Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fira, suna dariya sosai dan zuwa yanzu kad'an ne Sarauta bata iyaba a yaren kurame, tariga ta saba da Shubai'a, sosai suke firar su, har dare ya raba, gaba d'ayan su barci ya d'auke su, ta d'aya b'angaren kuma Ummee ce keta fira da d'an nata a d'akin ta ganin dare ya raba yasa yace Bari ya tafi ya kwanta, al'adar Ummee ce duk in dare ya raba seta lek'a yayanta baki d'aya, yauma kamar haka ne, d'akin Shubai'a suka lek'a inda suka tarar dasu kwance suna barci, Ummee tayi murmushi tace "Ohh kaga yarannan Anan sukayi barci" Shureim yace "Kama rasa firar me suke" Ummee tana k'ok'arin gyara ma Shubai'a kwanciyar ta tace "ai dayake ma tasamu abokiyar firar, a gaskiya Shureim d'ana Ina son yarinyar nan domin ba k'aramin d'ebe ma Shubai'a kewa take ba tana k'ok'ari sosai, kaga Kamata ka kaita d'akin ta dare yayi dayawa" ya k'arasa bakin gadon ya tsaya Yana k'are Mata Kallo, Ummee ta d'ago ta kalleshi tace "my hero what's going on" yayi murmushi yace "kyakkyawa amma Sam bata da Hali" Ummee tace "ahankli zata gane komai Ohk" yace "Ummee akullum Idan na kalli fuskar ta takan tunamin da goggota" Ummee tayi murmushi ta k'arasa saitin da Sarauta take tayi baya da gashin kanta tace "Nima tana tunamin da aminiyata" kawar da idonshi yayi daga kanta yace "Ummee atashe ta sena rakata" ahankli Ummee tasoma Kiran Sunan ta harta farka, amma kasancewar akwai barci a idonta yasa seda Shureim ya rakata har d'aki, seda ya tabbatar ta kwanta sannan ya tafi d'aki



*washe gari*


At 10:30am


"Asslamu alaikum" Maryam dake ta d'aya b'angaren tace "Sarauta Dagaske Kece wayyo Allah na Wai Kece da gaske, yakike ya Aikin" Sarauta tayi murmushi tace "lafiya klau amma ai yadace a amsa min sallamar" Maryam tayi dariya me sauti tace "Uhmm hakane Wa'alaikumus Salam" Sarauta tace "to yakike yasu Naja kuma ya karatu" Maryam tace "Alhmdll amma waya Gaya miki na koma school" Sarauta tace "da mukayi waya da Ummah ne take sanar min" Maryam tace "Allah sarki ummah munata kewar ki" Sarauta tace "Nima Haka amma in sha Allah very soon Ina nan zuwa karki waniji kin damu" Maryam tace "to Allah ya kaimu" Sarauta tace "Ameen Ameen, Yawwa Maryam kamar Dai yanda kika sani ne Bana iya b'oye miki komai dan Haka Nike son ki bani wata shawara please" Maryam ta k'ara nutsuwa tace "inajin ki ta gurina" Sarauta tayi murmushi tace "Sarai kinsan abunda ya kawo ni JIDDA ko to (ta bata labarin duk abunda ya faru daga zuwan ta har maganar dasu kayi da Shureim) shine nace se Idan munyi magana sannan zan bashi amsa, Maryam yakike gani kenan na amince kuwa ko kuwa"...............



