Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Larabawa..Lale..!
Jin Muryan yaya yasa ya kariso Cikin Fara"a nan Tsakar gidan ta Shimfida mai Darduma ya zauma suka Fara gaisawa Zeematu da Hamida suka gaisheshi ya amsa kafin mamanmu tazo ta zauna su gaisa Daganan ta koma Daki ta bar su shi da Yaya suna ta Fira
Amina dai tunda ta samu ta shigo Daki bata kara fitowa ba Hamida da Zeenatu suka karisa aikin suka maida komai Kitchen suka share wajem abayin Dakin tayi alwala tayi sallah Ta Haye kan gadonta bata Damu da Kwashe kayanta akansu ta kwanta bata Damu ba

Ya zeenatu ne ta shigo tana ta Fada Fadi take"Wlh Amina ki rika Karisa aikinki..Domin nan gidam ba bawanki..Ni ba Hamida bace Darajan Mamanmu kikaci Wlh..!
Amina na jinta tana Danne Dariyanta Daga kwamcen Tana kallonta kai ta kada kafin tace"Ba Laifinki bane..Mamanmu ce take Daure miki gindin Iskanci Watarana ai ba Maman ko..?
Naga uban da zai zauna kina wannan iskancin bai ci ubanki ba..!
Ita dai bata tanka ba har ta gajii da Mitan ta fice bayan Fitar Danmallam Daman Sallama yazo yi ma su Yaya Gobe Jirginsu na dare me zai tashi zuwa Jidda a Filin Sauka da Hawa na Aminu kano.

Sai da ta ficen ne Amina ta fito da Dariyanta tana Fadin"Allah Sarki..Ya Zenatu kawar ya Abida...!
Hamida ta kalleta kafin tace"Ke kam ki tashi ki gyara kayanki Amina Harda fa Sabbi ciki..!
Amina ta kyabe baki kafin tace"In kin Damu ki gyaramin Hamida!
Hamida tace"Na rantse kuma bazan yi Kaffara ba..!
Tsaki Amina taja Kafin tace"To sai ki kyaleni malama!
Hamida tace"Yau anyi Fada da Mariya da Sa"adatu..Har da Dambe sai da mallam Auwal ya Zanesu..!
Da Sauri Amina ta Mike tana Fadim"Don Girman Allah..?
Hamida tace"Wlh suna Zage Zage..Kinsan Hanne da tsoro sai kuka take yi..!
Amina ta Daka Tsalle har da shewa kafin tace"Ahyayyeee...Yau naji Dadi karshen alewa kasa.
daman ai xaman munafunci baya karko..Tacizi yatsa Kafin ta cigaba da Fadin"Naso yau naje..Da sai na kara Yamutsa wajen munafukai..!
Hamida tace"Gwara dai da baki je ba..!
Amina ta balla mata kafin tace"Ga Shedan ko..?
Hamida kina shigarmin hanci fa ki kyaleni.!.
Hamida tace "Daga Fadin gaskiya..?ai ba karya nayi ba Da kina nan wajen Allah kadai yasan iya inda abun zai kai..!
Amina ta karkace baki kafin tace"Hanne wai me aka mata take kuka..?
Hamida tace"Me kuwa..?tsoro gareta Taga suna Ta kwasan Dambe..!
Amina tace"Aikin banza Hanne banza ce..Meye abun kuka..?
Allah ya Tsareni..!
Hamida dai bata kara mgana ba Domin Har ga Allah taji Dadin da Amina bata zo ba Domin Allah kadai yasan Iya inda Fadan nan xai kai Amina sai ta hau Fadan ta siyeshi ta kara Maggi da gishiri.
Waashegari Da Safe ta shiga wajen Hanne ta iske Su Sakina suna gidan suna ta shirin Tafiya Ya Jafar zai kai su kano Ya Nasir yana da aiki a asibiti.
Amina ta kalli Hanne tana Fadin"Wai ganin ana Fada da Sa"adatun ne kike kuka..?
Hanne tace"Ni bana son ganin ana Dambe ne..Ko ke kike Fada ai ina kuka..!
Amina tace"Wlh karya kike yi..Natan Dai kike kuka ke mai yar"uwa Ki kama Kanki Hanne Domin in kece Dariyama zata yi kina abu kamar wata sakarya..!
