Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lalace ,yayi duhu tamkar majinyaci shekara guda .
Abdullah bai iya jan su ba sai Dr sagir ne yayi tukin shi da suna baya .

Bbu wanda yasan da dawowar dady a yau hatta shi kansa Abdullah bai sani ba sai da dadin ya nemishi a waya .
dan haka tun daga bakin get masu gadi gidan kowa ya fara yashiga taitayinsa .
duk da ita kanta mamin bata cikin cikakken haiyacinta Amman sai da dawowar dady ya dan tsorata .
bbu wani abu daya nuna na cewar yasan abinda ake ciki to sannan ne yake tambayar Abdullah ya nuna masa shi baya shiga part din kwata kwata .
ya dubi mami da ta shigo yana son karin haske cikin dakewa zuciya mami tayi masa bayanin halin da ake ciki har da bayanin a yau faiza ta tafi sokoto Amman jibi idan aka daura aure zata dawo.
ga mamakin dukkansu har ita har Abdullah din dady bai ce komai ba illa yace ai yayi kyau zumunci zaki hada .

Ya dubi Abdullah kai yanzu ina kake kwana kennan Abdullah yace a gidan baki dady ya sake maimaitawa Abdullah ya amsa haka ne .
mami tace ai key din part dinsa sunan hannu teema faiza ta bata ajiya dazata wuce abin ya sake bashi mamaki .

Dady yayi shr yana kallon mami ita kuwa ko gezau batayi ba .
sai ma ta tashi tayi ficewarta ,dady bai yi mata magana ba Abdullaha ma ya mike ,zai fita dady yace ya koma ya zauna sannan dady yanemi wayar side din su teema ya kirawo bayan yan mintina kadan sai gata ta sake shigowa a tun dazu da suka zo yi masa sannu da zuwa.
bai ce mata komai ba. Baya ga tambayar ta key part din Abdullah da akace yana gunta .
taje ta dauko ta dawo nan falon dady Abdullah yasa hannu zai karba Amman dady yace A'a .
ta Miko masa ya karba yace shikenan teema gud nig .
tana fita ya dawo da kallonsa kan Abdullah yace yashiga nan part dinsa ai akwai dakuna ya zabi duk wanda yayi masa ya kwanta a ciki.
Abdullah bai gane yadda Dady yake nufi ba iya tunaninsa shi dady zai bawa key part din nasa ya tafi can ya kwanta.
Amman sai yaga zura su cikin aljihun gaban doguwar rigar dake jikinsa.
Abdullah ya mike jiki a sanyaye yabi dakunan dake bangaren hagu da part din dady yake kwana ya shige ciki.


Har gari ya waye dady bai runtsa ba .
ita kanta mamin bata sake neman sa ba a daren tunda tabar part din nasa .
da safe abubuwa suka cigaba da daurewa dady kai a game da mami .
ita dai kawai hidimar biki take gobe daurin auren.

har Abdullah yazo ya gaishe shi ya sake ficewa gidan baki bai ce masa komai ba baya ga amsa gaisuwar da yayi.

Dama can ya kan dan zazzaga ma'aikatan gida lokacin zuwa lokacin to yau ma haka ce takasance tin karfe goma ya fito daga part dinsa .
gabadaya environment din gidan yayi clear.
tun asuban fari dan haka daga nan gidan baki ya wuce .

Har yammaci ranar bai shigo gidan ba mami kuma bata nemeshi ba shi .
kansa Abdullah bai ji wani abu daga dad din nasa ba.
dan haka shima office yayi wucewarsa yayi zamansa dan yadda yaga fuskar dady yau ko magana baya son yayi.
shi ma acan ya yini duk da anan hutu gobe daurin auren manager koda Dr sagir yazo nenanshi shima sai can ya sameshi .

Amman shi Abdullah ya kosa koma me zai faru gara ya faru dan ya riga yasan halin dadinsa.
idan yayi irin wannan shr to idan bom din yashi fashewa kowa sai ya shafa.
duk da yace ya hakura da Aisha zai iya yi rayuwar Sa haka ko ba macce.
Amman itama yakagu yaji abinda dady zaice a game daita.
duk da yaci alkawari n dady .
bai nemeta ba har gashi dadin yadawo kusan kwanaki dari da yan kwanaki kennan da rabuwarsu Amman har yau yana zaman jiran dady yaji abinda zai ce a kanta .


Da yammacin baki suka karaso daga abuja mawaftansu na can abuja wanda mami ta wakilta su zasu je a matsayin waliyan Abdullah.
hannu biyu biyu dady ya sauke su .
a gidan baki ganin su duk yadada tada hankali Abdullah shi dai yasan muddin ya auri faiza to yayi alkawari yabar Aisha kennan .
itama faiza baizaiyi rayuwa daita ba dan haka kasa zama yayi acikinsu dole yabar gurin duk da dady yana lura da halin daya shiga.

Aranar ma dady cewa Abdullah yayi ya kwana a inda ya kwana jiya.

Abdullah ya nemi su danyi magana har yana koro masa maganar mutane daya kora a company Amman dady ya daga masa hannu yace yaje ya kwanta .
zai neme shi akan hakan cikin sanyi jiki Abdullah yatashi ya barshi .
Amman a ranar shima kasa runtsawa yayi shi kadai yasan irin yadda ya dinga ji a jikinsa



Washegari garin ranar jumma'a kennan da yakama daurin auren Abdullah da faiza.
tun da safe da Abdullah ya shigo falon dady .
kallo daya dady yayi masa ya gane halin dayake ciki Amman har a lokacin bai ce dashi komai ba.
duk da yasan halin dady Amman har yashiga mamakinsa a ransa" Abdullah yayi dan Jim ....yana Jira ko dady zaice masa wani abu sai dai bai ji komai ba.
sai da zai tashi ya fita ne dady yace yabashi duka wayoyinsa Abdullah ya dago yana kallonsa da kansa yanuna masa alamun haka yake nufi.
Abdullah ya kwaso su duka ya mikawa masa sannan ya fita karfe takwas shima dady ya kulle koina na part dinsa ya fita gidan baki can ya iske Abdullah ..
Abdullah ya kwaso abinda za'a bada amatsayin sadakin faiza ya mikawa dady .
,dady ya jima yana jujjuyasu yana mamaki sabon halin da mami ta daukarwa kanta .
Abdullah ya nuna masa yadda mami tace ayi kennan.
dady ya girgiza kai kawai Abdullah ya fito zai shiga part din dady Amman yaga koina a kulle gashi part dinsa dady ya karbe key.

makullan gidansu da Aisha suma suna part dinsa na nan.
gashi dan gidan bakin dayake zuwa yana dan hutawa shima su dady suna ciki da baki .
yarasa ma ina zashi yayi tunanin tunda yarasa Aisharsa a yanzu duk abinda ya rasa sai yaji tamkar bbu wani damuwa a yanzu ko cewa akayi ya dinga kwana byn masallaci zai iya .

Tunanin yayi ya wuce office ya kwanta ya kulle kansa kawai.
dan haka ya sanarwa dady inda ya tafi koda za'a nemeshi .
tunda yaji mami tace tana son lallai idan an sauko za'a daura aure.

can ya yini daga shi sai salis sai ko tsirrarun ma'aikata.
har byn sallah la'asar sannan yayi tunanin ko dady ya masa guzirin ne shi ya zauna inyaso su sa tafi sokoto daurin auren .

Mami kuwa tun safen ranar ta kasa zaune ta kasa tsaye ba Abdullah ba dadinsa duk wayoyin Abdullah data nema duka a kashe suke.
ta aika gidan baki yafi sau goma bbu baki bbu Abdullah bare dady.
itama har yamma takasa sanin tudun dafawa dan ko har dady tanema a waya bata sameshi ba.
ga part dinsa koina a kulle.
sai kusan magariba sannan shima Abdullah ya baro company yasamu sallah a masallaci cikin gidan a sahu na karshe.
dan haka shine ya fara fitowa ,yayi gaba kadan musa driver ya karaso da sauri yana gaya masa dady yace ya jirashi to shima dadin din yake son Gani dan bbu waya ne a hannunsa .
da tun dazu ya nemeshi tare suka koma har part din dady suka ci abinci dady ya fara shirin yiwa Abdullah bayanin kennan .
sai ga mami tamkar anjihota tana tambayar ya batun daurin aure?dady ya zuba mata ido kmr me shirin shiga iska sannan yace tasamu waje ta zauna .
da kyar ta zauna din shi kuwa Abdullah kansa a sunkuye yake yana zaune kan karfet .

Dady ya dubi mami da kyau yace maganar daurin auren na dageta daga yau.
kuma na sallami kowa kmr yadda kika amincewa Abdullah to haka itama yarinyar da iyayenta sai naji daga garesu na farko kennan
tunda shi kika soma nema .

abu na biyu kuma nagode nagode da wulakanta min diyar yar'uwata da kikayi .
abunda ni bazan taba yi miki ba kennan har duniya ta nade a tunanina yarinyar ko b daga jinin take ba yakamata mata ki mutuntata
A saboda tana auren danki .
Amman duk na gode .
abu na karshe kuma da zan sanar miki yarinyar da kikayi kokarin raba Abdullah daita.
to ina yi miki albishir itace zata fara kawo miki jika a gidan nan .

Gabadayansu suka soma kallon dady ,dady yana murmushi sosai ya kalli Abdullah yace Aisha na dauke da ciki tun lokacin da kuka rabu .
haka tazu iyayenta suka bani tabbacin "sanda tabar hannuka ciki dake tare daita bai kai wata ba zuwa yanzu abinda da ake hasashe cikin ya shiga wata hudu .

Sauran kadan Abdullah ya narke a zaune a gurin saboda yadda yarinji a jikinsa.
hawaye ya fara zubo masa yana kallon dady da mami duk a lokacin daya.
fuskarsa ta nanu kmr ba daidai yaji abinda yace ba.
sai Kuma ya dinga murmushi yana zubda hawaye .
duka abubuwa masu mahimmanci a lokacin guda .
dady ya kalleshi yana masa murmushi shima dan tsabar abin farinciki da yajiyo ne yasa shi manta bakincikin abinda mami tayi masa . Kuma
ya fita a zuciyarsa .

Mami kuwa ta hade fuska tamau dan ita maganar takaici ta kara mata .
ta cewa dady ni ga abinda nake son ji takamaimai Amman ka fara min wata magana can .
Abdullah ya juyo yana kallon bakin mami tace shikenan hujjarka ta hanawa a daura aure a yau.
kana son mama hafsa tace banyi mata ba daidai ba kennan .
dady ya kalli Abdullah yace shikenan Abdullah zakana iya tafiya abunka .
sai na nemeka Abdullah ya mike dady ya kwaso wayoyinsa ya bashi .

har kusan tara na daren ranar mami na tare da dady tamkar wacce ranta zai fita daga jikinta tana fadan akan hana daurin auren dady yayi .
ita ba ma kowa take ji ba cikin al'amarin sai mama hafsa .
abinda ya kara girgiza dady kennan .
yadda take maganar cikin tsanyewar zuciya tana kuma fada masa duk abinda yazo bakinta kmr ba mijin ta ba .
yasan ta sosai tsahon shekaru da suka kwasa tare .
Amman bai santa da hakan ba.
ransa idan yayi dubu to duk yayi kaca kaca ya baci ya dubi mami sosai yace aure tsakanin Abdullah da yarinyar nan na haramta shi .
sai dai bayn raina mace daya na amince masa itace yarinyar da kika sa shi ya rabu daita sai dai kuma idan daga baya shi yayi ra'ayi dan kansa .
idan har da wani abu da zai faru to ni ishaq ina jiransa .
gashi nan ubangiji yana shirin nuna miki ikonsa a jikin yarinya .
Amman kin zauna kina hakilon banza.
dan haka duk abinda zai faru ya faru Allah yasa yankaki hafsa zatayi akan rashin yin auren to Bismillah.

Maganar ta Sosa ran mami matuka fiyye da tunanin mai karatu.
dan haka itama ta rinka fadar magana iya yadda zata huce.
ta kara da cewa randa duk mama hafsa ta tako gidan nan dole ayi wacce za'a yi .
Kuma wlh dole dole ayi yadda take so a karshen ta cewa dady kuma bazata taba amincewa da wasu can su lakawa Abdullah cikin banza ba.
byn ya rabu da yarinya sama da wata uku a dawo ace wai ciki gareta me yasa tun lokacin basu fadi hakan ba sai a yanzu .
mami tana huci ta kada kai ta bar part din dady ya zubawa kofar data fita ido "ko kwakwaran motse kasawa yayi.
saboda dacin da yake ji na bacin rai a wuyansa idansa yayi jawur tamkar zasu fito.
me yake shirin faruwa ne dashi da rayuwar gidan nasa .
yana nan zaune har tsawon mintina talatin bai bar gurin ba teema ce tashigo ta kofar da mami ta fita..
tana yi tana kallon bayanta .
kallon ta dady yayi .
Ya jima sannan ya dan hadiye miyo mai dacin daya tsaya masa a makoshi.
yace yaya dai teema .
Teema takaraso kusa dashi ta zauna.
yana kallonta Tace dady mami ce sai kwalla ta fara cika mata ido yace ya isa meyafaru da mamin ?
teema Tace dady kwata kwata mami ba ita bace ba yanzu .
kowama baya gabanta a yanzu .
dady mami bata da ra'ayin kanta a yanzu ta sake fashewa da wani kukan.

Dady ya rufe idonsa sai da ya barta ta danyi kukan sannan ya dakatar daita .
teema ta dan goge hawaye .
ta dan sharbe majina tace abin tsoro ma dady mami fa yanzu ko ibadarta bata gabanta sai tayi kwana biyu ko uku batayi ba.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun abinda dady yake fada a ransa kennan yana cikin tashin hankali abinda mami ta gama yi masa a dazu .
sai ga teema tazo da wani "duk akan mami ya zubawa teema ido kawai ya kasa magana "yasan teema da natsuwa ya Kuma san yadda suke da mami.
koma meye zata iya fahimta.
tace na kula da haka sosai yanzu ibada ba a gabanta take ba .
ita dai a yanzu duk yadda zatayi ta farantawa wannan mama hafsa shitakeyi .

Teema ta dan kalli kofar data shigo ta rage murya sosai.
sannan ta kara matsowa kusa da dady tace ni dady ko wani hali mami take ciki ina ganin akwai sa hannu wannan mama hafsa din.
tana da alhakin a ciki saboda ranan nan naji tana cewa mami wai iyayen aunty Aisha sun mata asiri ita da brother Abdullah .
dan haka ta kawo wani abu tabata tace shi zata dinga garwashi tana turara jikinta dashi kullum .
Brother Abdullah kuwa ta bayar da wani abu baki a Leda wai a dinga masa abinci dashi .
wai duk asirin daaka musu zai karye.
kuma ta dinga jadadda mata sosai tayi kada tayi kuskure yin haka .
mami ta dinga yi wani lokacin ita mama hafsa da kanta ke karba tayi mata .

Dady ya zubawa teema ido sanda ta dago tana kallonsa yace Allah dai yasa teema ba labewa tayi ba ta ji abinda iyayenta sukeyi ba .

atsorace ta kalleshi idonta cike da Hawaye tace wlh dady ba labe nayi musu ba .
ita mama hafsa din ce idan tana yin wani abun sai kaga kmr bata Gani.
duk abinda zatayi wani lokacin muna gurin zatayi .
Amman wannan da naji din ma ina bedroom din mami ne "a kwance ta shigo ta Sami mami ta dauka ko ina bacci ne .
take gaya mata ahankali.
rannan kuma ina wanka ta hawo da sauri take cewa faiza wai ta zubawa brother Abdullah din maganin kuwa gashi can za'a tafi kai masa abinci "tasan ance kada maganin ya wuce jiya zuwa yau da rana.
ban ji abinda faizar tace mata ba.
Sai dai naji sun canza magana .
dady yace na dauka labe kika tsaya yi musu yace dan bbu kyau musamman ma idan iyaye ne.
tace A'A wlh yace to shikenan kuyi hakuri duk zan san abin yi in Allah yaso .
komai zai gyaru kinji .
Ta amsa ta tashi tana fita .
dady ya rike gefen hakarkarinsa ya Kuma dafe kirjinsa.
ya mike da kyar ya shiga bedroom dinsa ya zauna a gefen gado ya jawo durowa yana dudduba magungunansa .
ya sha wani bai iya kai hannushi ya dauko ba dan haka ya hakura ya kwanta dan ya dan huta ya dafe kirjinsa sosai da yake bugawa .


Abdullah kuwa yana fitowa daga part din dady salis ya tareshi "ga Dr sagir yazo yana nemansa "da hanzari ya karasa inda yake gabadaya ya rike hannuwan Dr sagir yana dariya.


Wow Abdullah yi dariya cike da farinciki yau ranarka ce 😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃




MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page 65


Gabadaya ya rike hannuwan Dr sagir yana dariya.
yace doctor na taba gaya maka nayi mafarkin ni da Aisha muna tsakiyar macizai sun kewayemu" har wani me kyalli a cikinsu ya howa kaina ya sauka ya koma jikin Aisha daga nan na farka.
sau uku ana gaya min wadannan macizan dana Gani ya'ya ne..
gashi nafara jin kamshin cikin sananin farinciki yace doctor doctor doctor Aisha ciki gareta tunda muka rabu ban sani ba.

Dr sagir ya kalleshi da kyau yace friend waya gaya maka hakan?
yace dady bai je min daurin auren faiza ba.

sai yaje min bikon Aisha ya tarar ashe tana dauke da cikina .
Gabadaya shima Dr sagir hannuwansa ya jawo suka rungume juna suna murna.
Abdullah yace doctor kaima kana farinciki ko?
Dr sagir ya kasa magana sai dai yarinka girgiza masa kai .
sai da suka saki juna sannan Dr sagir ya sake miko hannu yace congrat...

Abdullah yace thank you doctor muje nayi sallar isha'i ka rakani gurinta yanzu zanje "bazan bari na kwana ban ganta ba
Dr sagir ya sake kallon.

Sai Abdullah ya idar da sallah ne Dr sagir yace friend ka bari zuwa gobe mana ,sai aje da manya Abdullah yace in mutu kennan.
Dr sagir yasa dariya yace baza ka mutu ba baban bby .
Abdullah ya mike ai maganar manya takare nima yanzu babba ne tunda zan zama uba.

Suka yi dariya ,Abdullah na kokarin fitowa Dr sagir yace are you serious friend zuwa zakayi .
ko ka manta sakin Aisha kayi Abdullah ya dago da sauri ya kalleshi Dr sagir ya amsa masa da haka ne ,"sannan ya Kuma cewa tsawon watanni kun rabu ka barta da ciki baka nemeta ba sannan yanzu kaje mata karfe tara na dare nasan abune mawuyaci ta kalleka.
idan da manya aciki sai a hadu a sulhunta.
a sake sabon aure jikin Abdullah ya danyi sanyi Dr sagir yace wlh gara ka kwana yau kana addu'a Allah yasa ba tayi fushi da kai mai tsanani ba .
,kaga gobe sai ka lallaba kuje da dady ma zaifi.

Har Dr sagir ya bar shi zuciyarsa natayi masa wasi wasi 'sau Tari idan wani abu na farinciki zai same shi sai garin ya daure masa" daga baya ya tsinke masa da alkhari.
tsawon watanni da yayi cikin ukubar rashinta har zuwa yau din .
daya zamanto inda zaije ya huta ma ya rasa a karshe gashi ya juye masa alkhari "zai zama uba nan da dan wani lokacin .
dan haka yasan koyaje da kyar in zai ji ko yaga wani abu na bacin zuciya .
dan haka ya murza sitiyarin motar sa shi kadai dan salis yariga yatashi daga aiki.

Amman har yashiga lungun gidansu shi kadai a kafa "ya tuna da wani ido zai kalli mlm abu" sai yau yake zuwa garesu cak yaja ya tsaya ya kasa karasawa .
gara zuwa da dadinsa zai fi har ya juya yaji yakasa tafiya ,nan yasamu jikin bango ya rabe" yana hango kofar gidan .
yana tuna akwai kadararsa a ciki "yana nan tsaye har yayyenta guda biyu suka zo suka shige gidan .
sannan ya hakura ya tafi duk da bai ganta ba Amman zuciyarsa ta masa dadi .
Yau ko ba komai zaiyi kwanan farinciki .
bayan yayi sallolin da ba zai iya kayyadewa ba .

Karfe shida wayar dady ta sameshi yana jiransa Abdullah yaisa cikin bedroom dinsa ya sameshi har zuwa lokacin yana kan abun sallar sa .
,cikin farinciki kmr yadda yaga dady ya karasa ya gaisheshi "dady ya karasa jan carbi sannan ya amsa "ya nuna masa nan kusa dashi da hannushi.

Abdullah ya matso ya zauna inda ya nuna masa cikin fara'a dady yace Abdullah Amman kayiwa Allah godeya da zai azurtaka da zuria ko Abdullah ya girgiza kai yana murmushi shima dadin dariya yayi .
yace a to dan nima tun jiya nake godiya ga Allah zai kara mu zuria a cikin gidana .
Abdullah baice komai ba illa murmushi daya sake. dady ya numfasa yace abinda yasa na nemeka tun yanzu nasan zakayi mamaki akan wannan Batun kuma ne yuwa zakaji wani bakon abu.
wanda ba mamaki bazai maka dadi ba .
kada ka taba sanya damuwa ko shakku a game da abinda ke jikin yarinyar nan Aisha .
ni dai na amince tabbas cikin dake jikinta na cikin gidan ne.
tun rabuwarku akwai wanda nayi waya na dora akan lamarin, to har likitan daya dubata na kwana uku da rabuwarku sai daya yayi min.
bayanin adadin kwanakin cikin dake tare daita a jiya.
dan haka komai maminka zata ce maka ka saurareta ne kawai ka amsa mata .
Amman kar ka bari maganar ta tayi tasiri agunka .
Abdullah ya daga kai dady yace Allah yayi muku albarka Amin Abdullah yakasa tashi daga gurin, dady ya fahimci yana son wani abu ne" yace uhm ina jinka da kyar Abdullah yace dady ita Aisha fa .

Dady ya kalleshi ya sake murmushi yace wannan Kuma ai ya rage tsakaninku ni tunda ma naji zance cikin "ban kara dora komai akai ba .
saboda har yanzu Aisha tana nan matsayin matarka .
tunda saki daya ne akayi dan haka ko a yanzu kace ka mayar da ita ta mayu.
tunda batayi Idda ba to auren ya mayu" Abdullah ya dinga yi masa kallon da gaske ?dady yacigaba abu daya ne nasan za'a samu yan tangarda wajen komarwata ko daga gun iyayenta ko ita kanta yarinyar .
wannan ne abinda nake son komawa na samesu sai dai tsakanin yau da gobe ina gida bana son fita koina ,saboda akwai abinda zan Jira Amman ko a yau na samu yadda nake so zan iya zuwa na sake nemansu naji yadda za'a yi dan gaskiya dai a musu ba daidai ba .

Abdullah ya dan yi murmushi jin dadi yace thank you my dad sannan ya tashi ya fita .

Dady ya bishi da kallo shima yana murmushi fitowar Abdullah kuwa ya fadi ya mayar da Aisha yafi sau dari a fili da cikin zuciyarsa.

Bayan kmr awa uku dady ya sake Nemo mami koda ta shigo fuskar nan a hade tamkar hadari ,shi kuwa anasa ya sake fuska sosai tamkar bbu wani abu a kasa .
byn gaisuwar datayi da kyar yace akan maganar da mukayi jiya ne duk na fahimci abinda kike so nima kuma dana yi tunani sai naga dacewar hakan "a tsakanin yaran dan ko ba komai hanya ce ta karfafa zumunci .

Mami da dago da sauri ta kalleshi da kyau tasan abu ne mawuyaci idan ya hau ya sauko da wuri. Dan dady ya sake bata haske sosai yace kinga ita hafsa tun ba yau ba take sonki "dan ta so hada diyarta da danki wannan ai ba aibu ne abu ne mai kyau "ina ganin Karin so ne ya kawo haka..
Mami ta saki fuska tace abinda nake son ka fahimta "kennan yanzu
jiya da ba'a je daurin auren nan ba" nasan duk laifina hafsa zata Gani .
ko meye ma nasan a kaina zai Kare .
dady ya kura mata idanunshi ya tabbatar da abinda yake zarge akan mamin "sannan ya dauke idanunshi yace duk ba wani abu da zai faru ,yanzu dai nasan me yiwuwa, su daga can zasu so jin abinda ya dakatar da zuwa daurin auren.
to kawai sai ace shirye shiryen bikin ne aka canza kinga akwai bukatar kayayyakin al'ada na auren .
duk naga anayi kuma suma zasu" bukaci wani abu ko ba haka ba" yana dan duban inda mami ke zaune .
Mami tace ai komai

Please Login or Register in order to submit comment