Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun dazu baki Daga Kirana ba..!

Tunda ta fara mgana wannan kamilar Fuska mai cike da Annuri da Tsausayi ta rine ta koma Bakar fuska mai Cike da mugunta da rashin Imani Cikin Wata Murya mai cike da Amon Takaici da Bakinciki tace"Da sanina Bazan bari haka ta faru ba Madina..!
Wlh ban sani ba..Kamar yadda kikaji abun Daga sama nima haka najisa..Shammatan mu Mallam yayi..Shammata mai girman da bamu Taba Tsammani ba Madina..!
Dagachan bangaran Agidan Baba Mallam ashashen Anty Amarya itama Cikin Tsakiyar Bedroom dinta tana Tsaye gaban makeken madubin Dakin nata tana kallon Fuskarta Data wani yarkace na Wunin yau kawai tun bayan Samun Labarin Daurin auran Amina da Umar..!

Cikin Muryanta mai Fadi da ba kowa ya santa da ita ba tace'"Lalle ko ya shammaceni Dayyaba..Sai da na Riga na gama Tsara komai..na gama Tunanin matsala tadaina shigomana cikin Aikinmu ashe suna chan suna Shirya ganina akasa..To basu isa ba..In a zaune suka kwana Ni Madina a tafe na kwana nayi alkawarin yadda bansamu Mallam ba ta bangaran Sakina Da Umar sai na Juya ragamar Mallam da duka abunda ya mallaka..Karya ne..Bayan sakina ba wacce ta isa Umar ya sota har ya Hada Jini da ita Sakina kadai keda Alhakin Haihuwa da Umar ita kadai ce Zata Haifama Mallam Yunus Bazanga Jika,Abaya nayi Sakacin da Har Ya"ya Biyu suka fara Fitowa daga Tsatson Nazir nayi sakaci Dayyaba..Sai dai kinsan aikin da mukayi ya"yan Nazir baza su taba Tasiri a wajen Mallam ba..Kacokan Burina na wajen Abunda Sakina zata Haifane..Sai da nace miki Mu kauda yarinyar nan Dayyaba kika ki bani goyon baya ta rasto cikin Aikin mu batare da Mun gayyaceta ba gashi nan yau Rana Daya ta Fadomin cikin Tsarina Tsarin da bazan taba bari ya Rushe ba Koda hakan na Nufin za"a rasa rai ne..Na kasa gane miki ko kin fara Sauya Ra"ayi ne na Sauya Duka Tsarina Dake..Kila kin hakura da Abunda Sa"idu yayi shekaru yana Kunsamiki ne shi da wannan Munafukar matar tasa..Ko kuma kin shagala kin Fara Kaunar wannan Hatsabibiyar yarinya Dake nemam batamin Shirina..!

Fuskar MAMANMU nake gani ta koma Jawur idanuwanta sun kala sun sauya Launi jijiyoyin kanta har sun Daga Saboda Bala"i cikin wata gigitaciyar Tsawa tace"Dakata Madina..!
Har Abada ni Dayyaba bazan manta Da Bakimcikin da Sa"idu shi da Hadiza suka Dade suna kunsamin ba..Wannan Kaunar wannan Tsausayin da Soyayyar da nake gani acikin Idanuwan Sa"idu kan Hadiza saura kadan su kaini kushewata Har Gaban Abada bazan yafe musu wannan ba..Sai sun Dandanan gudarsu bana yafiya.. ni din nafi Rama Sharri da Alheri..kamarni Sa"idu zai kallah gaban Ya"yana da Matarsa ya SAKENI madina kan wannan Shegiyar yar tasu..?Yarinyar da duk cikin ya"yan Hadiza nafi Tsananta saboda iyayanta sun fi sonta..Sa"idu ya Dade yana kunsamin Bakinciki ya fifita soyayyar Hadiza Fiye da tawa sannan yazo ya fifita ya"yan Hadiza Fiye da ya"yana Saboda Ban Haifi namiji ba ko..?akoda yaushe in na Bude ido na ga Jafar sai naji kamar na kashe kaina..Meyasa na barsa araye ban saka malamin mu ya Kashesa ba..Da yanzu ba haka ba Madina Da yanzu na Dade da kunsa ma Sa"idu da Hadiza bakin cikin da Har su koma ga Allah bazasu manta ba..Duk Saboda Cikar Burina na aro Fuskar da ba tawa ba Madina..Ina zaune cikin wadanda nafi Tsana ina Fifita ya"yam makiyiyata Fiye da ya"yana ina Faman kare ma wanchan yarinyar da bata da wani amfani a wajena...Madina Dukkanmu mafita muke nema saboda haka koma menene ki Fadeshi zan yarda zan amince zuciyata zafi take madina Amsa kuwar Sa"idu nake ji yana Fadamin ya Sake ni Saboda wannan Shegiyar yarinyar ina so suma su Dandana ina so suji yadda na daukii shekaru ina ji acikin raina..!