*tirk'ashi lallai to shin Maryam zata amince ko kuwa*




*karku manta Akan kud'i k'irk'irarren labari be danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*


@ *sherntee Ghayu* 😍 😍



@07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💴 💵

(A poor lady story)


*Story & writing*
*By*

@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚

👑J. W. A 👑


🅿........ *021 & 022*



...... Doguwar ajiyar zuciya Maryam tayi dajin wannan rikitaccen labarin sekace a littafi, seda ta tsaida hankalin ta Sannan tace "Sarauta kinsan wace shawara zan baki Anan" Sarauta tace "ah ah" Maryam tace "ki amince" Sarauta tace "what na amince kuma" Maryam ta gyara zaman ta tace "kwarai ma kuwa, kinsan meyasa, shi yanzu Sir Shureim d'in ai yasan komai game da Aikin da kikazo yi, kinga Idan kika amince Zaki samu Riba biyu na farko cikar burinki na biyu kuma ki farantama ummah, Idan kuma kika k'i amincewa ze koreki dan baze yarda ya zauna da wanda ze cuceshi ba korar kare ze miki, su kuma the five foolers kamar yanda kika ce zasu amshe gidansu da motar su dake gurin ki, kuma asirin ki ze tonu agurin ummah to mi akayi kenan, amma kinga Idan kika amince Zaki samu kud'in ki kuma kinga gurin wa'incan shashashun ma Zaki cigaba da samu sannan ga Ummee da Shubai'a Zaki samu arziki sosai k'arashe ki dawo gida kizo kinetic miji kiyi aure, gashi kuma zakiyi temako amma kuma sekin jure kuma kinyi dangana da duk abunda ya faru, Sarauta da Inada wata shawara bayan wannan dana baki, saboda Sam bamason abunda ze tab'a ki da tun farko shawara ta kika nema da bazan barki ma ki tafiba Ina k'aunar kine Sarauta " Sarauta ta goge hawayen dasuka zubo Mata tana cike da ladama da danasanin abunda tayima Maryam a baya tace" tabbas Maryam shawarar ki itace daidai har yanzu ke k'awace baki tab'a bani shawarar Banza ba Maryam Nayi miki ba daidai ba arayuwa dan Allah ki yafemin wallahi son kud'i ne yakaini aikata Haka kiyi hak'uri " Maryam na hawaye tace" Sam Sarauta karki d'aurama kanki laifin dama Allah ya rubuta shams ba mijina bane kiyi hak'uri kinji ni bakiyi min komai ba na yafe miki wallahi " nan suka cigaba da firarsu har gurin 12, tanata dariya, taji kamar shigowar mutum, ji tayi an amshe wayar ta bayanta, dasauri ta Mik'e, ajiyar zuciya tayi tace" kinga Shubai'a ki bani wayata wallahi waya me mahimmanci Nike kinga bani " Shubai'a ta mak'ale kafad'a ta juya ta fita da gudu, da gudu Sarauta ta rufe Mata baya," Shubai'a ki bani wayata please ki tsaya " shine kurum abunda Sarauta take fad'a ita kuma Shubai'a na gudu tana mak'ale kafad'a, gwaram taji tayi Karo da mutum, baya tayi zata fad'i dasauri ya rik'ota ta fad'o jikinshi, kallon juna sukeyi almost 2mins," kyasssss" sukaji k'arar camera na tashi duk suka juya suka kalleta, cigaba da d'aukar pix d'in tayi tana dariya, cike da mamaki Shureim yace "keeeh baki da hankali ne bani wayar nan" Kai ta girgiza Mai tana mishi Alama da "perfect match" dasauri shima ya rufa Mata baya, ganin