Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwance kusan 30 minti sannan yamike zubur kmr an tsikare sa ya bar falon mami na kallon kmr zatayi kuka addu'a kawai takeyi azuciyarta Allah yasa Abdullah ba gun yarinyar nan zashi ba ... ....


hankalinshi a tashe yake shi kadai yasan me yake ji a zuciyarsa yau dai komai za'ayi sai yaje yaga Aisha muddin bai je yaganta ba zuciyarsa na gaf da bugawa " ko wanka bai tsaya yi ba" har yace salis ya jirashi ya fito suwuce ,Amman suna fitowa ya sallami salis shi kadai yake tuki ,cikin kamarar benz baka yayi Parking agefen titi , ya fito ya kulle motar sannan yakarasa cikin lungun su Aisha goma batayi lokacin dan haka mlm abu yana nan a waje da kwarin gwiwa Abdullah yakarasa tare da sallama sannan har kasa ya risina yana gaishe da mlm abu...

Mlm abu yakashe radiyonsa dayake ji ,cikin natsuwar yake kallon Abdullah din byn ya amsa gaisuwar sa ko kadan bbu damuwa ko bacin rai atare da yaron hakan ya kara sa mlm abu cikin wasi wasi yasoma tunanin anya yasan halin da ake ciki a game shi kuwa ?a fili mlm abu yayi gyara murya ya dubi Abdullah har yau yana da wata kima da daraja a idanunsa ,yace Abdullah ko? ALHAMDULILLAH daman kai muke Jira koda bakazo mu akwai bukatar muje ga mahaifinka "mudan jinkirta wa zuwanka ne domin ta inda aka hau tanan za'a sauka ya dan tsagaita sannan yace Abdullah mahaifiyarka tazo .....a frigice Abdullah ya dago ya kalli baban Jin sa ya tsaya dip ... yadaina ji komai nawani lokacin kmr an dura masa ruwa a kunne haka yake ji sannan ya girgiza kansa yana mai sauraron mlm abu.....hakan ya nuna wa mlm abu cewar bai san da zuwan nata ba mlm yacigaba sun zo ranar lahadi ,kuma a yadda ta nuna bada saniyyyarta akazo nema maka aure ba ...Abdullah alahakikanin gaskiya anci zarafinmu sosai dan bamu da komai wanda har hakan yasa na kudirce araina nima duk ranar da ka sake zuwa kofar gidana da niyyar neman diyata hukumace zata raba mu" Amman daga baya nayi tunanin kafin ayi haka afarayin hannun riga daga baya in yaso idan wani abu ya faru ko ma menene sai ayi ....

Mlm abu ya numfasa yayin da kirjin Abdullah yacigaba da bugawa kmr ana buga masa guduma "kamar yadda akace tsiya ce tasa muke haukan son hada ka da banzar diyarmu to a haka nakewa Allah godiya har nan ka Tako bazan manta ba kozo neman ta.. dan haka duk haukan tsiyarmu da mukeyi sai da kazo sannan muka fara , saboda haka ni mlm abu nace kaje can ka nemi diyar masu arziki ka aura Amman ba dai diyata Aisha ba...... ZUCIYAR Abdullah CE ta tsaya cak tadaina aiki na wani lokaci sannan dagabaya tacigaba da bugawa da sauri da sauri sakamakon Jin maganar da mlm abu yace , duk wani kuzari da karfin jiki bbu shi atattare dashi hankali atashe yake bin mlm abu da kallo kawai yake Yi " mlm abu ya jijiga masa kai alamar haka zance sa yake .... Sai yanzu Abdullah yasamu yayi magana cikin sarkewar murya tare da dunkule hannuwanshi duka waje daya yace dan grman Allah baba kar kamin haka idan akai haka wlh komai zai iya faruwa dani ...

Mlm abu yayi murmushin takaici yace sai dai kayi hakuri , saboda mahaifiyarka ta Raina yadda Allah ya ajiye mu cewa tayi zata bamu million goma domin in raba diyata da kai ...dan haka ko kai kadai karage mata a duniya gara ta zauna jiran wani da na baka ita" saboda haka duk wani cin zarafi da cin mutunci da aka zo akayi mana har gida wannan munbarshi akan haihuwace ta tajawo mana haka .Amman halaka ta aure tsakanimu bbu shi har abada. in Allah yaso ni da kaina zan zaba mata miji da yayi min kuma daidai da ita ...

Abdullah ya zubawa mlm abu idanunshi jikinsa har karkarwa yake tsabar tashin hankali dayake ciki musamman da ya karanci hakikanin gaskiyar mlm abu yake fada masa ,yace to.....sai kuma yayi shiru yana juya kansa cikin sanyi jiki yace baba bari na koma gida gurin mami wallahi zata yarda idan naje zata amince in ....aure .. Aisha dan Allah kar kabawa kowa ita ni kadai ne mijinta ...

Mlm abu ya kalli Abdullah ya gane duk a rude yake da maganar.. ya dada fuskantar yadda yaron yake son Aisha Amman hakan da yayi shine kada zai sa su tsira da mutuncin su , yace Abdullah idan kaje ka samu mahaifiyarka da zamce ai asirin da ake fada munyi maka za'a sake kallo da har yanzu yana cinka , dan ma banda mahaifiyarka ce Amman yadda aka zo har gida aka keta mana haddi muka dauki hakuri,kaima hakan ya kamata dole kayi hakuri da Aisha....

Abdullah ya hadeye wani dunkulalle abu dayake Jin sa a makogaronsa yana kallon mlm abu daya fara nade tabarma dayake kanta ,tare da daukar radiyonsa ,idonsa suka yi jazir ya zube gwiwarsa a kasa yace na gode baba Amman dan ka taimake ni naga Aisha koda ganina da ita na karshe kennan ...

Mlm abu ya masa duban tsab kmr wanda yake son ya karya masa maganarsa banda ma darajar sa data mahaifinsa ai da yanzuya kore shi daga kofar gidansa ".yace wannan kana maganar wani al'amari ne da ya shude ya zama tarihi a game da fitowar diyata wajenka ina fatan idan ka koma zaka sanar da mahaifiyarka in Allah yaso gobe suzo su karfi komai na aurenka in kuma basu zo ba yana kan hanya , sannan mlm abu ya juya zai shiga gida.

Allah sarki Abdullah bawan Allah rasa yadda zaiyi yayi ya Mike a hankali tamkar ma baya cikin hankalin sa kmr ya manta dawa yake magana yace to baba idan kashiga kacewa Aisha ta taba cewa zatamin addu'a kuma nasan tayimin to yanzu ma dan Allah tayi min addu'a akan dukkan abinda zai faru a kaina a dalilin ta...sai da mlm abu yagama ji hakan sannan ya shige gida maganar Abdullah ta tsaya masa arai , musamman yanayin sautin daya fadi hakan dashi .....

Abdullah ya zubawa kofar gidan ido mami ke kallon yafi karfin Aisha Amman shi tun daura idanunshi akanta da yanayinta yake ganin kmr zatafi karfinsa ,a duk zuwan da yake gurinta a hakan yake kallonta har gashi a yanzu yake tsaye a kofar gidan su ya dada gane da gaske Aisha tafi karfinsa ...

Ya jima yana kallon kofar gidan jitake kmr ya shiga har inda take ya daukota ya gudu da ita, kowacce kasa a daura musu aure in yaso idan ta tasamu ciki ko ta haihu sai ya dawo da ita su bawa iyayensu hakuri" a sannan bbu mai raba su , hannushi duka biyu ya soke cikin aljihun wandonsa ya zubawa kasa Ido tare da tura lip's dinshi na kasa a baki ya dago Ido yana sake kallon kofar gidan idanunshi sun jazir dasu sannan ahankali ya juya ya soma tafiya cikin sanyi jiki shi kansa bai san a wani irin yanayi yake ciki ba ...

Tun tara da yan mintina ranar da mai gadi ya sanarwa alhj ishaq rashin ganin dawowar dan nasa gida hankalinsa yake a tashe har yanzu da gari yawaye ya sanar da police haka nan securities dinsa sun bazu koina ,ko mami basu sanarwa ba sai byn sallar asuba domin yasan ita bata wani hakuri akan ya'yanta don haka ya kyaleta ,sai da rana yadda mami ta dinga Yi kamar Abdullah kadai ne danta .....

inda mami sukayi magana da alhj ishaq akan aure ,daman abunda dady ya guda kennan ,to har zuwa karfe uku na safiyar ranar bbu wani bayani akan Abdullah Allah sarki dady har kasa zama yayi sai karfi goma da mintina sannan ya amsa wayar police da daya daga cikin wayoyin Abdullah, cewa yazo teaching hospital sir yahaya da gaggawa an tsinci Abdullah cikin wata benz baka mai dauke da number I. M sidi magaji yayi hatsari.. sai da dady yayi da gaske sannan mami ta hakura da binsu dan kusan tafi dady gigicewa ..........


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 16


Alhj ishaq ya isa asibitin tare da securities dinsa yayin da police suke tare dashi har cikin dakin da aka kwantar da Abdullah yakarasa kan gadon " Abdullah dinsa ne kwance bbu inda ke motse ajikinsa da oxygen a hancinsa sai bandejin dake daure a tsakanin kafadarsa da hannunsa sai kansa daure shima da bandage har yanzu jinin dake zuba a wajen kansa bai dai na zuba ba... ,...

Dady ya runtse ido sannan ya sake budewa tabbas Abdullah din nasa ya sake gani acikin wannan halin" kwance rai hannun Allah ya juyo yana tambayar doctor daya karbe shi
Likita ya soma masa bayani yadda abun yake Abdullah ya bugu sosai ga kariyya a kafadarsa sakamakon kokarin fitowa daga motar bayan ya bude kofar lokacin da abin ya faru sai raunikan dake kansa da kafadarsa sai buguwa da kirjinsa yayi har ya janyo masa matsalar fitar numfashinsa ,.. dady ya sake zubewa a gefen Abdullah har yanzu baisan ida kan sa yake ba "dady yace Abdullah dina ne da duk wayan rauninkan ya runtse idanunshi yana karanto duk wata addu'ar samun natsuwa ,ya Mike ya fito police suka biyo shi abaya suna sake mishi bayanin yadda al'amarin ya faru...

A ranar dady yasa aka masu visa zasu fita Germany dashi domin can ne kadai dady yake ganin zasufi duba masa Abdullah dinsa da karayar daaka ce yayi ,,, har daren ranar yana tare da Abdullah Amman bai farfado ba Mami ma takasa hakuri sai da taganta asibiti su duka ,sanin idan suka wuce da Abdullah damuwa zatasa mami ita ma kamuwa da wata cutar yasa dady ya shirya visa har da ita washegari ranar da safe suka bar Nigeria yayin da akabar su teema a gida .....



Koda mlm yashigo Aisha na tare da inna ta Mike shi kuma mlm abu ya zauna yana wa innarsu bayanin zuwan Abdullah da maganar da suka tsayar kan gobe za'a mai da musu da komai nasu na aure inna tayi shiru tayi tagumi da hannuta daya yayin idanunta ke kan mlm abu tashiga matukar tashin hankali wai Abdullah dan dan uwanta kennan danta ne halak malak ita ko yaushe zata bari a ayi auren nan gara dai ayi hakuri da abun kawai "wata zuciyar tace to in kuma wani abu yasame shi tasadin haka tasan dole zai shafe dan uwanta ita kuma batasan ganin tashin hankalinsa,alahakikanin gaskiya ita me son yanuwa ce balle shi kadai gareta duk da bai damu da ita ba tasake Jin sukar wani wasu hawayen da duka fi na dazu ciwo"" Amman takan mai uziri saboda rashin bai dace da macen kwarai ba, mlm abu ya jijjiga kai yace narasa gane kan ki tun zuwan iyayen Abdullah gidan nan ,kinki sanar dani damuwarki. munsaba raba farincikinmu tare haka ma akasin haka to meyasa zaki boye ?"duk da cikin duhu ne hakan bai hanasa ganin hawayen dake bin fuskarta ba, sannan cikin yin kasa da murya dan batason Aisha tajo mai zata ce dan tasan idanunta ta biyu " nan dai inna tayiwa mlm bayanin komai tun daga zuwan ta gidan alhj ishaq din bayan wani zuwa da sukayi ka'oje , mlm abu shima yashiga rudani matukar maganar ta jijjiga sa kwarai kasa cewa komai yayi sai ma shigewa daki da yayi yana mamaki da alajabi wannan hadin sai yanzu ya iya cewa ikon Allah kennan ....

Tun bayan shigowar mlm abu da kmr awa daya har yanzu idanunta biyu hakan nan duk da tana kwance bata da wani cikakken kuzari ajikinta tun byn faruwar abun har zuwa yanzu takasa raba kanta da dogon tunani ,komai akan idonta da kunneta aka fara aka gama dan haka duk wani tashin hankali da iyayenta suka shiga sai dai ta bawa wani labari "abin yaki wuce mata arai ko dai dai da second daya zubar hawayen inna a dalilin aurenta ,wanda tun randa tazo duniya bata taba ganin ba ,ta yarda idan tashin hankali yayi yawa hawaye ma basa zuwa dan haka ta gwammace da ma kukan tai tayi da abunda ke damunta a zuciya,ita daman tun zuwan Abdullah gurinta ta gane wani karan tsaye ne a rayuwarta duk wannan maseefar da yawan tunane tunanen da take Yi bai hana bacci lallaba idonta ba ya fige ta na mintina uku ....wata mumunar faduwar gaba ce ta farkar da ita ta Mike zaune ta dafe kirjinta hade da mai da numfashi sama sama gabadaya jikinta rawa yake Amman duk da haka gabanta bai dai na harbawa ba "a hankali ta dinga karonto innalillahi wainna ilaihi rajiun...ta jima tana maimaita wa sannan ta dan samu sauki da natsuwar zuciya. iya tunaninta batasan me yasa gabanta yayi irin wannan faduwar ba , haka nan jikinta baya bata wani abu na shirin faruwa da ita tunda bbu wanda tayiwa laifi sai dai ko daga Allah ne tashi tayi ta fito a hankali ta dau buta tayi alwala taxo ta shimfida pray,mat tafara nafila....

Duk motsinta akan idon innarta ne ,tana Jin tausayinta dan tasa damuwa sosai aranta ,har ramewa tayi inna tasawa ranta hakuri da dangana dan ko ba komai Abdullah bata ba yadda zatayi kallon da inna take wa Aisha yanzu yasake sawa ranta kiyyayar maza fiyye da da dama can tana kukan targade sai ga Karaya....
.

aunty Maryam takan aiko Aisha taje Amman da ta lura idan taje tana yawan mata zance Abdullah sai ta daina zuwa ko ta aiko saboda ita yanzu haka kawai taji ko sunanshi bata kaunar a ambata a gabanta ....

Su mlm abu basu samu damar zuwa gidan alhj ishaq ba a washegari da Abdullah yazo kmr yadda mlm abu ya shedawa Abdullah sai bayan sati daya saboda zuwan da mlm dahiru zai yi daga ka'oje ...

Tun a get din gidan abin yasake kwancewa mlm dahiru kai yayinda mlm abu yake sakawa ransa yanzu duk wannan tambatse tsen gidan na yayar matarsa ne Killa daman can wata manufa da yaudara ce akazo neman diyarsa dashi ....

masu gadi suka tare su ko ciki ba'abarsu sun leka ba bare su hangi cikin gidan byn gaisuwa mlm dahiru yayi bayanin suzo neman mai gidan ne , to Amman tun daga yanayi kallon da masu gadi suka yi musu Jin cewa me gidan gabadaya da kansa suka zo gani suka sha jinin jikinsu bbu wani cikakken bayani da masu gadi suka musu daya daga ciki yace to kujira zaku ganshi sannan yayi shigewarsa ya rufo get dayan ne ma yamusu bayanin yace gaskiya zan sanar daku ba'a zuwa ganin me gida kai tsaye sai tare da wata sheida ,ko da shidar ma sai anyi waya an sanar da mu in yaso idan kunzo sai musanar aciki ,a halin yanzu da ake ciki mai gidan baya ma kasar sabida haka dan Allah kuyi hakuri ku canza wani bangaren ....

Su mlm abu sukayi masa godiya suka wuce kowane zuciyarsa da abin da take sakawa...

Magana dai akan bbu me sake taka gidan ,ko ba dade dai sun zo neman kayan aurensu sai dai idan suka ji shirun yayi yawa ,abida mlm dahiru ya yanke kennan duk da mlm abu bai sanar masa da kowaye mahaifin Abdullah ba yafi son sai komai ya warware tukun ....


To shima dai alhj aminu a dawowar dayayi ya riske yadda al'amarin yakasance mamaki ne yacika shi,shi kam cewa yayi kada abiyewa al'amarin mata kawai ajira daga uban yaro dan ko ba dade zai waiwaye su .........


Manage please may be ku sake jina anjima


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO



Page 17

Likitoci sun rufa akan Abdullah tun saukar su Germany,hankalin dady na matukar tashin idan yakalli Abdullah da halin da yake ciki shi kadai Allah yabashi da namiji Amman ya fanshe masa abinda ya'ya zama goma zasu Yi ,Allah ya albarce shi da tarin dukiyar da shi kansa bai zai iya cewa ga iya kacinta ba, wanda a kalla da yana wasu ya'ya ashirin maza to kowannesu akwai bangaren da zai kama" yana sane da maganganun da mutane ke masa Amman sai yayi kmr bai sani ba "domin dai fuskarsa ce kadai akan abin sai kuma yanzu da Allah ya taso masa da Abdullah ko kadan ba raayinsa bane ya daura mace akan wani part na dukiya ,burinsa kawai ya basu illimi ya aurar dasu ,dan haka ko a daren da akawa Abdullah aiki a kafadarsa,ko kadan alhaji ishaq bai runtsa ba. neman tsarkaken guri yasamu yayi sallah nafila
..sai da aka fara kiraye kirayen sallah asuba sannan dady yatashi ya sak e wata alwala , bai tashi ba har sallah asuba ya dade yana rokon Allah yatada masa dansa ya bashi lfy kamar da ,to daman dai dady ba daga baya ba wurin ibada ....




Kwana da yini sannan Abdullah ya farfado cikin sa'a da nasarar aiki ya dawo hankalisa da natsuwa, daga mami har dady suna tare dashi ,a ranar Abdullah yana kallon suna ta tattalinsa sosai a zuciyarsa yace ni duk bawan tattalin nike so ba ni dai kubani Aisha kawai yana kallon mami abubuwa suna sake masa yawo tamkar mafarki wai bazai auri Aisha ba ......


Cikin kwanaki biyar jikin Abdullah ya fara kyau sosai wanda har dady da kansa ya amincewa hakan saboda haka yayi shirin komawa Nigeria ya bar mami a gurinsa domin ayyuka da dama sun tsaya bbu shi bbu Abdullah ranar da Abdullah yayi sati biyu yabaro Germany bayan ya sakar musu kudi sosai ta koina hatta likitoci sun san da zaman Abdullah a asibitin kwanan dady uku da tafiya su teema suka biyo jirgi dukkansu sukazo ganin Abdullah , Amma kwanan su uku teema ta juya tabar minal ..



Jikin Abdullah yayi kyau sosai illa dai har yanzu baya Jinsa daidai kmr da musamman kirjinsa saboda buguwar da yayi karayar kafadar ita ma ana san ran kwancewa cikin kwanaki kadan masu zuwa

Asibiti shikadai yake cikin daki dan basa son dan jinya dan haka mami da minal da suke tare da shi sai an basu izinin shigarshi sannan suke ganinsa ,dan haka kowane dare Abdullah bai iya runtsawa ta koina ya juya Aisha tana manne da zuciyarsa shi ahankali yake tunano maganar da tayi masa daren da zai tafi ,..nasan zakayi nasara in Allah yaso....
Ya lumshe idanunshi tasan shi fiyye da yadda yasan kansa kennan ,ya tabbatar zata iya kula da wasu al'amuransa idan ya aure ta , Amman duk hakan da ya gano ita mami bata gane ba ,mami bata son Aisha kennan .....yaji
. gabansa ya fara faduwa kmr kullun idan ya tuna hakan yanzu idan mami bata hakura ba shikenan ba zai auri Aisha ba? ya sake tuno kalmarta ta karshe gareshi I will miss you too....to ko daman tasan shikenan su rabu baza suyi aure ba shi yasa ta fadi hakan ,da sauri yayi jifa da magunguna da suke zube a gabansa yasoma juya kansa NO I can believe this i can believe this ....da sauri nurse tashigo tana tambayar sa me ya faru nan da nan ya natsu ya dawo haiyacinsa yasa tafin hannushi duka ya rufe fuskarsa dashi ....yawanci idan ya kwana da tunanin irin haka da safe km lokacin da su mami suka zo yake samun bacci ..

To yau idansa biyu har an samu suna hira da mami minal a gefensa ahankali mami take tambayarsa yadda abun ya faru Abdullah ya dago yana kallon mami ya fahimci shi take sauraro sannan ya sunkuyar da kai yana wasu wuraren na budewa a jikinsa bai tsaya boye mata komai ba tun daga yadda sukayi da mlm abu har zuwa sanda ya shigo mota ya taho gida baya cikin natsuwar hankalinsa saboda tunani har sanda ya lura daf din katako a gabansa tana yimasa hon yayi kokarin dauke kan mota Amman ya makara , mami ta xuba masa Ido har sanda yagama sannan shima ya jefo mata tasa tambayar , cikin tsanyi murya yace mami wai da gaske ba Kya son na auri Aisha ...kince a aurar da ita gawani ?....



Gabadaya ZUCIYAR mami ta gama hautsina a tun labarin sa na farko,tamkar mami ta manta a inda Abdullah yake ta daga masa hannu tana nuna shi da dan yatsanta tace kai Abdullah yanzu dama a dalilin diyar wadannan banzayen mutane kake neman kashe kan ka .....

Gaban Abdullah yayi mummunar faduwa a kunnenshi mami ke zagin mahaifan Aisha,ka tayarwa kowa hankali kasa mutane cikin wani hali , to bari kaji muddin ina raye bazaka auri wannan banzar yarinyar ba lallai na yarda da maganar hafsa da tace sungama da kai.....

Duk wata jijiya ta jikin Abdullah sai da ta sage ya kurawa mami Ido tana magana idanunshi ya fara kadawa a yadda yake Jin tashin hankali yafi karfin ayi masa kuka sai dai jan Ido a hankali ya zamo da kyar daga kan gadon da yake "ya zube a gabanta mami me yuwa so yasa Abdullah ya manta ida yake kuma ya manta gaban wa yake yace komai zakiyi min kiyimin mami Amman dan Allah kiyi hakuri ki tsanya hannu a aura min Aisha karki ce dan Allah mami wallahi mami Aisha bata da wani aibu tun ban kai haka ba nake rokon Allah ya samin son matar da zan aura kadai to tun haduwata da ita nasan itace wacce zanyi rayuwa da ita....mami ta kalleshi shekeke tace idan da gaske kai asirin su yacika mu bai cimu ba idan baka cikin nutsawarka to ni ina cikin tawa kai baka da Ido ne baka lura bakasan abinda yadace da rayuwarka ba ,mami tashiga juya kai tace "Oh"my God wlh Abdullah ka makance kaban mamaki duk wayewarka ka tsaya ajin wannan yarinyar kuma nasake Jin kamin zance banzar yarinyar nan uhmm ta jijjiga ka sannan tayi shr tanajin wani iri a ranta kmr tayi kuka shikenan asiri yayi tasiri akan danta mafi soyuwa acikin yayanta....

Hakan ce yasa Abdullah sake Jin tamkar wata cutar ce ta dada shigarsa ya kara wargajewa nan gaban mami tana lura da shi ranta yasake baci ,tace Abdullah ba cuta ba koma meye sai dai kayi Amman aure tsakaninka da wannan yarinyar kasawa ranka bbu shi har abada ..ya sake motso mami yana girgiza mata kai dan Allah mamina karki min haka ki duba halin da Abdullahnki zai shiga sadin rabasa da ruhinsa ta waro idanu waje tace bari kaji ko zaka sai dai......sai kuma tayi shiru tana jijija kafarta daya basake cewa komai ba ,ya kuma dada tabbatarwa ransa yarasa Aisha kennan tunda yakoma kan gado ya rufe idanunshi bai sake motsawa ba idonsa a rufe bai sake magana ba har sanda mami tagama maganganun ta na bacin rai....har washegari haka yake kwance tamkar mutun mutumi da yayi sallah sai ya koma ya kwanta ya runtse idanunshi ,ran mami yayi matukar baci akan halin da Abdullah yake shirin jefa kansa ,Abdullahnta da baya iya koda musu akan duk wani abu data yanka masa "Amman yau Abdullah ya fara canza mata akan wata yarinyar can yadda yake Yi yanzu ya kara tafasa mata zuciya cikin fushi mami ke cewa zata koma gida tabar shi in dai kan wannan yarinyar ne yake haka sai dai yayi duk

Please Login or Register in order to submit comment