Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambayar da Aisha tayi mata ba tacigaba dayi mata bayanin yadda ake samun lalura iri iri na laulayin idan macce ta samu ciki ,
tayi shr tana ji Amman ba abinda inna take fada take fahimta ba , tunanin ta yana can wani guri. tashiga uku Kar dai Abdullah ciki ya bankamata ,sannan ya sakota.
tasan inna bata fadar abinda bata da tabbacin a kansa aunty ce tashigo tana surutai kai nima fa yau dole a daga min kafa nima mara lafiya ce dani .
Aisha ta kalli aunty Maryam ,inna tasan maganar zata mata dan Allah ta kwashe kwanuka ta fita wankewa har aunty ta zauna Aisha nabinta da idanu ahankali murya adashe tace aunty wai ciki dani ?
Aunty ta kalli yadda tayi maganar tace au ke tun jiya baki sani ba.
cewa nake kinji ne shiya bangaya miki ba.
to ciki ne dake bai kai wata daya ba .
nace ke Kuma irin naki laulayin kennan ciwon ciki da zazzabi ".
Kwalla ta cika a idanunta kafin kace me sai hawaye shar ...shar... aunt tace to mayye haka Kuma ke me son kananan yara.
gashi Allah ya kawo miki shine zakiyi kuka Aisha kuwa da zaune tamkar an dasata , bata sake cewa komai sai cigaba da kukanta take ita kadai tasan abinda ta tuna .
aunty ta matso kusa daita sosai tace A'a ai yanzu ba kuka zakiyi ba abinda ya faru yarigada ya faru,.
ta lafiyarki zakiyi da dan dake cikinki tunda ....Dr salim ne yashigo ya katse su ganin Aisha na kuka yasa ya ja ya tsaya yana kallonta can Kuma ya matso kusa da su yace yaya jikin ne ?
Aunty Maryam tayi dariya tana girgiza masa kai tace ko daya .
wai dan an gaya mata ciki ne daita ,shine take kukan dadi .
Dr salim ya kura mata Ido baya son har baya so daukewa daga kanta ,dama takasance matarsa aka Kuma sanar masa tana dauke da cikinsa da bai san irin gatan da zai nuna mata.
ba har sai shagwaba ta isheta," har sai da aunty takira shi sannan ya dauke idanunshi daga gareta".
da sauri ya kalli aunty yace ina tunanin irin su abinda dariya ne dasu. haka nake da wata kanwa itama ko bacci zatayi yara suka hanata duk girmanta sai kiga hawaye.
aunty tasake kwashewa da dariya tace kusan duk jirgi daya ya kwasosu kmr wasu kawaye shima dariya yayi sannan yace excuse me sister inason na dan ganki na mintina kadan "
aunty tace ba komai ta tashi tabishi sanda inna ta dawo itama.

Dr salim yace mijin Aisha ya jima da tafiya ne ko kuwa daman tafiye tafiye yake aunty tace A'a ai... Daman ba tafiye tafiye yake ba ..sai Kuma tayi shr .

Dr salim ya dan nakalci wani abu ,.
yace sorry ina son nasani ne saboda irinsu da yanayin da take ciki yanzu tana bukatar kulawa ma'ana dole takasance tana da wani a kusa daita da zai dinga lura da ita sosai.
musamman ita da cikin yazo mata a haka.
duk lokacin dataji ciwon ciki tana iya shan duk wani abu datasan zataji ya daina.
ya numfasa sannan yace to idan kuwa mijinta yana kusa shi zamu bawa matakan da zata kiyaye da irin abin dazata dinga Sha.
har zuwa lokacin dazata daina jin ciwon cikin .
Aunty Maryam tace ai da yake yanzu ma tana gida ne Amman ko ni ko inna duk wanda ka yiwa bayani ma za'a san abinda za'a dinga yi .
dr salim ya furzar da iska hade kurawa aunty Maryam ido dan ba abunda yaso ji ba kennan Kuma maganisa a kawai alamomin tambaya sosai a tare da bayaninta ,Amman bai son ya fiyye shishigi da binkice akan komai.
yana son yabi komai cikin tsari dan haka ya sake numfasawa yace shikenan .

Har byn kwana biyu bata saki ranta ba kullum sai tayi kukanta .
Itama haka kawai tarasa dalili yin kukanta .
mlm abu yashigo inna ke sanar dashi gabadaya yau taki ma cin komai.
tasa damuwa aranta shi kansa mlm abu lallabata yake wannan lokacin.
ya dauko ledar yalon da yashigo dashi ya wanke ya ajiye mata.
yace yaya zakiyi da kaddara Aisha duk yadda mutun yaso sai ki ga Allah ne kawai zai tsara masa yadda yaso.
inda mlm abu ya godewa Allah ma .
allah ya nufa cikin ta hanyar aure zaa same shi .
gashi anyi auren ba a dade ba.
Allah yakawo rabuwar an rabu da rabo atsakanin .
Ahankali ya furta ba komai haka Allah yaso .
yana jinjina kai .
Usman ne ya matso kusa da inna ya zabga tagumi yana ji abinda mlm abu kecewa gabadaya tausayin yaruwarsa yake .
gobe in Allah yakaimu sati guda kennan da sakin .
Amman har yanzu bbu wani bayani daga garesu abinda mlm abu yace kennan yana tsare inna da idanu.
inna tace muma kada a nemesu in dai basu suka nema ba.
abar abun haka komai daren dadewa ai shi cikin zai nemi ubanshi .

Dr salim ya kalli aunty Maryam da suke zaune a wani ward su biyu yace abinda yasa na sameki anan sister domin na fayyace miki bala'in dana afka ,hakika Maryam kanwar nan taki nake maseefar so kai tsaye.
dan haka na kagu komai zai faru dani gara ma ya faru akan narasa .
Aunty Maryam ta zazzaro ido "wa kennan kake nufi ?ya gimtse fuska yace wace kike daita. aunty ta sake kallonsa sosai, .
tace wai Aisha kake nufi ?yace yes ita fa sister bbu yadda zanyi shiyasa na sanar dake ki taimakmin dan Allah.
"aunty Maryam tashiga rudani da frigice dan haka ta soma girgiza kai tana cewa doctor kasan abinda kake fada kuwa . kai ya kada mata ,. Amman ai
Nace maka Aisha matar aure ce .
gama ciki nan ya nuna maka hujja.
Dr salim ya dubeta dakyau yace sister Maryam tunda kanwarki ta Tako asibiti nan naganta nake addu'a r idan har ba alkharina bace Allah ya fidda min ita daga Raina .
Amman wlh kullum kmr ziga zuciyata ake akan soyayyarta . addu'ar dana dage dayi ne da Kuma hujjojin dana samu sune suka sa na tunkare ki kai tsaye da maganar .
Ban taba jin wani tashin hankalin daya sameni na farat daya ba kmr soyayyar yarinyar nan.
tunda na ganta na rikice narasa gane kaina.
kiyi hakuri sister Aisha tana gida a yanzu sun rabu da mijinta.
aunty taja numfashi tace kai ko wani me balain bincike ne ya gano maka haka .
Dr salim yace that's very good abinda nake son ji kennan .

aunty Maryam bata gane nufin shi ba sosai dan haka ta sake cewa maganar gaskiya doctor a ina kaji wannan labarin?dan nasan maganar nan ko makota basu sani ba ..

Dr salim yayi dariyar murna sosai har cikin ransa yaji dadi tarkonsa yace sister kennan ni bbu wanda ya gaya min hasalima ban san wanda zan tambaya wanda yasan Aisha ba sai ke.
Nina na gano hakan da kaina .
aunty tayi sororo tana kallon doctor .
tace doctor bbu maganar wasa a nan fa .
Shima yadan nutsu yace da gaske nake sister ina son kanwarki.
Kuma aurenta zanyi.
ta sake zaro Ido waje ina wannan maganar ba mai yuwa bace .
A cikin lokacin daya ta canza fuska tace doctor ba fa son irin wadannan magangunun an gaya maka Aisha tana da aurenta duk ma wanda yace maka bata da aure ya gaya maka gaibu .

Dr salim yace wallahi azim ke kika sanar dani yanzu .
sannan nasan zatona ya zamo gaskiya ..


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 53-54


Aunty Maryam ta dubeshi da kyau ta gano yadda ya nuna mata tsantsar wayo tun farko. taji haushin kanta na Subul da bakan datayi.

nan da nan ta sake bata fuska tace eh da gaske ne, Aisha sun rabu da mijinta "Amman doctor ina tabbatar maka bazaka taba samunta ba.
garama ma tun wuri kabawa zuciyarka hakuri ta hakura da abinda baza taba samu ba .
tana shirin mikewa Dr salim ya dakatar daita murya a sanyaye yace yi hakuri sister Maryam.
ni ban dauki abin da zafi haka ba ,kmr yadda kika dauka .
nasan Aisha kanwarki ce Kuma abin ikon kice .
na gane koma ya akayi akwai wani abu da kike gudu .
shiyasa kika yi saurin fadar haka a kaina.
Amman ki sani sister a yadda naje jina a yanzu dana rasa yarinyar nan na gwammace na rasa wannan ya Nuna farar rigar aikin dake jikinsa .
ya numfasa sannan yace dan nasan duk me mace irin wannan Kuma yayi gangancin sakinta komai daren dadewa zai waiwaye ta .

Auty ta kalleshi tace doctor duk kimarka da nake Gani ba zan hana na shaida maka cewa kana shirin sa kanka a uku muddin bakayi gaggawa cire son Aisha aranka ba .
Mike ko gezau baiyi ba sai ma murmushin samun nasara dayayi .

Ahankali yace afuwa dai sister Maryam ai ni nariga naga abinda yayi daidai da tsarin zuciyata dan karfin hali irin naki zaki tauyeni ina bazai yuwu ba wlh , a zafaffe tace to Allah yabada sa'a.
da karfin shi ya amsa mata da Ameen dan har da gaske kike . ta wuce shi har gabanta na dan faduwa uhm ba za'a fara jin mutuwar sarki a bakinta .shima yajima zaune a wajen yana saka da warwara hade jin haushin aunty Maryam .


Faiza tace dan Allah ni mama ki kyaleni na ci kaniyar wannan Yar iskar da bata gaji iskanci ba.
sai dai ta ara ta yafa.
kibarni nacasata na gurje bakin rashin mutunci shegiya Mar kirjin a gwagwa itama Sami kokarin rama zagin take Amman faiza dam ke bakin ta murde .
mama hafsa dake kokarin shiga tsakanin faiza da aminiyarta Sami.
Amman ina faiza taki sakinta sai jibgar Sami take kmr Allah ya aikota da kyar da sidin goshi mama hafsa tasamu ta rabu su .
Faiza ta bude baki zata lailayo wani a shar din mama ta katseta ke Ke ke tana nuna da dan yatsa.
ya isa haka nace sannan ta tura keyar Sami tana bata hakuri tanuna faiza ke dai akwai Yar jarabar yarinya ana yaki kina ga kura Tjeey din cin durin uwarki.
duk yawon danayi a kigajen bokaye da yan tsubu kenan zai tashi a banza.
ki wuce kebbi ga wanda ya fi Tjeey da komai ta koina can Amman kin tsaya kina asarar yawun bakin akan wannan mai sololon kan kmr na miciji.
Da wuya awa marakin lema .
faiza tace ai mama nasha gaya miki kece dai baki da fahinmta ina son Abdullah kodan kyaunsa Kuma wlh dole ne na aure shi tako wani hali na kanannade shi ta koina.
na dai tsaya ne naga ta karyar iskancin Sami wai daga naje mata sallama na tar daita da Tjeey.
dan na tsaya muna gaisawa dashi kawai tashiga bace bacen rai ni Kuma dana ga haka sai na dada shishige masa ni daman can yayi min. shima Kuma ya nuna yanayi dani shikenan take ta balain shine yanzu tabiyoni har gida dayake jakace .
ba dole nazage dantse na nuna mata karyar iskancin takeyi ba .

Mama hafsa ta rike baki tana jujjuya kai .
a ranta tace dole ma ayi tafiyar nan kebbi tare da ita zai fi ma'ana. Sannan cikin yin kasa da murya
tace nasan halinki da rawar jiki sauran kije kina zubda aji agunsa .

nasan duk yadda wannan banzan yaron yake bai kama kafar masu wankin Abdullah ba balle matsayi .

dan haka kibarwa Sami shi suje can sukarata idan mulke shi zatayi da mai kullum wannan ba ruwanki bane.
ke dai ki duba cigaban ya zo miki .

yanzu kije ki hada inaki inaki anjima nan zamu tafi har ni sai naga zaman naku ya daidaita sannan zan dawo.
dama naso kifara yin gaba ne.
saboda ni ma nan akwai abunda nasa ayi min saboda Abdullah din ya dinga rawar kafa akanki.
daya dinga yiwa waccen Yar matsiyatan masu tasan nono ,gara yadinga miki .

Sai yanzu hankali faiza ya dawo kan maganar mama hafsa tace wlh kuwa mama .
Dan yana daya daga cikin abinda nake tunani kennan akan auren Abdullah .
nifa ko kallona yayi nan duniya ji yake kmr ya kashe ni.
Ko cikin farinciki ko nishadi yake danazo gurin yanzu nan zaiyi kicin kicin yarinka cin magani .
mama hafsa tace kinga abinda yakama ki nutsu kiyi .
kisamu yadda zaki kwatowa kanki martaba a gunshi .
shine kika zauna kina fada da wannan cima kwance.
faiza ta kwashe da dariya tana Miko mama hannu wai sukashe .
Ai kuwa mama taba suka kashe suna tuntsira dariya .
Faiza tace nida nake da burin indan na aure shi na samu na sake dashi sosai.
to yana haka yaya za'ayi abu abubuwa su kasance .

Mama hafsa Tace ina..
wane shi dan ubansa dan baki san kullaliyar dana sake kullowa bane kai arziki ma idan ba a gurinka yake ba aikin banza ne.
Ko kana sa wutsiyar ido ka hango shi a wani guri ya zame maka balain ka kasa tsugunne da duwawunka duba ki ganni har Yar rama nayi saboda ganin auren naku ya yuwu..

faiza ta katse mama da cewa ni yanzu nafi so ayi abinda Abdullah zai dinga lashe ni tamkar dawisu saboda so shine kan gaba.
dan wannan jikin nasa idan ya kasance yana son mutun nasan zai sakaka ka more kuruciyyarka ka manta da kowa .
Mama ta zaro Idanu waje ka manta kowa fa najikince har dani ciki .
Faiza ta dan Susa kai ganin saba saiti . wayancewa tayi tace haba mama ai banda ai kece kan gaba in bake ai duniya zata min warbar kuno mama ta sauke ajiyar zuciya hade cewa abinda nake so naki kennan.
to kinga dama yau za'a gama abinda nasa ayi to kinga ko zuwa da yamma ne sai mutafi.
sai dai kuma idan duhu ne yayi .
sai mu bari sai gobe idan Allah ya kai mu .
ai baza mu tsaya kallon ruwa ba yanzu masha Kaye a gurin kwado suka sake kashewa faiza har jijiga jiki take zabar murna ...

Please kuyi manage da wannan kai ke ciwo😭😭😭

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO


Page 55


Bai san iya adadin cup din coffee da yaje sha a kullum kafin yabaro office.
Hotonta yana nan a bude a system dinshi ,shi ke tayashi hira da debe masa kewarta a duk sanda soyayyarta ta bijiroma masa , sannan yake samun ya gudanar aiyukansa .

Dady da kansa yace yadinga yin haka domin ya zama jarumi a office ko idan yana kallonta zai iya aiwatar da komai cikin natsuwa "batare da ansamu wata matsala ba .
Kiran dady ne yashigo wayarsa ya daga yana kallon hotota yasa hannu yana shafa beauty face dinta .
bangaren dady kuwa cewa yayi mhm Abdullah tell me tun safe zuwa yanzu sau nawa ka tuna Aisha?
Abdullah ya dan ciji karshen Biro da ke hannunsa yana tunanin. yayi dan yi murmushin takaici yace sau uku ne ma kawai.
shima sai yanzu dana bude system da rufewa nayi saboda ina son kammalawa da wani aiki ne .

Dady yace da kyau yarona kaga daga goma Sha ya fara raguwa gashi ya dawo sau uku .
Abdullah ya sake yin murmushin kadan dan shi kadai yasan halin da zuciyarsa ke ciki game da rashin matarsa ya dau cewa dady haka ne kawai ahankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yacire white glass din dake manne da idaonsa.
ya jingina bayansa da kujera yana jujjuyawa ahankali manner da wayar a kunnesa yace dady akwai hanyar dana gano wacce tafi waccen saukin fahimtar komai ina ganin itace zata kawo karshen komai da muke bukata .
dady yace da kyau ina jinka Abdullah yace sai zuwa anjima idan na koma gida zan maka bayanin komai .
Da sauri dady yace shikenan sai ka koma din"Abdullah yace yauwa sannan yakashe wayar .

Yana juyowa ya sake ya zuba mata idanunshi yace kin gani ko Aisha komai na rayuwata ya canza, narasa farinciki da sukuni tun sanda kika tafi kika barni .
bana son a bani dariya saboda bana son nayi ,dariyar ki kawai nake so a tare dani .
gashi dady yace kada naje gareki ni Abdullah ya zan yi da rayuwata komai ya taru ya cakudemin waje daya.
rashin ki kadai ya isa ya tarwatsani .
shi kadai yake maganar shi tamkar wani zararre .
kawai idanunshi ya gane masa tana yi masa dariya ta cikin system dinsa.
ai ko yashiga danne danne a jiki yana sake neman ragowar hotunanta wai shi lallai sai yaga wushiryarta data yi masa dariya yanzu.
har sanda salis yashigo da coffee ya ajiye masa bai san wani duniya yake ba .
Sai can hankalinsa ya dawo jikinsa .
Gashi lokacin tashinsa ya kusa Amman baya kaunar abinda zai saya doshi gidan. sai yarinka jin gabansa na wani irin faduwa" tun kwana biyu da faiza da mama hafsa suka sauka a gidan,
yaji gabadaya baya son kusantar gida dan haka gurin Dr sagir kawai yace a wuce dashi dan shi kadai yake tayashi hirar Aisharsa in ba cin dady ya hana aje da tuni Dr sagir ya je masa gunta .
to zaune agun Dr sagir ne mami ta neme shi a waya" dan tasan lokacin tashinsa yayi daga office tashin hankali da mami ta sake jefashi da yaje kiran nata yafi wanda yake ciki a halin yanzu .
dan magana ce akan faiza ita dai lallai ita take son ya aura Kuma tana son ayi komai kafin dawowar dady .
Tana son faiza ta zama matarsa ta hakika .
mama hafsa dake kusa da mami ta kara tabbatar da hakan suke bukata ayi auren da wurwuri .

Abdullah ya zubawa maminsa ido shi kansa ya amince tun ba yanzu maminsa na matukar kaunarsa fiye da komai .
a tun sanda batun aurensa ya bulo ta sauya masa kar dai mami ta tsane shi ne ayanzu yaji gabansa yayi wani irin faduwa da sauri ya kauda wannan a ransa saboda dady ma ya hana shi ganin laifin mami yace yin haka bbu kyau .

Yarigada yasan halin dadinsa dan haka sai daya gama yi masa dukkan bayanin tsarin daya shirya game da masu son salwantar musu da dukiyar .
dady yayi shr yana jinjina kai yayi Ammanna da shirin Abdullah din.
da yaba masa Sosai da irin dabararsa a karshe har yayi masa godiya dasa masa albarka.
Bangaren Abdullah kuwa ba wannan ne a zuciyarsa ba .
dan haka yana gama jin dady shima ya dora akan sanar da dadinsa halin da'ake ciki na game da maganar auren faiza da ake ciki .

dady yayi dif ... Na wani lokaci wanda har Abdullah din yasake kiran sunanansa.
dady yace inatare da kai Abdullah ina jinka yadda Dady yaji aransa.
haka shi ma Abdullah din yaji.
dady yakira sunan Abdullah din rai a bace.
yace ka gane ko Abdullah duk abinda mahaifiyarka zata nema daga gareka kayi kokarin kaga kayi mata yadda take so .
kasan bbu abinda yafi uwa a nan duniya .
Allah (s w t) dan kansa sai da ya ambaci uwa uwa uwa har sau uku kafin ya ambaci uba sau daya.
Abdullah ya girgiza kai game da dan rufe idanunshi dady yace to kaga duk abinda zata ce kayi kai dai ka mata biyayya .
domin muma mun gama da iyayenmu lafiya.
jikin Abdullah yayi mugun tsanyi akan yadda Dady yace haka zaiyi Amman ana shi tunanin me yuwa a sanadin haka ya rasa Aisharsa na har abada.
saboda yasan muddin ya aure wannan faiza mutuwa zaiyi .
Tamkar dady yaji shi ya Kuma cewa kada Kuma kayi zaton aurenka da wannan yarinyar zai sa baza ka sake auren Aisha ba .
A'a kai namiji ne Shari tabaka damar auren mata fiyye da daya .
dan haka ka sawa ranka ko kayi wannan aure .
in Allah yaso Aisha zata dawo gareka kaji .
Abdullah ya amsa da to.

dady ya sake yin kasa da murya yace Abdullah na rokeka ka sausautawa zuciyarka damuwa nan kafin na dawo .
idan wani abu yasameka ban san yadda zanyi ba .
Bansa kalar halin dazan shiga.
sannan dady ya ajiye wayar ya jima zaube bai iya motsa jikinsa ba saboda bacin rai da yake ciki.
iyakar fushi yayi da mami sai a yanzu ya gano dalilin raba Abdullah da matarsa datayi.
ita ko tsoron alhakin yaron bata yi.
ko musu baya iya yi mata "tun bai kai haka ba Amman yau an wayi gari saboda wasu can masu kama kaman dagin ta raba danta da abinda ya kwalafawa rai .
ta batar masa da duk wata walwalarsa yake fada a ransa.
ba Abdullah din kadai ba hatta shi kansa abin kullum dashi yake kwana a ranshi .
gashi koda acikin hira taki yi masa zance idan sunyi waya .
shima Kuma ya dau alkawari ba zai fara sanar mata yasan da maganar ba.

Har ya kwashi mintina talatin da rabuwa da dady a waya.
Amman bai san cikakken tunanin da yake yi ba.
abubuwa uku sun taro sun cakude masa cikin kwakwaluwarsa.
Kuma duka atare suke tafiya ko wanne yana bukatar ayi solving dinsa.
Aisharsa auren faiza matsalar ma'aikata.
ya rike kansa da karfi dan kada ya tarwatse.
da kyar ya iya tuna dady yace ya dinga ya waita addu'a idan irin haka takasance dashi .
addu'ar yayi tayi har ya kara da sallah raka'a biyu a haka ya samu sausauci a zuciyarsa .
ko abincin daren ranar bai ci ba.
domin shi kansa abinci ma ba kalar raayinsa bane .
dan a Yan kwanakin mami gabadaya ta fita batun tattalinsa da abinda zai ci rawar jikinta akan faiza da mama hafsa kawai yakare .

Ko a washegari daya shiga gaisheta kafin fitar sa office .
karara mami ta nuna masa ita fa yanzu so take ya dauki duk abinda mama hafsa take bukata da mahimmanci tamkar ibadarsa data zame mata dole.
ya kalli mami kmr ya zubda kwalla dan takaici abinda tace.
Amman sai yace bbu komai duk yadda kike so haka za'ayi .
a hakan ya baro part dinta daidai zai fita falon ne suka kusan cin karo da faiza da sauri ya tunkudeta tun kafin takai ga jikinsa.
tayi taga taga zata fadi sannan ta rike bango ganin zai bar wajen ne yasa tayi saurin Sha gabansa ta tare shi wai tana son magana dashi kallon da yayi mata .
sai da taji shi har cikin hantarta .
nan tabi shi da ido har suka fice shi da salis .


Abdullah ya zagayowa mutanen su ta bayan gida ya kamo su ta inda baza suyi tsammaninsa ba.
mutun shida dama ake zargi sai gashi an kuma samu n mutun biyu a kasa.
takwas kennan abin mamaki sosai ragowar biyun din duk abokan dady ne na kud kud wanda yake ji dasu .
ragowar Kuma manya ma'aikatan company ne .

Bai tsaya ji komai ba yasa aka kame su aka kullesu har da abokan dady .
Kuma fur yaki yarda da duk wani ban hakurin da'ake bashi .
da'aka dame sa da magana ma

Please Login or Register in order to submit comment