Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta Kira Baba Mallam wanda mamaki ya kamasa ganin Hajiya zaune gefensa suna Hira Cikin mamaki yace"Yau kuma Zolaya kike ji ne Abu..?
Kallonsa tayi kafin tace"zolayar mene Mallam..?
Wayarsa ya nuna mata yana Fadin"Kirana akeyi da wayarki fa..!
Cikin mamaki tace"To lafiya..?Wayata tana Daki na barta fa!
Jin haka yasa bai ce komai ba ya Daga Kiran kukan Hanne ya fara ji tana Fadin'Baba Kazo gidan Baba Sa"idu..Ya Jafar zai kashe Amina da Duka kazo da sauri..!
Baba Mallam Zumbur ya Mike Cikin tashin hankali yake tadin"Hajiya Wani abu ya sake faruwa..Muje gidan Sa"idu..!
Hajiya ta fara salati Hankalinta tashe ta Rarumi hijabinta ta saka Baba Mallam na kan gaba suka Fice Daidai Anty Amarya ta fito zuwa shashen Mallan taga fitarsu Cikin gaggawa tasan ba Lafiya itama sai ta Rufa musu baya ganinsu sun shiga gidan Baba Sa"idu yasa aranta tasan ba Lafiya Domin Baba Mallam baya zuwa gidan Baba Sa"idu haka kurum wani abu bai faru ba.
Cikin azama tabi bayansu Domin tana son Taga abunda ke faruwa..!
Abunda Su Baba Mallam suka gani Sai da Hankalinsu ya tashi Ya Jafar yayi m Amina Dukan kawo wuka Baba Mallan ne ya karbe sandan Hannunsa yana Fadin"Jafaru ashe baka da Hankali ban sani ba..?
Ya jafar na haki yace"Baba Mallam so take ta kashemana iyaye da bakincikinta..Shanshancinta ya wuce Tunanimku yau fa ganinta nayi a nan kofar gidan Rumgume jikin wani kato Mallam..Amina fa nawa take..?
Har ta gama lalacewa haka bamu sani ba..Shine kafin ta kashe su gwara ita ta Fara Binsu..!
Karaf manganganun akunnin Anty Amarya Data shigo Salatinta kawai akaji Tana Fadin"Innalillahi wannan yarinyar Tabbas zakka ce..Iskancinta nata har yakai haka bawanda ya sani..?
Kallonta kawai sukayi kowa ya kasa mgana Hajiya,Amina ta Duka ta Rumgume jikinta Duk ya Fashe da Duka Fadi take"Jafar kayi dukan ganganci..Ba haka akeyi ba..!
Mamanmu na gefe tana ta kuka ita da Zeenatu harta Jawaad Dake barci hayaniya ya tadashi ganin Dukan da Ya Jafar kema Amina sai shima ya Fara kuka..!
Baba Mallam Hankalinsa ya tashi Ya kalli Jafar yana Fadin"Ina Sa"idun..?
Da kyar yace"yana Dakinsa..!
Baba Mallam ya wuce gaba yana Fadin"Hajiya ki taikama Mamana..Kai kuma muje Ciki..!
Da haka ya tasa Jafar suka shiga Falon Aba Hajiya kuma Da Mamanmu suna Hawaye suka Daga Amina da Idanuwanta basa Buduwa Sai faman wash Wash take da kananun kuka Kilama ya Tardagata inji Hajiya Zeenatu ta kama musu suka yi Dakin Mamanmu da ita sai Lokacin Hamida da Hanne suka fito ganin Halin da Amina ke ciki suka Hade kai suna ta kuka Anty Amarya Fadi take"Ruwan zafi za"a Dafa ayi mata gashi..Allah ya kyauta bai mata karaya ba kinsansu in suka Fara Duka kamar mahaukata..!
Hajiya taji kamar ta Make bakinta sai dai batayi mgama ba batama san ya akayi tasan wani abu na Faruwa ba domin Anty Amarya sai dai ta Fadama wani Halinta..!
Ashashen Aba kuwa Baba Mallam suna shiga suka gansa kwance kan kujera Takure yana rawan Sanyi Fadi yake"Hadiza sanyi nakeji ki sakamin bargo..!
