Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana saka yakininsa da Kallonsa kan Aliyu da yayi Kasake yana kallon Umar din..!
Bai basa zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Sai dai abu daya na sani..Meyasa Mallam ya Zabeni..?
Bayan ni akwai Nazir,Ga Nasir ga Nazeem ayadda nake gani akwai kwaruwa yarinyace karama da batasan komai ba sai Shirme an cutar dani An cutar da ita Dukkanmu Rayuwar batayi mana Daidai ba Aliyu..!
Awannan gabar ji yake kamar ya saka kuka sai dai ina Jarumtarsa bazata barsa ba..!
Aliyu ne ke Bubbuga Kafadansa yana Fadin"Easy mana Shehi..Biyayya kayi kuma insha Allahu bazaka tabe ba..Komai da kaga ya faru tsarin Allah ne..Sannan da kake fadin gasu Nasir ai mallam din ya san dasu ko..?kuma ya Zabeka na Tabbata kamar yadda ya Zabeka cikin ya"yansa yana da kyakyawan yakinin bazaka basa kunya ba..Sannan kai din kafi su chanchanta kabar mganar yarinya ce Annabi ma ya auri Nana Aisha As tana da Shekara Tara ne kaga kuwa sunna ce sannan yarinyar nan ba karama bace yadda kake tsammani zata kai 16 to 17 fa Shehi ai kuwa batayi kankanta ba wadanda ma basu kaita ba anayi musu aure kuma su zauna Lafiya kuma mganar yar cikin ka yaushe ta zama yar cikinka..?Just 39yrs fa gareka Shehi ta ina zaka iya Haifanta banda Tsabar son girma da Sharri irin naka..!
Sai da ya Murmusa jin kalaman Aliyu kafin yace"Ammh dai kasan da auran wuri nayi..Da yanzu ko ban haifi kamar ta ba na kusa..!?
Aliyu na Dariya yace"Uhmm.Naji Ka dai kafin naji watarana yar cikin naka ta baka Wahala..!
Ya karishe fada yana kallon sa kasa kasa karamin Tsaki yaja kafin yace"kasha kwaya ne..?ko ka fara Hauka inaga..Ni fa duk ba wannan ba Ina cikin Tashin hamkali ko su Sakina ban yi mgana dasu ba fa..!
Aliyu yace"Tab..Ai sai kayi hakuri..Domin tama ji ta gama Tunda dai kuka zo nan..!
Dammallam ya Sauke Numfashi bai yi mgana ba Diramar da zasu kwasa Kadai yake hangowa in Sakina taji Labari ganin haka yasa Aliyu yake ta Kwantar mai da Hankali tare da bashi Shawarwarin da zasu mai amfani kuma ya natsu yana jinsu aransa yana godema Allah Daya Hadasa da aboki nagari kamar Aliyu.


Hakika an ga jama"a Domin kungoyin Matam malamai duk sun zo gaisuwa,Kowacce cikin masu auran nan Dangin mazajensu sun zo gaisuwa,Mutane ne suke ta Zuwa har abun yaso bama Mutane mamaki,sai dai kuma ba abun mamaki bane sanin Wacece Yaya shaidar duniya itace ta Lahira Tabbas yaya ta dace
Kowa sai mamakin Aba akeyi ganinsa Cikin natsuwarsa ba wanda yayi Tunanin Mutuwar bazata Gigitasa ba..Sai dai ina wadanda suke son ganin gazawar tasa basu gani ba Tabbas Mutuwar ta tabasa sai dai ya Riga ya yarda da Allah ke kashewa kuma ya raya alokacin Daya ga Dama sannan kuma Ga Baba Mallam agefensa Koda yaushe cikin mai Nasiha yake yi da karamai karfin Gwiwa Kuma cikin ikon Allah komai yazo da sauki yana Tsaye kan kafafunsa Cikin Jarumta da Takwalli..!