Anty Amarya tayi Mirmishin Dayafi kuka ciwo kafin tace"Sakacin ki ne Dayyaba..Tun Lokacin da aikin malam ya Tsallake Jafaru ya koma kan Amina nace a kaudashi kika yi yarda..Da yau baya Raye Da wane d'a Sa"iidu zai yi takama..?yau gashi dan Zaki ya Girma harda albarka Haihuwan wani karamin Zakin Dayyaba anya ke naki Tsarin ba Doguwar Tafiya bace..?
Da Sauri Mamanmu tace"Bana kallonshi a Faduwa Madina..Jafar da Abunda ya Haifa ba su da wani amfani kadan nake jira na karar da su..Yanzu ni Sa"idu zan fara mgani Tukunnah so nake naga bakimciki da Rauni acikin Idanuwansa Madina..!

Kai Tsaye Anty Amarya tace"Za"a rasa rai...YAYA ZATA MUTU...!

Mamanmu tace"TABBAS YA KAMATA TA MUTU..sai dai naso sai ta gama shakan bakincikin da na Dade ina Tanadama mata madina..!
Anty Amarya tace"Yanzu Lokacin Daya kamata ta Mutu ne Dayyaba..Mutuwar ta ne kadai zai sa kiga wannan Bakincikim acikin Idanuwan Sa"idu..Mutuwarta ne zai sai nima naga Sa"idu ya koma abun Tsausayi ya dade yana min katsalanda Shi da Hajiya Babba..Zamu fara ta kansa ne kafin mu dawo ta kanta da Saninsa aka Aurama Umar Amina..Da saninsa ta shigo Tsarina nima wannan Damar nake jira da Zan Dandana ma Sa'idu koda Rabin abunda nakeji ne game dashi..Komai na ke kokarin samu Shi da Hajiya babba sai sun tare ni Dayyaba..!
Cikin wata irin Dariya tace"TABBAS yakamata ta Mutu...!
Zata mutu..!
Anty Amarya tace"Zan kira mallamin mu Dayyaba zan sanar dashi ya yanke mata wa"adinta kafin wayewar gari bazan jira ba..bana son wannan karon asamu matsala..!
Mamanmu tace"Nima haka..Wayewar garin gobe Ranar mu ce..Na kosa na kosa naga wannan bakimciki akallon da zan ma Sa"idu..Babban kuskuransa shine ya Fifita komai na Hadiza akaina..Babban Raunina Ina SON SA'IDU..!
Anty Amarya tace"Shikenan kada ki damu ki Dauka an gama..Mganar kudi akwai wani abu a hannunki..?
Mamanmu tace"ki kamallah komai in mun hadu zamu warware komai..!
Anty Amarya tace"Shikenan..Mganar yarinyar nan baki ce wani Tsari zan kaita ba..?
Mamanmu ta saki Dariyan Nishadi kafin tace"Ban damu ba Madina..Ni Kaina na sani Dagani sai ya"yana..Ki kaita Duk Tsarin da kika ga Dama..Koda Tsarin na MUTUWA NE..!
Anty Amarya tace"Tsarin bana Mutuwa bane..Zata sha wahala ne kawai sai daga baya mu kaudata..Tsarin da na kai Balarabiyar nan Tsarin zan kaita Dayyaba..Hotuna zasu zama wajen Umar har Abada Sakina ce Zata Cigaba da amsa matsayin mata awajensa..Wannan alkawarin ne..!

Mamanmu ta jinjina kai tana Fadin"Hakan yayi daidai..Daga gobe komai ya Dawo hannuna..Daga Sa"idun har ya"yan nasa..basu san Wacece Dayyaba ba..Balaraba Ita suka sani..!
Dukkamsu Dariyan suka sheke da ita Dariyan cin nasara da samun Duniya lokaci daya suna yanke kiran atare..!
Abunda basu sani ba wani abun Allah ya Riga ya kaddaran Faruwansa bakin Alkalami ya Riga ya Bushe..!
Tabbas za"a rasa rai..Sai dai basu isa su Dauki ran wani ba..Daman chan ita ran Lokacinta yayi ne..!
Suna gama wayar ta Wurgar da wayar saman gado ta fara Zagaya Dakinta Cikin kaushin murya take fadin"Allah Sarki Yaya..Yau za"a amsa kiran Allah..!
Wayyo wayyo..!
Haka take ta fadi sai kuma ta kece da Dariya kamar mahaukaciya kafin ta koma ta Duke kuma sai ta saki kuka Lokaci Daya tana Fadin"Ba haka naso na zama ba..Sa"idu kai ne sila..Na soka Tun kafin ka fara son Hadiza..Me na rasa baka taba sona ba..?Kasha bansan auran biyayya kayi dani ba..?
Kasha bansan ka Tattara Zuciyarka ka bama Hdiaza ba..Wannan son shi ya ja maka kai da ita..Wannan Tsausayin shi zai kasheta Sa"idu..Ba Laifina bane..Laifin SOYAYYARKA CE..Bantaba son wani Namiji yadda na SOKA BA
Koda bazaka soni ba nayi alkawarin baka isa ka so wani ba..Komai na ya"yanta ya zarce nawa..Duk yadda naso hakan bata Faru ba sai da na zama koma baya agidanka..Kasha bansani bane.?bakayi karya ba nasan Amina ta fara soyayya da wani..bakayi karya ba..Nasani naki fadamaka Saboda Daman ina son damar da zata kara Ruguza rayuwar Hadiza..ban so abunda ya faru ya Tsaya nan ba na so ne Tayi Cikin shege na Tsawartsaku gabadaya..ba Laifina bane..Yaya ki yafemin Sa"idu ya ja miki MUTUWA..!

Take fada tana Hawaye Lokaci Daya Dadariya tana Tuna ranar data fara kama Amina tana waya da Aminu acikin bayinta bata nuna ta ganta ba..Hakan ya mata Dadi Domin bata kaunar cigaba Daga bangaran Hadiza ita da ya"yanta Tundaga Lokacin Da gangan take ijiye wayarta Har Aminan take samun Daman Dauka ta kuma fara Bibiyan Motsinta abunda kowa baisani ba Hatta Haduwar da take yi dashi duk tana sane..Taso ta shirya wani abu ne..Taso ta yi amfani da Amina ta Tsarwatsa Yaya da ahalinta sai dai Mallam ya shammesu matuka shammatam da basu taba Tsammani ba..!
Abunda bata sani ba..Ba Mallam bane Allah ne ya Rubuta abunda ya Faru Daki Daki..Su basu isa su Hana Al"amarin Allah ya Faru ba..Zanen kaddaran ya zama kuma bawa bai isa ya goge shi ba..!

Achan asibiti kuwa bayan fitan su ya Jafar Baba mallam bai kara cema Aba komai ba sai shine da kunya ta kamaasa yace"Nagode Baba..Allah ya kara Girma..Naji zabin da kayi ma Amina badomin kada nayi sonkai fa sai nace nafi kowa Murna da hakan..!
Baba Mallam ya yi mirmishi cikin wani yanayi yace"Sai da ga baya naga kamar nayi gaggawa Sa"idu.Abunda kuka zata ba haka bane..Jikina yayi sanyi naji kamar na so kaina nima dana aurama uwata Umaru a karancin Shekarunta na yarinta..Da ace na sani da na jira..Kadan da na aura mata wanda ke sonta Tsakani ga Allah ya kuma dace da ita..!
Yafada yana jin Tsausayin Aminu na kamasa yana Tuna yadda iyayansa suka nuna jimamin Lamarin bayan sun gayama mallan duk abunda Aminu ya fadamusu kan Amina ce ta Dakatar dashi na bayyana kansa sun yi sallama Cikin wani yanayi ya Rakosu har waje suka iske Aminu Cikin wani yanayi wanda Dole bawa ya Tsausaya masa..!
Baba Mallam yaji Dama ace ya Jirakadan..Da duk haka bata Faru ba..Sai da ga baya yaga kamar yayi gaggawa..Da ace Nazeem ya aura mata..sai daga baya yace dama Nasir ne..Umar yayi ma Amina girma Tazaran Dake Tsakaninsu kamar tazaran kasa da sama ne..!
Yaji da ace Aminu zai karbi Tayinsa Daya Aura masa Hanne ko Hamida Domin ya wanke kansa Daga wannan zargin sai dai ina Agaban idonsa suka sakashi a mota cikin wani yanayi suka Dauki Hanyar Yola..!
Shi kanshi Aba jikinsa yayi sanyi da bayanin Baba Mallam tun ma Daya bude baki yana fadamai abunda ya Faru bayan zuwansu Aminu..!
Dukkansu shuru sukayi sun kasa mgana sai chan Aba yace"Baba Komai fa Da kaga ya faru yau..tsarin Allah ne..Mu yi fatan wannan Auran ya zama Sillar warwarewan duka abubuwansu Allah ya amintar da zuciyoyinsu waje daya..!
Da Amen Baba Mallam ya amsa abunda basu sani ba sun yi addu"an akan gaba ammh Allah ya Riga ya amintar da Ruhin Amina da Umar waje Daya Alkaalamin kaddaransu ya Riga ya Bushe!
Sun dade suna kara Tattaunawa sai da Shamsu yazo shi da zai kwana da Aba ranar sannan Baba Mallam yayi mai Sallama ya koma gida Cikin Damuwa da Tunanin yayi gaggawa..!
Abunda ya Dade bai Faru ba yau ya Faru Baba Mallam bai isa shashensa ba kai Tsaye shashen Hajiya Babba ya Sauka kuma aidon matansa duk da Ba ita ke dashi ba Hajiya Nasara ne..!
Yana cikin Damuwar da ita kadai zata iya kwantar da mai hankali.
Haka yaje mata yana Fadin"Zainabu anya banyi gaggawa ba..?
Ina ji kamar na zalunci uwata..!
Hajiya bata Fahimci mganarsa ba sai da ya warware mata na zuwan iyayan Aminu ya karishe da Fadin"Meyasa na Zabi Umaru..?Meyasa ban zabi Nazeem ko Nasir ba..?Uwata tayi kankanta Umaru ba Tsaranta bane..ba zata iya zama cikin mata Biyu ba Hajiya..Nayi gaggawa..!
Yake fada lokaci Daya yana Cire rawanin kansa..!
Hajiya taji jikinta yayi sanyi itama Sai kawai ta Riko Kafadan Mallam tana maimaita Hasbunallahi cikin ikon Allah shima ya shiga amsa mata har ya samu natsuwa zaunar dashi tayi kan gado taje ta Debo masa ruwa mai Sanyi yasha yayi hamdala sannan ta kallesa tace"Bakayi gaggawa ba mallam...Daman chan Amina bata da miji sai Danmallam..Ba Tsarinka bane naa Allah ne..Ina ji ajikina wannan aueran Alheri ne zamu ji Dadinsa Watarana..shi kuma yaron Allah ya basa wacce ta fi Amina haka Allah yaso..!
Kalamanta sun kwantar mai da Hankali Cikin natsuwar daya samu yace"Ameen ya Allah zainabu Abu mai Tawagayen suna..Bani abinci in ci inji dadin saka miki albarka..!
Dariya kawai tayi tana Ficewa Daga Dakin ya Bita da kallo aransa yana Tunanin Har Abada bazai taba samun macen kwarai irin zainabu ba..!

Sai da ta dawo da farantin abinci ta Sauke agabansa sannan tace"Muna da bakuwa fa..?
Yana Saukowa saman Cafet din Daya malale Dakin yace"Bakuwa kuma..?
Tana kokarin zama gefensa tace"Eh Hajiya BATULA ce kanwar Uwani Tazo Dazu da yammah nan daga Tsafe..!
Bai ce komai ba illah kai daya gyada ita kuma sai ta fara kokarin zubamai Tuwon shinkafa miyar ogun din da akayi..!

*******
2:30pm na Dare..!

Acikin Tsakiyar Falon Hajiya Uwani Zaune suke ita da yar"uwanta kwara Daya da suka fito ciki Daya su ka kuma Taso acikin jerin ya"yan da Alhaji hamza mahaifinsu ya Haifa..!
Tayi aure mijinta ya rasu da Dadewa sai dai bata taba Haihuwa ba..Kuma tundaga Lokacin bata sake aure ba kasuwanci take yi..!
Haj.uwani Dakin da Umaimatu ke ciki ta kallah kafin ta sauke numfsshi Lokaci Daya tana Fadin"Anya Batula kina ganin ba Zunubaina ke shafan Umai ba..?
Duba kiga irin wahalar da mukeyi akanta har yanzu taki Lafiya Sa"o"inta duka Mallam ya aurar dasu ita ba Boko ba ba aure ba gani cikin kishiyoyi bana so aga gazawata..!
Wacce aka kira da Batula ta gyara zama suna kama da Hajiya uwani sosai..!
Cikin Yar dariya tace"Bai kamata ki karaya ba tun yanzu Uwani..Matsalan Umaima Daga Allah ne kin sani duk inda mukaje haka ake fadamana..Na Fada miki zata samu lafiya..Yanzu dai mu ijiye mganar Umaima agefe mu yi wacce Itace Dalilin zuwana..!
Haj.uwani ta gyara zama tana Fadin"Uhmm..Acikin Abunda muke so mu kauda Batula wani abun yazo ya kara shan gabanmu..Yakin ba yanzu zai kare ba Batula..Mallam yau da azahar ya Daurama Umar aure da Diyar Sa"idu Amina..!
Batula ta zari ido kafin tace"Aure kuma..?
Haj.Uwani tayi dariya takaichi kafin tace"Eh ba wanda ya sani sai da aka Daura mukaji..Kuma bai yimana bayani ba..Kina gani yazo ya shige shashen giwa bai nemi kowa ba..!
Batula ta karkace kai kafin tace"Shine yasa kika Tadoni tundaga Tsafe zuwa Gumel Uwani..?
Kai ta gyada mata karamin Tsaki taja kafin tace"Da kin fadamin tun awaya wlh da ban zo ba
Wannan ai karamin aiki ne..Me zai gagaremu Yarinyar wai me take takama dashi data baki tsoro..?
Haj.uwani tace"Ba komai yarinya ce karama Sa"ar Sadautun Amarya..Yanzu suke SS1 MA..!
