Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli Shureim ta cigaba da cewa "yaya dan Allah hak'uri zakayi ka bani kurum kaga zama a Ukraine Haka Babu kud'i a hannun mutum kuma baya da wata sanaa ai had'ari ne Babba nasan zan samu agurin ka fiye da kowa shysa naxo gurin ka" ba tare daya d'ago daga danna laptop d'in dayake ba yace "nawa kike buk'ata" tayi murmushi tace "10m yaya" ya d'ago ya kalleta kafin kuma ya mik'e ya d'au wayar sa da laptop d'in sa yace "I will transfer you 5m" daga Haka ya wuce bedroom Abun shi, Sarauta tayi murmushi tace "don't worry about it Uhm I will transfer you 10m seki had'a da nasa kinji" Juwaira ji tayi kamar Sarauta ta tsundumata gidan aljanna "10m fa kika ce sister, wow gsky Nagode Nagode sosai Allah ya barki da yaya Allah yasa mutuwa ce zata raba ya Baku zuri'a dayyuba Nagode y'ar uwa" Sarauta tayi murmushi tace "Ameen Ameen, karki damu kanki ai duk yima Kaine kinji kuma mu ai zaman lafiyar ki muke buk'ata Allah ya bada zaman Lpy" nan suka cigaba da fira sun d'an Jima suna fira kafin sukayi sallama Juwaira ta tafi ita kuma ta shiga bedroom gurin mijin ta. Fitowarsa wanka kenan ta shigo, harta juya se taji yace "Ina Zaki zonan inason muyi magana" tsayawa tayi tana saurarensa, Yana shafa lotion yace "meyasa Zaki bata kud'i masu yawan Haka kodan ba nema kikayi da kanki ba, Uhm to inason ki sani akwai companies d'inki da yawa da suke buk'atar gyara kuma akwai aiki da za'ayi sosai za'a cigaba da aiki dasu kamar dai da, ki Dena b'annar kud'in nan Haka, Haka kawai ki d'auki 10m ki bada kyauta Haba mana my Mrs" tayi m tana tuna rayuwarta da Maryam Akan kud'in napep ma rigima suke Wai yau kuma itace tayi kyautar 10m Allah me iko, tayi murmushi tace "Mr kenan tunda Allah ya bani ai sena temaka ma y'ar uwata ko kuma kaga aure zatayi ya Kamata a bata ko" Shureim yace "to me y'ar uwa" bata ankare ba seji tayi ya rungume ta tabaya, lokaci d'aya suka saki ajiyar zuciya, a hankali yace "yanzu gayamin na had'u kuwa" ta shagwab'e fuska tace "Uhm Nidai ka sakeni" yayi murmushi yace "sekin fad'a na had'u" tayi murmushi tace "ai mijina ya had'u sosai ba'a magana 👌, mijin mace d'aya ai had'add'en gaske ne tako Ina Malam ka had'u fa" murmushi yayi tare day juyo da'ita suna facing juna yace "really really love yhu my dear Mrs" ta kama kumatun shi tace "really love you more and more and more my dear husband" lokaci d'aya suka yi dariya, sunjima suna Kallon juna kafin kurum taji bakin sa Saman nata kissing d'inta yake sosai da sosai, tun suna tsaye har tsayuwar ta gagaresu suka kwanta, sunjima ahakan kafin ya soma romancing d'inta, cikin d'an lokaci kuwa, hummmnn, Tohm, (diamond kar Naji kince wani Abu Babu abunda ya faru to ko besty) kwance take ajikin sa se ankare zuciya suke, "baby Zaki bani Muje" bata iyayin magana ba se d'aga mishi Kai da tayi, ya kuma cewa "next two days zamuyi tafiyar" nan ma d'aga Mai Kai kurum tayi ganin bata cikin yanayin yin maganar kurum yasa ya rabu da'ita cikin d'an lokaci kuma barci me dad'i ya d'auke su.





