Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna tsantsar bacin rai mlm abu ya dubi Aisha yace yayi kyau da abinda kikayi ina son da hannuki ki koma ki kwashe kayan da kika watsar .yashiga daki ,zuwa jimawa ya fito da abin sallah a hannusa bai sake ce mata komai ba ya fita ransa a bace "tabbas ta manta yau jama'a babanta yana dawowa Sha daya zuwa Shabiyu"ya sake fita saboda masallaci banda haka da tuni ta kwashe kayan kafin yazo,dan haka gabadaya a tsorace take ganin yadda ran baba yake a bace ,tun hadiza bata kai haka take son yarinyar saboda surutunta yana bata dariya ,anan makotansu take,gashi yau surutun hadiza bai Yi mata rana b.tun bayan saukowa daga masallaci yake daki bai fito koina ba ,haka nan salis ma cewa yayi yaje har sai ya nemeshi ,yasan Daddy ma bazai bukace shi a yanzu ba don haka ya kashe duka wayoyinsa hakan yabashi daman tariyo abinda da yafaru a dazu ,me sanya Aisha zata yiwa soyayyrshi mummunan fahimta ,shi da kansa ya amincewa kansa tun ranar da idanunshi suka fara ganinta har zuwa yau bai taba koda kallon dan yatsanta yaba sha'awa irin wacce ita Aisha ke nufi ba,sai dai ya kalla bashi Sha'awa irin ta birgewa wanda so ne kadai ke kawa haka Kuma koda ya aiyana wani abu da ita yakan kaddara wa sai sunyi aure , to Amman duk ya gane abunda take nufi da shi yana tattare da rashin son take masa"ya runtse idanunshi gam yanajin wani radadi na ratsa ilahirin jikinsa tare da fadin dole in hakura dake Aisha tunda da gaske kike bakya Dona,cigaba sonki zai sa in cutar da zuciyarki sannan ya bude idanunshi da suka gama rikedewa suka koma ja "Amman zan samu Dr sagir .wayar landline dake bedside dinshi ita ta katse daga duniyar tunani yana dagawa muryar teema ce ke cewa bros mami tace ko kana nan ,an Yi checking dinka a handset baa sameka ba . yace na dan kwanta ne tana son ganina ne yanzu?teema ta amsa da Eh yace OK am coming duk da yanayin sanyin garin ,sanye yake cikin karamar riga baka da kadan hannuta ta sauko kafadarsa hakan nan takama jikinsa sai bakin wando jeans shigar ta kara fiddo masa da sigarsa ta cikakken "da" namiji gashin kan nan sa ya kwanta luf kmr koda yaushe saboda gyaran dayake samu akai akai" cikin takun nan nasa mai birge duk wanda yakallesa Abdullah yashiga part din maminsa ,a falo ya sameta tare da kannesa sai bakuwar dayaga sunyi " yasamu waje ya zauna tare da daukar remot control yafara dadfanawa minal ce taajiye masa farfesun hanta da apply juice wanda mami da kanta tayi masa ,ta matso masa da stool gabansa ta zuba masa sannan suka fita dama unguwa za'a kaisu mami ta kalleshi ta jiho masa tambaya halan wani abu ke damunka yadan kalli mami kadan yace noting na dai gaji ne , bakuwar ta matso ta gaisheshi ya amsa batare da ya kalli inda take ba" mami tayi murmushi tace faiza kennan daga sokoto tun wajen daya ta sauka"Abdullah ya dan yadan kalli faiza ta kasan idanunshi"Wanda ita tun shigowarsa ta kafa masa ido , ya tabe baki ya mai da kansa gafe shi sai yanzu ya gane kallon da take masa tun shigowarsa ,wato itace mami ke son ya aura diyar mama hafsa ,a kalla zata girmewa teema haka kawai yaji bai son yawan kallon datake binsa dashi yaji duk yatsani wajen cikin shagwaba wanda shi bai ma San yanayi ba yace mami ina son inje in ga Dr sagir ,ya fada tare da duba agogon farin gold dake hannushi .namu tace to baka ci abinda aka kawo maka yadan can ciza lip's dinshi yace bazan iya ci ba kuyi dinner da ni aransa yace yaushe zan iya cin wani abu bayan akafe ni da mugun kallo mami tace mekaci ya lashi basasun lebensa yace coffee tace coffee ba abinci bane ok mami indawo zanci yafadi haka tare da Mikewa yayin da faiza ta bishi da Ido tamkar kura taga nama ita duk yadda ta dauki Abdullah din sai taga yafi haka har yawuce da tunanin ta ,bata taba mafarkin zata samu irin sa ba ,yadda take ji ta a yanzu koda Abdullah bai da kowa da komai a duniya kyaunsa ya ishe ta haka daga ganin sa zai iya irin soyayyar datake mafarkin samu "mami ce ta katse ta tace karki damu yanayin sa haka idan yaga yana bukatar hutu .faiza tadanyi murmushin hade da sunkuyar da kai don ita har ta manta mami na zaune agun dan ta shagala da kallon danta .

Duk da abunda Aisha tayi masa ya bata masa rai matuka Amman sai tsinci kansa da kasa gayawa Dr sagir dukkan abinda tayi mada illa ya nuna maganganun da ta furta gareshi sune bai ji dadinsu ba Dr sagir ya numfasa yayi murmushin yace kasan mata fa koda suna sanka sai sun maka wannan borin na farkon balle ita Aisha abun a tsaya aduba lamarinta Kuma su mata suna son arinka fada musu kalmar so kai kuma sai dan banzar girman kan tsiya,ka kasa tsayawa ka sanarwa yarinyar karama damuwarka ,shi kace kana sonta shine aiki ok kabari ni zan rakaka inyaso sai sanar mata saboda ni nasan irin kamun data maka dan haka zance ka hakura duk bata taso ba "Abdullah ya aiko masa da harara shima ya rama , Dr sagir yayi dariya yace wallahi kayi mugun kamuwa Amman abunda nike so yanzu kadan bata hutu zuwa wani lokaci.dan ni gobe early in the morning zan wuce sokoto da ni da kaina zanje gurinta muyi arba ,har yau bamu taba haduwa ba,sai dai idan na dawo a hankali Abdullah yasauke hadiyar zuciya yace inga hakan zaifi kawai yana mai runtse idanunshi dan rashin ta tare dashi ba karamin illa bane" a kan haka suka Yi sallama .
Tara saura kwata na dare bayan yayi wanka ya nufi part din maminsa har yakusan shiga ko me ya tuna kawai ya juya ya koma part dinsa yayi teema waya ta hado masa abincinsa takawo masa ta amsa da to mami dake kinshingide a falon tana dan gyangyadi ta wartseke tace ke sake kiransa kodai jikin ne naga dazu kmr wani abu na dakinsa mami ta karbi wayar take tambayar lafiya yake ,tunda yace akawo masa abincinsa,ya amsa da lafiya sa lau tace sam bata yarda ba sai da Abdullah ya rantse mata da lafiyarsa kalau sannan ta yarda .

Abangaren bakuwa faiza kuwa duk kwakwa da kulafucin son ta sake ganin Abdullah a wannan dare hakan bai samu ba dole ta hakura tabarwa safiya .daga shi sai short niker sai white singlet yake faman motsa jiki yana gamawa gudu gudu sauri sauri yaje ya dawo sannan ya dinga daga karfen motsa jiki yana ajiyewa daga karshe ya zube akasan gress carfet ya ajiye karfen yana hali (kabar muna gida kada ma wani yazo yazaci nima irinka ce ) maganar tace take ta masa yawo akai yasa kafa ya Ture weight lift sannan ya rigingina ya runtse yanasake tunanin maganganun ta gareshi (kayi kuskuren idan kana tunanin zantaba sonka ) yasa hannushi duka ya dafe kansa .salis da sauri ya karaso gareshi shi kadai ya dan fuskanci abinda yake tsakaninsa da Aisha tun ajiya da suka dawo daga gurinta ya Miko masa robar swan Abdullah ya Mike zaune ya karba ya guntsa a bakinsa ya fesar sannan ya daga kai yana Sha kawai jikinsa yabashi ana kallonsa byn salis dake gabansa "ya sake kallo a hankali "ya juya faiza ya hango can barandar saman teema ta zuba masa idanuwana tamkar zasu fito cigaba yayi da shan ruwan ragowar ya tuttula a kansa sannan ya jefar da robar ya Mike salis ya Miko masa karamin towel ya karba yana goge ruwan dake kansa da yayi gaba zuwa part din sa salis nabin sa, dab da bakin kofar shiga ya tsaya yace salis kaje kasa a wanke min 4mat shadaya inason fita . salis ya amsa ya juya Abdullah kuwa yashige abunsa yayin faiza dake can sama tayi murmushi tare da sanya hannuwanta duka biyu ta rukunkume kanta gsky ta gama sa'a acikin mata muddin ta mallaki Abdullah .......

A takure take a gaban mlm abu ya Nisa tace tun tashi na arayuwata ban taba wulakanta kowa ba idan har nayi wulakancin daban kawo yanzu ba acikin rufin asirin Amman sai gashi a cikin gidan nan kin fito da naki salon wulakanta dan Adam in ko kika ce haka zaki Yi ,rayuwa baza ta miki kyau ba yaro me kima da mutunta mutane kina tunanin kina da wani abinda zaki iya wulakanta shi idan ma so ne ba kiyi masa baza ki Bari ku rabu lafiya ba,sai kin sako rashin daa a ciki.cikin bacin rai mlm abu ke magana , magana ta karshe duk randa yaron yasake dawowa baki bude baki kin basa hakuri ba ,ban yafe miki ba tunda duk cikin bbu wanda kika gado wajen wulakanta mutane......



MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AISHA A BAGUDO



Page 5


Yakira sunanta cikin tsanyi murya Aisha are you ok ? ahankali ta daga masa kai ya zuba mata manyan idanunshi hade da kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa ahankali "let me allowed you to rest "tayi shr still har yanzu taki tace komai ,ita kadai tasan abinda take sakawa a ranta " ko kadan hausar bakinsa bata fita da kyau hakan yasanya gara yayi da turanci zai fi masa sauki yakan dage yayi hausar a gurin dake da mahimmanci a wajen sa ,ya furta zai tafi yafi akirga Amman still yakasa barinta tashiga gida ya xura hannushi duka cikin aljihun wando sa yakara step biyu zuwa gabanta yana sake hango tsoronta a Fili yana kallon yadda ta gigice take fidda numfashi da sauri da sauri "ya runtse idanunshi tare da jin haushin kansa sai yabude baki da niyar sanar mata da sakon zuciyarsa Amman sai dai yaji hakorin sa sun datse harshen A'a bazan iya ba Aisha tayi kankata dayawa "Brain dinta bazai iya daukar wannan Kalmar ba yafi bukatar ya nuna mata A aikace duk a zuciyarsa yake wannan furucin yayinda idanunshi kai kanta ko kifta su yakasa ya salam ya furta akasan ransa jin hucin numfashinsa a fuskarta yasa tadan ja baya kadan ,gabadaya tarasa natsuwa zuciyarta ke beating sosai" sai kusan karfe goma na dare ya barta ya wuce badan yagaji ba sai dan yabarta ta huta.


Cikin sati nan biyu ya zamewa Abdullah jiki dole ne kullum sai yaje yaga Aisha sannan yake samun bacci da kwanciyar hankali musamman da yake mami na da bakuwa bata wani bincike kan yawan fitarsa da dawowarsa haka nan a bangaren Aisha iya kuluwa tayi da Abdullah domin duk yadda taso ta raba kanta dashi yadaina zuwa abun ya gagara ,da alama yasamu karbuwa a gidan ,ta fahimci Abdullah yagama gane aladar babanta ne zama a kofar gida duk dare ,dan haka yana zuwa kai tsaye mlm abu ke turawa tazo haka nan halayyar Abdullah ce yawan kyauta kullun ne idan ba'a aiko salis da abu ba to zai turo musa ,ba Aisha kadai ba hatta su salis suna yabawa da Abdulla da irin wannan halaiyyar tasa" hakan yasa ko zance Abdullah aka tayar wani lokacin a gidan sai ta shigewarta daki ta banko kofa sai ma ta wuni bata ci abinci ba saboda an yi zancensa dan ita bata ga abun birgewa a wajen sa.

A bangaren Abdullah kuwa yagama fahimtar inda Aisha ta dosa duk da bai sanar da ita abunda ke cin zuciyarsa ba Amman shi ya danganta rashin sakewarta har da karancin shekaru a ganinsa kurciya ce tasa takasa fahimtar sa Amman akwai lokacin da zata fahimce sa awajensa duk abunda zatayi sake birgesa takeyi .

Idan yazo yakan sake sosai da mlm abu suyi hira kafin A kira Aisha"Kuma yana karuwa da hirar mlm abu domin akwai ma'ana a duk maganar da zai fada ,a wajen mlm abu ma har cikin ransa yakejin Abdullah ya kwanta masa duk da yake da ganin Abdullah din zaka San daga gidan manya ya fito , Amman hakan bai hana shi shiga cikinsu ba sau Tari duk dare idan usman ya siyowa mlm abu goro shike karfa da akwai buta nan kusa ya wanke wa mlm abu ya bare sannan ya Mika masa, har ya zamanto shi din ma idan ba mantawa yayi ba duk zuwa sai ya kawo wa mlm abu goro.

Da yammacin ranar lahadi Aisha na sharar tsakar gida sai ga sakina ta shigo da sauri Aisha ta Yar da tsinsiya hannunta, suka rungume juna suna dariya ,rabon da su ga juna ko wani labarin tsakaninsu kusan sati hudu kennan tun kafin tafiyar sakina mina, byn ta gaishe da inna suka shige daki suka fara bawa juna labari sakina ta fito da tsarabar mina ta bata sannan cikin tsanyi jiki tace sister tare muke da bakonki fa yana waje .

Cikin mamaki Aisha ke kallonta bakona Kuma ?

Sakina tace wallahi Ahmed ne dan gidan mama hauwa tun randa mukaje dubota asibiti ya ganki shine yayi ta damuna Kar ki ga irin kakkauce masa da na dinga yi saboda sanin halinki Amman ya nace shi kawai in kawoshi sai in barshi dake ,dan Allah sister ki taimake ni ki leka wallahi tun kusan 12 yau yake zaune agidamu ya tasani gaba wai sai munzo .

Wani irin kallo Aisha kebin sakina dashi abu daya take jin rashin zuwanta wajen bakon zai sanya sakina taji ba dadi gashi tanason suyi hirar yaushe gamo ,baki ta dan tabe gami da gyada kafadarta any way ki sanar da inna tukun .


Cikin murna sakina ta rike hannunta tace am so happy thank you sister sannan tafita gurin Inna .

Kasancewa yammace bbu mutane sosai a cikin layin haka nan kofar gidan nasu ba kowa shi yasa suka tsaya a waje ita da Ahmed batare da sun shiga ciki soron gidan ba" ita dashi ne kawai tsaye dan sakina taki rakota hakan yasanya Aisha yi kicin kicin da fuska har ta sanya Ahmed din ya dinga inda inda yakasa yi mata magana .

Kanta a sunkuye taji yana kokarin son fahimtar da ita Kalmar so nan da nan tadago kai da nufin dakatar dashi Amman me sai cin karo tayi da idanuwan Abdullah cikin nata suna nufowa inda suke shi da wani da bata San kowaye ba ,ta dake taci gaba da tsayuwar karfin hali Amman haka nan taji zuciyarta na harbawa ,cikin kamewa da tafiyar mutunta kai ,su Abdullah suka karaso har suka shige su ,ganin sun shige inda suke yasanya Aisha sauke numfashi ta tsiri murmushin dole har Ahmed ya tambaye ta tace ba komai .


Shi kuwa Abdullah duk wata wuta dake jikinsa sai da ta dauke bai taba jin wani irin mugun kishi daya ji yau yana jin tamkar zuciyarsa take barazanar tarwatse gawani dake tsatsafowa masa ya cire hanky daga bayan aljihun wando sa a tsanake ya gogewa Amman kallon daya zaka masa kasan baya cikin natsuwarsa " komai ya tsaya masa cak tsammaninsa rashin fitar da Aisha take Yi yasanya Maza basu farga da ita ba ashe abun ba haka bane ,kinyiwa Dr sagir magana yayi sai da suka kai karshen layin suka sake juyowa suka zo suka shige su Aisha suka tafi batare da ya sake kallon inda suke ba ,barin su gun ya sanya itama taji gara ta tafi ,ta masa sallama ta shige gida abunta tana shiga ta tarar da usman da sakina ne a tsakar gida suna hira tana yiwa inna gyara kayan Miya sakina tace kai sister ashe anyi wani sabon handsome Abdullah shi ne bamu sani ba .

Aisha ta harari usman don tasan shi ya fesa mata tace dan sa ido banza kawai har suka shiga dakinta sakina nacewa A'a sister ni gara ki sanar mana kada Ahmed ya kwallafa rai . Aisha dai bata kulata ba har suka zauna tasake cewa kisanarmin da gaske ne maganar da usman yagayamin ,waye Abdullah ?

AISHA ta kalleta tace dan Allah sister ki manta da wannan zance muyi hirar mu yaya mina ?

Tun magarubar farko Abdullah ya sallame salis haka nan yace musa ma ya tafi sai zuwa gobe , sallah ishai a kofar gidan mlm abu tayi masa dan tare suka yi jam'i sallah da mlm abu byn an idar ne Abdullah yasami mlm abu yace shi dai yazo ne yana nema a gurin mlm abu daya bashi auren Aisha ,mlm abu ya zubawa Abdullah ido kana kallon Abdullah zaka gane irin mutane nan ne da ilimin boko ya yaratsa su tare da wayewa da natsuwa , uwa uba gata da jin dadi dake jikinsa ya nuna karara "sannan kamannin Abdullah din da yanayin sa ya nuna wata kabila ce da ta bambamta da hausa , hakan ma zai iya kawo wata matsalar wajen yuwar abun akwai baiwa da da natsuwa dake tattare da yaron hakan yasanya mlm abu ya dade yana tunani yuwar abunda yaron yake so"domin dai su din ba wasu bane Amman sai gashi Abdullah din da kansa ya durkusa gaban shi yana nema daya bashi auren diyar sa Aisha mlm abu yayi murmushin game da gyara murya sannan yace Abdullah ni kam dai ta bangarena dama mahaifiyarta haka muka fi so ace Aisha tayi aure yanzu domin shekarunta sunja a yanzu Aisha kadan yarage tacika sha takwas inda watan 12 ya tsaya da kwana 14 in banda karatun da ta tsaya yi da tuni ta dade a dakinta hakan nan Kuma nine mutun na farko da zai Yi farinciki da kasancewarta matarka.
Mlm abu ya numfasa sannan yacigaba Amman duk da hakan Abdullah bazan iya aura Maka Aisha ba tare da hadin kanku ba ma'ana bazan iya aura Maka Aisha ba sai ta amince da tana sonka domin shi aure ana yinsa ne dan mutun biyu matukar bbu jituwa tsakanin maaurata bbu abunda zai je yadawo illa rashin kwanciyar hankali. haka nan kaga Aisha ita kadai gareni Diya mace duka yayana Maza ne shine naci alwashin duk namijin da ta zaba matukar na duba naga yadace zan bata shi ", banason na mata dole dan haka Abdullah abinda nike so gareka kaje ka nemo so gurinta matukar kun hada kanku ,ni ne mutun na farko da zan soma murna km da yarda Allah nabaka Aisha .

Wanna shine KAKA KARA KAKA Amman duk da haka ya fahimci abinda mlm abu yake nufi shi kansa ya Karu Kuma hakan ya karawa Aisha kima a gurinsa domin yanzu dai yasan ko bbu komai yasan mlm abu ba zai taba mata auren cin fuska ko na kudi ba wannan ya nuna ita din mai daraja ce a gurin iyayenta Kuma ko da Allah yayi shi din ne zai aure ta yasan badan kudinsa suka bashi ba , kodan wani abu nasa ba .

Abdullah yayiwa mlm abu godiya sosai ya nuna ya fahimce shi ya Kuma ji dadin yadda ya nuna yana kaunar sa ta bangaren Aisha kuwa zai cigaba da kokarinsa in Allah yaso da kansu zasu kawo kansu a daura musu aure .kasa tafiya yayi sai da yaga Aisha domin dai har lokacin jiyake tamkar zata kubuce masa ",Amman ko sanda tafito ya zuba mata idanunshi zuciyarsa na sake hango masa ita tare da wani wanda bashi bane " Abdullah yadan bata rai yakafeta da manyan idanunshi yayi kasa da murya yakira sunanta cikin kwarewa da harshe turanci Aisha waye wanda na ganku tare dazu ?tayi shiru ya sake maimaitawa ta dan dago kai cike da dakewa tace da shi wani ne.
Abdullah yace Ok kina son kice min saurayinki ne "ina ganin ba mutunci ki bane kidinga tsayawa da namiji a waje kowa zai wuce sai ya kalleki .ita kam Aisha wannan magana dayayi ji tayi tamkar ya zageta ne dan haka rikici ya balle a atsakaninsu ,shi Abdullah da yaje da nufin shawo kanta gashi ya fito da kishinsa karara komai yasake tabarbarewa, dan haka da fada suka rabu . Amman cikin week din dole ya hakura ya dawo yashiga lallabata domin dai tunda yasan tana waje yanzu yasan batasa bace shi kadai . Haka Abdullah ya dinga iya kokarin sa akan Aisha a kalla kullum sai sanyata a idanunshi sannan zai samu zaman lafiya "ba dare ba rana muddin yataso daga office kai tsaye inna yake turawa dan aike ta turo masa Aisha haduwarsu da sakina ya zaman masa tamkar ya samu mai tayashi lallashin Aisha ne Amman bangaren sakina kuwa haduwarsu da Abdullah bakomai yajawo mata ba facce tashin hankali da da tsinkewar ZUCIYA .



Bangaren mamin Abdullah kuwa magana hada yayansu aure ta zauna daran Amman har zuwa wannan lokacin Abdullah bai San da zaman zance ba" domin ita mami tarigada tasan sai dai idan bata ce ayi ba ,indai tasanar da Abdullah zance ya zauna mama hafsa mai niyyar yin 1 week a gidan mami sai gashi ta share har kusan 4 weeks domin ganin daula da Hutu dake cikin gidan "ya dada haifar da shantakewarta , musamman da yake yanzu cigabansu mami sake gaba yake cikin sati na biyar tayi kokari tabar garin kebbi cike da alheri masu yawa domin ko Abdullah sai da mami tasa yama mata alkhari fiyye da yadda batayi tsammani ba, hakan bakaramin kara ingizo ta yayi ba shi Kuwa Abdullah yayi haka ne dan yakara wanke kansa awajen maminsa .

Mama hafsa diya ce gurin dan'uwan mahaifin mami domin mami ita kadai iyayenta suka Haifa asalin mami balarabiyar ce wanda har yanzu iyayenta suna Egypt ,karatu yakai ishaq kasar China yayinda itama karatu tajeyi suka hadu suka soma soyayya daga baya yabita gun iyayenta wanda da suka yarda suka yi aure shima dan diyartasu ta nuna bijirewa ne garesu" byn sunyi aure daf da dady zai gama karatun shi cikin ikon Allah mami ta haifi danta namiji , aiya rayuwar dady bai taba ganin kamanni mutane haka ba like mother like son Abdullah na matukar kama da maminsa anyi hidima sosai daban mamaki .bayan shekaru masu yawa mami tasake haihuwa ya' mace akasama sunan mahaifinsa ishaq wato amina baacike shekara uku ba tasake haifo Fatima dady na matukar kula da family dinsa sautari yana zuwa Nigeria sai dai da ya shirya da niyar zuwa kauyensu sai yaji gabadaya kmr gabobin sun sage yaji kmr ana cinawa jikinsa wuta haka zai tattara ya koma bayare da yaje ba,cikin ikon Allah dady ke sanar da mami yanaso sukoma Nigeria mami tace sam ita bata san da wannan zance ba bakaramin tashin hankali sukayi da dady ba dan har yakai ga cewa zai kwaishe yayansa yatafi dasu nan Kuma ta gigice tace tayarda sukoma Amman ba'anason ranta ba " zama yakawo kanin mahaifin mami Nigeria dalilin wani abokin karatunsa yataho Nigeria har yadu da wata bayarbiya yamata ciki a Lagos aka haifi mama hafsa baatashi kai mama hafsa dangin mahaifin ta ba sai da za'a mata aure
Sannan yanuwa suka ganta anan sokoto take aure "to dawowar su mami kebbi yasanya suka kulla zumunci sosai kasancewa mami bata da kowa Kuma bata taganin wani danuwanta .


Kwance yake a falon mami kan kujera da yammacin ranar asabar kwanaki uku kennan da tafiyar Mama hafsa duk wani abu daya bukaci yana son ci an zube masa teema na hadawa tana mika masa yana ci yayin da mami ke kallon tashar larabawa sai da ta bari ya kammala komai sannan ta rage

Please Login or Register in order to submit comment