Hanne tace"Bakomai naji..!
Kinsan yau su ya Danmallam zasu koma..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Jiya sun zo gidanmu naji Mamanmu na Fadin yau zasu koma
Dukkansu zasu koma..?
Hanne tace"eh mana..!
Amina tace"To in suka tafi sai yaushe..?
Hanne tace"Yace ma Hajiya sai wani abu ya taso..Im bai taso ba sai nan da wata Shidda zai zo..!
Amina tace"Allah ya tsare..!
Aranta kuma Fadi take"Allah ya raka taki gona..!
Lallabawa tayi ta gudu gida abunta batama san Tafiyarsu ba su yaya dai da mamanmu sun je sun karayin musu sallama sai yamma suka Dawo suna Fadin wai har ya Jafar ya Kira suna kano basu dai tashi ba sai Dare.
Sai washegari wajen chan Rana taji ana Fadin sun sauka a jidda Daganan zasu hau Mota zuwa Madina ko ajikinta Sai taji kamar wani Nauyi ya tafi Bata ko kaunar ganinsa ma ballatana jin muryansa.

*******

Bayan wata Daya..!

Amina na kwance da Safe tana barci Taji ihun Hamida asaman kanta tana Dukanta Lokaci Daya tana Fadin"Amina tashi..Tashi.!
Next week zamu fara zuwa makaranta an gama mana komai..!
Amina da sauri ta Bude idanuwanta cike da barci tace"ke a ina kika ji..?
Hamida tace"Yanzu naji Ya Jafar yana Fadama Mamanmu..!
Amina tace"Ina zamu koma..?
Hamida tace"Ina kuwa..?Unity...?
karamin tsaki taja kafin ta gyara kwanciyarta Tana Fadin"Yanzu dai chan zamu koma..?nifa na Tsani Unity din nam..Allah yasa banda munafukar nan Sa"adatu..!
Hamida tace"Kema kin sani..Gabadayanmu ne..!
Amina ta Yamutsa Fuska kafin tace"Ban so ba..!
Naso kowa ya kama gabansa..Ke ni fa Wlh nafi son zaman gidan nan akan komawa Shegiyar Unity din nan..!
Hamida tace"Ke yanzu zaman bai isheki ba..?Tab ni Wlh na gaji..!
Amina tace"Da an bari Second Term sai mu fara zuwa..!
Hamida bata bi ta kanta ba ta Fice tana Murna Amina ta Bita da kallon Na Tsausaya.
Da yammah ma sai ga Hanne tazo suna Murna ita da Hamida Amina tun Tana Daukan mganar wasa sai gashi ta Tabbata an kawo musu sabbin kayan makaranta na Senior da Jaka da takalma Da Safa da Sabbin Littafai ya Shamsu yakawo musu nasu Ranar Monday zasu fara zuwa.
Kowa na Murna banda Amina Tsakani ga Allah Hutun bai isheta ba ta so sai Second Time su koma makaranta ammh Ina ba wanda zai bar su su zauna agida ana kallonsu Takaicinta Daya Sa"adatu bata kaunar su na Hada Hanya don bata da yarda zatayi ne kawai.
Har ya Zeenatu sai da ta mata mgana Tana Fadin"Ke Amina Hanne da Hamida na Murnan Jjc yan SS1 KE banga kina yi ba..!
Amina tace"Murnan me..?Unity ce fa..?Daman wata kayan gabas ne ba nan ba..Ni gabadaya makarantar ta isheni..!
Ya zeenatu tace"Kina da aiki..Tun Zamamin su ya Nasir Unity ta kyankyshesu ballatana ke Zuwan yau yau..Yarinya Unity Dolen kowa ne indai D'an nan gidan ne ko dan Gidan Baba Mallam ne..!
Amina baki ta Tura bata kara mgana ba Ganin yadda ya Zeenatu ta zakal kale,Tana ta bayani Hamida na Tayata su adole suna kara yabon Unity a wajenta Tabe baki tayi aranta tace ko Ta Tsani makarantar nan ba Sauyi kowa ban yayi ya gama suma kuma nan din zasu gama..!
Kullum ba cigaba haba don Allah.