Seda aka maida Maryam Nigeria sannan aka tura mutane da jira domin su d'auko ta, anyi shagali sosai a bikinnan,iyayenta ma seda ya sauya musu gida na gani na fad'a wanda seda aka fara kace nace akai tsabar had'uwar sa, to dama surukan babban d'an kasuwa kamar Hisham wanda k'asashe kad'an ne ba'a San Shiba ai dole yayi musu fiyema da Hakan, satin su d'aya a mekkah kafin ya tattara matar sa suka koma Russia da zama saboda kasuwancinsa yanada k'arfi sosai a can. Suma suna zaune lafiya Maryam se tace akeyi wani ma kafin tace yakeyi (Uhm kaga mijin Kan tace wannan ai kafi k'arfin mijin tace, kuma aje waje ai tayima yaran mutane muzurai).






B'angaren su Hajja kuwa, suna barin gidan sukai d'auki hanyar barin gari, dab dazasu Bar garin suka samu mummunan hatsari wanda nan take Hajja Mubeena tace ga garinku nan ita kuma Hajja jumaima ta rasa k'afafunta duka biyu, asibitin kusa dasu ne suka basu temakon gaggawa ganin ba'a samu masu gawar Hajja Mubeena ba kuma ga Hajja jumaima bata hayyacin ta tsawon Kwana 5 yasa aka tara mutane akayi Mata sutura aka kaita makwancin ta (rayuwa kenan wannan babban balai ne, Kai kana ta haukan ka Aduniya bakasan yaushe ne lokacin mutuwar ka ba kuma a Ina zaka mutu kuma Me kakeyi zaka mutun to miye maganin tantamar ta hanyar zama ashirye mana mudena duk abunda ya zamana sharri ne, mu zauna a guri tsafta tacce mu RAYU da zuciya d'aya, Allah yasa mu cika da kyau da Imani Ameen Y hayyu y qayyum) kusan wata 2 Hajja tayi a asibitin tana jinya kafin suka buk'aci ta Kira wani nata domin xasu sallameta, Babu yanda zatayi Haka ta basu number Sirayya, da farko Sirayya taso tak'i zuwa to amma ai naka naka ne duk lalacewar sa balle kuma uwa mahaifiya, a kusa da asibitin ta kama Mata gida inda ta d'auki nurse biyu masu kula da'ita, duk in tazo dubata zata biya prison ta duba yarinyar ta wacce zuwa yanzu ta Gama yin ladamar duniyar nan. Sam nurses d'in da aka d'aukar ma Hajja basada kirki, rashin mutunci suke Mata sosai, ita kuma rashin hak'uri Aiko su Kamata su jibga kayar su kuma wata yayi a biyasu kud'in su.




Bayan wani lokaci kuma Hajja ta Dena magana kwata kwata se IHU kamar sabuwar kamu, gashi tayi ta fincike pampers d'in dake jikin ta, su kuma nurse d'in ta su jibga kayar su inta ishesu da IHU kuma su dod'e da airfees wani xubin ma Haka suke barin ta setayi Kwana da kwanaki da naja a jikinta, Watan ta 8 a wannan halin kafin ta amsa Kiran mahaliccinta, (Niko nace taje can ta had'u da nurse's d'in lahira kuma sudai na duniya sun gama Aikin su) tabbas uwa uwace, Sirayya tayi kuka WA mutuwar nan itada Khaleesat sosai da sosai, bayan ankaita kuma ta rufe gidan ta sallami nurses d'in ta biya tayi sallama da y'ar ta sannan ta wuce ta koma gidan mijinta ta NATSU ta maida hankali akai.





NEW YORK CITY




Watansu biyar da Baro gida basu wannan k'asar basu wannan, satin su d'aya da zuwa newyork sedai basuyi abunda ya kawo su ba sakamakon ciwon da Sarauta take fama dashi wanda kuma ko magana batayi Idan tayi magana se amai, gashi se wani sihirtaccen kyau take.




