Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basar damu, ko laifi mukayi miki kinsan zaman tare" Ummee ta k'arashe tana Kallon Sarauta, duk setaji wani irin, kafin kuma tayi murmushi tace "Laaa Ummee Babu komai Babu abunda kuka yimin Kwana biyu kawai kaina yayi min ciwo ne" Ummee tace "Eyyah Allah ya sauwake ai bamu sani ba" Sarauta tayi murmushi tace "ai yanzu kinga kun sani, Amm Ummee Idan na dawo zan Gaya miki wata magana kinji" Ummee ma tayi murmushi tace "to Allah ya kaimu ku dawo d'in, kingama wannan mashiriricin Haryanxu shuru kuma shike cewa banda African time" Sarauta tayi murmushi tana mik'ewa tace "Bari muyi sallama da Shubai'a" Ummee tace "Aikuwa kuma ya Dace" daga Haka tayi ciki.





"to yayanmu a dawo lafiya" Shuwaiba ta fad'a tana daga Kan dining, Shureim yayi murmushi yace "Aikin ki kenan ci Kedai kici ko" tayi dariya tace "ai ci nagaba da kowa" Khaleesat tace "yaya kayomin tsaraba" Juwaira tace "Ina buk'atar iPhone yaya Idan zaka dawo" Kai ya d'aga musu ya fice, Juwaira tace "Uhummm Muna furniture beba" Khaleesat tace "wallahi kuwa, Mudai mutum yabi ahankli damu ahee" Shuwaiba tace "Kai maintain mana dawa kuke ne" Juwaira tace "da ubanda ya tsargu" Shuwaiba ta mik'e tace "Aiko zanci uban yarinya" har Juwaira ta yunk'ura zatayi magana se Khaleesat ta rik'eta tace "Uhm Uhmm babe bakida time d'inta yanzu kibar munafukar zamuyi lokacin ta" daga Haka suka juya suka tafi, Shuwaiba tayi tsaki ta koma ta zauna ta cigaba da d'a'amun.





"tun d'azu ai take jiranka amma se yanzu" Shureim ya Sosa Kai yace "Uhm nad'an makara ne" Ummee tace "to yayi ai tana ciki seka kirata ku tafi ko sekun dawo" Shureim ya d'aga Kai ya tashi ya tafi, zaune suke suna fira kamar me magana haka Sarauta kejin dad'in fira da Shubai'a, Shubai'a na ganin shi ta mik'e tana nuni da "yayana ashe kazo, yanzu zaku tafi ne" ya d'aga Mata Kai Yana Kallon Sarauta, itama Shubai'a juyawa tayi ta kalli sarautar kafin tayi murmushi ta fice, ahankali ya k'araso cikin d'akin tare da cewa "my Mrs, yakike Kwana biyu bamu had'u ba" d'an k'aramin tsaki taja tace "let's do whats important" Shureim yayi murmushi yace "but your my wife" ta mik'e tana gyara suit d'inta tace "muje please" yayi murmushi yace "two minutes Ina zuwa, juyawa tayi tana tunanin dama Sir Shureim d'an iska ne.





" Uhmm Ina cikin farin ciki my golden boo zakazo na ganka" Diamond tayi maganar ta cikin wayar muryar ta cike da murna, shima Shureim yayi murmushi yace "Nima Haka my diamond nama fiki d'oki but you know what...." tace "ah ah seka fad'a my gold" yace "ashe zan iya acting d'in soyayya da gaske, tafa kusa kwaremin" diamond tace "yes my boy, Haka Nike so dama, dole mununa Mata kud'i ba komai bane a daular soyayya sena nuna Mata kuskuren ta" Shureim yace "essay mah diamond" tayi dariya tace "Uhm seka zo dai mayi magana kaji, yanzu kaje sekun zo, Allah ya kawomin Kai lafiya" Shureim ya amsa da "Ameen" sannan ya yanke wayar ya fito.