*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*🅿️15*

*Jumma"a*
9:00am

Labulen Dakinmu Mamanmu ta daga tana kallon Amina Dake zaune Saman gadonta ta tasa kayan da mamanmu ta gama wanke mata jiya ko fara ninkesu batayi ba.
Hamida na Gefenta itama wajen Dirowarta tana shirya Littafanta Cikin Sabuwar Jakar makarantarta Mamanmu ta kalli Amina Data Zabga Tagumi kamar wacce akace mata nata ya rasu Cikin Lallami tace"Amina baki Fara Ninke kayan nan naki ba ko..?yi hakuri ki adanasu ina aiki ne da na Gyara miki..Kwashesu ki saka cikin Dirowarki in anjuma in nepa sun kawo Wuta Zan saka Hamida ta goge miki sai ki adana Kayanki..!
Hamida na jin haka ta Dago tana kallon Mamanmu kafin tace"Ni kuma Mamanmu..?
Tafada Tana Bata Fuska Mamanmu tace"Eh ke..Ko bazaki yi bane..?
Tunda ita haka Allah yayi ta bata da Zafin nama ku kuma yan"uwanta ne kun fita karsashi ba sai ku taimaka mata ba..?
Hamida bata iya mgana ba ta maida kanta Gefe Amina kuma sai Danne Dariyanta take yi kafin tace"Dama ta barshi mamanmu..!
Bata bi ta kansu ba ta saki Labulan ta koma tana Fita Amina ta Fara Dariya Har tana ma Hamida gwalo kallonta Tayi kafin ta girgiza kai tana Fadin"Kiyi Dariya son ranki..Lokacin ki ne ammh ki sani akwai watan watarana..Da babu mamanmu ba Hamida wlh sai kin raina kanki..!
Kamar ba mace ba komai sai dai ki zauna komai Mamanmu tayi miki ko kuma ta sa muyi miki..!
Tafada Cikin jin haushi Amina ta kara saka Dariya kafin tace"ko ba mamanmu ba gaki ba..?
Hamida ta Harareta kafin tace"Ni kuma sai bazan yi aure ba sai na koma kula Dake..?Sannu Amina yar gata..!
Amina tace"To miye..?Sai ki auri kanin Mijina..!
Karamin Tsaki Hamida taja Amina ta kara saka Dariya tana Fadin"Hamdiya..Hamdiya..Hamdiya..!
Take Fada cikin Sigar waka Da sai da Hamida tayi Dariya tana Fadin"Ke kika sani..Allah yasa ki shiga gidan mai mata Biyu kece na uku..Ya"ya kadai sun isheki Amina..!
Amina tace"jar uba..ya auran ma kansa dai..Mai mata Biyun daya kwashi Amina ai mai Budurwan Zuciya ne..Sai yayi Nadama Tijara ne da Jidali ne zai gani harda na Siyarwa..!
Take Fada tana Dariya Hamida na Tayata Daganan suka shiga Hirarsu Amina na tusa kaya cikin Dirowanta batare data Tsaya Ninkewa ba Hamida tace"Kai Amina mugunta ma harda karan kanki kike yi mawa..?
Amina ta tsaki kafin tace"Ki kyaleni Hamida ni nagaji..!
Hamida ta mike tana Fadin"Zaki ma mike ne yarinya yau ke kike da gyara mana Daki..!
Amina tace"Kan bala balagagge..Ranar fa ni na gyara..?
Hamida tace"Ai ba sau Daya ake gyaran Daki asati ba malama..!
Amina ta Tura baki kafin tace"To nidai na gaji bazam iya ba..!
Hamida ta bita da kallo batayi mgana ba Amina ta cigaba da Fadin"Mutum kamar jaki aiki aiki..Ni wlh nagaji..!
Hamida baki ta rike ta kasa mgana wai Amina na Mganar aiki me takeyi..?
Aiki sai ya zama Dole Amina ke yi in ba zama ba zamanta take Mamanmu na Daure mata wajen iskanci sanin da tayi bafa zata gyara Dakin ba yasa tamike ta fara gyarawa Amina na Mata Dariya sama sama tana jinta tayi mata banza kamar bata jita ba.
