Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri Abdullah yakarasa ya bude mata kofar mota ta dan jima tsaye kmr mai tunanin kada tashiga. ganin dukkan idanunsu akanta yake yasa tashiga suka sake yin musabaha da Abdullah sannan da sauri ya zagaya yashiga dayan hannun ya tayar da motar Dr sagir ya sunkuya yana mata sallama Amman tayi banza dashi dan tasan duk dashi aka hada kai wajen rai namata wayo .

Ganin inda Abdullah ya tsayar da mota ne yatashi hankalinta ainihin gidansu na aure ne idan ba gezo idanunta kemata ba ai kuwa tana tabbatar da haka ta saka mishi kuka wato wani wayon ya sake mata ahankali tace ni gidanmu zaka kaini gurin innarmu haka kace .

Abdullah ya gyara parking ya juyo yana kallonta ganin ya tsayar da motar yasa tacigaba da kukanta .
Ahankali yace Aisha har yanzu baki hakura ba ?tace ni gida zaka kai ni sai da yayi wani tunani sannan ya rage murya yace kinga Aisha tunda kika baro gida na koma na gaya musu cewar zan biya na sauke ki dan haka duk su baba sun san yanzu kin gidana Aisha ta zaro masa ido tana yimasa kallon tsoro ya sake cewa kin san aurenmu ya maidu tunda nace na maidake yanzu matsayin matata kike .
Ai kuwa ta sake sakar masa wani sabon kukan tace ni bazani gidanka ba. ni gidanmu zani yayi shiru sannan yace to shikenan kiyi hakuri kiyi shiru .

Ta dan tsagaita kukanta yace kinga yanzu duk su inna su san muna tare tun karfe uku yanzu byn dare ya fara su ganmu mun koma musu .
me yuwa sun fara bacci baki ganin zasu dauka ko wani abun ne dan haka kiyi hakuri zan kai ki wani gida can ma gidan yan'uwane .
ki kwana inyaso Gabe sai naje na daukeki na kai ki gidan yafi muje musu da wannan daren.
tayi shr tana jinsa ya Kuma cewa kiyi hakuri muje can din duk gida ne a gurinmu shirun tayi ta sakeyi shirun da tayi ya fahimci ta amince .
Dan haka ya juya kan motar .

Masu gadin gidan suka bude musu get kafin ya karasa filin inda motoci suke yayi parking sannan ya dan kalleta yace ina zuwa ya fita can gurin masu gadi yana kiran yahuza ya karaso da hanzari daga inda yake dana tunda ya hango shi din ne yataso .
Abdullah yace yaje ya bude part dinsa .
,key din ya amsa da sauri ya tura cikin aljihunsa ya tafi ,. Abdullah na nan na jiransa har yahuza ya dawo ya Mika masa key ya karba yasa a aljihun wandonsa na baya.

Iya tunaninta yasa ne ayi musu iso kafin su shiga cikin gidan.
daga inda take tana hangensa yana magana da yahuza.
Amman bata iya jin abinda yake fada a saboda tana daf da inda injin yake faman aiki .
, Abdullah ya karaso ya bude mata kofar motar yana yi mata magana da kyar ta fito.
shi kuma ya hade fuska kmr da gaske tamkar bashi ne ke lallabata ba ,tana fitowa ta dan tsaya tana kallon tsarin gidan ahankali tace ina kuma ya kawota?
ita dai ta taba hange gidan gwana ta waje Amman bata taba shiga ciki ba.
dan haka tasan tun daga waje gidan ya tsaru iyakar tsaruwa fitilu ne suka haska koina kana Gani yadda wajen ya dau haske ,da duk kannin alamu ba gidan mutun daya bane saboda bangare bangaren da ta Gani .
ita tsoro ne ma ya kamata har gabanta yana dan faduwa .
shiyasa ta tsaya tana kalle kalle dan ta gane yadda gidan yake ,ita bata san inda Abdullah ya kawota ba.
dan haka ta dinga binsa ahankali ahankali har suka shiga part dinsa wani irin kamshi ne ya doki hancinta.
ba kamshin turare bane kawai naturaly ta saba jinsa a jikin da Abdullah , Abdullah ya waiwayo bayan ya rufe kofar bai tsaya wata wata ba ya kamo hannuta har ciki. Bedroom dinsa tana binsa a tsorace ,suna shiga ya janyota jikinsa...


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page 68-69


Abdullah ya waiwayo byn ya rufe kofar bai tsaya wata wata ba ya kamo hannuta har ciki bedroom dinsa tana binsa a tsorace "suna shiga ya janyota jikinsa ya matseta a kirjinsa har tasa kara "yaki sakinta ahankali ya tura hannusa kasanta yana shafo cikinta sai alokaci ya dan ji tudunsa .
tun dazu dasu ke gidan Dr sagir yake ta kallonta Amman bai ga cikin ba hakan ne yasa tasa iya karfin ta" ta fizge jikinta daga gareshi.
ta watsa masa harara sai kuma ta fara kuka ,yayi murmushi ya jata ya zaunar daita a gefen gadon.
yace ina meyye haka hade da shafo saman kirjinta da sauri ta buge masa hannu tana turo masa dan karamin bakinta ta turo masa bazato taji bakinsa kan lip's dinta ya hade yasoma tsatsa kmr zai cire mata lip's ,sai da ya tsosa san ranshi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya"ahankali yake tafiya da baya da baya har yabar dakin .

Yana fita tacigaba da dan kukanta wanda dagani duk na shagwabar ne . tana kallon dakin ahankali har idanunta ya sauka kan hoton data Gani a gefen gadon yasa ta dan fara gane kan abun .
hotonta ne wanda batama san ko wani iri bane " Amman dai ta san tabbas itace .

Abdullah ne yashigo da snacks a plate " ya koma ya kwaso kayan tea da flask , sannan ya duba store din shi .
ya ballo swan water da sauran lemuka guda uku saboda yaji Dr sagir yace ba'a son masu ciki su dinga shan tsanyi.
shiyasa bai debo a fridge ba ,ya kwaso yazo gabanta ya zube yana kokarin hada mata tea ta kalleshi tace Abdullah ina ne nan ka kawo ni?.
Yadda ta fadi maganar a natse" cikin mamaki yasa ya bar abinda yake ya kalleta.
sai kuma yayi murmushi yace gidanmu na kawo nan part dina ne ni dake ta zaro ido tana girgiza masa kai tace dan Allah kayi hakuri ka maidani gidanmu ni tsoro nake ji ta sake barkewa da wani sabon kukan "yayi murmushi
Yace me akayi kuma kike kuka nan fa gidanmu ne , mu kadai ne fa a gidan sai ma'aikata su mami basa nan sun tafi abuja bikin wasu neighbors dinmu shima dady dazu ya tafi daurin aure .
ta karkace kai tana kallonsa idanunta cike da Hawaye ya sake yin murmushi ya tura mata tea daya gama hada mata .
yace Aisha kici abinci Dr yace muna zuwa a nemam miki abinci kici tayi shr tana binsa da Idanu.
yadda tayi shr yaji har cikin ransa tayi mugun bashi tausayi .
ya mike ahankali yana murmushi yace ki sha tea bari nayi wanka rabona da wanka tun awanni tara har nasoma jin ba dadi ajikina.
bata kalleshi ba ballanantana ta amsa wanda shima yasan basamu zaiyi ba murmushi kawai yayi ya shige bathroom .
Tayi shr " wannan wacce irin rayuwa ce sukeyi ita da Abdullah kmr za'a yi kmr baza ayi ba "bata so bata so Abdullah ya sake dawo mata yasa ta a damuwa ta koina ta duba Abdullah ya wuce yadda take zato Abdullah na rayuwa anan Amman yake damuwa daita "da ta fito daga wannan lungun .

Bataso a kuma yin irin ta jiya gara duk yadda za'a yi ta lallabashi ya maida ita gidansu , idan ya maida ita kuwa da ikon Allah ta bar hannushi kennan sai dai ya nemi wata Aishar "duk ta gama tsara yadda zatayi idan ya maidata a ranta .
dan ita a yanzun duk da yace iyayensa basa gidan Amman ita gabadaya a tsorocr take dan alal hakikanin gaskiya tana mugun tsoron mahaifinsa kmr me .
gashi yau zata kwana a cikin gidan da take .
Bai dade ba ya fito kugunsa daure da white towel gashin kirjinsa na kwance suke luf luf luf dasu ga dan karami towel a hannunsa yana goge kansa zuwa tsantsar jikinsa .
Kallo daya tayi, masa ta dauke kanta daga gareshi dan bazata jure kallonsa haka .
"yazo har kusa daita yace "oh" my God this girl won kill me oooo Aisha har yanzu baki ci komai ba ya kalli agogo shadaya saura yace kalla Aisha a kalla kin yi awa takwas baki sawa cikin komai ba.
kina jin kuma abinda Dr ya fada .
Tayi banza dashi sai idanunta data zuba masa yayi dan murmushi iya bakinsa sannan ya zauna gefen gadon kusa daita ya ruko tafin hannuta yace please Aisha kiyi hakuri da komai kici abinci nan karki min haka kinji ta watsa masa harara hade da zame hannunta daga nasa .
tace ni na koshi ya dubeta dakyau yace Aisha yaro cikinki bashi da laifin komai ki tausaya wa bbyn mu dan Allah.
ni nayi miki laifi " to yaya zaki hukunta wanda bai san komai ba " idan kinci shima sai ya samu.
Suna nan zaune a haka har shabiyu ta kusa Amman bata da niyar cin komai.
Ran Abdullah yasoma baci yaji wani abu ya tsaya masa a wuya yana kallonta yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya" tabbas Aisha bata sonshi tunda gashi bata son dansa.
ganinsa muddin bata ci abincin nan ba .
wani abu zai iya faruwa da yaron cikinta .
to abu ne idan akace maka na fari ne anfi rudewa akansa .
sai ya dinga ganin dan bata damu da shi bane shiyasa take son yarasa cikin ,.
shi kuma a halin yanzu ganinsa yake ba wata kadara da ya mallaka da ta kai cikin jikin Aisha
Ya dan kalleta a nutse take kuma fuskarsa ta canza .
ahankali yake magana Aisha na rokeki kada kiyayyata ta shafi dana shi bbu ruwansa bashi ya miki laifi ba.
In kin tashi yin hukunci ni nan zaki hukunta ya nuna kansa da yatsansa yana sake daure fuska.
maganar tazo mata a bazata kuma wani irin da sauri ta dago kanta ta kalleshi shima ita yake kallo sun dan jima suna kallon juna da kyar tasamu ta iya janye idanunta ta sunkuyar da kanta.
batayi magana ba still ahankali Abdullah ya zamo daga kan gado ya zube kasa gabanta .
tana dagowa afrigice ta gashi a durkushe da kofin tea a hannunsa yana miko mata .
taji kmr an zuba mata wani abu ne a jikinta ne. ita wacce da kmr Abdullah zai durkusa mata da sauri tasa hannu ta karbi kofin hannusa ta kai bakinta .
ta fara sha a lokacin guda kwalla ta cika mata idanu.
ya mike ya zauna yana miko mata snacks tana karba cikin sanyi jiki har yayi mamakin abinda taci" bbu wanda yayi magana acikinsu har ta gama ya kwashe kayan ya fita falo.
ya zauna kan kujera yayi shiru yana jin dacin abinda Aisha tamasa ya jima a gurin" sannan yaji abinda ke wuyansa ya wuce.
Yarasa me zai mata aduniya in akwai abinda yafi so da muradin kasancewa tare itace .
iya kokarinsa yana yi "akanta ya runtse idanunshi ya dade Zaune a falo bai shigo bedroom din ba .

tana so tayi wanka saboda kayan jikinta sun dameta "Amman takasa tashi" anan kan gado ta kwanta tana jin ba dadi aranta" shr shr bata ji motsen shigowarsa ba sai har bacci yayi gaba daita.
da safe karfe takwas sai gashi har yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya sai kamshi yake zubawa " ya hawo har kan gadon da take.
Ahankali ta mike zaune tana kallon yanayinsa .
ya zuba mata ido tana so ta gaishe shi Amman tsoro yasa "ta kasa magana "Ko har yanzu yana fushi daita?
ya gane nufin ta dan haka ya lalubo tafin hannuta ya matse cikin nasa" yayi murmushi kadan yace gud morning my dear "yaya bby jiya laifi abbansa ya shafe shi ko ?
Ta dago kai tana kallonsa yace humm ya dan langwabar da kansa yana murmushi" itama kawai sai tsinci kanta da mayar masa tayi murmushi hade da sunkuyar da kanta.
ita duk tunanin abinda tayi masa jiya ya hanata sukuni "sai gashi shi har ya manta ahankali yakira sunanta yace Aisha a jiya nayi tunanin tunda dai har da gaske baki sona baki son zama dani.... .dan haka take taji gabanta yayi wani irin faduwa jikinta ya dauki rawa " har yana jin yadda jikinta ke shaking" Amman share yacigaba da magana yace har gashi ya janyo a jiya mun dan samu matsala dake shine na yanke yi miki abinda zai kwantar miki da hankali zan mayar da ke gurinsu inna har sai kin hakura da laifin da na yi miki" acan zakiyi komai da kike so , kuma shi kansa bbymu sai yafi samun natsuwa " ahankali ta sauke numfashi tana runtse idanunta "dan ba . abinda tayi zato bane.
can hankalinki a kwance yake to yanzu kuma da safen nan munyi waya da dady yace kiyi hakuri "zai dawo yau zaizo da kansa ya baki hakuri.
kada ki tafi ta dago tsumammu idannuta ta zuba masa a tsorace take kallonsa tana girgiza masa kai cikin frigice da nadama take kallonsa kmr zata sa masa kuka "cikin tsanyi murya tace haba Ab..dul..lah me yasa kake min irin haka ni " sai kuma tayi shr ganin yadda ya tsareta da manya idanunshi still hannunsu na cikin juna" yana mammatsa mata yatsunta "ahankali tace ya zaka gayawa dady zai yi magana" ta fara girgiza masa kai" ta fara hawaye tace Abdullah yanzu dan dan wannan abinda ya faru shine zaka gaya masa ya sake riko hannuta Sosai yace ke kike kallon haka Amman tafiyarki ba karamin abu bane wajena.
bbu yadda zanyi ne shiyasa kawai nayi tunanin na mayar dake din "saboda abin ne " ke neman yafi karfina yazanyi da Raina laifina na neman ya jamin maseefar " da zata shafi dana .
Tacigaba da kuka cikin rawar murya tace ni .. Abdullah idan za munyi duk abinda za muyi ,muyi mugama "Amman mu daina sa dady a ciki kawai yana zamansa zamu sako shi" ransa yazo yana baci .
ni dan Allah kayi hakuri kace masa na hakura .
ya sake dubanta sosai ta bashi sha'awa takara kima sosai a idonsa wannan ya nuna cewa tana girmama mahaifinsa "yaji dadi har cikin ransa" ya langwabar da murya yace to shikenan kiyi shiru ki daina kukan tunda kince kin hakura "tayi shiru kmr Jira take yace oya goge hawayen banson ganin su" da sauri tashiga goge fuskarta da bayan hannuta" yasa hannu shima yana kara goge mata" sannan ta kalleshi tace kace yau dady zai dawo , mu kuma fa ? Yace mu ma muna nan part dinmu " ki kwantar da hankalinki kowa part dinsa daban fa, ahankali ya dogota ya mikar daita tsaye" ya kamo hannuta suka shige har ainihin dakinta da dady yasa aka kara saboda ita ,wanda faiza ta lafta kaya ciki" suka shiga ya zaunar daita kan gado yace kinga dakinki ta dinga kallo tana mamaki irin yadda aka tsara dakin hatta kayan shafe duka gasu nan zube akan mirrow "dady yace ya mallaka wa mata komai na dakin tunda da kudinsa aka siya "sai kayan lefen yasa a kwashe yace a zube su a wani guri "zuwa wani lokacin duk zai rabar dasu ( hummmm nace idan da masu so sumin magana oooo😜😜lolz )

Ta juyo tana kallonsa ya dan daga kafadarsa yace idan bai miki ba sai a canza" takasa magana ya mike yana cewa dady zai dawo yau idan bai dawo yau ba "may be sai gobe su dawo tare dasu mami" gabanta ya shiga faduwa ta kira sunansa ya dawo ya tsugunna gabanta yana kallonta cikin murya mai kusa da kuka tace gara mu koma can gidan "ya dubeta sosai yana dan nazarinta ya gano abinda take tsoro yace any way duk inda kike so" na amince in dai muna tare.
kishirya yanzu muyi breakfast sai mu koma can gidan, yasa hannu ya dago habarta yana kallon kwayar idanunta yace gabadaya kwayar idanunki cike suke da tsoro Allah yasa kar wannan tsoro ya taba lafiyar bbyna . Ya koma lip's dinta ya dan tsotsa yana lumlumshe ido yaushe rabon daya ji taushin su "ahankali ya juya ya barta" tana kallon ikon Allah bata tashi a gurin ba sai gashi ya sake shigowa rungume da wasu kaya da jaka ya zube kayan akan bed tsarabar ki na tun tafiyata Denmark kafin muyi aure" na siyo miki sanda na dawo kuma ban samu ganinki ba "sai byn aurenmu ta zuba masa idanunta tana kallonsa sai yanzu ta lura da irin ramar da yayi ya kula da irin kallonsa datake ya dan kashe mata idonsa daya da sauri ta dauke idonta yayi murmushi yace ina jiranki sannan ya fita .


Har suka shiga falon wancan gidan nasu na ainihin aurensu tana lura da yadda yake binta da mayen kallo duk ta tsargu ta damu.
Abdullah yakamo hannuta ya janyota jikinsa atsakiyar falo suka zube kan kujera yana sha cikinta yace kinyi kyau sosai Aisha komai kikasa sai ya dace da jikinki ".
ta zame jikinta ta zauna sosai akan kujera ya dawo ya tsugunna gabanta ya kara zuba mata ido sosai har sai da ta kalleshi "ta dan haharesa kadan yace Aisha ina son zuwa wani guri ta yamutsa fuska ya lura da hakan bazan dade ba " fitar da zanyi ta kamani dole ne shiyasa Amman dan Allah ki kular min da kanki komai akwai na bukata tun jiya akayi clear din komai .

To Abdullah bai dawo gida ba sai byn magriba duk ranta dagule a bace yasameta ko magana ta kasa yi "saboda barinta yayi ita kadai "har yasa tarinka tunanin da sake sake abubuwa da dama a kansa "har tana ganin wautarta na saurin amincewa da zama dashi "saboda ruwa kawai zai sake mayar daita .
A kallon fuskarta da yayi ya gane ya karasa da sauri dan kar ya sake karawa kansa laifi.
dan haka yashiga lallabata hade da rararshinta yadda zata huce Amman taki sauraronsa har lokacin bacci yayi.
Yana falo yana kallonta har ta fito daga wanka cikin kayanta da tabarsu anan" ciki ta zabo night gown lemon Green mai shegen kyau ta saka sabuwce "a ledarta ta bare"ta tana tsaye tana gyara gashin kanta yadda zata ji dadin kwanciya "Abdullah ya shigo yadda ya ganta haka yayi mugun kaduwa hankalinsa ya tashi matukar" rigar bbu abinda ta boye na jikinta in ka debe White pant dinta dayake Gani Amman hatta kirjinta da nipply dinta bubu abinda bai bayyana ba "shi duk kyau da yaga ta kara bai kara tabbatarwa kansa ba sai yanzu "komai nata ya canza ta kara cika hatta kirjinta sun cika sunyi suntuma suntuma dasu gasu tsaye cak suna tsokanoshi .
ganin ya tsaya yana kallonta yasa ta zauna tacigaba da hada ragowar kayan fuskarta daure bbu walwala ita kanta bata san yadda rigar tayi mata ajiki ba shiyasa ma tayi zamanta bata wani damu ba.
kafarsa yaji kmr bazata dauke shi ba" gashi kuma yanayin fuskarta kmr tana gargadinsa da zuwa gareta .
dan haka ya ja baya baya ahankali ya koma kan kujera a falo ya takure jikinsa shi kadai yasan abinda yake ji a tsantsar jikinsa nan ya kwanta a takure bai iya dawo mata ba.
saboda ya gane gaf take da karasa rushe masa byn ya sha bakar wuyar wajen lallabata .

Da safe ya sameta har daki byn sunyi breakfast ya zauna kusa daita har cinyoyinsa na gogar nata wani irin shock taji ajikinta jummmmmmm ahankali yace madam naga har yanzu kmr ba'a huce da Abdullah ba. Ya kama kunnesa da hannushi duka yana bata hakuri
Yace kiyi hakuri Abdullah baya jin magana Amman amishi afuwa ba zai kara ba .
still tana zauneshr bata ce komai ba Amman fuskarta ba kmr jiya ba ya sake marairaice murya please now yace jiya naje gurinsu baba ne akan maganar tashinsu daga wannan gidan wanda tun shekaranjiya dama na rigada nayi masa maganar zanje jiya da mota" domin a kwashe su zuwa sabon gida .
Ta dago dara daran idanunta tana kallonsa da mamakinta yace Aisha ni a tunanina mun rigada mun zama daya Amman karki ga yadda nayi dasu baba sannan ya yarda ya amince wai mutane zasu zagesu.
kuma shi yarigada ya saba da unguwar koda muka zo gidan ma baba cewa yayi shi bai san da zance wani gida ba byn wanda kikace kin basu na sadakin ki .
nace wannan kyautarkice daban wannan kuwa tawa ce shima da kyar ya yarda su inna sai kusan magariba salis ya koma ya taho dasu ,shiyasa kikaga na dade Amman komai an siya an sa duk a gidan" sai wasu kujeru da za'a zuba a dakunan su yusif sune yau salis zai koma yakarasa sawa.

Ta dinga kallonsa abin yana tsumata.
me Abdullah ke nufi ya canza wa iyayenta gida Amman tun jiya ya barta tana fushi dashi kan yayi tafiyarsa ya barta.
ta dinga girgiza kai tana kallonsa idanunta ya soma cikowa da Hawaye Tama kasa magana yace dan Allah kiyi hakuri kar kiyi kuka nan , dan yin kuka bai wuya a gurinki.

Batasan sanda ta fada jikinsa ba ta rungumeshi shima matseta yayi tsam tsam ajikinsa yana busa mata iskar bakinshi sannu ahankali ya dago fuskarta yana goge mata hawayen dake silalowa ganin yadda yake mata yasa ta kara sakin kukan ya sake manneta da kirjinsa yana rararshinta ahankali take yin kukanta yasa hannushi yana shafa gashin kanta yana mammatsa mata jiki bata kula ba har sanda taji ya fara zame rigar jikinta sannan ta janye jikinta ta mike ya kamo hannuta yace please kiyi hakuri ki taimakawa min Abdullah bashida inda zai je yasamu ya fadi haka da kyar muryasa a sarke gabadaya yanayinsa ya sauya ..


MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗


AISHA A BAGUDO


Page 71-72


Watannisu biyu kennan a Denmark har a lokacin Abdullah yana cikin tsantsar farinciki dan kullum sunayi waya dady kuma yana nuna masa mami tana samun sauki sosai akan da .
To har kusan awa daya suna maganar ta a halin yanzu mami ba sallah ba har azumi tana yi koda yaushe.
dady yace Abdullah ka kara addu'a komai yazo karshe inshallahu koma ya Kare za'ace .. .
Abdullah dake kwance kasa kan kafet inda Aisha ke zaune turus da ciki tana tacin soyayyiyar plantain.
yayi murmushi a filli ya kalleta yace Aisha shi fa dady duk ya damu da zance haihuwar nan cewa yayi shi dabadan zan jima anan ba da can zan baroki .

Aisha kuwa murmushi tayi dan duk abinda zai sako dady ko mami ciki sai dai tayi murmushi ta sunkuyar da kanta .
hakan yasa itama ta tuna da innarta .
Lokacin da sukaje musu sallama haka tace Abdullah ya kallonta kunyar dadinsa take

Please Login or Register in order to submit comment