Baba Mallam ya Duka agabansa yana Fadin"Ashh Sa"idu me zan gani haka..?
Yana jin muryan Baba Mallam ya Bude ya Rarrafa ya tashi Zaune yana Cijewa Baba Mallam ya rikesa Hannunsa ya kamkame yana Fadin"Baba don Allah ina so cikin Almajiranka masu karatu ka Tallata Amina in akwai mai so..Bana so wunin gobe ya kare ban aurar da Amina ba..Ina jin tsorom wani abu ina Fargaba kada watarana Bakincikinta yayi ajalina..!
Baba Mallam yace"Baza "ayi haka ba kana cikin Fushi Sa"idu.
Mu Tsaya mu bincika zuwa gobe zan yi mgana da Mamantawa kan yaron Dake zuwa wajenta in har ya Chanchanta zan bashi Mamana..!
Jikin Aba na rawa yace"A"a Baba..Na riga nayi Rantsuwa ko bayan Raina Amina bazata samu abunda take so ba..Bata isa ta fita Zakka ba..Kada ka Saurareta Nidai ko Waye ka aura mata ta bar gabana na Daina ganinta ko zan samu Saukin Abunda nakeji..!
Baba Mallam yayi shuru yana kallon Baba Sa"idu ganin haka yasa ya kara Rike hannunsa sai Hawaye sharr yana Fadin"Kada kace A"a Baba Mallam
Kayimin wannan alfarman a mtsayin ka na Uba gareni ka yafemin in har ahalima suna goga maka bacin suna ka yafemim..!
Ya karishe Fada Cikin kuka,Da Jikin kowa saida yayi sanyi Baba Mallam yace"Kul..Kar na Sake ji..Kai jinina ne Sa"idu har gaban Abada..Kada ka Damu Zan aurar da Mamana kamar yadda ka Bukata sai dai bazan mata auran kaskasaci ba kafin waye wan garib gobe Allah zai bayyanamana Mijinta mafi Alherinta aduk inda yake Sa"idu kayi hakuri kada ka aibatata kila ita irin Tata Kaddaran kenan..!
Aba bai Sake mgana ba Tari ya Sarkesa kamar zai sheka Ya Jafar da Yaya suna Rike dashi yaya kuka kawai take Yadda take ji aranta baya Misaltuwa ita ta Haifi Amina Radadin da kowacce uwa take ji in Wani Daga Cikin D'anta ya zama zakka..!

Ganin Halin da yake ciki yasa Baba Mallam yace su tafi asibiti haka kuwa akayi Ya Jafar ya Tuka Motar Mallam dashi da Yaya suka tafi asibiti da Aba su Hajiya kuma suna tare da Amina da tasha gashi Ta samu Targade a Hannunta na Hagu da gocewar kashi a Kafarta Mamanmu da Hajiya suka Shafe mata da man zafi tana Hawaye sunayi Mamanmu ma kasa zama tayi ta koma Cikin Bedroom dinta tana kuka Anty Amarya na nan bata tafi ba da anyi abu sai ta Tafa Hannu tana Fadin"Oh..Allah dai ya shiryamana..An haihu dai a Ragaya..!
Sai da Hajiya ta gaji ta tanka mata da Cewa"Ki kama bakinki Domin kema Uwace..Akwai Sa"adatu da Sabeeha agabanki bakisam ina Kaddara zata kaisu ba!
Jin haka yasa ta Fara Fadin Hajiya na mata Mugun fata Cikin gatsali tace"Allah ya Tsareni kowa yasan ya"yana basu fita zakka ba..Daman ai wanda yasiya Rariya yasan zata Zubda Ruwa..!
Ba wanda ya kara bi ta kanta kuma taki Tafiya kamar mayyah har sai chan Dare Baba Mallam ya Dawo Jinin Aba ne yayi sama An bashi gado ya Jafar na wajensa zai kwana sai alokacin suka koma gida bayan Baba Mallam ya kwantar ma da Yaya da suka Dawo tare ita da Mamanmu hankali da kalamai masu sanyaya rai sun Daina kuka Amina kuma ta samu barcin Wahala Baba Mallam yace zuwa da Safe mai gyaran Targade zai zo ya gyara mata.
Sanda suka koma gida Dagashi har Hajiya sun kasa Runtsawa Fadi kawai Take"Na kasa gane meke Faruwa Mallam..?
Nasan Jafaru bazai yi karya ba..Nasam jikina na bani Amina ba haka take ba..!
Baba Mallam yace"Wani al"amari ne da Allah kadai yasan me ya Lullube aciki..!
Nan ya shiga Fadamata yadda sukayi da Baba Sa"idu ta sauke Tagumi tana Fadin"Kai..wata sabuwa to menene Mafita..?
Baba Mallam yace"zan kwana Istikara Zuwa Safe Boyayyan al'amarin zai bayyana Hajiya kema ki tayani..!
Da kai ta amsa mai,Tabbas sun kwana Gayama Allah Hajiya ce ma wajen Uku na Dare ta kwanta Baba Mallam sai karfe 4 ya iya barci saman Darduma bai tashi ba sai da yaji wayarsa Dake cikin Aljihunsa na Ringing yayi Zumbur ya Mike yana Lalubota yaga DANMALLAM.. !
Ne ke kiransa ajiyar rai ya Sauke ya Daga wayar da Sallama Dagachan bangaran Umar ya amsa cikin Sanyinsa yana Fadin"Baba..Nasan yanzu asuba ne a Nageria shiyasa na Bugo Domin na samu ladan tashinka Duk da nasan kila ma kana masallaci..!
Baba Mallam ya Mike a kasalance yana Duba agogon bangon Bedroom dinsa 4:55pm na asuba..!
Cikin karfin gwiwa yace"Na makara yau Umaru..Naji Dadin kiranka Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Amen Cikin Farinciki kafin suyi sallama suna gama wayar Baba Mallam yayi kasake na wani Lokaci kafin Lokaci Daya Mirmishi ya mamaye Fuskarsa Hajiya ya kallah Dake barci ya karisa ya Bubbuga Gefen gadon yana Fadin"Hajiya..Hajiya..!
Mika tayi Cikin Tattatusan lafazi yace"Ki tashi mun makara sallar asuba..!
Mikewa zaune tayi tana Mutsike ido Lokaci Daya tana Fadib"Mallam kasamu mafita kuwa..?
Wlh da yarinyar nan na kwana araina ita da Sa"idu..!
Cikin Mirmishin data kasa gane masa yace"Kada,ki damu..Cikin ikonsa ya kawo mana Mafita tashi kiyi sallah ki shiga gidan Sa"idu ni kuma Daga masallaci asibiti zan tafi na Dubasa..!
Kai ta gyadamasa tana kallonsa ya saka akyabbansa da Rawaninsa ya Fice acikin ranta tana Tunanin wata mafita Mallam ya samu wannan Fara'ar dake fuskarsa ta bayyana Koma wata Mafita ce ta zauna sosai acikin Ran mallam din.!


Ina godiya sosai masu sharhi yan wattapad ina gaisuwa..!



*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️21*

Suna idar da Sallar Asuba Baba Mallam bai Tsaya ba Ya Nasir ya Tukasa zuwa asibitin Tunda shima nan ya sallaci sallar asuba Ya jafar tun Daran jiya ya kirashi ya fadamai kafin su tafi sai da Baba Mallam ya Umarci Shamsu daya kira Mallan ya"u mai Dori yazo ya Duba Amina..!
Haka kuwa akayi gari na waye bakwai na safe Ya shamsu yazo da mai Dorin,Koda yaje Hajiya Babba tana gidan Amina jiki yayi Tsami sai faman kuka take ashe kadan tayi Domin wajen gyaran Targade da Goshewar data samu sai da ta raina kanta sai da su Hajiya da Mamanmu suka Riketa Hamida da Hanne suna ta kuka Ranar ko shirin zuwa Hadda ba wanda yayi acikin gidan sai dai chan su Sa"adatu ne Idi Direba zai kaisu..!

Yaya kuwa Hada hadar abun karin da zata kai asibiti take yi ko afuska bata bayyana wata damuwa game da Amina ba Ita ta Aba take yi,ammh sai dai karkashin Ranta Damuwa ne Dankare wanda Tsabar kawaicinta yasa bata bari a Fahimceta ba, sai dai fa Uwa uwa ce kuma bazata Haifi abu da Cikinta tace kuma bata kaunarsa ba sai dai kawaici da wasu abubuwan da kansa Uwa ta kauda kai kan abunda ta haifa sanin Halinta ma ba wanda yabi ta kanta Domin kowa yasan Yaya bata taba Shiga Sha"anin Amina sai abun yaci Tura yakai mata makuran da zata tanka..!
Ya bada mgani an shafa mata Cikin kwana Daya ammh Amina ta Fita Hayyacinta ta rame sai ido,Tasha wuya cikin kwanakin Wuyan da bazata taba mantawa da ita ba Hamida da Hanne sun fi kowa sanin Amina tafi kusa dasu shiyasa lamarinta yafi Damunsu gabadayansu suma Suku suku suke kamar basu da Lafiya sun tasa Amina da Tagumi tana kallonsu sai dai yau karon Farkon Bakin Amina ya Mutu bata mgana sai ido sai kuka acikin Ranta wani abu ne mai Girma Tana ji ajikinta komai yazo karshe ta rasa Aminu shima ya rasata sannan abu mafi girma tana jin kamar wata Kaddarace zata faru da ita yasa abubuwa suka kwabe mata Lokaci Daya sai dai koma menene Tayi alkawarin bazatace komai ba Tunda mai Faruwa ta Riga ta Faru babu Tsumi babu Dubara..!
Dakyar Hajiya ta Lallasheta tasha Tea da Panadol Saboda Zazzabin Jikinta sai ta samu barci sai alokacin suka samu Daman karyawa Mamanmu da Yaya suna shirin Tafiya asibiti duk da sunyi waya da Ya Jafar yace ya Dawo gida Ammh Baba Mallan nachan suka barsa tunda safe Ruwan zafi ma Nasir ya koma gida ya Taho dashi Da kayan Tea..!
Ya Abida ta shigo ta Duba Amina kafin su wuce Hadda ya zeena ma bataje ba su Sa"adatu ne suka tafi dasu ya Akilu sai Umaimatu,Misalin karfe Tara na Safe Hajiya Babba da Yaya da Mamanmu da Anty Shamsiya matar ya Jafar suka tafi asibitin da aka kwantar da Aba domin su Dubasa shi kowa kagani rai da zuciya ba Dadi.
Wani private Hoptal ne Daki na Musamman Aba ke ciki Vip.
Suna shiga Baba Mallam kadai suka Iske awajensa Aba din yana ta barci su Mamanmu suka gaisheshi Cikin girmamawa ya amsa yana Fadin"Mungodema Allah..Ya jikin uwar tawa?Nace shamsu yazo da Mallam ya"u sun zo kuwa..?
Wannan karon Hajiya ce tace"Eh har ya gyaramata ya bada mgani an shafa mata tasha mgani koda muka fito ta samu barci..
Ya shi Sa"idun..Ya farka kuwa..?
Baba Mallam yace"Eh ya farka da Safe jikinsa da sauki sosai bai dade da komawa barci ba koda Nasir ya bar nan muna ta Hira dashi..!
Gabadaya suka amsa da Alhamdulillah mai sunan Mallam ne Dake bayan Shamsiya ya fara kuka Mallam yace Hajiya ta karbo shi ,ta kwatoshi daga baya Ta mikama Hajiya ita kuma ta mikoma Mallam ya saka Hannu Biyu ya karbesa yayi wayau Yayi girma kansa ya dafa yana Tofamai addu"a sai da ya gama sannan yace"Ciwon kunnin nasa fa.?
Kan Anty Shamsiya na kasa tace''Yayi sauki..yadaina kukan tun jiya daddare..!
Baba Mallam ya gyada kai yana Fadin"In muka koma gida zan bama Jafar wani mgani ku rika Digamai Daga Saudiya nazo dashi..!
Kai ta gyada kafin tace"Jiyan ma Da daddaren wajen Mamanmu yacemin zai zo ya karbo masa wani mgani shine baidawo ba sai waya naji yana Fadamin yana Tare da Aba a asibiti..!
Baba Mallam yace"Wlh kuwa..Ammh ai da sauki yana ta cewa ma a sallameshi ya koma gida..!
Mamanmu tace"Daman ai baisan zaman asibiti..!
Hajiya tace"Sai hakuri ya bari ko zuwa gobe ne in ya kara jin Sauki..!
Suna cikin mganar ne Aba ya Farka Daga barcin daya kwasheshi suka fara Rige rigen mai sannu Mamanmu tana kokarin Taremai Filo Sai Yaya ta rigata sai ta sakarmata Ya jingina da Filo sannan ya tashi yana amsa gaisuwansu Lokaci Daya yana Binsu da kallo cikin Tsausayinsa Yaya tace"Ga Ferfesun kayan ciki nayo maka..In zubo maka zakaci..?
Mirmishi ya saki kafin yace"Zubomin Hadiza..Nagode Allah yayi miki albarka..!
Akunyace ta amsa ta Duka tana Zubamai Cikin Filet din da tazo dashi,Kadan yace ta zubamai ta mikamai ya karba Baba Mallan na Fadin"Ashe girkinta kake jira shiyasa bayan Ruwan Tea kaki cin komai..Duka abincin da matan yaran nan sukayi bai taba komai ba Hajiya..!
Dariya tayi tana Fadin"Sa'idu ne fa..Tun farkon auransu Girkin Hadiza yasa ya faramin yajin cin abinci kaga Tunda yayimin yaji nasan Hadiza ta Curi Tuta..har yayi aure adakina Sa"idu ke cin abinci Mallam har haushi yake ji na kwace masa yaro..

Gabadayansu Dariya sukayi Saboda yanayin yadda sukayi mganar Aba ma sai da ya Murmusa bai ce komai ba yana kallon Yaya basu sani bane aduniya ita kadai ce macen da yake Fatan Har aljannah ta zama matarsa Saboda kyawawan Hallayarta Tunda suka zama miji da mata shekaru aruaru bai taba ganin Ranar data Daga Muryansa sama da tashi ba..Yana kokarin Boyewa ne Sai Hadiza matsayinta Daga Allah ne ko ya Boye Kaunarta bazai taba Boyuwa ba Tana da wani irin girma acikim Idonsa da Rayuwarsa da ba wanda ya sani ita yake kallo yana jin zuciyarsa na Sauka Duk da cikin Halin Dayake ciki ita kuma kanta na kasa tana da kunya ballatana gaban Hajiya da Baba Mallam..!
Yaci kuma Ferfesun duka ya Cinye ya Dora da kayan marmari sai gashi garas dashi sai dai kallo Daya zakayimai kasan yana cikin Damuwa,Ya Jafar daman bai shigo ba sai gasu shi da Nasir sun shigo suka kara gaida Aba daganan su Mamanmu sukayi sallama dasu Jafar zai maidasu Gabda zasu fita Hajiya ta dawo wajen Baba Mallam daya mikama Jafar takwaransa yana jadaddamai yazo zai bashi wani mgani Jafar din ya Juya kenan Hajiya ta kalli Baba Mallam tana Fadin"Mallam naji bakace komai ba Har yanzu..?
Kallonta yayi yana Mirmishi kafin yace"Nazir ya Kirani da Safan nan yace yana ta kiran wayarki baki Dauka ba..Sai daga baya Abida ta Daga kiran tace baki nan kina gidam Sa"idun..!
Kauda mganar yayi ta sani tace"Ina na sani..Gida na bar wayar..Suna Lafiya ko..?
Yace"Lafiya lau..Shehin ne dai ba Lafiya yacemin kwanansu Biyu asibiti Ciwon ciki ammh sun dawo gida shine nake fadamai nima ina asibiti ga yayansu Sa"idu ba Lafiya..!
Hajiya tace"Assh..Allah ya Sauwake in na koma na natsu zam kirasa..!
Kai ya gyada mata bai ce komai ba,sai ta kalli Aba da hankalinsa baya kansu ya Lula Tunanin Halin da Amina ta Jefasa Cikin Damuwa Hajiya tace"Sa"aidu wannan Tunanin babu Riba cikinta..Ka kwantar da Hankalinka ba wata mtsala insha Allahu..!
Aba ya sauke Numfashi kafim yace"Hajiya in ban aurar da Amina yanzu ba..Watarana Jidalinta zai iya ajalina..Kinga Hadiza bata mgana ko..?
Na rantse tafini jin Dacin Amina tafini Sanin Ciwonta Domin itace uwa gareta ina Tsoron yadda take shanye abubuwa watarana Amina ta Dauko abunda zai yi sanadiyar zuciyarmu ta Buga Dukkanmu mu fadi mu mutu..!
Hajiya ta kama baki tana Fadin"Assh..Haba Sa"idu bama zai taba Faruwa ba..!
Tari ya farayi sai kuma jikinsa ya fara rawa Da Sauri Hajiya tace"Mallam yace komai zai daidaita ko ba Haka ba..?
Tafada tana kallon Mallam din wanda ke kallonsu bai ce komai ba Rawanin kansa ya gyara kafin yace"Insha Allahu..Zan Daura ma Amina aure in an idar da Sallar azahar da yardan Allah..!
Baba Sa"idu da Hajiya suka kallesa da mamaki Aba ya rausayar dakai yana Fadin"Ina fata da bada wannan Lalattacen yaron da suka gama Lalacewa bane ko..?
Baba Mallam ya yi mirmishin su na manya kafin yace"Bashi bane Sa"idu..!
Hajiya tace"To waye ne Mallam..?
Sai da ya kara Murmusawa kafin yace"Da wanda Allah ya kaddara..Shine dai wanda Allah daman ya Rubuta Mijinta ne dashi za"ayi..!
Hajiya daman tasan bazai fada ba Tunda bai iya fadamata ba kuma bai Fadama Sa"idu ba to Tattabata bazai Taba Fadama kowa ba..!
Aba ne yace"Kada ka Tursasama Mutumin Kirki sai ya aureta Mallam..Ka hadata da irinta sannan ka Sanar da kowaye halinta Baba..Kuma ina so aje a gwada Amina kada yazo wajen Lalacewarta ta Samo wata cuta..!

"SA"IDU..!

Baba Mallam ya katsesa Cikin Tsawa da Bacin rai kafin yace"Kul na Sakejin wannan mganar daga bakin ka..ina da yakinin Har Abada acikin zuru"ata baza"a samu bara Gurbi ba...Duk da Allah na Jarrabatan bayinsa ta kowani Fanni Ammh ta wannan gabar ban yarda ba..Amina bazata taba Rusa Tarbiyarmu ba Sa"idu ba abunda zan ce ma wanda zai aureta illah ya Rikemin ita Amana kuma in Cucuta koda abayan Idanmu ne Ban yafe MASA BA..!
cikin kaushinsa ya karishe mganar da ta ja Hankalin Aba da Hajiya suka kalli juna bai kuma basu zarafin mgana ba ya kalli Hajiya yana Fadin"Kinsan suna jiran ki ko?
Kai ta gyada kafin tace"Shikenan Allah ya kara afuwa..!
Har ta juya zata tafi Baba Mallam ya Kira sunanta ta juyo Cikin bacin ran da bai barsa ba yace"Ki fadama su Balaraba kada wata cikinsu ta kira yaran nan dake gidan auransu tace zata Daga musu hankali ko Husai ban yarda afadamata ba..!bana so a adaga musu Hankali..!
Hajiya tace"Insha Allahu ba wacce zata ji..!
Kai ya gyadaa mata ta juya ta cigaba da Tafiya har takai kofa zata fita ya Kira sunanta wannan karon a Taushashe ta juyo tana Fadin"Mallam..!
Kai Tsaye yace"Umaru ya kiraki kuwa..?
Cikin mamaki tace"A"a rabona dashi Tun shekaranjiya da safe..! lafiya kuwa.?
Mirmishi yayi kafin yace"Bakomai..Allah ya kaiku gida Lafiya sai na dawo.!
Hajiya ta jinjina kai kafin ta Fice ya bita da kallo Daman ai yasan bazai taba Kiranta ba Shi ya Haifi Umar ammh yana Daraja kyakyawan Dabi"ansa..!
Aba ne yace cikin Raunin Murya"Kayi hakuri Baba..!
Hannu ya dagamai kafin yace"Nace ne kada na sake jin irin mganar makamancin wannan abakin ka..Ba hakuri nace ka bani ba..!

Cikin Sauri Aba yace"Insha Allahu..
Sai alokacin Baba Mallam ya saki Fuska yana Fadin"Allah yayi maka albarka kaida zuru"arka Sa"idu.Har Abada ban taba Nadamar samunka Cikin zuru"ata ba..Ka warke da wuri ban shirya rasa Da"a na farko ba..!
Ya karishe Cikin barkwamci Da sai da Aba ya Murmusa Lokaci Daya Hawaye suka cika kwarmin idonsa yake Fadin"Nagode Baba..Nagode Ban taba jin kai ba Uba kake gareni ba..Ina Alfahari dakai..!
Baba Mallan yayi wani kayattacen Mirmishi kafin yace"Nima ina Matukar alfahari dakai Sa"idu..!

*******

Tana cikin Tiolet din Bedroom dinta taji Ringing din wayarta Allah yasa ta Gama wankan ta Dauro babban zaninta ta fito wayar tana kan Mirror dinta ne Jikinta yana digan ruwa takai Hannunta saman wayar wanda taga yana kiran nata ne yasa taji gabanta ya Fadi..!

"MALLAM..!

haka kurum mallam awannan Lokacin bazai kirata ba,Dazu Shamsu ke fadin yana asibiti wajen Sa"idu Har wayar ta kusa yankewa bata Daga ba sai Daga baya ta Daga kiran tana Fadin"Assalamu Alaikum Mallam..!
Dagachan Haraban asibitin Baba Mallam yace"Marliya kina ina ne..?
Cikin mamakinsa tace"Ina gida mana Mallam..!
Kai Tsaye yace"Marliya abunda ya faru jiya gidan Sa"idu kuskure ne da Rashin Fahimta ko..?
Cikin Mamakinsa da Tunanin inda ya Dosa tace"Hakane..!
Cikim Dattakonsa yace"To mu barsa ahaka..Kada na sake naji mganar nan ta fita..In har najita a waje Nasan kece..Bana son surutu da mgana Hajiya kinsani bata da wannan Halin Saboda haka ki kiyaye..!
Anty Amarya taji ta Muzanta Ranta ya baci wato Hajiya ba ruwanta itace mai Surutu ko lalle ne Mallan dinnan.!
Danne bacin ranta tayi tana Fadin"Ah..Wlh ban fadama kowa ba Mallam..yanzu dai nake shirin shiryawa na shiga gidan na Duba Amina ya jikin Sa"adun..?
Fata ya samu Sauki..!
Cikin son Dakile mganar yace"Yaji Sauki..Kada ki fita ko"ina nima ganinan zuwa. !
Bai jira cewarta ba ya Datse kiran yana wani nazari yasanta da kananun mgana sarai shiyasa ya taka mata Burgi in ba haka ba,kafin wani Lokaci ta gama Fesama ya"yanta su kuma su fara yawo dashi mgana har ta fita wacce bata da wani amfani..
Ita kuwa Anty Amarya Sororo tayi da waya a Hannunta mamaki bakin ciki da Kishi sun Turniketa wayar ta Dangwar nan saman gado tana Fadin"Aikin banza..Abunda kake son ka Rufe mallan bazai taba Rufuwa ba..Ko ba"a bakina ba Lalacewar Amina sai ya fita Duniya..!
Abunda bai sani ba ta Fadama ya"yanta Sa'adatu da Jidda da Sadiya Jidda ce kawai bata Dauki mganar ba Ammh Sa"adatu har tana Fadin daman idanuwan Amina na rashin gaskiya ne sannan abakinta Anty Amarya tasan Amina na karancen karancen Littafan hausa Sadiya dai da Uwar ta fadamata batace komai ba Domin bata cika Hayaniya ba.
Wayar Sakina tayi ta nema ta Tsegunta mata bata sameta ba Shiyasa da Tuni Labari ya isa Saudiya Arabia..!
Tana shiryawa tana Tsaki ita kadai ta rasa me Hajiya Babba tafi su da Mallam yake Fifitata akansu ta manta tun Tale tale Take tare da Mallam din kwafa tayi afili tace"Daga ita har Sa"idun duk sai nayi mganinsu Algumgumai duk su ke zuga Mallam..Da basu da Tuni nice Tauraruwa awajensa da gidan gabadaya..!
Abunda bata sani ba,ba irin Mallan ake ma haka ba ko ta manta Malami ne wanda bai zauna ba,kariyar Allah Tana Tare dashi kuma ilkonsa bazai bari acutar da bawansa ba..!
Baba Mallam na asibiti kafin ya baro ya Kira ya Jafar yace ya siyamai Dabono da Goro mai yawa zai yi amfani dashi bai damu ba sanin kila Mallam din zai yi wani abu dashi sai dai abu daya ya bashi mamaki Dayace su samu sallar azahar anan masallacin gida shima gashinan zuwa..!
Koda ya tafi Aba na barci Nurse tazo tamai allura kila tana saka barci ne shi kuma sai bai tashesa ba Idi Direba ya Kira yazo ya Daukesa zuwa gida Kai Tsaye Shashensa ya wuce domin ya Shirya Tunda azahar din ta kusa Shi kadai kawai yake jin karfin Gwiwa da alhafarin wani abu akaron Farko zai cika wani Burin Daya Dade acikin ransa bai Mutu ba kuma da Ransa..!
Wanka yayi ya shirya Cikin Shadda Fara harda babban Riga dataji aikin Hannu ya Dora rawaninsa sai ya Fito Tar dashi Farin gemunsa na kyalli yana tashin kamshinsa kamar koda yaushe adaidai Lokacin ya samu wayar Jafar yana Fadamai ya siyo abunda yace asiya din Baba Mallan yace yana cikin gida gashinan Fitowa..!
Bai Fadama kowa komai ba acikin gida yayi alwalansa ya fito Mutane basu wani mamaki ba in yana gari dashi ake yin sallah duk da akwai Limamin masallacin Mallam Muhammad Dayyab in Baba Mallam bai nna shi ke kula da masallacin har ya jafar da Ya Nasir suna bada Sallah da Mangariba haka ko isha"i Mallam din ke sakasu saboda gaba in watarana ya fadi ya Mutu ace akwai masu bin bayansa Koda Umar da Nazir basa kusa akwai Jafar da Nasir manyan dake bin bayansu..!
Kowa ya zata Baba Mallam din zai bada sallah sai dai ana shiga masallacin yace Mallam Muhammad yajasu Sallar,to sai mamakin bai yi yawa Tunda yana haka sau tari dadama.
Mallam Muhammad ya bada salla ana Idarwa Baba Mallam dake sahun gaba ya matsa gabansa sukayi kuskus kafin Mallam Muhammad din ya sanar da Daurin aure da za"a Daura shi yanzu Baba Mallam sai annuri yake yi Ya Jafar da Nasir Dake layi na Biyu ya yafito da Hannu Sai Shamsu Dake gefe duk suka taso suka kariso gabansa gaban Liman Mallan Muhammad..!
Suna karisowa yace su zazzauna suka zauna nan gefensa Cikin Dattakonsa yace"Jafaru dauko sakon nan..!
Ba Musu ya mike ya fita daman acikin Motarsa ya bar Huhun goron da Ledan Dabibon yaje ya Dauko ya kawo ya Mikama Mallam ya karba ya Mikama Mallam Muhammad yana Fadin"Araba shi Liman..araba ma Jama"a..!
Ba Musu Limam ya bama Ladani Umarnin ya rabama kowa Dabino da Goronsa kamar yadda aka saba Cikin Kankanin Lokaci yabi layi layi ya bama kowa,Mutane basu yi mamaki ba sanin Daman amasallacin bazanga koda yaushe cikin kawo Daurin aure akayi

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment