Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aida Maryam Nasir ce da yanzu an d'aga waya an kirata Wato itada ba'a so), bata kuma yin magana ba har barci ya d'auke ta duk da tana tunanin meyasa cikin kaso 100 na kulawar da yake bata yau ko 20 bata gani ba, ajiyar zuciya kurum tayi ta cigaba da tunanin ta har barci ya d'auketa. Shima Yana ganin tayi barci yayi ajiyar zuciya ya tashi ya tafi.






*Washe Gari*





Abiey na barin gida ya wuce Kuwait domin sanar da Taheer, Aikuwa Taheer ji yayi alokacin da Abiey ze amshi rayuwar sa a matsayin kyauta toda ze iya bashi Yana matuk'ar k'aunar Nur fiye da komai ai Nur ta cancanci ak'auna ceta, hakama mahiafiyar su, bak'aramin murna sukayi ba musamman samun labarin cewa harda Jikarta kuma d'iyar Sarauta d'anta, Sunyi murna sosai tun da Asuba suka tashi suka soma shiri domin tahowa JIDDA.






Gaba d'aya ahalin zaune suke a babban falon gidan harda Sarauta dake kwance jikin kakarta sarauniya Maya, mahaifiyar Sarauta, kowa a gurin Ummee yake saurare, ajiyar zuciya tayi ta soma basu labarin abunda duk ya faru kamar Haka "............






*TO SEMUN HAD'U BAYAN SALLAH* πŸ‘‹πŸ‘‹




*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'iraren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum dako yaushe*





@ *sherntee Ghayu*πŸ₯°πŸ₯°












@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)




.... 3rd July, 2023




*Story & writing*
*By*





@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°






πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





*inama d'auka kin masoyan littafin AKAN KUD'I Barka da sallah, Allah yasa mundace a wannan shekarar Ameen Y hayyu y qayyum*






πŸ…Ώ.....*065 & 066*






"Bayan nabar gidannan nad'au tsawon sati d'aya a hotel duk irin cigiya ta da kukayi Babu abunda ban sani ba amma saboda tsabar son kaina yayi min yawa yasa Nike Jin Akan Dai Dai Nike, da farko k'asar India naso tafiya amma sena samu labarin cewa duk wata k'asar dana tab'a ziyarta seda aka bada cigiyata hakan ne yasa na zab'i k'asar da bani ba duk ahalinmu Babu wanda ya tab'a zuwa kuma nasan Babu wanda hankalin sa zekai Wai inacan, k'asar dazakayi rayuwar y'anci ko baka da shedar haihuwa *NIGERIA*, Aiko cikin d'an lokaci na gama duk abunda zanyi na wuce, koda na sauka a Nigeria a wani gari da ake Kira da kano na sauka, nanma hotel na kama saboda Dama kafin na tafi seda na biya banki na kwashe kaf kud'i na dasuke ciki kafin, tsawon wata biyu nad'au ka a hotel d'in to kuma kawai senaji ya fita a Raina, nan na sallame su kuma na had'a kayana domin barin gurin, a hanya ta taneman inda zani na had'u da wa'inda suka zamo sune farkon darasi na a duniya dana shiga, Wato b'arayi, tare ni sukayi suka amshe komai ko kayan sawana Babu abunda suka rage min harda ma maruka suka k'aramin, seda Nayi Kwana biyu baci ba wanka, a wannan lokacin ne nafara tunanin AGASKIYA iyayenmu maza ba k'aramin aiki suke damu ba, Allah sarki Abba, mahaifi shine ci da sha, sutura da makaranta kuma ba iya nan ze tsaya ba shine tarbiyya kuma kud'in makaranta kuma fa ba mutum d'aya zeyi ma hakan ba ku Duka Koda kunkai 190 agidanku,sannan baze barki Haka ba shine wanda ze nema miki miji na gari wanda ze matuk'ar dacewa dake bayan Haka kuma yayi miki Gatan da duk wani jajirtaccen mahaifi yakewa y'arsa sannan ya had'aki da Abun sanaa domin ki rufama kanki asiri bayan duk wannan kuma zedunga zuwa Yana duba ki ko kuma ya turo adubamai lafiyar ki, ( *da wannan damar Nike son Nayi amfani gurin jinjina ma duk wani jajirtaccen uba, babana AGASKIYA Ina sonka Ina matuk'ar godiya a gareka, Kaine fitilar daka haskamin rayuwata Haka Kaine silar samun ilimina dahar nake tutiya kuma yazamana na fara rubutu Nagode sosai babana Banida abunda zan saka maka dashi face addua, Allah ya sakama da duk iyayenmu gidan aljanna*), Allah sarki abbana wane Hali ya shiga bayan tafiya na, a wannan lokacin naci wuya sosai na Kwana a bola, na Kwana a kango, yashi, gefen kwata da duk wani rusassen gini, Naji wuya sosai kafin Allah ya had'ani da wata Wai balaraba Mai abinci, Aikuwa ta d'auke ni aiki musamman Dana sheda Mata na iya abinci na k'asashe dabanΒ² Aiko tuni muka kulle, gashi ta k'ara samun customers domin wani koba abinci ze siyaba kawai zezo domin yaganni daganan kuma seya siya abinci, sosai balaraba ke nunamin soyayya ta dalilin Haka, cikin wannan yanayin Nayi tsawon shekara biyu Anan, zuwa wannan lokacin kuwa Nigeria ta zama Tamu, a bakin wata abokiyar aikina nikejin cewa Wai aiki a Niger yafi kawo kud'i Akan aiki Anan domin itama y'ar uwarta tanacan tana abinci kuma sosai tayi arziki, nikuma dayake awannan lokacin komai danike AKAN KUD'I nikeyin shi domin Ina buk'atar komawa k'asata, Aiko nan nasata ta had'ani da y'ar uwarta ta Koda balaraba ta samu wannan labarin Sam bataji dad'i ba amma tunda burina ne hakan kuma tasan komai akaina da silar barina k'asata, yasa ta amince amma ta nemi alfarmar na biya gurin k'awarta dake a KATSINA mu gaisa, kuma dan Allah karda na manta da'ita arayuwata, Aiko ranar rabuwa Ansha kuka domin Sabo akema kuka, har Tasha suka rakani, KATSINA na fara sauka gurin k'awar Aunty balaraba Wato Lami, itama tanemi alfarmar Nayi Mata Kwana biyu Babu yanda na iya shysa kawai na tsaya, kwatsam wata rana ta aikeni kasuwa, Anan ne kuma komai ya sauya, Anan ne nahad'u da wanda ko amafarki banyi tunanin ganinsa a 9ja ba, brother *M.S Sarauta* Yana siyar da kayan da kayan masarufi, shida wani dattijo kasheni ne kawai mamaki beyi ba koda na kwatan ta muku halinda Nashiga awannan lokacin ba lallai ku gane ba, ban ankare ba senaji Yana cewa meze bani, alokacin kuma Banida bakin yin magana hakan ne yasa na juya na koma gida, aranar na samu lami Nike sanar Mata dana d'aga tafiya ta Senan da wata biyu Aiko taji dad'i sosai saboda itama ba k'aramin k'aruwa take dani ba kuma na nemi alfarmar Anan zan zauna, Aiko tayi murna har tana zolaya na Wai kodai kodai, Nidai Babu abunda nace da'ita, nan kuma na k'ulle da Badiyya y'ar Aiken lami, wacce in Aike yakai d'ari ita zataje kasuwa tayo, Aiko tunda muka k'ulle tare muke zuwa kasuwa, nanfa na soma shishshige ma Shureim Aiko cikin temakon Allah shima ya saba dani, ana Haka kuma soyayya tashiga tsakanin mu, Nan kuma maganar Niger tabi ruwa, nikuma Nayi amfani da wannan damar nasoma bashi labarin shi Amatsayin labarin littafi ne Nike bashi, wani lokacin sedai yace Nayi shuru kanshi kamar ze tsage, kwatsam wata rana yazomin da labarin mutumin dasuke tare Wato Malam Muntari, Malam muntari mutum ne me sauk'in Kai da sanin ya Kamata ga kamala da dattaku yaran sa 8 uku sun rasu saura 5, 3mata 2maza, gaba d'aya mazan Kowannen su da kalar Aikin da yake yi matan kuma 2 Sunyi aure se k'aramar dake jiran Shureim acewar ta, koda na tambaye sa be bani labarin sa tun farko ba tunda ya gayamin shi ba d'an k'asar bane kurum murmushi yayi yace nasha wahala sosai kawai abar maganar.