Yanzu ma zaune take a had'add'en falon Nasu ta d'ora k'afarta Saman Center table, ga cikin ta da ak'alla zekai wata hud'u da satuka, tana sanye da Riga da wando na Sanyi masu kyau, film take Kallo a dank'areriyar tvn dake falon, kamar Ance ta d'ago Aiko tana d'agowa suka had'a ido daga Saman benen, saukowa yake Yana wani kashe ta da murmushin love, itama murmushin tayi tana Kallon sa, zama yayi gefen ta Yana rungumota yace "babyn nan namu be dubawa dad d'insa ba gashi ya Hana Ammerh magana Hum" Sarauta tayi murmushi taja kumatunsa, magana take son yi kuma tana tsoron ta k'ara b'ata kayan jikinta, Sam cikin nan baya bata matsala ta ko'ina gashi kuma cikinta ya bud'e abinci take ci sosai gashi tanajin k'arfin jikin ta amma fa sedai ba magana, HAR tambayar kanta take kodai kurma zata Haifa, suna son suyi fira amma Abun allah ya gagara, ko waya aka kirata yanzu tama Dena d'agawa sedai ayi chat da'ita, duk da Babu wanda yasan halin da take ciki, ya Jima nan zaune Yana Mata fira tana dariya kafin suka tashi suka fita domin tattaki, atare suketa rainon cikin su suna fatan Allah ya sauke su lafiya.





3months later





Tare suke had'a kayansu a akwatin, Shureim ya rik'e ta ya zaunar da'ita yace "ma'am zauna nan kinji banason kina Aikin nan wallahi ga wannan cikin naki yanda kikasan yanzu Zaki haihu ma KUMAFA ko wata bakwai kenan amma Babyn namu ko badai girma ba" Sarauta tayi dariya tace "Nidai muyi sauri kasan na k'osa naje Naga k'awa....." ai bata k'arasa ba se amai, murmushi yayi ya girgiza Kai, ya temaka Mata suka shiga toilet ta sauya Kaya sannan ya gyara gurin ita kuma ya kwantar da'ita domin ta Samu ta huta, kusa da'ita ya dawo ya zauna ya kama hannun ta yace "to waike Mrs Haka akeyi daga Babyn mu ya d'aga miki k'afa two days kina d'an yin magana kuma seki dungayin me tsawo Haka, to Allah Idan ma wahalar min da kanki zakiyi kawai mu fasa zuwa ko'ina mu zauna nan har sekin haihu sannan" ta shagwab'e fuska tare da girgiza Kai yace "please Mrs karki wahalar min da kanki kinji" ta d'aga Mai Kai tana kwanto da Kansa Saman k'irjinta, ya rungumota shima, nan kuma aka manta da maganar tafiya aka cigaba da harka.






Russia




Maryam ce tsaye agaban Shureim tana masa magana, amma yayi shuru, duk'owa tayi tare da kama lips d'insa tad'an ciza, Aiko ya jawota ta fad'o jikin sa, ya maidata ya kwantar ya soma yimata cakulkuli tana dariya seda ya tabbatar ta gaji sannan ya kyaleta, ya kwantar da Kansa Saman cikin ta yace "Babyn Abba kinga mamanki ko tanason k'awarta tazo tabar Abba" Maryam ta d'ora hannun ta Saman gashin Kansa tace "Wai husband waye yace maka mace xan Aifa" yayi murmushi Yana facing d'inta yace "inason baby girl ne me kama dake wify" tayi murmushi tace "to Allah ya bada Me albarka, ni dagani Muje ko, ya Harare ta yace "dama nasan Mrs Sarauta na zuwa za'a yardani" tayi dariya tace "Haba mana d'an shalelen mijina aikai d'in dai Kaine karka damu inanan tare dakai kaji" ya d'aga Mata Kai kamar k'aramin yaro tace "nan da 7 month rainon ze zaman min biyu gana baby gana Abban baby ko" yayi dariya ya mik'e tare da d'aukar ta gaba d'aya suka fita suna dariya.





