Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abdullah ya mika masa hannu suka tafa yace thank you doctor ...

kamar yadda ya fada washegari karfe hudu da rabi suna Tare daga cikin soron gidansu ,simintin ciki a share yake tas Abdullah na zaune kan kujera har sanda tafito bai ji isowarta ba ,sai da ta taba kujera zata zauna sannan ya dago ya dubeta kallo daya tamasa tagane yau cikin serious dinsa yake sosai duba da yanayin fuskarsa ,byn ta gaisheshi ya zuba mata idanunshi yana kokarin sanya kwayar Idanunshi cikin nata kallo daya tamasa ta dauke kanta ya kira sunanta yace Aisha tun jiya byn rabuwarmu zuwa yau sau nawa kika tuna ni ?taji tambayar wani iri ta juyo ta kalleshi murmushi ya sakar mata yace ko sau daya ko na amsa miki ,ita ma dan murmushi tayi" yayi shiru na wani cikin lokacin tamkar mai nazarin ta inda zai fara yayi dan gyaran murya ya sake Kiran sunanta yace magana nike son muyi please ina son ki bani hadin kai, tai shiru batace komai ba ya zubawa yatsun kafafunta dana hannunta Ido yakanyi mamakin yadda suke kmr nashi yayi jin yana sake nazarinta sannan yace please Aisha ina son ki amince min inzo neman aurenki a gurin baba ina bukatar ki kinzama matata ta aure Kuma uwar ya'yana , maganar tashige ta ta dago Ido tana kallonsa shi dinma ita ya zubawa Ido sun jima a haka yayin da take kallon Abdullah wato yana son yazama wani sirri na rayuwarta kennan ,ita da kanta bata taba zama ta tuna wata rayuwar aure da sirrin dake ciki ta ba,sai ayanzu da Abdullah ya haskota da hakan shiyasa take masa kallon wanda zai iya sanni sirrinta kamar wacce ta farka daga mafarki da sauri ta dauke idanunta daga gareshi ,yayin da shi kuma kallon da ta dinga masa ya sake rudashi yanemi yafi haiyacinsa idanunta tamkar wanda ta fara bacci ta farka take masa kallon tsoro da maganar da yayi mata har sanda ta dauke Ido Amman shi ita yake kallo har yanzu yanajin yadda kaunarta ke sake tsumashi "shr bbu wanda yasake cewa komai ,ya kamo lip's dinshi na saka yana cizawa ahankali ya hade rai gudun Karta kawo masa wasa cikin lamarin ,yace nasan komai yana bukatar nazari ko na barki zuwa gobe sai in dawo naji abinda kika yanke .

kawai taji kalmar gobe ya fitowa daga bakinta yace Eh mana gobe Sunday shine Nike da time sosai da har zan fahimci maganar da zamuyi in ba haka ba sai zuwa rana irin ta yau Amman me kika gani ta sake kallonsa batare da tace komai ba yace banason nayi miki gaggawa idan kince indawo zuwa next week ne sai na bari ,ta daga masa kai cikin sanyi jiki yace to shikenan yana sake karewa mata kallo .

Anyi hakan asabar lahadi litinin aka kai aunty Maryam asibiti tun safe suke can gabanin magrib ta haifi diyarta mace washegarin talata aka sallemesu Inna bata dawo gida ba sai ranar laraba ita Kuma Aisha aranar larabar tashirya kayanta ta tafi gidan da yamma Abdullah yataso aiki tanan gida ya biyo yaga sanyin idanunshi Amman bai sameta ba sai usman ne yayi masa bayanin inda take a ranar duk yadda yaso ganinta hakan bai samu ba dan dama idan yashiga gida mami bata wani amincewa da fitar dare idan dai ba Dr sagir ne yazo suka fita ba,.

Amman washegari da wuri yabar office ya sameta can gidan aunty Maryam yadda Abdullah keji tamkar ya dauke ya gudu da ita yace Aisha ko nema na ba'ayi Kuma kinsa hanyoyin da zaki bi ki ganni ko kiji murya ta tadan saci kallonsa ta sunkuyar da kai tana tuna ranar da ta dawo daga ka'oje cikin jakarta ta tsinci complement card din shi guda uku aciki , address dinsa numbers dinsa da matsayinsa na aiki a jiki a tsakiyar wani littafinta ta zuba su bata kuma bi takansu ba yayi murmushinsa mai sake fidda tsantsar kyaun da Allah ya masa"meyasa magana take baki wahala ne ,ina aunty Maryam tana ciki baki daukomin bbyn taki nagani ba ta dauka da wasa yake sai da sake tabbatar mata Sannan ta Mike ta shige, zuwa jimawa ta dawo dauke da bby a hannunta ta Mika masa ya karba yana kallonta yace ina son bby mace Aisha tana birgeni da dadin wasa tajima a hannushi daga baya tasoma motse Aisha ta karbeta ta mayar da ita ta dawo da juice da snack da aunty tayi masa tun zuwansa ya zame daga kan kujera yace kai nagode wa aunty kamar tasan inajin yunwa. Aisha tamasa wani irin kallo kmr mai jin tausayisa ,yana kallonta ta sunkuyar da kai ya gane kallon da ta masa kawai yayi murmushin gefen baki anan sukayi sallah magariba har salis yace tama aunty Maryam barka zaizo gobe in Allah yaso ta amsa ta shige yabita da kallo, a kasan ransa ya furta har yanzu bata fara damuwa dani ba .


Washegari bai zo da wuri ba sai gab da magrib bai dade ba yayi niyyar tafiya sai da zata tafi ne yace idan tashiga ta turo a dauki kaya a bawa bby aunty da nata Aisha tasanar da aunty salis ne yatarasu a falo kasancewa falon baban saifu ya bulla waje saboda baki .
Kayan sun kusan tsoro ta aunty domin dai duk wadatar Abdullah akace an Yi masa haihuwa a gidansa idan yayi wannan sayayyar sai anjin jina masa balle ita daya kawowa Aisha bata bi takan kayan ba tayi alwala ta shigewarta daki ,ba bby ba hatta mai jego tasamu rabonta a ciki jakar kayan Aisha kuwa tana fara dubawa ta rufe tana kwalla mata kira tace wannan yarinyar idan baki auri wannan mutumin ba mun banu sai Allah yakamamu ta fito da wata sarka Aisha ta gane ta cikin kayan da Abdullah yataba kawo mata ne wanda ta watsa masa aunty Maryam na kallon sarkar tasan mahimmanci ta farin gold ne inna ma bazatasan matsayinta ba shine ita ta dauka ta ajiye agunta dan akalla zata kai haif million a wannan lokacin da suke ciki sarkar guda biyu ce sai zobe da dan kunne duka acikin gidansu. bakaramin kaya ya hado mata ba Kannan kaya mayuka bra da takalma tamkar mai shirin hada lefe kowa yaga kayan bby Aisha akema godiya ita ko Aisha har da kuka dan tun jiya aunty Maryam ta hanata sakat da maganar sa har yau da aka dase taruwa a gidan aunty ,tun aunty na nasiha har ta koma rarrashinta tana idar da sallah la'asar ta shirya zata gidansu sakina akace mata ga Abdullah yana jiranta a waje .jitayi kmr tayi tsunsuwa ta fice batare daya ganta ba ,in yaso ace batan don taso kwarai taje taga sister dinta ta riga ta shirya kawai ta fito gurinsa sanda ta sameshi a falon baki yana tsaye daidai kofar data bulla waje da waya a hannushi yana yi ta nemi kujera ta zauna tana dan kallonsa a kaikaice wai don Allah me wanna halitta shine ke bata lokacin sa akaina kalli yadda yake turancinsa a waya baza ka taba cewa yana jin hausa ba yana lura da ita da kallon datake masa Amman yayi kmr bai ganta ba yacigaba da wayarsa ya leka yayiwa salis magana sannan ya juyo kanta tayi masa kyau Sosai kwalliyar ta koda yaushe a saukake bakin less mai rawa har manne mata yake ajiki. iya tunanin sa shi tayiwa kwalliyar dan haka daf da ita ya zauna yana mata murmushin yana cizan lip's dinshi yace kinyi kyau Aisha like a bride batace komai ba ta sake hade jikinta ganin datayi ya zauna kusa da ita sosai a hankali ta gaisheshi yana jin dadin, hakan yana nuni ita din mai tarbiyyace sun jima a haka yace Aisha today is Saturday what about our discussion ta dago dara daran idanunta ta zuba masa ya amsa mata da idanunshi da suka gama rikecewa ita sam tun ranar inda suka gama maganar anan tabarta yace please Aisha sanar dani me ZUCIYAR ta yanke a kaina?to Abdullah dai yagama daureta ta koina bata da hujjar ce masa ta manta da maganar da sukayi kuma ko ba haka ba ita yanzu idan tace bata son sa tasan baki ma kawai ya isheta ta dago suka hada Ido kwarjinsa duk yacika gurin, ita kawai yake sauraro ta sunkuyar da kai ya kuma cewa please tell me Aisha ta dan ja numfashi ahankali har ta rufe idanunta tace shikenan idan Allah yayi sai ayi" ya karkata kansa kasa ya jefa idanunshi cikin nata suna kallon juna yace you mean inje in neme auraki in Allah yaso sai ayi ta daga masa kai, kawai bai San sanda murmushin ya subuce masa ba , komai nata sai taja masa aji yace thank you my Aisha Allah ma zaiyi da ikon sa jikina yana bani ke din rabona ce ,duk kuma sai taji ta takura awajen ta dan kalleshi murnar datagani a fuskarsa ko ranar daurin aure ce sai haka ya sake cewa na gode Aisha kennan kin amince kina sona zaki aure ni a hankali yake maganar don yadda yake maganar kasa kasa kmr maiyin rada har yasa Tarinka jin wani iri abu ajikinta ya kuma cewa kin amince nazama abokin rayuwar ki tana jin hucin maganar sa a saman wuyanta gabadaya ajikinta yagama mutuwa murus kawai ta tsinci kanta da rufe idanunta duk ya ruda ta da maganganun sa idanunta har sun ciciko Abdullah ya gane yanayin da tashiga sai yayi shiru ya kafe ta da idanunshi yanason tasamu natsuwa shi kam tun ranar da yasoma ganinta ya wuce wannan matakin datashiga, shr yabakunci gurin na wani lokaci duk da haka bbu wanda yayi kokarin cewa komai Abdullah ne yasoma magana sunana Abdullah kmr dai yadda kika sani nine "da" na farko awajen iyayena akwai sister ta me bimi Fatima sai auta amina haifeni a China Amman mahaifinta asalin Yar Egypt ce can nafara karatu daga baya kuma yakasance duk inda muka zauna sai nayi karatu nayi university a jami'ar Oxford ina karantar final art,nayi Nisa afanin saboda wani dalili yasa na canza Carrier na koma karanta business shine dalilin dadewata ina karatu bayan nagama ne yanzu nike aiki a I.M magariyya company a matsayin M D na company yadanyi shr sannan yacigaba teema tana university of aliero yayin da this year amina tagama secondary school tare kuka gama kennan yace bana neman mata Aisha sai dai nata ba shan giya sau daya Amman har yanzu ina yin smoking ina shan sigari sosai musamman idan ina cikin damuwa ko bacin rai kuma har zuwa yanzu dady da mami basu san ina sha ba sai dai su fuskanta domin nakan kiyayye lokacin haduwa ta dasu kafin na sha. sauran bayani Aisha idan muka kasance tare zaki sani.tan dan kalleshi a hankali can cikin ranta kuma tana mamakinsa ya kalleta yace uhmm tambayi abunda baki fahimta ba ta girgiza kai can cikin ranta tana tunanin matsayinsa danata bazai taba zuwa daya ba da Kyar ne yuwar abun da yake so Abdullah balarabe ne kennan ta tambayi kanta ina ita ina shi take ayyanawa sai Kuma taji ya birgeta daya fada mata gaskiyar halanyensa ...

Washegari...




MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Page 11

Washegari ma yazo sai dai bai wani dade ba ya tafi ,byn ya matsa mata akan me take bukata koda tace ba komai ya daure fuska gabadaya sai taga yanayi sa ya canza ,yace dan bata damu da shi bane shi yasa bata son wani abu daga gareshi ,da Kyar ta iya ce masa ko menene sannan ta samu lafiyarsa ya tafi Amman duk da haka bai saki ransa ba, dan shi ji yake tunda ta amincewa aurenshi duk wani nauyi nata yakoma kansa .ranar sunan aunty Maryam bby ta amshi sunan maimuna wato sunan innarsu tun alokacin ake kiranta da khairat .

Tun wajen goma sakina tazo Aisha ko wanka batayi ba saboda bakin da suka agidan bandakin tashiga ta fito da ruwan wanka bayan gida tajata suka zauna akan kujera ta kawo mata dan abinda aka gama cikin jin dadi da murna tace sister Amman sai dare zaki tafi ko ? sakina tace nan da zuwa Shabiyu zan tafi shi yasa nazo da wuri zan raka mama unguwa ne tace kai sister sakina tace Allah kuwa namazo miki da albishir din result ya fito Aisha ta dafe kirjin ta ce dan Allah tace da gaske can kuma jikin Aisha yayi sanyi sakina ta tambayeta yana ga jikinki yayi sanyi" taja tsaki ni wallahi wannan Abdullah din shi zai takurani da Kyar zan Yi ma karatun.sakina ta kalleta kawai tacigaba da wata maganar daban dan batason jin zance Aisha ta lura da yadda Aisha tadan sauya akan Abdullah yanzu ,Amman itama sai tashare tacigaba dayi mata wata hirar sakina ta zuba mata Ido ,wani haka yake da sa'a a rayuwar sa ta tuna jiya gurmin da aka sha agidan su akan ita Aisha a dalilin abbansu ya sanarwa da mama cewa shi Aisha yake so ya hada da yasir ,mama tayi tsalle ta dire tace sai dai byn ranta Amman baza a hada" da" da wannan yarinyar mai kama da karuwai ba ,Abba yaji haushi har yamayar mata ai shiryuwar dan naki shine a hada shi da ita dan bakinsa abinda yake aikata acan ba, ai ko ta hau shi da maseefa yana zagin danta yace inkinga bai aure ba daman can ba matarsa bace aurensu shine kawai zai sa yadawo ya zauna ya daina tara matan banza a can ,ina dawowa zan sami mahaifinta kan maganar Aisha ta bugi cinyar sakina ta ce kai sister ina aka tafi ne tunanin kuma fa suka dariya ?
Ta kalli Aisha ko wanka batayi ba Amma tamkar wanda ta tsala kwalliya kullun kmr sake kara mata kyau akeyi ,jiya da yamma sunka je salon ita da aunty Maryam itama an gyara mata gashinta sosai kanta bbu dankwali ta rataya dan guntun towel a wuyanta sakina tace dan Allah sister ki tsaya ahaka ta fito da Yar karamar camera tace zakiyi wallahi sai kin tsaya na miki hoto Aisha dan bata fuska tayi kai sister a haka zaki wan.... bata gama magana ba har ta dauka da yamma tashiga dakin Aunty dake cike da kawayenta yawanci duk Yan wajen aikin sune ta gaishesu,aunty tace ga sako nan Abdullah ya aiko miki zata dauko mata tace barshi kawai aunty sai zuwa anjima ,ta fita wata daga cikin kawayen aunty tace kai wannan kanwar taki zaayi yanga Maryam kinga da Kyar take magana tayi dariya tace wallahi ba yanga bane nature dinta ne kawai haka wata tace ai idan ma tayi yangarma zata ci riba tunda tana da kyau da abubuwan yin yangar.


Alhj ishaq ya kalli dan nashi ya kira sunansa cikin sanyi yace Abdullah daman abinda ake so hali na gari ga kowane dan Adam to ALHAMDULILLAH anyi shedar yarinyar da iyayenta tun daga kan makwaftansu har zuwa can ka'oje inda aka haifin mahaifiyarta , mahaifiyarta itace kawai Diya sai dan uwanta wanda daba'asan inda yake ba wasu Fulani rigar dake can "sidi magaji )ne Amman duk da kakaninta na wajen uba ba'anan suke a ka'oje ba Killa ma da iyaye da kakanni suna nan raye da zasu San juna dan nima da kaganni asalin tushena kennan ka'oje cikin kauyen (sidi magaji) kmr dai yadda kasani sana'ace takawo mahaifinta nan mlm abu
Shedarsa itace talaka ne mai godiyar Allah suna zaune da matarsa uwar yayansa itama kuma Anyaba mata sai yarinyar data Kare karatu a makarantar yan'mata dake federal gwandu abin farinciki ,nagarta kamun kai da kokarin yarinyar yasa har tayi suna da aka santa a makarantar sosai ita ta rike shugaban dalibai dady ya dan tsagaita to daman wannan ake so a duk wani iri da'ake nema .

Dady ya janyo wasu hotuna guda biyu ya zuba masa a gabansa to Abdullah dai wani iri yake ji ajikinsa cikin sanyi jiki ya dauki hotunan yana dubawa hotunan Aisha ne sanye da uniform tare da yan'uwanta dalibai sai teacher dinsu sai Kuma dayan gurin wani daurin aure ne yagano mlm abu zaune a gefe shi da wani Abdullah dai yakasa magana dady yacigaba abinda na nunawa mamin ka kennan tun dazu ,nagarta yarinyar ta fito kuma shi zaisa a yada zuria ta gari dan haka tunda an samu wannan sai ature duk wani rashi tunda bashi ake bukata aure ba, ahankali yake kallon dady tamkar yasaka masa kuka farinciki haka yakeji ,dady na sonsa dan yadamu da damuwarsa alhaji ishaq yagama karanto hakan a fuskar Abdullah ya girgiza kai kasanar da iyayenta zanzo da kaina in ne ma maka aurenta murmushin Abdullah yayi dan tsabar farinciki, yana fadada murnarsa a fili yace thank you dady
Yace bbu komai tashi kaje ya fita yana rayawa aransa dadynsa ya dauki Aisha'rsa da mahimmanci da kansa zaije ya nema masa aureta sabanin yawancin abubuwa sai dai ya wakilta aje .

Tsantsar mamaki ne ya rufe mami to ita har yaushe Abdullah ya samu yarinyar dayake so batare da ita din tasani ba har zuwa yanzu dayake gabanta kallon mamaki take masa tace Abdullah tsawon wani lokacin kuke tare da yarinyar a garin nan batare da na sani ba Abdullah yayi shr ya fuskanci yadda mami ta dauki zafi akan maganar tace bazai yuwu ba dadynka yayi bincike akan yarinyar dole nima zanyi nawa bincike daban ,tashi kaje zan nemeka Abdullah yayi shiru kwance yake kan doguwar kujera a falonsa ya harde hannuwanshi a kirjinsa yana tuna maganganun mami ko me mami zatayi shi dai ta ceceshi ta amince ya auri Aisha shine kadai kwanciyar hankalinsa da samun lafiyar a rayuwar sa .to har yau dayadawo daga aiki yaje gurinta abubuwa biyu sun cushe masa farinciki da damuwa dady da mami ,yana matukar tsoron mami yadda tanuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna......


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Page 12


Yana matukar tsoron mami yadda ta nuna rashin son ta akan Aisha yasan mami sosai idan ta nuna kin mutun a fili bbu wanda ya isa yasata dole ,ya kalleta idanunshi suka Yi ja yace Aisha idan aka ce za'a daura mana auren cikin satin nan zaki amince ? A frigice take kallonsa tana girgiza kai gabadaya tagama rikecewa tace nidai kayi hakuri ba dai yanzu ba ,ta zuba masa idanunta shima ita yake kallo yace yes na matsu A ce kinzama matata " tace nidai kayi hakuri idan Kuma ka damu sai yanzu to kana iya samun wata ni sai zuwa wani lokacin "yaji haushi maganarta Amman yadda tayi maganar yagane yarinyarta ta a fili ya zabga mata harara yana mai jan tsaki yace ai ba sai kin gayamin ni kadai nike haukana akanki ba nasan bakya sona , takalleshi kamar zatayi kuka kayi hakuri dan Allah ba haka nike nufi ba" bai sake ce mata komai ba ya juya ya barta anan . Sai taji ba dadi aranta daman Kuma ta lura tun zuwansa ta fuskanci kmr yana tare da damuwa .

To har zuwa kwana biyu da maganar su da mami bata sake tada zance ba a iya nasa tunanin ko mami ta hakura ne" wani satin mami take sa ran tafiyar ta zuwa Egypt dubo mahaifinta dake kwance ba lafiya shine dalilin dayasa ta ajiye komai tabari sai ta dawo Amman a wayewar garin jumma'a labarin rasuwarsa ta same su dan haka cikin rashin shiri tayi tafiyar ita da su teema yayin da dady da Abdullah sai rana Saturday suka bi jirgin yamma suka isa, washegari uku dady yadawo Abdullah kuwa kwanansa goma suka juyo tare da su teema da minal saboda makaranta mami ta zauna saboda tafiyar bata kusa bace dole ta zauna har ayi arbain .

Ko sanda ya dawo da washegari sai da yaje yaga Aisha ya rinka nuna mata yadda yayi missing dinta na kwana biyu da bai banga ta ba Aisha taringa kallonsa yanabata mamaki ko kadan baya da riko iya tunanin ta fushi da yayi ranar da yayi zuwan sa na karshe shi ya hanashi dawowa ,sai da yasanar mata da rasuwar da akayi musu. Tayi masa gaisuwa yace idan mami tadawo zaizo ya dauketa ya kaita tayi mata gaisuwa ta amsa da to "Amman ita kam sai ta tsinci kanta tana mai tsoron shiga cikin family dinsu,

Sun sake zama na musamman da dady akan maganar sa da Aisha ya shidawa dady ya sanar da iyayenta cikin satin nan zaizo bai dai samu mlm abu a gida ba Amman yagaya mata ta sanar da inna, ko gwaggo Laure da tazo haka tasa Aisha gaba da zance Abdullah shiyasa har daren ranar da dady zaizo din da Abdullah yazo sai da yasake tuna mata akan tasanar saboda yasan halin kayansa, sai a wayewar garin ranar lahadi mlm abu yafito zai fita suna sallama da gwaggo laure domin itama a ranar zata wuce sannan tashiga rumfar inna da Kyar take gaya mata inna ta hau salati ta fito tana sanar da mlm abu yakira Aisha yana Kuma tambayarta ta amsa da yau da yamma karfe hudu .
Gwaggo laure tace ma'aiki anmabi Muhammad ke yanzu dan iskanci gidan sirikan naki zasu zo shine kika kiyin magana ?
Inna zata kuma yin magana usman dakatar da inna yace ai mun godewa Allah ma da aka samu Allah ya matsi bakinta ta fada ,ai da sai dai anjima kawai Kuga baki, inna tace zata aika ai wannan yarinyar bansa halinwa ta dauko ba gwaggo laure ta rike baki tace miskili kafi mahaukaci ban haushi yarinyar kin zama sai kace harsashi acikin gida Aisha ta hade rai hade shigewa daki mlm abu yace aiko bai ga tafi ba nan da nan akashiga gyara gida ,dakinsu yaya yusif dake soro aka bude aka gyara da yake daya kofar ta fita waje gwaggo laure ma fasa tafiyar tayi yayin da inna tabawa usman kudin machine yaje yagayowa aunty Maryam ,tayi musu dan abun da zata tare su dashi mlm abu da kansa yabar komai ya tafi yagayawa alhj aminu domin a ranar zai Yi tafiya to haka nan alhj aminu yaji maganar daga sama dole dashi za'a karbi baki to shima din sai barin tafiyar yayi yana jinjina al'amarin Allah yadda ya kwallafa ransa akan yahada jininsa da yarinyar Allah bai nufa ba har sapani sukai ta samu da maidakinsa .

Karfe uku aunty Maryam ta iso da kulolin snacks iri iri da juice dakinsu yaya yusif yasha gyara aka shimfida katuwar dadduma Aisha kuwa barin gidan ma tayi gabadaya .

Dady yacika alkawari ya dangana ga iyayen Aisha anyi barkwanci musamman ga alhj aminu to duk yadda dady yayi tunaninsu sai yatarar basu kai haka ba ,sai dai karfin hali da rufin asirin ubangiji Amman ta ko ina bbu, sai dai yaji dadin ganin mahaifin Aisha dagani zai Yi datako shidai mlm abu zaune yake yana bin alhaji ishaq da kallo tsabar kamamani dayake hangowa a fuskarsa tayi masa kama da wata fuskar a haka akayi abunda za'a Yi dady ya tambayar ma dansa kuma Mafi soyuwa acikin yayansa auren Aisha alhj
Aminu ne yaba da Aishar ga Abdullah cikin murna da farin ciki suka rabu .

Bayan dady yadawo Abdullah zaune agaban mahaifinsa yayi shiru yana jiran daga dadynsa yaji mai zaice dangane da zuwansa dan gabadaya baya cikin natsuwarsa burinsa Bai wuce yaji mai dady zai ce

Please Login or Register in order to submit comment