Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa anriga an gama shi ahankali cikin dabara duka dady ya bincike abinda yake son ji daga gareta "kuma cikin sauki kai duk mami ke masa bayanin komai har da abinda bai tambayeta ba.
dan har irin dukiyar da ta sakar musu da fitar dasu faiza sukayi hado lefe da kayan gado duk sai da yaji a karshe ta bayyana masa komai" na part din Abdullah dady har tsorata ya farayi da lamarin "yana can an kusan kashe masa gida kuma duk abinda mamin take a yanzu ya dada tabbatarwa kansa ba'a cikin haiyacinta take ba . Dama kuma duk shekarun da take dashi da ya'yan data yi .
idan ta masa wanin abun kallo daya zaka mata kasan diyar fari ce Kuma Yar auta Yar gata .
Dady ya jinjina girman al'amarin sosai a karshe shima ya nuna mata yadda duk suke so ita da mama hafsa shima haka zaiyi musu" ko da anzo daga can ma hakuri zai basu me yiwuwa ya bisu a daura auren a ranar .

Mami tasan meye kulawa a rayuwarta "ya amince da wannan tunda ga kansa har zuwa kan ya'yansa tana basu kulawa yadda ya kamata tana rawar jiki akansa sosai musamman idan yayi tafiya ya dawo.
Amman wannan karon yaga canji me yawan gaske atare daita tunda ya dawo baifi sau biyu tashigo part dinsa ba shima murtuke ,da fuska da rikici iri iri suke rabuwa .
sai a yanzu yaga fara'a ta sosai saboda abinda ya fada zaiwa mama hafsa har hira ta barke tsakanin su ya gaya mata abubuwa da makwaftan su na abuja suka zo dashi .
ya kwaso ya Mika mata ta karba tana Gani ya zuba mata ido jiya ko baccin kirki bai samu yayi ba.
yana ta addu'ar Allah ya fahimtar dashi abinda yake akwai har istahara yayi duka a daren jiya .
sai gashi Allah ya sanyaya masa zuciya yanzu gashin cikin dabarar da yayi mata game da zance biki yasan komai .
kuma yasan inshallahu komai ya wuce .

A yadda dady yazata kuma yake sauraro.
.hakan ce takasance dan karfe 1 daidai yakarbi wayar daga wajen masu gadin gidan "yana ajiye wa shima yayi tasa wayar Jim kadan sannan ya fito" da kansa" zuwa wajen get din gidan.
yadda yazata din kuwa haka ya Gani mama hafsa ce ita da faiza sai kanwar faizar rahma ganinsa yasa su da kansu suka tsorata a bazatan da yayi musu.
dan tun zuwansu da masu gadi suka tsaidasu basu sanar musu dady ya dawo ba .
dan mama hafsa har huci take tana numfarfashi hade da zagin masu gadin .
dama kuma tazowa mami da zafinta .
mintina kadan suka wuce bbu mai iya magana acikin su ,ba abin su gudu ba su fallasa kansu ko cikakken minti goma ba'a yi ba "sai ga motar police biyu cikin fararen kaya "dady yayi musu nuni da mama hafsa ai ko kmr Jira suke suka ciro I'd card dinsu suka nuna mata .
Hade da nuna musu su shiga mota a frigice mama hafsa take kallon abinda Ya ke shirin faruwa ita faiza so tayi ta gudu suka cafko ta sai cikin motor suna cewa bawani abu za'a musu ba illa yan tambayoyi .
dady yace aje dasu sai yazo nemansu.
motar taja bbu wani wanda yasan abinda ke faruwa a waje .
dan ko masu gadin tun kafin yan sandan su zo dady yace su shiga ciki mami ma na can cikin gida batasan wainar da'ake toya ba.
bare Abdullah da gabadaya baya unguwar ma haka aka tafi dasu dukkansu su uku rahma kuwa kuka kawai take tana kiran wayo Allah .. (wannan shine akoba adaba 'olon ma'jerin') inji yarbawa .



Tayi shr a daki mamaki abin take ,ta dade rabon data kawo shi a ranta tun byn rabuwarsu .
data dinga tunanin shi tana kuka a karshe ta hakura dashi "tunda bbu alamun shi.
komai nasa tabarshi sai a jiya da daddare data kwanta tayi mafarki dashi .
ta ganshi yana kuka kuma sosai har tazo kusa dashi ya kama hannuta yana cigaba da kukan sai itama taji tana neman tayashi .
adaidai lokacin da kukanta zai bayyana ta farka tun daren takasa komawa bacci .
dan bata gane kan mafarkin ba .
tasaba ada muddin ta kwana da tunanin Abdullah to tabbas ne ranar sai tayi mafarkin shi.
Amman sai gashi ko mai sunansa bata tuno ba sai gashi tayi mafarkinsa ,.

to byn saukowar masallaci jumma'a ne kadan sai ga babanta da saurinsa yashigo.
yana kwasar tabarmi da abubuwan sallah yana gayawa innarmu wai yayanta ne yazo .
tana kallon yadda innarta ke murna da dariya farinciki hade da daga hannuta sama tana addu'a .
to har zuwa byn la'asar Aisha bata motsa ba tana daki a kwance har sanda taji babanta sun shigo tare da dadyn Abdullah sun gaisa da inna sosai .
yayinda mlm abu yadan basu waje su gana .

Kwanaki biyu kennan da mlm abu yaje dubota da yaya yusif ta biyosu dan taga innarta .
idan ta kwana biyu zata koma dan tafi kaunar zaman can .

Tana nan har lokacin da taji uhun ya'yan aunty Maryam da hargowarsu sun shigo tare da aunty sai lokacin ta dan mike ta fito tayi alwala .
Aunty Maryam na can tsakar gida tare da inna da ta iddar da sallar la'asar .

tariga ta gama yanke shawara aranta dan haka tace ni aunty tare zamu tafi gidanki na dan yi kwana biyu sai na dawo na wuce ka'oje aunty Maryam ta dan kalleta kadan tace ai ni haka nake so da zaki yarda ma da muyi zamanmu tare idan su inna zasu ganki ba sai sunyi tafiya mai nisa ba .
Ta dan yatsina fuska tana kai aunty ke me fita kullum gara dai na koma can yanzu haka nasan inna nacan na kewata .
Aunty ta jinjina kai batace komai ba .


To a daren ma da ta kwanta sai da ta sake mafarki dashi ita har tsoro abin ya fara bata ita dai a yadda take ji ko me za'a yi sai dai ayi Amman tagama auren Abdullah ,.
cikin sa ne idan ta haife mishi zata bashi abinsa nan taji wata irin faduwar gaba itama tana son danta fa bazata iya bawa Abdullah ba sai dai kawai yayi hakuri ya bar mata ko su yan gidansu dokin ta haifar musu karamin yaro suke .

da safen ranar Sam Abdullah yakasa hakuri dole yaje ya samu Dr sagir din daya rakashi yace shi ko me babanta da yan'uwanta zasu ce zai rufe ido ya sauraresu ya Kuma basu hakuri shi dai kawai su sadashi da iyalinsa .
To yadda yazata abun ma ba haka yagani ba.

yayi sa'a ya samu mlm abu a kofar gida a adaidai lokacin da yake shirin fita ya tafi zariya kala kala duk dai akan maganar .tasu.
byn gaisuwa sai dan bayanin daya musu akan zuwansa zariya kala kala sai bayanin ita kanta Aishar . Abdullah yana durkushe kmr wani mai tsansar tsoron ko dago kai baiyi a karshe mlm abu yasanar dasu Aishar ma tana gidan aunty Maryam .

Tunda dai duk abinda Allah ya kaddaro bawa dole yayi hakuri dashi duk uban da akace an saki diyarsa a wannan halin dole zai so ace takoma dakin mijinta ta haihu dan haka duk yadda Abdullah yazata sai yaga ba haka ya Gani ba .
bbu wani batanci daga babanta har ma sauran yan'uwanta daya shigo gaisar da inna a zuciyarsa yace lallai jini daya ba wasa bane.
a karshe sukayi godiya sosai suka mike Abdullah yaji dadi Sosai abu daya "daya dan dameshi kmr yadda dady ma yayi masa kofafi akai har yau suna nan a mazauninsu daya san su.
basu da niyyar tashi saboda haka ne akasawa Aisha gidaje a cikin sadakinta tunda an san ita dai bbu abinda zatayi dashi .



Mijin aunty suka fara samu a waje yana shirin shiga gidan da fara'a sosai ya tare su .
ya shigar dasu sit room dinsa dake ta hanyar waje.
byn gaishe gaishe dan shiru ya biyo baya na wani lokacin Amman mijin aunty Maryam dayake yasan halin da'ake ciki ya gane nufin su dan haka.

Yayi dan Jim sannan yace koda yake bari a turo ita Maryam din ya tashi yashiga .

Abdullah ya rike hannu karamin yaron aunty Maryam yana tambayar sunansa Amman wayance yake tambayarsa Aisha aunty ta shigo hade da sallama ta dinga murmushi ganinsu dan ita tun jiya take murna saboda tasan wannan dan rigimar Dr salim bai san Aisha tazo kebbi ba gashin zuwan nata yazo . mata da alkhari tsohon mijinta mai kaunarta ya dawo gareta .
dama kuma tasan abu ne mawuyaci Abdullah din bai dawo ba .
Aunty ta zage sosai ta nuna musu bbu wani abu komai ya wuce Allah ya kiyaye gaba tunda dama wata rana dole a sake haduwa tunda me hadawa ya hada.

matsalar dai a gurin Aisha take ta nuna musu tun jiya dataji dadinsa yazo shine ma ta gudo gurinta.
to anan tsakanin su su uku suka shirya duk yadda za'a yi aunty Maryam takara da cewa ai ko yanzu da zata ji kunzo to bar gidan kennan.
Abdullah yayi murmushi kadan yasan za'a yi haka Aisha bazata son ganinsa ba ya fada a ransa..




MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Page 66-67


Aunty Maryam da Dr sagir ne.
suka tsara duk yadda za'a yi tafiyar " musamman da kowa yaji inda dan'uwansa ke aiki akwai wanda yasani a gun .


washegari da yamma sai da suka sake zuwa gidan Amman ko kadan bata bari Aisha tagane ba.
dan aunty Maryam ta kagu taga Aisha ta koma gidan Abdullah ko dan saboda wancan jarababben salim din yadda idan yata shi balbalinsa ya kone shi kadai .

Da daddare tana dakin aunty kwance Aisha tana kan gado sun gama wasa da diyar aunty Maryam har tayi bacci a jikinta.
aunty tace ni ko Aisha ina ganin yanzu yadace ki fara zuwa awo asibiti tunda kinga watan cikinki yanzu yashiga wata na hudu kennan.
Aisha tayi shr bata ce komai ba.
Aunty tace Amman yadda kika gani fa.
wai saboda lafiyar abinda ke jikinki ne dan akwai magunguna na musamman da'ake son mai ciki ta dinga amfani dasu" domin ta haifi yaronka cikin koshin lafiya .
da yake cikin na ranta dan haka ta tsaya sosai tana saurara auntyn.
Amman in kin fi son sai kin kusan haihuwa ne shikenan aunty Maryam ta fada batare da ta takura mata ba .

Aisha ta dan mike ta jingina da jikin gadon" ahankali tace ni aunty kawai sai a ganni na tafi wani asibiti kowa ya dinga" kallon ina da ciki.
aunty tasa dariya tace to ke meyasa kikayi abinda yasa kika samu cikin?
Aisha ta turo baki tana cewa haba aunty haba aunty da kanki .
Aunty Maryam ta sake fashewa dariya sai da tayi mai isarta sosai "sannan tace ai bangaren daza kije asibitin ko wacce ta kalleki itama abinda yakawota kennan .
Amman yanzu kina komawa ka'oje bbu wani zance zuwa asibiti akai akai.

Aisha Tace ai can din ma akwai asibiti sai ba sai naje ba .
aunty Maryam tace ki ajeye komai kizo na kaiki asibiti malam ki kwantar da hankalinki bama asibitin mu ,zan kaiki ba nasan saboda Dr salim baki son zuwa .
wani zan kaiki duk da akwai wadan da nasani acan za'a yi miki komai ko ba nan.
Aisha ta girgiza kai alamun ta amince .
aunty tace to kishiriya gobe in Allah ya kaimu sai muje a yankar miki card daga nan zasu gaya miki randa zaki dawo ahankali tace shikenan.
aunty kuwa har godewa Allah tayi da taga ta fada tarkon farko .

Tun shigarsu asibiti Aisha ta gane tabbas sun taba zuwa asibitin ita da sister dinta dubiya .

Wata nurse ce ta karbesu hannu bibbiyu da fara'ata sosai" inda ta dada birge Aisha taji dadi Sosai har cikin ranta kuma ta rike sunanta sister din kafin su baro asibitin.
komai akayi mata shi cikin sauki ba yadda ta zata ba .
A dan lokacin ma har taji tana sha'awar irin aikinta sister din.
Tama awo duk a lokaci sannan tace dole zata dawo jibi da akwai gwaje gwaje da za'a yi mata .

To hakan kuwa komai akan idonsu Dr sagir da uban tafiya Abdullah ya faru .
ta gabansu "su aunty Maryam suka wuce "tun shigowarsu Abdullah ya kura mata idanunshi ta canza sosai ta kara kyau matuka fiye da lokacin da Suke tare.
ko Kuma a lokacin dan yana ganinta ne koda yaushe ne .
yanzu kuma ya dan jima bai ganta ba sanda suka zo daf da inda suke da sauri Abdullah ya juya bayan wani ginin.
ya dafe kirjinsa ya rufe idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin dokawa da sauri da sauri.
ita kanta Aishar data zo daidai gurin da Abdullah yake a boye sai da taji jikinta yayi alamun wani abu dan itama hakance takasance daita .
Amman bayanta kawai ta dan juya sannan sukayi gaba itada Aunty Maryam shi kuwa Dr sagir bayansa kawai ya juya musu .


Ganin irin karbar da akayi musu yasa har suka baro gurin fuskarta a sake take Sosai .
Har aunty Maryam tarinka tsokanarta tace A'a kaga masu cikin fari ana murna dan ance zaki haifi da Kato .
Aisha tasa dariya tace kai aunty" har suka sake wuce wa su Abdullah na gun ya zubawa bayanta ido shigewar da tayi tana murmushi kawai Abdullah yaji gabadaya hankalinsa tashi .
garama yabita koma me zai faru gara ya faru wato ita rashinsa bai dameta ba ta sake abunta tana walwala har ya fito zai rufa musu baya da sauri Dr sagir ya fizgo hannushi yaja shi ciki sosai yace haba friend ka natsu mana.
zafa ka bata mana shiri idan ta ganka me yuwa baza kuma yarda ta dawo ba .
Abdullah ya tsaya kawai yana kallon Dr sagir hade da sakin naunauyen hadiyar zuciya sanda salis yakaraso da sauri ya tsaya yana duban Abdullah hade jin wani irin tausayinsa .

Agurguje ranar laraba aunty ta rakota " sai da ta bari ta tafi wajen awo sannan ta juya ta tafi gurin aikinta saboda aikin safe gareta.
duk wani gwaje gwaje da akewa mai ciki sai da aka wa Aisha.
sannan sis din tace ta dawo jibi da yamma ta karbi sakamakon da kuma ragowar magunguna a saboda jibi aiki yamma ne daita.
Aisha tayi godiya sosai tana shirin sallama daita aka turo kiran sister din tayi shr zaune a gurin tana tunane tunanen dan sister din tace tadaka ne da tuni ta tafi .
sister din ce ta sake shigowa tace kiyi hakuri fa na barki ke kadai Aisha ta mike tana ce mata ita zata tafi Amman sis din taki dole suka fito tare daidai lokacin shi kuma Abdullah yashigo asibiti shi da salis a bakar Jeep ya hangi zasu shiga mota itada sister kwata kwata yau aikin office ya hanashi ya dan fito gashi har zata tafi da sauri ya nemi Dr sagir a waya ya sanar dashi ta gama za'a kaita gida Dr sagir yace yayi hakuri shi dai kawai yakaraso office dinsa.


Ranar jumma'a kuwa bata shigo asibiti ba sai byn uku saboda cunkoson abin hawa .
ta gaban Abdullah ta wuce yana zaune cikin mota ya sauke glass din motar ita kadai ce tazo shigarta ta yau ta dada tayar masa da hankali tamkar tasan abinda zai kasance a yau.
sai da ya tabbatar takarasa gurin sister sannan shi kuma ya juya motarsa ya fita zuwa gidansu wajen babanta tana isa wajen ta tambaye wata dan Allah sister zahra fa? .

Wacce ta tambaya ta hada da wani ya nuna mata wani office tashiga ta tarar daita tana ganinta "ta fara dariya tace yanzu nake zancenki a Raina" ina tunanin zuwanki saboda nima bana son na wuce 4 anan " Aisha takarasa wajenta fuskarta dauke da murmushi suka gaisa
sister zahra tasoma dan janta da hira kadan kadan kan zance haihuwa .
sannan tace ina son dan kammala wani aiki ne sai mu tafi tare na biya gidan doctor na baki sauran magungunanki da result din ma yana can daga nan na sauke ki a gida .
.

Aisha tace ba komai illa ta kalli agogon lokacin sallah ma tayi ta fada a ranta .
sannan ta dan kalli sister zahra tace mata ko zan iya yin sallah.
sister tace har lokacin yayi nima banyi ba ko kibari muna zuwa can mukayi sallah sai mu fito dan yanzu toilet din ma sai an zagaya can baya Aisha ta amsa .
Tana nan har takarasa aikin suka fito tare .

A gidan Dr sagir suna shiga matarsa ce ta taresu a falo gidan.
sister zahra ce ke tambayar ko doctor yana ciki ta amsa mata da yafita Amman duk inda yake yanzu yana kan hanya tunda yasan da zuwanku tunda har ya sanar min .

Sister tanemi da suna son suyi sallah.
ita sister din ce ta fara shiga tayi sannan da ta fito Aisha ta shiga ta lura da irin kallon da matar ke mata har jikinta ya dinga bata to ko ta taba saninta ne ?
A daki tayi sallah dan sister zahra ta rigada tafito tana karasowa falo Dr sagir yayi mata magana suka fito waje har Abdullah Dr sagir yayi mata godiya sosai yace zata iya tafiya abunta tayi shr Amman sai satar kallon Abdullah take ta dai .
ta amsa kawai har zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi tayi gaba.
tare suka dawo falon da Abdullah Dr sagir ya kalleshi yace Abdullah me yanmmata kennan kai farin jinin naka akansu yakare ne Abdullah ya kalli Dr sagir yace dan malam ban son iskanci kabarni da rikicen dake gabana Dr sagir yayi murmushi yace a to ni ina ruwa ita fa wannan sister din kai take so .
Abdullah yadan zungure shi yace hankali da bayanka dai Dr sagir yadan waiga kadan daidai lokacin da Aisha ke shigo falon ya juyo yace wuuuuuu... Ana kukan targade ....
Abdullah yace kawai kana neman karasani. sukayi dariya a tare .
tsoro frigice ne taji sun kamata alokaci guda sosai tasoma rikicewa har gabanta ya dinga faduwa saboda ganin su datayi tsaye suna dariya .
Ahankali tace gaskiya sun shammace ta dayawa .
duk a dabarbarce take Amman tayi yunkurin dakewa ta dan zauna a kujerar da tun zuwansu anan ta zauna tana dan dube dube.
su dukkansu ,zama sukayi Abdullah ya zauna kujerar dake kallon nata ya zuba mata ido "kyan da ta kara ya wuce yadda ya dinga kiyastawa ,.
komai ya canza a tare da ita har Yar kiba tayi me yiwuwa ko dan albarkar cikinsu ne yasa takara kyau .

Aisha kuwa tarasa a wani hali take ciki abinda ya kara tsorata sai yanzu ta lura da hoton dake jikin bango da kyau Dr sagir ne da matarsa sai dansu dan kimanin shekara biyu alokaci ma yana gidan kakaninsa .

Aisha ta dauke kanta karda dai rai na mata wayo za'a yi ta fada a ranta .

Dr sagir ne ya fara magana bayan matarsa ta ajiye musu abinci da lemon" yace madam kinyi shiru friend fa ke yazo ya bawa hakuri kuma ayi sulhu da juna .
Sai alokaci ta dan kalleshi Amman Sam taki amincewa idannuta ya hadu da na Abdullah tace da gaske ne dai abinda ta, zata.
ta sake kallonsu a yadda suke bbu yadda za'a yi ta iya tsallakesu ta shige batare da Abdullah yayi wani abu ba.
ita ko da matar Dr sagir za'a barta tasan baza ta koina ba.
kawai kallon Dr sagir take yana ta magana a ranta tace idan ba zasu barta ta tafi ba kuwa sai dai tayi ta zama anan Abdullah kuwa ko daga hannunsa baya iyayi.
duk wani halin da tashiga a yanzu yariga ya gane shi.
yana ji tamkar ya karasa ya tausasa mata halin da tashiga da kansa.
Dr sagir ya lura dashi sai ya dan share sannan ya mike yace yana zuwa .

Yana fita Abdullah yatashi ya koma daf da ita" inda take ya zauna har sai da ta dan kalleshi jikinsa a dan sanyaye ya kirawo sunanta bata amsa ba.
yarigada ya saba da hakan Amman yasan tana ji yace Aisha lokuta da dama abubuwa suna samun mutun iri iri ya zamo yawanci duk inda ya juya bbu dadi har ya dinga tsammanin ko shi kadai ne ba'a so ...
Amman duk wannan ana gwadawa ne a gareka a ga yadda zaka dauki al'amarin kafin daga baya alkhari yasameka.
ka dinga ganin kmr kai ake so.
yayi shr yana dubanta kanta a sunkuye yace Aisha a da ina tunanin rabuwar da tashiga tsakaninmu mun shiga wani tashin hankali ne na rayuwa.
na rabuwar kusanci da mukayi Amman tun yanzu na gane cewa ni kadai na shiga halin tashin hankali Amman ni din ma ga shi Allah ya wanke min da alkharinsa da ban taba samu ba sai a tare dake .

Kiyi hakuri dan Allah Aisha komai ya wuce shi kansa danmu sai yafi alfahari idan ya bude ido ya ganmu tare dashi
sai yafi yin farinciki .
har alokaci bata dago kanta ba hawayen takaici ne duk ya dameta a idanunta .
kawai Abdullah zai sake dawowa ya yaudareta tana zaman zamanta lafiya ahankali yasake kiran sunanta ta dago suka hada Ido ganin da yayi zatayi kuka yasa ya dada rikicewa ya kara matsota sosai kmr zai cire mata abinda ke damunta .
Matar Dr ta fito tana ganinsu haka da sauri ta juya ta koma .
su duka biyun suka bita da kallo har aka kira sallah magariba har sannan bata ce komai ba Abdullah kadai ke maganarsa ita taji ta hakura da abinda a kamata ya wuce har a cikin zuciyarta .
Amman ita kam bata kara yarda Abdullah ya Kuma yaudararta ta kuma komawa aurensa.
anan gidan sukayi sallar magrib har isha'i matar Dr sagir tayi saving dinsu abinci Amman shi Abdullah kasa ci yayi ganin har yanzu Aisha taki sakin ranta bare ita da tun lemun data dan kurba a tun dazu da suka zo da sister zahra.
har Dr sagir yana magana yace gaskiya Aisha abun naki zai zama da Kwara fa saboda bake kadai kike cin abinci ba idan baki ci ba na jikinki ba zai samu ba Abdullah ya kalli Dr sagir sannan ya juya kanta ya zuba mata ido yakoma kalar tausayi Dr sagir ya sake fita falon ya kara zama su biyu Abdullah yace Aisha tashi mu tafi na kai ki gidan inna.
Shr bata amsa ba sai daya sake dan matsota sosai yace kinga fa dare ya fara zamu takurasu .

Sai alokaci ta kalleshi itama tayi tunani haka tun farko ba dan zata takurasu ba ita ko akan kujera zata iya kwana. tunda dai tasan Abdullah ba zai barta ta fita ta je gida ba ..
da kansa ya nuna mata yes haka ne.
yace kinga damu zauna muna shiga hakkin wani gara mu tafi maganar ta dan shigeta dan haka ahankali ta mike.
ganin ta mike ne ahankali ya dan sauke numfashi sannan shima yamike yana kiran Dr sagir tare suka fito da matarsa da kyar Aisha ta kakaro murmushi karfin hali tayi mata sallama sannan tayi gaba abinta Abdullah kuwa suka jiro tare da Dr sagir hannunsu rike da juna suna magana da

Please Login or Register in order to submit comment