Su Sarauta sunzo Russia lafiya, tunda Maryam ta gane abunda ke damun Sarauta kuma se dariya, WAI k'awarta taxama kurma har wani kwantar dakai take tana cewa Allah sarki Mrs billionaire kuma an kurmance" ranar Maryam tayi Mata fira sosai duk da itama takan d'an jefa nata aciki shidai Shureim ba kunya ba tsoron Allah yak'i barin Sarauta tayi sakat dan yasan tana samun Dama kuma se surutu ai tayi ta Amai karshe ya sakar Mata zazxabi.




Kwanan su uku a Russia kafin suka wuce 9ja domin gaida iyayen Maryam, duk da Shureim be wani so hakan ba amma kuma ai iyayen Maryam ne, sinje kuma Maman Maryam taji dad'i sosai da sosai duk da itama Maryam d'in bata dade da zuwa ba domin duk in tana son zuwa Hisham yakan rakota a prvt jet d'in shi inkuma yanada meeting ma Sukan zo tare seta je gida wani xubin tazo ita kad'ai, Maman Maryam da malam ko kuma Ince Alh Nasir sunji dad'in zuwansu sosai da sosai, seda sukayi sati Anan, HAR Layla seda tazo suka gaisa lokacin itama ta Haifi yarinyar ta Amina kyakkyawa black beauty me kama da baban ta, Sarauta taji dad'in samun labarin yanzu Layla y'ar kasuwa ce sosai takoina kud'i zuwar Mata suke gashi kansu had'e itada Maman ukasha Wato kishiyarta, satin su d'aya suka d'auki hanyar komawa gida.




Tafe suke a mota, kamar Ance Sarauta ta juya kurum ta hango ta tsaye itada me napep sunata jaraba, da hannu tayima Shureim Alamar ya tsaya Aiko ya tsaya, seda ya fito ya temaka Mata saboda yanzu cikin ta 9months ne wahala yake bata sosai, zagayawa tayi tare da dafa kafad'arta, Sam Hauwa Mansour me gidaje ma bata Ankara da waye ya tab'a ta ba Aiko ta ture ta dasauri Shureim ya tare da, tasssss kake ji Shureim ya d'auke hauwa Mansour da Mari Har guda biyu, hauwa ta juyo tare da cewa "durin uwarcan...." cak ta tsaya sakamakon ganin Shureim a gaban ta dayayi Mata kwarjini kamar Ance ta kalli Sarauta kuwa ta kalleta "Kut Maryam Sarauta" Sarauta tace "dalla Malama Ina miki magana amma kinacan kina hauka" hauwa tace "daallah rabu da wannan tsinannen ne yake son b'ata min rai Akan kud'i" Sarauta tace "nawa ne kud'in nashi" me napep yace "150" Sarauta tayi ajiyar zuciya yaushe rabon dataga 150 ita kuwa tun tana Maryam Sarauta ba Mrs Sarauta ba, kallon Shureim tayi da yake ta b'ata rai tayi murmushi tare dasa hannun ta a aljihun shi tad'au ko kud'i, dubu biyar taba me napep d'in yayi Mata godiya, hauwa tace "matsiyaci" yace "akwai matsiyaciya ne kamar ki Banza y'ar Tasha Haka xaki k'are k'aruwa kawai, wallahi yau da ba'a biyani kud'in nan ba dasena nuna miki k'arashen tashan ci mtsww y'ar iska" daga Haka yaja napep d'insa Yana cewa "Nagode hajiya Allah ya sauke ki lafiya" Shureim ya amsa da "Ameen" Sarauta ta dafa hauwa tace "Meya faru hauwa Mansour Ina karatun naki kuma me kikeyi a 9ja" hauwa tace "Hum Maryam Sarauta kenan to dama kinsan ni Babu abunda na iya amma aka wani daukeni aka kaini Malaysia Wai karatu Aiko kusan sau uku Ina d'auko carry over, ganin kar Nayi 2/0 yasa na ajiye karatun kurum muka koma harka, Wato Dai drug abusers bamu wannan club bamu wannan, shekara na biyu acan aka sendo mu 9ja, Dana dawo kuma old man ya amshe komai dake hannuna yanzu in kinganni da kud'i to kayan kud'i na bada aka bani amma sab'anin Haka kuwa sedai nayita haukana a d'aki amma Babu me bani ko sisi dazan ja harka, Uhm nifa sauri nike ana jirana kar Kaya su k'are amma nace ke kin cika naki burin" Sarauta tayi ajiyar zuciya tace "Uhm lallai hauwa, Allah ya kyauta, amma Hauwa kinada ilimi fa meze Hana kiyi amfani da ilimin ki dan Allah ki Dena wannan rayuwar mana ki koma hauwa dai wacce muka sani please hauwa" hauwa ta tuntsire da dariya tace "tun Ina Lissafin irin ku yanxu ni harna Dena, anyi har an hak'ura dama wani Abun ba alkhairi bane Arayuwar ka k'ilama dake kikaje da k'asar tayi alfahari dake wata rana amma mukayi amfani da son zuciya, kinga nizan wuce a gaida Maryam Nasir" Sarauta ta rik'e ta ta Mika Mata kud'i hauwa tace "inma kinbani fad'uwa zasuyi dan yau nasan maidani gida za'ayi Idanma na koma dasu gidan amshewa za'ayi, kinga cikani Malama kina b'atamin lokaci fa mtsww" ta fisge hannun ta ta juya ta tafi, Sarauta kuma ta juya ta rungume Shureim tare da fashewa da kuka tana tunanin da yanzu fa itace a wannan halin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Shureim yasan Komai na daga rayuwar Sarauta kuma ya gane hauwa ta hanyar fad'in sunanta da Sarauta tayi Haka ya Kamata suka koma mota, dakyar ya lallasheta amma Haka Dai suka tafi jikin ta duk yayi Sanyi ita yanzu rayuwar nan ma tsoro take bata.





Ganin halin da take ciki yasa seda suka biya ta Kuwait taga ummahnta sannan suka wuce JIDDA. Kowa mamakin ganin ta da wannan tsohon cikin yake, Kwana d'aya sukayi a gidan Ummee sannan suka tare gidan su, duk da Ummee taso ya bar Mata itanan don ta kula da'ita amma se cewa yayi ai dacanma shiya kula da'ita bare yanzu, hakanan Ummee ta rabu dasu.





2months later





TSAYE take a kitchen tana juya miyar da ta had'a se ji tayi an rungumota, murmushi tayi tace "Uhummm Uhmm" tallabo cikin ta yayi yace "Haba mana Mrs wannan fa Sam be dace dake ba, haihuwa fa kike jira amma shine Zaki wani fito kiyi girki kuma bayan hakan ma ai wannan d'in Sam ba kalar Naku bane you're the trillioneire ba" tayi yak'e Don ita Kad'ai tasan tsallan bala'in da ake Mata a Mara tace "ai wa mijina Nayi" yayi murmushi yace "Allah yayima mar'atussalaha albarka" tace "ameennnnn" kafin ya kuma yin magana ta wani duk'e tare da fasa k'ara tana Kiran mutuwa zatayi shikenan kwanan ta ya k'are yauce ranar dan Allah atambayar Mata kowa yafiya, hankali tashe ya d'auke ta suka tafi asibiti, a hanya ya Kira Ummee ya sanar Mata, suna k'arasawa aka shiga da'ita Labor room, Shureim be tab'a amsar haihuwa ba amma yau ya shiga labor room domin amsar haihuwar matar sa, besan Sanda hawaye suka fara zibomai ba sakamakon ganin irin wahalar da akesha a gurin haihuwa, almost 2hours tana nak'uda, kafin da temakon Allah aka fara ciro yaronta kyakkyawa, Shureim daya shigo amsar haihuwa kuwa kasa komai yayi ganin wannan ikon Allah tabbas shi likita kuma duk yasan wannan abubuwan to amma be tab'a gani ba Akan idonshi se yau, cikin ikon Allah kuwa ta k'ara aifo yara biyu na mace da namiji, yara uku at the same time wannan Abu yabama likitocin mamakii gashi kuma tana hayyacin ta har yanzu, yarinyar aka mik'a Mata ta amsa tana maida numfashi tare suka amshi yarinyar itada Shureim, kallon sa tayi cikin farin ciki tace "Mr duba kagani Nima nazama uwa na haihu kamar dai kowa kuma zanyi Raino kamar dai kowa Mr, kagani bakaga yarinyar mu ba" Shureim ya rik'e hannun ta ya fashe da kuka yace "Mrs bakiga halin da kika shigaba ne Kinci wuya fa sosai kuma yanzu har kina magana Mrs ni kad'ai Naga abunda ya faru" Sarauta tayi murmushi tace "wannan fa y'ata ce ganin ta kurum ze wanke min duk damuwata da wahala ta ku......" bata k'arasa ba kuma se wani nauyayyen barci ya d'auke ta, hankali tashe Shureim ya jawo Dr najwa, Dr tayi dariya tace "karka damu barcin gajiya ne takeyi" ajiyar zuciya yayi, Dr ta kalli wata nurse tace "sister d'auki wannan ma a shirya ta" daganan ta tura gadon Sarauta sukayi ciki.




Cikin Mintunan da basu wuce 30 ba aka shirya baby's d'in da Maman baby's, wannan Abu yabama kowa mamaki har Umma ma tazo su Shubai'a kowa yazo ankaita resting room domin ta samu hutu, y'an uwa kuwa se hannun hannu ake da jarirai su Maryam ma sun taho, Sanda suka iso kuwa Maryam hada hawaye tayi tsabar murna Wai Sarauta ce ta aihu kuma har yara uku alokaci d'aya Haka Kai Alhamdulillah Allah Abun godiya.





3days later.





An sallame su daga asibiti kuma Babu gidan wanda sukaje gidansu suka wuce kullum fa gida a shak'e da mutane ANZO Barkar triplets, lokaci d'aya soyayyar yarinyar ta tayi zarra data sauran, amma kuma a lokacin data amshi na karshen data Haifa setaji tanason yaron matuk'ar so, har Maryam da Shureim ma sun fahimci hakan Idan tana Kallon yaron ko amsar sa batason ayi.




Zaune take Akan gadon tasa yaron ta gaba tana Kallo,HAR Shureim ya shigo bata sani ba babyn dake ta kuka ya d'auka tare da zama kusa da'ita ya jawota jikinshi, Aiko tayi firgigi ta dawo hayyacinta, hancinta yaja yace "kinason boy d'innan dayawa fa" ta duk'ar da kanta tace "Ahah ba haka bane kawai dai Yana da kyau kuma kaga fa kama kuke" yayi murmushi yace "Mrs kenan wannan yaron ai ko aduhu kinsan ke yabiyo kamar ku kamar an tsaga kara yanzu dai amshi madam d'innan ki shayar da'ita" amsarta tayi tasoma feeding d'inta, tana Kallon ta, Shureim ya shafa Kan yarinyar yace "Daddy's Girl, Mrs wane suna ya Kamata mu samata ne" Sarauta tayi murmushi tana goge hawayen ta tace "SHUWAIBA" yayi murmushi yace "Allah ya raya Shuwaiba kawota ayi Mata hud'uba anyima y'an uwanta dama" ya amshi babyn yayi Mata hud'uba da Shuwaiba.




Ranar suna yara sunga gata kuma sunsha kyaututtuka, babban yaci Sunan MUHAMMAD SHUREIM (ZAIN), SE BABY KUMA SHUWAIBA (AZRA), SE K'ARAMIN MUHAMMAD LADTEEF (AZAR), anyi murnar Sunan yaran sosai.




"Zain, Azra, Azar sune yaran ki ma'am" Shureim ya fad'a Yana dariya, Sarauta ta kalli yaranta cike da farin ciki tace "M.S MUHAMMAD SHUREIM SARAUTA, S. MUHAMMAD SHUREIM SARAUTA AND M.L MUHAMMAD SHUREIM SARAUTA THAT'S THE FAMILY OF M.S² (MARYAM SARAUTA AND MUHAMMAD SHUREIM)" Shureim yayi murmushi ya rungumota. A cikin hidimar sunan kuma Shureim ya sama Mata admission na karatun likita 4years a India, domin cika burin late Abba Muhammad Shureim, Aiko ita kanta Sarauta tayi murna da Hakan watan yaran su uku Maryam ta Haifi yaronta me kyau itama YUSUF (JUNIOR), bayan gama Sunan Maryam ne kuma Sarauta's family suka wuce India domin cigaban karatun Mrs.





*8 YEARS LATER*





Zaune take a falon tana danna laptop, matar da seda na k'ara bud'e ido na matsa kusa da'ita sannan na gano wallahi Lashe money ce Sarauta lashe money, aiki take a laptop d'in sosai, kyakkyawar yarinyar dake gefen ta ta mik'o Mata wayar dake hannun ta cikin lafiyayyen turancin ta tace "Ammerh ana Kiran ki" hannu ta mik'a ta amsa ta d'auka, cikin indianci take magana "karku damu da rashin farkawar shi ze farka very soon" tayi Jim kafin kuma tace "Ahah ita wannan abari sena xo sannan kun gane" bata kuma magana ba ta yanke wayar, wata kyakkyawar yarinya ta sauko da gudu daga Saman benen tana kuka "Ammerh Wayyo Ammerhnmu na bani Ammerhnmu" Sarauta tayi tsaki ta rufe laptop d'in ta Mik'e ta kamo yarinyar ta d'aga hannu zata bugeta kurum taji an rik'e hannun, juyowa tayi tace "dan Allah Mrs ka Bari na faffalle yarinyar nan da Mari komai na shiga uku ita bata da aiki se ihu" Shureim ya jawota ya rungume yace "calm down Mrs kyalemin Oum Suleim d'ina Naji me akai Mata" jawo Oum Suleim yayi yace "Meya faru ne Uhm Oum na" tana Kallon Sarauta gefe² tace "brother Azar ne ya bugeni fa" Sarauta tace "to uwar sharri yaronma da beda lafiya shi zakiwa sharri" Oum Suleim tace "na rantse Allah Allah kingani ko shine ya bugeni" ta fad'a tana dan gwalo harshen ta da k'asa, ana cikin maganar kuwa Sega Azar ya fito, lokacin kuma Zain ya shigo da jakar iPad d'in daddy, daddy ya tambayi Meya had'a su, Azar ya harari Oum Suleim yace "daddy Wai yarinyar nan saboda tsabar bata da hankali ta rasa mezatayi wasa dashi se kud'i ita bata da hankaline" Oum Suleim tace "to ai kud'in dake jikin reader na ne ko ba kud'in gaske bane ba ahee" yace "zan bubbuge miki wannan bakin mummuna kawai, tosu kud'in reader ba zanen kud'i bane nace koba kud'i bane" Zain yace "kaidai Azar wallahi ka bani da son kud'i" Azar yayi murmushi yace "AKAN KUD'I Babu abunda bazan iya ba Ammerhnmu ce kad'ai bazan bayar ba" Shureim ya kalli Sarauta itama ta kalleshi kafin wani yayi magana Azra tace "Ammerh, daddy dan Allah kuzo muci abinci nifa yunwa nikeji" Azar yace "mayya batada magana se abinci, daga Ina kike abinci Ina Zaki abinci me kikayi abinci me zakiyi abinci firarki abinci kinji haushi" Azra ta mik'e tace "Kai nifa ba sa'ar ka bace ka kiyaye ni tom" Azar yace "Ammerhnmu kiyima yarinyar nan magana mana nida ita Waye babba ne" Shureim yace Kai Dallah kuyima mutane shuru ku kullum cikin rigima kuke Allah Azar ka kiyaye ni fa Tohm kowa ya wuce yaje yayi abunda ke gaban shi, " ya kalli Zain yace" ka kaimin file d'in nan d'aki kaji babban mutum seka zo Kaci abinci" ya kama hannun Sarauta sukayi sama, suna tafiya yace "Banga yarona ba" tace "d'azu su Junior suka zo suka tafi dashi gidan su

Please Login or Register in order to submit comment