin ta gaji da Lallashi da Tambayan Sakina meke Damunta taki gayamata gabadaya Tunda suka iso take kuka taki mgana ballatana tasan meke Faruwa..
Dagachan tace"Waye..?
Da Sauri Sa"adatu tace"Nice Anty..!
Tashi tayi taje ta Bude Kofar da Sauri Sa"adatu tace"Anty Ya D'anmallam yazo yana Falo..!
Da sauri tace"Yazo .?
Ta daga kanta Sakina ta juya tana kallo wacce ta Dunkule kan gado tana kuka kafin ta Dawo da kallonta kan Sa"adatu tana fadin"Kice mai gani nan zuwa..!
Daganan Sa'adatu ta juya ita koma ta maida kofar ta Rufe ta Dawo bakin makeken gadon Dake Bedroom din inda Sakina ke Dunkule ta Dade tana kallonta kaf ta gama Hasashenta bata hango abunda zai sa Tunda suka iso Sakina ke wannan kukan ba ta kuma yi Tambayar Duniyar nan Sakina taki Mgana.
Kai ta kada Kafin tace"Ai shikenan Tunda bazaki mgana ba..ga Umar din chan yazo..Bari naje na tambayesa kila shi ya fadamin abunda ke faruwa..!
Har ta bar Dakin bata Dago Daga kukan datake yi ba ballatana tasaka ran zata kalleta
Ta iskeshi Tsaye bai ko zauna ba Sadiya ta fito sun gaisa Sa"adatu ta shiga Dakinsu ta Fadamata zuwanshi.
Yana ganin Fitowarta ya Rage tsawonsa ya Durkusa kan kafafunsa yana gaisheta ta amsa Lokaci Daya Tana zama kan Daya daga cikin kujerun Dake Falon.
Daga gaisuwan ne bai kara cewa komai ba kansa na kasa yana kallon adon Zanen jikin Tattausan Cafet din Dake Falon.
Anty ta kalli su Sadiya kafin tace"Ku tashi ku shiga ciki..!
Ba musu suka mike zuwa Dakinsu sai da taga Shigewarsu kana ta maida Hankalinta kansa kafin Tace"Umar meke Faruwa ne..?ko kun samu Sabani da Sakina ne .?Tunda kuka iso take kuka gatachan kwance kuma nayi Tambayan Duniyan nan tayi banza dani har yanzu taki cemin komai..Shine nace bari kai na Tambayeka meke faruwa ne .?
Kansa na kasa bai Dago ba abu Dayane ya kara bashi mamaki me Sakina ta Dauki kanta ne..?tana Tunanin kukanta da Rigimanta zai sa afasa komai..?ai ta makaro Domin bakin Alkalami ya riga ya Bushe..Sannan bata isa yasa ya Sauya abunda Allah ya Tsaramai ba Duk da karin aure bai Cikin Tsarinsa.
Yasan yana da Sanyin Hali baya son Damuwa da Hayaniya ammh tasanshi Yana da zuciya mai karfi wanda in yagaji da baka baki bazai biyema iskancinka ba zai Fita batunka ne kamar ita yadda tayi mai tun suna Madina yake bata baki ganin yadda Hankalinta ya tashi bayan ya gayamata bayan an Daura auran Abunda yasa ya Biyemata yana ganin ya bata mata Tunda shima abun Daga sama yazo mai ammh akallah ba Dadi Kaji Mijinka yayi aure Lokaci Daya sai dai ya gaji da Lallashinta zai kyaleta In ta gama kukan don kanta ta Hakura shi bai kuma san da wani Kalma zai kara lallashinta ba.
Anty Amarya ta gaji da jiran amsar sa bai ce mata komai ba gabanta nata Faduwa kada matsalan yazama babbace Fiye da Tsammaninta.
Yasa ta gyara zama tana Fadin"Kayi Shuru..!?Ina fatan Allah yasa abun bai kai ku ga Saki ba..?
Sai alokacin ya Dago yana kallonta bata ga wani abu a Fuskarsa ba Illah Haibarsa da Zatinsa Cikin kakkausan Muryansa mai Cike da Sanyi yace"Babu ma mgana makamancin wannan Anty..!
Ajiyar rai ta sauke na samun natsuwa kafin tace"To me ke faruwa..?
Nan ma Shuru yayi mata ta kara kallonsa tana nazarinta har ta Fidda rai da zai yi mgana sai chan taji yace"Tunda bata gayamiki ba..Bakomai kenan..!
Kai Tsaye ya fada batare da Tunanin wani abu ba ya mike yamata Sallama ya Fice Daga Dakin tana Binsa da kallon mamaki.
Aranta tana ayyana wani abun Meke Faruwa..?meyasa Sakina taki mgana..?tana ji ajikinta koma miye babban al"amari ne sannan ta godema Allah daya kasance ba Zencen Saki bane Komai miye ai zai zo da Sauki.
Tashi tayi ta koma Dakin ga mamakinta sai ta iske Sakina ta shiga wanka sai taji Dadi,Yasa ta fita da Sauri zuwa Dakin su Sadiya tace su tafi Kitchen su sama ma Sakina abunda Zata karya dashi Dakin ta koma ta iske Sakina ta fito Fuskarta Duk ta kumbura idanuwanta duk sun shige Saboda kuka.
Anty Amarya ta kalleta tana Fadin"Ko kefa Sakina..?
Dagowa tayi ta kalleta Fara ce kyakyawa Daidai Misali sannan ita din mai matsakaicin Tsawo ce Tana da Jiki kadan da Jikin mata.
Kai Tsaye tace"Ya gayamiki wani abu..?
Anty tace"Kema kinsan bazai yi mgana ba..Umar yafi Ubansa Miskilanci da kyaluwa..!
Dan Mirmishin Fatan baki tayi Lokaci Daya tana Cije bakinta Towel ne Babba ajikinta taja Kujeran gaban madubi ta zauna ta Fara Shafa mai,Acikin Ranta tana jin kanta yayi mata Girma kamar zai Rabe Biyu Saboda Tsananin Kunar da zuciyarta ke mata.
Tana gama Shafaa mai ta Sauya kaya Cikin Wata Riga da wando Saukakku,Lokacin Sadiya ta shigo mata da Faranti shake da kayan karyawa Tea kadai ta sha bata iya cin komai ba,Bakinta ba Dadi Saboda yanayin Datake ciki.
Tagama kenan sai ga Anty Amarya ta shigo Dakin tana kallon Farantin Dake gabanta take fadin"Ya haka..?naga baki ci komai ba..?
Sakina na Sake komawa kan gadon tace"bakina ba Dadi Anty..!
Anty ta waro ido kafin ta karisa gefen gadon ta zauna tana Dafata Lokaci Daya tana Fadin"Ke na tabaki da Alheri Sakina..Allah yasa abunda muka Dade muna jira ne..?
Cikin Mamaki take kallonta kafin tace"Me kenan..?
Kai Tsaye tace"Ciki mana Sakina..Naji kince bakin ki baya Dadi..shine nake Tunanin kodai kodai..!
Da Sauri ta katseta ta fadin"Ba ciki bane Anty..Wannan al'amarin yafi gaban na..Rufo kofa kizo kiji..!
Da Sauri tatashi ta Rufo kofar ta Dawo ta Zauna kusa da ita kamar wata kawarta.
Sakina ta Fara matsan kwallah kafin tace"Anty Umar fa aure ya kara..!
Anty tayi wani Sansarai rai kafin tace"Aure wani irin aure kuma..?
Sakina ta ballo Hawaye saman kumatunta kafin tace"Aure da kika Sani Anty..Abun bakin cikin ma bai Fadamin ba sai da aka Daura auran. !
Anty Amarya ta Dafe Kirjinta kafin tace"Daman da gaske kike yi Sakina..!Wani irin aure kuma ana Zaune kalau..!
Sakina tace"Uhm yadda kikaji haka naji Anty..Ni ba komai yafi Tadamin Hankali ba..Irin matar daya aura..Anty Balarabiya ina ni ina kishi da Balarabiya..?
Ta karishe fada tana Kuka Wiwi Anty Amarya ta Dora Hannu akanta tana Fadin"Na shiga tara ni Marliya..?wannan wani irin kaddara ne..?
Sakina ta kwanto da kanta Saman Cinyar Anty Amarya kafin tace"Kaddara mai muni ma Anty..Kinga kyan yarinyar..?wlh ko gasar kyau ta Shiga sai taci..Tafini komai da komai ta bangaran kyau da Zati da nasaba da asali Wlh Anty wannan suka fara zama da Umar ni Bora zan zama..!
Ta karishe Cikin gunjin kuka Anty Amarya gabadaya jikinta rawa yake yi Cikin Tashin Hankali tace"Wai garin Yaya haka ta faru...?Diyar wacece ya auran..?
Sakina tace"Diyar abokin Baba Mallam ne..!
Anty Amarya tace"Kattab..?
Da Sauri ta Daga kai kafin ta cigaba da Fadin"Ita..Diyar su din nan kwara Daya Sarood..yadda Umar din yace min shi Abu kattab din ne ya bashi Auran kuma bazai iya kin karba ba..Ni ban sani ba saida aka Daura auran a Satin da zamu taho..!
Anty Amarya gabadaya Hankalinta baya Jikinta Har Sakina ta cigaba da Fadin"Tashin Hankalina Daya Anty..In tazo ta Haihu fa..?wlh Bora zan zama a idon Umar da Danginsa na zama bani da wani amfani..!
