Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba .
Dady ya yadan Nisa sannan yadago Ido yana kallon Abdullah sosai yaron nasa ke bashi tausayi ganin yadda soyayya tamai dashi cikin kankanin lokacin, wajen yadauki shiru zuwa na wani lokaci sannan dady ya iya Kiran sunanshi Abdullah ya dago yana duban dady ,dady yace Abdullah Aisha dai tayi Maka ko ? ya sunkuyar da kansa kasa yanajin yadda gumi ke bin jikinsa dady yasake numfasawa ya girgiza kai yace shikenan yanzu a yadda nike ganin a aika musu da dukiyar aure da duk wani abinda ya kamata Amman abari sai zuwa hutun karshen shekara sai ayi bikin ta yadda zaka samu hutun ka gabadaya .
Abdullah yajin jina kai dady yacigaba sannan yace akwai bukatar a sai musu gida babba mai wadatar guri musamman saboda taron daurin auri sai mota Hawa ina ganin biyu ko uku zata musu sai maaikatan da zasu taimaka musu da gyara koina ,Abdullah ya dago idanunshi yana wa dady kallon murna yana sakewa dady godiya. dady ya girgiza kai yana lumshe idanunshi shi awajen sa Abdullah ya cancanci fiyye da komai agunsa domin Samar masa farinciki.


Tun safiyar ranar litinin dady yasamu sakon da yake Jira daga South Korea suna neman su domin yin interview anan reshen su dake Denmark dan haka dady yasa hannu akan Abdullah ne zaiyi tafiyar wayewar garin talata kennan zai bi jirgin Lagos domin ta Lagos zai zasu tashi , yakasance Abdullah cikin uzuri yake har gurin magriba da Kyar ya samu bayan sallar ishai ya tafi gurin Aisha shi da salis yaya yusif ne ya fito yake masa baya ai tana can gidan aunty Maryam Abdullah ya duba agogon sa yana da sauran lokacin ,yayi sallama da Yaya yusif suka wuce.

Tun yamma taje gidan aunty Maryam ita kuma tarike ta sai ta kwana dan haka sallar ishai kadai tayi ta nade a gado har ta fara bacci Aunty Maryam ta taba ta taje inji Abdullah ta Mike tana kallon aunty Maryam sannan ta dubi agogo tara saura kwata sannan ta Mike a hankali ta canza kayan jikinta .

Da sallama tashiga falon bakin yana tsaye daidai kofar da zata sadashi da ita hannayensa rungume a kirjinsa ya langwabar da kai a jikin bango ,bata ji amsawar tasa ba Amman ta lura da yanayin kallon da yake binta dashi ta dauke idanunta dan tarigada tasaba da wannan mayataccen kallon nasa a hankali yazo daf da ita ya zauna suka hada Ido ya gane har tafara bacci ,ya lumshe idanunshi yana mai tabbatar wa kansa muddin yasameta zai ji dadin rayuwa da ita ya fada a kasan ransa komai nata bata cika daukarsa me wuya ba , hasalima ita ba komai yada meta ba,duka Bai fi rabin awa da mintina da idar da sallar ishai ba Amman har tayi bacci takan sauka kawa rayuwar ta akan abubuwa da dama ,hakan yasa take sake shiga ransa Sosai da sosai , yanayin kallon yake mata yasa kirjinta yarinka bugawa , Abdullah yakira sunanta yace Aisha I love you ,I really love you please tell me do you love me? ........




MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page13


Tayi shr batace komai,tashiga wani yanayi na daban, tarasa gane kanta meke shinrin farawa da rayuwata ta furta haka acikin ranta , Abdullah nasan ruguzamata zuciya da wayan nan idanun nashi masu frigita ta ZUCIYAR duk wanda aka kalla dasu, ta takasa amincewa da farinciki take ciki ko tashin hankali a lokacin guda km taji kamar ta tambaye shi ko zai iya amsa mata tambayoyin da suke cunkushe akasan ranta masu neman tarwatsa mata zuciya da tsantsar jiki "da idanu take binsa da kallo tanason taganu ko shima yashiga makamancin halin datake ciki " shima ita yake kallo ,yayi murmushin daman yasan bazata iya furta Kalmar daya nema daga gunta ba " , acikin zuciyarsa ya furta" OH" ni Abdullah tawa tasamini nashiga one chance , ya zuba mata manya idanunshi yace gobe zanyi tafiya ta dago dara daran idannuta ta kalleshi yasake yin murmushi yace a kallonki nagane tambayar ki , Aisha ni bazan yarda da wannan shr naki ba idan munyi aure kidinga kinmin magana ba gaskiya ya fada har da turo baki batasan sanda murmushin kufce mata ba shima dariya yayi Amman nasan abinda zan dinga miki zaki dinga yimin magana sosai ,ni kadai nasan abun.
Tasake yin murmushi yana kallonta kaunata na sake huda masa zuciyarsa, yadan gyara murya cikin natsuwa yace Aisha zanje interview a Denmark gobe zamu wuce Lagos ta can zamu tashi nan da kwana uku zan zauna interview Aisha kiyimin addu'a samun nasara ,dady ya zabi da inje in zauna masa ,har inajin tsoro Kar inyi disappointing dinsa ya fada yana kallon kwayar idanunta yanason tace wani abu ta fahimce abinda shr nasa yake nufi ta dan girgiza kai sannan ahankali tace zakayi nasara ya dan kalleta yace meyasa kika ce haka tace nasan zakayi nasara in Allah yaso "ya lumshe idanunshi yana mai jin tsanyi na ratsa kowani sashi na gangar jikinsa ko ba komai yau tazo masa da abubuwa masu mahimmanci daga gareta yace to Allah yasa Aisha bbu igiyar aurena akanki Amman ina da matukar kishi most especially akanki sati biyu kawai zanyi Aisha dan Allah kada kibari wani yashiga tsakaninmu Kar ki Amince da duk wani abu da zai bata tsakanimu a yanzu haka nasan ni ba wani zaunanne ne a ranki ba Amman ina sa ran idan muyi aure zaki soni , Aisha inajin tamkar in tafi dake idan muje can a daura mana aure Aisha ina son Allah yabani ikon Yi miki abunda zaisa ki so ni idan muyi aure .
Yadda yake maganar ya dada sa kirjinta yacigaba da bugawa..
. wuraren daban daban na halittar jikinta ke bude suna karfan sakoninsa" a zuciyarta tanason ta furta masa koda kalma daya ce mai mahimmanci da zai tafi dashi Amman hakan ya gagareta sai binshi take da shanyayun idanunta yayinda take sake kashewa Abdullah jiki , Abdullah ya dubi agogon hannushi karfe goma ta shige yace wai Kar aunty tayi fushi dani pas ten Aisha ta Mike cikin sanyi jiki uhmm har sauri kike ki tafi kibarni ko, ta sunkuyar da kai shima ya Mike yace akwai zanen company da guest house da zanyi acan shine Nike ganin zai tsayar dani har tsawon sati biyu ban da haka da next week zan juyo "tsaitin datake tsaye nan ya tsaya suna kallon juya ,ya suke hannuwanshi duka acikin aljihun wandonsa kara step uku yayi zuwa inda take har suna jin bugun zuciyoyinsu ya xuba mata idanunshi shidai yana son ta har bai san yadda zai misalta ba ,ita din wata sashi ce ta zuciyarsa yasake tsareta da Ido yace Aisha me zaki bani zan tafi ?
Tayi shr takasa cewa komai ,yace to ke me kike so daga gareni ?ta girgiza kai yayi murmushin yace gobe salis zai kawo sako har da Nasu yaya yusif dukansu ,ta kalleshi tana tunanin shi baya gajiya da kyauta ne ,ta tuna kyautar kudin da yayi mata ba a kai sati guda ba har tsoro suka bata da sauri ta rufe ledar ta wurga su bayan akwatin kayanta har zuwa yau bata kuma bi ta kansu ba. hakan nan bbu wanda yasan dasu yanayinta ya kalla ya gane tana son Yi masa godiya ne kawai ya share ta yacigaba yasake duba agogo yace let me go Aisha please say something for me wanda zai yimin rakiyya da ragemin yawan kewarki da zanyi har tsawon sati biyu ya zuba mata idanunshi yace I'm gona miss you Aisha please ya maimaita kusan sau uku kicemin wani abu mana ..... still tana tsaye kmr an sassakata ,yaga alamun bata da niyar yin magana yace ba zaki gaya min komai ba ko haka kike son na tafi ya furta hakan yana mai langwabar da kai to muje har gaban aunty nace ta roke ki kigayamin abinda zai dinga tayani bacci , ahankali yake matso ta tana ja da baya har ta mannu da bangon dakin yayin da zuciyarta ke dokawa tana harbawa gabadaya jikinta yagama mutuwa murus kafafuwa sungaza tsayuwa akaran kansu da Kyar ta iya tattaro dukan wani kuzarin dake jikinta ta furta I will Miss you too........ Hade da lumshe idanunta tana jin wani tsanyi na ratsa sansar jikinta yasake motsata sosai ya tsaya kawai yana kallon bakinta da yadda ya hudu ya furta Kalmar sai yaji kmr ya daura bakinsa akan nata mai abin sha'awa ya zuba bakin Ido yana mai cizan lip's dinshi gefenshi ta bi zata wuce dan baza iya jurewa kallon dayake binta da shi ba,ya kamo tafin hannunta cikin nasa ya matsesu gam wani shock suka alokaci guda yana musu yawo ajikinsu sakamakon haduwar da tafin hannyensu ,kokarin cire hannunta takeyi daga nasa batare da sun kalli juna ba sausauta rikon ta yayi ta zame hannunta ta saya dai dai bakin kofar ciki tana kallonsa yadda yake kallonta ne yasa tarinka jin wani abu atare da ita nan da nan ta juya ta shige dan bata son irin abun da tafara ji a game dashi din bata San iya lokacin da ya bata kafin yatafi ba, .


Tafiyar Abdullah da kwana shida maminsa tadawo Nigeria to abinda ta tarar ya maseefar gigitata domin dady yagama zartar da komai na batun auran Abdullah abin ya daure mata kai tana can dady na nan yana shirin yiwa Abdullah aure batare da itama an tuntubeta ba "tsawon kwanankin dayawa da dady ke nuna mata me za'ajira tunda Abdullah din yadamu da yarinyar kuma ta kowani bangaren yarinyar tayi illa daya gareta shine su din bawa wasu bane "ya nuna mata wannan ba wani abu bane tunda Abdullah yana son yarinyar bbu abunda zai gagara"mami tace Amman auren farko daza'atabayi a gidan nan yadace ace Yar manyan mutane zai aura koma ba haka ba a samu wacce akasan halinta ciki da waje ba irin wannan ba dan ni halin danaji daga bakin mutane batamin amatsayin matar da Abdullah zai aura.

Dady yayi murmushin to ke bakisan mutum da shi da kansa bai san yadda halinsa yake ba sai mutane sun fada ,to duk yadda dady ya bullo mata sai tace ba haka ba ,akarshe yace shi kam yariga ya gama magana ,in Allah yaso Abdullah bashi da wata mata sai zabin ransa sai kuma idan bangaren yarinyar ne suka ki.
Ran mami in yayi dubu to ya baci kwata-kwata a wannan taki jinin yadda dady yake mata musamman akan Abdullah Dr sagir ta fara sa aka nemo mata ta tunhumeshi akan maganar yarinyar da Abdullah yake nema iya abunda yasani shi ya fada mata to shi din yana da sauran kima a idon mami "Amman salis kuwa fata fata tayi masa ta kuma rantse akan idan har ta kamashi yana da hannu a hadin Abdullah da yarinyar nan to ya kawo karshen aikinsa . domin wannan karon bada salis Abdullah yayi tafiyar ba tare da security din dady sukayi RK da Immanuel shima (SS)ne na dady hatta part din Abdullah mami da kanta taje bbu wani abu data samu na game da yarinyar .

Mami na cikin wannan tashin hankali mama hafsa ta dira a kebbi tazo yiwa mata gaisuwa ta tarar da wannan mummunar labarin kusan ma hankali mama hafsa har yafi na mami kololuwar tashi, ita mama hafsa a yadda suke ji ayanzu ita da faiza da su rasa Abdullah gwara su rasa mahaifin faiza .to duk dai yadda mami ta kai ga bincikenta akan Aisha bata samu komai ba mama hafsa ce ta fara kawo shawara suje inda iyayen Aisha suke su samesu , haka kuwa akayi da yamma ranar lahadi mami tasa musa ya tuka su dan tasan duk munafukanta ne" sun san inda Abdullah ke neman aure har gidan mlm abu tun daga inda suka sauka suka Tako lungun gidan komai yafara tsinkewa mami kmr ta zubda kwalla haka takeji , tama yaya Abdullah me kamkyame yake iya shigowa wannan kazamin lungunan .

Aisha na tsakar gida tagama daka kayan Miya tana gyara zogale da zata musu Miya kmr wadda akace ta tashi kawai tashiga dakinta ita kanta ta rasa me ta shigo dauka ta jiyo sallama daga kan da zatayi ta window tagar tayi arba dasu mami Amman su basu ganta ba ,idan aka cire shekaru za'aiya cewa Abdullah na biyu ne yazo gidansu Amman sai dai wannan macce sabanin shi" Aisha ta fadi haka aranta tunda take a rayuwa bata taba ganin halitta da sukai kama sak ba irin Abdullah da wannan bawair Allah da batasan kowace ce ba,tabbas Abdullah balarabe ne akamaninsa da yanayin shigarsa zaka gane haka ko bai sanar ba, murya mama hafsa ce ta doki kunneta tana cewa A'a mu ba zama muka zo Yi ba ...........



MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 14

Murya mama hafsa ce ta doki kunneta tana cewa A'a mu ba zama muka zoYi ba" mama hafsa tadan juya ta kalli sashin gidan duk ba kowa sai yaya umar dayashigo zai dibi ruwa a botiki sannan ta juya takalli Inna tace ke kadai ce a gidan kece uwar yarinyar kennan to ina uban nata yake ? Gaban inna ya fadi ita bata fahimce ta ba sosai domin idanunta nakan dayar matar dake tsaye wacce tun shigowasu suke bin juna da kallon sani "sai da tace iyayen Abdullah ne wanda kuke son manna masa yarku ita kuwa mami karewa gidan kallo take tun daga sama har kasa tana girgiza kai tana gudun Kar ma wani abu yafado mata aka.
Mlm abu yana titi inda suke zama inna tasa yaya umar yaje ya kirawo sa suka taho atare ,tunshigowarsu shima da kalmomin mami yagane daga inda bakin suke da saurin jiki mlm abu yakaraso Amman daga kallon da mami tai masa yasa jikinsa ya danyi sanyi ,zai Yi magana mama hafsa tace dakata malam ba maganar ka muka zo ji ba ,kasan ko daga ina muke ?
Mlm abu ya tsareta da Ido shima duk da tarin talaucinsa bai san wulakancin , tacigaba mu iyayen Abdullah ne wanda tsiya tasa kuka masa kiranye mlm abu yace tsaya kiyi magana da kyau ki fuskanci abunda kike fada "mami ce tayi magana ba tsari ne yakawo mu ba Abdullah ya taka ya burma an kulle shi saboda haka nake son dan Allah abar mana dashi , ma'ana karaba banzar yarinyar ka da dana zan mallaka maka duk abunda kake so tun daga kan naira daya zuwa million goma nasan bakasan ni ko wacce ba Amman ita wannan tasanni ta nuna inna da yatsanta ,ke kuma kin xubamin idananu kmr zaki cinye ni ki masa bayanin ko Wace ce ok saboda kinkasa shawo kan ishaq da asiri shine zaki bi takan " dana" to wlh bazai yuwa ba ,mlm abu tsaye ke yana bin inna da wannan matar wato mahaifiyar Abdullah da kallon saboda maganganun ta suyi masa kama da mai tabin hankali , mami tace ka tsare ni da Ido ka tambayi matarka zata maka bayanin koni wacce ,mama hafsa ta karba idan karaba atsakaninsu yarka da Abdullah kaga kunyi hannu riga da talaucin kennan.

Yaya umar ya dago zai mayar mata mlm abu ya hanashi cikin matsanancin bacin rai yake dubanta shi kam ba girmansa bane ya tsaya yana sainsa da mata ,ya dubi mami tana da wani nasibi atare da ita tamkar yadda Abdullah din nata yake uwa uba daraja da kimar da mijin nata yake dashi wato mahaifin Abdullah ,taci albarkacin hakan da ya mayar mata da wacce tafi nata na zafi, yace duk abunda aka fara shi cikin arziki ya kamata a kareshi a hakan saboda haka za'a barmu ku danku , koma ince an bar muku , Amman ku bakuda abunda da zaku bamu wanda zai wadatamu da mutunci a idanunmu ,"mama hafsa tayi sauri ta cafe ai magana takare in dai kun rabar mana da Abdullah , Amman banda haka uhmm taja numfashi , kuje kutako daidai ku mana ko wanda yadan gota ku Amman dan tsiya sai ku tabo kuloluwarku .
Anan inna zatayi magana mlm abu ya sake hanata mami tana kallonta tana girgiza kai ita duk yadda ta tsani abu sai taga bai kai iyanzu da take tsakar gidan ba, ta dubi zogale dake gaban inna ita dai wlh sun gama da ita yanzu haka irin abinda suke bugawa Abdullah kennan a cikinsa ta fada a ranta ,.

Mlm abu ya numfasa yace ina fatan idan kun koma zaku sanar da kafar data zo neman diyata tazo ta karbi duk wani abu da aka kawo da sunan neman aure domin yanzu bama bukata .
Mami tace shiyasa nace idan kuna bukatar Kari kuzo zan kara muku duk wani abu da aka kawo muku na Abdullah ko ninkinsu ku tattara kurike abarmuku Abdullah din kawai muke so ku rabu dashi. Mama hafsa tace kun samawa kanku lfy idan kuka rabu da Abdullah haba to da angaya muku tsiya ko talauci hauka ne ,da zai sa duk ku rufe idanuwanku ku kasa duba abunda zai yuwu kuyi ta hauka tamkar masu karfi .

Maganar tayi tsaye a ZUCIYAR duk wanda yake gurin hatta mami da suka zo tare tana ganin kamar maman na nema kauce hanya Amman da yake itama zuciya na zugata nan da nan Kuma abin ya mata dadi ,mlm abu yayi sai da ransa yana yimata kallon wanda ta fisu hauka da talauci ,Killa ita ce dukiyar ta ruda take neman haukacewa dan da ganinta ko kadan ba jinin arziki bace .

Inna kuwa bakin ciki ne kawai ya turnuketa har bata sanda take zubda hawaye ba ,gashi mlm abu ya hanata yin magana ,yaya umar dake tsaye shima ganin inna na hawaye kawai shima yasoma kuka yanaji aransa da Ali ne daya fi kowa zuciya haka tafaru a gabansa baba ya hanashi magana Killa da tuni zuciyarsa tayi bindiga .

Mami tace magana ta karshe kuma ina fatan zaku hanzarta aurar da diyarka ga gajeyaye irinku .
Mlm abu yace wannan abunda ya shafemu ne gargadi kuma ki koma kiyiwa danki ,domin duk randa ya kara tako harabar gidana hukumace zata raba mu dashi..

Mama hafsa tace idan har ba tune abinda aka binne masa ba ai kuwa dole zaku ganshi .ta dubi inna hade da mata kallon banza tace dan Allah akoma riga a tone sirkulle da akayiwa yaro ko yasamu ya huta ,a daina mana haukan karya,sai da suka Yi rashin mutunci son ransu sannan suka tattara suka bar gidan .

Ko a mata ma haka mama hafsa tayi ta tsenewa Aisha da danginta, ta juyo tadan kalli mami tace naji kmr kina wani zance ishaq da ita wacen banzar matar manene a tsakaninsu" mami tayi shr tana kallon gefen titi yayin da tashin hankalinta ka sake nun kuwa,tabbas tasan da dadyn Abdullah yasan inda yar'uwarsa take da tuni ya sauya mata rayuwa kuma tanaji ajikin baisan wacece yarinyar da Abdullah ke nema ba" Mama hafsa ta maimaita maganarta ta kai sau uku Amman shr takeji akaro na hudu ne mami ta juyo ta zuba mata Ido tace kanwar dadynsu Abdullah ne uwa daya uba daya .....daga haka bata sake cewa komai ba ta dauke kanta tamayar gefe ,banda gume bbu abunda ke fita daga jikin mama hafsa hankalinta har yafi na mami tashi surutai kawai take acikin ranta lallai zama bai ganta ba .

Washegari mama hafsa tabar kebbi bbu yadda mami batayi da ita ba akan ta zauna Amman taki ita kwata-kwata hankali har yanzu a tashe yake gara taje tayi da jikinta tunda tayi da baki dole mami ta hakura ta barta , Amman tace cikin satin zata dawo .


Cikin yardar Allah jirginsu Abdullah ya sauka a Nigeria karfe shabiyun rana cike da kwarin gwiwa da farinciki Abdullah din yake ,tare dimbin nasarori daya samu fiyye da yadda dadynsa ya zata ,har byn karfe hudu suna tare da dady sai karfe biyar na yamma yashiga part din mami anan ma mami rikeshi tayi da girke girkenta tana tattalinsa har zuwa dare tafi kaunar yasamu natsuwa sosai kafin tayi masa zance yarinyar dayake so ,tana kallonsa tare da yan'uwasa tana sake Jin kaunar dan nata fiyye da komai da ta mallaka kallon shi take tana tausaya masa " teema tace bros what do you buy for me?
Abdullah yayi murmushin i will tell you letter bana son minal taji suka Yi dariya gabadayansu teema tace banda ni kennan yace kowa da nasa ..mami ta zuba masa Ido har yanzu ZUCIYAR ta tana damuwa da inda yaje neman aure Abdullah ya lura da yanayin kallon da mami ke Yi masa Amman bai kawo komai a ranta ba .

Sai byn sallar ishai yashiga part dinsa,ya furta sunanta Aisha.....akasan ransa ita din wani part ce na rayuwar sa dan haka dukkan wani abu da yakeyi tunaninta yana makale dashi dan haka yanashiga part dinsa tasake zuwar masa daman sai dai in bai kadaita ba "har ya fito daga wanka yanajinta sosai aranshi ,ya fito da system dinsa ya bude a tsakiyar gadonshi ya danno hotonta daya dauka da school uniform a jikinta tana dariya ,ya kura mata idanunshi yana tuna murmushin da tamasa daren da zai tafi hatta dasashinta da wushiryarta sai da yagani ,kusan duk sanda ya rufe idanunshi sai yaga hakan yatafi da yanayin fatarta chocolate sosai colour dinta tadace da ita, wanda bai sani ba kai tsaye zaikirata da farar fata ,yaja numfashi black American kennan ya fada a ransa jikinsa yabashi tayi masa addu'a r da tace zata masa a daren ranar da zai yi tafiya kuma yana da yakinin Allah ya amsa gashi yayi nasara fiyye da zatonsa dan idan aka cire mami da dady itace uku da zata masa addu'a ta sameshi. shi yasa yake son itama takasance wajen raba farinciki sa , Amman hakan bai samu ba saboda shi kansa bai samu kansa ba har dare.......


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 15

Washegari tun safe suna tare dady suna tura sakwanni wa sauran branch din company dinsu dake sansa daban daban "Dady sai
shagwaba Abdullah yakeyi hade da ririta shi saboda namijin kokarin dayayi".Sai bayan sallar ishai sannan yashiga part din maminsa yayi dinner ya Mike hade da mata sallama mami takira yadan juyo yana karyar da kai ta tsareshi da idanuwanta ina zaka kuma yau kusan kwanaki masu yawa ban saka a idanuna ba balle muyi hira Abdullah yayi murmushin mamina ina zuwa ba koina zani ba tace A,a sam banyarda ba dawo ka zauna yadawo kmr yadda tace kallo daya ta masa tagane inda yake son zuwa, ta hadiye abinda taji ya tsaya mata a wuya.. sannan tasoma Yi masa hira tun yana gane kan zance nata har yazo bai Gabe abinda take cewa gashi sai yamike da niyyar barin falon sai dawo dashi , uhmm yauwa Abdullah sai ta kuma dauko wani zance a haka dai yasoma tunanin yasan yauma dai maminsa tana son ta rusa masa burget dinsa daga karshe yagama fuskantar mami batason fitarsa ne ya Mike yayi kwanciyarsa akan three site din falon ya runtse idanunshi yana Jin yadda zuciyarsa ke harbawa ""ya daura hannushi daya a dai dai saitin da zuciyarsa ke harbawa gabadaya ji yayi hankalinsa bai gangar jikinsa tun yanajin mami sama har yazo bai jinta yanan

Please Login or Register in order to submit comment