Sai da akayi addu"ar bakwai kana aka Rufe zaman gaisuwa akuma ranar Baki suka fara tafiya hatta yan gusai da yan bazanga maza da wasu daga cikin matan sun koma da Rana yaran dai duka suna nan,sun samu zama Tunda Mallam bai ce komai ba shi kuma so yake sai ya Hadasu yayi musu Nasiha sannan ya Umarci kowacce ta koma Gidan Mijinta
Haka kuwa akayi ranar da yaya ta cika kwana Takwas da Rasuwa da Daddare a Falon Baba Mallam ya tarasu kowa da kowa banda ya Nazir da ya koma Tun ranar uku saboda aiko ko Umar da yazo basu hadu ba..!
Yara da manya Harda Jawaad dake jikin Aba wanda tunda akayi rasuwar Aba ne komai nashi yanzu..!
Mazan gabadaya suna zaune akasa ne gaban Baba Mallan hatta Aba yana zaune akasa ne sai su Hajiya Babba,da su Hajiya Nasara da Anty Amarya da Anty Uwa sai gefe Mamanmu ita ke zaune ita da yaran gabadaya Amina na can karshe kusa da Hanne kanta na kasa Tun bayan rasuwar sai yau tayi wanka shima sai da Hajiya ta nuna bacin ranta..!
Bayan Bude taro da addu"a da Ya Nasir yayi Baba Mallam ya fi Minti Talatin yana musu Nasiha da jan hankulansu gabadaya harda Aba Daga karshe yayi musu Fatan suyi hakuri su Rumgumi wannan Rashin da fatan Allah ya haskaka kabarin Hadiza aka amsa da Ameen..!
Ba zato ba Tsammani Mallam ya Fadi auran dayq daura Tsakanin Umar da Amina,Kowa daman ya sani wannan Mutuwar ne tasa ba wanda ya Tada mganar Sakina na wajen sai dai ta Riga ta samu Labari bakin Sa"adatu data tambayi Anty Amarya ta tabbatar mata,Bata wani damu ba Domin Anty Amarya ta mata alkawarin ba inda auran zai je ayadda aka Kullashi hakaza"a warware shi ne..!

Danmallan Sakina yake kallo yaga yanayinta sai dai bai Fahimci komai ba Illah Mirmishin Fatan baki data Saki aranta Tana Tunanin kishi da wanchan mara kunyar yarinya ai bata Lokaci ne ta tabbata ko a kafa aka Daurama Umar ita sai ya kwanceta yayi ta kansa to me zai Dameta..!
Dukkansu yaran sunyi Fatan Alheri batare da sun ji musabbin abunda ya Faru har Lamarin ya koma haka ba Sai dai sun san da abunda ya Faru haka kurum Baba Mallam bazai Sauya Tsarinsa na aurar dasu in sun yi Candy ba,sai dai tunda bai sanar dasu ba sai suka bar mganar hakanan..!
Daganan addu"an tashi akayi ya sallamesu da Umarni goben goben nan kowacce ta shirya komawa gidan Mijinta Angode hakanan da Toh suka amsa suna ma godiya domim sun ga ma kokarim sa daya barsu suka yi kwanakin nan bai yi mgana ba..!
Ya sallami kowa illah Hajiya Babba Dayace ta Tsaya ita da goggo Husai da Ya Danmallam sai Aba kadai yace yana son mgana dasu..!
Amina ta mike zata fita Baba Maallam Dake Lura da ita ya Dago yana Fadin"Mamana kariso nan ina son mgana Dake..!
Hannunta na cikin na Hanne ta zame ta fara tafiya zuwa wajensa tana jin yadda Ido ya koma kanta abunda bata sani ba Uban gayyar kansa na kasa ko Dagowa bai yi ba Duk da yasan itace Mallam yake kira da Mamarsa..!
Har gabansa taje ta Duka kanta na kasa Lokaci daya tace"Gani Baba Mallam..!
Tattausan Mirmishi yayi kafin yace"Na ganki Mamana..shin ko yima Babanki gaisuwa..?Gashi nan Sa"idu nake nufi..?
Yafada yana Nunasa sai Alokacin ta Dago tana kallon Aba Rabonta da ganinsa gani mai kyau Tun ranar da aka kaisa asibiti sai yau dataga ya Rame yayi baki yana cewa ya Tsufa sai yau taga Tsufansa ta bayyana yana Sanye dajallabiya Mai ruwan madara da Bakin wando kansa ba Hula Furfuransa duk ta bayyana Idanuwansa sun Zurma ciki alamun akwai rashin Barci da kwamciyar hankali..!
Batasan sadda tace"Aba ka rame..Ka dade kana cemin ka fara Tsufa ban taba ganin tsufanka ba sai yau..Sai yau bayan kasa ta Rufe idon yaya..!
Take fada cikin raunin Raunin da Tun da akayi rasuwar bata saukan mata ba sai yau datake ganin Aba agabanta da yanayin daya koma..!

Kowa afalon sai da jikinsa yayi sanyi Aba kwalla ta kawo masa yana kaunar Amina kaunar Hadiza ne ta shafeta ba saboda komai ba sai Saboda kammaninta da Hadiza!
Cikin Dauriya yace"Na Dade da Tsufa Amina..Sai yanzu ne tsufan ya bayyana..bayan na rasa Hadiza..!

Akaron farko Amina ta fashe da kukan daya rike mata zuciya in Tana ganinsu ya Jadwa na kuka sai taji su gwara su yaya bata bar duniya tana Fushi dasu ba gwara su sun samu kyakyawan Mu"amala ita fa bata da wani abu da zata Dorar Tsakaninsu in yaya ta saka baki a lamarinta to na Bacin rai ne ba na Dadin rai ba..!
Kuka take kamar ranta zai fita cikin kukan ta Rarrafa gaban Aba ta kama kafarsa tana fadin"Aba ka yafemin..Don Allah ka yafemin kada kai ma ka rasu ka barni baka yafemin ba kamar yadda yaya tatafi ta barni tana Fushi dani..!
Haka take fada tana wani irin gunjin kuka,wanda duk mai Tsausayi da Imani sai ya Tsausaya mata hatta kuwa da Danmallam Dake gefe sai da ya Dago ya kalleta cikin wani yanayi..!
Hajiya baya ta juya tana sharan kwallah Baba Mallam ne mai Dakiya yana Binsu da kallon Tsausayi..!
Jawaad yayi barci shi yasa Aba ya kwantar dashi kan kujera sannan ya saka Hannu ya Dago Amina yana Fadin"Hadiza bata rasu da Haushinki ba Amina..Komai kikayi sai dai tace Allah ya shiryaki..Bata taba aibataki b .....Addu"ata gareki mai kyau ne Amina..!
Hajiya babba ta amsa da cewa"Kuma addu"anta baza ta taba fadi abanza ba.Da yardan Allah zaku yi alfahari da Amina Hadiza zatayi alfahari da Amina ko bayan kasa ta shafe idanuwanta ne..!

Yanayin falon ya koma na Jimami Barin ma yadda Amina ke kuka Data Rumgume Aba tanayi kuka mai Cin rai Baba Mallam ne yaga kukan yayi yasa yace"Mamana tashi nan bar kukan nan hakanan kina tadama Babanki Hankali..!
Sai Lokacin ta bar jikin Aba ta sulale kasa tana Fadin"Ka yafemin Aba..!
Yana kokarin Dauke Hawayen idonsa yace"Ban taba rike ki ba Amina..Komai kikayi min na bacin rai ina yi miki uzuri Wlh..Hadiza koda yaushe fadi take mu yi mata Fatan Shiriya mu yi fatan Allah yasa in ta Girma ta sauya..Na yafe miki Duniya da Lahira Amina Allah yayi miki albarka..!

Tana kuka take amsawa da Ameen kafin ta Rarrafa gaban Baba Mallan rikota yayi ya Tadata ya zaunar da ita gefensa ya saka Gefen rawaninsa ya Share mata Hawaye yana fadin"Bar kuka..Addu"a zaki rika mata in kin Tunata kinji ko..?
Kai ta gyada mai tana sharan majina Hajiya Babba tace"Kabarta tayi kuka Mallan tun fa rasuwar nan banga tayi kuka ba..!
Sai Alokacin goggo Husai ta tanka"To zainabu sai kuma abarta ta tadama Mutane da Hankali..?
Tana Raye bata huta da Jidalin Amina ba bayan ta rasu bazata barta ta Huta Cikin Salama ba..!
Da sauri Baba Mallan yace"Husai kibar wannan mganar..Hadiza zata Huta cikin kabarinta da yardan Allah Shaidar duniya itace ta Kiyama..!
Dole ta koma tayi shuru domin ita bata da wannan Sakewan da yara shiyasa Tuni taso Sa"idu ya bata Amina tatafi da ita da Tuni duk wannan Tabaran ta daina shi
Ita gani take harda da Laifin Sa"idun da su Mallam din..!
Nan Baba Mallam ya cigaba da Lallashin Amina har sai da ta bar kuka sannan ya kalleta yace"nima zan baki Hakuri Mamana..Nayi miki laifi nayi sonkai..Na rabaki da wanda kike so na aura miki Da"a na..!

Sai kunya ta kama Amina ta kalli Baba Mallam da manyan Idanuwanta kafin tayi mgana Ya saka baki ya Kira Umar Dake gefen Aba kansa na kasa kamar baya Falon
Gaban Baba Mallam yazo ya Durkusa Cikin Sanyin sa yace"Gani Mallam!
Ba zato kawai yaji ya Damki hannunsa ya Hada cikin na Amina cikin Dattakonsa yace"Ga Amanar Hannun Mamana nan Umaru..Ko bayan raina ban yarda ka saki ba..Ko Laifin me ta maka ka Duba girmana ka mata afuwa ka yi juriya kan Hallayarta ka zama mai mata Nasiha yayinda ta bata maka Sannan Daga karshe ina fatan zaka riketa Bisa gaskiya da Amana sannan ka kwantatanta adalci Tsakanin matanka..,!

Gabadaya sai jikinsa ya Mutu hannuwan nasu yabi da kallo kamar yadda Amina itama take bin Karamin hannunta Sarke cikim Tattaausan hannun yaya Danmallam mai cike da gargasa da kallo..!

Bakinsa yayi nauyi da wannan Abunda Mallam yayi shiyasa ya jinjina kai kafin yace"Insha Allahu Mallam..Allah ya kara girma..!
Ya amsa da Ameen har Lokacin hannayensu na Sarke da juna Hajiya Babba ta kallesu farimciki ya cikata Cikin wani yanayi tace"Yadda kuke rike hannun juna..Allah yasa ko a Lahira tare zaku tashi rike da hannun juna..Allah ya Hada zuciyoyinku Waje daya..!
Gabadaya aka amsa da Ameen Aba na gefe yama kasa mgana Alherin Baba Mallan garesa ai mai girma ce..!
Goggo hussai tace"Sai faman bashi Amana kuke yi kun manta Amina..?Kai Umaru kalleni nan..Kada ka damu da mganar Mallam ko ta Hajiya..Amina sai da wuta..In tayi maka ba Daidai ba kaci Zarafinta kada kayi mata da Sauki Domin kai zaka sha Wahalanta Ahtto..!
Tafada bilhakki da gaskiyanta Dayasa Hajiya ta Murmusa tana fadin"Ke fa Goggo ce Husai..!
Tace"Ai na sani shiyasa nake Fadamai gaskiya..jidalin Amina ai Allah kadai yasan shi Har Hadiza ta bar Duniya bacin ranta Daya kan Amina..Allah yasa ta samu ma uwar goyo ta gari ai da ba Domin Balaraba ba da Amina kuma sai Allah..!