Ana Haka kuma maganar aure ta shiga tsakani, inda brother Shureim ya soma ginin filinsa dake nan cikin garin KATSINA, Sam ko kad'an Malam muntari be nuna masa Jin haushi ko kuma hassada ba hasalima shine jigon hidimar, inda kuma matar sa da d'iyar ta suka tada hankalin su Akan Abun Wai Dama ai tsintattar mage bata mage, in tak'aice muku Akan auren nan seda aurenta ya mutu saboda tace Wai ni shegiya ce haihuwar Titi, Haka dai akayi Hidima tsakanin ango da amarya Babu wanda yake da dangi, aranar kuwa Nayi kukan ahalina sosai madadin ace sune azagaye dani amma Sam Wai se y'an abinci ne zasuyi min nasiha dama Haka rayuwar take ai,





Rayuwa muke cike da farin ciki da k'aunar juna zuwa wannan lokacin kuma brother Shureim ya Riga ya gano gaskiya, munyi duk k'ok'arin da zamuyi domin dawowa gida amma kuma se muka gano Abun ba b'acewar tunani bane kamar yanda mukayi tunani ba Aikin asiri ne kawai, Haka muka hak'ura Akan cewa Haka Allah ya tsara muka cigaba da neman Magani da addua, sannan muka cigaba da rayuwar mu gwanin burgewa.





Se bayan auren mu da d'an lokaci sannan Malam muntari ya dawo da matar sa, zuwa lokacin kuma sun ladaftu, nan fa yarinyar ta ta fiddo miji inda mukaje muka sha biki, acikin d'an lokacin ne ma kuma Badiyya tayi aure itama na Taya ta murna sosai.






Bayan tsawon lokacin da mukayi Allah ya azurta mu da yarinya, Gatanan Maryam, mahaifin ta shine wanda ya fara kiranta da Sarauta a rayuwa, soyayya irin ta gidan duniya Babu kalar wacce brother Shureim be nuna ma yarinyar sa ba, Sarauta nada wata biyu a duniya Allah yayima balaraba rasuwa, Aiko munsha kuka kamar babarmu ce tarasu, Kwana na uku na dawo gida saboda Sam brother Shureim bayason tafiyar Kwana dan ni alokacin ma sati naso Nayi amma hakan nan nadawo, munyi rayuwa zomu zauna zomu sab'a, kullum hirarsa itace Idan an koma gida Aikin kenan, kullum maganar sa yasan Idan d'an uwa Zabvier yayi aure yaronsa na farko Sunan sa za'a samai, tun Sarauta na yarinya yake da buri akanta na ta zama cikakkar likita yayi alkawarin ze salwantar da komai Akan ta zama likita.





