Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

..

Ya Mike har ya juya zai tafi ya sake juyowa ya kalleta yana Jin kmr ba zai iya barinta ta kwana ita kadai ba ",Amman yasan ko ya zauna yadda take yi dina bazata taba sakewa dashi ba" koda kuwa bbu abunda zai mata .
a falon yayi zamansa ya kunna sigariinsa ya kuna yasoma suka yana tuna kallon da mami tayi masa dazu,k komai yarinka dawo masa a kansa" hankali yake aiyana muddin mami bata saki ranta tabbas bazai iya moran sansar jikin Aisharsa ba yadda ya dauki lokacin mai tsawo yana tanadin wannan ranar akanta ga dai Aisha can a daki Kuma tazo a matsayin mallakinsa abinda yafi kauna kennan fiyye da komai" yau ranar farinciki ce gareshi da zai kwana gida daya tare da ita. Amman ga maminsa abin bacin rai ya juye mata tayaya zai iya kasancewa da ita cikin wannan halin shan ya furta zan zan jure har sanda zan samu natsuwa " yanzu haka ko sun haifi ya'ya da Aisha killa mami bazata so su ba ya fada a ransa wanda a filli ya rufe idanunshi yace mami mami dan Allah kiyi hakuri ki sawa auren Abdullahnki da Aisha albarka shine kadai zai jiyar dani farinciki dake tattare da Aisha" hakan ya dinga yi yana busar da hayakin sigarinsa lokacin lokacin yakan tashi ya dubu Aisha sai ya hangeta kan gado kwance sai ya dawo ",ya kwanciyarsa yayi akan doguwar kujerar dake falon har sanda akafara kiraye kirayen sallah asuba yakarasa kashe sigariinsa cikin kauli guda daya Sha sannan akayi kiran asalatu ..

Karfe bakwai da mintina ya leka dakinta har kan gadon ya haura kusa da ita ,tana kwance abunta Amman da dukkannin alamun itama ta tashi tayi sallah "ta takure sosai a gado ta rufe duk jikinta sai fuskarta da tabari. dan haka ya xuba fuskar dake tattare da sanyi idanunshi yasa hannunsa ya shafi gefen fuskarta , har kan jajayen lips dinta bakinsa yakai yakamo yadan tsotsa sannan mike ya fito ya janyo mata kofar yana fita tana bude idonta tana sauke ajiye zuciya itama yadda bai samu bacci ba haka ta kwana tana murkususu ..

.. takwas da mintina part din dady tayi masa " mamakin ganinsa dady yayi Amman ya danne mamakinsa ..Abdullah yakaraso yana gaishi. dady ya dan nakalceshi kadan sannan yacigaba da abinda yake yace har ka fito ina Aishar?.
Abdullah ya dan sunkuyar da kai yace na barota gida ,sannan ya dan yiJim yace jiya na bar mamina kmr ranta a bace ,na shigo yanzu nashiga bata tashi ba, ya fada yana dan murmushi dan boyewa dady damuwarsa bai san wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, dady yayi shr yana kallonsa yana sake nazarin tilon "dan nasa da sauri Abdullah ya canza hirar bakin da zasu tafi a yau. dady yace eh zuwa karfe Shabiyu motoci zasu zo wasu zasu fara yin gaba ..
Har zuwa tara suna tare da Abdullah ya Mike yace zai je ya sake dubu maminsa ko ta tashi dady ya kirawo sunansa ya juyo yace idan kaga maminta ka ,sai ka koma gida ku shirya karfe biyu zuwa uku zaku wuce Abuja in yaso sai ku tashi tacan zuwa Germany Abdullah ya bude Ido yana kallon dady duk da yasan da komawarsa Germany ,Amman bai dauka da wuri haka ba. yayi sororo yana sake kallon dady yasan magana daya dady yakeyi dan haka ya amsa kawai ya fita ,sai da dady ya tabbatar Abdullah yabar gurin mahaifiyarsa sannan ya matsa intercom ta kiran mami..

mami tayi sallama tashigo fuskarta ba wani yabo ba fallasa ta nemi kujera ta zauna tare da gaisuwa tsawon lokacin dady bai Yi magana ba balle ta ran zai amsa gaisuwarta dady yayi tamkar bbu wani a tare dashi "daga can ya numfasa yace Abdullah zai koma gadon asibiti kmr yadda kika likita yace , Amman ki sani abu ne mawuyaci ya samu lafiyarsa" ko yatashi ko Kuma akasin haka ....
A dan frigice mami ta dago tana kallon dady yayi kmr bai gane yadda tayi ba ya kau da kai gefe fuskarsa a hade yacigaba Amman ina son idan kin koma daki kiyi sallah rakaa biyu ki godewa Allah da ya baki "da "mai biyayya me hakuri me gudun bacin ranki ne"me damuwa da damuwarki ,wanda a wannan zamanin nasan tabbas irin su Abdullah basu da yawa "ya sauke ajiye zuciya saannan yacigaba Kuma ki godewa Allah Abdullah da ne kuma ya cika dan halak "Abdullah ya nemi da yayi auren Sunna Amma ke kinki yarje masa saboda wani dalili naki na banza mara tushe, bansani ba kodan Aisha daya aure ne kesani tun Gini tun zane kinyi kokarin rabani da yaruwata wacce ita daya gareni yayinda ke kike tare da naki family din" sai dai me Allah ya nuna miki ke bakowa bace shiyasa ya jarabi tilon danki mafisoyuwa a zuciyarki da son diyar yaruwata batare da sanin shi ba ,to ALHAMDULILLAH duk randa da Abdullah ya haihu da yarinyar nan tabbas ya tabbata jinina shi " Kuma bbu me kiran "dan"da "dan "titi.

wanda a wannan zamanin ba wai wani abu bane agun namiji baligi musamman wanda yashiga matsalar aure irin haka ..
Jikin mami yayi sanyi.d dady ya numfasa tsoro bakya son aurensa da Aisha yasa shima yace ya hakura ya zabi farincikinki ,akan nasa kisani yadda muke da hakki akan sa shima haka yake da haki akanmu, haka ne ma yasa na tsaya tsayin daka naganin nabashi farinciki sa da lafiyarsa akan ko ma me zai faru ya faru" abin takaici da damuwa duk gur biyu ya kamata atoshe masa .ga dai Abdullah ya auri yarinyar da yake so . wanda burin rayuwar sa kennan sai gashi rashin hadin kanki yasa damuwar dai har yau bata barshi ba bbu koma bbu komai Allah yaraya min shi idan Kuma sanadiyyar hakan wani abu ya faru dashi har narasa shi , shikenan sai kiji dadi ki samu wanda zaki aurawa wacce kike so, ya fadi hakan yana girgiza kai ya sake cewa bbu komai kmr zaiyi kuka dattijon ya koma kalar tausayi .. mami tasan ya kai karshe kennan tunda ya nuna haka ,tasan sa tasan halinsa, tsawon sama da shekara talatin da suka fara rayuwa tare. zuciyarta fal tsoron yadda yayi mata magana. ta kalleshi bai sake cewa komai Ba kuma tasan a yadda suke ko zasu Kuma kwana a haka ba zai sake mata magana ba" a yadda taga yanayinsa ta jima anan zaune daga baya ahankali ta Mike jikinta yayi mugun tsanyi kafarta kmr bazata dauketa ba ..koda ta koma part dinta ma tunanin duk ya hanata sakat ko dazu daya shigo ta lura yanayin sa. ya kara ramewa akan sanda ya dawo daga jinya maganar dady akan hanya take "yadda Abdullah ke ratsawa kasashen duniya yana ganin yan'mata iri iri na turawa ai da tuni labarin yasha bam bam bama zai bukaci yin auren ba. ita daman ta dan soma sadudu biris din da tayi dai shine ya Dame yaron. Kuma gashi yawan damuwa ita zata haifar masa da ciwon zuciya amatsayinsa na wanda bai gama samun lafiya ba. ta furta kalma na shiga uku ,haka kawai ina neman kashe dana da kaina ...

Mu dai tafi hankali shin da gaske mami ta saduda kmr yadda tace ko kuwa dai tayi likimo ne "amsar ku naga Yar mutan bagudo ku dai biyoni a sannu ahankali dan kusha labari mai tsansar abin tausayi😭😭😭😭😭


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


AISHA A BAGUDO


Page 28




Karfe daya da rabi daidai byn dady yayi sallah ana masallaci cikin gidan. biyu daidai kuwa a gidan Abdullah tayi masa Abdullah ya shigo dakin ita kadai yasamu domin aunty ta wuce tun dazun.

Tayi kyau tayi gayunta kmr yadda yadda ya Gani. ahankali ya matso kusa daita ,yana murmushin ya sanar daita zuwan dadynsa ,a frigice take binshi da wani kallo cikin marairaicewar fuska tace me nayi Kuma . har taso bashi dariya Amman ya dake baiyi dariyar ba" yace bawani abu bane ina ganin dai kan tafiyar ne, ba dai kince bazaki bini ba sai muje kusanar dashi da bakinki "dan kar ya dauka ko daga gareni ne yasake hade rai ,ta sauke ajiye zuciya ahankali yayin da tacigaba da kallon Abdullah, baya ya juya yasoma barin dakin yace yana falo .

Tabishi da Ido kawai ita dai da Abdullah ya tsaya sun sulhunta kansu zata bishi ba sai ya hada da dady ba" dan ita tsoro take ji ,batasan abune yafi karfin Abdullah din ba shi yasa ya sanar da dadynsa..


Tayi sallama ta isa falon ta nade jikinta da abayar har da dan kwali tamkar wata balarabiya cikin natsuwa ta nemi can gefe ahankali ta zauna ta takure jikinta waje daya .

Dady yana waya sanda tashigo sai da yagama ya ajiye wayar sannan ya kalleta ta sunkuyar da kanta, kwarjinin dady ya cika falon ahankali ta gaishe shi ya amsa yace Aisha kennan yasake maimaitawa ahankali yace taso zonan ki zauna yanuna mata kan carfet dake gefe kusa dashi" sai da ya Kuma maimaita hakan sannan ta taso a dan tsorace wanda har kallon da Abdullah ke binta dashi kasa kasa yasa ta kusan faduwa a diririce ta zauna .
Inda dady ya nuna mata. tare da sake sunkuyar da kanta sosai " poor Aisha dady ya fada akasan aran shi duk yadda ya dauketa ba haka ya ganta ba, dukkanta bata fi girman aminarsa ba ,ya kara jin tausayinta yashiga ransa matukar,a fili yace Aisha kun kwana lfy a gidan ko ?ta daga masa kai yayi murmushi madallah bayan dan shr yayi na wani lokaci sannan dady yace da gaske wai kince bazakibi mijinki ba "taji kmr kasa ta bude ta nutse ciki ta kara sunkuyar da kanta har ya gane tsananin nauyin data ji" yayi murmushi .

Yace Aisha dubi kigani ya nuna mata Inda Abdullah ke zaune" mijinki peticent ne daga gadon asibiti yazo daurin auren ku kinsa tun accident din da yayi kin sami labarin ko?

Ta daga kai yace to har yanzu bai gama warwarewa ba likita yace daurin auren "na daga ciki abinda zai taimaka gurin warwarewarsa .

Ko kadan ita batasan da wannan ba dan haka a yanzu ma dagowa tayi takalli inda yake 'dady yacigaba to kinga zai yiwu adaura auren Kuma yabarki anan ya koma shi kadai "kiyi hakuri kibi mijinki da taimakon Allah da taimakon ki zai karasa samun sauki hakan yasa gabadaya jikinta ya mutu ita duk batasan da haka ba..

Shi kuwa Dady kallonta yake sak maimunarsa tana karama Amman ita Aisha kusan har tafi ta komai ,yana jinjinawa al'amarin Allah , a ganinsa kmr tayi karama da tabi Abdullah din. bugu da Kari yana ganin kmr ta yiwa Abdullah yarinta ,sai dai ba,a nan take ba tunda daga kallonta zatayi hankali ,a fili ya sake cewa kiyi hakuri kibi mijinki ki duba shi kinji ..

Ta daga masa kai yace yauwa Allah yayi miki albarka Allah yabaku zuria ta gari ya dade yana Yi musu addu'a sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsala tace bbu yace taje ta huta ..
Karfe hudu zuwa biyar zasu wuce ta amsa ahankali ta Mike ta shige ciki dady yabita da kallo yana girgiza kai ya koma ya jingina bayansa da kujera "ya Kuma jin tausayinsu na ratsa shi ,yace aransa duka abinda mami kewa rikici kennan "dan shi dady bai taba ganin Aisha ba sai yau haka ma mami "ya waiwayo ya kalli Abdullah ya kira sunnansa yace Abdullah Aisha ba suruka ta bace diyata ce ko bbu aure tsakaninku ni mai iya rike ta ne "tare da duk kan dawainiyar komai nata dan haka kai ma dan Allah ka rike amanarta..

To abangaren dady ya wanke ZUCIYAR Abdullah din tas domin ya yaba da Aisharsa ciki da waje. "byn tafiyar dady ya shiga dakinta ya sameta ta daga Ido tamkar wanda tayi kuka ganin da yayi zata yi magana yasa ya matso da saurinsa ahankali tace su innarmu basu san yau zamu tafi ba yadda tayi maganar ne tayi matukar bashi tausayi" ta sake cewa ga sister tun jiya bata zo ba. Ya kamo hannuta cike da kulawa yace bari yanzu naje gidan, me yiwuwa baba yabiyoni sai kuyi sallama Inna ce dai nasan da kyar ne" shi Kuma salis sai yaje ya dauko miki sakina

To shima mlm abu addu'a yayi musu sosai sai dai su yaya yusif da umar da Ali ne suka biyo Abdullah dan dama ita aunty tabiya ta fadowa su Inna koda ma Abdullah baije ba daman za'a tura wani ,sai ga salis shima ya dawo wai sakina ta wuce zuru tun safe ..
A falo Abdullah yabar ta da yanuwanta yaya yusif ya Mika mata sakon su inna ta duba taga har da dan karamin alqurani me kyau wanda aka taba bawa baba abu tsarabar saudiya ,suke ta rige rigen ita da usman ya basu kowa yana so baba yace abar masa abin sa shima yanaso, tayi murmushi ta rungume shi a kirjinta tace ina usman .umar yace ai tun jiya da aka tawo dake yayi kuka har zazzabi ya rufe shi har yanzu yana gida bai fita ba "idanunta suka ciciko da hawaye tayi murmushi tace aranta bazai san yayi tarashina ba sai nabar garin gabadaya.basu fi mintina talatin ba duk suka Mike .

Abdullah da ya amsa wayar teema ,daga cikin wayar take sanar dashi mami ke nemansa nan da nan yadan Sha jinin jikinsa ko wani abun ne kuma ya faru tare suka fito da su Ali .

A part din mami zaune yake kusa da ita kanansa duk suna zagaye dashi . ya dan sake musamman tunda su faiza sunbar gidan tun ranar daurin auren tun kafin adawo faiza ta hau iskar karya tana fizge fizge tana surutai tana hadawa da sunan Abdullah, Amman duk haukan nata bata tona irin abinda tayi ba. Da bai samu Abdullah ba". nan kallo ya dawo kanta mama hafsa naganin haka ta tattara ta suka bar gidan ko cikakkiyar sallama basuyi da mami ba" dama haka abin Allah yake idan Allah yariga ya tseratar da kai ka tsira.

Mami tarinka kallonsa wata rayuwa ta daban dan nata zai shiga wacce acikinta girma yake shigar mutun" koda mutun bai shirya hakan ba .duk yadda taso da kasancewa auren nasa ba haka yazo mata ba. "ga Abdullah din zaune a gabanta matarsa a can wani waje daban wadda bata ma san ko wace kala bace "daman Kuma dady ne ya hana akawo Aisha gidan yace kai tsaye a wuce da ita gidanta ,mami ta jinjina kai Amman ita yanzu rayuwar dan nata ita tafi damunta, ta numfasa tace yanzu yau din kennan zaku tafi yadda yaga tayi maganar cike da kulawa ba kmr a yan kwanakin nan ba ,yasa ya ji ko mamin tasa ta fara saukowa ne .
Ahankali ya dan kara matsowa kusa da ita yace dady yace yau yake so mutafi ta sake numfasawa tace tunda yace yau din ne nasan bbu fashi ta girgiza kai sannan ta Kuma cewa shikenan sai kun dawo Allah yabada zaman lfy ..

kukaramin hakuri sakamakon rashin yimuku typing da yawa zuwa wani lokaci komai zai tafi yadda ya kamata



MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AISHA A BAGUDO



Page 27


Da hanzari Abdullah yashiga dakin "har kan gadon inda take zaune a takure ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam a fadadan kirjinsa" ahankali ya kai bakinsa cikin kunneta am sorry.... am sorry.... my Aisha na barki ke kadai ko tun safe na shigo kina bacci naje naga su mami ne "ya matse a jikinshi sosai har suna jin numfashin juna sannan ya dago fuskarta yana kallon kwayar idanunta duk batayi kuka ba Amman da ganin idanunta ya gane bata samu ishashen barci ba. ya sake saita bakinshi daidai kunneta ya rada mata wani abu wanda har yasa ta janye fuskarta daga hannushi . yayi dariya sannan ya ziro kafafunsa daga kan gadon tare da fadin kin shirya ko? Sai muje muyi breakfast



Ahankali ya sake juyo wa yana mata kallon tsab idai har ba idonsa bane yake masa gizo sai yace tun kayan jiya datazo dasune ajikinta.


Ya sake kallonta tabbas su din ne Kuma ko fitar da yayi bai sa ta tashi tayi wanka ta gyara ba .ya dan zubawa jikinta Ido zuwa wani lokaci sannan yayi murmushi gefen baki.a hankali yace wayyo Allah ita da kanta ma bata yarda da kanta ba, Kuma tun a jiya ya lura da kayan sun da meta.
dalilin haka ma ya dada sawa ya bar mata dakin dan ta samu ta canza wasu yasa hannu ya kara jawota yana Yi mata dariya yasan lallai zai dan Sha wuya wannan yanayin Nata" yana matsa mata hannu ya kira sunanta bata amsa ba Amman ta dago da kanta yace idan munyi breakfast zanje gidan Dr sagir domin a yau din nan zamu wuce Abuja dan ta can zamu tashi idan na fita sai ki shirya duk da kaya biyu ya isa shima don zamu bi ta Abuja ne .

Ahankali ta zare hannuta daga gareshi tana narke fuska ta kallonsa yace mhm ko kina so in dawo in shirya ki da kaina ? Tayi saurin girgiza kai sannan ahankali cikin tsanyi murya tace tare zamu tafi ..

Yace yes mana wazan barwa ke hade dage mata girasa daya ...da sauri ta hau girgiza masa kai "tace Abdullah dan Allah kayi hakuri ka tafi kabarni anan ,ni zan zauna har ka dawo, bai tsammaci jin haka daga bakinta ba" ya dora hannunsa kan nata cikin sanyi murya yace me yasa bazaki bini ba Aisha kina ganin zai yiwu ina can wata kasa zuciyata na nan ,ban san halin datake ciki ba" please Aisha kada ki min haka ki tausayawa ZUCIYAR MASOYINKI yana sake matse hannayenta cikin nasa" ita kam zance tafiyar su tare ne ya tsorata ta . dama taji wai. Amman bata zaci da gaske bane" tace dan Allah kayi hakuri kome kake so zanyi Amman ni dai ka barni anan in yaso sai a samo wani mu zauna tare" tuni idanunta sun gama ciciko Jira kawai take taji me zaice .

Abdullah yayi shiru ya xuba mata Ido kawai yana kallon yadda take furta magana duk ta gama kashe masa sansar jiki ko kadan ita wannan yarinyar bata san wani abu rikici ba a rayuwata "Amman ita gashi gabadaya maganganunta na neman rikita masa lisafi. ya lumshe idanunshi da suka fara kadawa ya sake kallonta dasu ahankali cikin kalar tausayi yace Aisha saboda ba Kya sona shi yasa baza ki bini ba ko ? Ya nuna kansa da yatsansa daya

A frigice ta kalle shi a idanunta ya karanci ba haka take nufi bai sanda yasaki hannuta yayi rigingina akan gado tare da runtse idanunshi gam anan wancan ga wannan tun kafin ya aureta a duk sanda yake tare da ita yakan manta da duk wata damuwarsa" ya dinga jin wata ni'ima a tare dashi har sai sun rabu hakan yasa shima ko kadan baya son ya ganta cikin wani hali. yadda ta nuna a yanzu yasan tabbas bata son tafiyar su tare ya karanto haka sosai atare da ita. shirun daya yi mata yasake tsoratata" tana so tayi masa magana Amman gabadaya bata da kuzari .

Sallama suka jiyo wanda Abdullah a hankali cikin sanyi jiki ya tashi ya fita. aunty Maryam ce da yara tare da kulolin abinci ya gaishe da aunty batare da ya wani tsaya ba saboda yanayin daya tsinci kansa ya wuce dakinsa .

Zuwan aunty Maryam yasa ta dan sake "taji tamkar ta sami wani security ne "nan da nan tafada wanka yayin da aunty ke ta fada da tunhuma yaya ta ganta a haka .

Sha biyu ta gota Abdullah ya sake fita" Aisha kara sake jiki tayi sosai abunta, har take sanarwa aunty zance tafiyar da yayi mata .

Maganar dai tafiya dady yarigada yayita, dan ma kusan angama komai na tafiyar tasu Abdullah zaune agaban dady . Inda yake sanar da dady da batun Aisha ta zabi zama anan akanta bishi .
Sai Dady ya gama ji komai sannan ya kalle shi "da kyau duk sai yaga hankalin Abdullah din ya rabu kashi kashi. yayi murmushi karfin hali sannan yace to me akayi kennan ,idan har baku tafi tare ba , yasake yin murmushi zanzo gidan naku da kaina .

Abdullah ya amsa sannan acikin zuciyarsa yana mamaki dadynsa. dady yace shabiyu ga wannan watan hutun ka zai fara dan haka idan doctor ya sallameka, kana iya wucewa duk kasar da kuke bukata ..
Ya amsa da to daga nan gurin Dr sagir ya wuce da salis ya bar RK a can gidan .

Manage please.....


kumin uziri rasuwa akamin , .dan haka zan rinka kokarin ko read more daya ne kunasa muπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»



MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
ZUCIYAR MASOYI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




AISHA A BAGUDO



Page 29




Da sauri Abdullah ya dago idanunshi yana kallon mami ,ta daga masa kai alamun haka take nufi "tuni hawaye ya fara zubo masa a karo na biyun daya zubo masa a jin abinda ya danganci farincikinsa" na game da auren sa da Aisha ahankali yace thank you mami thank you mamina ..... tacigaba da murmushi ,su teema ma gabadaya suka hau murna ita kanta mami taso su bar tafiyar sai zuwa gobe domin su dan kara sakewa, minal tace bros idan kuntafi Kuma sai yaushe zaka dawo mana da aunty mu. yace ba dadewa zamuyi ba zamu dawo, mami ta karfa Allah ya dawo da ku lafiya ya tsareku...

Teema ta zagayo daga bayan mami tana dariya tace Ameen maminmu..
Mun gode ,Nan Abdullah ya kwanta a gabanta ji yake tamkar ya dauko Aisha itama ta zauna a cikinsu ,anan yayi sallar la'asar har kusan biyar suna tare" duk da rabin zuciyarsa na gurin Aisha bai san a halin da take ciki ba itama, sai da dady ya yo masa waya sannan ya fito ya iske dady a bakin get ya shiga part dinsa agurguuje sannan ya fito ya samu dady tare da direver da zai kai su airport har bakin get su minal suka biyoshi yayin da mami ke makale can jikin Window dakin ta tana hangensa ..

Sai karfe shida suka bar kebbi shi da Aisha da RK .

Kwanan su biyu a tsohon gidan su, na Abuja inda anan ne taga ainihin hotunansu na family shi. dady da mami sai kannensa tun ma yana teenage dinsa kafin Tafiyarsa oxford anan taga inda Abdullah ya samo kyau har gidan wani friend dinsa ya nema suka je wanda sukayi secondary school tare alokaci suna matasa shima ya dade da yin aure har da ya'yansa biyu .
Ranar laraba suka bar Abuja da daddare suka isa Germany karfe shadaya agogon can gabadaya su a gajiye suke duk da sun dan sami bacci ,a abuja har kusan shabiyu basu yi bacci ba har Abdullah ya fito daga wanka da rigar wanka ajikinsa tana zaune har yanzu a gefen gado "ya dubeta yayi murmushi ya dauki fam dinsa yace idan kinshirya ina falo kisame ni sannan ya fita ya barta .

Ta dan jima zaune tana karewa yanayin dakin kallo daga

Please Login or Register in order to submit comment