Har ta gama gyara Dakin bata gyara wajem kayan Amina ba ganin haka yasa tace"Hamida Kashi nayi miki akan gado da baki gyara barayina ba..?
Hamida tace"Bansani ba.!
Amina ta tabe baki kafin tace"Allah ya baki Hakuri Anty Hamidaaa..!
Ta karishe Fada tana mata gwalo karaf suka Hada ido Hamida tace"Don Allah nake yin komai ni..!
Amina tace"Allahu akbar..Allah ya Biya malama Hamdiya..!
Danne Dariyanta take yi kada Hamidan ta gani ta fasa gyara mata Sauran kayan ma Hamida ta gyara mata ta Ninke mata da kyau ta saka Cikin Wardrope din Amina ta kuma gyara mata gadon ita Amina Tuni ta shiga Tiolet din Dake Dakin zatayi wanka.
Koda ta fito har Hamida ta gama gyaran Dakin ta share ta goge ta saka Turaran Wuta Amina ta Hura hanci tana Fadin"Kai Allah yayi ma Hamida albarka..!
Komai yana son gyara ko"ina yayi kyau tas dashi,Zama tayi ta shafa mai ta saka wata Doguwar rigar Material tana cikin Daura bakin Dankwalin abaya ne Mamanmu ta kara Daga Labulan Dakin ta leko tana Fadin"Hamida zo don Allah..!
Gishiri ya yankemin ina girki..!
Amina ta Dago tana Fadin"Bata anan fa Mamanmu tana waje..!
Mamanmu tace"Ai ban ganta bane..?
Ta juya tana kiran"Hamida
Hamida...hamida..!
Yaya Dake Kofar Kitchen tana Taya Mamanmu gyaran wake tace"Hamida fa ta shiga makewayi..!
Mamanmu tace"Gishirin nan fa ya kare Yaya..Bansani ba ina Dago Buhu sai bakomai aciki..!
Yaya tace"Yafa Dade ya kusa shekara Tun Gishirin nan da Jafar ya hado cikin Wani siyayyan kayan abinci ne fa..!
Mamanmu tace"Gaskiya ya jima..Gashi Babansu ya fita ba kowa agidan..!
Yaya tace"Sai dai ki kirasa a waya,ki Fadamai ko kuma ki bada asiyo in ya Dawo sai ki samar dashi..in za"ayi Siyayyan kayan abincin wannan Watan kada a manta da gishirin..!
Mamanmu tace"Nayi tunanin haka bari Hamida ta fito ta leka shagon baya ta siyomin ta dawo da wuri kafin cikin yayinsu su ganta nasha Surutu..!
Yayaa tayi Dariya kafin tace"Aifa kinsan su masu yayyi ne..!
Mamanmu tace"Nasani ne Yaya..Yaran da ba"ason ko nan da chan sufita..!
Hamida wai ina ta shige ne..?
Yaya tace"Ki aika Amina mana..Tunda Hamidan bata fito ba..!
Mamanmu tace"Yauwa..Amina..Amina..!
Ta tafi tana kwala ma Amina Kira sai gashi sun hadu a bakin kofar Dakinsu Tana Fadin"Gani Mamanmu..!
Mamanmu ta kwanto kudi a Haban Zaninta ta mika ma Amina Dari Biyar Sabuwa tana Fadin"Maza sa Hijabin ki kije Shagon nan na baya ki amso min gishiri na Dora sanwa kuma na Duba ashe Gihirin ya kare yi maza Amina don Allah..!
Amina ta karbi kudin ta koma Daki ta Dauko Hijabin Hamida Data gani Saman gadonta ta fito flat din Takalminta ta saka baki tazo tana Fadin"Gishirin nawa Mamanmu..?
Tana gaban Famfo tace"Ki siyomin babban Jakan nan..Ki hadomin da Amo Amina wannan naga bazai kai an juma ba kuma shima shikenan jiya Zeenatu tace ta Dauko acikin Kwalin..!
Da Toh Amina ta amsa zata fice Yaya na Zaune kan kujeran yar Tsugunno ta Dago kanta tana Fadin"Saura kuma ki Dade..!
Juyowa tayi tana kallonta kafin tace"Ina zani to..!
Ta fada tana Tura baki Hararanta Yaya tayi kafin tace"Daman baki bace..Inda aka ijiyeki ba nan kike Tsayawa ba..!
