Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Wai wannan bata magana ne" Ummee tayi murmushi tace "tana yi ki juya ku gaisa" Shubai'a tayi nuni da "inayi Mata amma ita ko kallona batayi" seda Ummee ta d'an ji Babu dad'i kafin tace "karki damu kinji Bari na Mata magana" Ummee ta juya ta kalli Sarauta tace "Sarauta wannan k'anwar Shureim ce kurma ce" wani irin rasss Sarauta taji kafin tace "kurma kuma" Ummee tace "Uhm tad'au tsawon shekaru a Haka" jiki a sanyaye Sarauta ta juya suka gaisa tana Mata nuni da ban hak'uri, Ummee tace "idamma kika d'anyi magana da k'arfi tanaji itace batayi" Sarauta tayi murmushi tace "Toh Ummee Allah ya bata lafiya" da amin Ummee ta amsa tana barin falon, kusa da Shubai'a Sarauta ta k'arasa tana kama hannun ta tace "dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban sani bane da banyi abunda Nayi ba amma ki yafemin" ahhh dama su Shubai'a sarakan labari ai man take ta nunama Sarauta komai ya wuce suka hau fira duk da Sarauta batason yawan fira amma Dai yau tayi kuma ma da kurma, wani ikon Allah a lokaci d'aya sukaji k'aunar junan su,


Sunanan zaune Sega Shureim ya fito dasauri, beyi mamakin ganin Shubai'a na fira da Sarauta ba saboda yariga da yasan halinta, tana ganin shi taje gurin shi tana murmushi tana mishi nuni da "gaskiya P.A d'inshi nada kirki" Kai ya d'aga Mata yace "sauri nike sena dawo" Shubai'a tayi nuni da "Duka yaushe ka dawo kofa hutawa bakayi ba, Ina kuma zaka" cikin tsigar lallashi yace "yanzu zan dawo kinsan Abba Taheer Yana nan ko to ciwon shine ya tashi zanje na duba shi na dawo" (Taheer da besamu auren Nur ba Haryanxu beyi aure ba kuma Yana saka ran indai ba gawarta aka ganiba to itace matar shi tun mahaifin su na Raye harya mutu, yanxu shike mulkar k'asarsu) Kai kurum Shubai'a ta d'aga mishi, ya juya ya tafi yana ma Sarauta nuni data taho su tafi, tashi tayi tana d'aga ma Shubai'a hannu suka tafi,

Suna fitowa ya mik'a Mata mukullin motar yace "mu kad'ai zamu fita kiyi driving d'ina sauri nike" tace "to where" yace "Hospital" Kai ta d'aga tana shiga motar shima gaban motar ya shiga yasa belt, harta kunna motar zata tafi, taji kamar ana kallonta ta juya ta kalleshi, Aiko itad'in yake Kallo, "lafiya" shine abunda ta tambaya, Yana kauda Kai yace "ke baki da hankali ne zakiyi driving bakisa seat belt ba" Kallon belt d'in tayi batasan Sanda murmushi ya kwace Mata ba tunawa da k'asarta Nigeria, tosu suna ma da belt ne a motar, ko kuwa akwai basudai maida hankali akai bane shysa, Allah sarki k'asata, ta k'arashe maganar zucin ta tana murmushi tasa belt d'in sannan ta tada motar suka tafi, a bakin asibitin suka tsaya, escorts d'in dake gurin dasauri suka zo suka bud'e, cike da haiba yake tafiya harya k'arasa cikin tank'amemen office d'in shi, tana biye dashi harsuka k'arasa, wani fari kuma kyakyawan dattijo tagani kwance idonshi a bud'e yana Kallon siling, gefen shi Shureim ya k'arasa Yana kama hannun shi yace "Abba Taheer duk miye hakannan yakamata ka cire wannan damuwar aranka kaji kaima kayi aurenka dan Allah" Abba Taheer na Kallon Sarauta yace "Humm Shureim d'ana kenan yanzu yakake son Nayi wace zata zauna dani na fara haukacewa, kaga wannan Budurwar ta gabana kama take min da NUR d'ita, Haka idaniya na ke nunamin, Shureim ni Haka tawa k'addarar take so karka damu kanka kaji" Shureim Yaja dogon numfashi yaci "shikenan Abba andai yimaka gwaji ko" Abba yayi murmushi Yana d'aga Kai ya kalli Sarauta yace "y'ata Sannu ko" murmushi tayi tace "Ina wuni Abba ya k'arfin jiki" Abba yace "lafiya klau Me kama da Nuriyyata" murmushi Sarauta tayi tace "zanso ganin Nur d'innan" Abba yayi murmushi sannan yace "Shureim wannan fa miyiniyar kirki da'ita" Shureim na juyawa yace "she's my P.A " kafin Abba yayi magana ya juya ya fice, seda suka k'ara gaisawa da Abba sannan ta fito suka tafi.



Duk zaune suke a falon kowa yayi shuru, Hajja Mubeena tace " yanzu Wai ke Maryama (Ummee) meyasa acikin gidan nan baki k'aunar ganin anyi zaman lafiya ne, yanzu Sarai kinsan da maganar aure a tsakanin yaron nan Khameel da kurmar y'arki amma kike k'ara nisanta su ko yanzu kin kyauta kenan" Ummee na hawaye tace "wallahi Hajja Sam bansan Haka ya faru ba ya za'ayi na hanata zuwa Kiran da Khameel ke...." cikin wata irin tsawa Hajja jumaima takatse ta "ke Dallah munafuka rufe mana baki ubanki kike ma kuka Anan ko miye, to yau sekin Bar gidanan shegiya bak'ar iri kawai ta kawo mana bak'in iri a gida zakiga yanda zanyi dake yau" kafin Ummee tayi magana sukaji sallaamar Shureim da Sarauta, cak Shureim ya tsaya Yana Kallon taron, besan Sanda k'ijinshi yace wani rassss ba saboda Sarai ya sani ko sanarwar arzik'i bata had'asu a babban falo balle fira yasani wani Abun sukayi "Wa'iya xubillah" shine kurum abunda ya furta Yana wucewa upstairs d'in, Sarauta na cewa " Sir Shureim baka saka hannu a document d'innan ba fa kuma yanzu zamuyi meeting d'in" "kisaka" shine kurum abunda yace Yana Hawa upstairs d'in, juyawa tayi tana d'aga Kai ta kalli mutanen gurin kaf ta yatsina fuska ta juya zata tafi abunta, dasauri Neenah tace "Uhmm ke zonan" KO kallonta Sarauta batayi ba ta juya zata tafi, Ummee tace "Sarauta bakiji ana kiranki ba" "Sarauta!!!" duk suka maimaita Sunan suna mik'ewa tsaye, kallon su Ummee tayi tanajin tasamu maganin mutanen nan aranta, Sarauta ta juyo tace "Wai ku miye Matsalar kune tsufa ko jahilci" Khameel yace "ke ya isheki fa wa'innan d'in iyayene kuma kakanni na baki da hankali ne" itama ad'an tsawace take cewa "malamai yafa isheku Baku fa Nike ma aiki ba Anan Sir Shureim shinike ma aiki, wallahi zan wulaqantaku sha..." Shureim da tunda aka fara wannan fitinar ya fito yake kallonsu, a zahiri yaji dad'i ai gwanda ta tambayar musu wa'innan tsoffin meke damun su tsufan ne ko kuwa jahilci, Hajja jumaima tace "amma Khameel wannan shegiyar yarinyar Ina ka samota" Khameel na Mata Kallon mamaki yace "Hajja Nigeria" ai kamar daga sukaji salatin Hajja Mubeena na fad'in "aww y'ar NIGERIA yanzu Kai Khameelu ka rasa y'ar wace k'asa zaka lalubo se y'ar waccan k'asar da matan su basuda Imani ko kad'an, dan ubanka ungo naka sakarai kawai ai in batayi abunda ya kawo ta ba muta koremu a Banza a wofi" Sarauta tace "uban me matan Nigeria sukayi ake cemusu y'an ta'adda to Bari kuji AKAN K'ASATA zan iya yimuku komai wallahi" daga bakin k'ofa sukaji Ance " mace ta kashe abokiyar zaman ta, saboda kishi zata kashe mijin ta, zata Bama yaran abokiyar zaman ta wahala mace ta k'ona mijin ta da abokiyar zaman ta, ta Kai jinjiri ayi asiri dashi, uba ya lalata y'arshi uwa tayi Zina da d'anta tirrr wannan duk se a Nigeria k'asar taki ake aikata shi zaku iya aikata komai domin cikar burinku" Juwaira ta k'arashe tana nuna ta da yatsa, kafin Khaleesat ta cigaba da cewa "kuma tsaftsaf Muna lura dake game da irin yanda kike shishshige ma mijinmu zamu iya aikata komai Akan hakan" Shuwaiba ta cigaba da cewa "ai Baku bata kanun labaran ba, wallahi kika yi kuskuren fara soyayya da Shureim sena wulak'anta ki senaga bayanki mayya kawai" Sarauta tayi murmushin wulaqanci tace "kuma fa kunsani matan Nigeria xasu iya yin komai domin cikar burinsu, ba danku nazo k'asarnan ba amma kuma da Alama tsautsayin ze koma Kan mashek'iya ku kiyaye" ta k'arashe tana juyawa zata fita, cikin wani irin zafi Khaleesat tayo kanta, da niyyar marinta, aiko Sarauta ta had'a da'ita da hannun nata ta malkwaye ta turata Kan Center table d'in, Aiko nan take ya fashe, ita kanta ya fashe, a zabure duk suka mik'e, cike da Jin rad'ad'i Khaleesat tace "Zaki San wakikawa Haka yau yau d'innan base gobe ba my zata zo zakiga yanda zamuyi dake shegiya kawai wlh sena Rama" ta k'arashe tana d'aukar flower verse d'in dake gefenta ta jefamata dasauri Shureim ya jawota ta fad'a jikinshi hakan yasa flower verse d'in betab'a taba, cak kowa dake falon ya tsaya ganin abunda ke faruwa a gurin, cike da dauriya da k'arfin hali ya cireta a jikinshi Yana kama hannun ta yace "Hajja dan Allah kuyi hak'uri itad'in fa bak'uwa ce kuyi hak'uri dan Allah" ya k'arashe yana yin sama da'ita, Uhmm Babu wanda ya furta a gurin se kukan y'am matan ke tashi, tunda Shubai'a take ba'a tab'a yimata abunda yayi Mata dad'i ba sama da yau, Haka zalika Ummee ba k'aramin farin ciki suke ciki ba a yau, Haka aka dunga watsewa a hankali aka manta da main topic d'in da ake ciki, Ummee da Shubai'a kuma suka wuce b'angaren Shureim.


"ke baki da hankali ne, wa'incan kakanni nane dole kiyi respecting d'insu inba Haka ba..." Ummee ta katse shi da cewa "Kai Dallah yima mutane shuru dama ai Kai kullum abunda ka iya kenan, tayi min daidai da bata bari sun wulak'anta taba ai hakan shine daidai" Shubai'a ma tana murna take nuni da "Naji dadi sosai Allah na yau Dai mun tsira daga hannun munanan can" Shureim ya k'ara hade gira yace "fita ki bani guri kuma ki wuce meeting d'in Zaki saura inkuma Jin wata fitinar ta taso maza wuce" Kai ta d'aga mishi ta juya ta fita.


Bata tarar da kowa a main falon ba shysa ta wuce hankali kwance.

Ta d'aya b'angaren kuma dakyar aka lallashi Khaleesat aka ce Mata karta damu za'a rama mata, duk y'an matan seda akace Idan sarki ya dawo za'ayi maganar auren su sannan suka Dena kuka, itako Sarauta ko ajikinta ta tafi meeting d'inta,


Yayinda su Khameel suka soma tunanin kodai wannan P.A d'in akwai hadin baki sak'aninta dasu Ummee kaddai ma Yarima ya aureta dasun shiga uku sun lalace.


*BAYAN WATA D'AYA*


*karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labari ne danayishi domin fad'akarwa, nishad'antarwa dakuma tunatarwa, nice taku me Nishad'antar daku akullum da ko yaushe*


@ *sherntee Ghayu* 😍😍



@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)

...... 10th May, 2023


*Story & writing*
*By*


@ *sherntee Ghayu* 😍😍



πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS*πŸ“š


πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘




πŸ…Ώ........*019 & 020*


*JIDDA*


*BAYAN WATA D'AYA*



"kadaiji abunda na sanar maka ko hakan kuwa shine ze faru" Shureim dake zaune a k'asa gefen k'afarta yace "Ummee ban tab'a jayayya dake ba wallahi, amma Taya zanyi hakan Taya kike son Nayi hakan kuma ko Abieyna ma baze amince ba" Ummee na k'ara had'e rai tace "tashi ka fita tunda ban Isa dakai va" dasauri yace "Sam Ummee ba haka bane Naji na amince zanyi hakan yayi miki" ta d'an kalleshi tace "in gani ak'asa" Kai ya d'aga Mata Yana tashi, daga Haka ya fice Sega Shubai'a data b'oye bayan gadon ta fito, ihun murna sukayi suka rungume juna "Ummee tace" k'asaΒ² beyi nisa ba fa "Shubai'a tayi Mata nuni da" ashe da gaske Zaki iya d'aurewa har Haka "dariya sukayi gaba d'aya su, Ummee tace" duk yau Banga Sarauta ba "Shubai'a ta d'aga kafad'a tana nuni da tun jiya da dare rabonsu da juna, Haka suka cigaba da firar su Abun su.


*Quwaiz Garden JIDDA*


" wai Sarauta meke faruwa ne Khameel yasanar damu komai ya akayi hakan ta faru meyasa zakiyi hakan " Fawax ya k'arashe Yana Kallon mutanen gurin Nabil yace "mu munji ki shuru Idan bazaki iyaba ki sanar damu kawai koba Haka ba guys" jabeer yace "wannan haka ne" Sarauta tayi murmushi tace "zuwa jibi zan kammala muku Aikin ku na koma k'asata, dan zuwa yanzu nasan komai kuma Naga komai zan had'o muku takardun na baku Nima na wuce na tafi sannan Kai kuma babu ruwanka dani karkaga ku Nike ma aiki to nasan darajar kaina gwara kasani" ta k'arashe tana nuna Khameel, ajiyar zuciya yayi yace "amma meyasa zakiwa kakanni na Haka" Sarauta tace "komiye su sukaja dan haka nizan wuce se munyi waya ko" ta mik'e ta tafi, nan sukai ta yin sak'a da warwara Akan lamarin.



Tana fita daga Garden d'in aka kiranta, Ali khan ne, murmushi tayi ta d'aga wayar, suka cigaba da firar su har ta k'arasa gida sannan sukayi sallama, tana ta k'ok'arin fita, Sega Kiran ummah ya shigo dasauri ta d'auka tana me matuk'ar Jin dad'i Nanna sunsha fira da fatan alkhairi da Ummah taita yimata, itama kuma tayi Mata godiya Akan komai na rayuwa wannan ne yasa bata tab'a tambayar waye babanta ba, seda suka gama wayar sannan tafita daga motor tafi.



"Asslamu alaikum" ta shiga main falon da sallama a bakin ta, su Hajja na nan shysa bata tanka kowa ba, harzata wuce taji jumaima na cewa "Ohh Mudai mun had'u da alak'ak'ai, Ynx yaron an harya fara ajiye karuwai a gida" a fusace Sarauta ta juya ta kalleta tace "wace shegiyar ce karuwa" ta k'arasa tana dawowa falon, Hajja Mubeena tace "Kece karuwar angaya miki bamusan komai ba Sarai mun sani kallonku kawai muke" Sarauta tace "ai ba'a karuwa d'aya agari, kuma wasu ma nasu kasuwancin gadonshi sukayi wallahi ku kama girman ku ni bataku Nike ba kuna son ku k'ureni ko to yayi ku cigaba" ta juya zata tafi Neenah tace "ke tsaya karki kuma yimana jam'i Banida had'i dake ki kama kanki" Sarauta ta d'age kafad'a tajuya, hajja jumaima tace "karuwar gida" Sarauta ta juyo tace "karuwai Dai kuma ni ko a karuwancinma naci Riba tunda ban tab'a bin bokanya ba" a hassale sukayo kanta da jaraba suna neman Kamata, hannu Hajja jumaima ta d'aga da niyyar marinta, "tassssssss" kawai kukeji, dasauri Sarauta ta dafa kumcinta tana dubawa zuwa can ta fahimci ashe ba'ita aka Mara ba, tana d'ago ido ta sauke su Akan fuskar Shureim dahar tayi Ja, jumaima tace "Wato Kai munafuki ko, da amareta gwara a mareka to ai ko Bari kaga" ta k'arashe tana k'ara d'aga hannun ta daniyyar sauke Mishi wani marin "tassssss" kakeji, Shureim daya rumtse idonshi Yana jiran saukar wani marin amma se yaji shuru, k'arar marin dayaji ne yasashi bud'e idonshi abunda yabashi mamaki ya Hana shi ko kwakkwaran motsi, ganin yanda P.A d'inshi ta tak'ark'are ta wankama Hajja jumaima Mari, bashi kad'ai ba duk wanda ke falon seda ya tsorata da lamarin, cike da nuna fusata Sarauta tace "how dear you slap him, har ke kin Isa Wacece ke, kina ganin Idan aka barki dashi akwai ubanda ya Isa ya ceceki ne eye, kamar Mrs billionaire Zaki Mara, Yana biyana kud'i ni kuma AKAN KUDI Babu abunda bazanyi ba Raina ne kurum bazan bayar ba, Idan kika kuma marin shi Anan nagane sekinyi mummunar ladama tsohuwar Banza kawai, gashi matso y'allaba matso ta Mareka data....." "ya'isa!! Ya'isa Haka banaso banason ji, Wai m..." Ina ya kasa k'arasawa sakamakon numfashin shi dake sark'ewa, dasauri Ummee da Shubai'a da hayaniyar ta fito dasu suka tare shi sukayi sama dashi, Sarauta ta juya ta kalli sauran mutanen falon dasukayi tsuruΒ² tace "duk wanda ya kuma attempting kirana da karuwa ko marin Sir Shureim...." tayi Kwata ta juya ta tafi, a zabure Khaleesat tace "Wai me wannan shegiyar yarinyar ke tak'ama dashi ne dahar zata d'aga hannu ta wanka miki Mari Haka ita Wacece" jumaima da mamaki ya kashe Anan tsaye tace "kiramin Sirayya" Shuwaiba tayi tsaki ta fice dan ranta ya b'aci sosai Wai har ze tarema waccan jakar fad'a.

Ankira Sirayya, angaya Mata duk abunda ya faru amma se cewa tayi ace da Hajja ta tayi hak'uri tadena biye musu, seda akace Mata harda Khaleesat d'inta ta Mara, nanfa hankalin ta ya tashi suna syprus amma ta d'aga hankalin mijin ta Akan se sunzo JIDDA, next week zata zo, da aka Bama Khameel labari shi dariya ma ya hau yi danshi yanzu kome Sarauta zatayi mishi bata bashi haushi tunda ta kusa cika mishi burin shi.



"Sannu my boo kadena sakama ranka damuwa yau da ciwon ka ya tashi da ya kenan daya zamuyi please ka kwantar da hankalin ka" Ummee ta k'arashe tana shafa kyakyawan gashin Kan shi, Sarauta dake tsaye ita da Shubai'a, suna mishi dariya k'asaΒ², da hannu Shubai'a tayi mishi Alamar "Sannu" itama Sarauta tace "sorry sir" Yana had'e gira yace "both of you disappear from there" kansu a k'asa suka fice, suna fita suka tintsire da dariya, harsuka k'arasa d'akin Shubai'a dan zuwa yanzu Shubai'a da Sarauta sunzama Amina juna,


"Ummee kinga yarannan ko" Ummee na murmushi ta shafa kanshi tace "sorry my baby boo xasu Dena yanzu gayamin Meya had'a fad'an" "Ummee a gabana sun kirata da karuwa kuma Babu abunda ba'iya yi akai wallahi "Ummee tace" Shureim kayi abunda na saka ka shine mafita fa gwara kawai ka aikata hakan "yayi ajiyar zuciya yace" tabbas ma kuwa Ummee zan aikata hakan inajin shine solutions naduk wata Matsalar masarautar nan baki d'aya "Ummee tace" tabbas ma kuwa my son " kafin wani yayi magana sarki ya shigo hankali a tashe yace" my boo what's wrong " Shureim na ganinshi ya kwab'e fuska kamar zeyi kuka yace " Abieyna" Abiey ya k'araso Yana jawoshi jikinshi yace "sorry ya k'arfin jikin wani abune ya faru" Shureim ya girgiza Kai yace "kawai nad'an ji jirine that's why" Abiey yace "my hero kaima ka cikama kanka aiki da yawa kanajina banason hakan dubi halin daka shiga yau ni Allah duk Banji dad'i ba ai hakan Sam be Kamata ba ko Jaruma ta" ya k'arashe Yana Kallon Ummee, Ummee tace "calm down dee bafa wani Abu bane kawai Dai yad'an ji jirine shine karka sama kanka damuwa Ohk" sarki yace "dole na damu d'ana d'aya aduniya bashi da lafiya ai dole na damu, yanzu kanason cin wani Abu" ya k'arashe yana tambayar Shureim, Shureim yayi murmushi yace "ice cream" Abiey ya shafa kanshi ya mike yace "Ohk give only 5mins my hero" Shureim yace "Ohk dad" daga Haka sarki ya fice, Shureim na kwanciya Kan cinyar Ummee yace "Abiey na matuk'ar k'auna t kamar Dai ke d'innan ko" murmushi tayi ta sha gashin kanshi suka cigaba da fira abunsu.




*two days later*


"komai da nikeyi Akan kud'i nikeyinshi" Shureim ya k'are Mata Kallo yace "kenan Akan kud'i kika baro k'asar ki kika zonan" Kai Sarauta ta d'aga mishi tace "kuma Akan kud'i zanyi duk abunda suka sani" Shureim yayi ajiyar zuciya yace "amma Ina fatan kinsan kud'i halaka ne" Sarauta ta girgiza Kai tace "kud'i ba halaka bane kyauta ce kuma baiwa ce da Allah keyi wa wasu daga cikin bayinshi" Shureim yace "Ohk zakimin wani aiki amma kome yabiyo baya babu ruwana" Sarauta tayi murmushi tace "AKAN KUDI Babu abunda bazan iyaba Raina ne kurum bazan bayar ba" Shureim na zama Saman kujerar shi yace "yanzu fad'a min yazakiyi da Aikin su Khameel" itama zama tayi tace "karka damu dasu dama ai sud'in banzaye ne sena k'ara banzatar dasu har zuwa Sanda zan gama maka naka Aikin amma nawa ne kud'in Aikin" Shureim yace "nawa suka baki" tace "10m naira" yace "ni kuma Idan kika gama min nawa Aikin zan baki 20 billion dollars amma Idan kin amince" cike da rud'u da mamaki ta mik'e tana Kallon shi tace "what you mean 20 billion dollars" ya d'aga Kai Yana mamakin San kud'i irin na y'an Nigeria, ta shafa gashin kanta tace "wane irin aikine wannan ko miye zan aikata matuk'ar ba rayuwa ta zan bayar ba" yace "farin ciki, farin ciki kurum Nike buk'ata Nida ahalina" Sarauta tace "zan bayar dashi kuwa har se yayi yawa, amma Aikin ze iya kaiwa kamar yaushe" yace "Koda yaushe, ko yau ko gobe ko anjima indai kin gama Aikin ki zan baki kud'in ki name sallame ki sedai aikin naki baze tab'a tafiya ba matuk'ar kina Amatsayin P.A d'ita, ta kalleshi tace" kamar ya kenan "yace" you most be my wife " ta juya ta kalleshi tace" aure kuma " yace" karki damu auren wucin gadi ne kuma domin kiyi Aikin ki cikin sauk'i ne amma zan baki Damar yin tunani akai kar asamu matsala ko " ta d'aga mishi Kai...


*Some minutes later*

" Aiko indai wannan Aikin ne kad'an ka angama dole kowa ya shiga taitayinshi acikin gidan nan Ummee itace sarauniya nizan dawo da Hakan tabbas karka damu akai "ya mik'e Yana fita yace" you should think about it "daga Haka ya wuce, a yau tasamu Damar gyara a Hali dakuma cikar burin ta na zama billionaire, taya zata Bari Damar ta sub'uce Mata kuma, sedai kuma taya zatayi aure batare da sanin ummahnta ba Kai maganar nan fa akwai Abun dubawa, tana ta tunanin ta, tafita Kiran da five foolers ke Mata dan da Haka ma take Kiran su.




A inda suka saba had'uwa Anan suka had'u, Fawax yace "Sarauta ki bamu documents d'in da komai da komai ga sauran kud'in ki zuwa gobe Zaki wuce" Khameel yace "gaskiya Kam yanzu ki kawo files d'in" tayi ajiyar zuciya ta zauna tace "ku Baku da hankali ne, kunsan irin ilimin da Sir Shureim yake dashi kuwa kunsan abunda ya faru ne" Jabeer yace "Ohh no Mike faruwa Meya faru kaddai kema ya koreki" tace "se kace baneman kud'i Nike ba, Tukunna Dai kad'an ya Hana ya kamani, Nabi duk wata hanya dazanbi domin samun cikar burinku amma Kash ko wace hanya ya toshe, amma na Kira k'awata ta 9ja nasata tayi min wani aiki Idan Aikin yaci da kanshi ze nemeni da maganar aure nikuma Dana aure shi burin kowa ze cika "duk had'a baki sukayi gurin fad'in "aure" tace "kwarai kuwa" Nabil yace "amma Babu abunda kike shirya WA kuwa taya Zaki aure shi" ta d'aure tace "nifa y'ar NIGERIA ce Idan na nufi Abu to shi kawai zanyi better ku yarda dani, aikina kawai zanyi na koma k'asa ta Akan 10m Babu abunda bazan yi muku ba, Kai Koda ranshi ma kuke so xan Baku Ohk" duk suka kalli Juna, Khameel yace "yanzu zan miki transfer na 3million a account d'inki Allah ya bada sa'a amma Inada tambarinmu Prince baze tab'a auren ki ba Kedai ki canza wata hanyar" Sarauta tayi murmushi tace "Haka kake gani amma Idan ya amince ya aureni ya kenan" Khameel yace "I will transfer you 2.5million" tayi murmushi tace "fine ai Dai kuna sheda ko" duk suka d'aga Kai, Haka sukaita k'ullaΒ²r su har yamma sannan Sarauta ta tafi, sun yarda da Aikin Sarauta sosai domin sun d'au yards sunba y'an Nigeria k'asata.




Zaune suke a Saman gadon suna

Please Login or Register in order to submit comment