Da Sauri Anty Amarya tace"Ina.karya ne..Ba wanda ya isa wlh..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ture kan Sakina Daga Jikinta ta mike tana Mazari Cikin bacin rai tace"ba wanda ya isa ya maidake baya Sakina..Kamar yadda ban zama baya ba..Wani Cikin ya"yana bazai taba zama baya ba..!
Take Fada tana Huci Sakina ta Mike Zaune tana Sharan kwallah kafin tace"Nama zama..Domin da ita muka zo kasar nan..!
Da Sauri ta zaro ido tana Fadin"Eyee...!
Sakina ta Daga kai tana Fadin"Eh tana ma Cikin gidan nan..Inaga Shashen Hajiyarsa yace shamsu yakaita..!
Anty Amarya ta rike Haba Kafin tace"Kenan iyayen nasa sun san da Labarin auran shine mu bamu ji ba..?
Sakina tace"Ni bansani ba..Ammh dai Malam ya sani Da Baban su Jafar tunda naji suna mgana tun muma chan..!
Anty Amarya ta Lailayo Ashar ta Dankara kafin tace"Sa"idu...Sa"idu..Ko bai kira Malam ba..Ina mai Tabbatar miki Sa"idu zai fara kira..Sa"idu ne ja gaba kan komai..Ko Malam da Hajiya basa tsallaken Shawaran Sa"idu abunda yace shi akeyi acikin Gidanan Sakina..!
Sakina ta Sharce majina tana Fadin"Anty ya zamu yi..?wlh karki so ki ganta Kinga kyanta..?
Anty Amarya Haushi ya kamata ta Ballama Sakina Harara tana Fadin"Kyan me..?kyanta na banza..Takai ki wayau ne..?Kyan ne kawai ammh batakai Budewar ido ba ..ina taje ina ta taka..?Irin wadanan kyan ne kawai da zaman waje Daya na Tabbata bata samu wata Sakewa ba..!
Sakina tayi shuru tana kallonta kafin tace'"Eh kam..kamar sakara haka take..Sai dai namiji ba ruwansa da wannan..!
Anty Amarya tayi Mirmishi kafin tace"Kada ki damu kanki..Ki Share Hawayenki kada ki kara kuka..Waannan auran wani matakin Nasarmu ce Sakina..!
Sakina tace"Taya ya..?
Anty Amarya ta kama Hanyar fita tana Fadin"kidai ki saka ido kawai..Mu zuba mu gani..!
Shege ka fasa..!
Daga haka ta Bude Kofar ta Fice tana Tafe tana Mirmishi ita kadai kamar an ce mata an biya mata aikin Hajji.
Falo ta koma ta Zauna ta Dora Kafa Daya kan Daya tana Kadawa kamar wata yar yarinya yar shekara Goma sha.
Sakina kuma tana Fita ta koma ta kwanta Damuwarta ya ragu,Saboda tasan duk abunda Anty tace kada ta Damu to tasan cewa kada ta Damun komai zai zama Daidai,Daman ga Rashin barci ga Damuwa yasa batasan Lokacin da barci ya kwasheta ba Cike da Mafarkin yadda makomarta zai kasance Tsakaninta da Umar da Sarood.

******

Amina sai gabda Azahar tatashi Daga barci tana mika Hamida bata Dakin yasa bata damu ba tatashi ta shiga waanka Lokaci daya ta Dauro alwala sai da tazo tayi Salla kana ta Sauya kaya ta saka Riga da Sikat na wani leshi da Mamanmu ta Dinka musu ita da Hamida.
Sannan ta fita Tsakar gida ba kowa ko'ina tsit,Kitchen ta Zarce ta iske ya Zulahait ta gama abinci Kuskus da Miya da nama Amina tayi Dariya kafin tace"Mijin ya Zulaiha zai ja kaya Wlh...!
Haka take fada tana Dariya kafin ta Diba iya sonta ta cika nama ta koma gefe taci tayi kat ta koshi,sannan ta fito taje bakin Famfo ta wanke hannu Dakin Mamanmu ta leka ta isketa tana Sallah Tana jin Hayaniyar Hamida a dakin Yaya taki Shiga Daki ta koma ta Sake kwanciya taci ta koshi Takaichinta Daya bata zuwa da Littafin hausa agida iya makaranta take karatunta ko boko ko Islamiya.
Ammh bata zuwa dashi gida ba Domin tana jin Tsoro ba ko wani abu ba, Aron daman iya makaranta ne ana tashi zainab take karba Saboda na mamanta ne take aro mata itama ba"a Sani ba agida.
Yasa barci ya kara Daukanta bata Sani ba sai Bayan azahar ta tashi Shima Mamanmu ce tatasheta tana Fadan ta Daina barcin yammah ba kyau.
Lokacin datasahi  ta ga mamanmu Sanye da Hijabi tana Mitsike ido ta Sauko Daga kan gadonta tana Fadin"Mamanmu ina zaki na ganki da Hijabi..?
Mamanmu tace"Gidan Mallam zamu shiga ni da yaya..Danmallam sun iso tun Safe..!
Zamu je maraba da barka da zuwa..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Mamanmu sai ku bisa..?bashi zai zo ba..?
Mamanmu na Dariya tace"Basai kin Fada ba zai zo..ammh yana da kyau mu bara zuwa din..!
Ta fada tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ki tashi kiyi sallah tunda ke bazaki shiga ba..Tun dazu hamida tatafi..!
Mamanmu bata tsaya ba ta fice Amina tana so ta tambayeta chan gidan nasa Hamida tatafi ko gidan Baba Malam..?
Bata samu mai bata amsa ba yasa ta Tabe baki ta fito Bakin famfo tayi alwala tazo tayi sallar Ta gaji da kwaciya bayanta har ya gaji yasa ta zauna tana Tunane tunane Zulaihat na Dakin Yaya tun Safe batama zauna adakin ba Tana jin tashin mganar Ya Zeena na tashi,Yau Alhamis ba islamiya Shiyasa suke gida.
Bata fita ba Sanin Yau jidalinta na Saman kanta in taje Bakinta bazai yi Shuru ba kuma baza"a samu Zaman lafiya ba.
Yasa ta Cigaba da zama inda tayi Sallar har ya Zeenatu ta Shigo ganin yadda Amina ke zaune da Hijabi yasa abun ya bata mamaki yasa ta kalleta kafin tace"Amina yau kuma Lazimin yammah aka fara..?
Amina ta kalleta shekesheke kafin tace"Uhmm..!
Daga haka bata kara mgana ba Ya Zeena tayi Dariya tana fadin"Gwara dai kiyi shuru..yau gidan ya Sarara..!
Amina batace komai ba Tunani take taje gidansu Hanne ko A"a tana Shawara da zuciyarta ne Har ya zeena ta Dauki abunda zata Dauka ta Fice ta bar Amina nan zaune tana cigaba da Shawara tasan Hanne Sarai in taje sai ta basar da ita Kafin su shirya.
Tana nan zaune har su Mammanmu suka Dawo bata tashi ba har Lokacin kuma Hamida bata Dawo ba Amina ta Mike tana Fadin"Alqur"an sai naje naga ni..Hamida iyayan gulma ba"a Dawo ba..!
Ko Hijabin jikinta bata Cire ba,Ta fice batare da tace ma kowa gata zuwa ba.
Mazan duk basa nan suna msallaci wajen karatun yammah Da Baba Mallam ke yi,yasa kai Tsaye ta Nufi Shashen Hajiya Babba.
Daga Kofar ta fara kiran sunan Hanne kafin ta shigo tana Fadin"Hanne ni zaki Wulakanta ina ta Kiranki kinyi banza dani..!
Tafada Lokaci Daya tana Shigowa Falon batare data Tsaya Lura da kowa ba,Idanuwanta suka fada kan Hanne da Hamida dake gefe sun hada kai suna mgana Amina ta rike baki Tana Fadin"Hamida an ci amanata..Shine ko ki tasheni sanda zaki taho..!
Tafada Lokaci Daya tana karisawa gabansu Hannu tasa tana jan hannun Hanne Lokaci Daya tana Fadin"Hanne taso kiji..!
Hanne taki tashi lokaci Daya tana Fadin"Ba inda zani..Lokacin da naje ina miki mgana kin manta me kikacemi ..?
Amina tace"Hamida ce zata Hadamu Hanne..?Haba hannenta Hannen Aminene..!
Tafada tana Dariya har tana Jan kumatun Hanne da Duk Dauriyanta sai da tayi Dariya.
Hamida tace"Amina kinzama abun kallo kin shigo baki gaida kowa ba..!
Sai alokacin ta juya tana bin wadanda ke falon Idonta ya Sauka kan Sa"adatu lokaci Daya ta balla mata Harara,Sai kuma wacce ke kusa da ita Tana Sanye da Babban lullube asamaa kanta Sakina ce Anty Amarya ta saka Sa"adatu ta rakota tazo ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya ta shige ta barsu da yara.
Sakina taki tafiya ne tana so taga ta inda Sarood zata fito Saboda ta tabbatar tana Shashen Hajiya,Shi kanshi Umar din bata kara jin motsinsa ba ance yana Masallaci Wajen karatun mallam
Sai ga Amina ta shigo Tunda ta shigo Kowa ya koma kallonta Saboda yadda ta Fado falon kamar Daga sama.
Amina ta Dawo da kallonta kan Hamida kafin tace"Su waye..?
Ta fada tana yamutsa baki Da Sauri Hanne tace"Matar

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment