Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace wai ko yajin bakya ji zafin sa .
sai karawa kike yi idan yajin yayi yawa bazaki gane dadin abu ba.

Ta dan kalleshi kadan tace kaine dai baka san dadin ba.
ai duka wani dadin duniya anan yakare.

usman yayi dariya sosai har inna ta karaso tana tambayarsa ita ma tashiga dariya tace kaga duk randa wannan baturen zai zo ganin dansa sai yayo min buhun barkono .
Aisha ta bata fuska inna tayi shigewarta daki tana kara cigaba da dariya.

usman ya tashi ya dibo mata ruwa a randa yazo ajiye mata kusa da kwano "usman ya dubeta sosai ahankali yashiga gaya mata irin borin haukan da Dr salim ya dinga yi musu saboda ta tahowarta .
saboda balain naci daya dinga yi musu a waje yana aike har sai da yaya Ali yace wa baba wlh idan bai tafi ba kuma bai daina zuwa ba .
zaiyi masa duka ko yasa ayi masa usman ya dan yi dariya yace kinsan kuma zai aikata bare yanzu da yake soja ..

Usman yayi dan shiru ko zata ce wani abu Amman Shir batayi magana ba.
sannan ya dan sake yin murmushi kadan yace Amman wlh yaya Aisha ni nafi sonki da yaya Abdullah dan kunfi dacewa da juna .
haka koda mukayi zance da innnarmu tace tafi sonki da Abdullah koba komai danta ne .
kuma tasan bashi da wani laifi akan rabuwarku .
dan tasan sharrin maminsa.
wai wata killa tsanar da tamata ne.
ta shafeki in gaya miki innarmu har da kuka tayi a jiya daza Muzo .

Sai alokaci Aisha ta dago da sauri ta kalleshi har ta katseshi shima yana kallonta duk abinda daya zata ko itama daman tafinson haka ne.
sai dai ,tana gama kallonsa yaji tace innarmu mantawa tayi tace zata dakamin yajin tafarnuwa kuzomin dashi .

Usman yasanta sarai kadan daga cikin halinta kawai yayi murmushi yace me yiwa ko sai zata zo .

Idan ka kalli rayuwarta a ka'oje baza ka taba tsammanin ta taba zuwa ko da airport ba .
bare taga jirgin da zai fita daita waje .

Yadda ta karbi rayuwar kauye itace zata sanyaka ka fadi haka abinda ta kaddara daman rayuwa tana iya canzawa na wani lokacin"
abinka ga mai ciki , kuma tana samun abinda take so nan da nan ta murje kyau.
kyaunta ya fara dawowa har ma yaso yafi na da ....


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AISHA A BAGUDO



Inna lillahi wainna ilaihi rajiun😭😭😭😭😭😭😭
Ina Mika ta'aziyyar gaisuwata ga yar'uwa faiza anfa marubuciyar danfashi ,akaro na biyu Allah ya jikan gwaggonki yamata rahma yasa ta huta, ya raya abinda tabari . Ku kuma Allah yabaku hakurin rashi .
Allah yasa idan tamu tazo ,yasa mu cika da kyau da imani Ameen πŸ™πŸΌπŸ™πŸΌ Allah sarki faiza 😭😭😭😭😭😭😭


Page 60



Faiza tace kai mama mutane nan fa sun wuce duk yadda muke zato fa.
ta koina abin arziki a jike yake .
ba ga mami ba ba ga uban ba hatta shi kansa Abdullah din mai tsansar abun duniya ne .

Mama hafsa Tace ke sai yanzu kika san haka kennan .
ai shiyasa na tsarawa uwar duk yadda zasu bada sadakin kmr dai yadda suka bada na waccan Yar masu tatsan nono gidaje shida da motoci kinga ai an nininka kennan .

Faiza tace kai mama kina wuta ina binki da fetir wlh ta Mika uwar hannu suka kashe. sannan tace ke in banda bana so abin ya wuce wannan lokacin ai da watar kasar za'a kaimu mu zabo kayan gado kinsan su masu fita ne .
Sun fi sanin inda za'a samu na garari .
Faiza tace dakata mama bangane maganar ki ba .. ai a hakan ma dole ne kayan kitchen lefe da sauran kayan duk a waje za'a siyo su.
ai ba wani batun dan za'a yi biki wani a kurarren lokacin.
tunda dai ba'ariga an soma raba AV ba.
me zai faru abinda ance shi dady sai yayi kusan wata hudu kafin ya dawo.
ko ana sauran sati ne ya dawo aka daura ai dai an daura.
kuma komai kwakwa da nacin sa dole ya hakura .
Mama hafsa Tace haka ne fa .
kinibabbe banza kawai , ai ni nafi son kisamu kmr wata daya da aure Abdullah akanki kafin yadawo.
sannan nasan mun dan fara tatsan abinda muka tatsa kafin yazo ya hanamu rawar gaban hantsi.
akwai abubuwa na musamman dana zan tsumaki dasu.
saboda Abdullah din dan haka ana daurawa ,zaki lillike masa ajikinsa sai yadda kikayi dashi .
idan ya dandana zumarki kuwa.
zai mannemiki har sai kindinga korarsa.

Faiza ta saki shewa dan murna hade girgiza nonuwa irin dai yadda manyan yan iska keyi .
tace A'a haba dai mama bawani korarsa da zanyi ai sai dai na kwashi da....... can Kuma tayi shiru jikin faiza yayi mugun tsanyi tuno halin Abdullah datayi.
mama hafsa Tace karki taba damuwa naga kin wani canza kisha sha'aniki diyata .
idai Abdullah ne muna nan zaki zo har nan kibani labari komai.
kema ai yanzu kinzama babbar yarinya .
Faiza ta mike tana dariya har zata fita kuma ta dawo tace uhm mama kigayawa mami fa ni nafi son mu zauna acikin gidan nan a part din Abdullah bazan zauna a wani guri ba


Mama hafsa ta kalleta a bazance tace meyasa ke tsamiyace .
ga gida can ke kadai bbu wani dan sa idon da zai dami rayuwarki da takuran yan'uwan miji.
komai kuma yayi a gidan sai abinda kike so zaki canza .

Faiza ta dan sake rage murya sosai tace uhmmmm ke Abdullah din nan fa da kike Gani bai da kyau fa .
ni na fi son ko meza'ayi Gani ga uwarsa .
mai sashi yayi mai hana shi ya hanu .
yanzu kina ganin duk abinda aka sha wahalar yi a kansa idan ranar da aka kaini ma yaki zuwa fa gidan fa! .
kinga tun anan ma wani abun zai karye idan kuma anan ne fa.
nasan karyashi tasha karya dole mu kwana tare .

Mama hafsa Tace kuma fa haka ne .
faiza tace ke dai kice mata ana zamu zauna kawai naga part din nasa ma wata aljannar duniya ce .

Mama tace to ni ina zan wani san hakan tunda bashiga na taba yi ba. Kinga haka ma za'a yi bari kiga na koma gunta .


Kwana takwas kennan dayin maganar a maimakon ranakun bikin faiza .
mama hafsa da faiza da kanwar faiza rahma suka Lula waje hado kayan amarya mami ta bude musu account dinta sosai suyi yadda suke so .

Abdullah Yayi shr kansa a sunkuye byn ya gama jin abinda mami ta fada cewar ya rubuta takardun gidaje gudu shida da motoci hawa guda shida a matsayin sadakin faiza.
kansa har ciwo ya farayi saboda girman al'amarin Amman ko dagowa bai yi ba yace shikenan mami za'a yi yadda kike so.

Fita zai yi Amman ya kasa dole ya dawo part dinsa ya kwanta.
yayi shr kullum abin ma gaba yake yi bbu wani sauki acikin al'amarin.
sai randa Allah ya kawo .


Kwanaki sun shude da yawa komai ya gyaru a ma'aikata.
Amman banda bangaren rayuwarsa tunda ya rabu da Aisha bai kuma ganin wani mai kamanin ta ba sai a hoto.
Wani lokacin har wani dan shawagi yake yi da daddare akan hanyoyin gidansu .
ko gidan aunty Maryam Amman cikin ikon Allah kmr anyi ruwa an dauke ko a yan'uwanta bai taba cin karo da kowa ba .
sau daya ne ma ya taba hango umar akan machine traffic ya tsayar dasu.
kuma ba a hannun dayake bane kafin yayi wani yunkuri tuni sun wuce.
yayi ta hange hange bai ko ga alamunsu ba.
Amman ranar ko ba komai ya dan ji dadi har yayi tayiwa masu gadi da ma'akata kyautar kudi balle salis da a rana ya warke .

Duk yadda mami tace haka yayi .
komai kmr yadda tace haka yayi .
Da yayi niyyar sanar da dady sai ya ga kmr idan ya fada tamkar ya kai karar mami ne .
dan haka kawai ya kyale tunda dai abun ba gagara zaiyi ba .
haka ya bude account ya fidda kudi masu dunbin yawa .
kuma yadda ya siya komai na sadakin faiza haka ya kwashi makudan kudin ya zuba a account din Aisha.
wanda ya bude mata hatta pin din ATM da card suna hannuta. yabata tun ana gobe zasu rabu bai dai yi mata bayani bane.
haka Kuma daman yawanci yana tura mata kudade a cikin salary dinsa.
dan shi tunaninsa tana can tana bukata dasu .

Ya tuna wata aunty dinsa a Egypt sanda suka je ta kalleshi .
cikin yarensu tace Abdullah matarka na da kyau kuma tana da shiga rai .
ko zaman mitina biyar kuka yi daita kyaunta da yanayinta mai tsayawa mutun arai ne .

Ya dafe kanshi da duka hannuwansa yana jin kmr ya saka kuka ballanantana shi da ya zauna tare daita ya kusanceta yasan dadinta.
sannan wai Dr sagir zai ce wai ya rage tunaninta saboda ya rame da yawa ai bbu ranar daina tunaninta sai ranar da aka dawo masa da abarsa .


Satin su faiza biyu mama hafsa azalzala mata akan su dawo.
saboda shirye shiryen biki.
Mama hafsa tayi tayi daita .
Amman ina ita kuma faiza ta kafe ita lallai sai tagama abinda ya kawota .
dan haka dole tasa mama ta barta .
ta fara yin gaba a saboda ta dan yan shirye shirye cikin gidan kuma a fara rabon AV faiza Kuma tayi alkwarin dawowa zuwa wani sati to ba yadda mama hafsa ta iya haka ta yarda .
a acewarta dai dama ce tasamu shi yasa ita faizar zata tsaya din .

Kai tsaye tsaye ta sokoto mama hafsa ta sauka ta fara raba goro sannan taje Kano kwananta daya ta dawo.
tasa mami ta aika da duk wasu kayan aure can sokoto haka kuwa akayi hatta makota sai da mama tasa akayi musu fenti .
saboda yan daurin auren idan an zo aga layin da gaske .
takama iri iri take diyarta zata aure mai kudin wuce sa'a.
tace wanda duk taga dama shi za ta taka.
ta kwana lfy saboda naira ta zauna alokaci kuma da gaske ta zauna din


Faiza ta dawo kasar Amman sai da sukayi sati biyar da kwanaki ai kuwa tasha tsinuwa da zagi iri iri agun mama hafsa.
dan ko goro ma da aka rarrabawa mutane .
Sai da aka tambayar faiza .
Ita ko aka dinga cewar amarya ana can kasar waje yo siyayya aure.
Faiza ta kara sati uku akan yadda sukayi da mama hafsa saboda tana son a gyara mata jiki.
dan haka hatta inji daye fata da gyaran jiki sai da tashiga.
kuma kai tsaye gidan mami ta zarce da suka dawo batayo sokoto ba.
a saboda bata son mama hafsa ta dibar mata wasu kaya data siyo.
ko tace a bawa ragowar kanneta.


Gidan mami gabadaya ya rikice a lokacin .
takai ta kawo ko kwana Abdullah baya yi a gidan saboda mami ta karbi
Key part dinsa.
wai nan faiza zata zauna daman kuma akwai extra rooms wanda dady yasa aka Gina tun aurensa na farko .
duk sukayi parking din wasu kaya gefe aka shiga shiryawa faiza dakinta ..
dan haka shi kansa Abdullah ya tattara abubuwansa masu mahimmanci ya kulle bed room dinsa.
ya koma kwana a wani part din.
Dan bai iya zuwa gidansu na aurensa da Aisha .
saboda shigarsa yafi komai tuna masa da ita.
da komai nata dan hatta kayan data sa a ranar da zasu rabu suna a gefe gado cikin basket ya gansu.
ranar da yaje gidan kwaso wasu mahimman files hatta kayan da tayowa yan'uwanta tsaraba suna cikin akwatina duk suna nan yadda suke.
ranar daya shiga kasa fitowa lfy yayi dan har zazzabi yaji a jikinsa kafin ya baro gidan .


Iyakar rikicewa kuwa gidan alhj ishaq yayi.
dan hatta masu gadin gidan sun fahimci haka kowa surutun yake.
ita dai mami sai abinda aka tsara shi takeyi .

Shi kuwa uban gayya duk abinda mami tace shi zai yi to haka yakeyi. minal kuwa duk fushi take da kowa a gidan atun rabuwar Aisha da dan'uwanta .
hatta mami bata kulata sosai sai ya zama dole sai ta yini a part dinsu bata sauko ba sai idan mami ta aika tazo idan tazo ma bbu wani sakin fuska dan ko gaida mm hafsa batayi .

Teema kuwa da ita tafi kowa sanin halin mami ita ke jin jiki sosai dan ganin yadda mami ta koma yanzu yasa kullum sai tayi kuka a daki .
tana lura daita da duk yanayin da take ciki yanzu babban abinda yafi frigitata mami sai tayi fiyye da kwana uku batayi sallah ba .
wannan abu shi yafi komai tada mata hankali dan haka kullum sai tayi ta yiwa mami addu'a Allah ya dawo daita daidai .

Dan haka ya zama hatta ma'aikatan gida idan kaga an dan taru to kus kus din abinda ke faruwa a gidan sukeyi

Akasa bikin faiza sati biyu masu zuwa haka Abdullah ya shedawa dady ta waya .
dady yace bbu komai shi dai yayi ta addu'a Allah yasa hakan yazama alkhari .


Kwana biyar ya rage daurin auren Abdullah ya shiga part din mami ya danka mata files din gidajen da motoci kmr yadda tace masa ta karba ta Gani.
sannan ta mikawa mama hafsa domin a ranar ta doka samako tun safe a gidan.
a dalilin faiza taje sokoto jiya ayayinda Mama hafsa bata nan yasa ta kwaso akwatinan lefe ta kawo part dinta Abdullah inda zata zauna ta kulle.
tun ajiya mama hafsa ke bala'i bbu abinda Faiza ta bari ko irin dan mai da zasu rabawa mutane.
bare dan abunda ake cirewa na uwa.
mirsisi faiza tayi tace komai na kasar waje ne ba irin na rabo bane zata siya na rabon a bawa mutane .

To mm hafsa ta nike file din gidaje shida cif da motoci shida sai ta kuma ta canza shawara, dan wani tunani ne yazo mata hakan yana nufin Abdullah baza shi daurin auren ba kennan.
gashi tayi niyar ana gama daurin auren zata sa'a kirawoshi idan ya shigo .
da akwai wani turare da boka yabata yace ta turarawa Abdullah daya shaki hayakin take zai ji komai ya canza masa hatta uwar da ta haifi shi bai kuma ganin darajata kmr ita ..
shiyasa
Ita kadai tasan da wannan dan ko faizar bata bari tasani ba.
dan haka sai tasa mami ta sake kiransa a waya ya shigo ta Mika masa files din cewa ya ajiye a gunsa ranar daurin auren ya taho dasu.
bbu yadda zai yi dole tasa ya karba dan shima har cikin zuciyarsa bai yi niyyar zuwa daurin auren ba .
shi yasa yayi hakan yadda yayi mama hafsa
Ta kara gane dabarar ta tayi daidai .
dan abunda ta zarga haka ne.
bashi da niyar zuwa da kuwa ya cuceta yasata asara mai tarin yawa .
dan bazan yaro mai dan karan daurin kai wannan har ya zarce uban nasa ta fadi haka akasan ranta .

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AISHA A BAGUDO



Nagode da yadda kuke matukar sona da kaunar novel din nan ,Kuma kuna Raina domin kuwa KAUNACE SILA komai dan kuna cikin kololuwar zuciyar Bagudo.
kuna ina πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£yan ZUCIYAR MASOYI FANS ku matso kusa this page belongs to you ol na bakushi free of charge kuyi duk yadda kuke so dashi. na kune, haka ma Bagudo takuce har abada ana mugun tare irin sosai din nan 🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝



Page 61-62


Abdullah yayi shr ya jima zaune a bedroom dinsa ya gane mama hafsa duk yadda yaso ya kauce mata sai ta kure shi.
ta wani koma kmr itace ta haife shi .
ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa Amman nasan yadda zan bullo musu ya fada aransa.
ga dukkanin alamun rashin Aisha yana nema ya zama gaske .
shi Kuma ya rike alkwarin byn Aisha bbu wata ya maccen da yake ganin zai kuma kusanta .
dan haka ya gano wata tafiya a gabansa a tun safe .
ya samu sako ajikin system dinsa cewar company da suke son budewa a South Korea wanda har suka kirasu interview kwanakin baya Denmark.
suna bukatar wani wakili daya wanda zai je ya zauna a can har tsawon watanni bakwai zuwa tara ko shekara har sai komai akammala .


Dan haka bbu wani bata lokacin ko jin wani abu kawai Abdullah ya wakilta kansa .
dan haka ya tura sunansa da komai nasa akan shi zai yi tafiyar .
byn dawowar dady kennan" a yadda yake ganin al'amarin sai wani ikon Allah yasake rayuwa da Aisha.
jikinsa har ya fara hakura da rashin ta.
dan haka ko anyi aurensa da faiza bazai bari su san da zancen tafiyar ba sai dai su shafa Suji shr .
kuma muddin yashi tafiya .
Ko duk duniya zata hade ba zai tafi shi kadai ba .
kafarsa kafar Aisharsa sawa zaiyi a sato masa ita kawai .
Ba zai yarda yayi wani rayuwar aure da wata byn Aisha ba .
dan haka yana tafiya zai manta da wani auren faiza dake kansa.
in tagaji da jira tasan yadda zatayi da kanta .
in baya ga iyaye ma da idan yayi gaba.
ya tafi kennan sai dai idan yaso lekowa.


Tunanisa ya dawo kan kujerar sa ta office idan yayi tafiyar nan .
tunaninsa wanda zai riketa da amana yayi shr yasan dady zai iya hadawa har nasa kujerar.
Amman yasan ayyuka zasu yi masa yawa sosai Dr sagir yake dubawa a yanzu shima yana da aikinsa.
Amman yana da kyau yayi wa Dr sagir wani abu mai mahimmanci a rayuwa.
saboda Allah shi ya hada shi Aisha Amman ta dalilinsa .


Faiza ta kankane komai nata da duk wani abu da akayi oder sa ta juye shi a part din Abdullah .
kayan gado dana kitchen iyakar tsaruwa komai part din ya tsaru yadda ake so matuka gaske.
cikin abinda yabawa mutane mamaki gabadaya ta tare a part din tun ba a daura auren ba.
tun dawowarta daga kasar waje sau biyu ta taka sokoto.
shima direba ne yakaita kuma a ranar ta juyo hatta kawanyenta na can daidaiku ta gayyata .
dan haka duk bikin da'ake a sokoto bbu amarya suke gudanar da komai.
amarya tana can gidan mijin nata.
dan Abdullah yabar part dinsa acan take kwana mutane kuwa suka samu abin fadi sai surutu ake ..

Wata yayar baban faiza ce tace kai jama'a ai sai a zage mu koma ana kan zaginmu .
ace amarya ana biki a gidan ubanta ita kuma tana ca.
har takai kanta tana can gidan iyayen miji ai ba zai yiwu ba wlh.
dan haka sauran kwana biyu a daura auren tun asuba suka baro sokoto zuwa kebbi tace dole su tafi da faiza a kalla dai ta bari ko daura auren ne ayi tana can.
idan yaso ta biyo yan daurin auren.
da kyar da sudin goshi dai aka lallaba faiza ta biyosu duk da tayi ta bata musu lokacin "tana zumbire zumbire don da basu sameta ba a gidan taji labari zuwansu.
bazata dawo ba ,sai dai suka raci zaman su .
, su koma byn ta hada komai nata ta kulle part din Abdullah ta bawa teema ajiyar keys din saboda kada ta tafi dasu can a faki idanunta a dauka a dawo a taba mata wani abu .
sai byn sallah azahar sannan suka bar kebbi daga ita sai kaya kala biyar


Tun. Karfe uku ,na ranar har biyar Abdullah yana tare da Dr sagir .
Dr sagir ya kalleshi yace haba friend har yanzu baka saduda ba kennan jibi ne za'a daura yakamata ace ka dan ajiye wani abu .
tunda dai shi aure yarigada ya zama dole kawai ka saki jikinka , a dan yi wani abu kada ma ka sake ka fito da damuwarka a gane .
,tunda duk aure sunansa aure .

Abdullah ya kalleshi ya girgiza kai yace wani aure sunan sa ne kawai aure Amman ba aure bane , yanzu zaka hadashi da auren Aisha koda nake cikin damuwa a lokacin .
Amman wlh Allah Allah nake a mallakamin ita na ganta a kusa dani.
wannan kuwa baka ji yadda nake jin zuciyata ba kmr zata buga haka nake ji.
sannan kace na daina damuwa ina... Doctor nayi asara fa sosai dana rasa Aisha ,.
ina sonta ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan gaya maka ba .
ina jinta a cikin naman jikina , .
doctor ban san haka so yake ba sai yanzu kullum na tuna yaya zataji lokacin da aka bata takardar sakina ..
sai naji wani daci ya tsayamin a makogaro. Sai danayi kwana uku bana jin test din komai Idan naci.
why why da zan dauki aurenta dana wata daidai ai kai ma kasan fada kawai kayi.
Dr Aisha yarinya ce bata san komai ba na rayuwar duniya ,baya ga zama gaban innarta .
,sai da Allah ya hadamu ni koyawa Aisha koma ciki harda yadda zata soni .
baka ga yadda nayi rayuwa daita ba komai a nutse take yinsa .
Ta yaya zan iya manta ta haka .
Abdullah ya runtse idanunshi sosai.
hakan ne yasa Dr sagir yaji kwalla ta yakawo a idonsa .
nan da nan ya wayance dan kada Abdullah ya Ganshi.
Shi kuwa Abdullah samma bai ma lura dashi ba.
yace Amman yaya zanyi doctor dole ne ma na hakura daita .
gobe ko jibi iyanzu an daura aure na da wata ko daga baya Aisha ta dawo min cewa za'a yi duk abinda nayi daita dole ne nayi da faiza .
ni Kuma wlh bazan taba iya rayuwar aure da wata ba bayan Aisha .
sai dai wani ikon Allah shine naga da haka gara nasawa Raina hakuri shi zai fi min sauki.
tunda safe yau dana tashi jikina yake bani komai ya kusan zuwa Karshe .
na sawa Raina ba zan iya yi komai da wata macce ba .
to Aisha ma na hakura zanyi rayuwata a haka bbu ita ballanantana wannan .
kawai ba komai ba ko.....
Wayarsa ce ta katse shi tana kida .
Sai da tayi kara sau biyu yana ji .
sai daga baya Abdullah yasa hannu ya dauka ya kara a kunne.
daga can daya bangaren dady na saukowa daga matattakalar jirgi yace Abdullah kana ina ne?
Jin muryar dady tasa Abdullah ya dan natsu yace ina nan gida .
dady yace to ai mun iso yanzu ko kai ko wani a samu mai zuwa dauko ni yanzu .



Bye bye faizaπŸ‘‹πŸ»πŸ‘‹πŸ»πŸ‘‹πŸ»πŸ‘‹πŸ»πŸ‘‹πŸ»


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AISHA A BAGUDO




Page 63-64



Da sauri Abdullah ya mike zumbur jikinsa har rawa yake yana kiran dady....
dady kuwa tuni ya kashe wayar da gudu Abdullah ya fito Dr sagir ma ya biyo shi yana tambayar sa abinda ke faruwa.

A airport ma haka yarinka yi gudu gudu sauri sauri suna yin arba da dadinsa kuwa ya kankame shi sosai .
tun sanda wannan tashin hankali ya faru sai yanzu Abdullah yaji hawaye sannan Dr sagir ya karaso shima da murnarsa ya risina yana gaisar da dady .
da kyar dady ya bambare Abdullah daga jikinsa saboda hawayen da yake bayason mutane su Gani.


Dady yayi mugun kaduwa da irin ramar da yaga Abdullah yayi .
koma yace ya

Please Login or Register in order to submit comment