Amina na jinta ita yanzu komai ma ya zama mai Sanyi awajenta in da abayane ta Tabbata Sai ta Tura mata baki tayi gunaguni kamar baya ammh yanzu sai taji ta kasa bata cikin Hayyacinta har yanzu Aminene bata Dawo ba Amina ce da kanta yanzu..!
Ta manta da Hannunsu dake Waje Daya sai da taji ya Sabule hannunta Sannan ta Dago suka hada ido Saurin Dauke kansa yayi saboda wani irin abu yaji acikin ransa kamar na Tsausayi itama kanta ta Dukar tana wasa da Hannunta gabadaya kalaman Baba Mallam sun gama riketa ita kuwa me ta aikata ne..?
!Da Alherin Baba Mallam da Hajiya ya Lullbe Rayuwarta haka..? Har Abada bazata manta dasu ba kamar yadda bazata manta da kaddaran data Hadata da Masoyinta Aminu ba..!
Baba Mallam yayi gyaran Murya yana Fadin"Umaru me ka yanke kan Mamana..?Ina Nufin kana da wani Tsari ne..?
Kansa na kasa har Lokacin yace"Tsari na na Ubangiji ne Mallam..ba ni da wani Tsari..!
Sai dai bazan ki duk abunda ka Zartar ba..!
Baba mallan yaji Dadi Cikin Fara"a yace"Naji Dadin haka shiyasa na Tambayeka..Zan yi ma Mamana adalcin da nake yi ma kowa..Bazata Tare ba sai ta gama makaranta Umar..Nan da shekara Daya da wani abu kenan tunda Hajiya tace suna aji Daya na Babbar makaranta sun kusa shiga Aji Biyu..!
Zata kamallah makaranta da Walimar sauka zan hadata da sauran yan"uwanta Hamida da Hannatu da Sa"aadatu na aurar dasu ita kuma sai ayi Bikin Tarewarta alokacin bazan karbi Uzurinka ba na baka Lokaci ka Tsara komai inda zaka ijiyeta da yadda zaka zauna da iyalanka..!
Goggo Husai tace"Mallam me zai hana tunda anriga an Daura ayi Tarewan ba Nisa?
Kai ya Girgiza kafin yace"A lokacin Auransu nayi gaggawa Husai..ban kuma bama yaran nan dama ba Husai..Bana so na kara maimaita irin haka Shiyasa na Dibi wannan Lokacin bana Fatan wani Daga cikin su yaji aransa ban mai adalci ba..!

Ba wanda bai gamsu da mganarsa ba Ya Danmallam kamar ya goya Mallam haka yaji dama Fargabansa ace ya tafi da ita ko kuma mganar Tarewa Amina kuwa acikin ranta itama Hamdala Take yi Domin bata shirya ba..Bata Shirya karban wannan Kaddaran ba Har yanzu..!
Goggo Husai tace"Shikenan..Ni na Dauka zaka hadata dasu Zeenatu ne.?

Kai ya girgiza kafin yace"A"a ai ba Sa"aninta bane..So mganar su ma tana nan Rasuwar nan ne ta hanani nayi mgana yaushe ne zasu fara Jarabawar Fita ma kikace Hajiya..?
Hajiya tace"Sati na sama Abida tacemin Mallam.!
Cikin Dattakonsa yace"Zan bama Mazajensu dama zasu fara zuwa su gana dasu..Mai son Zeenatu dan wajen Aminina Mallam Hamza ne Dake Gombe,Babbar D'ansa Ahmad Soja ne..Sai mai son Abida na gida ne Jikan kawuna Lawali na Bazanga Dake Jamus..? To yaron wajensa ne Yana Porthercourt yana aikin Zanen gidaje ko wannan Gaisuwan da suka zo shi kawu Lawalin ya karamin mgana..!
Goggo Husai ta fara fadin"Masha Allah..Allah yasa a kulle alheri..!

Aba ma yayi fatan Alheri shi da Hajiya
Baba mallan ya kalli Danmallam yana Fadin"Baka ce komai ba Umaru..?
Cikin Ladabinsa yace"Hakan yayi mallam..Allah ya saka da Alheri ya kuma kara girma..!
Cikin Fara"a yace"Ameen Allah yayi muku albarka..Tashi kaje ka Dauki iyalanka kuje gidanku ku huta..Ina fatan zaka kwana Biyu kafin ka koma..?
Cikin Kankantar dakai yace"Jibi zamu koma Mallam..Saboda aikina na iya adadin kwanakin da aka bani kenan..!
Baba Mallan ya Jinjina kai yana Fadin"Shikenan Allah ya kaimu..Mamana tashi ki bisa ka rakata har kofar gida ko wajen Hajiya zaki kwana..?
Kai ta girgiza kafin tace"Eh..!
Da sauri domin bata son ahadata dashi jin haka yasa Danmallan yayi musu sallama ya Fice daman shima Takuramai Mallam zai yi ko Cikin gida bai koma ba ya Kira Sakina awaya yace ta fito su tafi..!
Amina kuma sai da tattabatar da sun tafi Domin taga Budewar get da Fitan Mota ta kuma tabbatar da Shine sannan tayi musu sallama ta wuce shashen Hajiya..!
Koda taje har ya Abida tayi barci sai ya Aisha ce da ya Zulaihat ke zaune ashen nan sukayo Dadi taji Dataga su hanne da Hamida Zafira sun koma gida Tun jiya..!
Bata ma kowa mgana ba Kujearan falo mai zaman mutum uku ta Dungule akai tana Sauke ajiyar rai su kuma sai suka sauya hira daman Hirar Aminar Suke da Al"ajabin Auranta da Yaya Danmallam,Sai dai kuma ko su Hanne da sukasan Dalili basu ce komai ba Domin Sirrin Amina Wajensu bazai Taba Faduwa ba koda ba awaje bane na gida ne..!
Sai awannan ranar Amina ta samu barci Domin batasan Dawowar Hajiya ba
Washegari kuma su ya Jawahir suka fara tafiya,sun yi kuka Lokacin sallama kafin yammh gida ya Rage sai ya Jadwa da Goggo Husai da Goggo Jumai duka sun koma Gidajensu har su ya Zahra..!
Chan gidan Baba Mallam ma Duka sun koma gidan auransu gida yayi tsit dayan washegarin kuma Ya Danmallan suka koma shi da Sakina Basu hadu da Amina ba itama Goggo Husai taji Tana mganar Tafiyar tasa..!
Tun Ranar ashashen Hajiya suke kwana har Hamida sai da su goggo Husai suka samu Visa suka tafi gida ya zamana ba kowa yasa Hajiya tace su Amina su koma basoda Mamanmu kada kadaici ya Dameta..!

Kwana Goma sha daya da Rasuwar yaya suka koma gida ya rage daga Amina sai hanida sai zeenatu da Jawaad sai mamanmu da Aba. !
Sati biyu da rasuwar suka koma makaranta Boko da Islamiya,Saboda zasu fara jarabawa su ya Zeenatu har sun fara Neco..,!
Komai ya tafi kan tsari sai dai Abu Daya ne yayi ma mamanmu cikas Wannan Raunin data so gani awajen Sa"idu bata gansa ba sai ma wani Takwalli Daya shigesa..!
Ko sau daya bai zubar da Hawaye agabanta ba..!
Balle taga Rauninsa ko kananan kukan gulma take sai dai ya kalleta yace"Muma fa jiranta muke yi Balaraba..Hadiza batayi gaggawa ba..!
Fatanmu Allah ya rahamsheta..!

Bata gani ba har yau bata gani ba..Sannan Gurbin yaya har Abada Sa"idu bazai taba bata ba..bayan Mutuwar taso komai ya zama karkashinta abunda bata sani ba Allah ya riga ya Rubuta kaddaran kowa ciki harda nata in ta Kauda yaya to ba Lalle ta samu cikar Burinta ba zata samu wani wanin kuwa har ta koma ga Allah bazata taba samun sa ba..!





*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️25*

*BAYAN WATA DAYA..!*

Acikin Wata dayan daya gabata na rasuwar yaya komai ya fara dawowa daidai,Wadanda akayi ma rashi sun Dauki Dangana da Tawakkali,Mussaman Aba da su Amina da yanzu ta fara dawowa da Walwalarta sai kuma yanzu take matukar kulawa da Jawaad tana Taausayinsa gani take daga shi sai ita sukayi rashin yaya basu da wata matsala Domin mamanmu tana Tsaye kansu da Fuskar da suka santa da ita,ya taimaka wajen dawowa da walwalar yaran har wadanda ke gidan auran nasu,Uwa uba ga Hajiya babba da bata bari sun yi kukan maraici ba Duk da ga Mamanmu tare dasu tana zaryan zuwa Dubasa barin ma in Taga Amina ta kwana Biyu bata leko ba
Acikin kamshin Nasaran da Mamanmu take gani ta Samu bayan kasa ta Shafe Idon yaya abu Daya ne zuwa Biyu na Farko ta samu yardan yan"uwa da Duka Dangin Baba Sa"idu sannan Aminci Data gina shekaru masu yawa da yaran bai gurbace ba yayi mata amfani sosai gabadaya su ya jafar da komai nasu yana Tafin Hannunta ne tun yaya nada rai yaran da ita Suke shawara sai dai yayan taji Daga bakinta to har yanzu bata Sauya Zani ba ballatana yanzu da ba Uwarsu sai Duka yardan da Amanan ya koma kanta Harta kuwa Jafar da Abaya yake da Kulafunci nuna yaya ce uwarsa ba Ita ba shima yanzu wani girma yake bata kamar me yana ganin ta tamkar makwafin yaya..!
Gida ya zama nata ita kadai Yaran suna Tafin Hannunta sai dai Abu Daya ya Gagareta Samun SA"IDU yadda take so,Sannan kuma wannan Raunin da taso gani atare da Sa"idun bata gansa ba,Sai ma wani Jarumta da Takwalli bata so ta gansa Tsaye kan kafafunsa ba taso ace yana kwance ne yana Fama da wannan Babban rashin sai Taga akasin haka sai dai bata Sare ba ai ta Rabasu Wannan kallon kauna da Tausayin Sai dai in ya Bita chan Lahira ya nuna mata anan Duniya dai ta gama Shiga Tsakaninsu..!

Bayan Bakwai da rasuwar yaya ta kasa gane kansa ya daina cin abinci baya Fara"a baya Hira da ita ballatana mgana mai Dadi haka zasu kwana su tashi in ba ita tayimai mgana ba shi bazai ce mata ba  tasan wani Lokacin bai da Hayaniya ammh tasan Rashin mganarsa yafi Faruwa akanta In yaya ce keda Turaka kusan Raba Dare suke suna Hira cikin Nishadi bata san Darare nawa ta bata cikin bakincikinsu ba Domin tana Daga Dakinta in Dare yayi tana jin tashin muryoyinsu In kuma ranar itace keda shi Daya gama cin abinci yayi wanka Sai ya fara Hamman barci tana mai Hira sai ya fara barci ma"ana baya son Hirarta ta Dade tana kunsan bakincikin Sa"idu shiyasa bayan Rasuwar yaya ganin zai bata wahala yasa ta sa madina ta kai ma malaminsu korafi aka Samo mata kansa shine har ta Fara Tunanin Burinta ya fara cika Sa"idu da komai nasa yana Hannunta..
Tunda yanzu In ya dawo aiki yaci abinci yayi wanka ya kan zauna su yi hira koda bazai amsata yadda take so ba ammh cikin kaso goma tana da Nasaran kaso Takwas aciki Abunda ya Rage mata shine ta fara sanin komai nasa kamar yadda yaya ta sani sai dai har zuwa yanzu yaki bata Damar haka!

Yau ma kamar kullum safiya ranar asabar ce ta hutun karshen mako,Ba kowa agidan duk sun tafi Hadda,Sai ita kadai da Aba bai fita yau da wuri ba,Kamar yadda ta tsiro dashi yanzu Gari na wayewa kafin Aba ya fita sai ta Chaba kwalliya Kamar wata yarinya bayan makircin karkashin kasa har da na Kissa Madina tace ta Dinga Hadawa duk a Kokarinta na sai taja Hankalin Sa"idu akanta gabadaya..!
Abunda bata sani ba ita zuciya ba"ayi mata Dole kan abunda tagani kuma tasan dashi ammh ta nuna bata so..Sannan duk da tana son mai kyautata mata bata cika bashi matsayin daya Zarta wanda ta zabe ta da kanta ba koda bai taba mata wani abu na Alheri ba..!
Zaune suke afalonsa yana karyawa ita kuma tana gabansa kamar mai kirga yawan Numfashinsa Hira take yi mai yana jinta yawancin Labaranta ba wasu masu amfani bane,Shiyasa yake mata Shuru kawai batare daya tanka ta ba,Har kuma gobe bazai daina kukan Rashin Hadiza bai jin zAi iya mantawa da ita.
Jin tayi shuru yasa ya Dago Daga cin Soyayyan Dankalin data soyamai ya ganta tayi Tagumi tana kallonsa Cikin dan mamakinta yace"Lafiya..?Me kike Tunani..?
Alokacin bakincikin Tambayarsa taji Saboda tafi kama data rainin wayau ta Zauna tanayimai Hira yayi mata banza sannan ya Dago yana ce mata Lafiya..?Saurin Daidaita kanta tayi ammj bacin rai yasa Kiris ya Rage Dayan Fuskar tata ta bayyana.
Cikin sosa ido da hanci ta fara fadin"Yaya na tuna..Bana iya kwana na Wuni ban yi kukan rashinta ba..Ballatana in na gifta Dakinta sai naji gabadaya Duniyar ta Juyamin baya..!
Tana Fade tana matso hawaye kamar gaske ya Dade yana kallonta kafin ya maida kansa ya cigaba da cin Dankalinsa yana jinta tana Fadin"Wlh nima sai naji Duniyar duk ta isheni Abbansu..Dama nima na mutu kamar yadda yau ba yaya adaron Duniya..!
Sai da ya Kurbi Tea din Dake hannusa sannan ya Dago yana kallonta Cikin Sanyinsa na koda yaushe yace"Zo nan Balaraba..!

Baki ta bude tana kallonsa Ganin haka yasa ya gyada mata kai alaman tazo ba musu ta mike ta isa kusa dashi ta zauna Juyowa yayi suna kallon juna Hannayenta ya kama Duka ya Rike yana Tuna Nasihan Baba Mallam aranar da Hadiza tayi arba"in da Rasuwa ya Horar dashi Kada rashin Hadiza yasa ya cutar da Balaraba ya sani Ko sau Daya ya Danne mata Hakki Allah zai tambayesa..!

Cikin Idanuwanta ya kallah kafin ya fara fadin"ki daina Fadin haka Balaraba..Mutuwa ta Allah ce..Hadiza batayi gaggawa ba sannan muma da muke Duniyar jiranta muke..Ko yau ko Gobe zamu mutu..Saboda haka ki Sani Hadiza tatafi ba domin tana son Tafiya ba..Addu"rmu take Bukata ba kuka ba..Don Allah in kin Tunata,ki Dinga mata addu"a don Allah..!
Kai ta gyada tana kara Jan hanci Lokaci Daya tana fadin"Wlh Abbansu na kasa ne..Kullum in na tunata sai nayi kuka..Barin ma in na Juya naga gidanan yanzu Dagani sai kai yau babu Yaya..Sai naji kamar nayi ta kuka har Abada..!
Sharr sai

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment