Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kyaleta karkasanarda ita sai zuwa wani lokacin zan sanar da ita . Abdullah ya amsa sannan dady ya sallmi Abdullah ya tafi,yayin da yabi dan nasa da kallo , yaji matukar tausayinsa duk jarumta irin ta Abdullah gashi lokacin daya soyayya na neman rikita shi wanda shi kansa Abdullah bai gane ta ba "yana matukar jin kaunar yaronsa aransa domin yakasance mai tsananin biyayya ga uwa da uba, gashi da taren nasarori wani lokacin yakan zabi Abdullah din yayi abu akan shi yayi cikin yarda Allah Kuma sai yayi nasara" shi yasa ya damu da lamarin Abdullah din.

Wani abun mamaki duk wannan dadewar da Abdullah yayi a part din dady faiza na makale tana jiran fitowarsa dan haka yana shiga part dinsa ta rufa masa baya frig ya bude ya dauki lemon kwali ya bude ya daga kai zai Sha ya hango ta tana kokari neman wajen zama yayi kmr bai ganta ba yacigaba da abunda yakeyi har yagama yayi jifa da kwalin ya juya yana shirin shigewa cikin bedroom tayi gyaran murya tace Abdullah wajenka fa naxo kana kallona.abdullah ya juyo ya tsaya mata wani matsiyacin kallo, tasake cewa please ka zauna magana naxo nayi maka wani irin kallo yasake mata mai kama da harara yana nazarinta a karshe ya numfasa hade cizan lip's dinshi sannan yasamu kujera nesa da ita sosai ya zauna ,bbu kunya balle tsoron Allah faiza ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa dashi duk dai bai dago ya dubeta ba ,yajingaina da kujera yayin da kansa ke kallon sama cikin salo murya na Yan duniya takira sunanshi Ab..du...llahi..Yaya kake son inyi da rayuwata da soyayyar ka da takamani cikin farar daya , tun zuwana gidan nike binka Amman kai sam bana gabanka kasan dai iyayenmu sun rigada sun gama magana , Kuma mami ta tabbatar min da bakada wata mata nan duniya sai ni" ko kana tunanin tsallalakewa maganar mahaifiyarka ne ,ka auri..... Abdullah ya buga mata wata razananniyar sawa yana mai watsa mata mugun kallo how dare you talk 2 me like dat ,yana mai tsareta da manyan idanunshi masu firgita mutun bata ma kula da duk abunda yake ba sai sake birgeta da yayi "da kallon da ta masa na very serious man kiyi maganar da takawo ki kawai Amman Kar ki kuskura kisa mami a maganar ki.ok naji bazan sake ba Amman ina son kasani zan iya yin komai a kanka muddin burina zai cika Abdullah ya dakatar da ita dan Allah yimin shiru malama ke wawiya ina ce indai akai nane a she zaki mutu burin naki bai cika ba
Ta zuba masa Ido meyasa zakayi haka nifa ina so ka saboda zan iya sallama maka komai da kake bukata kaajiye komai muyi soyayyarmu Abdullah ya dinga Yi mata kallon mara hankali mike tsaye yayi itama ta Mike ta rike hannushi mamaki yasa yabi hannun nata da kallo da ta rikeshi ,yasa ta dauka ko yafara kamuwa ne ", gabadaya sai ji yayi ta fada jikinsa ta rungume shi tare da fadin wallahi Abdullah bbu wanda zai San abunda ya yafaru da sauri abdulla ya hankadeta wanda har sai da ta buge da kujera huce yake yana kallonta ta Mike da Kyar tana kallonsa hade da shafa kugunta "sake motso sa tayi am very sorry....ai bata rufe bakinta taji saukar lafiyayen mari a kicin ta wanda ya gigita ta maganarta ta tsaya cak na 2 second sannan ta make kmr ba ita ba ,ta sake kokarin yin magana yasake dauke da wani agigice take binsa da kallo da kwalakwalan idanunta kmr mayya" if you do any stupid I will del with u now get out from my site "

Tayi murmushin karfin hali ok irin rayuwar da zamuyi kennan idan muyi aure ina son haka muddin zamu kasance matsayin miji da mata I said get out in my site "yasake fada cikin tsawa tsawa .
Tasake yin murmushi sannan ta juya tana juya masa mazaunai ta fice Abdullah yaja tsaki stupid girl kawai "ya fada sannan yabi bayanta ya sanyawa kofar key ya shige ciki ya duba agogon sa shadaya har ta wuce ya raya aransa duk inda zuciyarsa take tana can jikin Inna ,ta dade da yin bacci ba irin faiza ba, tsaki ya ja ya shige toilet ya sakarwa kansa shower ya gama ya dauro alwala don yanzu babban burinsa ya fuskanci ubangiji da matsalar sa ko zai samu saukin damuwar sa".


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 9


Part uku ne acikin gidan na dady ne daga dan gaba sai na Abdullah sannan na mami daga can barin ita da su teema a hade sai dai su teema suna sama yayin da mami ke kasa sai Kuma ragowar BQ na masu aiki gidan ,gida ne da aka shimfida shi tamkar baa son ciwon naira ba"dan tun daga dakunan masu gadi gidan "farkon shigowa zaka gane masu gadin suna hutawa da jin dadi parts din Mami kawai aka daura sama na su teema "dan haka in dai kana saman balcony zaka iya hange kowane part na cikin gidan da duk mai shigowa tundaga get saboda haka duk wani shige da fitan Abdullah akan idon faiza yake tun zuwan ta gidan ta gama karantar yadda Abdullah ke da matsayi acikin gida .kmr da wasa taji teema na cewa ai mami tace tayi wa dady maganar aurenku da bros shine dalilin kafa idanunta akan al'amarin har zuwa yau da taga shigar Abdullah part din dady tsammaninta maganar sukayi shine dalilin dayasa ta binsa part dinsa .


Kissa da iya kwantar da kai idan mutun yanason abu, wannan sai dai mutun yayi cos wajen su faiza tamkar zata yiwa mami sujjada wajen biyayya hakan ya dada birge mami har yasa tasaki jikita sosai da yarinyar yawan ci duk wata cima ta Abdullah faiza tasani Kuma tare da ita ake shirya komai mami ta bayar da umarnin a dinga koya mata "mami da kanta takira Abdullah ta dada tabbatar masa da maganar auren su da faiza bbu fashi iya tunanin mami aure be bai damu Abdullah ba shi yasa baya wani damuwa da zance faiza" Amman tasan komai dai abin sa idan an daura masa ita bazai ki zama da ita ba .

Faiza ta tsinci kanta da dana sanin fitar da maitar ta fili akan Abdullah dan haka tashirya masa text na ban hakuri gashi sati daya sukayi da mama hafsa sai gashi har ta zarta sati 2 ita kanta muddin zata ci gaba da zama a gidan tana ganin Abdullah ta gwamace ta rasa karatunta da duk wani abu mai mahimmanci na rayuwar ta" Amman ta canza shawara dole ta tafi a Yan kwanankin nan ta koma tasawa mama hafsa kuka koma yaya zaayi ita dai tana son ta mallaki Abdullah dan tagane ita kadai ke haukarta .

Tun dare hadari ke daure a garin yayin da Werther garin gabadaya tacanza sakomakon iskar dake kadawa Amman ba'ayi ruwa ba sai wayewar garin lahadi aka sharara ruwa musamman dayake ranar hutu ce sai wajen 12 tukun ruwan ya dauke gari yayi tsanyi ni'ima yasauka a koina, mami tasanar wa Abdullah tafiyar faiza gobe Monday tana kuma da bukatar siyyayar wasu abubuwa dan haka da Abdullah take son suje tare ya tayata zabe abunda take so, bbu wani zance musu a maganar mami ,Amman ya gwamace ta rufe shi da duka ko ta hada shi da wani aikin wahalar akan wannan fitar . Sai dai yayi kokarin dane bacin ranshi ya amsa mata, karfe hudu daidai fitar ta kama yayiwa amina waya tashirya su fita tare ko kadan ba haka faiza taso ba taso abarta daga ita sai shi a mota, sai da suka shiga mota ita da amina sannan ya fito daga part dinsa da waya a kunne yana magana .faiza ta zuba masa Ido sosai ita dai kamar ita kadai take ganin kullun gari yawaye sai yakara kyau da kwarjini fiyye da ko yaushe Yar rashin kibar da bai daita, yasa kowace shiga yayi take masa kyau " sanye yake cikin kananan kaya masu colour ja da baki sai farin glass daya manna a idonsa yakaraso jikin motar tare cire wayar sannan ya kashe salis ne ya bude masa dayar mota yashiga ya rufe yashiga ya tuka yayinda musa ya tuka su faiza suka biyo bayan su gabadaya ranta ya gama baci ita da taso Abdullah din ne ya tuka su daga ita sai shi "sai gashi kusan mutun hudu akan uzirinta daman ita sam jininta bai hadu dana salis ba saboda yadda taga yana kaf-kaf da Abdullah din duk inda yasa kafa yana binsa "shima Abdullah yaso yadda ni'imar garin tayi masa dade yakasance cikin nishadi da tarin farinciki Amman duk ransa a bace yake tun fitowarsa daya lura da mayataccen kallon da faiza ke masa Abdullah daga cikin mota ya zubawa waje Ido ai ko idanunshi yayi arba da wasu dattijai guda biyu suka shige su yace salis stop the car .

Salis yayi gaba ya daidaita yayi parking ganin su tsaya ne yasa musa tsayawa Abdullah ya murda kofar ya fito ya karasa inda suke yana cewa musa suyi gaba kafin su karaso salis yakaraso da wata jaka ya mikawa faiza ya koma mota yayin da Abdullah ya dubi dattijain, har suka kure faiza na waigensa tana mamaki musamman da taga bai koma mota ba yacigaba da tafiya . Abdullah ya riske mlm abu da abokinsa bbu wani abu da ya Dame su ,suna tafe suna hira kamar daga sama mlm abu yaga Abdullah yakasa boye mamakinsa yana dariya Abdullah shima murmushin kawai yake ya rusuna ya gaishe su sunan tsaye har salis yakaraso da mota da hanzari shima ya fito har kasa ya gaishe su Abdullah ya karbi kayan hannun mlm abu ya bude musu mota yace Bismillah.mlm abu yace ai munzo gida ma Abdullah yayi murmushin yace kuyi hakuri baba ku shiga mukarasa daku .

A mota hira sosai tsakanin su har sanda aka sauke mlm dauda yayi godiya mlm abu yayi su sauke shi shima anan" suka ki har gida suka kai shi ,salis yayi parking a gefen titi sannan ya dauki ledar baban yayi gaba yayin da Abdullah da mlm abu suka Tako ahankali suna hira har zuwa kofar gida,mlm abu yace kadakata a kawo maka taka tsarabar nima ya'uri mukaje tun jiya . Abdullah yayi murmushin yana girgiza kai ni na gode baba.

Aisha kuwa tun azahar taje gidan aunty Maryam ta karbo sako saboda gobe zasu tafi ka'oje aunty Maryam tabata kayan su saifu tace abawa kannen hadiza makotansu dan haka tana isowa kawai tashiga tabawa babarsu hadiza bata wani bata lokacin ba ta fito har tazo soro hadiza tabiyo ta ahankali tace yaya Aisha da daddare idan mamana tayi baccin nan nata zan dibo kayana in kawo miki da safe sai in zo kawai mutafi ko bata sani ba.bata tsaya jiran amsa ba ta ruga da gudu ta koma kan aikin da akasa ta"Aisha na dariya ta fito kawai idannuta suka sauka akan Abdullah shima yana dariya mlm abu yadage sai ya tsaya an bashi tsarabar sa.

ba idanunsu ba hatta zuciyoyinsu sai da suka Yi clashing suka neman tarwatsewa" duk sai ta dabarbarce saboda da bazatan da Abdullah din yamata yayin da shi kuma ya xuba mata idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa idan har ba dan kamamnin gidan ba ba zaka taba cewa daga gidan mlm abu ta fito ba , sanye take da saukakken less mai design din apply ajikinta tayi masa kyau matuka fiyye da yadda take a baya , gaisuwar usman ce tasanya ya dauke idonsa akanta ,ta sunkuyar da kanta yayin da takasa motsawa tana jin yadda numfashinta ke barazanar barin gangar jikinta , zuciyarta tasoma aikin nata wato motsa kunjin halitta da Allah yayi mata ta tsinci kanta cikin wani yanayi da ba San ko menene ba"usman yashiga ciki gida yayin da salis yayi murmushi shima ya juya ya koma gurin mota , Abdullah yabishi da Ido ,bbu wanda yace uffan a tsakanin su haka Kuma bbu mai niyayar barin dan'uwansa , usman ne yasake fitowa soro, yashige dakinsu yaya yusif sai gashi ya fito da tsofafun kujeru guda biyu ya ajiye musu cikin soron ya fita , Aisha tabishi da kallo zuciyarta ke beating dum... dum ...dum..ba karamin karfin hali tayi ba wajen yiwa Abdullah nuni da yashiga ya zauna ta hanyar nuna masa da hannunta , Abdullah mai niyyar da sun kawo baba zasu bi bayan su faiza" Amman bai San meyasa ba sai ganin sa yayi akan kujera ahankali itama ta karasa ta zauna , shiru yabiyo baya har zuwa na wani lokacin bbu wanda ya iyayi magana cikin su"kowane yana gudun yin abunda zai taba ran dan'uwansa ,balle ita in ta tuna da maganar babanta akanta game da Abdullah " a boye take sauke hadiyar zuciya kasa kasa tayi magana cikin sanye murya ,kalma daya ya fahimta Kuma ya gane gaishe shi take Yi yaji dadin haka matuka har cikin ransa zuciyarsa tarinka kai kawo a tsakanin kirjinsa da Kyar ya iya tattaro duk wani kuzarin dake jikinshi yace Aisha how you doing "a motsen bakinta ya gane ta amsa ,yadan saki face dinsa kadan yayi murmushin so dai daya ne a rayuwa duk ma wani abu da tamasa ganinta a yau yasa yaji tamkar ya zube agabanta ya roketa ta so shi dan Allah kada tasake jefa shi a irin halin da tasashi abaya ya zuba mata idanunshi ji yake kmr ya fizgota gareshi "duk ta takura da kallon da yake mata ya ta rasa yadda zatayi sai ta dago idanunta sai taga har yanzu ita yake kallo , a kallon da yake mata yagane tashiga wani yanayi gashi kmr tana son Yi magana ya kira sunanta ahankali Aisha what do u want say,?
Ta dago dara daran idanunta ta kalleshi cikin sanyi ..muryar na rawa tace kayi hakuri yace me akayi yana sake tsareta da idanunshi "murya kasa kasa tace abinda ya faru gabadaya ya gama kewayeta mata zuciya" dan bbu abunda takeji banda idanunshi dake yawo ajikinta wanda yasa har tasake dagowa ta kalleshi "tabashi tausayi Kuma ta birgeshi Kuma dada shiga ransa wani irin kallo yake mata shi kadai yasan yadda yake jinta a jinin jikinsa "yace wuce Aisha ke ma kiyi hakuri nashigo muku gida ba yadda tsari yace ba"yaci gaba da kallon yantsunta masu kusan kama da nashi wanda itama din su ta zubawa Ido "yace Aisha 21 days rabon da muga juna sai dai kin canzamin kin kara kyau .
Aisha ta dan sace kallonsa kadan yayin da ya sakar mata murmushin har dimple point din shi na lotsawa "
Har cikin ransa haka yagani yayin da ita Kuma taji haka a matsayi. Dadin baki ne kawai,a zuciyarsa yarinka karanto duk addu'a data zo masa game da samun natsuwa , Aisha ta sauke hadiyar zuciya ta dan sake kallon gefen da yake Abdullah ya gane tana son ta tafiya ne ya dan ciza lip's dinshi yana mai duba agogon dake daure a tsintsiyar hannushi yace bari in tafi sai zuwa gobe a nutse take magana tace ai gobe bana nan Abdullah yaji gabadaya ya rikice shi fa baya kaunar yaji zata fita ko yaganta awaje ya dube ta sosai yana mai kafeta da Ido zaki je ina kennan?
Tace zamuje ka'oje yasake maimaitawa ka'oje ....... Yasake cewa Kuma ke kadai zaki tafi tace da yaya Ali , Abdullah yayi shiru yana tunanin throughout gobe cikin busy yake a office bbu halin ya subuce ya kaita ya girgiza kai yace shikenan akwai maganar dazamuyi dole sa kin dawo kennan" Amman zan ga yaya Ali kafin na wuce "tayi shiru ta kalleshi daga baya ta gane me yake nufi ta Mike ahankali
Ta shige ciki yabita da kallo yana addu'a Allah yanrantsar da rabonsa atare da ita ,har sanda ta fito yana zaune tace yaya Ali bai nan"yayi shiru sannan ya Mike tsaye cikin sanyi jiki yace to Aisha sai kin dawo kennan.yadda yayi maganar cikin shagwaba da langwabar da kai tamkar yaro karami , kamar ba hakan yaso ba shi ya kusan bata dariya sai kawai tayi murmushi ta juya ta shige ,yaji tsanyi aransa yau duka sa'ar a gurin take ciki fara'a yasa meta yau ta dan sake dashi ",har tayi magana mai dan tsayi dashi gashi har da kyautar murmushin da yafi bukata atare da ita ya lumshe idanunshi bai ki ace a daura aurensu a daren yau ba saboda gudun kada ta Kuma rikice masa yau tazo masa da abubuwa da dayawa masu mahimmanci........







MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Page 10


Ita dai bata San waye ya kai su ka'oje ba, Amman ta gane type din motar da suka shiga limousine ce bbu abunda bbu na jin dadin rayuwar dan Adam a cikin motar daga ita sai yaya Ali sai direver haka Kuma da suka isa direver bai juya ba sai da mlm dahiru ya tsareshi yayi sallah yaci abinci sannan yabaro ka'oje .

Duk wata ayar Allah dake raunana ZUCIYAR dan Adam sai da mlm dahiru yasanya aka rubuta mata ita , inna hajo tasa ta a gaba ta shanye tsawon kwananki uku ranar alkhamis suka je har zariyar Kala kala sukaje Suka dubo iya har gidan gwaggo Laure suka je kwanan su biyu suka dawo ka'oje washegari tun safe Aisha ta shirya a tsammaninta da wuri zasu taho ,yaya Ali yace sai an sauko daga masallaci dan haka shigewa dakin inna hajo tayi kwanciyar ta,koda ta tashi tayi sallah komawa tayi "can cikin bacci taji inna hajo na tashinta "anyi baki daga kebbi duk da gurin a gyare yake Amman sai da inna hajo
Ta shiga sabon gyara mlm dahiru yashigo da sauri yace ya tura kasuwa a siyo musu kwaryar nono da kwan zabi ta bayar da kwano me kyau za'a diba a damo musu fura cikin rawar jiki Inna hajo ta Nemo kwanuka biyu sababbe ta Mika masa ,ta tura yaya Ali yayi maza ya karbo zabbi a gidan kaninsa yakai can gidan su innarsu a gyara yanzu ta fito da sababbin tabarmi a karkashin gado ta aika dasu waje ta shimfida daya anan tsakar gida .duk Aisha na kallonta ta Mike ta nufo inna tana tambayar ta ita ko sai hada wancan da wancan take ,sanye take cikin riga da wando na wani material na kasar India mai kalar orange abokiyar aikinsu aunty Maryam ce taba ta tsaraba yayi mata kadan shine ta bawa Aisha ta tura gashinta cikin farar hula , Amman saboda yawan gashin sai daya burtso ta baya da wanda yabi gefen fuskarta tananan tsaye taji murya mlm dahiru yana Bismillah.

Juyawar da zatayi idanunta suka sauka akanshi tare da wani suna shigowa kamshin turaren su tuni ya game gurin cikin shiga ta alfarma,"sanye Abdullah yake cikin farin voyal mai ratsin gidan sugar dinkin doguwar Riga zuwa gwiwa kallo daya zaka masa kaji yayi matukar birgeka , cikin sanyi jiki Aisha ta juya ta shige daki,abdullah da Dr sagir ne a zaune kan tabarma suna gaisawa da inna hajo tace ai bangane mijin nawa ba acikin ku,naga duk kun shawo min kwalliya Dr sagir yayi dariya ai kowa so yake ki zabe shi , sannan ya nuna Abdullah . Abdullah ya sunkuyar da kai "Inna hajo
Tace Af to kai me ya tsaya birge ka da wannan mai karamin bakinta koko muryar ta ne mai kama da ta gyare ce ta dauki hankali ka ,sukai dariya gabadaya tace Allah in kuma ma jar fatar ce kai ma ga ka nan da ita" Dr sagir yace kodai ya fasa da ita ne ya dawo gunki tace ashe dai kagane ".

suna zaune
akarinka shigowa da kayayyakin tun daga bahun Hunan shinkafa taliya makaroni sabulai abun dai tamkar za'a bude shago"tsarabar su Abdullah kennan mlm dahiru yarasa inda zai saka bakinsa dan gaskiya ya yaba da Abdullah yaji ya kwanta masa a rai cikin lokacin daya "kyautar kudi kuwa Abdullah tamkar wanda yake da injin bugo su agida "mlm dahiru har kasa magana yayi sun sha fura sunci zabbi da aka soya musu anan sukayi la'asar sannan sukayi shirin tafiya Aisha dai tana daki tamkar ta fasa ihu da Kyar tayi sallah ko abinci kinci tayi ta sanya dan guntun hijab hular kanta ya sauko mata iya kafadarta ,farin takalmi tasa sai farin handbag data makale a hannunta ,a haka mlm dahiru yakarayi mata nasiha ta fito dan hasken ranar da ya nufi gabas zai fadi tana fitowa shi ya hasketa tasa hannu ta Kare fuskarta ,Dr sagir ya kallota ya girgiza kai yayin da yadan zunguri Abdullah ga madam nan fa. Abdullah ya kalleta tsab yayi murmushin a hankali yace ai aganinta duk mun matsa mata ne fa,suka sa. dariya ,lafiyayyun motoci tamkar na wasu shugaban kasa aka bude mata daya ta shiga ta gane direban da ya kawosu ne,ashe Abdullah ne ya turo shi,mlm dahiru na tsaye har sai daya ga tafiyar su tare da tsaraba man shanu nono fura kwan zabbi musamman dayake lokacin sane.salis da yaya Ali sune a motar gaba sai musa dake tuka su a dayar mota kuma shida Aisha a baya yayin da Dr sagir a gaban gurin me zaman banza Dr sagir ke ta kokarin janta da hira wani ta amsa wani tai shiru shi kuma Abdullah inda ka ganshi tamkar wanda akayiwa gafara jin sa yake kmr ya aure ta ne sun fito yawon ziyara yasa hannushi ya dauko jakarta dake kan cinyarta tana kallonshi batai magana ba har ya bude bbu komai a ciki sai kayan make up dinta yayi murmushin ya Ciro wani passport dinta na makaranta da uniform a jikinta har da dan kwalin perfect akanta ya zubawa hoton idanunshi sannan ya dago ya kalleta itama anyi sa'a ta dago da niyyar ta saci kallonsa ai kuwa suka hada Ido ,Ido cikin Ido suke kallon juna ya kashe mata idanunshi daya yayi murmushin ya zura hoton a aljihunsa , Aisha ta dauke kanta tacigaba da kallon hanya shida saura suka shigo birnni kebbi taso ace sai dare suka shigo , Amman ko sanda suka sauka daga mota Ido CA akansu musamman ita da Abdullah daman Kuma abunda bata so kennan gashi biye yake da ita jakar ta ma tana hannushi nan da nan tarinkajin tamkar ta nutse dan kunya yanayin ta ya sauya jikinta har rawa yake hatta Dr sagir sai da ya lura da yanayin da tashiga har kofar gida suka rakata suka Yi sallama da Dr sagir , Abdullah ya Mika mata jakarta ta juya zata karba ya lura hatta idanunta sun cika da kwalla ya rike jakar yana kallonta ya kira sunanta cikin sanyi murya Aisha..... are you alright .....?ta daga masa kai are you sure tasake daga masa kai sannan a hankali ya Miko mata jakarta tare da fadin I will come back letter ,ta amsa ta juya ta shige gida ya tsaya yana binta da kallo bbu halin yabita ya rarrasheta ya karaso inda Dr sagir yake yana ganinsa ya fashe masa da dariya yace kai friend be a man duk kabi ka susuce akan karamar yarinya "tension ne kawai ta samu na rashin sabo na gane irinsu duk kabi kawani rude Abdullah yayi murmushin karfin hali dan shi kadai yasan halin da ya tsinci kansa lokacin da suke tare Dr sagir ya bugi kafadarsa yace my friend a dage da addu'a .dan yarinyar taci ayi komai a kanta

Please Login or Register in order to submit comment