"in sha Allah Abieyna zamu kiyaye semun dawo" Abiey yace "yawwa y'ar Abiey adawo lafiya Allah ya baku sa'a" Sarauta da Shureim suka amsa da Ameen, har Airport suka rakasu seda jirgin su ya tashi sannan suka koma.






*to Allah yayi su Sarauta an d'aga zuwa 9ja*






*karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne, danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum dako yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)


....... 2nd June, 2023



*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ....... *043 & 044*





"daga Ina kike, bayan tun d'azu Nayi waya da Maryam Akan ki dawo" tsabar yanda Sarauta ta dibirbirce rasa ma mezata ce tayi seta fara y'an kameΒ², Hisham ne cikin yaren larabci yace "ah ah ummah ki barta kawai Babu komai" Ummah tace "ai dole Naji inda taje kullum burina shine na bata tarbiyya Aiko kaga dole na bibiyi rayuwar ta d'an nan" Shureim yayi murmushi yace "ai itad'in yarinyar karkice Ummah ko a makaranta bata zuwa ko Ina Koda kuwa party sukeyi atsakanin su d'alibai" Ummah tayi murmushi tace "Aini ako Ina zanyi alfahari da yarinyar nan tawa Sarauta akwai hankali sosai" Shureim yayi murmushi kurum, ummah ta kalleta tace "to Gasunan malamanki ne na makaranta kinsan kun gama abunda kukazoyi amma kika taho, tokin Sanma dayake yaran kirkine shine suka cema hukumar makarantar taku zasu biya Spain da d'alibai domin yin yawon bud'e ido, zasuyi ak'alla sati d'aya Anan kenan kinga zasu barmin ke Anan sannan su kuma sauran d'aliban za'a kaisu hotel su zauna ke kuma zasuna zuwa suna dubaki, Naji dad'i sosai wallahi bakiga godiyar Danayi musu ba" Sarauta tayi yak'e kafin tayi magana ummah tace "Ina zuwa" daga Haka ta wuce ciki, a fusace ta juyo tare da nuna ma MS Sarauta yatsa tace "how dear you, harkai wayene eyeh, what are you proud of, Ohh kazone ka sanar da'ita abunda yarinyar ta keyi Wato Idanma zata mutu ta mutu ko, you don't care about it, bcos she's not your mother, Humm Muhammad Shureim zan iya aikata komai Akan mahaifiyata, kuma ka gaggauta barin gidannan Ince it's not your father's own ko" Shureim ya mik'e tare da Kallon hanyar da Ummah tabi yayi murmushi yace "like mother like daughter, sedai itan tafiki kyau kuma bata da irin halin ki, ke you better calm down naxo ganin sirikata ne and kuma na ganta tama fiki kyau sosai" Sarauta ta rufe idonta ta bud'e sannan tace "Shureim!!!, disappeare from here" Shureim yayi murmushi yace "wannan mukullin dakike gani in-law tace ta bani tace mu zauna a d'akin k'asa har Sanda xamu tafi, dan Haka Babu ruwanki aciki Ohk" ta kalli Hisham dake Kallon dramar tasu tace "daga nan har zuwa Sanda zaku Bar gidan nan zaka iya samun gawar abokin ka" daga Haka ta juya a zafafe zata tafi, caraf yayi ya kama hannun ta yace "let's change the topic mana, daga Ina kike da aure na acikin Daren nan" ta kalleshi tace "ai tun a airport d'in JIDDA na ajiye shi sannan na taho aw Kai kayi tunanin da auren ka zan taho nan Hhh Kaci Kai wallahi" d'aurewa yayi ya koma ainahin Muhammad Shureim yace "daga Ina kike" kafin tayi magana Hisham yace "kunga Idan kunason Dagaske ku rufama kanku asiri to fa dole kowa seya ajiye wannan jinkan nashi Haba Haka akeyi ne" Shureim ya kuma d'aurewa yace "ke daga Ina kike" ta yunk'ura zatayi magana Hisham yace "wait Maryam Sarauta Ina kika je da daren nan" Sarauta tace "Wai kamar ni wannan ze dunga ma irin Haka a k'asata kuma gidana" Hisham yace "eh amma kiyi hak'uri Ina kikaje" tad'anyi Jim sannan tace "gidan su k'awata Maryam Nasir" Hisham ya kalli Shureim yace "to kaji gdnsu k'awarta taje Ohk dan Allah wuce mu tafi mu kwanta ni Nagaji" Shureim na tafiya yace "bazan iya Kwana cikin akurkinnan ba gaskiya" Sarauta ta bud'e baki tana Kallon shi kafin tayi magana harya sauka k'asa, Hisham ya tare ta dayaga tayi niyyar bin Shureim d'in yace "wait wait dan Allah kiyi hak'uri he's just joking, Anan zamu Kwana wuce ciki kawai" tsabar takaici kasa magana tayi Haka ta wuce d'aki.





"Humm gaskiya malaman makarantar nan taku sunada matuk'ar kirki nan suka zo sukayi ta Bani labarin k'ok'arin ki a makaranta gaskiya Naji dad'i sosai kema ya Kamata kuma ki k'ara maida hankali kinji" se sannan Sarauta tayi Jimm tana tunanin Ina Shureim yasamu labarinta kenan, ya akayi yasan gidan su, tabbas wannan maganar Abun dubawa ce to wayema yasan da Hakan, "Maryam Nasir" shine sunan da zuciyarta ta kawo Mata, tabbas Maryam Nasir ita Kad'ai ce tasan wannan sirrin, Kai ah ah Maryam bazata aikata min Haka ba, to amma kuma bayan ita waye wanda yasan da hakan, gaskiya Babu, kenan Maryam Nasir taci Amanata... "Sarauta lafiya kuwa" Ummah ta tambaya, yak'en dole tayi tace "lafiya klau Ina wani lissafi ne ummah" Ummah tace "to yayi Idan kin gama ki kashe mana hasken dama na gaji da firar" Sarauta tayi murmushi tace "tab lallai Aini nasha Kwana zamuyi Muna fira" Ummah tace "to ai Kece kin k'i bani labari ma sedai kiyi murmushi kuma fa yanzu 2 tayi kinga ya Kamata muyi barci kimaza ki gama wannan Lissafin naki ki kwanta" daga Haka ummah ta juya baya ta kwanta, nan Sarauta ta shiga yin tunani kalaΒ² Akan Maryam Nasir.






"abokina dole fa ka rage wannan yawan d'aukar zafin naka if not bazaku tab'a yin zaman lafiya da Maryam Sarauta ba gwara ka gyara" Shureim yace "wallahi Hisham Idan baka Dena ambatar Sunan nan Kai tsaye ba sena maka rashin mutunci Banza kawai" Hisham yayi murmushi yace "to ai Idan nace Sarautar kawai rud'ewa nake sena ma rasa cikin ku dawa Nike" Shureim ya tab'e baki yace "kaidai kasani" Haka suka cigaba da firar su duk da Hisham shine jigon firar.






*washe gari*





Tunda suka dawo sallah se suka samu guri a falon suka zauna duk da akwance suke amma Babu me barci a cikin su saboda ba sabon su bane gashi kuma akwai Sanyi Sanyi a garin ga kuma sanyin Asuba.





Around 8:30 Sega Maryam Nasir ta shigo, cak ta tsaya tana Kallon su kafin tazo da niyyar ratsa su ta wuce, Shureim nata kallonta zuwa can kuma seyayi d'an murmushi ya kauda Kai, harta hau Saman benen tana juyawa tana Kallon su tana idasa Hawa kawai ta juya ta kashe ma d'aya daga cikin su ido kuma hakan yayi daidai da fitowar Sarauta daga bedroom d'inta, cak ta tsaya tana Kallon abunda Maryam d'in keyi, tad'au almost 5secs kafin ta juyo da Alama Dai ta karb'i amsar abunda tayi ne, Sarauta ta danne mamakin ta da takaicin abunda Maryam tayi Mata tace "ah ah y'ar halak Ina nan Ina tunanin ki Ashema kina tafe" Maryam ta juyo ta fara zareΒ²n ido kafin tace "Uhm wallahi dama Mama ce tace na kawo miki kunun shinkafa datayi miki" kafin Sarauta tayi magana Sega ummah ta lek'o, kallon su tayi kafin tace "konace ashe motsin mutum nikeji" Maryam ta duk'a tace "Ummah Ina Kwana" Ummah tace "lafiya klau Maryam Ince dai kowa lafiya" Maryam tace "lafiya klau suna gaida ke" Ummah tace "Sarauta Kindai je kin gaida bak'in nan na k'asa ko" Sarauta tace "ah ah amma ai Maryam taje" ta k'arashe tana yin hanyar kitchen, ummah ta kalli Maryam tace "Aikin kyauta kuwa malaman Sarauta ne" Maryam tayi murmushi tace "konace ashedai da gaske turawan ne Nagani Aida farko na kusa rud'ewa Ince ma ummahrmu surukai akayi" ta k'arashe itama tanayin d'akin Sarauta, ummah tayi dariya ta girgiza Kai ta nufi kitchen domin ganin shafa'atu tagama had'a breakfast d'in, Sanda taje bata wani gama ba shysa kurum ummah tace Mata tabarshi kawai zatayi, Maryam ce ta Taya ta sukayi har suka gama abunsu.





"wallahiΒ³ Maryam Nasir Idan Nagano akwai wata alak'a ta munafunci a tsakanin ki da Shureim Allah kad'ai yasan abunda zan miki Munafuka kawai" Sarauta ta k'arashe tunanin ta tana me danasan in yarda da Maryam Nasir datayi Arayuwar ta.





*JIDDA*





"to dama maganar dazanyi muku kenan yanxu kwa iya tafiya" sarki ya fad'a Yana Kallon Ummee da Shubai'a da keta kuka, Ummee tayi yak'e tace "to Allah yasa hakan shiyafi alkhairi amma kuma jarumina se Nike ganin abarsu su k'ara samun kusanci kaga zuwa lokacin shima ya Gama karatun shi kuma ya nemi aiki" sarki yace "wannan ba matsala bace yaro dai yace auren yakeso ayi kuma inaga kawai ayi shid'in" Ummee ta yunk'ura zatayi magana sarki yace "kinga Babu gudu Babu ja da baya auren nan fa se an d'aura shi Kindai jini" da gudu Shubai'a ta fita daga d'akin tana fashewa da kuka, Ummee tace "Ina zataje kuma" ta fad'a tana k'ok'arin tashi, sarki yace "rabu da'ita duk inda taje seta dawo" amma duk da Hakan seda Ummee ta lek'a sedai Kash harta hau mota ta tafi, gudu tayi sosai kafin ta k'arasa Saman dogon tsaunin da zuwansa ma had'ari ne balle hawan shi ita kuwa ta hau ta Haye har can sama.




Runtse idonta tayi tanajin rad'ad'in abunda take shirin aikatawa dawanda mahaifin ta ke shirin aikatawa, baya taja daniyyar fad'awa, "Shubai'a!!!" yakira sunanta Yana haki da Alama ba k'aramin gudu yayi ba, cak ta tsaya kafin ta juyo tana tsoron ace Abiey ne ko yayanta dantasan zasu iya hanata abunda tayi niyyar aikatawa, murmushin takaici yayi kafin yace "kashe kanki zakiyi, nace kashe kanki zakiyi saboda wancan d'an iskan da Idanma kin mutu Babu damuwar shi aciki Babu abunda zeji dan kin mutu, meyasa Zaki mutu saboda shi Haba Shubai'a ki rayu mana kodan saboda mu kit rayu mana kodan soyayyar da muke miki" Fawax ya k'arashe maganar kamar ya fashe da kuka, tana bud'e ido taga waye setaji tak'ara tsanar kanta data tsaya tana sauraron wannan Munafukin, murmushi tayi kafin tayi mishi nuni da "wane munafunci kuma aka turoka nan kayi, bayan duk tare kake dasu me kuma ya kawoka nan kayi gaggawar barin gurin nan" ta k'arashe tana juyawa da niyyar fad'awa, dawani irin k'arfi ya jawota tayi gefe shikuma ya koma bakin Ramin ya tsaya "kina matsowa zan fad'a" ya fad'a Yana k'ok'arin fad'awa, dasauri ta tsaya ta matsa baya tana girgiza Mai Kai, "Yazanyi yakike so Nayi ne Shubai'a kasheni kike Son yine, Shubai'a INA K'AUNAR KI meyasa bazaki fahimta bane nasan bana supporting d'in abunda suke aikatawa, INA SONKI SHUBAI'A meyasa bazaki gane bane Kece farin cikina Kece damuwata gashi yau kuma kinason ki kashe kanki saboda wani Banza can ko to yayi kizo ki kashe Kan naki ki gani ni Idan zan rayu matso mana ki taho" ya k'arashe Yana bata hanyar, ai ita tunda ya furta Yana k'aunar ta light d'inta ta d'auke diffff, kusa da'ita ya k'araso tare da tsugunnawa kamar Dai yanda tayi ya kama hannun ta yace "Ina k'aunar ki Shubai'a wannan gaskiya ne dake kad'ai na tsara rayuwa ta maganar bakya iyayin magana ni ba damuwata bane, tunda dai nasan bakin ki ne baya magana amma zuciyar ki tanayi, Shubai'a please" ya k'arashe hawaye nabin fuskar shi, d'agowa tayi ta kalleshi hawaye nabin fuskar ta, magana take son tayi a yau Amman Abun ya gagara inama ace zata iya yin magana ayau, yanda take kuka Haka yake kuka, ganin kukan ta yayi yawa ne yasa Fawax ya jawota ya rungume, hak'ik'a Yana son Shubai'a dalilin Shubai'a abubuwa da yawa suka sauya a rayuwar shi Toshi meyasa baze yi k'ok'arin sauya nata rayuwar ba.






*KATSINA*





Se around 9:30 sannan su Ummah suka gama had'a breakfast d'in, a basket ummah ta had'ama su Shureim tace ma Maryam ta Kai musu, kafin Maryam ta d'auka ta tafi Sega Sarauta to fito sanye da atamfa doguwar Riga tayi kyau sosai, ummah tace "Yawwa Sarauta na maza Zoki raka Maryam k'asa ta kaima bak'i abincin safe" Sarauta ta kalli Maryam data duk'ar dakai a zuciyar ta tace "munafuka dama yaushe Zaki so Na rakaki karnaga munafuncin dakikeyi ko to duk zakaran da Allah yanufa da cara seyayi mtsww" ta k'arashe maganar zucin ta tana Jan tsaki kafin kuma a fili tace "shikenan muje ko Maryam" ta fad'a tana d'aukar wasu daga cikin kayan abincin, Maryam ma tayi murmushi ta duk'a ta d'auka suka sauka k'asa, a wannan lokacin Hisham ne kawai a falon, ajiyewa sukayi kafin Sarauta ta gaida shi ta juya fuuu zata koma sama, Hisham ya kalli Maryam yace "ita kuma Ina zata daga zuwan ku" cak Sarauta ta tsaya kafin ta juyo tace "to Inna tsaya mezan muku Aiga Maryam nan inace zaku iya zama tare" kafin ta juya Sega Shureim ya fito sanye da jallabiya yayi kyau sosai, ko Kallon inda yake batayi ba balle ta gane miye abunda ke faruwa, murmushin shi taji, tana d'agowa yad'an d'aure kafin kuma yace "kinyi kyau sosai" a fili taja tsaki ta wuce sama, Maryam ma tabiyo bayanta.






"dama Aina Gaya miki senaci girkin ki kuma gashi yau naci" Shureim dake kwance ya fad'a fuskar shi cike da annuri, ta cikin wayar akayi murmushi kafin tace "my golden boo Ina tunanin Sarauta fa ta fara gane komai akwai zargi sosai a tsakanin mu" Shureim yad'anyi jimm kafin yace "tabbas hakane Nima nafara wannan tunanin amma kinsan me zamuyi" diamond tace "ah ah bansaniba" yace "ita nata ilimin k'aramine zan nuna Mata babancin kwakwalwa, zamu biyo Mata ta hanyar da bazata tab'a tunanin wani Abu ba zamusa ta b'ata lokacin ta Akan tunanin gaibu mununa Mata babancin hankali mana" diamond tayi dariya tace "that's my baby boo, shysa banajin akwai abunda ze gagare mu, ammm yanzu nasan zatace zataje mahuta ko, to dan Allah golden ka barta taje, kaga muma zamu samu lokacin zama mu keb'e ko" yayi ajiyar zuciya yace "wallahi banason tana yawo sosai" diamond tace "ohonma dai" yayi murmushi yace "yi hak'uri b'acin ranki tashin hankali ne a gurina, shikenan duk yanda kika ce haka za'ayi" diamond tayi dariya.





"ah ah Maryam Wai dawa kike waya ne haka tuntuni" Maryam ta cire wayar a kunnenta tace "wata k'awata ce, ummah Ina Sarauta ne" tana can d'aki Wai kanta ke ciwo" Maryam ta mik'e tace "Bari naje na duba k'awata" Ummah tayi dariya tace "Allah ya k'ara had'a min kanku" Maryam ta fita tana fad'in "amin Dai ummahnmu"





"k'awata yadai" Sarauta ta yatsina fuska tace "Babu komai" Maryam tace Yawwa kinko San dalilin dayasa aka denayin shirin perfumes" Sarauta tace "Yawwa kin tunamin dama tun jiya Nike son Gaya miki" nan ta kwashe komai ta sanar da Maryam, Maryam tad'anyi Jim kafin tace "to Kije mahutar mana kiji mana miye dalilin kinga fa Kece silar auren nan" Sarauta tace "Uhmm Nayi tunanin hakan amma sir Shureim baze Bari ba" Maryam tace "ki gwada Dai k'awata" Sarauta tad'anyi jimmm tana tunani akai...........





*Karku manta Akan kud'i k'irk'irarren labarine Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)


....... 4th June, 2023





*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š




πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ........ *045 & 046*






Seda tad'anyi tunani akai sannan tace "shikenan Maryam zan gwada tambaya Amman Idan yayi min wulaqanci fa a kanki zan huce" Maryam tace "ah ah fa ban yarda ba Tohm" Sarauta tad'an tsuramata ido tana Kallo, Maryam tace "lafiya Dai ko kike kallona kodani Zaki tafi JIDDAn ne" Sarauta ta kauda Kai tace "keni abunma danike tunani daban wallahi" Maryam tace "me kike tunani ke kuwa k'awata" Sarauta tace "wani English literature ne nafara karantawa ya had'u sosai shine Nike tunanin yanda k'arashen ze kama," Maryam tace "har yanxu kina karanta literature ne Aini rabona dashi tun Ina school, amma Wannene kike karantawa" Sarauta tace " *THE BETRAYERS* " Maryam tace "maciya Amana, gaskiya da Alama ze had'u fa amma kuma tunanin k'arshen me kike bayan kin karanta" Sarauta tace "na karanta farkon amma har yanzu ba'ayi k'arshen ba, inason ganin yanda k'arshen nan ze kama wallahi" Maryam tace "to kiyima marubuciyar magana mana aiseta turo miki" Sarauta tace "marubuciyar a JIDDA take amma mawallafiyar a 9ja take kuma yanzu ake Kan littafin ki Bari kawai yakai k'arshen kema dole Zaki karanta shi" Maryam tayi murmushi tace "ke amma ya maganar auren ki" Sarauta tayi murmushi tana jinjina makirci irin na Maryam itada take tare da mijin da abokin shi shine take Mata wannan tambayar Wato ta k'ara kwasar sirrinta ta sanar Mata kenan to Ansha ta ta warke, ajiyar zuciya tayi tace "kinga Mubar maganar nan Bari inje in tambaye shi Inji dan ta ummah Babu matsala" Maryam ta d'aga Mata Kai.






"Asslamu alaikum" ta shiga bedroom d'insu bakin ta d'auke da sallama, Hisham kurum ta gani a zaune "Laaa yaa Hisham ashe Kaine Anan" Hisham ya juyo ya kalleta with full surprise yaya dai Anya yaji dakyau kuwa, murmushi tayi tace "brother Hisham Wai Ina abokin ka yake ne" Hisham ya mik'e Yana nuna Mata bayi kafin ya fice, almost 30mins segashi ya fito d'aure da towel a k'ugunshi, Sarauta tayi saurin juya baya, tsayawa yayi yana kallonta kafin yace "any problem" ta soma girgiza Kai tana kuma d'agawa, yace "Malama Talk now" tace "Uhm ai dama, towai kasa kayan mana se muyi magana" murmushi yayi kafin ya zagayo gabanta yace "abeg Malama open your eyes, ki kalleni mana nifa mijin ki ne, and forget about that yakika ganni na had'u kuwa" ya k'arashe Yana d'aga gira, rud'ewa Sarauta tayi zuwa can tace "kaga dan Allah ka Bari nan fa gidanmu ne kuma Ummah na tananan please" yasa k'afa ya tura k'ofar kafin yace "shikenan Nima ai Ummah tace ko, to namadai rufe k'ofar, yanzu bud'e idon seki fad'a min na had'u" Kai ta girgiza Mai cikin shagwab'ar da'ita kanta batasan tanada itaba tace "ah ah waikai koma ka tambayeni Meya kawoni" ya jawota jikinshi yana rungumeta yace "kafin nan Bari na fara yin k'orafi, meyasa d'azu baki saka Hijab ba kuma dai Sarai nasan kinga Hisham ko forget about that meyasa da kuka kawo abinci baki tsaya ba" itafa tunda taji ta ajikinshi gaba d'aya light d'inta ta d'auke, shima ta b'angaren shin Haka ne amma hakan kawai ya dake, Sarauta tace "Nidai yanzu ka sake ni sena sanar maka" rungumeta ya k'ara yi kafin yace "Meya kawoki ma Dai" ta d'an had'e gira tace "inason naje mahuta" yace "again Ina ne can kuma" ta marairaice fuska tace "labari ne me tsawo amma Idan na dawo zan sanar maka" yad'anyi Jim, kafin yace "shikenan to amma Allah Idan kika dad'e Nida Kene" batasan Sanda ta rungume Shiba tace "Nagode Nagode sosai my Mr" yayi dariya Wato Mr Idan tana buk'atar wani Abu, Sir abakin aiki, Shureim Idan rashin mutuncin ya tashi, dariya yake yi sosai, tsayawa Tai tana Kallon yanda wannan kyakkyawan bawan ke dariya ashe dama Haka faraa keyi mishi kyau, "dama kana dariya Har Haka ashe kana zamowa acikin farin ciki irin haka" d'an tsagaitawa yayi da dariyar kafin yace "farin ciki, tun Randa na fara ganinki Naji araina cewa tabbas na samu farin ciki, inaji ajikina Kece farin cikina" tayi murmushi tace "farin cikinka, nikuma zan baka farin ciki na iya adadin

Please Login or Register in order to submit comment