Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kawai zai tashi .
ta kudindine jikinta har kanta da bargo Amman sai ga Abdullah din har acikin bargonta yana shashafa mata jiki da kaiwa wuyanta sumba. domin a haka suke kwana ita dashi wai sai taji shi yana tayi mata rada a kunne yadda yasaba tasa hannuta duka biyu ta toshe kunnenta tana mai runtse idanunta gam.
Amman still bata fasa jin hannushi a tsantsar jikinta yana sarrafata ba kmr yadda yake manne mata a duk lokacin da suke tare .
Kawai taji wasu hawaye masu dumi nabin gefen fuskarta , ahankali take kukanta tana sake felling din tumin jikinsa yasan zai barta meyasa kullum yake mata hudubar da zata so shi , tabbas ita da kanta bata ja akan soyayyar Abdullah tasan zuwa yanzu son shi ne zai yi ajalinta .why why Abdullah why did you do this to me ?
meyasa sai da ka koyamin yadda zan soka sannan kabarni "meyasa ka cutar da zuciyar da bata san komai sai tsabar kaunar ka da tunaninka.ta takure jikinta waje daya wlh ina sonka ina sonka dan Allah kadawo gareni zuciyarta bazata iya hakuri rashinki ba tana sake jin Yadda yake yamutsa a bed ahankali tacigaba da kukanta acikin bargo batare da inna ta fargaba .

Dr salim ne ya shigo da kayan Niki Niki ya ajiye sanye cikin kananan kaya suka gaisa da inna har inna na mamakin siyayyar da yayo.
Shi kanshi Dr salim ya gano hakan a fuskar inna.
Dan haka nan da nan ya sauya dan karta dagoshi yace sister Maryam bata dawo ba kennan ?
inna tace ta dawo dazu Amman yanzu ina ganin Kuma sai gobe .

Dr salim yace ok to idan tazo ace gashi inji wannan likintan salim idris a bawa mara lfy inna tace madallah an gode za'a gaya mata.
cikin rashin kulawa sosai ya dan kalli gadon da Aisha ke kwance yace har yanzu mara lafiyar bata tashi bane ?

Inna ta dube shi cikin sakin fuska tace ta tashi tayi sallah har taci abinci bata dade da kwanciya ba.
ta kirawo sunanta bata amsa ba tace ina jin bacci ya Kuma dauketa .

Dr salim yace musamman saboda allurar bacci dake jikinta sannan yayiwa inna sallama cikin sanyi jiki ya fita .

Duk tana jin su bata ta amsasu gudun Kar su Gane kuka takeyi shiyasa tayi kmr mai bacci .

Dr salim idris da gangan yaki zuwa asibiti da wuri a washegari a dalilin shi yake son yacigaba da duba tafiyarta.
,dan haka ya kulle file dinta a office dinsa gudun kada ma a gano hakan ya hada tare da files din wasu marasa lafiyar hudu ya duk ya rufe a office.
dan haka har aunty ta iso shi bai karaso ba da kyar tasa ta gyara jikinta ta sauya kayan aunty da tazo mata dasu masu launin pink wanda suka kara fito mata tsantsar da kyaunta tamkar ranar bikinta .
fuskarta fayau babu make up Amman kallo daya zaka mata kaji tashiga ranka .
ita da kanta aunty Maryam sai da ta tsaya kallonta to ko daman cikin ne yasa tayi wannan shegen
kyau.
a haka tana kallonta Dr salim yayi sallama gabadaya suka amsa masa Amman banda Aisha dake zaune tana da yatsunta aunty Maryam tafara dariya tana gaishe shi hade da godiyar kayan da ta tarar. shima murmushi yake yayi yana gaida inna ya waiga inda Aisha take gabansa yayi mugun faduwa a yadda ya ganta shigar da tayi ta bugar masa da kwalkwalwa ,meyye ke shirin faruwa dani ne tambayar daya fara watsawa kansa kennan . ya kasan ransa kuma yace gata Kuma sanye cikin colour's din dana fi kauna a rayuwarta.

har yakai bakin gadon inda take bata dago ta kalleshi ba.

shi Kuma kallo daya yayi mata ya Gane I don't care ce .
yaji numfashinsa na kokarin sarkewa saboda dagowar datayi ta dan kalleshi yayi dan gyaran murya sannan yace sannu .
Bata amsa ba , Amman ta dai daga masa kai sai ma yarasa me zai ce mata.
kawai ya bude file dinta yarafa dubawa duk jikinsa yabashi har yanzu su aunty Maryam shi suke kallo aunty takaraso tace doctor ai naga jikin nata yayi kyau tun dazu wai ta matsu a tafi gida .

Yabar abinda yake ya dan kalleta fuska a sake yace yaya kike jin jikin naki ta kalleshi da tsumammu idannuta da suka kara birkitawa dr salim brain.
ahankali muryata a sanyaye tace ni na warke .
Gabadaya ma kennan ya fada a ransa ,yadda ta fadan kmr zata saka mishi kuka yaji wani abu na masa yawo ajiki .
ya saki numfashi ahankali yadda bbu wanda ya fahimci halin da yake ciki.
ganin ba zai iya cigaba da kasancewa a gurin ba.
yayi murmushi yace to kikara hakuri ki dai kara bari zuwa anjima sai a sallame ku ni zanje in duba patient ya fita .

A office dinsa ma dafe kansa yayi yace wannan wacce irin maseefa ce take son afka masa na son matar aure.
komai da yake tare daita hatta tsarinta shi yake nema a gurin macce da yake son mallaka.
jiya fa ko wadataccen bacci kirki bai yi ba a saboda matar wani .
ko kadan batayi kama da marasa kamun kai ba, dan haka zance ko cikin shege ne a jikinta ma bai taso ba .
musamman dayaga bbu wani daga hankali da family dinta sukayi da batun cikin ,idan kuwa yakasance shegene kuwa da shi da kansa zai fahimta a tsakaninsu abu biyu ne cikin daya da lura dashi lokacin daya sanarwa sister Maryam zance cikin ta dinga maimaitawa? Amman Kuma zai iya kasancewa ko saboda cikin fari ne me yuwa ko tayi saurin samu ne .
Shiyasa take dan mamaki ya sake numfasawa ya jingina bayansa jikin kujera yana jujjuyawa hade da rufe idanunshi ya dan langwabar da kai tamkar me jin yuwar daya rasa abinci ci kwana da kwanaki .
Ni na warke" ya tuna yadda ta fada me yuwa Kuma Yar auta ce shi yasa take a haka
kmr zatayi shagwaba.
ya hada hannuwansa guda biyu ya harde a kirjinsa yana tunanin mafita da kyar dai ya samu dan wani abin kamawa da zai tunkari sister Maryam dashi sannan ya Mike ya sake fita


Uhmmmm it's just the beginning oooooo




MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ina, Mika ta'aziyyata ga faiza Anfa marubuciyar danfashi Allah ya jikan mahaifinki ya Kuma mai rahma yasa ya huta ya Kuma kyautata namu , Allah ya raya abunda ya bari yabasu hakuri rashi Ameen .



Page 45 -46


"Oh,oh ni hafsa ,Allah baki ga Yar yarinyar da Abdullah ya aura ba duka bata fi rahma ba ,inji cewar mama hafsa faiza tace Allah mama .

Yo ina takai cikar rahma sai kayan nonuwa da shegen idanu suna narai narai sai kace wata macijiya .

Faiza tace wayasani ma ko macijiyar ce,
Tarikide ta manne masa kinsa fa suna yin haka .

Mama hafsa Tace Ko daya, kinsa fa asalinsu fulanin dajin nan ne.

mama hafsa ta rage sautin muryata tace to komai fa ya gamu tun shekaranjiya yarinyar tana gidansu .

Faiza ta daka wani irin tsalle murna hade da rungume mama hafsa. Cikin rawar murya tace mama gaske kike ?

kina nufin Abdullah ya saki banzar yarinyar nan .
Zauna nan an gaya miki ni din ta wasa ce , ai tuni rauhanai sun gano sakin tun wajen duba gashi Kuma an yi shi,. Dan haka kishirya gobe gobe nan.
ki tafi dan nafison ayi abin da gaggawa tun kafin kinibabben wancan uban nasa ya dawo .

Haka kawai muda shan wahala wasu da jin dadi ai wannan ma bazai taba yuwa ba .
ai tun da mami ta lasamun zuma a baki naji nakasa hakurin kirasa Abdullah .
gara komai zai faru ya faru wlh.
da dai kirashi dadi yasake kama faiza .
Faiza ta tashi bbu kunya ta dinga tikar rawa tana juyi a gaban mama hafsa.
tace jaira tunkuna dai kibari kishiga daular Abdullah sai ki cashe yadda ranki ke so .
faiza tace ai wlh kodan kyansa kadai zan'iya aure shi ,
gashi namijin duniya tana magana tana girgiza jiki .
Ke matsa can wawiya banza ana maganar masu nauyi kina magana wani kyau.
ai idan bbu kudi ai ko shi kansa kyan baya wani tasiri ,.
faiza tace ai wlh dan dare yayi ne da yanzu zan tafi tunda kince ( boka dan ina da Kare) yace wuyarta a raba su ,idan aka rabasu komai zai daidaita .

Mama hafsa Tace haka yace Kuma bakisani ba har uwar ma a yadda ta nuna min sai yadda nace .
, dan haka banason abin yawuce wata daya ke Kuma kina shiga sai ki san yadda zaki mallaki dukiyar kinsa gidajen wannan ubanku nasa a market na siyar .
kinga sai amaida masa batare da ya ankare ba .

sannan takara rage sauti sosai tace duk cikinku kece nake ganin zaki biyo ni, kinsa Allah banki ace wannan kanjamammen uban naku ya mutu ba nima in koma in aure uban Abdullah.
tunda an yarda da halacci haka ,faiza tace kai mama babanmu Kuma tace shifa.
to meyake tsinana muku ,shege mutun sai dan banzan son abin duniya tsiya.
mai kan goruba kawai faiza ta saki wata uwar dariya har da rike ciki ,.
mama hafsa tace ai wallahi bari kiga mugama da naki .
ko yaya naga waje fadawa zanyi mutaru ayi ta damawa damu.

faiza sake kecewa da wata dariyar tace kinga munkasa mun tsare kennan mun hana gaba mun hana baya komai yadawo hannunmu tabawa uwar hannu duka tafa .. .

Mama hafsa Tace uhmmmm ana magana ma shiyasa nake sonki dan nasan duk abinda na tsara bakya kii..
sai dai kinsan Allah ina tsoron alhj ishaq har cikin Raina.
faiza tace dady ko tace shifa ,kina ganin ko irin dan wasan nan na dagin mata bai so.
bayan gaisawa ba yarda wani abu ya gilma. Amman nasan ta yadda zanyi ai duk wani taurinkai akwai maganinsa .

Faiza ta Mike tace bari kiga mama naje nasoma shirina tun yanzu kinsa da zazafi ake buga karfe .
mama hafsa tayi murmushi tabi diyartata da kallo tana rayawa a ranta ai ba zaki sha dadin ke kadai ba.
har dani za'a.
yadda nayi sintiri a gidajen bokaye da makabartu ne zan zauna sai kin mikomin ahankali ta Mike itama .


Duniya gabadaya ta cukede ta tsayawa Abdullah waje daya ,.
yarasa wacce irin rayuwa mahaifinsa take son yayi byn taraba shi da tsanyin idanunshi .
Tun yana kuka da idonshi har yadawo yin kukan zuci ..

Gabadaya wayoyinsa ma a kulle suke komai ya tsaya cak rabonsa da zuwa office tun ranar da dady yabar kasar.
ya gwammaci yacigaba da zama a mataccensa har ran da za'a kaishi kabari da dai ya fida
koina ,

kwanansa uku duk wata al'ada ta rayuwarsa ya barta inka dauke sallah . Ko magana bayason yi idan mami ta turo yazo haka zai zauna a gabanta bai fahimtar komai, ko fada take har tagama bai jin abinda tace ,.
shi a lokacin ko mami yankashi zatayi bazai damu ba .
Dr sagir ne yake buga kofar part din Abdullah da karfi gaske,
yana kiran sunanshi Abdullah Abdullah jin muryarce yasa Abdullah ya zubawa kofar ido yana jin Yadda kirjin ke radadi da ciwo mara misaltuwa.
jin an cigaba da bugun kofar ne yasa ya Mike da kyar ya bude yana budewa yayo gaba abinsa.
Dr sagir yashigo yana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun..ganin yanayin abokin nasa .. friend meyye haka kana da lfy kuwa five days kana cikin daki a kulle.
ko ma'aikatanka , ka hana su , shigowa su gyara maka guri,
Abdullah dubi yadda kadawo ya zauna agabansa yana nuna shi da yatsa .
salis ma yace ko shi kaki yarda ka Gani why..

Abdullah yayi kwanciyarsa akan kujera bai ce komai ba domin zuciyarsa ke wani dokawa yasa hannunsa duka ya dafe kirjinsa dashi .
cikin mamaki Dr sagir yake kara kallon koina sannan yace ina matar gidan take.
ina Aisha nace, sunanta dayaji ne yasa ya dan ya kalleshi ,Dr sagir ya sake maimaitawa Abdullah tambayar , Abdullah ya dubishi yace na saketa da sauri Dr sagir yace what .
Abdullah ya amsa da kansa alamun haka ne.
why ar you talking rubbish Dr sagir ya fada a fusace ,.
Abdullah ya dan yi murmushin takaici ya sake kollonshi , Dr sagir ya sake dafashi cikin sanyi murya yace my friend meyake damunka ne na nemi wayar ka bansamu ba ,na dauka ko baka kasar ne jiya naje office ance baka zuwa, .
anjima zan wuce sokoto shine nabiyo nayi checking din ka .
ance baka ganin kowa salis nasamu sannan nashigo friend meyasa Meka haka kasan abunda kafada min kuwa.
Abdullah ya dan Mike zaune ya kalleshi ido jajur murya a raunane yace Dr sagir lafiya ta kalau .
da gaske na rubu da mamata, mami ce ta zabi haka ,dan haka na saketa.
Dr tunda na auri Aisha duk abinda zai sani farinciki shi take min to yanzu bata nan mun rabu me zai sani farinciki kuma ? kawai ya koma ya kwanta yana sakin numfashi sama sama tamkar mai cutar asma.
ya rufe idanunshi gam yana tuno Aisharsa bai sake yin magana ba sai wasu zafafan hawaye dake gefen idanunshi can kuma jikinsa ya dauki kirma ya kamo lip's dinshi gabadaya ya tura abaki ya datse da hakoranshi wannan lokacin yazo masa da abubuwa munana masu wuyar mantawa ko awani hali Aisharsa take ..a kasan rashi yace killama tana can cikin jin dadinta tunda daman ba sonshi take ba shi kadai yake shan wahala akanta mamina maye yasa ...meyasa kikawa Abdullanki haka baki san bazan iya rayuwa ba muddin kika rabani da ruhina ,.
Aisha zuciyata ita bugun zuciyata sosai jikinsa ke rawa yayinda idanunshi ke runtse ahankali fizgo numfashi yana sake dafe zuciyar.....


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 47-48

Dr sagir ya zuba masa ido watau har yanzu dai rikicin mami na nan kennan na rashin son auren Abdullah da Aisha.
a ganinsa zuwa yanzu ya dace ace mami ta barwa Allah komai .
ya jima, yana jinjina al'amarin sannan ya numfasa yace Abdullah a hanya nake yanzu.
bbu wani hanzari da zan iya Amman karaba kanka da wannan kadaicin .
,kada ka mutu a cikin daki kai kadai.


Ganin yadda jikin Abdullah har yanzu rawa yake kmr mazari yasa Dr sagir yin hanzarin Mikewa ya ja hannunsa zuwa bedroom ya kwantar dashi kan gado sannan ya dubo wayoyinsa duka ya kunnansu da duk wata na'urar dake dakin.
sannan ya koma waje yayi kiran salis yace a shigo a gyra koina.
ya koma kusa da Abdullah wanda yake kwance yana numfashi ahankali, yace da sati guda zanyi a sokoto Amman ya zama dole na rage kwanakin su koma hudu zuwa biyar saboda yadda na sameka Amman dan Allah ka tashi yanzu kayi duk abinda kasaba Aisha...sai kuma yayi shr yakasa magana ya dan dafe kai shi yarasa ma wani abu zaiyi akan lamarin ,ya girgiza kai yana duban agogonsa yace dole ne in dawo da wuri saboda kai Amman zan neme ka dana isa.

Abdullah ya dan daga masa kai a hankali.
Dr sagir ya fice saboda shi Sam baya son ma kallon yanayin da Abdullah ke ciki gashi Kuma abinda damuwar wai mami ce da alhakin haka .

Ko minti goma Dr sagir bai yi da fita ba.
daya daga cikin wayar sa ta fara kuka ta danyi kmr sau biyar sannan yakai hannu ya dauka dayake kusa dashi Dr sagir ya zube su.
yana dubawa bakuwar number ya Gani ya kara a kunnesa Amman sai murya dady Abdullah yaji zuciyarsa ta sake tsinkewa tamkar ya fara mishi kuka,
dady yace Abdullah where ar you gobe nake shirin yin abinda ya kai ne Denmark, Amman duk na nemi wayoyinka ba same ka ba ,
Da duk wanda yakamata na nema na nema Amman ance ba'aganka ba meke faruwa da kai ne ?.

Muryasa ta sake rauni sosai yace dady ina gida a daki ,da sauri dady ya Kuma tambaya meyasa Meka kai ne ko Aisha ba lfy .

Shr yayi dan wani abu dayaji a daidai makogaronsa yana shirin tokare mishi numfashi .
sai da dady ya sake magana sannan yace dady Aisha bata gidana mami ta tilasani sai na rabu da ita,
shiyasa nasaketa kuma da gaske mun rabu yau kwana biyar da rabuwarmu .
da sauri dady ya katse shi yace Abdullah be a man ka nutsu sosai zan bugo byn minti goma.
sai ka maida hankali kamin bayani yadda zan fahimta dady ya katse wayar .

Yana nan zaune har minti goma suka cika dady yasake kira dady yace yanzu kana ina kana gidanku ko side dinka yace ina part dina yace mhn ina jinka .

Ahankali Abdullah yawa dady bayanin komai tun daga ranar ya tafi har zuwa yanzu da yake zaune .
dady ya numfasa yace to Abdullah shine kake neman ka susuta kanka saboda macce ? maganar ta dan shigi Abdullah har ya kara tada hankalinsa .
dady yace yes macce gishiri ce ta rayuwa ,.kuma dukan wani jin dadi na rayuwar duniya ya kan haduwa da macce ,Amman macce wani fanni takan zama hadari ga rayuwar wasu.

har yakansa wasu su gwammace yin rayuwarsu su kadai batare da macce ba . Abdullah Allah yabaka maccen da kake so. kuma ka aura to idan ya karbi abunsa fa .
sai kace dan me ,.
ma'ana idan Allah ne ya karbi ran AISHA shi kennan baza ka sake amfanuwa ba kennan.

Abdullah yayi shr dady ya sake maimaita tambayar Amman still Abdullah bai ce komai ba dady yace ka auna da kanka ka Gani zan sake bugowa byn awa daya .


Ahankali ya sauke wayar a sanyaye ya dan kalli agogo dake gefen gadon sannan ya mai da kasa ya zubawa Tay's din dakin ido yayi shr yana tunanin maganar dady.
shine kake neman susuta kanka akan macce ,barin da ya tuna ma yadda Aisha bata wani son sa.
kawai mikewa yayi ya shige bathroom ya kunna fonfo dake manne cikin sink sai daya cika sannan gabadaya ya tura kansa ciki yayi dan Jim sannan ya dago yana maida numfashi ahankali ya kurawa kansa ido ta cikin mirrow din gashin kansa daya jike duk ya kwanto goshinsa ruwa na dinga .
idan Allah yakarbi ran Aisha shikenan baza ka sake amfanuwa ba kennan maganar data sake zuwa masa kennan.
ya runtse idanunshi sosai yana sakin numfashi ahankali ya furta alhamdulilllahi tunda Allah yasa Aisha ba mutuwa tayi ba .
ya sakarwa kansa shawa yayi wanka Amman har alokaci yana jin kadaicinta ajikinsa , ya fito yana goge jikinsa ya ya koma yayi rigingine da jikin gado ya zubawa celling dakin Ido ,duk son da yake mata idan wanda ya hallice tane ya dauketa bai isa yace komai ba,.
ya rufe idanunshi gam ahaka har wayar dady ta sake shigowa ya Mike zaune yana amsa wayar dady yace ina sauraronka .
Ahankali Abdullah yace kayi hakuri.
dady yace kai za'a bawa hakuri dan kai aka batawa.
Abdullah yayi shr dady ya sausauta murya ya kirawo sunansa yace Abdullah ba tun yau ba nake nuna maka mahimmanci idan wani damuwa ya sameka ka daina sa shi a ranka .
ka dinga barwa Allah komai inda ba haka ba zaka sa kanka a wani hali.

Abdullah tabbas nasan an bata maka tunda aka saka rabu da matarka an katse maka wani farinciki na rayuwa duniya.
ni nasan da haka to Amman karike aranka bbu wani dadi dayake samuwa batare da an Sha wuya ba.
kuma muddin kasan zaka samu wata rana dole zaka rasa .
Zuciyata ta amince maka da yarinyar nan Aisha.
dari bisa dari Kuma na amince ka zauna daita ko byn Raina , kuma ko ba komai wannan yarinyar diyata ce halak malak bazan so wani mugun abu yasame ku kai daita ba.
domin kuwa nasan adaidai wannan yanayin maimuna na can cikin bakin ciki da tashin hankali fiyye da wanda ka tsinci kanka ciki ..
dan haka Abdullah ina son ka daurewa zuciyarka na rashin matarka a kusa ka ajiye komai har sai na dawo.

ko inda take kada ka dosa hakan zai iya sa zuciyarka sake karyewa ko wani ban yarda ka tura ba.
har sai na dawo da kaina zan same iyayenta dan yanzu duk wanda za'a tura zasu ga an dauki auren wasan yara .

Amman bbu komai nasan maminka ni tabatawa bakai ba .
Saboda haka ka sawa ranka hakuri matukar Aisha rabonka ce.
gaba zaku sake zama ,ka maida hankali kan abinda nabarka dashi a game da ma'aikatan Abdullah idan ba'ayi da gaske ba company yana iya durkushewa a dalilin wannan satar.
Abdullah mutane nan so suke suga karshenmu Abdullah gashi bananan nasan zaka mayye gurbina har yafi idan ina nan.
dan haka Abdullah idan baka ajiye al'amarin Aisha a gefe zuwa wani lokacin ba zamu kwana aciki fa.
Abdullah ya jinjina kai ahankali yace inshallahu zan ajiye komai zai daidaita.
dady yace Mashaallah zan sake nemanka .
Ita kanta mami taga canji a ranar hatta kannensa yau sun dan sake dashi salis kuwa tamkar sallah haka yaji jin Abdullah yace zasu fita .

Amman daddare sai da Aisha tazo, ta hanashi bacci da tunanin halin da take ciki bbu yadda zaiyi da kaunarta ta zama naman jikinsa .

Wani tashin hankali da yazo masa nan da nan jikinsa ya dau rawa karfe biyu da mintina na dare ya lalubi wayarsa yasoma neman dady yaji duka wayoyin dady a kulle .
tunanin da fadomasa arai akalla dady zai yi wurin wata uku zuwa hudu kafin ya dawo , Kuma sai ya dawo zai je masa Biko AISHA .
to idan kafin lokacin suka aurar daita fa ?dan a wancan karon ma mlm abu cewa yayi zai aurar daita ga duk wanda yagadama.
Allah ya kiyaye to har dare ranar haka ya kwana yana surutai ba wanda yaisa ya aurar masa mata.
tashi ce shi kadai .

Da safe wayar dady nashigowa korafin daya farayi masa kennan dady ya danyi shr yana jinjina al'amarin Abdullah game da yarinyar .
sannan yayi dan murmushin yace to Abdullah a ganina duk maccen da,aka aura aka saka sai tayi idda kafin ta sake yin wani auren.
ma'ana sai tayi jini uku kennan kaga a kalla zai dauketa wata uku zuwa hudu ina ganin itama Aisha ai haka ne malam Abdullah dole sai tayi idda kafin suyi mata aure dan haka a tunani sai tayi idda itama ko ba haka ba ne .
Abdullah yadan sotsa keya kmr dady tamkar dady yana kallonsa yace haka ne .
dady ya sake yin murmushi to kaga kuwa har na dawo ..
Abdullah yadan janye wayar yayi .
yana murmushi dan gabadaya yagama rudewa gashi har yasa dady ya fahimceshi ya fada aransa .
Shima bangaren dady dariya yayitawa Abdullah .


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 51-52


Aunty Maryam na can bangaren aikinta ,inna ke sanarwa zance ciki da abinda ya kawo ciwon yayi tsanani , ta bar abunda take ta zubawa inna ido sosai , ahankali cikin mamaki tace innarmu cikin me Kuma har gabanta yana faduwa .
Inna bata bi takan

Please Login or Register in order to submit comment