Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'ana wannan tunanin dakayi shine daiΒ², gaskiya Ina alfahari dakai, Yusuf ya tafi ya barmin d'an uwa Anan," murmushi kurum Khameel yayi suka cigaba da firar su gwanin burgewa.


**KATSINA**

Lokacin zana exam d'in su Sarauta yayi, kasantuwar makarantar su babbar makaranta ce yasa aka fitar da scholarship Akan duk d'alibar datafi k'ok'ari za'a turata abroad karatu hakan yasa kowane d'alibi ya dage, cikin d'aliban da suka dage kuwa harda Sarauta wanda take ganin Idan tabar Nigeria shine burinta na zama billionaire ze cika shysa ta dage sosai.
Zuwa wannan lokacin kuwa an saka ranar auren Maryam da masoyinta Shamsudden, bayan exams dinsu da wata uku.

Tafe take tana k'ara biya calculation d'in datayi a gida wata mota tayi parking a gaban ta, wata budurwa ce ta fito daga motar tana kallonta, itama Sarauta kallonta kurum take domin ta gane ta y'ar makarantar su ce Hauwa Mansour me gidaje kenan ko a school basa magana balle kuma Akan hanya, hauwa Mansour tace "my dad need to see you" Sarauta tace "because of?" hauwa tace "Idan munje kinji" Sarauta tayi tsaki ta juya da niyyar tafiya, dasauri hauwa ta rik'emata Hijab tace "please Maryam Sarauta" kallonta Sarauta tayi kafin ta juya ta shiga motar tana cewa " muyi sauri kinsan karatu Nike yanzu ma Maman su Maryam Nasir ce ke kirana" hauwa tace "sorry Idan kun Gama sena kaiki gidan" tab'e baki kurum Sarauta tayi ta juya. Driving hauwa keyi Babu me magana a motar har suka Kai gidan, babban gidane wanda daka ganshi zakasan ba laifi a irin kud'in Nigeria yana da kud'i, har ciki hauwa tayi Mata iso, zaune suka iske Alh Mansour me gidaje, d'agowa yayi ya kallesu fuska Babu yabo Babu fallasa yace "wannan itace Sarauta?" Kai hauwa ta d'aga mishi tana yin hanyar kitchen, guri ya nuna Mata ta zauna yace "Barka Dai my daughter" tana jinta a takure tace "Barka Alh" murmushi yayi yace "my daughter ya karatu" tayi murmushi tace "Alhmdll, but Dan Allah Alh ka kirani da Sarauta na kurum banason daughter nan" ya d'aga Kai, kafin yayi magana hauwa ta dawo falon tare da hajiyar ta, seda suka gaisa da hajiya sannan Alh Mansour yace "Sarauta a iya binciken danayi na gano cewa aduk fad'in highlights college babu d'alibar datakaiki k'ok'ari dan haka Nike son ki zana ma hauwa jarabawa taci domin taje abroad ke kuma zan baki kud'i kimanin dubu d'ari biyu cash ba transfer ba" hajiyar hauwa taci gaba da cewa "y'annan ki temaka haka shine burin mu please ni zan ma k'aramiki da 50k please" kallonsu kurum Sarauta keyi kafin ta Mike tace "Nima Ina buk'atar inje abroad d'in hakan shysa na dage da karatu gaskiya Alh bazan iya ba tsawon wata biyu kenan Ina Hana kaina zaman lafiya da nutsuwa amma kuke son Nayi wannan gangancin kuyi hakuri gaskiya" hauwa tace "please mana Maryam Sarauta kinga zamu baki 300k indai kin amince please" kallonsu kurum tayi kafin ta juya ta fice, da sauri Alh yace "kiyi tunani akai y'ata Ina jiranki har zuwa anjima" daga Haka ta fice abunta.


Zaune suke a gaban Maman Maryam nasiha, fad'a, dakuma tunatarwa take musu Akan exams d'insu da rayuwar duniya, kallon Sarauta tayi tace "Sarauta kinada k'ok'ari sosai don Haka ki dage kinji karki biyema wannan mashiririciyar kinji ko" Sarauta tayi murmushi tace "Mamanmu kenan to ai ita jarabawa ciyarwa ce ta Allah sekiga na fad'i itad'in taci" Mama tace "gidanku sakarai kawai kisama ranki ke zaki ci exam din kinji, ke kema zakiji Insha Allah" da Ameen suka amsa duk suna dariya, mik'ewa Mama tayi tace "Ehm wannan shiriritar taku bata k'arewa Bari in tashi inje in kad'a miyar nan kafin su Naja (k'annan Maryam) su dawo" daga haka ta fice ta barsu, Maryam ta kalli Sarauta tace "Anya Sarauta Babu abunda kike shiryawa kuwa?" Sarauta ta kalleta tace " kamar ya ban ganeba fa" Maryam tayi dariya tace "k'awata kenan kefa k'awata ce nasanki kamar yunwar cikina, kuma nasan Zaki iya komai AKAN KUDI" Sarauta tayi murmushi tace "k'awata baki da kyau fa" duk dariya sukayi suka cigaba da fira.

At 7:30pm

"Alhaji Mansour na amince amma zaka bani 150k yanzu Idan na gama Aikin seka cikamin" cike da farin ciki Alh Mansour yace "Kai amma Nagode Sarauta Allah ya biyaki ya cika miki burinki" da gudu hauwa ta rungumeta tace "thanks you so much dear Sarauta" Sarauta na cireta a jikinta tace "you're welcome" hajiya ma tayi Mata godiya, nan take suka bata 150k sannan hauwa ta kaita har k'ofar gida.

"assalamu alaikum " ta shiga gidan da sallama a bakinta, " wa'alaikumus Salam " Ummah ta amsa tana fitowa daga kitchen, kallon tuhuma tayima Sarauta kafin tace" Ina kika tsaya? " Sarauta na cire hijabin jikinta tace" ana~asfun ya Ummah, tazahab ilaaa darul hauwa (kiyi hakuri Ummah naje gidansu hauwa ne) " Ummah tace "Wacece hauwa" Sarauta ta k'araso ta d'ora hannun ta Akan kafadar Ummah tace "Humm Ummahna k'amshi, Miyene haka kika dafa min" ta shashantar da waccan maganar, Ummah tace "salad ne da wainar fulawa ai Zaki ci ko" Kai ta d'aga tace "Ina k'aunar ki Ummah na takaina, Wai Ummah Ina kika iya yare dakuma abincin larabawa?" Ummah tayi murmushi tad'anyi Jim kafin ta kalli Sarauta tace "muje ki zauna kici abinci ki bani labarin inda kikaje kuma me kikaci" dariya Sarauta tayi tace "Kai ummah sekace dai yarinya" Ummah ta dungureta tace "ked'in jaririyata ce kuma yarinya ta" Haka suka ci firar su cike da raha Abun ba'a magana.
A k'asan kayanta ta ajiye kud'in da alhaji Mansour ya bata dan bata tanadi abunda zata sanar da ummahnta ba.

**BAYAN EXAMS**

Anyi exams lafiya angama inda Sarauta bata zana exam ko d'aya da sunanta ba dasunaan hauwa Mansour ta zana, bayan fitowar exams kowa yayi mamaki ganin hauwa Mansour itace taci exams ba Sarauta ba, hauwa da ko school bata cika zuwa ba Taya akai taci wannan scholarship d'in, kowa Dai yabarma cikin shi sanin daga Sarauta har hauwa Babu me mutunci Idan aka tab'a shi shysa kowa yayi shuru Abun shi.

Yanzu ma tafe suke ita da Maryam daga makaranta suka dawo, tun da suka gano result d'innan Kan Maryam ya kulle Tama rasa mezatayi tunani akai, a bakin titi suka tsaya domin tsaida napep su tafi gida, Maryam ta juyo ta kalli Sarauta da ko ajikinta tace "Sarauta ki fad'a min me kika aikata ne haka, tabbas nasan ke kika ci scholarship d'innan amma ya akai aka bama hauwa Sarai kinsan makarantarmu basa corruption balle ince, tabbas kinsan komai gayamin ya akai hakan ta faru" Sarauta ta kalleta tace "Ohhni Maryamu, Wai Dan Allah Maryam ke wace irice kidunga d'orama kanki damuwa kamar dole, kinga ki kwantar da hankalin ki Nida kaina na siyar da scholarship d'in yanzu ma Zaki rakani na amso cikon kud'in kuma ke zan bama ajiyar su kafin nasan yanda zanyi da Ummah " shek'ek'e Maryam ta tsaya tana kallon Sarauta kafin a d'an harzuk'e tace" Wai Dan Allah Sarauta duk miye hakanne eyeh, waike bakida hankali ne, wannan fa shine burin rayayyiyar mahaifiyarki dakuma mataccen mahaifin ki, yanzu kin kyauta ma kanki kenan eyeh, Wai tsaya duk ma saboda ne kikayi hakan.. " ko ajikinta tace "KUDI" Maryam tace "Zaki mutu da kud'i ne?" Sarauta tace "Zaki mutu da ilimin boko ne?" ajiyar zuciya Maryam tayi tace "yanzu shikenan kin siyar da ilimin ki na shekara da shekaru" Sarauta tace "ah ah Nadai siyar da scholarship d'ina Amma ilimi na yana nan" ta k'arashe tana nuna Mata kanta, Maryam tace "baki kyauta ba yanzu me Zaki sanar da Ummah ma Dai" Sarauta tace "shysa nace ki ajemin kud'innan a gurinki kafin na yanke shawara" Maryam tace "Nidai bazan Dena gayamiki gaskiya ba Sarauta mutunci shine d'an Adam, baiwa, ilimi da sanin ya kamata, wallahi kud'i halaka ne musamman agurin mutane irin ki" Sarauta tace "Maryam Kenan Nima bazan Dena gayamiki kud'i baiwa ce da Allah ke yiwa bayinshi Dan Haka ki kyaleni dan Allah ki wuce muje na amshi cikon kud'i na" Maryam tace "hmm Akan me zan rakaki?" Sarauta tace "ni zanje ne AKAN KUDI ke kuma zakije ne akaina" Maryam tayi murmushi tace "Allah ya kyauta Sarauta na lura AKAN KUDI..." Sarauta tayi caraf tace "Babu abunda ba zanyi ba raina ne kurum bazan bayar ba saboda miye amfanin bad'i ba rai" duk dariya sukayi, daga nan suka samu napep suka wuce, saurayin dake gefensu tsaye tun fara firar su yake jinsu har suka gama, murmushi yayi ya d'auko wayar shi ya danna Kira, bugu biyu aka d'aga, Yana murmushi yace "ranka ya dad'e ansamu kalar yarinyar da kake buk'ata a Nigeria yanzu ya za'a yi" ta cikin wayar akace "ka bibiyi rayuwarta na tsawon sati d'aya Nima Ina zuwa k'asar taku" saurayin yace an gama boss " daga Haka sukayi sallama........

KAR KU MANTA AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARINE DANA RUBUTA DOMIN NISHAD'ANTARWA, FAD'AKARWA DAKUMA TUNATARWA, NICE TAKU ME NISHAD'ANTAR DAKU A KULLUM DA KO YAUSHE.


SHERNTEE GHAYU

@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI*πŸ’΅ πŸ’΄

(A poor lady story)

........ 26th April, 2023

*Story & writing*
*By*
@ *Sherntee Ghayu*


πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘

*Ina @⁨~πŸ’žMrs ABπŸ’žβ© wannan page d'in nakine ta wurina*

πŸ…Ώ....... 009 & 010



*JIDDA*

Zaune yake a main parlorn hankalin shi kwance dakaga fuskar shi Kasan yana cikin farin ciki, a hankali yake danna wayar shi yana sipping pineapple juice d'in dake hannunshi, da d'an sauri ta shigo parlorn tana sanye da doguwar Riga pink colour har gurin k'orin k'afarta se bakin wando, kanta sanye da dark pink d'in bandaner akanta ta kama gashinta tayi baby park gwanin kyau, d'an bakinta d'auke da pink lipstick, fuskar nan kamar ko yaushe d'auke da fara'a, sallama tayi ta shigo parlorn, kallonshi ya maida kanta yana fad'in "wowww see my pretty angel" d'an daure fuska tayi tayi mishi Alamar Hii da hannu, hannu ya d'aga Mata Yana mik'ewa yace "you look so beautiful" d'an murmushi tayi ta juya zata tafi ya rik'o hannunta yana jawota jikinshi yace "come on, zo mana taho Inji Ina kikaje ne kinsan Dai keba magana kike ba ko" tana tureshi tana mishi Alamar, ya saketa bata so miye haka ya saketa, kuma jawota jikinshi yayi, nan tasoma kiciniyar kwacewa gashi ita ba bakin magana ba balle, hawaye ta fara tana kuka tana tureshi amma Sam kamar bada shi take ba, atsawace yaji muryar Prince da idonshi ya kad'a yayi jajir saboda duniya Babu abunda ya tsana sama da ganin hawayen k'anwarshi kuma Babu abunda ke faranta mishi sama da farin cikinta yau gashi duk iya k'ok'arin shi akanta wannan la'anannan yasata zubar hawaye, a tsawace yace β€œKhameel!!!” dasauri Khameel ya saketa ya juya yana kallon muryar dako amafarki yajita yasan me ita, dagudu taje ta rungume Shureim tana fashewa da kuka, wanda hakan ne ya k'ara tab'a zuciyar Shureim, a zabure Shureim yayi kanshi da sauri Shubai'a ta rik'eshi tana girgiza mai kai, amma ina seda ya k'arasa wani irin gigitaccen Mari ya zabga ma Khameel wanda seda hakan yayi silar d'aukewar ji da ganinsa nad'an lokaci kafin ya dawo cikin hankalin shi, hannu Prince ya k'ara d'agawa daniyyar sauke mishi wani marin dasauri Shubai'a ta rik'e hannun tana share hawayen ta ta nuna mishi tadena ita tadena yin kukan ya kyaleshi, ai dagudu Khameel yafita daga part d'in yayi hanyar na sarki fuskar shi d'auke da zanan yatsun Yarima. Shima Yarima a fusace ya wuce b'angarenshi, Shubai'a ma d'akinta ta wuce tasa kuka kamar ranta ze fita bata son taga ran yayanta ya b'aci ko kad'an.

Bayan wasu mintuna

Falon cike yake da mutanen gidan, duk tsoffin suna Saman kujera yayinda sarki da sauran mutanen gidan ke k'asa zaune domin sarki ladteef da matarshi akwai biyayya matsayi, kud'i da mukami betab'a sa sun wulak'anta waniba, Shubai'a na gefen Ummeenta zaune duk ta takure, yayinda Khameel ke gefen kakarshi jumaima, se surfa bala'i take, a fad'ace take cewa "Wai wannan tsinannan me ya maidamu ne kaga shege Mara mutunci yakama d'an marayan Allah ya zazzabga mishi Mari kawai daga yace Yana son wannan nakasassar k'anwar taka Toh idamma ba khameelu me zuciyar Imani ba waye zece yanason nakasasshiya amma shine zaka tadama da d'an maraya jini abanza shege d'an iska so kake yanda ka iskance bakayi aure ba itama ta iskance Idan ma kana tak'ama da kud'i Kana lalata da yaran banza yanda ka saba to wallahi baka mari banza ba ai zaka fito ka sameni banza kawai " kowa shiru yayi, murya na rawa Ummee tace" kiyi hak'uri Hajja Neenah yayi kuskure ki g.... " cikin gatsali ta dakatar da ita da cewa" yimin shuru munafuka aiduk Kece silar komai kind'auka bansan komai ba eyeh sumumu kasau macijin sari ka nok'e to nasan komai duk k'ullaΒ²r ki da hassadar ki dakike Akan soyayar dake tsakanin Zabvier da d'anshi Khameel nasan komai karkiga kamar ban Saniba nasan duk wani nuk'ufurcin ki ehe " sarki ladteef ya d'ago ya kalli matar tashi fuskar shi cike da tantama, Kai kurum ta sunkuyar bata kuma cewa komai ba.
A hankali yake saukowa daga Saman benen kanshi sunkuye a k'asa ya k'araso kusa da Ummeenshi shima ya zauna, seda jumaima ta Gama sauke Mai tujarar duniya taga Babu wanda ya tanka ta harta gama ganin hakane yasa ta fashe da kuka tana fad'in "Allah sarki sarkin adalci sarki junaid maleek dakana Raye da an amsarma d'an marayan jikanka hakkinsa, wannan gantalallen a gantale ze k'are" ajiyar zuciya sarki yayi yace "Shureim miya had'aka da Khameel d'an d'anuwana har kamareshi shatin yatsunka ya bayyana Akan fuskar shi" Prince ba mutum bane me yawan magana kuma bayason fitina ko hatsaniya kokad'an bayason ace yayi kokuma na jikinshi yayi kwanda ayi zaman lafiya shine kawai. Kallon shi kowa ya keyi Yana jiran abunda zece, sedai abunda ya furta bak'aramin mamaki yabani ba amma kuma da Alama mutanen gurin Babu wanda yaji mamakin maganar dayayi, "ana~asfuhn" Kallon Khameel sarki yayi yace " Allah Abieyna mugunta ce kawai, daga yazo yaji nace inason na auri sister Shubai'a shine kawai wannan matar tasashi ya wawwanka min Mari dama wallahi batasona har gorin baba takemin kuma bayan tasan ya rasu amma tak'i denawa" ya k'arashe maganar Yana nuna Ummee data saki baki tana Kallon ikon Allah Dan ita bata d'auka sharrin su yakai Haka ba, ajiyar zuciya sarki yayi yana mik'ewa yace "na yanke hukunci kuma umarnine ba shawara ba, Shureim yanzu kabama Khameel d'an d'anuwana hak'uri base anjima ba, sannan muddin Ina raye Shubai'a matar Khameel ce, ke kuma...." ya k'arashe yana nuna Ummee da jikinta yagama yin Sanyi, dagatanta da matsayinta wai kamar ita *MARYAMU BINT RAQIZ* ake ma Haka ba komai, Kai kurum sarki ya girgiza daga Haka ya fice a fusace mik'ewa Shureim yayi ya k'arasa gurin y'ar uwar shi dake kuka suka mike sannan ya juya ya kalli su Hajja jumaima yace "kuyi hak'uri" daga haka suka wuce ciki, hajja Neenah ce ta mike tana fad'in "Humm wallahi kudai gyara rana dubu ta b'arawo ce duk fa abunda kukeyi Ina sane dakufa Tohm ku cigaba, ke kuma MARYAMU kiyi hak'uri" daga haka ta juya ta fice, Ummee ma hak'uri tabasu ta tashi ta wuce b'angaren mijin ta.



*KATSINA*

*Bayan sati d'aya*

"Maryam magana nike son muyi me mahimmanci dake Dan Allah ki bani hankalin ki" Maryam na cigaba da cin gurasarta tace "uhmm inajin ki Sarauta nifa nasan maganar bazata wuce AKAN KUDI ba dan haka inajinki" Sarauta tace "tabbas AKAN KUDI ne amma wannan Karon tasha banban da sauran dan Allah ki fahimceni ke Kadai ce Nike iya sanarma da matsala ta ki fahimta" Maryam ta cigaba da cin gurasarta tace " Humm komadai miye Akan kud'i ne kawai ni kisanar min inaji" ajiyar zuciya Sarauta tayi tace "Humm Maryam yau Kwana uku kenan dana had'u dawani mutum waishi Yakub, yazo har gidanmu yashaida min dacewa suna da Oga wanda shikanshi besan iya adadin kud'in shi ba, P. A suke nemar mishi a k'asar JIDDA yake zaune, aiki zanyi musu ta hanyar gano musu duk wani sirrin kasuwancin shi da abunda ya shafi dukiyar shi, shi ogan nasu a duk wata zedunga biyana albashi kimanin dubu d'ari biyar, sannan sukuma aduk Sanda na Kai musu wani important bayani zasu bani kimanin dubu d'ari biyar suma, kinga in anhad'a 1m kenan aikin shekara zekaini samun 12m yakike gani Nidai na amince harma munyi magana dasu akai, zasuje gidanmu su sanar da Ummah cewa nice wacce nasamu scholarship d'innan, Dan haka zan tafi k'asar India domin cigaba da karatu na, kinga Ummah zatayi farin ciki kuma sannan zata amince da sauri, kuma kinga danayi kud'i na gama abunda naje yi zasu rakoni har gida su sanar ma ummah cewa mamallakin makarantarmu ya rasu dan haka aka rufe makarantar, shysa suka dawo dani tare da kud'ad'en dazasu isheni inyi rayuwata har ingama makaranta kinga daganan sena cigaba da makaranta na Anan kuma gashi burina ya cika koba Haka ba” Maryam ta tsaya cak tana Kallon Sarauta, harta yunk'ura zatayi magana seta tuna halin Sarauta tunda harma sungama magana sun yanke shawara ai ita dama Babu wanda ya Isa da'ita, kallonta Maryam tayi tace "hakan kike ganin ze fisheki ko" Sarauta tace "Ehm akwai matsala ne" Maryam taja dogon numfashi ta mik'e tana saka Hijab d'inta tace "Allah yasa hakan shiyafi alkhairi Allah ya sadamu da alkhairi" Sarauta ta mik'e tana fad'in "Ameen, ahah Ina zuwa kuma" tana fita daga d'akin tace " shams ne yazo yake kirana sena dawo" Sarauta tace " ah ah Toh jirani mutafi Nima gida Nayi" Maryam ta tab'e baki ta fice, Sarauta kuwa ko ajikinta tafi to itama, awaje suka iske shams, ko gaisawa basuyi ba saboda ita dama Sam shams be Mata ba, wucewa tayi kurum.

Tafe take, harta zo Kan layinsu taji horn d'in mota a bayanta, tsaya wa tayi har motar ta k'araso gaban ta, a hankali ta sauke glass d'in motar, fuskarta d'auke da murmushi tace "Barka" with surprise Sarauta tace " *LAYLAH M. K ME BULAWUS* " Laylah tace "yeaf nice, please can you come in, inason muyi magana" Sarauta tayi murmushi tace "why not" daga haka ta zagaya tashiga motar, seda suka gyara parking sannan Laylah tace "amma Maryam Sarauta ko" Sarauta tace "kwarai ma kuwa, you know what duk Sanda za'ayi show d'inki inanan bakin TV gaskiya kin iya show ga d'aukar wanka, shirin perfumes show ba k'aramin k'ayatar wa yake ba" murmushi Laylah tayi tace "Allah sarki, Nagode sosai, please wani temako nazo nema agurinki" Sarauta tace "Humm inaji Allah ya bani ikonyi" Laylah tace "inason shams, shams shine rayuwa ta, tun ba yanzu ba Nike cikin wannan halin amma kullum Babu wani ci gaba, kwatsam sena ji labarin ansa mishi rana, hakan ba k'aramin gigitani yayi ba kafin kuma nasamu labarin ki agurin sis hauwa, please Sarauta ki temakamin wallahi Ina sonsa sosai konawa ne wallahi zan baki indai kin amince" kallonta Sarauta tayi kafin tayi ajiyar zuciya ta kalleta tace "ki kaini gida" batare da Laylah tace komai ba taja motar har k'ofar gida takaita, tana k'ok'arin fita daga motar Laylah ta rik'e hannun ta tana fad'in "ki temaka min Sarauta" β€œzanyi tunani akai” shine kurum abunda Sarauta tace tafice daga motar, ajiyar zuciya Laylah tayi taja motar ta tabar unguwar.

*Bayan Kwana biyu*

Zaune suke su uku a Kan tabarmar, daka gansu kaga turawa, Nabil, Yakub, da Jabeer, Ummah data gama yarda da bayanin dasu kayi Mata tace "Ehm Tohm ranka ya dad'e bank'i ta taku ba amma gaskiya banason yin nisa da y'ata, ita kad'ai gareni kuma kunga mahaifinta ya mutu ita Kadai ce dani yanzu" jabeer yace "ma'am kiyi hak'uri yarinyarki nada k'ok'ari ya kamata taje" Nabil yace "Humm ma'am kiyi hak'uri" ya k'arashe Yana mik'a Mata wasu takaddu yace "ma'am wannan takaddun gidane dana motar da gwamnati ta bawa mahaifin yarinyar Tohm kasantuwar ita batada baba shysa muka baki wannan kuma dubu d'ari ukune da aka had'o dashi (kud'in da alhaji Mansour ya bata)" d'an had'e gira ummah tayi tace "gwamnati kuma" dasauri Sarauta tace "eh ummah Nima bakiji mamakin danaji ba wallahi Humm ummah mun godema Allah" Ummah tayi jugum tana Kallon takardun aranta tana Jin inama ace mijin ta na raye dayafi kowa farin ciki d'auka tayi tana murmushi tace "Nagode Allah yasaka da alkhairi" Yakub yace "daga yanzu zuwa Koda yaushe zaku iya komawa gidanku domin komai is ready base kun tafi da komai ba" Ummah tayi murmushi tace "uhmm ai bazamuyi hakanba tukun se zuwa jibi Idan munyi sallama da mak'ota ko" haka sukayi ta fira har suka tafi. Awannan rana ummah har kukan farin ciki tayi Don murna.

A ranar ta sanar da Maryam komai Babu abunda Maryam tace se Allah ya temaka ya had'amu da alkhairi.

Bayan Kwana biyu su Sarauta suka tare, gida yayi gwanin ban sha'awa, akwai bene agidan gidan ya tsaru irin gidajen manyan y'an kasuwar nan ne.


KAR KU MANTA AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARINE DA NAYI SHI DOMIN FAD'AKARWA NISAD'ANTARWA DAKUMA TUNATARWA, TAKU CE ME NISHAD'ANTAR DAKU AKULLUM DA KO YAUSHE.

@ *SHERNTEE GHAYU*


*kuyi hak'uri da rashin post danikeyi Kwana biyu Babu nefa ne wayar ba charge sosai ga wannan ayi manage ba yawa*

βœ…βœ…βœ…βœ…


πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΅ πŸ’΄

(A poor lady story)

... 27th April, 2023
*Story & writing*
*By*
@ *sherntee Ghayu*πŸ₯°πŸ₯°


πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘


πŸ…Ώ........ *011 & 012*


*JIDDA*

"Ummee please ki dena kukannan kukanki babban bala'i ne a gareni, Ina kuke son insa kaina, duk kun juyamin baya kuduba fa ko abinci kun k'i ci ya zanyi ne" ya k'arashe maganar kamar yayi kuka, Ummee ta share hawayenta, ta dafa kafad'ar shi tace "my son kaima nasan halin

Please Login or Register in order to submit comment