Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auke Sarauta da Mari, cak kowa dake falon ya tsaya, Sarauta ta juya ta juya tayi kukan kura tayi Kan Khaleesat, ganin irin dank'ar datake shirin yimata yasa ta zuba dagudu tayi b'angaren dining room d'in......





"waikai miye kake aikatawa Haka Idan suka gano fa" Shureim ya k'arashe maganar Yana Kallon saurayine dake gefen shi, saurayin yace "ba haka bane yaya kawai Dai nakasa rik'e kaina ne" Shureim ya tab'e baki yace "fine amma duk abunda kajama kanka Babu ruwana kaga katsaya a Aikin ka komai fa zasu iya aikatawa Akan cikar muradin su so better ka kula" saurayin yayi ajiyar zuciya yace "amma Taya inaji Ina gani za'a aurama Shubai'a wani wanda bani ba a duniyar nan" Shureim yace "nace ka kwantar da hankalin ka" a d'an fusace saurayin ya mik'e Yana fad'in "karma na damu kake gayamin yaya Shureim, Uhm Tohm yayi zan tafi kuma karka sake ka nemeni" ya juya daniyyar fita, dasauri Shureim ya rik'e hannun shi yana fad'in "Haba mana brother Fawax da k'anin, karka damu bani nace maka karka damu ba ai Dai tananan ko to da'ita zamuyi amfani" Fawax ya kalleshi cike da rashin fahimta yace "waa fa..." Shureim ya kashe mishi ido, Fawax yace "Kai Wai kana nufin Sarauta" nanma Shureim ya kashe mishi ido, Fawax na zama yace "to amma Tayaya d'an uwa" Shureim ya zauna Saman kujerar shima "AKAN KUDI Babu abunda bazatayi ba ranta ne kawai bazata bayar ba, to ta hakan zamuyi amfani" Fawax yace "that's my brother, to amma kana ganin zata amince ta b'ata auren" Shureim yace "AKAN KUDI Babu abunda bazatayi ba Nina Gaya maka hakan" Fawax yace "to Idan kuma tak'i amincewa da Hakan fa Koda kuwa ambata kud'in" Shureim yace "itad'in fa mayyar kud'i ce Abun a jininta yake so hakan ma dole ya faru" Fawax yayi murmushi yace "Bari naje kasan munata shirye²n zama lawyer" Shureim yace "kwarai a k'arashe dai zaka cikama Shubai'a burinta" Fawax yayi dariya sallama sukayi inda shima Shureim d'in ya wuce gida.........



*ikon Allah, su madam Fawax ashe hakan ta faru, Allah sarki Tohm, Ohh yaude ammari Sarauta su oh oh koya za'ayi, Ashema sarautar shegiya ce Uhm, Ummeen baba fito kiga ikon Allah* 🤔





*karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍







@07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💴 💵

(A poor lady story)

......... 22nd May, 2023



*Story & writing*
*By*


@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




🔔📚*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS*📚



👑J. W. A👑




🅿........ *031 & 032*






........"ke harkin Isa ma Wacece ke, nizaki Mara" Sarauta ta k'arashe tana rufe Khaleesat da bugu, irin bugun datake ma Khaleesat duk ya basu tsoro, Juwaira data rasa ta yanda zatayi ta temaki Khaleesat, zuwa tayi ta d'auko mirror dake cikin dining room d'in ta bugashi Akan Sarauta ji kuke tasssss glass ya fashe akanta, Aiko within a second Sega jini nabin fuskar ta, dasauri tasaki Khaleesat ta d'ago tana Kallon Juwaira datayi tsamo² da'ita, Sarauta ta juya dama ta juya hagu Aiko Allah ya had'ata da flower base, d'auka tayi se a kaf'adar Juwaira, wani irin ihun azaba Juwaira tasa dan ba shakka ta nakasata, tasssss kakeji Shuwaiba ta fasa dinning table d'in gaba d'aya da k'arfen hannunta, kafin tayo Kan Sarauta dashi, itama Khaleesat data samu damar tashi ta d'auko flower base, sarkin yawa yafi sarkin k'arfi hakan ne yasa Sarauta ta juya da niyyar rugawa amma Kash ta taka kwalba saboda adining room d'innan Babu abunda suka rage me amfani duk sun fasa su dama kayan glass, dagudu ta juya duk da kwalbar data taka tayi falo, gwarammm taji tayi Karo da mutum, ganin Shureim ne yasa ta shiga bayan shi ta b'uya, Khaleesat dake ta dafe bakin ta daya kumbura tace "y'ar shegiya ki fito mana kiga yanda akeyi" Shuwaiba tace "fito dan uwar ki" Juwaira tace "kuma ma ai bamuyi k'arya ba munafuka" Sarauta tace "wallahi acikin ku duk wacce ta kuma zagina sena nuna Mata cimar mu ba d'aya bace" Shubai'a tace "Ance miki shegiya" Khaleesat tace "kokina da ubane" gimm kakeji Sarauta ta kwad'a ma Shuwaiba k'arfe a k'afa nan take ta duk'e tana kwalla ihu, dagudu tabi Khaleesat, roses na flowers ta jefa Mata a k'ugu tana rufe ta ta Duka tana cewa "ubanki ne shege, ke harkin isa ki Kira wani da siege bayan wanda kika ajiye a Banaja Bad mekkah jedda, ko kind'auka ke kad'a kika sani...." ruffff, taji an rufe ta da duka, kuma ta kasa d'agowa sosai Juwaira da Shuwaiba ke jibgar ta, ita kuma tana jibgar Khaleesat.





Shureim da mamakin yanda suka maida Mai gida ya kashe shi dakuma yanda suke dambe kamar y'an wrestling, yasa ko motsi ya kasa amma ganin suna niyyar yin kisan Kai yasa ya daka musu tsawa, nan take suka tsaya da jibgar Sarautar Sasuke yi amma ita Sam tak'i Dena jibgar Khaleesat gurin ya k'arasa tare da jawota da hannun shi, duk irin yanda jini ke zuba a kanta be hanata yin jarabar da take ba, cikin jaraba da k'unar zuci take cewa "ku barni na kashe ta seta sanar min Wacece shegiya tsakanina da'ita ka sake ni nace banaso ka sakeni" (Sam Shureim be San miye d'aga murya ko hayaniya ba hasalima sune abunda yafi tsana kaf rayuwar shi) murya a sanyaye yace "ki kwantar da hankalin ki kiyi shuru" ya k'arashe Yana jijjigata, a hankali tad'an soma nutsuwa, Minti kad'an jiri ya d'ebeta sakamakon jinin dake zuba a jikinta, within a minute ta suma, Talladega yayi ya kaita Saman kujerar ya kwantar, kafin ya dawo ya temaka ma ko wacce suka k'arasa falon, seda yayi ma kowaccen su dressing sannan yayi musu allurar barci domin su samu su dawo daidai, kafin itama sarauta ya juya yayi Mata duk abunda ya Kamata, yad'an jima Yana Kallon fuskarta kafin yayi murmushi ya sumbaci goshinta ya mik'e ya wuce ciki.




Companyn shi ya Kira inda suka zo suka kwashe unused glasses d'in suka kawo sabbi suka jera, kamar ba gurin bane akayi danbe aciki ba, shima wanka yayi yad'an huta, zuwa can suka farka.




Sarauta ce k'arashen farkawa saboda no lie taci wuya, kallon su kurum ya keyi da Alama kowa jikinta yayi tsami, d'an murmushi yayi yace "ku tashi kuje waje driver na jiranku" duk Kallon shi sukayi kafin Sarauta t mik'e tace "me kake nufi" Shureim na mik'ewa yace "kar in dawo in same ku Anan" daga Haka ya wuce ciki Abun shi, Sarauta ta gyad'a Kai tayi tsaki ta juya ta fita, driver ta iske Yana jiranta, Aiko suka tafi, sukuma su Khaleesat dakyar suka iya barin gidan saboda sunsan halin shi Idan ya fad'a, dukkan su kuka sukeyi har suka tafi.




*12hrs later*



"wallahi hajjana sena kashe yarinyar nan Dubi halin da my and only daughter take ciki duk ta dalilin ta wallahi Idan batayi wasa ba yau se kwanan ta ya k'are wannan ai nufin kisan Kai tayi" Sirayya ta k'arashe tana duba gefen bakin Khaleesat daketa gunjin kuka, hajja jumaima tace "gaskiya ne Kam wannan ai Babu alamun Imani atattare da wannan bugun se kace ta samu jaka Aiba haka ake ba" Khaleesat na sheshsheka tace "Nidai My ki kirashi dan Allah" Sirayya tayi tsaki tace "Haba My Wai wane irin so kikema wannan sakaran yaron to gaskiya kiyi hak'uri amma bazaki koma gidan wannan la'anannan ba" Khaleesat ta fashe da kuka tana fad'in "wallahi wannan maganar taki tafimin bugun nan zafi Akan me zakice bazan koma gidan mijina ba to wallahi koki kirashi ku bashi hak'uri na koma daga baya an ramamin ko kuma in tafi can setten Rd gurin y'an uwan Abbana dama ai sunfi sona, ke baki wani sona dama Abun naki duk k'arya ne "Sirayya tace" Nike miki k'arya Khaleesat "Khaleesat ta mik'e tace" Ehmana ai basona kike ba Idan hakane ki maidani gidan mijina kuma ki d'auka min fansar abunda waccan she.... "kasa k'arasawa tayi ko saboda me oho, ta cigaba da cewa" kawai setten Rd zan tafi "tana k'arashe tana juyawa da niyyar tafiya Sirayya ta rik'e ta idonta na cika da hawaye tace" ah ah y'ata karkiyi haka, Idan nabarki kamar naci amanar mahaifin ki ne, Sam y'an uwanshi basa sona, shima saboda haka ya yanke duk alak'ar dake tsakanin shi dasu yanzu Idan kika koma azabtar dake zasuyi dan Allah sun tsanemu, amma Dai Aike damuwarki ki koma gidan Sarauta ko, karki damu Muhammad Sarauta naki ne kuma yanzu zanje Nayi magana da yayan" Khaleesat ta rungumeta tace "Ina k'aunar ki My" Sirayya na hawaye tace "I love you too My, more and more makuwa" hajja tayi murmushi tace "Yawwa to kokefa yanzu muje ciki Kisha magani" Khaleesat tace "Uhm Uhm Allah Babu dad'i" hajja tace "to ai lafiya ake nema miki" Sirayya ta kama hannun ta sukayi sama tana fad'in "kawai tunda bataso hajjana a barta"






"Kedai har yanzu baki Dena wannan kukan ba ko kina son kiyima kanki illa ne" hajja Neenah tace "Haba Ni'imatu miye haka so kike ki rud'a ta kibarta taji da abunda take ji mana Haba yanda fa Nike sonki haka Nike sonta dan haka ki kiyaye ni Ina fatan kinji" ta k'arashe tana jawo Shuwaiba jikinta, Ni'imatu tace "ni bangama abun so a gurin wannan banzan yaron ba amma kuma yarinyar nan ta nace mishi yanzu Dubi halin datake ciki ko kwakkwaran motsi batayi da kafad'ar ta" Shuwaiba tace "hajjarmu dan Allah kice Mata tafita Bana santa, ta tsaneni itama, hajjarmu wallahi ba laifin shi bane shima besan miye ya faru ba, amma ta d'ora mishi laifi ni kawai ki kiramin shi na bashi hak'uri, amma dan Allah ki koreta daga nan Bana son ganin ta" Ni'imatu tace "base kin koreni ba dama tafiya zanyi ai, amma kuma kisani dole sena ramamiki wannan zaluncin da akayi miki" hajja jumaima tace "karki damu yarinya anjima dakaina zan kirashi kuma nasan zezo kinji ki Dena kuka" Shuwaiba ta d'aga Kai tana cigaba da kukanta.





"wallahi hajjana sena wulak'anta wannan la'anannan yarinyar Dubi irin bugun datayi ma Juwairana, ai Babu Imani aciki" hajja Mubeena tace "gaskiya Kam ni kaina sena wulak'anta yarinyar sena Bima jikanyata hakk'in ta" Juwaira ta kwalla k'ara tace "Nashiga uku k'afa ta zata cire Wayyo ummahnnaa ki temakamin k'afar zata cire" hajja Mubeena ta rik'e ta tana cewa "ki tsaya aduba miki kinji jikanyata, doctor matso ki duba Mata" Doctor na matsowa , Juwaira tayi baya tana fad'in "Nidai ku kirashi, Idan Baku kirashi ba Babu wacce zata tab'a min k'afa, Aidama k'afata ce bata mutum ba" Safiyatu tace "ki tsaya kinji zamu kirashi zuwa anjima ai dole ma yazo" Juwaira tace "kunyi alk'awari" duk suka amsa Mata da eh sannan ta yarda aka duba k'afarta ta.





Kwance take Saman gadon, tana Sanye da sleeping gown fara iya gwiwa, kanta nad'e da bandage, dawasu b'angarori na jikinta, ta lullub'e da white blanket d'in, idonta a lumshe seka d'auka ma barci takeyi, amma tunanin da bata tab'a yiba yau shi takeyi "wane ne mahaifin ta??, a Ina yake?,ya Sunan shi?, itad'in ma kuwa d'iyar sunna ce?, meyasa ya tafi ya barsu?, Dagaske ita shegiya ce?, yau gashi ankirata da shegiya kuma Babu abunda ta iyayi akai saboda ita kanta batasan amsar wannan tambayar ba, gashi bazata iya tambayar ummahnta ta waya ba, yanzu ya zata yi?" hannu tasa ta goge zafafan hawayen dasuka zubo Mata, "Sam kuka ba naki bane kyakkyawar y'ata, ked'in fa jaruma ce hakan be Dace dake ba" a hankali ta bud'e idonta ta juya ta kalli Ummee dake had'amata coffee, murmushi Ummee tayi Mata,ta temaka Mata ta zauna Akan gadon, Ummee tace "wannan damar kice y'ata, kidena damuwa Sam damuwa ba taki bace" a wannan lokacin Sarauta ta kasa tsayar da hawayen ta, kuka take sosai, zuwa can tad'an dafe kanta tana runtse ido, dasauri Ummee ta ajiye cup of coffee d'in ta Kamata tana fad'in "kamar yanda na gayamiki ne damuwa ba taki bace ba, tunda Nike ban tab'a cewa yarona ko yarinya ta su aikata wani abuba, amma a yau danaga zubar jininki senaji Ina son na d'auka miki fansa, zan nuna musu cewa hak'uri na ya k'are ninan zan tsaya miki kidena kuka" Sarauta tace "ah ah Ummee da fad'an na Kai da Kai ne amma yanxu ya koma na tsakanin mu, zan nuna musu bambancin dake tsakanin mu" dasauri sukaji an bud'e k'ofar an shigo, kallonta sukayi, Idanta cike da hawaye ta k'araso tana kama hannun ta takema Ummee nuni da "banzaye shine sukayi Mata wannan bugun to Bari in Kira yayan yazo se anbimiki hak'kin ki" dasauri Sarauta ta amshe wayar tana cewa "ah ah kyaleshi Shubai'a ki rabu dashi kurum" Ummee tace "kuma Koda yazo Sarauta y'ata karki bashi fuska, kuma karki amince ki koma gidan shi kinji kuma ba nan part d'in Zaki zauna ba ballema Idan yazo ya dunga ganin ki" Sarauta tace "Ummee Nima bazan amince na koma musu gidan ba saboda sesun gommaci mutuwar su da komawata gidannan sena gasasu sena nuna musu bambancin dake tsakanin mu" Ummee tayi murmushi ta shafa kanta tace "Yawwa y'ata yanxu dai ki kwanta ki huta zuwa anjima zanzo na baki maganin ki dan Allah kiyi barci banason tunanin Banza kinji" Sarauta ta lumshe musu ido ta kwanta daga nan suma suka tafi.





"kagayamin miye yafaru, Sam banason ganin hawayen yarinyar nan balle kuma jininta, inajin kamar jininka ne ko kuma jinin my princess ya zuba Haka nikeji banason abunda ze faru da'ita kagayamin Meya faru" Shureim yace "Abieyna ban sani ba" Ummee tace "tabbas be sani ba, amma Shureim d'ana ka maida matan ka kowaccen su kaje kace Mata ta koma d'akin ta" Abiey yace "miye na saurin haka jaruma ta" Ummee tace "gwara ya maidasu kafin su had'a mishi family meeting" kafin wani yayi magana wayar Shureim tayi ringing, kallon wayar yayi sannan ya kalli su Ummee yace "Ummah Sirayya ce" Ummee tace "kagani ko jarumi na" Abiey yace "kwarai kuwa tashi kaje D'ana" Shureim ya d'aga Kai ya juya daniyyar tafiya Abiey yace "Muhammad Shureim" Shureim ya juyo yace "Na'ammmm" Abiey yace "Idan ka dawo ka biya ka Bama Sarauta drugs d'inta" Kai Shureim ya d'aga ya fita dan baze iya yin gardama dasu ba.





Yaje gurin kowacce cikin su, sund'an tab'a hira kafin yacema kowaccen su xasu iya komawa gida, dukkan su sunji dad'i, Shuwaiba harda rungumeshi, amma seda Sirayya ta zage Sarauta tass, amma Shureim komai bece ba, Haka ya Gama ya wuce gurin uwar gidan shi.





"Asslamu alaikum" yashiga d'akin da sallama, a hankali ta bud'e idonta tace "Wa'alaikumus Salam" bedside drawer ya zauna Yana Kallon ta kafin yace "ya k'arfin jikin" ta d'aure fuska tace "Babu ciwo" yace "masha Allah Bari na baki magani" ya k'arashe Yana had'a drugs d'in, ta amsa ta rufe ido Tasha, Jin kamar ana kallonta ne yasa ta juya ta kalleshi Aikuwa itad'in yake Kallon, d'an yatsina fuska tayi tace "lafiya" yayi murmushi yace "ki tashi mu tafi gida" tad'an Harare shi tace "am sorry to say Babu inda zani please Sir Shureim can you leave" ajiyar zuciya yayi ya rik'o hannun ta yace "tare zamu tafi bazan iya barin ki Anan ba" ta amshe hannun ta tace "Sir..." yatsan hannun shi ya d'ora Saman kyakkyawan lips d'inta ya girgiza Kai yace "Mrs please stop calling me with something like Sir, nifa Anan mijin ki ne you can call me with Mr, Ohk" tad'an Jima tana Kallon shi kafin tace "please leave" tashi yayi ya koma d'ayan side d'in ya cire takalmin shi, ya hau yad'an k'ishingid'a yaja blanket d'in ya rufa, dasauri ta yunk'ura domin ta tashi, rass taji kanta ya Sara Mata, dasauri ya dafe Mata Kan Yana zama yace "Omg sorry, Ina zakine haka" ya k'arashe Yana d'an dafa kannata, kusan Duka jikinta a jikin shi yake, dasauri ta k'ara yunk'urawa zatayi baya, ya rik'eta yace "Wai Ina zakine" ta Harare shi tace "Wai Malam miye hakan ka sauka mana" ya kalleta yace "amma kuma Nida d'akina Zaki koreni" se asannan ta lura d'akin shine, kallonshi take kafin tayi baya tace "Bari na fita" yace "noop Zaki iya amfani dashi kafin mu tafi" ta Harare shi tace "Babu inda zan bika" k'ara jawota jikin shi yayi har tanajin bugun zuciyar shi, yace "Zaki koma gidan ko kuwa" kafin tayi magana wayar shi tayi ringing, d'an k'aramin tsaki yaja yacemata "waye ke kirana" saboda wayar na gefen ta, Sarauta dake neman hanyar guduwa dama ta lek'a takalleshi tace "something like diamond" dasauri Shureim ya amshi wayarta, ya kalli Sarauta Yana sauka gadon yad'aga wayar, gani tayi Yana duk'ar dakai Yana murmushi yace "afternoon my diamond star" shuru yad'an yi kafin yace "am zan Kira doing something very important" murmushi kurum yayi yana fad'in "uhm Uhm fa Tohm se anjima" daga Haka ya yanke wayar.




Juyowa yayi ya kalli Sarauta yace "please ki tashi mu tafi" ba tare data ce dashi komai ba ta mik'e tayi hanyar waje, saurin rik'ota yayi yana jinginar da'ita da bango yashiga gabanta yace "magana fa Nike" tayi tsaki tace "Wai duk miye hakan" Shureim ya kalleta yace "ni kikewa tsaki Mrs" irin Kallon tambayar dayake Mata ne yasa bata iya bashi amsa ba, yace "dani kike Mrs" shuru tayi kafin tace.......



*Tohfa nifa bangane ba, Wai Sir Shureim yadai, nace yadai ban gane bafa, Tohm Naga kana niyyar cin Amanar mu fa Tohm*





*Karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da koyaushe*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




@07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💴 💵

(A poor lady story)

...... 23rd May, 2023



*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚




👑J. W. A👑





🅿..... *033 & 034*





Ta kalleshi tace "to dakai d'in nike" yayi murmushi kalar murmushin da ban tab'a ganin irin shi Akan fuskar Shiba, kamar dai na mugunta Haka, hannu yasa yakashe light d'in d'akin, "Wayyoh Allahna wallahi banason duhu dan Allah ka kunnan light d'in" ta fad'a tana rungumeshi da Duka hannuwanta tana rufe fuskarta a k'irjin shi, murmushi Shureim ya k'ara yi agaskiya Yana son yaganta cikin hali irin wannan halin nuna tsoro, shagwab'a da kuka, amma ita kullum fuskarta a d'aure, shima rungumeta yayi yana petting bayan ta yace "ki kwantar da hankalin ki sun d'auke light d'in ne" Sarauta na k'ara cukwikuyeshi tace "mu kunna touch light mana" yace "ai wayar na gefen gado" haka suka k'arasa gefen gadon amma tak'i sakin shi, zama yayi itama ta zauna gefen shi amma almost Duka jikinta na Saman Nashi, ad'an tsorace tace "please ka kunna light d'in" shuru Shureim yayi yana Kallon d'an k'aramin bakin ta daketa motsi. Dasauri ta k'ara hayewa jikinshi haryana kwantawa, ita kuma ta kwanta Saman shi sakamakon motsin dataji, diffff sukaji an kunna light d'in , dasauri Shureim ya maidata k'asa shikuma yahau samanta ya rufe idonshi gam, besan waye ya shigo ba amma fatan shi ace ba Ummee bace ko Shubai'a ko Abiey, kunya yaji sosai kamar ya nutse, dasauri Sarauta ta tureshi tana mik'ewa zaune, shikuwa Bema d'ago ba, "Subhanallah" shine kurum abunda Ummee ta furta tana juyawa ajikin Abiey ta kwanta dan bak'aramin kunya taji ba, Abiey yayi dariya ya Kamata suka juya suka fita.





Dariya yake Mata sosai kamar k'aramin yaro, Haryanxu ta kasa bud'e idonta, Abiey yace "Wai har yanzu bazaki bud'e idonki ba, Dallah ki bud'e idonki ninefa Anan basu ba" ya k'arashe Yana lek'en ta, hannu tasa ta buge mishi kafad'a tace "duk bakaine kaja ba, Wai kaji ihunta kaidai kawai tsufa yakaima Karo amma zakace kaji ihunta" sarki ya zare ido yace "mene tsufa fa kikace, nine ma tsufa yakaima Karo Aiko yanzu zakiga Aikin tsoho" mik'ewa tayi Tai bedroom dagudu Don Sarai tasan halin shi, shima binta yayi, a bedroom d'in yakama ta, Saman gadon suka fad'a suna dariya, ya sumbaci goshinta yace "love you more and more, more than everything my jaruma" ita tayi murmushi tace "love yhu more than the way you do"





Se alokacin ta fahimci abunda ya faru Sam ta kasa d'ago kanta Koda shine ta kalla, ashe haka akejin kunya gaskiya bata tab'a Jin kunya irin na yau ba, Wayyoh ita tabani, hannunshi taji Saman nata, shima bata iya d'aga ido ta kalleshi ba, kanta ya shafa yace "dare yayi Mrs ki kwanta gobe semu tafi" nanma batace mishi komai ba harya tashi ya d'au wayar shi ya fice, Yana fita ta kwanta Saman gadon tare da rufe fuskar ta, kamar ta nutse Haka take ji.





"Hhh Allah diamond ba haka bane" ta cikin wayar tace "karkaji ka damu Babu matsala indai ta wannan hanyar zamu ladaftar da'ita, dole fa ta ladaftu karma kayi kuskuren fara soyayya da'ita dan itad'in Sam ba ajinka bace" Shureim yace "Toh shikenan yanda kike so Haka za'ayi" tace "Yawwa my golden boy" dariya yayi yace "kinganki ko diamond" Haka suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa.




*washe gari*




"Haba jaruma ta kitashi Kije ki duba ta mana kinga fa batada lafiya Sam hakan be kyautu ba" Ummee tace "Allah kunya nikeji" sarki yace "Haba dan Allah Wai wane irin kunya itad'in fa y'arki ce kitashi Kije" Ummee tace "to sedai in zamu tafi tare ne" Abiey ya zaro ido yace "Nidai kuma, ah ah gaskiya bazanje ba tab lallai" Ummee ta zumb'uro baki tace "tonima dai Babu inda zanje" sarki yace "Naji Nidai tashi muje".





"Asslamu alaikum" suka shiga d'akin da sallama, ko sallamar acan ciki ta amsa ta, Ummee se faman duk'ar dakai take, sarki kuwa ya dake kamar bega komai ba, kusa da'ita ya k'arasa Yana kama hannunta, tana sanye da Hijab irin jalbab d'in nan, "Sannu my daughter ya k'arfin jikin" Kai ta d'aga mishi tana sauka k'asa tace "Ina Kwana" har lokacin bata iya d'ago Kai ba, ahakan ma ta gaida Ummee, sarki ya d'agota yace "tashi ki zauna kinji, Kindai karya ko" Kai ta d'aga, Abiey yace "Anya kuwa, haa Naga bakin" batasan Sanda tayi murmushi ba tace "ai azumi Nike" Abiey ya shafa kanta yace "Allah yabada lafiya kinji ni Bari naje, amma fa ahalin dakike ciki Sam azumi be dace dake ba" Ummee tace "gudun maganine kawai" duk sukayi dariya, Abiey yayi musu sallama ya fita Yana kashema Ummee ido, ko tanka shi batayi ba ta koma Kan surukarta, ranar haka suka zauna kamar surukai

Please Login or Register in order to submit comment