sun Mata rufa² yasa tayi d'akin Ummee, Ummee na zaune gaban mirror taji shigowar su dagudu, abunda ya bata mamaki shine ganin harda Shureim ake gudun, saurin kama Shubai'a tayi tana fad'in "ya akayi ne Zaku samin auta tsakiya mitayi muku" ta k'arashe tana kama Shubai'a, Shubai'a na dariya sosai take nuna Mata pix d'in tana Mata nuni da "Ummee karki Bari su goge pix d'innan Allah Sunyi kyau sosai kimishi magana karya goge" Ummee ta amsa tana duba pix d'in tace "kul Idan ka goge pix d'innan kaga Shubai'a naso" Sarauta tace "Ummee ta bani wayana" Shubai'a tayi nuni da "Ummee kice ta Bari na tura sannan" Ummee ta had'e rai tace "kinga Sarauta barta ta tura mana bamfa sanki da Haka ba Tohm" Sarauta bata kuma yin magana ba har Shubai'a ta tura pix d'in, Shureim yace "kinga kinga Idan na Kam....." Tarin daya tsark'eshi ne yahana shi k'arasawa, dasauri Ummee da Shubai'a sukayi Kan shi suna mishi Sannu, Ummee tace "Sannu my son, kaga Miyasa ka biye musu kukayi gudu bayan kasan kanada asthma kanason cutar da kanka ne" ita keta surutun ta amma shi harya Kai k'asa, dasauri Sarauta ta d'auko ruwan dake gefenta ta mik'ama Shubai'a, Kai Shubai'a ta girgiza Mata, Ummee tace "Shubai'a maza d'auko min inhaler d'inshi jeki maza" dasauri Shubai'a ta fita daga d'akin, almost 4minutes bata dawo ba yasa Ummee tace "Sarauta Bari naje na d'auko mishi kinji kinga wannan mashiririciyar har yanzu shuru" bata jira amsar Sarauta ba tafice, tari yake yi sosai, haryana shid'ewa, dasauri Sarauta ta Kai k'asa tana kamashi tace "sorry sir yanzu zasu zo da Abun karkaji kawani damu kayi hak'uri" sosai ya rik'ota Yana Tarin, harya fara bata tausayi, sorry kurum take kira mishi, Haka harsu Ummee suka dawo, kasa sakinta yayi shysa Ummee ta bata inhaler tashak'a mishi, tana shak'a mishi wani wahalallan barci ya d'auke shi, ajiyar zuciya sukayi ganin barci ya d'auke shi, da temakon su Ummee ta kwantar dashi a saman gadon Ummee. Mik'ewa tayi tace "Allah ya bashi Lpy Ummee" Kai kurum suka d'aga mata, Shubai'a na zaune gefen shi ta kaama hannun shi tana murzawa, Sarauta tace "Shubai'a ki taso mu tafi" Shubai'a ta mak'e kafad'a, Ummee tace "Kije kawai y'ata ai Idan baganin ya farka tayi ba bazata tab'a tashi daga nan ba" Sarauta tayi murmushi ta fice, ita lamarin nan ya fara bata tsoro mutum Rabi ciwo, komai yayi ba lafiya, daga ciwon zuciya se ciwon asthma Allah Dai ya kyauta, Haka harta k'arasa d'aki, jikinta duk ya mutu, seda tayi wanka tayi sallah sannan ta kuma Kiran Maryam, "Wai d'azu Lafiya Muna waya aka yanke kuma baki kuma kiraba se yanzu" Sarauta tayi murmushi tace "wallahi Shubai'a ce ta amshe wayar Wai adole se munyi wasa" Maryam ta tab'e baki tace "Aida yake ta fini" Sarauta tace "Sam ba haka bane kawai Dai..." Maryam tace "kawai Dai me" Sarauta tace "towai ko kina kishi akaai ne" Maryam tace "kinga makaranta zani se anjima" daga Haka ta yanke wayar, itadai Sarauta kalar kishinnan na Maryam yana burgeta, aranar a gida suka wuni.



At 9:08pm


"ya maganar mu" Shureim dake zaune Saman kujera ya tambayeta, ajiyar zuciya tayi tace "na amince sedai akwai sharad'i" yace "fine inaji" tace "zaka had'amun da motoci guda uku, gidaje biyu da kuma company d'aya da filaye hud'u Idan ka amince fine" Yana mik'ewa yace "zan had'a miki dasu amma da sharad'in sekin gama aikin zan baki kuma koma miye ze faru Babu ruwana kin amince" tayi murmushin Jin dad'i tace "karka wani ji kadamu, indai Akan kud'i ne Babu abunda bazan iyaba Raina ne kurum bazan bayar ba" ya kalleta ya girgiza Kai cike da jinjina ma haukanta ya fice Yana fad'in "gobe za'ayi d'aurin auren" dasauri tace "to maganar agreement letter fa" yace "goben xaki saka hannu daga Haka ya fice. Nan take ta Kira Maryam ta sanar da'ita komai, Allah sarki to dama ita Maryam me zatace Idan ba fatan alkhairi ba, Haka suka gama wayar har ta Kira ummah suka sha fira abunsu.





*washe gari*


" Yawwa yarona so nikeyi kayi kyau sosai yau d'innan maza amshi sa" Ummee ta k'arashe maganar tana mik'a mishi agogo, yamutsa fuska yayi yace "Ummee wannan fa ba auren gaske bane dan Allah ki bari Wai duk miye ne hakan" Ummee ta dungure mishi Kai tace "gidanku Idan bakayi hakan ba Taya mutane zasuce auren soyayya kayi, kashirya kaima kamar Kowanne ango kodan ka b'atar musu da tunani Ohk" Kai kawai ya d'aga Mata ya cigaba da shiri seda ya Gama shiryawa tsaftsaf sannan ya kalleta yace "kina ganin Abieyna ze amince kuwa" tace "karkaji ka wani damu kaje kawai ba matsala" Kai ya d'aga Mata ya fice, direct masarautar ya nufa, rabonshi da palace d'in harya manta amma yau gashi ya d'au hanya, gaishe shi kurum ake amma shi Bama tasu yake ba, mamaki ne ya kusa kashe mutanen fadar ganin Yarima da kanshi yazo fada, shikanshi sarki yayi mamaki, guri ya samu ya zauna, seda aka mishi iso gurin sarki sannan sarki yace "Allah Dai yasa lafiya Naga Yarima dakanshi" Shureim na duk'ar dakai yace "lafiya klau ranka shidad'e Inada buk'ata ne" sarki yace "buk'ata kuma, Akan miye" Shureim yad'anyi shuru kafin yace "aure Nike son ad'auramin yau Nida masoyiyata" ba sarki kad'ai ba duk mutanen dake gurin sunji mamaki akai sosai, cikin dakewa sarki yace "aure kuma Yarima kaida WA" Shureim yace "Allah ya temakeka Nida masoyiyata" sarki yace "wace ita kenan" Shureim yace "abokiyar aikina ce ranka shidad'e P.A d'ita Nike magana akai" sarki yace "shikenan zanyi bincike akai" Shureim yace "Nayi duk abunda ya dace akai Muna son junane ranka ya dad'e ka temaka a d'aura auren nan Anan yanzun nan" sarki yayi shuru nad'an lokaci kafin yayi ajiyar zuciya yace "kiramin yarinyar" Shureim ya fiddo wayar shi ya kirata, cikin minti 10 ta shigo fadar, tana sanye da doguwar rigar abaya ja, tayi kyau sosai duk da fuskar ta Babu ko powder, kowa seda ya yaba da kyanta, ta zauna gefen Shureim ta gaida kowa harda sarki, seda aka d'an d'au lokaci sannan sarki yace "yarinya mine sunanki" kanta a k'asa tace "Maryam Sarauta amma Sarauta ake kirana dashi" ba iya sarki ba duk dattijawan dake cikin masarautar sun girgiza dajin Sunan nata, sarki yace "Sarauta Dai" Sarauta ta d'aga Kai, sarki na k'ok'arin b'oye mamakin shi yace "miye tsakanin ki da Yarima" tayi k'asa dakai yayin da Shureim ya kafeta da ido sekace Dagaske soyayyar akayi, murya can ciki tace "masoyina ne mund'au tsawon lokaci a tare Muna son junan mu sosai" sarki yace "kin amince Zaki aure shi" Sarauta tace "hakan swine burimmu ranka shidad'e na amince" sarki yace "Babu ruwan mu duk abunda yaje ya dawo" ta d'aga Kai ta kalli Shureim suka had'a ido tace "indai Yana nan nasani Babu abunda ze faru" sarki yayi ajiyar zuciya yace "Imam Uzaif zoka d'aura aurennan, nan take aka d'aura auren inda Shureim ya bada zoben gold d'in dake hannunshi Amatsayin sadaki, nan take masarautar ta d'auka, and'aura auren Yarima, wannan lamarin ba k'aramin d'aga hankalin wasu daga cikin mutanen masarautar yayi ba wasu kuwa Sunyi murna sosai dan awannaan lokacin Shubai'a na d'akinta tana rak'ashewa..



*3 hours later*



"tabbas kin cika Aikin ki kamar yanda kika fad'a" Sarauta tayi murmushi tace "indai na Hari Abu tofa senayi nasara akai yanzu Dai samin kud'in a account d'ina" Khameel yayi murmushi yace "ai Ina samun labarin d'aurin auren na tura miki kud'in ki" ta fiddo wayar ta taduba tayi murmushi tace "kayi Abu me kyau yanzu Bari inje karsu zargi wani Abun" jabeer yace "kidai kula" tace "karku wani ji kundamu" daga Haka ta tafi, fawaz yace "Bros nifa yarinyar nan ban yarda da'ita ba Anya kuwa Baku ganin akwai abunda take shirya mana" Khameel yace "amma Kai fawaz dak'ik'i ne wallahi kana ganin wannan yarinyar zata ci amanar mune sauran kud'ad'enta na hannun mufa" fawaz yace "amma ai.." JABEER ya katse shi dacewa "amma ai me Wai Kai wane irin d'an shegiya never kaga Banza dak'ik'i ze b'ata mana shiri ku tashi mu tafi shagalin bikin d'an uwa mana" daga Haka duk suka tashi suka watse suka Bar fawaz da jimami.




"mene aure fa kuka ce, shi harya Isa dan ubanshi ya auri wacce ba Khaleesat ba Aiko abunda baze yiyubane gobe gabennan jirgi na ze sauka a jidda da farar safiya ma kuwa zeci ubanshi" Hajja jumaima dake rik'e da waya a hannun ta tace "ki kwantar da hankalin ki Sirayya komai ze zodasauki kinji" Khaleesat dake gefe ta k'ara fashewa da kuka tana fad'in "na shiga ukuna zuciya ta mutuwa zanyi" Sirayya tace "na kwantar da hankali na agidan ubanwa kinaji shalelena na kuka nabani na wallahi kar abari na k'araso gidanna nan shalelena ki kwantar da hankalin ki kinji komai ze wuce ai gamunan ma mun taho" Haka saketa yin wayar, Idan jumaima ta lallashi Sirayya ita kuma Sirayya ta lallashi Khaleesat, abundai ba magana.




"yanzu ke dama kina da masoyiyata zeyi auren nan amma baki sanar min da wuriba" Ummee na sunkuyar dakai tace "kayi hak'uri jarumina Nima sau d'aya muka tab'a yin maganar amma banma d'auka da gaske yake ba Allah" sarki ya kalli Shubai'a yace "nasan kinsan komai gayamin ya akayi" Shubai'a ta girgiza Kai tana nuni da "Allah bansan komai ba Abiey" ajiyar zuciya sarki yayi yace "to Aidai an d'aura auren ko to yayi kyau Allah ya bada zaman lafiya" duk Kai suka d'aga Mai, ringing d'in da wayar shi keyine yahana shi yin magana, Yana Kallon screen d'in wayar yaji gabanshi ya fad'i, kallon Ummee yayi ya kuma Kallon wayar, Ummee tace "lafiya wake Kira" Yaja dogon numfashi yace "Sirayya ce" Ummee tace "Sirayya kuma, Wai Allah maza ka d'aga kafin ta yanke" d'aga wayar yayi bakin shi d'auke da sallama, kuka ta fashe mishi dashi tana cewa "yanzu yaya abunda kayi ka kyauta mun kenan gaba d'aya kadena sona kasani Banida farin ciki sama da Khaleesat amma ka aikata mana Haka Sarai kasan tanason Yarima amma kayi Mai aure yanzu ka kyauta kenan ni nasani da d'iyar Nur ce hakan bazata faru ba dolema seya aure ta amma ni saboda ba'asona ba'ason farin cikina shikenan ganinan zuwa gidan zakuga abunda ze faru sena k'ona gidan kowa ma ya huta wayyo ni mataccen mahaifina ka mutu kabarmu da d'an uwa meson kanshi da ahalinnan da yawa, Allah seya saka mana wiwiwi "ta cigaba da kukanta sannan ta yanke wayar, ajiyar zuciya sarki yayi yace" tabbas Inada son Kai da d'iyar Nur ce dole zansa shi ya aureta koyana so ko beso, amma Ita na Aikata Mata haka " ya k'arashe Yana duk'ar da kanshi, Ummee ta matso kusa dashi ta dafa shi tace" karka damu ka Bari tazo d'in se muga yanda za'ayi "sarki ya d'aga Mata Kai, Shubai'a ta Mik'e ta wuce d'akinta abunta ranta k'al.




" hummmm *HISHAM* kenan komai ya faru yau dinnan" ta cikin wayar akayi dariya kafin yace "ango mijin amarya nifa Abunnan ba k'aramin mamaki ya bani ba Allah, Wai Dagaske ta amince kuma harma ta aureka" Shureim yace "yarinyar zata iya aikata komai Akan kud'i banajin zan iya sake Mata komai" Hisham yace "karka damu hakan ma wata dama ce kasamu kayi amfani da'ita" Shureim yace "Hisham yaushe zaka dawo ne Allah Inada buk'atar ganin ka" Hisham yace "karka damu zanje Nigeria na dawo kasan harkar audugar nan ta fad'a so dole nizanje Idan na dawo sena biyo ta nan" Shureim yace "shikenan yanda kace amma dazaka Bar sana'arnan amma kaidai Naga Ka yarda da'ita sosai" Hisham yace "gaskiya Kam barni Anan d'in nafi Jin garau, Wai Ina y'a kurma ne shuru kakaje" Shureim yace "zamu samu matsala fa kadena kiranta da kurma Kadai ji" Hisham yayi dariya yace "ita Bama magana take ba balle na kirata mu gaisa amma Dai ka gaisheta da yaren dazata gane" Sarai yasan Mize faru shysa Yana gama magana ya yanke wayar Yana dariya, shima Shureim murmushi kawai yayi......




*karku manta labarin AKAN KUDI kirkirarren labari ne wanda Nayi shi domin nishad'antarwa fad'akarwa dakuma tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*


@ *sherntee Ghayu* 😍 😍



@07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💴 💵

(A poor lady story)

....... 15th May, 2023


*Story & writing*
*By*

@ *Sherntee Ghayu* 😍 😍



🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚


👑J. W. A 👑


*Tohm Allah yayi na dawo, y'an uwana Ina barar adduar ku am in a difficult situation I wrote my interview exams please help me with your prayers*





🅿....... *023 & 024*





"kaidawa kake ta waya ne haka" ya d'aga Kai ya kalleta yace "Hisham ne Ummee ki shigo ciki mana" Kai ta girgiza tace "dama na leko kane ashe bakayi barci ba, shikuma wancan sakaran yak'i dawowa se y'ar banzar waya" Shureim yayi murmushi yace "Nima seda Nayi mishi maganar" Ummee tace "to shidai ya sani ai seyayi ta zama, kanajina kaje ka duba Idan Sarauta tayi barci, seka dawo kaima ka kwanta" baya iya gardama da Ummeenshi ko Abieyna shiyyasa ya d'aga Mata Kai kawai, daga Haka ta juya ta tafi.



"Asslamu alaikum" ya shiga d'akin bakin shi d'auke da sallama, bata nan, yatsaya domin jiran fitowarta, tana bayi, kuka takeyi sosai har ranta, Wai yau ita aka d'aurama aure da wanda batasani ba meyasa zata aikatawa ummahnta Haka tabbas tasani ummah bazata yafe ba bata kyauta Mata ba, dama kullum cikin kukan ladama take gakuma wannan gungumemen laifin data aikata, seda taci kukan ta me isarta sannan ta wanke fuskarta ta fito, turus tayi ta tsaya ganin shi tsaye a bakin k'ofa yad'an jingina, saurin kawar da fuskarta tayi daga Kallon shi tace "lafiya" Yana gyara tsayawa shi yace "k'a'idar gidannan ce aje a duba ya mutum ya kwanta kuma ya yatashi" tad'an harareshi tace "amma Naga hakan kamar Aikin Ummee ne" yace "kwarai aikinta ne amma ga single baga marriage ba" ta d'ago ta kalleshi, yad'an Ja yaji yace "Meya saki kuka" ta d'aure fuska tace "kuka nace maka Nayi" ya girgiza Kai ya juya ya nufi k'ofa Yana fad'in "seda safe" bata tanka Shiba harya fice Abun shi. Yanda taga rana Haka taga dare domin Abun duniya ne yabi ya isheta jitake yi inama ace ummah tasan komai da hankalin ta yafi kwanciya.



*WASHE GARI*



Duk ahalin sarki junaid maleek sun zo, Sirayya, Ni'imatu, safiyatu, duk yaransu ma sunzo, gaba d'ayansu zaune suke a falon, Shubai'a, Juwaira da Khaleesat inbanda Aikin kuka Babu abunda sukeyi, sarki ya d'aga Kai ya kalli Shureim sannan ya kalli sauran y'an uwanshi da yaransu yace "ni yanzu Babu abunda zance daku face...." cikin sauri Sirayya ta katse shi da "face me, nace face me fa, duk cikinmu Babu wacce kake k'auna, munan mune k'annan ka amma baka k'aunar mu kafin k'aunar wannan munafukar matar taka wacce da'ita aka had'a baki gurin tafiyar Nur amma ni nasani Ni'imatu kema kinsani kema Safiyatu kinsani yaya bayason mu baya k'aunar mu ku dubi halin da yarannan suke a ciki, kuna ganin da d'iyar Nur ce Anan zebari hawayen ta su zuwa abanza ne ai baze tab'a Bari ba Mudai kawai munyi rashin uba " ta k'arashe tana fashewa da kuka, Safiyatu tace" wannan Haka ne wallahi yaya bakason mu nisheda ce da d'iyar Nur ce a matsayin Shubai'a ko Juwaira Babu abunda ze Hana ayi auren nan amma Babu komai yaya Sirayya kidena kuka" Ni'imatu tace "Safiyatu barta tayi kuka ai kuka damu ya dace mu y'an marayun Allah wallahi yaya kaji tsoron Allah, Allah fa ze sakamana, tun bayan mutuwar sarki akwai wacce ta tab'a zuwa maka da buk'atar tane bayan yau amma ka kasa mukawai zamu je munemi wani d'an uwan dama ai ba uwa d'ayace ta haife muba "ta k'arashe itama tana saka kuka, Neenah tace " yanzu Zabvier ka kyauta kenan abunda kayi Haka kake son zumuncinku ya rabu " sarki yace " yanzu ya kike son ayi Hajja Neenah "Neenah tace "kasashi ya auri Shuwaiba kawai" Hajja jumaima tace "kiji tsoron Allah Neenah Ina laifin ya auri yarinyar nan Khaleesat tunda Dai ita ke matuk'ar so shi" Hajja Mubeena tace "uban son nace uban son idanma maganar so ake ai Juwaira ita ta dace dashi ba suba" Sirayya tace "kinga Hajja inajin kunyar ki Babu wacce ze aura face Khaleesat kuma duk wacce tace zata kawomin wawta Anan se'in kashe ta kowa ma ya huta Aikin Banza kawai Kai yaya kasan abunda ka'iya faruwa gwara ka sanar da d'anka ya

Please Login or Register in order to submit comment