Bayan shekaru biyar




Allah yayima Malam muntari dakuma lami me abinci rasuwa munyi rashi awannan lokacin sosai, inda kuma yaransa suka amshe komai nashi dake hannun Shureim haka muka koma rayuwa Babu dad'i, Abun farin cikin kuma Anan shine zuwa wannan lokacin ya samu lafiya sedai kuma bamuda hanyar da zamu dawo, nan fa yace ze siyar da gidansa da duk abunda ya mallaka yasani a jirgi na dawo gida Idan naxo yasan shima tahowarsa bame wahala bace, Aiko nak'i amincewa domin Ina tsoron na k'ara rasa shi arayuwata, awannan lokacin kuwa yasaka yarinyar sa a makaranta Me tsada a Nigeria wacce ko a mafarki akace min d'iyar Mr billionaire zatayi ta sena Musa, amma gashi ga halin da shi Kansa Mr billionaire ya kasance, saura Kwana biyu azo asayi gidan sa kawai yahau ciwon ciki" tad'anyi jimm tare da k'arama kukanta sauti ta cigaba da cewa "ashe ajali ne, cikin mintunan da basu wuce 30 ba Allah ya d'auki rayuwar sa wanda kuma adaren ranar ne muka gama tsarama kanmu abunda zamuyi a JIDDA yanata murna zedawo gida sannan yarinyar sa zata tashi a matsayin ta na gimbiyar Kuwait kuma billionaire amma ashe Muna namu Allah na nasa, munyi kuka dagani har d'iyar sa fad'in halin da muka shiga awannan lokacin se wanda ya gani dama da ransa abinci Yana gagararmu balle kuma ya mutu, nanfa rayuwa ta k'ara tsananta komai ya sauya, semu Kwan mu wuni bamu ci ba, ganin har Sarauta an koro amakarnta yasa na siyar da kayan d'aki na na biya Mata makaranta ta koma sannan na siyo kayan abinci domin sanaa Aiko na fara yin wainar safe kullum, ita sarautar ai tasan komai tunda zuwa lokacin ta fara wayo, Akan makarantar ta kuwa semu Kwana ba muci ba duk wani k'ok'arina da nikeyi akanta ne amma ashe tace Banza ki gama haukan ki ni AKAN KUD'I nikeyin nawa, duk kalar wahalar da nasha tasani ko aiki ban cika Sata ba ita ai tasani kawai domin ta maida hankali tayi karatu, na hanata abota da kowace k'awa saboda karsu lalata min ita da son kud'i, Maryam Nasir itace kawai yarinyar dana yarda suyi abota saboda yarinyar mutuniyar arziki ce sosai tun basu da wayo sosai suke abota har kawo wannan lokacin.





Duk wani motsin da Sarauta keyi Akan idona takeyin shi, Haba Sarauta nifa uwace yazaayi ace bansan halin dakike ciki ba a rayuwar ki, duk motsin dakike na sani kawai dai basarwa Nike, tun kafin Kije zano jarabawa, *Little M.S Sarauta* yaje gida, Naji mamakin zuwansa sosai inda ya gayamin cewa yayi bincike me yawa kafin ya gano inda Nike tin alokacin ya nemi dana koma gida amma tsoron abunda ze faru yasa nak'i amincewa, nan yace to Nayi hak'uri nabar Sarauta taje Babu yanda na iya na amince amma da shara d'in ita ba y'ar ahalin bace Aiko ya amince, inda ya samu FAWAZ yaron kirki yasanar Mai daya gayama y'an uwansa sunsamu wacce zatayi musu aiki a Nigeria Wato P.A, Aiko suka amince, inda Shureim ya Bama Fawax gida, kud'i, dakuma motoci, yace za'a Bama wacce zatayi Aikin domin ta samu karsashi sukuma suka amince, Haba Sarauta ke bakiyi tunanin wace irin uwace ni ba, da har aka baki gida da mota hade da kud'i kuma naki bibiyar Abun, kuma ace za'a tafi dake outside shima na zuba ido Nayi Kallo, bakida hankali ne, Humm Maryam Nasir itace wacce tayi hak'uri dake bayan ni, kin zab'i kud'i akanta amma still tana tare dake, kin siyar Mata da soyayya shima still tana tare dake kin tafi kin barta shima tana tare dake sannan yanzu kuma kin ci Mata mutunci kuma duk kike tunanin tacigaba da zama dake mtsww, to Bari kiji ko alokacin da kukaje 9ja dakikaga tana ta yimiki b'oyeΒ² Bakomai take b'oye miki ba face soyayyar ta da Hisham domin tanajin tsoron shima ki kuma rabata dashi Kewai dan Allah bakiji kunya ba, nace bakiji kunyar abunda kika aikata ba, Humm Babu komai nasan laifin Danayi ma ahalina ne Nima Allah ya jarabceni dake shysa ma ya d'auke mahaifin ki a doron k'asa domin karyaga wannan bak'in cikin madadin kizama likita da ake alfahari da'ita sekika zama y'ar iska mayyar kud'i kinbar mahaifiyar ki AKAN KUD'I, kinyi aure AKAN KUD'I, kinzabi KUD'I Akan komai kin bani haushi Sarauta Sam bakida amfani ko kad'an agurina matsa min agaba" ta k'arashe tana fashewa da kuka itama Sarauta kuka kawai take se yanzu take tunanin daya Kamata ace acan baya tayi shi meyasa duk ta aikata hakan me yasa tayi hakan kowa dake gurin kuka kurum yake.






*After 8hrs*





"Wai Shubai'a kukan nan na miye kikeyi haka" Shureim ya tambaya cikin K'OSAWA, ta goge hawayen ta tace "yaya ai dole Nayi kukan wannan lbrn to Wai Taya ma kasamu masaniyar tana 9ja" ya zauna gefen ta yace "kinsan Hisham Yana zuwa 9ja, to a wani zuwa dayayi ne se y'ar gidan kwamnan KATSINA ta gayyace shi birthday party d'inta da farko k'in amincewa yayi amma daga bisani kuma seya amince, bayan sun gama taron ne yafita domin zagawa Anan kuma ya had'u da Maryam da Ammerh xasu tsallake Titi, tundaga wannan ranar yaji Yana matuk'ar k'aunar Maryam ni kuma ya kirani a waya yace min yaga wata kamar goggo ta danike gwada Mai photon ta amma dandai wannan yarinya ce ba Babba ba, a wannan lokacin kuma bana wasa da duk wani Abu daya shafi ummah shysa na shirya naje can d'in acan kuma komai ya warware" Shuwaiba tace "ikon Allah" Shubai'a ma tace "Aikuwa Dai" Shuwaiba tace "Allah sarki rayuwa gashi kamar komai be faru ba, to tunda dai angano gaskiya koma ai yakamata ace Muje mubama cikin mu ko" Shubai'a ta buge ta a cinya, Shureim kuma yayi murmushi ya fice.





Wayarsa dake ringing ya fiddo, Ammerh shine sunan daya bayyana Akan screen d'in, d'an k'aramin tsaki yayi kafin ya d'aga, dagajin muryar ta kasan kuka take, tace "yaya dama inason Nayi magana dakai ne" yace "inaji" tace "please Idan da afili mukayi maganr setafi mahimmanci" yace "banada lokacin wannan yanzun" tad'anyi shuru tana tunanin Anya lafiyar sa itada kullum Abun riritawa ce agurin sa yau kuma shine yake Gayamata magna Haka, tadai kuma dannewa tace "shikenan to seka samu lokacin" yayi dogon tsaki ya yanke wayar, Yana yanke wayar Sarauta ta kuma fashewa da kuka, soyayyar Shureim zata kasheta fa, ita yanzu ya zatayi *RANA ZAFI INUWA K'UNA*






*NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN XUWA GA DUK WANI JARUMI KUMA JAJIRTACCEN UBA DAYA TSAYA MA YARANSA, JINJINA GA IYAYENMU DAKUMA FATAN ALKHAIRI* πŸ’ͺ🏾πŸ’ͺ🏾πŸ’ͺ🏾πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°







*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe*






@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°







@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)



..... 4th July, 2023




*Story & writing*
*By*


@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°





πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š




πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ.... *067 & 068*






Ummah ce tafe kanta na Kallon k'asa harta k'araso Kan dining d'in, a hankali ta d'aga kanta ta kalleshi tace "sabahul khair ya akhie Zabvier" d'agowa yayi ya kalleta kafin ya kauda Kai ya mik'e yana d'aukar tissue sannan yabar gurin, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo Akan fuskarta, hak'ik'a ba k'aramin kuskure tayi ba na barin gida towai Akan ma wane dalili tabar gidan, Jin Ummee ta dafa kafad'ar tane yasa tayi ajiyar zuciya tabar wajen.





*BAYAN SATI D'AYA*





"Yanzu temako d'aya zakiyi mana kawai ki kashe ta" Hajja jumaima ta fad'a tana Kallon Hajja Mubeena, tsaki mama unana tayi tace "harkun manta tujarar dakukayi min ne, toni ban manta ba kutashi ku bani guri kawai kafin Raina ya b'aci" Hajja Mubeena tace "amma mama" tsawar data daka musu ne yasa duk suka mik'e "toku banda Allah yasa anyi zaman Amana da kuna tunanin akwai wacce zata fita gurinnan lafiya ne, Dallah marasa hankali kawai ku fita ku bani guri" Aiko dasauri suka fice.






Su had'u ne zaune a gurin shak'atawar, hajja jumaima, hajja Mubeena, Khaleesat se wani k'aton mutum, wani irin karkata baki yayi yace "to yanzu yaushe kuke son akashe ta" Kallon juna sukayi kafin hajja Mubeena tace "yau saura sati d'aya afara hidimar bikin Shubai'a, yaushe kuke ganin za'a aikata" hajja jumaima tace "mu Bari ranar dinner ana gobe biki kenan" Khaleesat tace "hakan ma seyayi daidai, yanda kowa ze d'ora zarginsa Akan tsinannar" k'aton mutumin ya juya ya kalli k'attin dake bayansa guda biyu yace "Muna da deal nan da 12 days" suka d'aga Mai Kai, ya mik'e tare da d'aukar bandir d'in kud'in dake ajiye agabansa ya kalli na bayansa yace "kowa ya watse" daganan kowa yabi wata hanyar daban.






Ya dad'e Yana kallonta acikin motar kafin ya bud'e ya fito, seda yazo dab dasu sannan ta gansa, murmushi tayi tare da cewa "Laaa brother Shureim dama kananan" murmushi yayi Mata sannan ya mik'a ma na gefen ta hannu suka gaisa, Juwaira tace "yaya wannan shine Mahboob my husband to be In sha Allah" Shureim yayi murmushi yace "Allah yasa albarka" Mahboob ya sunkuyar dakai, Shureim yace "to Adai kulamin da kanwata sosai domin ji Nike da'ita" Mahboob yace "in sha Allah babban yaya" daga nan Shureim ya wuce yana Mata fatan alkhairi.





Yana shiga ya wuce d'akin ummah, tana zaune itada Shubai'a da Shuwaiba sunata fira saboda d'an lokacin da sukayi atare ba k'aramar shakuwa sukayi ba, Yana shiga Shuwaiba ta Harare shi tace" Waikai Mr billionaire tun jiya fa banganka ba" yayi Mata murmushi yace "yanxu ai kinganni ko, kud'an bamu guri zamuyi magana" Kai suka d'aga Mai suka fita Shuwaiba na cewa "Muje mu Kira first Lady Muje muci abinci" daga Haka suka fice, zama yayi gefen ummah yace "Wai yaushe Zaki fito da baiwar Allah nan ne" tayi murmushi ta kama hannun sa tace "karka damu, zuwa anjima ko gobe da safe, sannan kuma kaga Shubai'a da Shuwaiba lafiya Lau suke shiga gurin d'azu ma munje" Shureim yace "what of Ammerh" Ummah ta d'aure fuska tace "seta gane kurenta" Shureim yace "please mah diamond kiyi hak'uri mana ki barta taji da Abu d'aya" Ummah tace "amma...." ya katseta da cewa "amma me, mah diamond nifa zakiyi ma wannan alfarmar please dan Allah" tayi ajiyar zuciya domin ita kanta tana kewar gimbiyar ta ta kuma farin cikinta, tace "shikenan to dazarar yaya ya yafemin Nima zan yafe Mata" Shureim yayi murmushi yace "shikenan to, ni bara naje gimbiyar nasan had'uwa dani" Ummah ta doke shi a kafad'a tace "Mara kunya" daga Haka ya fice.





Zaune suke a Saman gadon tayi filo da cinyar sa, fira suke sosai Yana koya Mata larabci Yana Mata dariya domin shi yariga da ya iya hausa, knocking sukaji Aiko dasauri Maryam ta yunk'ura zata tashi ya maidata Yana Mata hararar wasa, tace "what if mother in-law ce" ya d'aga Mata gira yace "tazo taga love" ya juya yace "come in" Maryam ta k'ara yunk'urawa zata tashi ya danne ta, ahankli ta bud'e k'ofar ta shigo, ganin sunata kokowa yasa ta duk'ar dakai tana tunanin inama ace itada Mr M.S ne haka, gyaran muryar datayi ne yasa ya saketa ta mik'e tana galla mai harara, kallon Sarauta yayi kafin ya mik'e Yana cewa "Ahhh Mrs billionaire ashe Kece, kinxo ganin amarya kenan to sannunki da zuwa" ta d'ago tayi murmushi tace "ai gani naxo tunda Amaryarmu tak'i tazo mu gaisa" yace "tuba muke, wannan laifin namu ne, amaryar ce ko fita batason yi" daga Haka ya fice, dakyar Sarauta ta iya d'agowa suka had'a ido da Maryam, Maryam ta kauda Kai tana cewa "you're highly welcome Mrs billionaire ki shigo mana yazaayi ki tsaya daga waje kuma" Sarauta tayi ajiyar zuciya ta k'araso tare da zama inda Maryam ta nuna Mata, ruwa da juice ta d'auko Mata ta zuba Mata juice d'in a glass cup ta mik'a Mata, amsa Sarauta tayi, ta ajiye tasoma cewa "Maryam bana ma da idon dazan kalleki awannan lokacin balle kuma na baki hak'uri amma Zaki iya yimin duk hukuncin daya Dace da marar tunani kamar ni" Maryam tayi murmushi tace "amma ni kuma Mrs billionaire Meya had'a ni dake kuma, ai inaga kamar Babu komai ko, Duka ma yaushe nazo gidan" Sarauta tace "Maryam dan Allah kidena duk wannan ki dawo Maryam d'inki please" Maryam ta saki ajiyar zuciya ta d'aure fuska wanda harni dakaina seda ta bani tsoro ta kalli Sarauta tace "tashi ki fita ki bani guri" Sarauta tace "please Mrs Hisham ki saurare ni, inason muyi magana" Maryam ta furzar da iska tace "waike bakida tunani ne nace meyasa kike da saurin mantuwa to Bari na k'ara tuna miki Idan kin manta, ko agaban ka'aba muka had'u to kiyi ta kanki, Maryam Sarauta bani bake dan Haka ki tashi kibar min d'aki" Sarauta ta goge hawayen ta domin cikin y'an kwanakin nan Sam kuka baya yi Mata wahala tace "Maryam komai fa Nayi shine Akan...." Maryam tace "AKAN KUD'I ko, Akan kud'i kikayi komai ko, toni nazabi mutunci na AKAN KUD'I Don haka ki tafi Kibarni Babu ni Babu ke kuma Bana buk'atar wata magana ta k'ara had'a mu, please leave..." ta k'arashe tana kauda kanta domin kar Sarauta taga raunin ta, Sarauta ta yunk'ura zatayi magana sukaji an bud'e k'ofa an shigo, dasauri Sarauta ta goge hawayen ta, ta juya suka kalli k'ofar, Khairat da Khaleesat ce suka shigo, kallon Sarauta Khaleesat tayi tace "ahahh first Lady dama kina nan" Sarauta ta kalleta, tun lokacin

Please Login or Register in order to submit comment