Batula ta karaa sakin Tsaki kafin tace"Abu mai sauki..Ai tunda muka iya kai Sakina kasa kowa ma ta auri Umar sai mun kaita kasa..Hajiya babba ta samu Mallam da duka komai nasa to ta bar shi haka bata isa ta bangaran ya"ya kuma ta miki Zarra ba..Kada ki manta mu mukasa akayimana aiki kan manyan ya"yansa da sukaki zama kusa da Hajiyan da Mallam din mu ka Tura kurciyan Umar Madina yadda bazai ji sha"awan Dawowa gida ba kuma muka Tura Kurciyan Nazir Lagos yadda Har Abada zai iya zaman Gumel ba..Abu kadan ya ragemana Nazeem da Uzairu su gama karatu su Dawo gida Lokacin sai mu maida Sa"idu mara amfani alokacin Mallam bai da wata mafita sai ta ya"yanki sune Jagora Uwani!
Haj.Uwani Ta saki kayattacen Mirmishi tace"Kin manta baki Tunanin Jikokin ya"ya na ne kadai Mallam zai kallah yaji Dadi ba..Tunda Mama ta fadamana Mallam yana matukaar son ganin kwam Umar aduniya na Mike Tsaye,Duk Shigen Shigen Marliya sai da nasha gabanta Bata sani ba ko gobe Sakina ta samu Ciki sai ya Lalace Mama ta tabbatarmin Umar haka zai zo ya koma bazai taba ganin kwamsa aduniya ba..!
Batula tayi dariya kafin tace"Wai itama balarabiyar madina din kin gama mata aikin..?
Haj.Uwani tace"Tun yaushe..Tare suka sha mganin Mama cikin Ruwan Tea din da suka tako har Fadona na Hada musu sun koma ba Dadewa..Sakinar tayi bari har Umarun yaxo karban mata mgani da Marliya ta karbi mata na Hausa..Araina nace kyayi ki gama..Wannan gidan na Uwani ne da ya"yaanta..!
Atare suka saka Dariya kafin Batula tace"To wani mataki zamu Dora sabuwar zuwan namu..?
Haj uwani tace"Tsarin da na Dora na gabanta zan dorata..Duk da nasan ma Umar b abunda zai ci da wannan mara kunyar yarinyar sai dai kinsan Namiji baka rainasa..Awajena bata da wani amfani kamar yadda na Maida yaron nan NASIR mara amfani a wajen Mallam in ba ya gansa bama mantawa yake yi dashi..!
Wata Dariya suka saka har da Tafawa kafin Batula tace"Don Mallam din da Giwar suna Tsaye ne..Ai da tuni burin mu ya cika..!
Haj.uwani tace"Abu daya na kasa..Kai Maallam kasa shi da Hajiya..Mama tace har Abada bazan ci galaba akansu ba sai dai kan yaran
Basa wasa da ibada sannan azkar kamar ya zama jikinsu in ba ikon Allah ba Sihiri bazai taba kamasu ba..!
Batula tace"Shiyasa nace ki bar asaran kudinki..Mu koma inda Mama tace sai muga riba..!
Haj.Uwani ta saki kayayyatacen Mirmishi kafin ta koma ta kishingida kan kujera Lokaci daya tana Fadin"Aikuwa naga Riba Batula...!

Ashe ashe basu sani ba..Suna Tufka ne..Daga gefe wata Boyayiyar Fuskar tana Faman warwara..!







*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*



*🅿️23*

Rai bakon Duniya..!
Misalin karfe 7:00am..!

Gabadaya gidan Baba Sa"idu haka suka tashi zuciya ba sukuni,Wasu sun samu barci da yar natsuwa ammh akwai wadanda basu runtsa ba ciki har da Amina domin yadda taga Rana haka taga Dare ita ba kuka take ba Domin zuciyarta ta kekashe bata ma jin yin kukan abu daya ta sani bata son tuna inda kaddaranta ta jata ta kaita domin in tana tuna yau ita ta haramta ga Aminu sai taji gabadaya Duniyar na juya mata,Abu daya yake mata nauyi acikin kirjinta Aminu shi take so ta san wani hali yake ciki ammh babu dama sannan sai Aba da Yaya wanda bata taba tsammamin Fushinsu zai dameta ba abu daya ke damunta Shedar iskanci da suka Zargeta dashi sauran bata damu ba Domin ta aikata ammh abu daya ke sata bakinciki yadda aka kasa Fahimtar abubuwan da suka faru kan yadda suke..!
Tun bayan data idar da sallar asuba bata jirga daga inda take zaune ba ta kalli gabas da katon hijabin haddarsu bangon Dakinsu ta kurama ido ita ba kuka take ba ammh kana ganinta kasan bata cikin natsuwarta cikin kwanakin nan gabadaya Amina ta Zafge sai idanuwa fuskarta tayi wani iri tayi zuru zuru Hamida da Hanne ne ke tare da ita acikin Dakin Domin Ya zeenatu ta fita Kitchen ita bata koma barci ba.
Hanne ce ta gaji da ganin Amina ahaka yasa tatashi tsam ta koma kusa da ita tadafata tana fadin"Amina don Allah kiyi hakuri..Ki yi hakuri..Haka Allah ya kaddara miki!
Kamar bazata tankata ba tama yi Tunanin bata jinta yasa ta kara Girgiza kafadanta tana Fadin"Ameena kina jina kuwa..?
Sai alokacin Amina tayi motsi da bakinta Cikin wani irin Sautin da Hamida da Hanne zasu iya Rantsewa da Allah basu taba jin Amina cikin wannan Sautin ba..!
Asaman lebenta mganar ta fito cikin karyewan zuciya da Rayuwa tace"Ina jinki Hanne..Tun jiya keda Hamida kuke maimaita kalmar nayi hakuri..Tawa kaddaran kenan baku Tunanin na Haddace wannan..?
Tafada Lokaci Daya tana sakarma Hanne manyan Idanuwanta cikin wanu yanayi na neman ma tallafi Dayasa Hanne saurin kauda kanta Tana fadin"Na sani..Ammh ki sani mai hakuri shi ke da riba watarana..Ko Hamida..!?
Hamida da duk jikinta ba Dadi tace"Sosai ma Hanne..!
Tana jinsu gani take su din suna cikin Farinciki tunda rayuwarsu bata yi musu juyin waina kamar yadda tayi mata ba..!
Kara murmusawa tayi wanda kana ganinsa zakasan ba Annuri ko jin Dadi acikinsa tace"Hakane..Nagode bazaku je hadda bane..?
Ta fada tana son kauda mganar domin tasan bazasu taba gane wani Hali take ciki ba..!
Hanne ce tace"Bazamu ji dadin zuwa baki ba Amina ki saki jikinki..Sati mai zuwa sai mu koma tare..!
Amina taji kamar tayi kuka alokacin Dama dama ace baya zata dawo Da tafi kowa jin dadi bata samu zarafin mgana ba Hamida tace"Ni kaina bazan ji dadin zuwa ko"ina ba baki ba Amina..Tare muka tashi muke komai tare..Wh damuwarki tamu ce Amina don Allah kiyi hakuri..!
Tana Fada sai kuka hakama Hanne sai ta rumgume Amina tana kuka hamida ma tazo suka hadu suka Rumgumeta suna Fadin"Amina wlh mu zamu shaidarki..mun sani Fahimtar hakane basu yi ba..!
Amina cikin wani irin kuncin zuciya tace"Wlh ban taba iskanci ba..Bantaba kadaicewa da Wani Namiji ba da sunam alfasha ba..Abunda ya faru ranar Tsausayi ne..Wannan itace kaddaran daman datake jiran bawa koda yaushe..?
Itace kaddarata sannan kuma natabbata na Fita zakkan da ake yawan Fadi akaina Tunda gsshi ni Tawa Rayuwar ta kare ba yadda ta kowa take karewa ba..Hanne da Hamida kun ji dadinku bakinciki bai gauraye jin dadinku ba..Wlh ayadda nake ji dama ace Ban hadu da Aminu ba dama komai kamar mafarki ne..!
Take fada sai kuma ta fashe da kukan da ba Hawaye daga gani abun yana Fitowa ne daga kasan ranta ne
Haka suka hadu suna ta kuka kamar wasu yara bame lallashinsu cikin wannan yanayin sukaji muryan Ya Zeenatu tana Fadin"Jawaad wai lafiyan ka kuwa..?
Me yayan zatayi maka Dakake ta mata wannan uban kiran..!
Muryan Jawaad sukaji a Tsakar gida yana Fadin"Ya zeenatu tun dazu nake tashinta taki tashi..!
Tana daga kofar kitchen ta Hararesa yana Sanye da zani da alamu wanka yayi Cikin dan fada tace"Bazaka je ka shirya ba sai Idi ya tafi ya barka ko..?
Cikin Tura baki yace"To ai ban ga Jallabiyata ba shine nake ta tashin Mama ta Daukomin taki tashi..!
Domin kaf gidan nam Jawaad kadai ke kiran Yaya Mama shi har alokacin sunan Yaya bai kama bakinsa ba..!.
Ya zeenatu da mamaki ya kamata tasan yaya bata barcin safe In ta idar da Sallar asuba sai gari ya waye tana Lazimi koda bata ga fitowarta ba Tasan tana da Bayi adaki kila ciki tayi Hidimarta ammh cikin son kwantar da Hankalin Jawaad yasa tace"Kila barci ne ya Dauketa bayan tayi sallah jeka ka Duba cikin Dirowa kila ka gani kayi sauri fa..!
Har ya juya sai ya juyo yana Fadin"Batayi sallah ba fa ya Zeenatu..!
Dam gabanta ya fadi cikin Fitan hayyaci tace"Bangane ba..!?
Cikin yarintarsa yace"kuma fa bata motsi..!
Karaf Sai a kunnen Mamanmu Dake zaman jiran wannan sakon ya isketa Mikewa tayi bakinta kamar ya Tsage Cikin Yar dariya tace"Komai ya kamallah..!
Daga haka ta gyara yanayinta Lokaci Daya tana fitowa alamun barci a idonta tace"Zeenatu me ya faru nake jin hayaniya..!
Zeenatu da Hankalinta ke tashe tace"Mamanmu jawaad fadi yake yaya bata motsi fa..?
Ido ta zaro tana fadin"Bata motsi kamar yaya..?
Tafada cikin bayanna Firginta Wanda ya fito dasu Hamida Daga daki har da Amina Da suke jin meke faruwa gabanta ke fadi jikinta ke rawa tana Fatan ba wani abu bane zai kara kutse Cikin Rayuwarta ba..!
Ya zeenatu ce kan gaba wajen shiga Dakin Yaya har bedroom dinta jawaad suka kara samu akanta yana jijjigata yana faman fadin"Mama ki tashina ina jallabiyata..?
Yake fada ammh ko gizau dukkansu kamar an dasasu sun kasa karisawa gareta tana kwance sambal Cikin Hijabinta,fuskarta tar ta kara wani Haske sai dai abu daya ya Sandarar dasu shine ganin Idanuwanta suna kallon Saman Dakin ammh kuma bata Motsi gabadayansu kamar an Sassake jikinsu haka suka kasa karisawa..!
Jawaad daya gansu ya sauko yana jan Hannun Mamanmu yana fadin"Mamanmu taho ki gani..!
Haka yake fada kamar rakumi da akala haka ya jata har gaban gadon yaya inda take kwamce daidai Lokacin da sukaji sallaman Ya Jafar Ya zeenatu kamar walkiya ta fice da Sauri kamar ta kifa a tsakar gida taga ya Jafar Bayansa Aba ne,Kaya ne ahannun Ya Jafar da bargo da Filo sai Kwandon abinci,Bata Tsaya ko Gaida Aba ba tace"Aba ya jafar kuzo ku gani Yaya bata NUMFASHI..!
Dukkansu haka mganar ta shigesu Aba kuwa dakyar ya iya Tsayuwa da Kafarsa Meke faruwa ne..?,Tabbas wanu abu ya faru ko kuma zai faru Domin Tun jiya yake fama da Faduwar gaba da yanayi mara Dadi sai ya Danganta haka da Kila abunda ya faru ne na Amina ammh kalaman Zeenatu sun saka gabbansa kara Saki Cikin wani yanayi.
Ya jafar ne ya tsaya yana fadin"Bangane bata Numfashi ba..?
Aba bai Tsaya sauraransu ba ya taka ya shiga Dakin yaya jafar na ganin haka ya watsar da kayan Hannunsa yabi bayansa Zeenatu sai ta kasa Binsu kafafunta sun kasa Daukanta koda batasan Mutuwa ba Ta tabbata yaya MUTUWA tayi..!
Ba wanda yasan da shigowar su Aba sai dai ganinsu kawai akayi Kamar Daga sama Hamida da Hanne da Amina sun rirrike hannun juna cikin wani yanayi Mamanmu tana ganin Aba sai ta fara sauya yanayinta Taga yadda take kallon yaya tana Sakin Mirmishin jin dadin.
Kan jikinta ta fada lokaci Daya tana Fashewa da kuka sai kuma ta Mike ta Nufi Aba tana nunamai yaya Lokaci Daya tana fadin"Sa"idu duba ka gani..Kamar yaya ta MUTU fa bata motsi..!
Kalmar ta Mutu shi ya shiga kunnen Amina da wani yanayin da har Abada bazata manta dashi ba..!
Aba kuma sai ya Ture Mamanmu

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment