Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa aka buga kara kotu .
To can ne ma ya kori ma'aikatan na har abada..
Sannan yabi didigi kowacce kadara dake garesu anan cikin company .
a karshe dama yasan ba komai ne zai dawo ba.
Amman cikin dari an samu kusan kashi tamanin da wani abu .

Teema ce tayi nouking kofar part din Abdullah ya bude .
tashigo da jug a hannuta ta same waje ta zauna sannan ta tsiyaya masa fresh miki ta bashi ya karba.
ita kanta teema yaga duk ta canza masa komai cikin tsanyi jiki take yinsa .
sai daya shanye .
sannan tace bros dama naxo ince maka ni zan rika kawo maka abinci da zaka ci.
da kaina zan dinga girka maka ina kawo maka saboda a gaskiya ban yarda da zaman su mama hafsa da faiza acikin gidan ba .
dan akwai wasu abubuwa da nake ganewa idanuna .
gashi Sam mami mai da hankali balle ta taka musu birki.
Abdullah bai ce komai ba sai dai ya amsa mata da kai.

itama tana gama fadar haka ta Mike har ta kusan kaiwa kofa sai Kuma ta juyo tace bros duk wanda zai kawo maka wani abinci byn ni ka barshi kawai .
ta juya shi daman baya iya cin duk abinci da,ake kawo masa .
saboda ba irin test din da yake so bane.
kwata kwata sai dai masu gyaran wajen su fita dashi .

Ya kalli agogo tara ta dade da wucewa yayi murmushin gefen baki Aisha tasan lokacin da yake bukatar fresh milk a dan zaman da suka yi tare.
bata taba bata lokacin bare ta manta.
a yanzu kuwa tunda maminsa ke shareshi wata rana salis ke siyo masa a waje ya Sha ya ci takeway ya kwanta .

Yayi shiru yana tuna yau kusan kwana talatin da shida da tafiyar dady iya kwanakin rabuwarsu da matarsa kennan .
ya Mike jiki a sanyaye ya shige ciki ya kwanta akan royal bed dinshi.
ji yayi gabadaya kwanakin ma kmr bayin su akeyi ba .
ya fada aransa a kalla yanzu za'a kuma ninka kwanakin sau biyu kafin yaji wani bayani daga gareta.
gashi su mami tamkar zasu sa ya gudu daga garin haka yake ji kansa.
Akan maganar auren faiza shi kam yace dasu suyi komai ba sai an nemeshi ba.
tunda da auren suke so ayi .
Amman shi kansa yasan yanzu ba wani auren da zai dauke shi da daraja byn na Aisha
sanda ya aure ta bata son shi ,shi kansa ya san da haka .
bata damu dashi kuma ba bata son wani abu nasa ba, Amman dan zaman da sukayi suka tare shiga ran juna ko bacci bata iyayi sai dashi.
nan take jikinsa ya sauya yarikece ita kawai yake kishirwa a halin yanzu, .
Gabadaya idanunshi sun gama canza kala sunyi jawur .
ya jawo pillow ya kankame ajikinsa yana shafa ahankali Amman bai daina jinta a sansar jikinsa ba .
barin da ya tuna yadda ta ringa rikita shi adaren da zasu rabu ,
Ko tasan zasu rabu ne yasa ta rinka masa abubuwa masu cracking brain .
ya Mike tsam ya shige bathroom .
ya sakarwa kansa ruwa ya dade tsaye ruwa na zuba kansa .
sannan ya fito Amman yana sake kwanciya sake jin ta biyosa ta manne akirjinsa ,.
Jikinsa ya dauki rawa ya runtse idanunshi ya kankame jikinsa waje daya yana surutai iri iri .
adaren dai yayi wanka ya kai sau goma .
dan ya samu saukin sha'awarta har aka fara kiraye kirayen sallah bai runtsa ba haka yakaraci haukansa shi kadai a adakin.
har sanda aka kira assalatu ya kara tabbatarwa kansa lallai so bala'in ne .
bai gane hakan ba a tun farko sai a yanzu

Basu da lecture yau Amman tun jiya da babanta ya sanar daita zance Aisha take tunanin can zata wuni.

dan haka tayi shirinta tamkar wacce zata je makaranta ta fice Abba ya gaya mata zance ne domin ko su mamanta bai bari sun sani ba .
Tana shiga gidan daita ta fara cin karo .
ta fito daga bandaki da buta .
suka sawa juna dariya Aisha har da dan kwallarta na murna ..

Sakina taja hannuta zasu shiga rufar inna .
Aisha tace shiga inna tana ciki ku gaisa tukun .
ni ina nan tana fitowa suka shige tsohon dakinta dake kusa da na inna wanda byn barinta gidan ya zama na usman.
Amman a yanzu ma duk da kayansa yana ciki anan din take kwana .

Sakina ta dubeta da kyau cikin sanyi jiki tace sister ya jikin naki Abba yace baki da lfy .
Aisha ta dan langwabar da kai tace to da sauki kennan sister .

daga can suka dan yi shiru sakina tace a she sister kun rabu da Abdullah kuma ?

duk son da yake miki Aisha tayi shr bata kalleta ba ta sake cewa me ya faru ne har haka da zafi har ya kai gayin saki .
Aisha ta kalleta tayi murmushi takaici tace haka Allah yaso zaman ne iya haka.
sakina tace haka ne Amma ba haka aka so ba.
abin ma har da abin alajabi wai sister ciki gareki ?
.. Aisha ta sake yin murmushi itama sakina dariya tayi .
tace koda yake ke ai kin haye kin cigaban arayuwarki .
tunda da wani zai samu irin taki .
ai da yayi tsalle da kukan murna "Aisha ta dan dago ta kalleta tana mamakinta .
eh mana sister dubi yadda kika zama ke kinganki kuwa .
kinga kyau da kika kara .
sai dai Yar rama .
itama ina ga ta rashin lfy ce.
na farko kennan kin auri miji mai kyau gashi zaki haihuwa da shi dan Abdullah ko daga nesa mutun ya hange shi .
dole ya tabbatar da kyaunsa .
kinga kuwa ina tabbatar miki danki ko "ya" zasu yo kama dashi .
Aisha ta kalleta sosai ita fa haka take kullum a na cikin magana daita yanzu nan zata subuce wani gurin tamkar Yar fari .
haka ta fada a ranta ahankali tace sister ke abinda Dame ki kennan ni ban Dame ki ba ko
sister?
Haka ranar da za'a tafi dani ma guduwa kikayi kika barni sai yau na sake ganinki .
gashi yanzu kinzo,
komai ma ciwo yake min Amman kina maganar wani abu na daban can .
sakina tayi saurin rike hannuta dukka tace sorry sister ayi min afuwa .


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page 56-57


Da farko Kamar bazatayi laulayi ba, Amman kwanaki kadan laulayi yazo ya sata a gaba ko ruwa tasha baya zama acikinta.
gashi duk nisan abu idan ta kafa ranta shi zata dole taci dan idan bata ci ba sai taji duk cutar duniya kanta ta dawo ,.

kuma har dare bazata iya cin komai ba idan ba shi din ta samu ba wani lokaci har kuka take yi .


Gashi duk kinta da tunanin Abdullah sai da maraicinsa ya taba ta.
duk ta rame ta dashe tayi fari fat.
idan ta fara kakarin amai kuwa tamkar hanjinta zai fito.
magana ma wani lokacin da kyar take iya yin sa .
da kafar ta ma tafiya take dan yawancin duk unguwar an san da a yanzu tana gidan maganganu kuma iri iri bbu wanda baya tar dasu.

Ita sai daga bayan nan taji bayan tafiyar su da Abdullah.
dadinsa ya dauki nauyin hidimar makarantarsu yaya yusif da duk abinda zasu bukata.
akwai mutun na musamman da aka daura akan haka .
a yanzu haka akarkashin I M sidi magaji yaya Ali ya tafi NDA Kaduna ,.

sai gidanjenta wanda aka mallaka mata cikin sadakinta wanda tun bata dade da dawowa gida ba, da mlm abu yamata maganarsu .
Amman tace ita wlh gabadaya tabar musu Amman suna nan a rufe har yanzu ba abinda akayi dasu .
takardun ma suna gun alhaji aminu .
motoci kuwa ko yau suke so za'a kawo musu daga company dan haka duk wannan a idanun mutane suke har yau surutai ake a gari ballanantana da yanzu aka ga tana gida .

Aunty Maryam tazo da yammacin wata lahadi suna gaisawa da inna daga kitchen inna ta fito sai da ta samu gurin zama sannan take mata bayanin .
yawan zuwan da Doctor nan yake yi.
inna yayi shr tana sauraronta hade da kallonta aunty Maryam.
cikin tuhunna inna tace nifa abin har tsoro yake bani kullum ne sai yazo wai yazo dubiya ai ina jin kalla yazo gidan nan ya kai kusan sau talatin. Mlm ma da kansa abin ya dame shi .

Aunty Maryam ta dan langwabar da kai tace to inna yaya zanyi.
na rasa yadda zanyiwa doctor "can ma idan kinga yadda yake yi min sai kiyi mamaki "tun bana bi ta kansa har na hakura.
shi inna wai ita yake so da aure har cikin dake jikinta .
inna tayi murmushi kawai dan ita har yanzu ranta Abdullah take so da diyarta ,aunty tace baki ga abinda abun ya zame masa kmr wani ibada yazo kullum ya tambayi lfyr ta a gurina kafin ya fara aiki.
,har na rasa yadda zanyi da nacinsa .
inna tace haba nasan za ai haka abin yayi yawa fa da idan zaizo fa ke baki ga abinda yake tahowa dashi ba .
daga baya da muka fara fahimtar haka aka daina karba, aunty Maryam tace wlh ni kaina basan ya za a bullo abin ba ,.
gashi da bin diddigi maseefa ni fa kawai zuwa ya yi yace min wai kuna gaishe ni .
ban san ya'akayi yasan gidan nan ba ..

Inna tace a to rayuwa kuma iri iri kowa da irin tasa Amman shi yana daukar abu tamkar yanzu ne ,.
dan wani lokacin idan yazo ma bai ga kowa a kofar gida ba .
sai yafi awa bai tafi ba aunty Maryam tace ai shi bai ki da cikin a daura musu aure ba ko ayau ,inna ta rike baki.

Aisha na daga daki tana jiyo su ita dama ta dade da gane hakan .
tun a ranar zuwansa na farko da inna ta matsa ta je tsoro wai yazo ganin jikinta.
yana mata yan tambayoyi akan jikin Amman ta fahimci sarai me yake nufi .
ta Kare masa kallo tsab ,bai da laifi sai dai Abdullah dinta ya fishi komai nisa ba kusa ba ,shi Abdullah ma dazakaga jikinsa tamkar na bby sabon haihuwa sabo tsabar kyau gashi gentle man .
Amman shi wannan sai tsari da iya magana kmr wani lauya.
haka ta karaci kallonsa ta bar shi nan tsaye .
daga ranar ko magunguna ya aiko tasha na masu ciki bata sha sai dai tayi wasi dasu dan ita basu take so ba tafin so ta jita karkashin Abdullah dinta ta lumshe idanu sakamakon yadda tarinka jinsa yana yawo ajinin jikinta .

Aunty Maryam ce ta shigo ta katse mata tunani .
ta zuba mata ido tace kai Aisha haka kika kara zama dubi idanki fa .
Ta riko hannuta tana dubuwa .
tace har kin fi da dashewa fa duba kmr mara jini a jiki.
inna takaraso da kunun tsamiya data dama mata tace nima dai kallon haka nake mata aunty tace wlh ma haka ne inna ai sai muce
tare kawai an jima in yaso da safe muje asibiti a dubata.
cikin muryar kuka tace ni aunty ki barni kawai ba inda zan je wani dube dube .
Aunty Maryam tace ji ikon Allah kina cuta kina cewa a barki .
kinsan ma ko ba haka ba yana da kyau ki dinga zuwa asibiti saboda abinda ke jikinki .
Aisha ta bata rai tayi sosai tace nifa bazani ko ina ba a barni.
har aunty Maryam tayi fushi daita.

Washegari ne su gwaggo laure da matar mlm dahiru ne suka zo dubata yadda matar mlm dahiru taga jikin gabadaya cewa tayi zata wuce daita can ka'oje saboda yinin ranar cur ciwon ciki ya dawo sabo ko iya tashi batayi.
ga bala'in yinkurin amai tamkar dan zai fito ta baki .
dan ita gwaggo laure dan tausayi har kuka tayiwa Aisha.
ranar da zasu Wuce da safe takin cin komai ga yunwa tana ji kmr tayi hauka komai wari yake mata in dai a gidan aka dafa shi .
a sa'a sai ga aunty ta turo mata da dafaffen wake da kawai da ganye shi ta dan samu taci tana murmushi tace aunty ta huce kennan .
inna matar mlm dahiru kuwa da taga taci sosai sai kawai ta juye mata sauran acikin Leda suka wuce.
Amman kafin su kai ka'oje duk sai da bata ina motar da amai saboda warin man mota da yake cika mata ciki .
a motar har wasu na jin haushin yadda take bata musu guri.
yayinda wasu kuma ke tausaya mata .


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 58-59


Tunda suka rabu da Abdullah duk daren Allah sai tayi kuka rashinsa musamman inda tazo kwanciya .
gara ma da rana idan tana tare da mutane bata cika tuna shi sosai ba.
ita da kanta bata sanda soyayyar Abdullah tayiwa zuciyarta mummunar illa ba sai a wannan lokacin .
barin ma irin rayuwar da take ciki ayanzu.
yasa tafi tuno shi sosai akan da musamman yanzu daga ita sai inna matar mlm dahiru .

mlm dahiru yawanci shi ke siyo mata duk abinda take son ci, in da har yafi can gidansu a kebbi kennan.
Duk abinda take bukatar za'a tafi nemo mata shi.
kuma ba laifi takan dan cin abinci inna .

da kansa mlm dahiru ya matsa a kaita asibiti da kyar dai Aisha ta yarda suka je .domin daman acan kebbi bata son taga Dr salim shiyasa taki bin aunty suje .
har aka mata fadan rashin zuwa asibiti inda akarshe suka rubuta mata magunguna sosai dazata dinga Sha.

Da yammacin ranar tana zaune mlm dahiru yashigo taga ankama dan marakin anfita dashi aka siyar.
wai ashe magani za'a a siyo mata da kudin .


Karo na farko data bude handbag dinta da minal ta bita dashi tun ranar da Abdullah ya saketa ,.

ta zazzago abinda ke ciki har da check din da Abdullah ya taba bata lokacin suna Germany na miliyoyi kudi .
ta zuba musu kudin jiki ido ya isa ya kawo maganin karshen duk wani bbu .
Amman ita basu take so ba kuma basa birgeta tafison sanya Abdullah kwayar idanunta .
yafi komai mahimmanci a gareta.
ta tuna rayuwar da suka yi dama haka kawai lokacin sai tarinka jin zaman su ba me dorewa bane.
saboda ta koina abin bai zo daya", kawai taji hawaye ya shiga bin fuskarta . Tana kukanta
Inna ta leko tace mata zata shiga makwafta tayo musu barka" dayake bbu wuta a dakin sai Yar fitilar kwai " yasa inna bata fahimci abinda take yi ba.

tana fita kuwa ta sake barkewa da wani sabon kukan tasa hannu ta shafo cikin nata tace ko yaya Abdullah zai ji idan yaji zata haifa masa da ko "ya ? .
,Ta tuna wani kokarin can da suke American ya taba ce mata Aisha idan kika haifa min Yar bby mace zanyi ta ttalinta sosai zan koya mata gayu " ita kuma tana kwance akan cinyarsa tana dariya .
yace Allah musamman idan nasamu tayo kama dake ..Kai ai sai wanda nagadama zan bawa tayi, ta sake yin dariya tace to idan namiji aka haifa fa ?
kake wannan abun yace kinsan ance duka gadon haihuwa yawanci daga na namiji ne.
to kinga ni Kuma duk gidanmu matane ni kadai ne namiji .
dan haka killa nima da mata zan fara.
sai kiga wata rana nima ana min layi a gida wallahi sai na duba nutsatten siriki .
Tasa dariya tace uban "ya" kennan yace yes haka ne .
yana dariya itama tana yi .
To sai dariya ta kubce mata tamkar a lokacin suke maganar tana kukan tana dariya.
har tadan kware kadan ai ko nan da nan ta fara Tari ta fito waje da sauri tana yunkurin amai .
ai kuwa sai data amayar da duk abin ta ci tana haci ta kwanta anan kasa gashi inna bata nan .
tana kwance kusa da Aman sai data huta sannan ta mike da kyar ta dan kora ruwa sannan ta rarrafa ta koma daki ta kwanta .
aranta tace kowa yazo yaga jikinta ko dazu ma daga zariya dangin babanta sunzo .

Amman Abdullah yaki zuwa yaganta shikenan Abdullah da gaske ya daina sonta.
a da ko dan begewa tayi sai yaji kmr ajikinsa yaji .
idan rashin lafiya take"
yi yake tamkar wanda zaiyi karamin hauka.
tun bata damu dashi ba har yazo yakoya mata yadda zata so shi .
gashi da shiga rai ko yaya kake tare dashi sai yasan yadda ya faranta maka.
Amman lokacin daya gashi yanzu ya mata ciki ya barta da damuwarta ita kadai wanda ahalin yanzu tafi bukatarsa fiyye da komai.
ita Tama sanya shi a idanunta koda bazai cigaba da sonta ba .
tayi kuka sosai .
abin tausayi ita da kanta bazata iya tuna sanda tayi kuka irin haka ba.
tayi fushi da Abdullah da bakinta tace in Allah yaso ko waye Abdullah tabar shi .
ahankali take cewa Abdullah na barka na barka dama kai kasa na soka yanzu kuma tunda baka sona ka barni.
nima na barka in Allah yaso har abada bazan kuma barin sonka yay min illa ba.
har inna ta dawo ta leka ciki tayi kiranta Amman shiru batayi magana
ba .
inna ta dauka ko ta dade dayin bacci ne shiyasa ta kyaleta.
ita ko har lokacin hawayen rabuwa da son Abdullah take da tunaninsa .



Tun ranar kuwa yadda tayi alkwarin haka ce takasance dan ko sunansa bata sake tunawa ba.
abinda ta kaddara ranta daman can ai bata san shi ba .
daga baya ta san shi yanzu kuma tunda ya wuce shi kennan .
duk abinda ya danganceshi ta barshi. inna tana lura daita" yanzu nan zaku sha hirar cikin nata Amman da zarar ka bullo da zance uban cikin zatayi cikin cikin da rai tabar zance.
koma tayi kwanciyarta ta kudundune har kanta .

Haka kawai kuma taji Allah ya daura mata maseefar kaunar abinda ke cikin nata.
taji tana son duk abinda zata haifa din.
dan haka lokuta da dama idan tana zance cikin inna har fada take mata .
wai su anan basa yin haka acikin fari .
dariya kawai zata dingayi inna a ranta kuma tace ita wannan innar daukar kowa take yan zamanin su .

Dr salim ya riske su biyu bai yi tunani ko ba ita kadai bace.
ya dubi aunty Maryam idansa jawur.
sai faman huci yake yace sister yanzu akan ina son yarinyar nan.
yasa kuka dauke min ita kuka bar garin kwata kwata daita.
aunty ta dinga kallonsa wani irin tamkar me shirin dukankata .
Cikin zafi itama tace kaga dakata doctor abin fa bai zama na daga harshe ba.
Aisha dai ba yarinya bace" ba kuma igiyar kowa akanta "dan haka tana da right din da duk inda taga zai fiyye mata dadi dole taje .

Dr salim ya dubeta yana dan murmushi idansa har neman fidda kwalla suke dan tsabar bakinciki.
cikin Yar kwausashiyar murya yace sister Maryam kina daya daga cikin masu neman salwantarmin da rayuwa kennan .
tunda har kina goyon bayan barin Aisha garin nan.
saboda an san ko ban ganta ba idan naje kofar gidan na tsaya ina jin duminta a jikina tunda nasan tana cikin gidan.
shine dan bakin ciki kika sa hannu akabar garin daita saboda ki kuntatamin ko .

wata kawar aunty Maryam da suke zaune tare "tace haba doctor duk me yakawo wannan ko menene ma yana da kyau abi" abun cikin sauki mana.
ya dube kawar aunty Maryam ya watsa mata wani mugun kallo wanda yasa tayi tsit da bakinta .

Yace ai dukkanku dakikai ne shiyasa baza ku gane kan abun ba.
Amman muddin ina da karfina da lafiyata da hankalina bazan yarda na kasa magance abinda zai cutar da rayuwata ba '.
ya ja tsarki mai tsawo sanann ya juya kan aunty yace nakan kyale abubuwa da dama su wuce ni koda zasu dame ni bazan nema ba, saboda ban cika son na samu matsala a rayuwata ba.
nakan share koma menene bana bari yakai zuciyata.
dan bana son ya dameni Amman tunda naga Aisha sau daya na tabbatarwa kaina tawa ce .
ni kadai wani ne kawai yarigani yamin shigar sauri .
a yanzu kuma ya barmin ita tadawo gareni sannan kuma sai na bari wani yasake min shigar sauri.
ke kinsa impossible Aisha ta shafi komai na rayuwata .
dan haka zan iya damun kowa na tashi hankalin kowa akanta .
ciki kuma har da wanda bai sona daita .
kmr ke ba ya nuna aunty Maryam da yatsansa.
dan haka sai ki kiyaye ni wlh bai tsaya jiran wani abu ba yayi gaba abinsa.

Aunty Maryam ta zuba masa ido .
Wanda idanta har rawa rawa yake saboda takaici da ganin ikon Allah na Dr salim.
Sai da taga wucewa tace to ba sai kayi duk abinda zakayi ba.
ka tashi hankalin duka duniya ma, kagani kai ma idan bata hade da kai ba.
banza kawai .
kawarta ce ta dafa kafadarta .
tace kai haba ya isa haka mana wai duk mai me ya kawo haka ne?

Aunty Maryam ta numfasa tashiga yi mata bayani tace kinji wani ikon Allah kuma.
shine bai sani ba dan ko a lisafin Aisha bai ciki.
Da zai zo ya damu mutane iface iface.
Ta sake mai da hankalinta sosai kan kawarta tace dan tana yawon tunanin tsohon mijinta ne shiyasa aka tafi daita ka'oje.
shine zai zo ya dinga wa mutane bala'i ko an taba so da karfin dole ne" oho"

tace ai tunda aka dawo dashi asibiti nan" nake masa kallon irin yan kaidan nan .
ga girman kan maseefa da fadin rai .
Shiyasa rananan fa har ina mamaki da yazo har inda muke zaune "daku aka gaisa" ya wuce ashe ke da biyu yasa yayi haka.
Aunty tace biyun ma.
Idan mai yuwu wa ne ba .
ai ni wallahi har cikin Raina nafi kaunar Aisha takoma gidan Abdullah.
dan idan akayi auren da irin wayan nan.
Akwai matsala dan wannan irinsu duk randa zafin zuciyarsu ya tashi har ita Aisha zai yiwa duk son da zai mata .


Ita kam Aisha tana can ka'oje tana fama da laulayin karamin cikinta ita ko sunansa ma .
bata sani ba ballanantana ko me sunan shi taji ta dan tunoshi.
ta rame ta koma kmr baita ba shiya dan cikin nata ya fito a wata uku zai yashiga na hudu.
sannan tafara samun saukin laulayi "da yawan amai duk ya ragu kuma tana iya cin abinci duk da tasamu .
sai dai har yanzu akwai kwadayi iri iri musamman na yaji .


A washegari ranar ne su usman sukaje ka'oje dubata" shida aliyu da yazo hutu daga Kaduna suka tarar inna tayi mata kwadon zogale tana ci usman yana tare daita yayinda aliyu kuma ya tafi zariya kala kala gunsu iya.
sai inna dake can tana dora abinci rana usman ya dinga kallonta bbu laifi tayi kyau Gani sosai kmr ba sati uku da suka wuce tazo ba.
yana kallonta shi da inna haka ya sata a gaba tamkar ya dawo da cutar jikinsa haka yake ji .
ya zubawa abinda take ci ido

Please Login or Register in order to submit comment