Mamanmu tace"Amina kyale Yaya..Yi maza ki dwo yar albarka.
Da haka ta fice tana kunkuni afili tace"Yaya bata taba Fadin Alheri akaina..Yoni ina zani..!
Sai kuma Tayi Dariya sanin Halinta sai ta iya juya alaqanta zuwa gidansu Hanne ta ma manta da aiken Mamanmu karamin aikin Amina kenan.
Sakamakon Safe ne anguwan tayi shuru ba kowa maza sun tafi wajen aiki yara kuma duk suna makaramta Shagon yana ta bayansu kadam ne ba zuwa shago suke yi ba komai na Bukatar gida a kasuwa ake siyo shi,sai dai in wani abu ya yanke kamar irin rana mai kama ta yau
Bazata kirga Sau nawa tataba zuwa shagon ba kamar bai fi sau Biyu ba,Shagon babban Shago ne babu abunda baya saidawa mai shagon ba Dan garin bane bakano neyazo ya samu waje sai Allah ya saka ma kasuwancin nashi Albarka.
Samda ta shiga shagon akwai Layin mutum uku agabanta sai ta koma gefe sai da aka sallamesu sannan ta matsa kusa da katan Shagon ta mikamai kudin Hannunta Lokaci Daya tana Fadin"Bani gishiri babbar jaka da omo..!
Karban kudin yayi yana kallonta Ganin bai taba ganinta ba yasa yace"Wani irin Omo..?
Amina ta yamutsa fuska kafin tace"Kowani iri..!
Dauko mata yayi duka yana nemam ya Hadasu a leda Daya da Sauri tace"Tsaya tsaya..Mallama a ina kataba ganin an Hada gishiri da Omo waje Daya..?
Yana yar Dariya yace"Au na manta ne..Yi hakuri don Allah..!
Hararansa Amina tayi batayi mgana ba ya Raba kowannen Ledansa Dabam yana Fadin"Nace ba..A ina kike ne..?
Naga bantaba ganinki ba..!
Amina ta Tsaya tana kallonsa kafin ta saka Hannu ta warce ledan hannunsa tana Fadin"Ina ruwanka..?malam bani Chanjina na tafi..Tunda ba Sana"ar kake yi ba tambayan inda mutanen da suka zo siyayya shagonka suke kake yi..!
Tsiwanta ke bashi Dariya yanzu ma Dariya yayi kafin ya Hado mata Chanjinta ya bata Kamar zata Dakesa haka ta Fizge chanji kadan ya Rage ta Hada da hannunsa baki ya rike yana Fadin"Kai..Allah ya baki hakuri..!
Ko jinsa batayi ba tayi wucewarta Hankalinta na kan chanjin hannunta Tana Kirgawa shi kuma ya Sawo kansa Shagon Kansa na kasa yana Danna Wayarsa Daga bayansa kuma wani ne kebinsa yana Fadin"Oga da ka bari na amso maka..!

"Bazan iya da shiriritarka ba Nura..Na ri..!

Mganarsa ta makale ne sanda suka ci karoda juna kusan Tsawonsu Daya In maya fita da kadan ne yasa suka Daki Goshin juna Dayasa kudin hannunta da Ledan duka suka zube a kasa shidai Allah ya taimakesa wayarsa bata Fadi baya riketa Dakyau.
Amina ta saki karamin Tsaki ta Duka tana kwashe chanjinta da omon Daya Fado a leda Daga saman kanta taji anaa Fadin"Baiwar Allah ki rika Tafiya kina kallon gabanki ok..?
Sai da ta gama kwashe komai kana ta Dago suka Hada ido Hudu dashi Kallonta yake yi da Fararan Idanuwansa kamar yadda ta sakarmai nataa manyan Idanuwan Cikin kallon kama Raina ni tace"Dakata mallam..Ni dakai waye baya kallon gabansa..?
Ni fita zan yi kai kuma zaka shigo acikin ni dakai wazai kalli gabansa..?
Ta karishe Fada tana Hararansa Harda Murguda baki kafin ta Raba ta gefensa zata wuce.
Cikin Wata sanyayyar Murya mai Cike da yanga taji tace"Ya zaki tafi..?,Alhalin baki bani hakurin Laifin da kikamin ba..?
Juyowa Amina tayi tana kara kallonsa kafin ta Nuna kanta tana Fadin"Ni..?
Kai ya gyada mata cikin yanga Lokaci Daya yana Jaye Hulan kansa Facing cap Kyakyawan Farar Fuskarsa ta bayyana.
Amina tace"ai ban yi maka wani Laifi ba ballatana na baka Hakuri..Kumani Amina ban cika bada Hakuri a laifin da ban aikata ba wani Lokacin ma ko nice bani da gaskiya bana Laushi da wuri..!
Ta saman Lebenshi yace"AMINA...!
Nice name..!
Kin fada min sunanki batare da na sha Wahala ba..!
Amina ta Tsaya sake da baki tana kallonsa Wabda ke gefensa ne yace"Oga..!
Bai bari ya karisa ba ya Laluba aljihunsa ya Dauko Walet dinsa ya Mikamai yana Fadin"Kayi abunda ya kamata Nura...!
Karba yayi yana kallon Ogan nasa Daya Fara susucewa ganin wannan Kwailar yarinya to kwaila mana wannan ta wuce sha Biyar tsawon kafa ne kawai Kafada ya Daga kafin ya Nufi Cikin shagon Dutse zasu koma yanzu nan Kati ya yanke ma Ogansa acikin waya suka Tsaya su siya to lokacin ankirasa a waya ya Dauka sai Ya kasa jira ya fito da kansa zuwa Cikin Shagon..!
Amina bata kara mgana ba ta fara tafiya da Hamzari ya sha gabanta yana gyara zaman Jaket din Dake Jikinsa Cikin Mamaki da Budewar ido Amina tace"Malam lafiya?Mtsamin Daga Hanya tunda bata gidan ku bace..!
Mirmishi yayi har sai da Fararam Hakoransa suka bayyana Cikin Muryansa yace"Wani ya taba Fada miki kina Burgesa..?
Yafada yana kallonta Cikin wani Salo Sai kuma taji mganar ta shigeta Cikin Sausasauta Murya tace"Ni AMINA ba wanda ya taba cewa ina Burgesa..Ni ai bana Burgewa kowa.!
Wayarsa ya saka Cikim Aljihun Jaket dinsa Lokaci Daya yana Fadin"To yau Ni AMINU BUBA nace kina Burgeni...!
Ido Amina ta zaro tana kallonsa mganar ta shigeta kanta ta kara nunawa kafim tace"Da gaske ina Burgeka..?
Kai ya gyada mata Sai ta washe bakinta kafin tace"Nagode..yau na fara ganinka ammh naji Dadin Haduwa Dakai domin kai ne Mutum na Farko Daya fara cewa Amina Aminene na Burgesa bazan manta da wannan ba..Thank you..!
Tafada tana Juya idanuwanta cikin bayanna Farimcikinta Shagala da kallonta yayi baisan ya Furta"She is Beautifull...!
Bai an kara ba yaga tana Shirin Tafiya da Sauri yace"Ya zaki tafi kuma ki barni..?
Da mamaki Amina tace"Bangane ba..?
Mirmishi yayi kafin yace"Ke yar nan garin ce..?
Da kai ta amsa mai cikin mamakinta da kuma kara ganin yarintarta yace"Ammh baki sanni ba..?
Amina tajuya ido kafin tace"To a ina zan san ka bawan Allah..?
Da sauri yace"Sunana Aminu..Aminu Buba..!
Nayi matukar mamaki da baki sanni ba Shekararki nawa ne..?
Amina tace"Shekarata goma sha Biyar da Wata Goma saura wata biyu na cika Sha shidda..!
Tafada tana Kirgamau da hannu Dariya ta kamasa har sai da Wushiryansa ta bayyana.
Tsayawa tayi tana kallonsa yadda yake Dariya abun sha"awa.
Cikin Matse Dariyansa yace"Amina..Amina kina Burgeni..!
Zan so na rika ganinki koda yaushe ko domin ki rika sakani Nishadi Aji nawa kike a makaranta..?
Kunya Amina taji yasa ta sunkuyar Dakai kafin tace"SS1 sai monday ammh zamu fara zuwa..!
Yana mata Dariya yace"Kice Jjc ne...!
Amina yan matan SS1..!
YAadda yake Dariyan ne ya fara Kular da ita yasa ta Hade ranta Nura Daya Fito Daga shagon tun dazu ya gaji da ganin wannan Drmar yayi gyaran Murya yana Fadin"Oga lokaci fa na Tafiya....!
Hannu ya Dagamai kafin ya fiddo da wayarsa yana mikama Amina Lokaci Daya yace"Sakamin Lambarki..Amina ai daman Amina kawar Aminu ce ko..?
Yafada yana Dariya itama Dariyan Tayi Domin Farat Daya taji ya burgeta kamar yadda yace itama ta Burgesa.
Noke Hannu tayi kafin tace"Ni ai bani da waya..!
Ido ya zaro kafin yace"Duk girmanki Amina saura fa wata Biyu ki kai shekara goma sha Shidda!
Ya karishe Fada Cikin Zolaya Da sauri Ta kauda kai tana Mirmishi Kara Tura mata wayar yayi yana Fadin"Ko lambar Antynmu Babu Amina..?
Amina tace"Tab..Bafa mai waya agidanmu Daga yaya sai mamanmu to ta yaya ma Jawaad ya jefata ruwa
Ta mamanmu ce kadai ta rage sai kuma ta Aba..!
Da sauri yace"To sakamin ta mamanmu ko ta Aba din..!
Ido ta zaro kafin tace"Tabdijam..Rufamin asiri ba ruwana kaga mallam bansan ka ba sai anjuma..!
Kafin yayi mgana ta wuce da Sauri harda gudu Kiran sunanta yake yana Amina..Amina ita ko Waige batayi ba sai dai ta kule ya Daina ganinta sannan ya Dafe kansa.
Nura ya kariso yana Fadin"Oga Oscar na Kira na fa kuma nasan kai yake nema..Sannan ka koma mota kafin mutane su farga Dakai..!

Lokaci Daya yana mikamai katin Daya siyo Airtel na 1k Mtn ma haka bai tsayama karba ba ya wuce Ya bude gaban wata Farar Bugatti ya shiga yana Fadin"Nura bana son mita..Kyale Oscar tukani muje kawai..!
Kai ya girgiza yana mamakin Yar yarinya karama Oga ya zauna yana bata Lokaci a kanta kafin ya Zagaya ya shiga Mazaunin Direba ya Tada Motar sukar bar Layin da gudu kamar zasu tashi Sama.

Koda Amina ta koma gida sai da Mamanmu tace"Amina ina kika Tsaya..?
Amina tace"Mamanmu chanji ne Babu..!
Da wannan karyan ta Kashe mganar Duk Surutunta ta kasa bama ko Hamida Labarin Haduwarta da Aminu buba kamar yadda yace sunansa Ranar duk in ta Tuna sai tayi Mirmishi ita kadai a kallah yau ita Amina ta samu wanda yace komai nata na Burgesa ashe itama Macece kamar kowa wannan yabon ya xauna aranta da Har Abada bazai fita ba.
Ko washegari a hadda bata yarda ta Fadama ko Hanne da bata boye mata komai ta kasa bata Labarin Haduwarta da Farin mutanin da ya kasa barin Ranta Ko yaya ta Tuna dashi sai ta murmursa acikin Ranta.
Da suka tashi Sallah ne Amina ta kalli Hanne suna wajen alwala Tace"Hanne ashe nima ina Burge mutane..?
Hanne na kuskure baki sai da ta Furzan da ruwan bakinta kafin su hada ido da Hamida suka kwashe mata da Dariya Duka Amina ta Dirkama Hanne a baya tana Fadin"Bana son iskanci ban tambayi Hamida ba sanin Halinta yar bakin ciki ce.!
Hanne na Dafe inda ta Daketa tana Fadin"Muguwa..Uban wa zaki Burge..?
Hamida ta Karbe da cewa"Sai dai ki Gunduri mutane Jidalinki Amina wlh bamai iya Daukansa sai mu da muka Saba..!
Hanne tace"Wlh wani waje duka zataci in taje tayi..!
Dariya suke ta mata ita kuma bata su take ba Hankalinta ya tafi Tana Jin Muryan Aminu sanda yake Fadamata Tana Burgesa ita din abar Burgewa..!
Daga Ranar bata kara musu mganar ba sai dai yana Ranta Lokaci bayan Lokaci yana Fado mata acikin Ranta.
Har tazo Ranar Monday suka fara zuwa makaranta Sun samu Dalibai irin su da suka Cigaba da Unity sannan akwai Sabbin Dauka kamar yadda aka saba Amina ta cigaba da abunda ta saba sai ma abunda yayi gaba ta addabi Dalibai da malamai Sai kuma akayi Rashin Sa"a aka hadasu aji Daya da Sa"adatu Hanne da Hamida Ajinsu Daya.
Amina kamar ta mutu saboda Bakimciki tace ma Hanne"Naso aji Daya aka hadamu hanne..Sai dai ban da Sa"a anhadani da Shegiyar Sa"adatun nan..!
Hanne tace"Ina Ruwanki da ita..?
Amina tace"Ta shiga Harkata Dakuwa zatayi..!
Sa"adatun bata shiga Harkan Amina Saboda Anty Amarya taja kunnenta Sosai kan Amina shiyasa ko Aminar Zata takaleta bata bi ta kanta.
An hadasu Aji Daya da Zainab Isa Kawar Amina sai suka Kulle atare Sit dinsu Daya Dalili kuma tana Aro mata Littafan Hausa na kishiyar mamanta take Sato musu ta kawo makaranta su karanta ita Zainab Amina take kawo mawa,ita sai agida ta ke shigewa Dakinsu ta Boye ta karanta sannan bayan su Hanne Zainab isa ta jure Gwagwarmayan Amina da Jidalinta.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah su Amina sun mika cikin Zangon karatunsu na Farko a SS1 dinsu cikin salama da kwamciyar Hankali kamar Amina tayi sanyi Saboda ta Rage Tonon Fada sai dai jidalinta da Masifarta sai abunda yayi gaba Dakyar Hajiya ta rokar musu Baba Mallam ya bari Idi Direba yakai su gidan ya Ikram Dukkansu har da su ya Abida su Amina an sha Murna har Fada sai da taja su hanne suka shiga da karambaninta.
Abida tace"Kai amina bala"i wlh watarana sai takai kanta inda zata mutu..!
Ya Ikram tace ko ita sai da mijinta take shiga Gidan Sarki batama san Hanya ba sai ga Amina tana kutsa kanta Kusfa kusfa,Chan suka mata wuni sai yammah suka dawo suna Santin Haduwar gidan kamar aturai Amina tace"gaskiya gida biyu suka tabamin kyau..Daga gidan ya Danmallam sai gidan ya ikram..!
Hamida tace"Gaskiya gidansa shima ya Hadu tsarin daidai kamar aturai..!
Haka dai sukayi ta santin gidan Har Mamanmu na saka baki tana basu Labarin Tsaruwan gidan Sadiya Dake Dutse Amina tabe baki tayi batayi mgana ba sai da Hamida tace"Kai zan so naje ngani mamanmu..!
Yaya na gefe tace"Naji kamar ance cikin watan man zata bi mijin chan kasar Dayake aiki..!
Mamanmu tace"Nima haka naji Haj.Nasara na tadin ita da Haj.Uwa..!
Amina tace"Ni kam ban sha"awar zuwa..Nasan bazai kai yadda nake Hasaahe tsaruwa ba..Shiyasa naga yau Sa"adatu nata wani yamutsa Fuska araina nace an ga inda aka fi su..!
Hamida tace"Kai Amina baki son zaman lafiya..?
Balla mata Harara tayi kafin tace"Eh din ke kuma an tabo masoyiyarki..!
Ganin zasu fara fadan nasu ne mamanmu ta Tsawarta Ya Zeenatu na Gefen Yaya tace"ZAman lafiya ko na Minti Daya ne Amina bata kaunarsa..!
Amina na jinta ta Daga kanta sama aranta tana Fadin"Eh din..!
Nan dai mganar tatashi ta koma Tsakanin su Mamammu da su Hamida Amina bata kara saka baki ba Kada tata ta karayin zafi.
Ana cikin haka acikin Satin Matar ya Jafar ta Haihu Anty Shamsiya.
Su Amina Sai ana

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment