Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne yayi nan da nan salis yace bakiji ba gashi nan fa , ahankali ta sake juyowa duk tsammaninta mai taxi ne ,tana juyowa abdulla dake jingine da jikin mota ya harde hannuwanshi a kirji ya zubamata manyan idanunshi yanabinta da kallo ganin duk ta daburce yasa yadan saki murmushin har gefen kumatunsa ya lotsa , salis yace madam ba gaisawa sai ki leko Kuma zaki koma . kallonsa kawai tayi mai hade da harara ,ta sake juyawa ta shige abunta salis yadafe kai yayin da abdullah ya cije lebansa yana mai runtse idanunshi,salis yace ta leko ta hararemu ta wuce abunta . Hade da cewa kai dagani madam fa za'a dama daita . abdullah ya dubi agogonsa muje kawai salis ai munga inda tazo yashiga suka wuce .

Tana shiga aunty Maryam tace me kika manta tace bakomai wlh aunty, irin banzayen kwarorin nan kawai" sukayi me kwarorin?inji aunty su dai nagani awaje aunty Maryam tadanyi dariya hum kedai baki da kara akan Maza .

Yana idar da sallah yashiga part din maminsa yasame ta itama ta idar da sallah duk da agajiye yake yadan zauna kusa da maminsa ,sister dinshi amina ta Miko masa fresh milk a Kofi ya karba ya Sha ,ya bata cup ta wuce kicin yace mami zandan fita bazan dade ba dan ita mami irin mutane nan ne dabasason arabeta ko ita tarabi mutun haka ko mijin bata barinsa ya sakewa da kowa inba ita da yayanta ba,mami takarasa jan carbi ta shafa ta kallesa tace Amman kasan salis yatashi daga aiki ko,ko a haka zaka fita daga kai sai musa yace ni kadai nike son fita ba direba mami tace no abdullah banason fitarka kai daya ga dare gashi kai bawani sanin gari kayi ba sosai" kayiwa salis waya kawai yazo ku je tare abdullah yadan langwabar da kai yace mami banason takurasa cikin iyalinsa ,tunda yarigada ya tafi a kyaleshi nima ba dadewa zanyi ba ta kada kai ,shi kennan Amman banso ka dade a waje" yayi murmushin ya Mike bazan dade ba har zai fita tasake cewa yanzu kai kadai zaka fita kennan ahankali yace don't worry mamina I can drive my self tace agaida sagir zatonta can zashi taci gaba da abunda takeyi yayi murmushin ya fita ,.

Cikin natsuwa yake tuki cikin dark green din benz har ya iso badariya dai dai kofar gidan dazu yayi parking cikin sa'a mai gidan ya tarar tare da wani bako ya isa yayi musu sallama tare da gaishe su , sannan yadan koma gefe basu jima ba sukai sallama bakon yashiga motarsa ya wuce .

Abdullah ya matso ya sake dukawa kusa da mai gidan cikin natsuwa yayi masa bayanin bakuwar data zo gidan tazu" mai gidan bai fahimce ko wacce ba daga baya yayi wani tunani sannan yace yana zuwa yashiga gidan bai fi minti biyar ba ya fito a nutse ya karfafa kallonsa ga abdullah wanda tun tafiyar sa zuciyarsa ke wassafa masa abubuwa da yawa M .Auwal mijin aunty Maryam ne "ita Kuma aunty Maryam Yar kanwar mlm abu ce uwa guda uba guda ,yadanyi gyaran murya tare da cewa malam.....koda yake bansan sunanka ba cikin sanyi yace I'm Abdullah M .Auwal yace ashe abdullahi ne madalla bakuwar yarinya da tazo dazu ai AISHA ce ,a AI.....SHA.. ya maimaita sunan a ransa M auwal yace kanwar matata ce Yan dakika da sukayi da abdullah ya nakalci wani abu hakan ya sanya ya warware masa cikakken inda zai samu Aisha gidan iyayenta da unguwar da suke zaune Abdullah yayi godiya sosai tare da Yi masa sallama .
Da fari yayi tunanin ya bari zuwa gobe tunda salis yasan gari sai su nemi unguwar da gidan haka nan zuciyarsa taji ba zata iya Bari zuwa gobe ba "a kasada yayi nufi yaje , ance mai tambaya baya bata sai ga shi a unguwar ,nesa kadan da lungu da akayi masa kwatance yayi parking sannan ya fito ya gaisa da mutanen da yasamu a gurin sannan ya kulle mota ya karasa . har yashige lungu da wayarsa yarinka haskawa saboda ya rike lokacin da M auwal yake masa kwatance mota baza ta shiga lungun ba hakan koda zai tarar bbu wuta yayi ahankali da kwatami idan yashiga lungun" yana magana yanasake duba jikin Abdullah to anyi dacen akwai wuta Amman duk da haka Abdullah nasake haska wajen da wayarsa gudun Kar ya sanya kafa acikin kwata byn yayi sa'ar shige kwatocin ne ya karasa kofar wani gida yara na wasan guje guje ya kirawo daya daga cikinsu ,yara 2 ne suka taho ya tambaye su gidan mlm Abu ko gidan su usman da sauri suka ce ga gidan can ya nuna masa da hannu abdullah yace na gode ya fida kudi cikin aljihun wando sa na baya ya basu ai ko suka shiga murna abdullah ya nufi inda yaron ya nuna masa wani datijo ya samu a kofar gidan kishigide yana kokarin kamo tasha abdullah ya isa yayi sallama sannan ya risina ya gaishe shi malam abu ya rage radio ya amsa ganin da yayi Abdullah bai sake cewa komai ba yana Kuma tsugunne ya sanya malam abu ya sake rage radio sosai daga bisani yace masa kana son gani wani ne ?
Ahankali yace E nazo gurin Aisha ne ko kadan Mlm abu bai kawo haka ba iya tunanin sa cikin yayyen Aisha yazo nema wani cikin su to bari asa a kirawo ta,ko bata kwanta ba dan bata da wuyar bacci ,Abdullah yadan sunkuyar da kai kasa don yasan duk laifin zuciyarsa ne data danace da son ganin Aisha a yau "a daidai lokacin da taran dare ke neman Yi "M abu yayi kira cikin gida kanin Aisha ne yafito , Amman idan baka sani ba zaka dauka yayanta ne saboda girman jiki gareshi yayin da ita Kuma Aisha bata da jiki.

usman shiga ka turomin Aisha tayi bako baban ya fada . usman Kuma ya juya ciki mintuna kadan suka shude yayin da malam abu yake nazarin Abdullah da tsabar kamar dayake dawani ya sani ya sanyashi ya zauna a gefen dakalin dake kofar gidan , usman ne ya katse shiru da cewa gata nan fitowa ,haka kawai Abdullah ya tsinci kansa yana tausayi wayannan bayin Allah don haka tun fitowar Aisha yake mata wani irin duban da yakejinta har cikin ransa, yayin da ita Aisha ke masa kallon tsoro karara a fuskarta jikinta har bari yake , Abdullah ya lura da hakan Amman sai ya dake hannushi duka cikin aljihun wandonsa ya hade mata fuska da Kyar ya iya bude baki may be an tasoki kin fara barci ?bata iya cewa komai ba duk da tana kokari son yin magana Amman bakinta yakasa furta wani abu, yawan duban hanyar waje da take ya sanya Abdullah yadan rage murya cikin sanyi jiki yakira sunanta a frigice ta sake kallonsa ,jin wani tashin hankali karara wai har sunanta ya sani ta fada a ranta ga wani babban tashin hankali babanta da kansa ya sanya Akira ta Kuma har yanzu yanan a kofar gida banda haka da tuni ta ruga gida ,kmr ya shiga zuciyarta ahankali ya sake kiranta Aisha ko na tafi ne gobe na dawo da sauri ta daga masa kai murmushin gefen lebe yayi ya dubi agogonsa nima ina son in wuce din tunda naganki da inda kike .

har yanzu fuskarta nan nashi ba yabo ba fallasa kallon tsoro take masa yace yes haka nike nufi ya dan ciza gefen lip's dinshi ,shikenan gobe na dawo ya zuba mata idanunshi masu rikita kwanyar duk wanda ya kalli cikinsu kallonta yayi son ransa sannan a hankali ya juya ya fice gabadaya ,ta saki ido tana binshi da kallo hade da jin wani mummunar faduwar gaba ta dafe kirjinta tana jin yadda zuciyarta ke beating.


Waye malam abu ?haifaffan garin zariyar kala kala ne, dake jihar kebbi shine da fari a gurin iyayensa tun bayan rasuwar wansa yanzu Kuma daga shi sai kanwarsa Laure mahafinsu yarasu tun lokacin Laure nada shekara goma a duniya alokacin rikonsa yakoma gun kakarsa data haifi babansa, yayin da kanwarsa ke hannu mahaifiyarsu laure tana da shekara gama shabiyu tasake wani aure, ko kadan kakarsa ba irin kakaninan bane masu sakarwa jikoki, don haka ta tsaya tsayin daka akan karatunsa da tarbiya ,sai dai ita sam ta tsani karatun boko yara tsaransa masuyin karatun bako sai ta hanasa Hulda da su, acewarta boko ko a wuta.

ta Mika shi makaranta allo acan garin akaoje malam abu yakasance mai tsananin hakuri da biyayya yacigaba da karatunsa har lokacin da yakamala yana zuwa gida duka huta inda kawarsa Laure tasa muji har an tsadaaganar aure, tafiya tayi tafiya yasoma siye da siyarwa a lokacin ya hadu da maimuna suka kula soyayya atsakaninsu , byn yagama shekartunsa da dadewa ya aure maimuna itama su biyu ne agun aiyayensu ita da yayanta wanda tunda yasamu scholarship karatu zuwa kasar sin baakarajin dauriyyarshi.
Daman da tazara dayawa a atsakaninsu .
Kuma har zuwa lokacin da iyayensu suka koma ga Allah bai dawo .

fataauci mlm abu yasoma daga kaoje zuwa cikin kebbi zuwa zariyar Kala kala, , sosai yake samun cigaba asanar dayakeyi , kafin daga baya yakoma can kebbi da zama inda yasamu mai gidan da yabude masa shagon siyar da kayan shinkafa da sabulai takarma da dai sauran su , watan su biyar acan , rasuwar mahaifiya sa ya riske su haka suka koma sai byn da akayi arbain suka dawo ,yakasance iya CE kadai ta rage masa, gidan da suke ciki daki guda daya hakanan Allah bai hanasu abun da zasu sama bakin salati ba har suka kai ga samun haihuwa .

shekara yusif biyu da watanni aka haifi Umar duk da ba haihuwar fari bace Amma gida maimuna takoma tayi wanka yaransu biyu abun sha'awa ga kyau musamman yusif dazata dawo ne tazo da Aunty Maryam shekara Umar biyu aka tashe su daga gidan hanyar dasuke adai dai wannan lokacin uban gidansa ya kwanta rashin lafiya dan haka aka karbi dakan daga cikin kudin dayake juyawa duk da haka Allah bai hanasa samun wasu kudi da yakama musu haya nan kusa dasu ba ,aganin malam abu bai cancaci yakoma gida acikin wannan hali ga yara ,duk da shima daki daya ne a wannan gidan innarsu yusif tasake haihuwa da namiji akasawa yaro suna Ali watan Ali bakwai Allah yayiwa uban gidan mlm abu rasuwa dan haka aka kwaice shagon dake hannushi saboda kayan ciki yashiga cikin gado.

byn share makoki mlm abu ya koma saide saiden takalma silifas da roba har da gajerun wanduna na yara wata rana asamu kasuwa wata rana Kuma sai godiyar Allah Amman dayake ZUCIYAR masu rikon iyali ne da mlm abu yana bakin kokarinsa sai dai abinda yazama dole ya Gaza idan lokacin damuna tayi yakan koma gida yayi aikin Gona tunda dama akwai guda dayar data rage musu shida kawarsa Laure duk shekara ana Yi sai a biyasu shine yanzu yakeyi idan ya girbe ya saida wasu yabi bashin da yayi aikin Gona wani yakawo gida ya kaiwa iya nata da Laure shiya abun baya wani dadewa a dalilin haka itama innarsu yusif har da saide saide takeyi anan cikin gida tana Kuma daurawa yusif da Maryam su shiga makwafta dan neman abin rufa asiri.

Shekaru na dada ja komai na rayuwa na dada tsawaitawa su inna da mlm abu musamman dayake yanzu sun dan taru wani lokacin kafin mlm abu yashigo da daddare tuni inna ta bayar a siyo masu garin kwaki ta jikamusu su ci su kwanta shima idan yadawo yasamu yaci wani lokacin kum idan yasamu waraka yadan ya shigo musu da abinda zasu ci ,kasancewa wannan lokacin silifas din roba yake kasawa abakin titi wani lokacin tun safe har ya taso babu mai tayawa bare a siya ko da wari daya ne cikin wannan lokacin ga inna da karamin ciki yana matukar bata wahala da taimakon Allah ta ke iya duba yaranta a haka take daurewa tana zuwa asibiti saboda lalurar ciki tayi yawa, ita tsammaninta duk dan ta dan jima bata yi ba tunda tunda lokacin Ali shekara uku har da watanni bbu wanda ya jima kmr sa duk cikin yaranta .

Cikin inna ya tsufa da Kyar take iya komai ga wani sabon tashi hankali daya samesu ,mai gidan ta basu notice nan da wata 3 zata gyara gidan danta zaiyi aure Kar kaso kaga yadda hankali mlm abu ya tashi a kullun da zance yake kwana yake tashi har rama yayi a wannan lokacin a safiyar laraba har ya fita can bakin titi inda yake zube takalma sai wajajen Tara sai ga yusif da gudu yaje yakirasawoshi yazo inna bbu lfy a gigice ya taho byn bar kayansa gun makocinsa daman tun jiya bata jin dadi ganin abun ya gagara ne yasa tani makwaciyarsu tace akirasa su wuce asibiti yana zuwa ko yace su tafi saboda yadda yaganta ita kuwa inna da taki kasancewa ita bata taba haihuwar asibiti ba sai a gida tani tarike zuwa titi a sami mota tare da mlm abu basufi mintina da tsayuwa moto ci nata wucewa Amman bbu ta haya wata mota kirar passant mai dauke da lambar sokoto har ta gota su sai km ta dawo ahankali ,ta sauke gilashin motar wani mutun mai fuskar fara'a ya tambayi su mlm abu yayi masa bayanin mutumin yace bbu laifi su shigo ya taimakesu su duka duka shiga domin a wannan lokacin bbu rashin gaskiya sosai a duniya a motar yake sanar dasu shima asibiti zai je dauko matarsa ta haihu tun jiya da daddare yau za a sallemesu .

Asibiti ya zarce da dasu ya tabbatar an gama musu komai an tura ta dakin haihuwa saannan ya karasa gurin iyalinsa mlm abu kuwa bai iya tsayawa ba shima ya bishi suka shiga tare suka tarar har an basu sallama ,suna hada kayansu ita da wacce suke tare alhj yakarasa ya dauki bby yana kara mata addu'a sannan ya mikawa mlm abu ya juya yana ma matar sa bayanin sa ya karbi yarinya yayi mata addu'a sannan suka sake gaisa da matar mutumin yana kara Yi musu Godiya sosai da sosai alhj yace bbu komai nima nan jiya bananan makocina ne ya kawo su dama ai haka rayuwa take a haka suka fito yana so yaga likita domin jin dai dai da sallamar tasu, tani ce ta tare su da murna ai har ta sauka yanzu da sauri suka sake karasawa ciki lafiya ta haifi diyart mace har an fito da ita an gyara yarinya ita ma inna ana gyarata,duka basu fi minti ashirin ba da zuwa ta haihu , nurse din tace dama da an dau wani lokacin mai tsawo sai dai ta haihu a mota aka gyaro yarinya tasa siyo mata kayan bby aka turasu inda zasu huta sannan su mlm abu suka karasa ya dauki bby baki yaki rufuwa yana Yi mata addu'a ya mikawa alhj yana karbarta yana murmushin shima yamata addu'a ya yaba kyaun da Allah yayi mata ya mikawa tani yarinya sannan suka fita a haka sukayi sallama da mlm abu yana kara jaddada godiyarsa ga alhj da bai San sunnansa ba, da zasu rabu har kudi ya bawa mlm abu akan su nemi mota idan zasu koma mlm abu har yarasa bakin magana illa iyaka ya nemi yasan inda alhj yake zaune don idan komai ya natsa yaje yasake masa godiya ,alhj yace bbu komai Amman yana iya zuwa a gaisa yayi masa kwatance unguwar da gidansa a haka sukayi sallama .


Wanna karan cikin kebbi akayi suna inda yarinya taci Aisha iyaka dangi da suka samu zuwa suna har da kanwarsa Laure tun ana sauran kwana biyu suna ta iso.

kwana uku da suna mlm abu yabi kwatance da alhj yayi masa har unguwar aka nuna masa gidan alhj aminu yakara yayi sa'ar samunsa a gida sun gaisa sai gashi mlm abu ya fito da goro da alawa har da Naman sunan Aisha yabawa alhj aminu ya karba yana godiya mlm abu ya tambaye sa iyali da Sunna jaririya , alhj aminu yayi dariya kawar Aisha kennan tana ciki ta karbi sunanta sakinatu sun dan taba hira sukayi sallama ,alhj aminu mutune mai son Hulda da jama'a gashi wayayye yana da rufin asiri dan boko ne sannan yana taba kasuwanci duk abunda yasan zai samu halak dinsa akai ,yana da mata biyu yayansa hudu yasir musba ummulkursum sai sakina yayin da amarya dukka watanta bakwai kennan hakanan alhj aminu yana da raayin kansa idan yace ga abunda zaiyi bbu mai iya canza masa ra'ayin ba iyalinsa ba ko wansa a yanzu da suke ciki daya idan ya tsaya kan abu.........



MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page 3



Ko wansa da suke ciki daya idan ya tsaya akan abu sai dai ya kyale shi, ma'ana kaifi daya ne idan zaiyi zaiyi ,idan ba zaiyi ba ba zaiyi ba ,Kuma ko kadan baya yarda hakan yasashi shiga hakin wani wannan kennan.

Duk da wannan lokacin mlm abu yayi girbin amfani Gona dan haka ya raba har gidan alhj aminu Yan magana dai sunce naji dadi shine gari, a bangaren alhj aminu shima yaji dadin abinda yayi masa ,a lokacin har ya nema sanin inda Mlm abu yake da zama , Mlm abu yayi masa bayanin sai dai ya nuna masa a halin da suke ciki yanzu na shirin tashi suke alhj aminu yace muddin ya samu daki a garin nan zaizo yasanar dashi in km bai samu ba zaso koma garinsu ne ,alhj aminu ya tambaye shi tsawon shekarunsa a garin da km lokacin da aka basu notice duka mlm abu yayi masa bayani komai alhj aminu ya Nisa yace yanzu dai zaiyi tafiya gobe ,km in Allah yaso nest week zai dawo dan haka yazo nan da kwana takwas ko Tara yazo yasamesa yace yadan jinkirta tashi har ya dawo, haka suka rabu ,A aminu yace a gaida masa da Aisha.

Ranar alhamis ta kama kwanansu Tara da yin magana ,jiya laraba kennan A.aminu ya dawo daga tafiya da yayi zaune a sitting room din A aminu tare da mlm abu byn gaishe gaishe A aminu ke tambayar sa dama can shi baya wata Sana'a ne mlm abu ya sanar da shi irin sana'ar daya tabayi da wacce yakeyi yanzu ,alhj aminu yace ai yanzu ina gani komawa gida ba naka bane hakan yawon biye biye gidan haya ba mai yuwa bane ,ina ganin abinda yafi ka tsaya ka nemi naka na kanka ka siya ka zauna da iyalinka .

Mlm abu ya zaro idanu zaiyi magana A Aminu ya katse shi ,ta hanyar daga masa hannu ,yace akwai wani dillali dake kawo min filaye ina siya byn Yan watanni kadan sai na siyar ,haka nan ya kawomin gidaje kanana har sau biyu na siya daga baya siyar dasu ,to nayi magana dashi tun a Daren da zanyi tafiya nasa ayi cigiyar gida karami a wancan zuwa da kayi kasanar dani kana da Gona a garin ku , dan haka zaka koma ka tsaida wancan Gona.

Mlm abu yasake zuba masa ido , A aminu ya cigaba "haka nan a labarin daka bani yanzu ba aikin da baza ka iya ba,.

ka iya tuki da sauri mlm abu yakada kai to ALHAMDULILLAH dan haka zanyi kokari naga nasamarmaka tuki a wani kamfani ka fara ,ba zasu biya ka ba har sai kayi wata biyu su hada su gabadaya ,to da wannan albashin naka da kudin wancan Gona ina ganin zasu isa ka nemi gida karami naka na kanka .

Mlm abu ya hadaye yawu da Kyar ga bikin zuwa .... A aminu yace kafin wannan yana da kyau kafarayin shawara tare da tunani akan hakan mlm abu yadan sake gyara zama sosai yace alhj ni banida kowa a garin nan sai matata da ya'yana sai kum abokin arziki irin ku ,don haka wannan shawara daka kawomin ma tayi min sosai na km gode kwarai da gaske ,sai dai km ita wannan Gona bani kadai ke da ita ba gadarta mukayi nida kanwata , haka nan a jikinta muke dan samun abinci na wani lokacin , wannan shine matsala , maganar komawa gida dama nidin ma sai takama dole don banason komawa alhj aminu yace wannan gaskiya ne sannan yace abunda zaayi mlm abu ....yasakeyin shiru can ya Nisa yace abunda zaayi kasake bani kwana biyu zuwa uku zan sake ganinka.

Mlm abu yayi godiya tare dayin musabaha alhj aminu yace muje na sauke ka a gidan.a hanya suna ta hira yanayin rayuwa ta titi da su mlm abu ke kafa tebur suka wuce har ya nuna masa inda yake zama alhj aminu ya sauke shi kofar gida da yake yammace ,a dai dai lokacin sai ga yusif da Umar Maryam na rike da hannun Ali antaso daga makaranta Allo dukkan su da allunansu a hannu da gudu sukayo wanjen mlm abu, yayin da Ali ya tsaya baya yaki tawowa wai don sun rigashi zuwa mlm abu yana dariya ya karasa ya dauko shi ya cika ZUCIYA ,alhj aminu ya rike hannu yusif da Umar yana tambayar su sunansu mlm abu ya karaso ya ajiye Ali yana lallabashi alhj aminu ya kama hannusa yace taho nan abokina ka rabu da su anan yake tambayar yaran ajinsu nawa a makarantar boko yusif yayi caraf yace ai bama zuwa alhj aminu yace subuhanallahi ya akai kuna cikin birni ba kwa karatu boko ,ya dubi mlm abu.

Yace wannan km laifin ka ne mlm ya'ya irin wadannan basa karatun boko mlm abu yayi murmushin saannan yace dasu yusif suje gida dazasu wuce A aminu ya fiddo kudi cikin aljihun babbar rigarsa ya basu , saboda sabon da innarsu tamusu suka ki amsa sai da mlm abu ya sanya baki sannan suka karba sukayi godiya suka wuce gida , A aminu ya bisu da kallo yana yabawa da yaran Masha Allah.

Sun Tautauna akan wannan matsala ta rashin karatun yara kafin surabu inda A aminu ya Dora laifin kan mlm abu shi km har a lokacin mlm abu yanaganin akwai saura lokacin da Allah zai kawo yaran suyi karatu tunda shima daman akwai soyayyar karatun aransa Allah ne baiyi ba,a haka suka rabu A aminu yace zai nemeshi acikin kwana kin nan.

Mlm abu zaune akan titi da suke kafa teburin takalma shi da makwabcinsa mlm dauda suna hira mlm abu yana dariyar mlm dauda yana bashi labarin iskar daakayi jiya cikin dare wajajen biyu saura shi Kuma a lokacin ya farka daga bacci ya tashi ya nufi bayi sai ya iske wani abu baki yana reto a kofar bayangidan, ya tsaya cak bai Yi auni ba sai iska ta fizgo abun yayo kansa aiko ya juya da gudu hannu rike da wando har yana bigewa da abun ya kusan hantselawa yashige daki yana kokarin rufe kofa ne abun ya sauka kasa sai yaga ashe ma bakar Leda ce ,mlm abu yana cikin dariya motar A aminu ya tsaya ya fito mlm abu yarasa inda zai sanya shi dan murna sai kujera ya aro can gaba da su suka samu guri ya sanya masa ya zauna sun gaisa mlm abu yake nuna mamakin ganin A aminu a daidai wannan lokacin domin duka goma na safe a lokacin, A aminu ya shedamasa yasamo

Please Login or Register in order to submit comment