Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

budewa zata rukunkume shi da maganin a jikinta ..

Yayi sallama ya shiga dady yana ganinsa ya fara murmushi" kamar dai kowane dare sanye yake cikin kaya marasa nauyi yana binciken wasu file ,Abdullah ya isa gareshi ya zauna a gefen tuntun dake kusa da shi baza baza dady ya zube file a gabansa har katin daurin auren yana dubawa shr Abdullah byn ya gaishe shi dady ya dago Ido ya kalli yanayin da dan nasa yake Sannan ya dauke kai yacigaba da abinda yake. yace yaya dai Abdullah any problem?
Cikin sanyi jiki da sarkewar murya Abdullah ya sunkuyar da kai ya ma kasa maganar dady yace mhm ina jikinka ?

Abdullah yadan kalli dady da rawar murya yace dady mami tadaina kulani yakarashe maganar yana zubda hawaye..... kallon da dady ya masa shi katse shi yasake yin kasa da kanshi yace dan Allah dady in zai zai yiwu a daura auren da duk wacce mami ke so dan idan na aure Aisha mami bazata Kuma kallona ba.. Ido jawur yacigaba dady da gaske mami bata son abun nan cikin inda inda yace ni ...Ni na .hakura kawai dady ya bar abinda yake ya zubawa Abdullah Ido na tsawon lokaci yana nazari akansa sannan yakirawo sunansa yace Abdullah ka kwantar da hankalika kana yawan sa damuwa ya zama over a ranka byn duk abinda doctor yace a kanka ,ya dan yi shr sannan yace Abdullah bbu abunda aka fara shi ba a karasheshi ba duk wani abu da za'a yi a rayuwa to tabbas wata rana zai zo ya wuce yana magana yana kallonsa yace Abdullah yau aka wayi gari bbu Raina kai ne ke da alhakin rike min dukkan iyalina dana bari to sai nakasa yima abunda zai kyautata taka rayuwar .
wacce maminka take son ka aura ko kadan bata dace da rayuwarka da nayi niyyar ka hada su duka ka aura Amman dana sa ayi bincike akan banji dadin abunda akatarar akanta ba , ya numfasa Sannan yace yawancin bata garin zuria idan ka duba ya faro ne daga ainihin maaurata ,Abdullah mace ta gari itace ke sa mutun ya samu natsuwa da kwanciyar hankali da zai zama cikakken mutun mai iya rike gidansa dan haka ka dai na maganar ka fasa aure da yarinyar nan awanni kadan ya rage a daura auren ku muddin kaga baayi ba yin Allah ne bai karasa da numfashin na ba Amman sai anyi Sannan Abdullah na tokeka karike amanar yarinyar nan ba wai dan tana diyata ba, saboda bakasan iya wahalar dana sha ba kafin kasamu aurenta Abdullah ya kada kai yana duban mahaifinsa dady yace Allah yayi muku albarka kai da ita ka rike wannan a ranka itama mamin da kanta wata rana zata sa muku albarka" dan yanzu bata San gatan har da ita akayiwa ba ..jikin Abdullah yayi sanyi sosai dady yace ka cire dumuwa a ranka komai mai wuce wa ne ya dubi agogo tashi kaje ka kwanta dare ya fara gashi za'a tashi da wuri ahankali Abdullah ya Mike cikin sanyi jiki ya juya zai fita har ya kusa fita dady yayi gyaran murya Abdullah ya waigo ya nuna masa hanyar bedroom dinsa yace ka shiga ciki ka kwanta Abdullah ya juyo yana kallonsa sannan a hankali ya dawo yabi hanyar bedroom din dady ya shige sanin dady ne mai yiwuwa idan ya koma part din nasa yacigaba da yawan damuwar shi yasa yace yashiga nasa dakin ya kwanta ..

Hummm Su faiza kuwa an tsufa can cikin shuke shuken fulawowi dake daf da kofar da zata shiga da kai part din Abdullah ,duk da damuna ta dan gota Amman har yanzu ciyayi da shuke shuke sunan a korensu haka ne ya taimakawa faiza samun maboya a cikin su a tsugunne take a takure gashi ko kwakkwaran motse batayi saboda kada yaga motse a gurin yaki fitowa ga warin maganin da ta shafa a jikinta duk ya Dame ta har dare ya tsula ba Abdullah bbu alamunsa anan tagane wasu abubuwa sukeyi tare da dady na daurin auren, shi yasha kansu a koda yaushe yana iya fitowa yazo ya kwanta dan haka tacigaba da Jira ga sauro sai cizo suke sun samu nama" jiya tayi kwanan ha'ulai a kofar gidan boka mai gani har hanji gashi yau ma zata sake kwanan gidan sauro. baya da kugunta duk sun rike mata sai da takai ga zaman dirshan a wajen iya tashin hankali faiza ta ganshi agun dan har kwarika suka dinga bin jikinta ga bacci a idonta Amman dan jaraba da kafiyar irin nata ko gezau balle ta bar gun ita dai sai burinta ya cika " har sanda akafara kiraye kirayen sallah a wasu masallatai dake kusa da su tun tana karyata kunneta har taji a masallaci dake cikin gidan duk ilahirin ruwan jikinta ya kusa tsotsewa bata amincewa ranta ba har sanda taga kofar part din dady an bude dady ne da Abdullah suka fito a tare da alamun masallaci zasu je dan ca suka nufa nan duniya mutumin dake cikawa faiza Ido Kuma yake balain yimata kwarjini irin dady. Ban cin haka ai da tunin tayi gudu ta Tari Abdullah a wannan lokacin duk da tasan kaidar da boka ya gaya mata Amman tasan muddin ta doshi Abdullah a wannan lokacin tasan daga ita har mama hafsa kashinsu ya bushe dan sai anyi tambari da gabadayansu anyi sama da su ..

Tun karfe bakwai Dr sagir ya iso gidan, dady ya turo da kayan da Abdullah zai sa hum maikaratu ba sai an tsaya kwatanta tsaruwarsu ba, tun safe kuwa manya manya da kusoshin gwanatin duniya suke cincirindo a gidan har police aka sanya sannan akabar Abdullah ya fito ya shiga motar zuwa gidan alhaji aminu kai daga kallon shigar manya kayan da Abdullah yayi kasan dole ce kawai tasa shi sanya su don hatta leben babbar riga a hannun salis take shi kuwa da kyar yake iya daga dayar ya mai da kan kafadarsa ...


Hummmm ga dai Abdullah zaije gun daurin auren to jama'a ko ya auren zai kasance , to kudai biyo Yar mutan bagudo kusha labari🀝🀝😜😜


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


AISHA A BAGUDO



Page 25


Aisha zaune a dakinta ta hada kai da gwiwa sai sharban kuka take duk da tun satin da'aka soma shirin bikin, take cikin halin tashin hankali, rashin sanin meyye makomarta agidan su Abdullah" tun safe datayi wanka wanda shima sai da gwaggonta ta sata a gaba sannan tayi ko byn da yashirya ma zaman tayi tasoma rizgar kuka tamkar wacce akace wa Allah yayiwa mlm abu da inna rasuwa "tun karfe bakwai daidai salis ke kofar gidan mlm abu yana jiran fitowarta Amman shr" kusan tsayuwar minti 30 yayi awajen bbu wani bayani dangane da fitowarta " can kuwa cikin gida ba yadda ba'ayi da Aisha ta fita ba, Amman taki sauraron kowa dan gani take kowa bai damu da halin zata shiga a sabuwar rayuwarta " gwaggo Laure ce tasake shigowa dakin tace kun ganarmin jairar yarinya mai daurin kan tsiya ke dai Allah shirye ki yashige miki gaba, dan wannan halin naki wata rana sai yakai ki yabaro mutun arinka yi masa magana sai dan bazan taurinka awa mutane farko " Aisha tasake barkewa da sabon kuka.kar all yasa ki fita kiyi tazama daurin aure ne dai ba fashi sai dai ki mutu,inna dake daki tare da baki tarinkajin motsawar zuciyarta ita ta fuskanci abinda diyarta ta keso "tashi tayi tsam tashiga dakin. yadda taganta sai da taji gabanta ya fadi hankalinta a tashe ta karasa inda diyarta ke zaune ta yakamo hannunta hade da kiran sunanta Aisha ta dago hawaye nabin fuskarta ai tana ganin inna ta fada jikinta ta fashe da wani kuka inna ta daura hannu a bayanta tana shashafawa ahankali har dai taji kukan nata ya dan tsaya "sannan ta dagota ta mai da ita mazaunin ta ido cikin ido inna ke kallon Aisha" murya a dashe tasake kira sunnanta Aisha kina son ki tozartani acikin jama'a gidan salon asamu masu cewa uwarki bata baki tarbiyar kwarai ba ? Aisha ta girgiza kai to meye dalilin rashin fita akai ki inda za'a daura miki aure" byn yau ranar farinciki ce garemu baki daya , ga mutun can waje tun sanyi safeya yake zaman jiranki dan tsabar wulakancin Kiki fita idan Abdullah ne baki so shi mayye laifinsa ciki "ai kifito kai tsaye ki nunamin ban isa dake ba. tunda ni na saki amincewa auren Abdullah bawani ba. cikin sarkewar murya tace wlh inna ba haka bane " ni dai haka kawai nake jin tsoro gashi ina yawan ji faduwar gaba" inna tayi shr dan itama kusan tun karatowar auren take jin haka Inna ta numfasa sannan tace to maza share hawayen nan bana bukatar ganin su" da bayan hannu tashiga gogewa inna tace addu'a zaki rinkayi a duk sanda kikaji haka ..bbu abunda yafi karfin addu'a "sai da inna tayi ta rarrashinta wanda daman abinda Aishar ke bukata kennan daga innarta "inna da kanta ta sake gyara diyarta "ta rakata har tsoron gidan sannan suka fita tare da yan rakiyyarta .


Takwas ga watan uku ranar lahadi kennan misalin goma da minti biyar ,dubban jama'a suka shaida auren Abdullah I.M sidi magaji da Aisha abubakar bahindi domin sai da aka shafa fatiha da kusan mintina goma sannan shafarwa ta iso gurin wasu a dalilin cunkoson jama'a" don titi unguwar gabadaya police ne zagaye da gun ..
Babban abinda ya tsuma ZUCIYAR jama'a wanda ya hana mutane saurin watsewa an daura auren yarinyar akan sadaki naira dubu hamsi wanda kudin abin a rike baki ne sosai a wannan lokacin tare da takardun gidaje gudu biyu hadi da motocin hawa guda biyar wanda alkawarin dady kennan "dan ka'idodin mlm abu yasa yamasa haka "saboda kwanakin abaya yaje har gida yawa mlm abu datayin gida ,su tashi dag gidan dasuke ga gida can yaba su. Amman fir mlm abu yace shi dai ya gode Amman yafi son nashi ,domin dashi yasaba dady yasan yanzu dole ya amshe su a matsayin sadakin diyarsa abinda ya ruda zuciyar mutane kennan ..

Dady na cikin jama'a ana gaisawa cikin fara'a gashi yanata nan nan da mlm abu "musamman alhj aminu domin har sun saba shima mlm abu rashin sakin jiki ne da basu yi ba, an dauki lokacin kafin a fara watsewa sai da mutane suka ragu sosai sannan Dr sagir suka taso shi da ango suka dinga gaisawa da jama'a da likitoci abokan Dr sagir shi Kuma yana masa bayanin su..

Abdullah ya tsaya yana kallon kofar gidan alhj aminu yace salis yakawota nan din ne?Dr sagir yayi dariya yace wa kennan Abdullah ya dan Harare shi cikin dariya yace to amaryarta Dr sagir yasake darawa tun safe ya kawota tana ciki
Abdullah ya ja ya tsaya Dr sagir yace ya ko amana magana da ita ne? Ahankali Abdullah yace kai dai bom....ne wlh 'wane ni yanzu kana jin tun satin bikin nan take kuka bare yau nasan duk fushin da haushinta a kaina za'a juye ..suka sa dariya , Abdullah ya dafe kirjinsa yace washi.... da sauri Dr sagir yace kai lafiya , Abdullah ya runtse Ido jikina ya nuna min kadarata ta cikin gida nan, tacan tana kuka,dr sagir ya ja tsaki wlh ka tsorata ni sauran suka dariya Amman baza kaji ainihin abunda da suke cewa ba...

Daga gun daurin auren kai tsaye reception aka wuce kmr yadda dady ya tsara .


Usman yashigo gidan gwaggo Laure ta tambaye shi har andaura .
Usman yacire hularsa ya ajiye yace wlh an daura kwarara igiyoyi guda uku . yashiga gaya musu yadda yaji sadakin to a haka ma unguwar ta dauka wasu ke cewa sun haifi arzikinsu yayin da wasu ke kallon arziki ajinin yarinyar yake hakan ce ta faru can gidan alhaji aminu inda aka mamansu sakina tayi shr abin yayi mugun tsuma zuciyarta" to daman haka abin Allah yake idan Allah yaso ka to kowa ma yakika ba wani abu bane ..

Yadda ake ta ririta zance a unguwa ,su kuwa gidan mlm abu jikinsu ne yayi matukar yin sanyi ita kuwa amarya uwar tafiyar takara tsorace wa da al'amarin angon nata ...

Misalin karfe daya ranar ne Dr sagir ya turo musu da motoci kmr yadda aunty Maryam tasa aka kira shi tayi masa korafin har yanzu baa san gidan amarya ba "gashi ana son kai kaya shima Kuma sai da ya kutsa cikin jama'a yasamu dady akan maganar shine yanzu aka turo musu..
Shi kan shi Abdullah bashida masaniyar ba a nan cikin gidan zai tare da amaryasa ba", sai a wannan lokacin wani shiryayen gida dady yasa aka tsara musu wanda duka bai fi part din Abdullah da rabinshi ba bbu wani nisa me yawa tsakanin su da gidan .zuwa karfe uku sai ga su aunty Maryam sun dawo dama dai daga ita sai aunty amarya sai kawar aunty Maryam din sai ko usman don wani abun sai da namiji gwaggo Laure kecewa Kar dai har kun gama jeran ...

Aunty Maryam tace bari dai gwaggo ai haka muka dinga yawo da kayan mu a cikin gidan dan ko ina muka bude a shirye yake da komai a cikinsa daki daya muka samu acan karshe da bbu komai a ciki muka zuba su sai dai gidan ya hadu ya wuce tunanin mu abin duniya tamkar aba san ciwon sa ba.

Ahankali ta motso ta shafa kan Aisha dake kwance awa ruwa ta shafawa diyarta dake hannun kawarta tace Allah ya yiwa yayanmu haka . wannan yanayi yasa mlm abu yasa aka sauke alqurani mai girma fata na gari kennan Allah ya zaunar da maaurata lafiya.
Karfe takwas daidai Dr sagir yasake turo motocin dazaakai amarya,nasiha mai matukar ratsa jiki mlm abu yayi wa tilon diyarta sa wanda har ya hawaye ballewa a idanunta "babu yadda zatayi da auren Abdullah ,ita inda son ranta ne tun da dai auren ake son suyi to sun yi. Amman a kyaleta tayi zamanta agida ko boarding da take jin takaicin duk sanda zata koma sai taji nafila ne akan akai ta gidan Abdullah "a hankali mlm abu ke tambyarta abinda za'ayi mata da sadakinta ta dago jajayen idanunta tana kallonsa irin kallon nima ban sani ba tana langwabar da kai daga ganinta kasan tagama saduda da al'amarin. hawayen dake zube a idonta shi ya dada karyar masa da zuciyarsa yace kukan ya isa shi kennan .

Inna ma tayi iyayinta sosai duniya nan kusan ita tafi kowa sanin halin diyarta dan haka itama takara yi mata nasiha har batasan innarta ta damu da ita sosai haka ba sai yanzu yadda tarinkajin tana maimaita cewa kiyi hakuri da komai duk ma wanda zai miki wani abu da ba daidai ba ki kalla kawai ",sai dai abunda kikaga zai wuce iyaka, sai a yanzu Aisha tayi magana me yuwa ma tun safe dataji a yadda aka daura aurenta bace ko uffan ba ,ta kalli inna murya a raunane tace innarmu to maman Abdullah fa?anan inna tasake kallonta kawai ta kasa bata amsa a haka aka fita da ita ..
Hankali Aisha yayi mugun tashi gashi sakina ma tun magariba tace zata je gida yakai wasu kaya ta dawo Amman shiru sai duban hanya take yi ,ta kalli aunty data rike hannuta zata fita da ita tace aunty sister fa ?ta tafi bata dawo ..aunty tace sakina ba nima narasa meya tsayar da ita Amman tunda motocin da dan yawa Killa ta biyo wasu a haka aunty ta tafi da ita badan Aisha taso ba a raayinta taso ajira sakina ..aunty Maryam sai sauri take ganin tara saura .. Aisha dai tagama sadaukawar zuwanta gidan Abdullah koma meye zai faru daita tabarwa Allah komai.. ita takara karyawa aunty zuciya tasata hawaye da har ta zauna kusan karfe goma a gidan wanda sakina ce ya cancanta ta zauna wannan lokacin to ita Kuma kwata kwata tunda ta tafi bata dawo gashi kowa ya tafi shiru gidan har aunty ta fara ganin rashin hankali ta ,sannan suka jiyo karar shigowar motoci guda biyu Dr sagir ne da Abdullah sai salis da RK suka iso yayin da Dr sagir da Abdullah shigo falon salis da RK suka tsaya a waje wanda daman agidan zasu kwana da sauri aunty Maryam ta Mike shi kennan Allah yabamu alkhari Aisha ta rike ta gam jikinta har karkarwa yake aunty tace bakya son gobe na dawo kennan? tace ina so tace to sakeni Dr sagir ne yasoma dawo kai daidai nan Aisha tasaki aunty da sauri ta zauna ta kara rufe kanta Abdullah har da dan risinawarsa ya gaida aunty Maryam da sauri ta amsa tafita daman akwai deriban dake jiranta zai mayar da ita .suna shiga wani hotonsu da computer ta hada tamkar dai tare suka Yi ita da Abdullah ya doki idon Dr sagir yace kai friend za'a hafi hurul aini fa a gidan nan .
Abdullah yadan kalli pics din bai ce komai ba yayi gaba yasa hannu ya kunna AC yana cewa kai zafi fa yana gyara labule Dr sagir to idan ita amarya sanyi take ji fa?ko amarya shr ba amsa shima Abdullah bai Yi magana ba ,ya dawo kusa da shi kan doguwar kujera ya dan shinhida wanda har yanzu bai kalleta ba ,Dr sagir yace idan Kuma akayi sa'a ita ma amarya haka take kaga sai ku yi ta zama a kasahen turai duk maganar da Dr sagir yake Yi Abdullah shr yayi yana ta danne danne waya .ita kuwa Aisha shigowarsu ta shiga wani yanayi musamman da ta tsinkayi kamshin turaren Abdullah wanda ko a ina be sai ta shida shi.kuka tacigaba dayi kasa kasa wanda shi Dr sagir bai gane ba Amman shi Abdullah ya gani ya bar abinda yake yana kallonta kukan yarinka shiga jikinsa har Dr sagir yana magana ba shi bai ji ba ya kalli shi yayi murmushi yace wel ni bari in barku ya Mike yana duba agogon hannushi yace to 11 yayi musu addu'a yace amarya kin ki muga idanunki..suka fito tare da Abdullah Dr sagir yace to a dai bi a hankali naga har kasoma birkicewa kasan dai Aishi dai she is young Abdullah ya zabga masa harara cikin murmushi yace Shari Kuma zaka min wani sharri kai da ka dade da barin duniyar da muke ciki sai dana taba ka fa ka dawo haiyacinka gabadaya suka tafa suna dariya Dr sagir ya wuce yana masa sallama yayin da shi Kuma ya leka salis ya tabbatar masa da arufe koina .....






MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AISHA A BAGUDO


Page 26


A hankali ya shiga dakin ya dan jima tsaye yana binta da kallo kmr wanda yarasa abinyi daga bisani ya tura wayarsa cikin aljihun wandonsa na baya "yasa hannu ya kamo nata ya dago ta kai tsaye gaban madubin dake manne cikin dakin ya kaita ,a tsorace take binsa wanda har mayafin dake lullube a kanta ya zame daga jikinta ya fadi kasa yasa hannunsa ya cire yayi cilli dashi gefe ya matso da ita gabansa cikin sanyi murya yace Aisha see ur face tsawon watanni biyu da kwanaki rabon da su ga juna" tun daren da zai tafi Denmark sai yau din da idanuwansa suka hadu ta cikin madubi "sunyi shiru suna kallon juna daga bisani ta janye idanunta ta sunkuyar da kanta "ya juyo da ita suna fuskantar juna ya rike duka kafadunta a hankali yake magana yace Aisha kuka kuka har yanzu dai please ...stop crying ya kamo hannuta cikin nasa yana murzawa daga can kasa yace haba Aisha ki tausayawa Abdullah yana cikin wani hali na barazana gaf yake da rasa numfashinsa ya maida hannushi ya dago habarta ya zuba mata narkakun idanunshi cikin nata suna fuskantar juna take
. idanuwansu suka sarke waje daya wasu abubuwa masu wuyar fassara ke fitowa daga idanunshi suna shiga nata " tayi saurin rufe idonta ahankali wayyo meyye wannan Kuma ? yayin da hawaye suka cigaba da biyo fuskarta. gabadaya jikinta ya dauki kirma lokacin daya wani tsoro yayi barazanar neman kai ta kasa '" tun kafin takai ga zubewa kasa ya taro abarsa ya manta da jikinsa "Abdullah ya sake zuba mata manya idanunsa dasuka gama rikicewa . akasan ransa ya iya furta rayuwa! rayuwa!! rayuwa!!! AISHA itace rayuwarsa Kuma Mafi soyuwa halitta acikin zuciyarsa" duk tsowan lokacin daya dauka batare da sanyata a idanunshi babu wani abu da yaragu game daita. sai ma kyaun data kara yi masa Sosai.. hancina yakai gefen wuyanta ya manna mata rikitattaccen kiss wanda wanda gabadaya ya susutawa Aisha tunani. tarinkajin tsigar jikinta natashi kadan kadan har suka Mike tsaye cak . , tana jin wani yanayi daban ajikinta ,wanda dabasan da zamansa ba, yahade jikinsu waje daya ya fara mata fushin bakinsa kamshin jikinta yana ta ratsa jikinsa yasa hannushi duka biyu yana share mata hawayen sannan ya janyo ta suka dawo kan gado ya zaunar daita yayinda shi ya zame ya dan tsgunno gabanta ya kai nasa hannayen akan nata dake zube kan cinyoyinta. ya kira sunanta ta dago ta kalli cikin idonsa ya runtse idonshi ,kallon da take masa yarinka rudashi daman can haka idanunta suke tsumashi duk lokacin da ta kalleshi ballanantana a yanzu da ya hadu da tsabar gajiya bacci ga kukan da tasha" tsigar jikinsa suka Mike yarinka jin wani sanyi nabin ajikinsa yayi saurin dauke idanunshi daga kanta "dan bai son hakan ya rude shi har ya rikita masa lisafin da zai manta da yanayin daya baro maminsa a dazu kafin su taho "ya jima bai ce komai ba ,sai da ya saisaita kansa sannan yasake kiran sunanta batare da ya kalleta ba yace Aisha ba kuka yakamata kiyi ba yanzu. duk kan wani abu daya faru ya wuce ina so dan Allah ki manta dashi a yanzu" gabanmu kawai zamu duba , abinda ya faru yarigada ya faru sai dai mu tsaya mu rungumi rayuwarmu ta gaba Allah ya nufemu da zama maaurata sai murike juna da amana. yana magana yana kara matse hannayenta cikin nasa nufi shi su rike hakan sosai ,ya koma ya zauna kusa da ita akan gado jikinsu manne da juna, yana son nuna mata yadda matsayin yake cikin zuciyarsa Amman bazai iyayin haka yanzu ba ,sake tuni maminsa dayayi ya aiyana aransa ko tasamu runtsawa " yasan daidai wannan lokacin indai bawani tashin hankali take ciki ba yakamata tayi bacci"ya runtse idonsa yana Jin yadda zuciyarsa ke dogawa dum...dum..kusan minti goma sannan ya bude su
ya kalli agogo dake daure da tsintsiyar hannunsa Shabiyu ke neman wucewa" yace Aisha mugabatar da nafila sai mu kwanta ko batayi musu tare suka Mike yayi gaba tabisa kamar yadda yaja hannuta zuwa toilet din dake manne da dakin ..

Sun idar da sallar nafila yayi musu addu'oi sosai kmr yadda dady yace suyi ko kadan yaki yarda su sake hada Ido da ita 'dan kallonta nasake riketashi ya maida ita kan gado ya jawo hannuta ya sumbata yace Aisha zanje in kwanta kiyi baccinki anan "kar ki sake yin kuka idan kika sake zandawo mu kwana tare

Please Login or Register in order to submit comment