Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jamin Kallo da Zubewar kimata a idanuwan Malam Kimar da nayi Shekaru ina Ginata Sa"adatu Kin jawomin Kafar Zargi da kallon Reni Daga ya"yan Cikin gidan nan Sa"adatu ki kyaleni da abunda kika jawo na raasa yau ki barni nayi Tunanin yadda Kimata zata dawo a Idanuwan Malam..Naki mai Sauki ne ki je ki bama Amina Hakuri Shikenan Mganar Zata kare..!
Daga haka tana Huci Fuu ta shige Bedroom dinta ta bango Kofa Sadiya ma ta mike batace komai ba ta wuce Dakinsu aka bar Sa"adatu da Sabeeha.
Gaskiya Anty ta Fada Mallam bazai Sauya mgana ba in tana son Tsira Daga Fushin Malan tayi yarda yace.
Kwana Tayi kuka da Bakimciki Zata kaskantar da kanta gaban Amina sai dai bata da Mafita Baba mganarsa Dayace kuma ba Sauyi.
Dole yasa da Safe tana Shiryawa na Tafiya makaranta,Tace Sabeeha ta rakata gidansu Amina Lokacin da taje gidan kowa yayi mamaki Saboda ya"yan Anty Amarya basa zuwa gidan Sai da wani Dalili mai karfi
Sanda Take bama Amina hakuri ita tasani Aranta wani abu ya faru Sai da sukaje Makaranta Hanne take Fada musu yadda akayi Amina tayi Dariya ta Hura Hanci kafin tace"Amina Aminene..Wlh badai ta Mutum ba sai Allah..!
Tundaga Lokacin Sa"adatu ta Fita Sabgan Amina bayan Baba Malam ya Kirasu ya musuvFada sosai atare sannan yasa suka yafi juna baisan na Ciki na Ciki ba ita kuwa Anty Amarya Sai da tasan yadda tayi mallam ya yarda ba wajenta Sa"adatu taji mganar ba Har Kara Dukanta tayi Saboda malam din ya yarda da ita kuma Hakanta ya Cimma Ruwa Saboda Har gidansu Aminan taje ta kara bata Hakuri ta yi mgana da Mamanmu wannan abun yayi ma Malam Dadi har ya yarda da Gasken Amarya bata da Masaniya kan abunda Sa"adatun ta aikata yarinta ke Damunta daganan aka bar mganar ammh Dai Sa"adatu da Amina sai dai kallo Daga nesa basa mgana ballatana wani abu ya kara Shiga Tsakaninsu.
Amina bata Sauya ba Tana nan da Jidalinta a gida da makaranta,acikin Satin ma sai da aka bata Suspention na Sati Daya saboda ta fadama wata yar ajinsu Anty Sara Basic Teacher dinsu Tana warin maza ita kuma ta Fada har mgana takai kunnen Anty itakuma Anty Sara ta kai mgana Gaban Sir Gumel ya Rabbata mata Kora Daman ta Taba yima wani English Teacher dinsu Dariya dan Bautar kasa wai wuyansa kamar Lema Mgana Har sai da Ya Jafar yazo makaratar Duk da Dukan da Amina taci agida da makaranta baisa tayi Nadaman abunda ta aikata ba to wannan karon Allah ya Ceceta Mamanmu bata bari mgana takai kunnen Aba ba ta kai ma Baba Malam Waya kadai yayi mganar ta wuce ammh da Sharadin in ta kara cin Zarafin wani malami kora ce Baba Malam yace ya yarda Yayi ta ma Amina Fada da Nasiha wanda yasa Jidalinta yadan Ragu ammh Dalibai Kam bata Daina ba Kafin atashi an sha Fada in an tashi ma Amina yi take Wani Lokacin ya Shamsu ke taka mata Burki.
Da gaske ne mganar Auransu Ya Zulaihat ya taso kamar yadda Hanne ta Tsegunta ma Amina,Ya Zulaihat wani Dan Sanda zata aura Dcp ne anan garin Jigawa kuma yana Daga Cikin Daliban Malan Duk Ranar jumma"a Wajensa yake zuwa Daukan karatu Daga Jigawa shi dan asalin kano ne aiki ne ya kawosa nan kuma Baba Malan yana da Hannu wajen zamowarsa a wannan matsayin.
Ya Aisha kuma a kaduna zatayi aure Itama wani Soja zata aura sojan kasa ne mai Mukamin Captain,shi Mahaifinsa ne abokin Malam sai Ikram da anan garin Gumel zatayi auran kuma agidan Sarauta Domin Jikan Sarkin Gumel zata aura Sai Sadiya da zata Auri Yaron Yayan Anty Amarya yana America yana Karatunsa har yafara aiki achan kan abunda ya Shafi Dilar magunguna.
Duka ya"yan Baba Malam auran gida ake yi musu yawanci ya"yan abokan Malam ne da kuma Dalibansa bashi yake Hadin ba Baya Tallar ya"yansa Sai dai akwai masu son Hada Zuru"a Dashi Sosai Da an zo Tambaya zai yi Bincike in yayaba da Hali da kuma abunda Annabi yace aduba shi zai ga wacce ta Dace da Mutum Wata Shida kafin mganar tataso sai ya bada Izinin ganawarsu da juna Sai dai Kiji ance ki Shirya yau kina da Bako Gabadaya yan"matan gidan haka yake Faruwa Dasu Mazan ne kai zaka nemi abunka da kanka ya aura maka sannan baya bambamci Da gidansa da Gidan Baba Sa'idu komai na auransu shi yake Gudanar dashi babu wani bambamci Shi kanshi Aba sai da yaji Baba Malaman yana Fadamai wane kaza yazo nema ma Dansa aure acikin Gida na yanke Hukunci cikin ya"yanka zai zoya gana da Daya daga Cikinsu nashi Shima Bin Umarni ne Domin Malam ya wuce komai awajensa.
Mganar auran tatashi Sannan kowa yasan Hajiya Babba itace ke Rufe Amaran da komai itace Malam ke sawa agaba Kayan Daki kuwa da komai da komai Daga Dubai ake Oda sai dai akawo kayan abinci kuwa Store ne guda basu da mtsalansu Domin ashekara ba wanda yasan adadin abunda Baba Malam ke Nomawa.

Duka duka nan da Wata Biyu Baba Malam yace za"ayi Bikin Tunda su Ya Zulaihat sun gama WAEC har sun Fara Neco dinsu sannan za"ayimusu Walimar Sauka ana gobe Daurin auransu ne,Shiyasa Duka bangarorin ke ta shiri Amina ba Haka taso ba taso harda ya Zeenatu Daki ya zama Daga ita sai Hamida ammh itama ai wata Shekara ne zasu bugar dasu kamar yadda kowa ya sani.
Bikin yana Saura Wata Daya Dan Malam Dake Madina yayo ma Malam Waya yace cikin Satin nan suna Tafe Shida iyalansa Hutun karshen Shekara da kuma Bikin Sannan yace Jirgin yawo zai Fara yo gaba da kayansu su sai daga baya zasu iso.
Sai Shagalin ya ninka na Baya Ga yadda aketa Murna ma zakasan ko waye wannan ana Matukar ji dashi agidan Anty Amarya sai Shiri take Saboda Zuwan SAKINA nageria Mganar Shirin Biki kuma yana Hannun Hajiya Babba ne da Hajiya Uwa Ita da Hajiya Nasara yan Shawara ne da kallo kawai..,!








*Janafty**TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty)Alherin Allah yakai miki aduk inda kike*



*🅿️05*

*SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA* Haifaffan garin Bazanga ne Dake Yankaji B karamin gari ne cikin karamar Hukumar D'anja ta Jahar katsina,Mahaifinsa Maigarin Bazanga Abdurrahaman da mahaifiyarsa Aminatu auran zumunci ne a Tsakaninsu Domin suna matsayin abokan wasan juna ne. sakamakon Bazanga karamin gari ne yasa Gabadaya Rabin garin Dangin Abdurrahaman ne da Aminatu wanda suka fito daga Tsatson mai Maigarin na Bazanga Tun Tale tale Duniya tana kwance.
Kowa yasan garin bazanga gari ne mai yalwar amfani gona da kuma Kyautata Kiwo,Dukiya da arzikin Baba Malam ba Haye yayi ba Gadonta yayi Tun asali Mahaifinsa ya Rasu yana da Shekara goma aduniya ya barsa Da Mahaifiyarsa da Tarin Dukiya na gadon gonaki da kuma Dabbobi.
Abu Daya Yususa ya rike dayasa ya Fara Fafutukar nemam Ilimi shine Kafin Mahaifinsa ya rasu ya Fadamai Yunusa kada ka zauna ka fita ka nemi Ilimi Domin Watarana kazo ka iya rike Dukiyar da nabar maka sannan komai sai da ilimi Yunusa da wannan kalmar yasa ya matsa sai da aka kaisa Makarantar allo acikin garin Bichi Dake kano yana da shekara goma sha Daya alokacin Aminatu taki yarda sai dai kuma Hujjar da aka bata na Neman Ilimi yasa ta amince Sannan kuma abaya babu Macuta masu hawa kan Dukiyar maraya,Yunusa bai Samu matsalam Komai ba Saboda wan Mahaifiyarsa shi ya Dinga Noma Gonakin Daya gada da kuma Kula da Dabbobinsa.
Yunusa wannan Nasihan ta Mahaifinsa ita ke rike dashi yasa Duk inda yaje ya zama mai kwazo sannan Yana da baiwar Dauke abu akansa Lokaci Daya shiyasa kafin ya Rufe Shekara Uku ya Sauke aqur"ani Cur asaman kansa Daganan ya Dawo gida ya Fara Cucukin yadda zai Fara Karatun boko Domin ya Fahimci ko na addinin gareka in baka da na Boko baya Tafiya Daidai.
Lokacin yana da Shekara sha uku A Danja ya fara primary dinsa Tunda alokacin Yara da girmansu suke shiga Karatunta,Saboda Ilimin bai yawaita kamar yanzu ba yana Gabda gama Primary Aminatu ta rasu sakamakon Saran Maciji abunda yasa Yunusa ya bar Bazanga kenan kwata kwata ya nausa neman Ilimi Duk da kananun Shekarunsa sai dai ya bar Kula da Dukiyansa Hannun wan Mahaifiyarsa Bala.
A makarantar kwana yayi Duka Secondary School dinsa sannan bai Zauna ba yana neman Sani a Duk inda ya Samu kafin ya gama yayi suna Ba wanda baisan sa ba wajen Kokari da Kuma Sanin ya kamata ta Fanni Addini da kuma Bokon Ba inda akayi masa Zarra yana zuwa gida Lokaci Bayan Likaci in Bukatar kudi ya taso mai yakan je wajen Kawu Bala ya basa Kudi Domin yayi amfani Dashi Wajen Karatunsa.
In suka samu Hutu baya zama Waje Daya yakan shiga Har kano wajen Malaminsu bai yadashi ba yana Daukan Karatun Sauran Littafi a wajensa Shiyasa Lokaci Daya Ilimin Yunusa ya shahara batare da an Farga ba.
Bayan ya gama Secondary Diploma yayi kafin ya bar karatun ya koma Zurfafa a neman ilimin addini Duk inda ya san akwai wani Malami mai karantar da Al"umma Yunusa baya zama Waje Daya yana zuwa ya zauna aduk inda yasan zai karu zai kuma Samu ilimi bai koma makaranta ba Sai da yasan abubuwa da yawa ya Sauke wasu Littafan addini da Hadisai bisa kansa sannan ya koma makaranta yayi Degree dinsa akan Islamis Studies anan Abu Zaria.
Kafin ya gama yayi suna ya Rike Shugaban Dalibai na Bangaran addini musulunci MSS, Sannan Kafin Gamawarsa har Limanci yayi zaman yi a masallacin Cikn makaranta sannan bashi da girman kai ko ka girmesa indai kafisa Sani zai Duka ya nemi Sani a wajenka Sannan shine Overoll student a site dinsu sannan bayan ya gama ya Zama Shine First class alokacin
Babu wanda alokacin baisan Yunus Abdurrahaman Bazanga ba Ana ganinsa wani Dan kauye alokacin sai dai mai Tarin hazaka da Ilimi wanda da Fara raina masa wayau akeyi sai Daga baya aka Fahimci iliminsa da Baiwarsa.
Ya samu Shedar kwalin Degree sannan kuma ya kara Sanin addininsa Sosai,Tun yana da Kananun Shekaru ake mai Lakabi da Malam sannan alokacin ba kasafai akesamun yan Baiwa kamarsa ba yasa Takardarsa ta bama Department dinsa mamaki da Taimakon Shashen addinin Musulunci na Jami"ar Ahmadu Bello Yunusa ya samu Scholorship na Tafiya Jami"ar Madina yayi master dinsa kan Islamis Studies Daukakarsa ta Farko da bai Taba Tsamani ba Domin alokacin har ya koma Gida yana Taya Kawu Bala Kula da wasu abubuwan kafin ya kuma yasan inda Zai Lula sai ga Takarda ta Fito Dauke da Sunansa sannan Ita Jami"ar ita tayi komai Har kudin Jirgin Tafiyarsu.
Shiyasa Har gobe bazai manta da Malamnsa na Abu Zaria ba Domin sune matakin Zamowarsa koma meya Zama arayuwa.
Acham Madina wata irin Rayuwa Yayi Domin waje ne garin Manzon Allah sannan Zaka ga abububuwa kala kala da bakayi Tsamami ba bai da matsalan Wajen kwana da abinci Sannan Har kudi suna samu bai zauna ba,yana Fita yayi aiki ana Biyansa Sannan Nemam ilimi yunusa bai gaji ba Larabawan Malaman nan nasu Haka yake binsu Daya bayan Daya yana kara Fahintar abunda bai Sani ba Yunusa shine Yazo Daga Jahar Katsina Sannan akwai Sauran bakaken Fata irinsa Da kuma Labarawa mazauna chan din sai dai Duk da Haka Yunusa ya Dokesu Duk da ya Sauya Karatun nasa wannan Karon yama Karantar Hadith and Islamis Studies ne a islamic University of Madina.
Ko Larabawan wucesu yake yi basa iya Ja da Yunusa shiyasa tun kafin ya gama kowa yasan Ustaz Yunusa Abdurrahaman bazanga Daga Nigeria Ita Nasara Daman ta Allah ce sannan kuma da Dagewa anan din ma Shine ya Fito da Firstclass kaf a Site dinsu ba ga yan Madinan ba Har ga Bakaken Fata yan Nigeria Jami"ar ta karramasa Sannan ta roki data rikesa yayi mata Koyarwa Duk da alokacin Shine mafi karancin Shekaru acikin Malaman wannan itama wata nasara ce yana da Shekaru Ashirin da takwas a Duniya ya samu wannan Daukakar Daga Ubangiji Duk da yana son ya koma gida kasarsa ta amfana da iliminsa Da kuma Shima yana ganin ilimin bai isheshi ba yana Bukatar kara Sanin Wasu abubuwan.
Ya zauna Amadina Tsawon Shekaru Biyar ya samu Cigaban Rayuwa sosai ya Samu Daukaka da kuma arziki Ta Dalilin iliminsa sai dai bai manta da gida ba yana Turo ma kawu Bala Kudi Daga chan shi kuma batare Daya Fadamai sai ya rika siyan Dabbobi yana karamai Cikin Garkensa.
Alokacin Yunusa yaji gida yake son Dawowa ba yadda Jami"ar madina batayi dashi ba yaki Tsayawa Dole ta Rabu Dashi ya Tattaro ya Dawo Mahaifansa da kowa yake mamakin Yunusa ne ya koma haka..?bakinsa ya Hade da Labarci Da Turanci Hausa ma Kadan kadan ne yake ji yayi matukar mamaki yadda yaga Dabobinsa sun kara yawa sai da Kawu Bala yayi mai bayani Sannan ga amfani Gonar nan da ake Fitarwa Duk Shekara bayan ana Fitar da Zakka Daman Tun a shekarun baya ya hana Kawu bala Noma Sai dai biya suke ana Noma Gonakin Duk Shekara shiyasa yana da kananun Shekaru yana da Dukiyar da baisan iyakarta ba.
Da Farko anan bazanga ya fara zama Yana koyama matasa masu tasowa Cikin Abunda ya Sani Rasuwar Kawu Bala yasa Yaji garin ya fita kansa,Dabbobinsa ya saida wasu wasu kuma yayi kyauta dasu sannan amfanin gonarsa ya Raba ma yan garin Gonakin ne kawai bai saida ba ya barsu Domin Watarana ya Kalla ya Tuna da Mahaifansa.
Daga garin bazanga Yunusa Maidurguri ya zauna yayi Shekaru uku achan yana neman ilimi kuma Shima yana karantarwa sannan yana Noma yana kiwo Domin shine gadonsa Tun kaka da kakkanni Duk inda yaji wani Babban Malami mai Karantar da addini Yunusa sai ya taka baida Girman kai sam shiyasa yake Samun Nasaran Rayuwa Daki Daki.
Hajiya Babba mai suna Zainabu yar Garin Bama ne alokacin yan Boko Haram basu Rikita garin ba Sannan a wajen Mahaifinta ya zauna Mallan Zanna yayi shekaru ukun nan yana neman ilimi Da zai tashi Tafiya ya Dauki Zainabu ya bashi auranta Saboda ya yarda dashi.
Hajiya Babba ba yar kowa bane Mahaifinta Malan zanna malamin Zaure ne bai da komai sai Rufin asiri Duk garin da Yunusa ya zauna zai yi Noma da kiwo in kuma ya tashi Tafiya zai sai Raba biyu ya Dauki Rabi sannan ya bar ma Inda ya Zauna Rabi haka ta Faru da Malan Zanna Da karamcin da yayimai Duk da ya Fadamai Asalinsa da kuma Burinsa na neman ilimi Har ya koma ga Allah.
Malam yunusa ya zauna agaruruwan Nageria baisan iyaka ba Duk inda yaji Labarim Malami sai yaje ya nemi Ilimi Shima ya Bayar Daga Cikin abunda ya sani Sannan Dukiyarsa ya zama kamar Rabata yake duk inda ya Zauna ya sami Riba sai ya bar Abunda yazo Dashi ya tafi da Ribansa Shiyasa Acikin matansa ba kamar Hajiya Babba ita tasan shi tun yana matsayin Malam Yunusa ta kuma yi kokari da Jeka kadawon da suke yi shi da ita har Kuma alokacin ko Fegin Fili bai dashi na kansa Duk inda yaje za"a basa Gida ya Zauna har sai ya gaji ya tashi Tunda alokacin Duniya na kwance Malamai Darajasu akeyi sannan ana Kimantasu da musu kallon su din magada Annabawa ne ba kuma kamar yanzu da suka yawaita ba Alokacin basu da yawa.
Agarin da Malam Yunusa ya fara Zama agarin Gusai ne anan ya siya Gida mai suna gida Suka zauna Domin su samu natsuwar zuciya Shida Zainabu Tunda Tana da karancin Shekaru malan zanna ya aura masa ita kimamin Shekaru goma Sha Biyar alokacin.
Yayi Shekaru akallah zasu kai goma agarin na Gusai Anan ya bar Zainabu sai dai yana yin Tafiye Tafiye ballatana alokacin Malamai sun Fitar da da"awan da suke zuwa gari gari suna yi Domin Sanar da addinin Allah kuma Malam Yunusa yana Daga Ciki bayan Haka a Inda yake yana karantar da Kimamin Dalibai da baisan adadinsu ba Sannan itama Zainaba Daga Cikin Gida Tana karantar da mata kafin kace me Sunan Malam Yunusa yayi Tambari a garin Gusai da kewanta ballatana kowa da arzikinsa ya gansa Yana da katon Fili kusa dashi nan yake kiyonsa da masu kula dasu samnan yana da gonakinsa na garin bazanga da ake Nomamai Duk Shekara sannan Duk garin daya zauna yana samun kyautatawa da kyautar gonaki da Dukiya tunda bai Taba amsar ko Naira Biyar Domin wani ya amfana da Saninsa ba.
Shikenan Kafar Nasararsa sai ta bude alokacin yan Siyasa sukayi Tunanin irin nasu ne, suka fara zuwa mai da Bukata sai dai yana kokarin Sanar dasu shi baya Shirka baya Duba ammh in kace ya tayaka Rikon Allah Domin Biyan wata Bukata naka zai Tayaka wannan Dattakomsa nasa da Wadatar zucci da ko Duniya zaka basa bazai karba ba,Yaje Saudiya Da kudinsa Har Sau biyu ballatana Lokacin yana Madina Duk Umura da Hajji Dashi akeyinta.
Shikenan kimarsa ta Karu aka Fara Gayyatansa Taron karama juna Sani na Malamai sannan Har ana gayyatansa Gidajen Radio da Gidajen Talabijin Abunda ya karamai Daukaka yana Daraja na sama Dashi Malamai haka yake Daukan su Tamkar Madubinsa komai girmamsa haka zai Duka gabanka yana neman Sani wannan Dabi"a ta Siyamai Soyayya da Daukaka da Nasara Lokaci Daya da ba"a taba Tsammani ba.
Har kuma zuwa Lokacin da Daukakar nasa ta fara ko bari Zainabu bata tabayi ba Duk da yana Fatan Samun magaji bai Taba Korafi ko nina wani abu da Zainabu zata Fahimci ya Damu ba Mutum ne mai Tsantsani da Tsoron Allah da Wadatar zucci.
Ana cikin Hakame kwatsam Allah ya Hadasa da Shaharran Dan Siyasa nan wanda ke rike da Mukamin Kakin Majalisar Ta Jahar zamfara.

*AMINU GUSAI* basu hada komai ba sai da sun Taba Hada yin Makarantar allo anan garin na Bichi kano A talabijin yaga Malam yunusa yana ganinsa ya ganesa Domin alokacin ba wanda baisan Yunusa bazanga ba, Yayi Tattaki har gida yaje ya samesa sukayi Zumunci da Tambayan bayan Rabuwa,Aminu ya sanar dashi bayan Sun yi Sauka yayi karatu shima Har matakin Masters sannan kuma sai ya Fada Siyasa Daman gidansu gidan yan Boko ne da kuma Tsofaffin masu Kudi Dayake awanchan zamani Karatun allo yana da Daraja ba kamar yanzu Domin yawancin manyan mu na yanzu in da zasu baka Tarihinsi zaka Ji cewa sai da suka fara da Karatun allo kafin su dawo su Dora na bokon
Aminu yaji mamakin ganin yadda Malam Yunusa ya koma sannan ya kara yarda ma kamsa yana na nan bai Sauya ba Tunda Har ya iya bari Garin Madina yazo kasarsa yana Wahala.
Daganan Zumunci ya fara Har Ya kawo Iyalinsa Hadiza da Dansa Daya mai Suna SA"IDU mai kimamin Shekaru goma sha biyar alokacin tun gaanin Farko da Yunusa da Zainabu sukayi ma Sa"idu ya shiga ransu Matuka suna son yara suna kewarsu sai dai Allah bai basu ba,Sannan ga Hadiza mai kunya da karamci Sa"idu shima yana son zuwa gidan Malam Yunusa kodomin yaga Dabbobi kaunarsu acikin Ransa yake Ranar har cema Malam Yunusa yayi Baba ina son ka bani Rago in na kara girma na kula Dashi alokacin gaban Dukkan ne ya Fadi mganar Malam Yunusa ya Dafa kansa Cikin Kauna yace"Insha Allahu Watarana kai zaka kula dssu Sa"idu..Fatana ka Dake da Karatu..!
Wannan mgana ta saka Sa"idu Farinciki kuma abunga ga yaro ya rike mganar acikin kansa.
Tundaga Ranar yake murna yana Fadin in ya girma zai zama mai kula da Raguna kowa yana ganin Shirme ne da yarinta.
Duk da alokacin Zainabu zata girmema Hadiza ita Allah ya bata Haihuwan da Wuri tana da kananun Shekarunta Ammh sun zama kawaye tunda Zainabu batasan kowa agarin ba sai suka zama kamar yan"'uwa koda yaushe suna ziyatar juna Sannan Sa"idu duk karshen Sati wajensu yake yi kaunar yaron ta fara ne tun Tuni Sannan Shi kauna Allah ke hadashi ma Mutum ba.
Akwai Ranar da Malam Yunusa suna mgana da Aminu ya kallesa yana Fadin"Aminu ina kaunar Sa"idu ina jinsa kamar dan cikina..Ina ji kamar ya zauna Dani har Abada..!
Alokacin Aminu Dariya yayi ya Dafa Kafadar Malam Yunusa yana Fadin"Haba yunusa ai ni da kai mun Zama Daya..Wlh har araina na yarda da wannan kaunar Dake Tsakaninka da Sa'idu Dama Hadiza nada juna Biyu sai ta Haifa mana wani kai kuma ku rike Sa"idu kai da Zainabu har abada na tabbata ko bayan Raina Sa"idu zai fi Alheri Dakai Fiye Dani..!
Wata mganace da Malam Yunusa ya Dauketa kamar Fadice sai dai ba Haka bane Har azuciyan Aminu haka take Malam Yunusa bai Tabbatar ba sai da Aminu ya Tara Duka yan"uwansa ya Fadamusu ba wanda yayi gaddama Sanin Waye Malam Yunusa Shiyasa kowa yayi Na"am da Batun Hadiza ma bata kawo Damuwa ba macece mai kunya da kawaici Duk da kasancewarta Bazanfara gaba da baya.
Malam Yunusa yayi kukan Murna Aranar da Aminu da Hadiza suka Dauko Sa"idu da duka kayansa suka kawo musu shi Har abada shi da ZAINABU sun kasa Daina kuka suna ganin kamar mafarki ne sai dai Zahiri ne,Sa"idu bai damu ba ya Saki Jikinsa Sosai Saboda Dabbobi daman yafi son gidan Baba Malam kamar yadda Sa'idu shine Mutum na Farko Daya Fara Radamai wannan suna kuma yake binsa yana alfahari dashi.
Abu kamar wasa karamar mgana ta zama ba Sa"idu ya dawo hanun Malam Yunusa da matarsa zainabu abun Tsusayi Cikin Da Hadiza ta Samu ta Haifeshi ba rai ammh duk da Haka basu Damu Sa"idu ya cigaba da zuwa makarantar Boko sannan kuma Malam da Zainabu suna Karantar dashi karantun addini acikin Gida sannan suna iya bakin kokarinsu wajen Tarbiyansa da Rike Amanar da aka basu
Wajen sau uku Hadiza na Haihuwa ba rai sai ana Hudu ta Tsaya macece mai Suna Hafsah sunan Mahaifiyar Aminu ce suna cemata Husai sai kowa ya samu nashi Sa"idu na zuwa ganinsu Lokaci bayan Lokaci kamar yadda suma basa gajiya da Ziyartan Juna.
Tun alokacin ana ta yima Malam yunusa Tayin ya"ya Domin ya kara aure ko zai Samu Haihuwa sai yace A"a Domin Zainabu nada kima awajensa,Sannan koda an mai mganar Haihuwa sai yace Sa"idu ya isheni Rayuwar Duniya da Lahira Saboda irin kauna da Shakuwar Dake Tsakaninsu suna bashi Dukkan wani Gatan Duniya sai dai suna kokari wajen Kula da Tarbiyansa.
Cikin Ikon Allah kamar yadda Malan Yunusa yace Haihuwa ta Allah ce Hakan ce ta kasance Domin Sa"idu ko Shekara uku bai yi da Dawowa Hannunsu ba Zainabu ta samu Ciki kuma Haihuwarta na Farko Ta Haifi Namiji Malam Yunisa ya saka masa Suna UMAR IBN YUNUS..!
Koda zainabu ta Haihu mganarsa Dayane Sa"idu ne babban yaro na Domin kafin na Samu Umar Sa"idu na Haifa,Duk da Mutane sunsan ba Dansa bane ammh suna Girmama Kaunar dake Tsakaninsu kuma koda suka samu nasu babu abunda ya Sauya Daga soyayyar da sukemai.
Yayinda Aminu Daga Husai Hadiza bata kara ko barin wata ba kuma basu Damu ba Tunda Da ga Allah ne sun Tabbatar Sa"idu yayi Dace da iyaye nagari kuma ko bayan ransu Watarana sai yayi alfahari da hakan
Tundaga lokacin Haihuwa ta Budema Hajiya Babba Daga Umar tazo tayi Nazir wanda Tsakaninsu ba Nisa alokacin kuma Malam Yunusa ya kara aure Shima Bashi matar akayi sun je Da"awa garin Tsafe na Jahar Zamfara gidan Malamin da suka sauka Malam Hamza ya Dauki Yarsa Kwara Daya cikin jerin ya"yansa Uwani ya bama Yunusa shi kuma bazai iya Bijiremasa ba ya karba Hannu Bibbiyu achan aka Daura aure sai dai ya Dawo da mata kawai Sannan bai samu matsala da Zainabu ba ta karbi Uwani Hannu Bibbiyi suka cigaba da zaman Amana ko ita sai Daga baya tasan ba Malam ya Haifi Sa"idu ba shima sai da ya Fadamata ta yarda ammh tana Girmama wannan kaunar Daga Malam din har Zainabun da ya"yanta basu da Mganata sai ta Sa"idu ko"ina kaje agidan nan Sa"idu ne wannan kaunar Daga Allah ne.
Haka Rayuwa ta cigaba da gangarawa da Dadi ba Dadi Malam na Cigaba da nenan sani da Da"awa sannan Lokaci Daya yana karantar matasa Abunda ya sani na Addini Alokacin Aminu gusai akayi Chanjin gwannati bai samu Kakin majalisa ba sai aka Nada wani Daga Shekarar kuma Jinya ta kamasa na Ciwon kafa Daga Sama Sama sai abu ya Zarce baya iya tashi Sai dai a kwantar atayar Jinya tayi Jinya anyi mganin Asibiti anyi na gargajiyam Duka ba"a Dace ba Sai da Duka Abunda Alhaji Aminu ya Tara ya kare Malam ma bai zauna ba Shima Duk in da yaji wani mgani zai amsomai

2 Comments On TA FITA ZAKKA BOOK 1
avatar
amina-2-2-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
zahra-muhammad

12 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment