Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce ya rika jin tashin mgana kasa kasa yasa ya Dawo da baya sai ya Fahumci Daga Dakin yaran ne.
Kafafunsa suka jasa ya isa Bakin kofar Dakin Tar yaji muryan Amina tana mgana mamaki da al"ajabi yasa ya Daga Labulen Dakin ya Leka ya ganta kwance tabama kofa baya waya a kunnenta tana mgana duk da bayajin me tace cewa ammh yasan ko wata wayar ce bata Alheri bane.
Har ya tako ya shigo Dakin agabanta bata sani ba Bai gama jin jikinsa ya Saki ba sai da yaji Amina na Fadin'"Haba Amin dina..Kasan nima ina sonka..Kuma nayi maka alkawarin Rayuwa Dakai har Abada..!
Baisam Tunyaushe ta Fara ba sai da jikinsa ya fara mazarin da karkawan wani Bala"i ko yace wani Kangarewa ne ya samu Amina..!
Amina fa itace cikin Dare tana waya da wani Gardi tana Fadamai tana son shi yar Amina da batasan komai ba.!
Ganin yadda Amina ta yi sumar wucin gadi ne ga waya a kunnenta ta kasa Sauketa Saboda yadda Hanjinta ya Cure waje Daya.
Aba ransa ya baci baisan ya karisa gabda da ita ba sai da taji wani gishiri Gishiri wajen bakinta Mari ne Aba ya Kamtseta dashu sai da bakinta ya Fashe wayar ta fadi gefenta Daidai Sanda Aba ke fadin"Ba mgana nake miki ba..Nace da Uban wa kike mgana da Daddare acikin waya..!?
Amina sai ta Fara ganin hazo Cikin Daburcewa take fadin"Ba...ba..kowa Aba..ba kowa..!
Ransa ne ya kara baci Bacin rai ya Kwashe sauran Hakurinsa baisan sadda ya Hada kanta da jikin gadon data ke kwance ba ji kake kummm...!
Lokaci Daya ya hada da marin gefen Kumatunta yana Fadin"Zan miki karya ne..?
Nace zan miki karya ne..?
Yake fada Cikin bayanna bacin ransa Ihu Amina ta kwalla Saboda Ziyartan wani azaba Dataji asaman kanta da Aba ya,kumata Tuni wajen ya Fashe sai jini Daidai Lokacin da Aminu ya Katse kiran bazai iya jura ba bazai iya Juran jin Kukan Amina ba.
Innalillahi kawai yake maimaitawa ya kasa zama yana Zagaye kyakyawan Bedroom dinsa a kano.
Gabadaya su Hamida sun Rude sun kasa ma mgana Mamanmu ce da Sauri ta Dira gaban Amina Daidai Aba ya kara Daga hannu zai kara Sauke mata ta Tareshi tana Fadin"Babansu zaka kasheta ne..?
Nace zaka kasheta ne..?
Tafada Cikin Tsawa hannunsa na rawa ya Nunata yana Fadin"Kauce ki bani waje Balaraba..!
Yau Sai yarinyar nan ta Fadamin Tun yaushe ta fara wannan lalacewar bansani ba..?
Waya na kamata tanayi balaraba da wani kato tana Fadamai bazata iya Rqyuwa bashi ba wani shegen ne yake Lalatamin Tarbiya yarinya bansani ba..!
Yake Fada yana saka hannu ya Ture Mamanmu gefe da hanzari ya Riko Amina tana Ihu ya jawota ya makata da kasa,Daman Sa"idu bai iya Fushi ba bai iya Duka ba in ya fara kamar zai kashe haka yake yi.
Hamida da Zeematu suka Rike juna jikinsu na Rawa Hatta Yaya ta Rude Amina kuka take tana Dafe da kanta Aba ya saka kafa zai taka Amina yana Fadin"Zaki gayamin ko sai na kasheki na Huta..!
Yaya bata bari ba ta rikosa da Sauri Tana Fadin"A"a kabi a hankali kada kayi Hukunci cikin Fushi..!
Mamanmi kuwa Amina ta Tarairayo Jikinta ta fashe da kuka tana Taba jinin goshinta Lokaci Daya take fadin"Abbansu jini fa..Zaka kashemin Diyata ne..?
Bai Saurareta ba wayar ya Dauko Daga Saman gado yana Laluban wajen kira Lambar Aminu ce ta karshe kuma ita ya Kira yana so yaji wani Lalataccen ne ina Tarbiya yana Daga waje yana kokarin Rusa komai..!
Lokacin da Aminu yaga Kiran yana mgana da Nenne a Dayan wayarsa ne yana gayamata Halin da ake ciki ganin kiran yasa da Sauri yace"Nenne MEENA na kira..!
Tana so tace mai kada ya Dauka kila ba Aminan bane ammh bai jita ba ya Datse kiranta ya Dauki na Amina.
Aba a speaker ya saka wayar Daidai Sanda sukaji Muryan Aminu yana Fadin"MEENATA..meena Aba bai Dakeki ba ko..?
Hankalina ya tashi!
Su hamida suka kwalalo ido Amina ai sai taji miyan bakinta ya Tsaya Cak yau kafin safe kila sai dai Buzunta Aminene sai dai Tarihinta
Aba yaji kansa ya Sara Cikin kaushin Murya Da takaici yace"Ba Meenar bace..Uban Aminan ne Sa"idu..Waye kai..?Meyasa ka zabi ka Lalatamin Tarbiyan da nayi Shekaru ina ginata..!
Nace meyasa..?
Aba ya karishe cikin Tsawar data gigita su mamanmu Hatta Aminu dagachan bangaransa ya kasa mgana baisan sadda ya Datse kiran Ba shikenan komai ya kare.
Wannan Ranar daman yake gudu.
Yanzu ta ina zai fara?
Ko yace ba yaudaran Amina yake yi ba wazai yarda dashi?
Abun ya Zama wani iri..Al"amarin yayi kwabewar da bai da wata mafita.
Wannan shine mafarin komai Mafarin abubuwan dadama da zasu faru daga Rayuwar Amina da kuma Rayuwar wanda bai tsammmaci Aminar cikin Kaddaransa ba..!






*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️19*

Gabadaya jikin Aba rawa yake saboda Bacin rai idanuwansa sun rufe jijiyoyin kansa sun mike cikin Tsananin Fushin da ko su yaya sun Dade basu gani ba ya Nuna Mamanmu da wayar hannunsa yana fadin"Wayar waye wannan..?
Nace wayar waye wannan Balaraba..?
Ya karishe fada cikin Tsawa Lokaci daya yana sakar mata jajayen idanuwansa da suka sauya Launi Saboda bacin rai.
Awannan gabar kowa bai da bakin mgana Yaya bazata kare Amina ba Daman Hamida da Zeenatu bazasu iya cewa komai ba Mamanmu ce Daman ke da wannan ikon itama ta rasa mafita Domin Amina ta bata komai wannan kiran wayar da kalaman Aminu ya gama tabbatar da cewa Amina ta aikata abunda ya Fada din.
Amina kuwa jikin Mamanmu ta shige jikinta ba inda bai rawa shikenan ta gama wayo wannan Ranar daman take tsoro gashi tazo ta sameta bata shirya ba.
Aba baya duka sai dai Fada baya Hukunci da kansa sai dai su ya Jafar ammh duk ranar da ka shiga hannunsa sunanka Sorry bai iya Duka ba in ya fara bai iya bari ba,Shiyasa wani Lokacin baya son bacin ransa kuma baya son yayi duka.
Tasani komai ya gama baci bata kuma da kalmar da zata kare kanta ballatana Har Mamanmu ta samu kwarin gwiwar kareta kamar yadda ta saba.
Aba ganin mamanmu tayi shuru ta kasa mgana sai kuka take taya Amina yasa yayi mirmishin Saman baki Mirmishin Dayafi kuka ciwo yace"Balaraba mgana nakemiki..?
Nace wayar da Amina ke amfani da ita wayar waye..?
Mamanmu ta Dago cikin wani yanayi kafin tace"Wayata ce..,ammh wlh..!
Bai bari ta karisa ba ya Daga mata Hannu Cikin wani yanayi muryansa ta Cunkushe waje Daya yace"Basai kin ce komai ba Balaraba..Na Fahimci komai..Duk Abunda Amina ta aikata ko take aikatawa da saninki da kuma Daurin gindinki Balaraba..!
Mamanmu ta Kallesa cikin wani yanayi haka ma Yaya bata samun Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Eh da saninki mana..in baki sani ba Meyasa kike barinta da wayar..?ai na Fada muku ku daina bari suna Daukan wayoyinku saboda gudun irin wannan ko ban fada ba..?ammh baki ji ba..Komai Amina zatayi mai kyau ko mara kyau Daidai ne awajenki Balaraba baki Taba nuna mata Tayi ba Daidai ba wannan ne so..?wannan ba So bane Balaraba..Kuma kin Cuceni kin Latatamin Tarbiyan da nayi shekaru ina ginata kan ya"yana bazan yafe miki ba..!
Yake fada cikin wani yanayi muryansa kamar ya yi kuka,Yaya mamaki yasa tama kasa mgana ballatana Mamanmu data kafe Aba da ido zuciyarta na suya mamakin kalamansa ya kamata.
Amina kuwa rudewa tayi da kalaman Aba da sauri ta mike daga jikin Mamanmu ta rarrafa gaban Aba cikin kuka take fadin"Aba Wlh Mamanmu bata sani ba..Bata sani ba..!
Kafa yasa ya Shureta in ya kalleta ransa har wani kara baci yake,Dukewa tayi awajen tana kuka cikin Fusata yace"Karya kike ta sani..Tasan komai akanki..Balaraba tasan komai akanki Amina..Hadizam haihuwanki kadai tayi ammh Matsayin Uwa balarabace gareki baki yarda da kowa ba sai ita..Abun bakinciki ace kamarni acikin gidana na samu mai Bijirema Umarni na..SAnnan Tsorona Daya tun yaushe kika fara haka Amina..?
Na Dade ina addu"an kada watarana ki Zama Zakkan da mutane ke Fada sai gashi Tun ba"a je ko"ina ba Abunda nake tsoro ya faru....!
Yake fada cikin bacin rai kafim Lokaci Daya ya Dago Amina wuyanta ya Shake Cikin Zare mata ido yana Fadin"Ban yarda Dake ba Amina..Dom Ubanki ki Fadamin saunawa kika yarda yayi Lalata Dake..?
Ki Fadamin yaushe kika san maza haka ban sani ba Amina Duk kafa kafan da muke ni da Baba Mallam a kanku..bamu tsira ba..?
Ki fadamin nace kafin raina ya baci na Shakeki kimutu kowa ya huta..!
Zuwa Lokacin Amina ta fara kokuwa da Numfashinta Yaya bazata ce komai ba Tana baya hankalinta atsshe Hamida da Zeenatu kuka Mamanmu kuma kalaman Aba sun gama kashe mata jiki ganin Amina ta kusa Mutuwa ne kada ayi kisam kai yasa Mamammu ta mike da Sauri ta isa garesa tana kokarin bambare hannunsa a wuyan Amina Lokaci Daya tana Fadin"Haba Abansu zakayi kisa ne..?
Kalli fa zaka kasheta Amina bata Numfashi..?
Take fada Cikim kuka Hannu yasa ya Tureta da karfi da sai da ta Fadi kugunta ya Bugu wani kara ta saki da yasa Yaya dasu Hamida sukayi kanta da yatsa ya nunata yana Fadin"Kada ki kara sakamin baki in ina ma ya"yana Hukunci balaraba..Domin ke ba Matata bace Yanzu
NA SAKEKI Saki Daya..Tunda na Fahimci kin bada gudummuwa a Lalatamin tarbiyar Amina..!
Ya fada Cikin bayyana bacin ransa Ba su Hamida Dake rike da Mamanmu ba Hatta Amina Dake kokuwa da Numfashinta sai da kalaman Aba suka Girgizata ta zaro ido tana kallon Aba Cikin Firgita da rawan baki Hamida hannu ta Dora akai Zeenatu kuwa hannun Yaya ta kamkame tana kuka wacce ta saki Mamanmu kamar bata da laka ta koma ta zauna Dabas kanta na juyamata ji take kamar amafarki komai ke faruwa
Cikin Muryan da basu taba sanin Yaya tana dashi ba ta Kira Aba Cikin Tsawa"SA'AIDU..Me ka aikata haka..?
In har baka gode mata kan Amina ba bazaka zageta ba..Kayi kuskure kayi kuskure Sa"idu kayi saurin gyarashi kafin Lokaci ya kure maka!
Kallonta yake yi bai yi Nadama yace"Kema Kada ki kara sakamin baki..In kuma ba Haka sai ranki ya baci..!
Yaya sai hawaye Amina ta zama bala'i tayi sanadin mutuwar auran matar da ta zama bango gareta Kallon Amina kawai take ta Durkushe tana wani kuka kukam Nadama da bakin ciki acikin Ranta Tana Tunanin Dama ace
.Dama ace bata Hadu da Aminu ba Dama ace bata yarda dashi ba..Da duk haka bata faru ba me ta aikata..?
Ta kashe auran Matar da ko Uwar data Haifeta bata kaita sonta ba Matar data kasance wata aba mai Daraja a wajenta ita kam Amina wannan Ranar bakar Ranace a wajenta soyayya bata mata adalci ba ta Datse mata komai alokacin da bata tsammaci Lalacewar abubuwa kamar yadda suke Faruwa ba.
Kuka take kamar ranta zai fita ta Rararrafa ta kama Kafan Aba cikin kuka take fadin"Don Allah kayi hakuri..naji ni ka Hukuntani kayi ta Dukana har sai na Daina Numfashi ammh kada ka saki Mamanmu Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa Mamanmu bata sam komai ba Wlh bata sani ba!
Take fada tana kuka wannan karon ba Aba bane ya Tureta Yaya ce Lokaci Daya ta shiga Dima ma ta Dundu kota ko"ina Bataji bata gani tana kuka Tana Fadin"Kin yi asara Amina..Kin yi asara Tunda rashin jinki yasa,kikayi Sanadiyar Mutuwar auram matar da bata taba barinki ke kadai ba akowani Hali Tana Tare Dake..Kin Fita Zakka Amin Da gaske ne ke Zakka ce..Tunda kika Rama Alheri da Sharri..Ki ka kuma yi Sanadiyar Mutuwar auran da ya yi Shekaru na rasa da wani suna Zan kiraki ji nake in na barki da Raina bam Huce ba..!
Kowa ya kasa hanata Yaya bada wasa take dukam Amina ba Fadi take"Abun kunya zaki jawo musu Amina..?
Su kike ki kasheta ki huta..?
domin ita kadai ke Daukema Jidalinki Amina kin fara bin maza?
Aure kike so baki fada anyi miki ba.?
Gwara na fara kasheki na Huta kafin ki zo ki Kashe sauran Rayuwanka da suke kare miki..!
Dukanta take yi kamar bata cikin Hayyacinta Amina na kuka bakimta na Zubar da jini take fadin"Wlh yaya bana bin maza
Wlh ni ba yar iska bace..!
Bakinta bai mutu ba..Daman bazai taba Mutuwa ba yau da Mamanmu zata Ceceta bata ceceta ba tana gefe har alokacin Shock din Daya kamata bai saketa ba sannan ko tana son tashi ta kasa kugunta ya Bugu da Gadon Hamida ta kasa tashi Kuka take daga Zaune ba kukan kalaman Sa"idu kukan yadda Amina ke kuka Yaya na Dukanta Cikin karyewan Murya tace"Yaya ki daina dukan ta don Allah..Ki bari raina na kuna..!
Yaya ta Dago idonta jajir tana Fadin"Yau dai..Yau dai Kadai ki bari na Shiga Lamarin yarinyar nan..Ki barni na yau kadai!
Mamanmu sai ta kasa mgana Ya Zeenatu ne taga Abun ya rikice Aba na Tsaye bai yi mgana ba Shima baya son ya kara saka mata hannu ne sai ya Illlatata,Rugawa tayi ta Fice Daga Dakin ba Mayafi ba Takalmi ta nufi waje ita ta Bude gida sai gidam Baba Malam an Rufe get haka ta Dinga Bugawa da karfi megadi yana Lekowa ya ganta ya Bude Mata da Sauri yana Tambayanta ko Lafiya ina bata Tsaya Sauraransa ba da Farko Cikin Gida ta so ta wuce sai taga Falon Baba Mallam abude ssi ta kwashi gudu zuwa chan.
Yana Tsaye gaban makeken Dirowan Dake falonsa mai shake da Littafai da Farin Gilashinsa da Jallabiya yana Duba wani littafi ne sanda Zeenatu ta Fado kamar an korota tana Haki Sama Sama Hakinta yaji da Numfashinta yasa ya Juyo da sauri ganinta Cikin wannnan yanayin yasa Hankalinsa ya tashi da sauri ya baro inda yake Tsaye ya kariso gabanta Cikin Dattakonsa yace"Zeenatu meke farruwa ne..?
Ganin yadda ta Duke ne tana kuka Jikinta ba inda baya rawa yasa yace da Sauri"Kada kicemin wani abu ne Mummuna ya samu Sa"idu bayan yanzu bada Dadewa ba yabar nan wajen..!?
Zeenatu na kuka Dakyar ta iya cewa"Aba..Ya saki mamanmu..Sannan ga yaya chan na Dukan Amina..Baba mallam kazo kafin su yi kisan kai..!
Hankalinsa nan da nan ya tashi Cikin wani yanayi ya shiga maimaita"Innalillahi wani"inna ilaihirraju"un..!
Muje gidan muje..!
Yake fada yana karisa wajen Daya Ijiye wayarsa ya Daukota yabi bayan Zeenatu data Fice da Sauri Lambar Hajiya Babba ya Kira bai rude ba sosai Saboda yana ta Kiran sunan Allah..
Itama ta tsorata data ga Kiran nasa Domin bata Dade da komawa Shashen nata ba ba ita keda dashi ba Hajiya Nasara ce,Cikin Wani yanayi ta Daga Wayar tana Fadin"Mallam lafiya dai ko..?
Cikin Dattakonsa yace"Ki sako mayafinki ki Sameni gidan Sa"idu..!
Zumbur ta mike daga kwancen Datake tana Fadin"Innalillahi me ya Faru ne Mallam?
Cikin Natsuwarsa yace"Bansani ba..Sai mun je zamu ji..Ki yi Sauri..!
Daga haka ya Datse kiran cikin Sarsarfa ya Fice Daga falon bayan ya saka wayar tasa aljihu Tuni Zeenatu ta fice Daga gidan megadi ganin Mallam ya fito da kansa yasan ba Lafiya bai Tsaya tambayansa ba ya shiga mai Fatan Dawowa lafiya
Gudu gudu sauri sauri Baba Mallam ya isa gidan su Amina kamar zai fadi Saboda Damuwa zeenatu na shiga Dakin ya shiga Saboda ya Jiyo kuka da mgana Har Lokacin Yaya Dukan Amina take yi Cikin Tashin hankali ya karisa gabanta baasusan da shigowarsa ba mganarsa kadai sukaji Daga sama
"Kada ki Sake Dukanta HADIZA...!
Ya fada Cikin Kaushinsa kamar koda yaushe,Cak yaya ta Tsaya sai Lokacin Aba ya gansa Mamanmu na gefe tana kuka tana ganin Baba Mallam tace"Yauwa gwara da Allah ya kawo ka..Mallam kalli Dukan da suka ma Amina..?
Kashemin ita zasu yi.?
Aminar Baba mallam ya kallah Goshi na zubar jini baki ma haka gabadaya bakin ya sumtuma sun sauya mata kammani Tama Daina kuka sai Hadiyar rai kawai Daidai shigowar Hajiya Babba cikin tashin Hankali ganin yanayinsu yasa tace"Wai meke faruwa ne..?
Sa"idu..?
Ba wanda ya iya mata mgana Sai Lokacin Mamanmu ta iya mikewa Dafe da kugunta Baba mallam ya kalleta Sau Daya ya kauda kai Hajiya Babba ya kallah yana Fadin"Hajiya kama Amina..bari na kira Idi yakai ku Asibiti mafi kusa a dubata tana Zubar da jini..!
Sai Lokacim Hajiya Babba ta Lura da Amina da sauri ta karisa ta Dagota tana Fadin"Innalillahi waye yayi mata wannan Dukan..?
Zaku kasheta ne..?
Amina kuwa ganin Hajiya yasa ta fashe da kuka tana Fadin"Hajiya ki fadama Aba da yaya..Wlh bana bin maza..Ki kuma fadamai ba Ruwan mamanmu don Allah ya janye Sakin da yayi mata..!
Hajiya ta ji ta shiga Tashin Hankali Cikin wani yanayi tace"Innalillahi Wani"inna Ilaihirraju"un..!
Baba mallam bai saurari kowa ba ya Fiddo wayarsa ya Kira Idi Direba daman gidansa ba nisa yace mai ya Fito akwai Fitar da gaggawa yana Gama wayar ya juyo yana Fadin"Hajiya kuje har da Balaraba itama adubata!
Hajiya ta kalli Mamanmu yadda ta kasa Tsayuwa tana Fadin"Mun shige su ni Zainabu..Wai me yake faruwa ne..?
Baba Mallam bai mata mgana ba Aba ya kallah wanda kansa ke kasa yace"Biyo ni Dakinka..Ku kuma kuje Daga waje..Yanzu Idin zai iso..!
Daga haka ya saka kai ya Fice Aba yabi bayansa Falon Aba suka isa Baba Mallam ya fara shiga Aba yabi bayansa su kuma Hajiya ta kama Amina tana kuka jini agoshi da baki Hamida ta kallah Dake gunjin kuka tace"Miko mata Hijabi Hamida..!
Da sauri ta rarumo nata ta mika ma Hajiya ta saka mata Yaya kuma Ficewa Tayi Daga Dakin cikin yanayin da ba wanda ya gane.
Hajiya ta kalli Mamanmu Tana Fadin"balaraba sako mayafinki muje..Allah yayi mana mganin wannan masifar data kunno mana kai da Daddaran nan!
Zeenatu taje ta dauko ma Mamanmu Hijabi ta saka ta riketa Saboda Dakyar take iya takawa suka fita Kofar gida Har idi ya iso har ya fito da Mota suka shiga Hajiya da Amina da Mamanmu da Zeenatu Hamida kuma Hajiya tace ta koma gida Wani karamin asibitin kudi Hajiya tace Idi ya kaisu Saboda kada su bata Lokaci.
Achan Falon Aba kuwa suna shiga ko Zama Baba Mallam bai yi ba ya Juyo yana kallon Aba cikin wani yanayin Bacin rai Aba kansa ya maida kasa Domin in yana gaban Baba mallam baya iya Daga kansa saboda Biyayyah..!
Shuru na wani Lokaci yaji Baba Mallam bai ce komai shiyasa ya Dago kansa a hankali kafin ya bude baki zai yi mgana Baba Mallam ya Daga mai hannu Cikin Dattakonsa yace"Bana son jin komai yanzu..Kafin na tambayeka me ya faru..Ka maida Balaraba Dakinta in har kana so na Saurareka..!
Aba ya Dago kansa cikin wani yanayi yace"Baba m...!
"Bana son jin komai kayi abunda nace in har na isa Dakai..!
Dole yasa Aba yace"Shikenan..Na maidata Dakinta na Janye Sakin Dake Tsakanina da Balaraba..!
Sai alokacin Baba Mallam ya sauke Nunfashi ya samu kujera ya zauna yanuna Aba gefensa shima ya zauna kafin yace"Ina jinki...Fadamin abunda ya faru tundaga farko..!
Nan Aba ya Sunkuyar dakai ya Sanar da Baba Mallan komai ya karishe da Fadin"Abu daya yafi min ciwo..Meyasa Balaraba ta Boyemun..!
Sannan da Taimakonta ta Lalatamin Tarbiyar Amina Mallam..Na tabbata da saninta..!
Kallonsa kawai yake ya Dade bai yi mgana ba sai chan nisa ya fara mgana cikin Kaushinsa kamar ko yaushe"Sa"idu kaifa mai ilmi ne..To ina Ilimin ka yake..?
Me Annabi yace..?
Kada muyi Fushi..Kuma mu daina Saurin yanke hukunci cikin Fushi..Meyasa da haka ta faru baka bari kayi bincike ba kafin ka yanke hukunci ba..Kana da Tabbacin ita Balarabar ta sani..?
Baka sani ba..Kun taru kai da Hadiza kuna neman kuyi kisan kai..?
Yanzu inda wani abu ya faru mara Dadi wa gari ya waya Sa"idu.?
Kan Aba na kasa yace"Kayi hakuri Baba Mallam!
Mirmishi yayi kafin yace"Akoda yaushe ina Fada maka Duka baya Tausasa yaro..Sai ma ya kara karangarar dashi Nasiha da Lallashi ne mafita Sa"idu ban ji dadi ba..Kana aibata yarka ina ji ajikina Bamu aikata barna Lokacin kuruciyarmu ba..Muma Daga cikin ya"yanmu ba Zamu samu bara Gurbi ba Sa"idu...!
Aba ya dago yana Fadin"Yaron da take waya dashi fa Mallam..?
Ansan meke Tsakaninsu..?
Baba Mallan yace"Koma menene alheri ne Sa"idu..Baka haikema ya"yan wasu ba kaima da yardan Allah bamai haikema ya"yanka da yardan Allah..Wannan ai ba wani abu bane Komai zai daidaita Zan yi mgana da Amina yaron da suke wayar zan nemesa naji abunda ke Tsakaminsu in Yana sonta da Gaske ni zan ce ya Fito in nayi bincike na gari ne zan bashi Auran Amina Kamar yadda na Saba..!
Aba ya saki baki yana kallon Baba Mallam bai samu zarafin mgana ba yaji yace"Kiramin Hadiza..Itama na nuna mata ta Daina yanke hukunci Cikin Fushi..Sannan ku daina aibata ya"yanku Dafi ne garesu..!
Ba Musu ya mike ya fice koda yaje ya isketa tana ta kuka,Ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kizo Falo na Baba Mallam na mgana..!
Da haka ya fice share Hawayenta tayi ta saka Hijabi ta shiga Falon ta samu Baba Mallam yayi mata nasiha sosai da jikinta yayi sanyi Cikin wani Rauni Yaya tace"Mallam Amina ta fitta zakka..Tayi Sanadiyar da saki ya shiga Tsakanin Mahaifinta da matar da ta Zamemata komai a rayuwa..!
Mallam ba Amina ce agabana ba
Kuka nake Saboda Alherin Balaraba ya koma Sharrin awajem Sa"idu..!
Baba Mallam yace"Wannan ya wuce Hadiza...Sa"idu ya maidata Dakinta Yanzu nan..Mganar Amina kuma ba Ruwanka zan yi mgaba da ita..,!
Dukkansu basu kara mgama ba Domin Duk Abunda Baba Mallam yace daidai ne Yaya hankalinta ya kwanta Dataji cewa Aba ya maida Mamanmu sai alokacin taji Hamkalinta ya kwanta.
Hajiya ce ta Kira Baba mallam awaya sukayi mgana basu ji me tace ba cewa kawai yayi sai sun dawo..!
Suna mgana ya kallesu yana Fadin"komai lafiya..Amina goshinta ne ya fashe anyi Dinki sai Balaraba data Bugu kadan..suna hanyar Dawowa..!
Kai suka gyada gabadayansu Baba mallam ya cigaba da musu nasiha yana Nuna musu illah yanke hukunci Cikin fushi da aibata ya"ya da kalamai marasa Dadi sunan nan sai gasu Hajiya sun Dawo falon Aba suka shigo Gabadayansu Hamida ta Tsaya Daga wajen Daman tunda suka tafi ta ke kuka Tasani Amina tana da Jidali sai dai bata taba Tsammanin Jidalin Amina yakai har ya huce yadda take tsammani ba
Amina da plasta a goshinta bakinta kuma wankeshi akayi ya Kumbura mamanmu kuma mgani aka bata baba Mallam ya kalli Amina Dake Nanike da Mamamanmu kafin yace"Hajiya ki tafi da Amina ta zauna awajenki har ta samu sauki..Ke kuma Balaraba kiyi hakuri kin ji..
Sa"idu ya maidake Dakimki Don Alllah ina so har Abada bayan mu anan kada wani yaji wannam mganar..!
Mamanmu tace"Insha Allahu mallam..Bakomai..!
Baba Mallam yaji Dadi yana ta saka albarka kafin ya Mike shi da Hajiya wacce ta Riko Amina da hannunta ke cikin na Mamanmu kanta ta Dafa tana Fadin"Kada ki damu
Har Abada ina nan a matsayin Mamanki Diyata.!
Gobe zan shigo na Dubaki zan zo miki da kayanki..!
Kai ta daga mata Zuciyarta ta Sauka Tunda Aba ya janye sakin da yayi mata radadin Dake ranta ya Sauka haka suka fito har kofar gida suka rakasu dukkansu Hamida ta rike ma Amina hannu sai haawaye Amina ta Rike Hamida tana Fadin"kuyi hakuri Hamida ku yafemin..!
Hamida ta saka mgana har Hajiya taja Amina suka tafi wannan wani irin almari ne..?
Bata fatan kara ganin mai kama da wannan Ranar.
Achan gidan Baba Mallam kuwa Su Hanne duk sun yi barci Dakinta Hajiya takai Amina ta saka mata Ruwa mai zafi tace ta shiga tayi wanka ta gasa jikinta ita kuma ta Fice Shashen Mallam shi yake karanta mata abunda ya faru bataji Dadi ba ammh Tunda Mallam yace zai yi mgana da Amina shikenan komai zai Daidaita.
Bata jima ba ta Dawo shashenta,Saboda Hajiya nasara tazo wajen Mallam koda ta koma Amina tayi barci Dayake an mata allura a asibitin Tsausayinta Hajiya taji wata Kaddaran bamu ke Dorama kanmu ba Allah ne..!
Hajiya shimfida tayi akasa ta kwamta ta bar Amina akan gadon sai Washegari ne su Hanne su ka ganta Shima Hajiya ce tace su shiga su Duba Amina bata da lafiya kafin su tafi makaranta Allah yasa ma suna Revesition ne su Amina su kuma su ya Abida suna Mock ne.
Da suka Tambayi me ya sameta sai Hajiya tace Zamewa tayi a bandaki Hanne tafi shiga Damuwa da Halin da Amina ke ciki,Sannan kuma Amina ta Riketa tana Fadin"Keda Hamida nayi muku laifi ku yafemin Hanne..!
Bata iya gane komai ba,Sai da Suka je makaramta suka hadu da Hamida ta Fadamata komai Hanne ta shiga Tashun hankali Fadi take" kin ji ko.Hamida..?
Amina ta Debo jidalin Dayafi karfinta..!
Hamida tace"So nake ta kara jin Sauki..Sai mu turketa ta Fadamama yaushe ta fara aikata abu batare data sanar damu ba..!
Hanne tace"Tabbas..!
Da haka suka bar mganar sun fada a makaranta Amina bazata samu zuwa ba bata da lafiya bayan sun dawo ne suka shiga Har hamida gidan Baba mallam ta Duba Amina har da su Sa"adatu da yake an Fada Aminar bata da lafiya da ya Shamsu yaga bai ganta ba Hamida ta Fada acikin mota sanda Idi ya Daukesu
Taji sauki sai dai Kumburin bakin kadan shima ya Sauka goshin ma yayi Sauki Mamanmu ma ta warware ta shigo har Fatan wake da Hanta

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment