Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata magana, yanzu ma hakan ne tana kwance tayi filo da k'afar shi, daya motsa take rik'e shi, kowa se dariya yake musu. Aunty jameelerh ce tace "Uhmm dama su Mr billionaire an iya lallab'a haka" ya Harare ta yace "Toya San ranki, da bazanyi ba Idan banyi Mata ba ke zanwa" Aunty Rama tace "yanzu ko kunyar Ummeen taka bakayi" ya kuma Hararar jameelerh yace "to ai itace se wani tsokanana take Bama ta gani Mrs d'in tawa bata da lafiya" khairy tace "Allah ya bata lafiya" kafin wani yayi magana su Abiey suka shigo, seda suka gaisa da imamu sannan sarki ya kalleshi yace "imamu yunus gata nan tana barci" Imamu ya kalleta kafin ya matsa ya d'ora hannunshi Saman kanta, Shureim yayi yunkurin matsawa, imamu yace "ah ah ka zauna Idan ka tashi zata iya farkawa" Shureim ya tsaya Yana kuma gyara Mata kwanciyar, tunda imamu ya d'ora hannunshi akanta yake addua, kusan 10mins kafin yayi ajiyar zuciya ya kalle su, Shureim yace "imamu lafiya dai" imamu yayi wata k'akk'arfar ajiyar zuciya yace..........





*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa dakuma tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)



...... 16th June, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu*






πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ......... *053 & 054*





....... "karku damu kanku da yawa, bawani Abu bane yake damun ta face d'imuwa tad'an lokaci wanda hakan ke faruwa sanadiyyar wani ko wata babbar jinnu ta shiga jikinta kuma, wannan shine Karon farko da sukayi magana Ajikin ta dan Haka karku damu zuwa gobe zata dawo daidai, a yanxu Shureim kawai take gani Amatsayin wanda ta sani, amma Idan tayi barci zuwa gobe in sha Allah komai zezo lafiya, Kai kuma Shureim ka karanta Mata Fatiha sau 7 a ruwa ka bata Tasha before ta kwanta da ayatul kursiyyu in sha Allah zata dawo daidai kunji" kowa yayi ajiyar zuciya Yana Kallon imamu kafin sarki yace "amma imamu bazaka iyayin magana dasu ba" imamu yayi murmushi yace "karka damu da wannan komai lokaci gareshi amma dan yanzu ma aljanar bata jikinta bazamu iyayin magana da'ita ba ni zan koma d'alibai na jirana" ya k'arashe maganar Yana mik'ewa, sarki da uncle Yusuf suka rakashi, nan kuma aka b'arke da jimanta ma juna Akan abunda ke faruwa.





*Washe gari*




Kowa Yana zaune Kan kujera a falon, hajja Mubeena ta kalli Ummee tana had'e rai tace "ke maryama ki tashi Kije b'angarenmu akwai maganina Akan drawer ki d'auko min" Ummee tayi murmushi ta yunk'ura zata mik'e, Shubai'a da shigowar ta kenan tace "wait wait wait Ummee d'an koma ki zauna Naga d'an shegiyar daze tada ke ya Aika" Shureim ya mik'e Yana Kallon ta yace "are you out of your sense Shubai'a, hajja kike fad'ama Haka maza bata hak'uri" Shubai'a ta juya ta k'arasa gurin hajja Mubeena asaitin kunnen ta tace "you know I know everything ko Tohm, kid'au mataki da gaggawa kafin Raina ya b'aci" da sauri hajja ta mik'e tana cewa "no need ma yaro, Muje kiji kinji my granddaughter" Shubai'a tayima yayanta dariya tabi bayan hajja, hajja jumaima ma ta tashi tabi su, Ummee ta kalli Aunty Rama tace "Wai meke shirin faruwa ne haka" Aunty Rama tace "Allah Dai ya kyauta kawai amma wannan fa Tohm" ganin Shureim ya mik'e ne yasa suka bishi da ido, gurin Sarauta ya nufa da take k'ok'arin saukowa daga upstairs d'in, murmushi ta sakar ma Ummee kafin ta Ida saukowa, Shureim ne ya kama hannun ta yace "ya kika tashi" ta zame hannun ta daga nashi tace "Alhmdll yakuke" ta fad'a tana zama kefen Ummee, Ummee ta kama hannun ta sannan suka gaisa, seda suka gaisa da kowa kafin cikin zumud'i Sarauta ta kama hannun Ummee tace "Ummee albishirin ki" Ummee tace "goronki se anjima" Sarauta tace "mafarki Nayi Shubai'a na magana" Ummee to kalli mutanen falon duk sukayi dariya kafin tace "to ai Dagaske ne my Shubai'a ta fara magana tun day before yesterday" Sarauta ta mik'e with more surprise Akan fuskar ta tace "Wayyo Allah na Dagaske kike, tana ina naje Naji maganar masoyiya ta, Wayyo dad'i Muje Nagani" Ummee na murmushin farin ciki tace "tana part d'in su Hajja" Aiko da uban saurin ta, tafita zuwa part d'in kowa se dariya yake Mata.





"munsan kinsan komai Shubai'a, to Ina fatan Zaki iya bakin ki, domin gujema abunda ka iya faruwa" hajja jumaima ta fad'a cike da tsabar tsanar ta, hajja Mubeena tace "Idan kina ganin a wannan Karon kin tsira to agaba Babu wanda ya Isa ya kubtar dake" Shubai'a tayi dariya harda shewa tace "ko abaya ma aibaku d'auka zanyi magana ba, to ikon Allah ne yasa Nayi magana awannan lokacin, kuma kome zaku sake yimin seda izinin Allah ze kamani, kuma ku sani tara ku Nike da ace wani mummunan Abu yasami d'an uwana da gaba dayanku sena saku rayuwar k'unci da bak'in ciki, amma zuwa yanxu Babu abunda zanyi muku saboda yayana yakawo muku daidai daku, Aike inace ta tab'a marinki ko, kinsan yanda marin ta yake, kawai dan kinyi k'ok'arin tab'a mijinta Ina kuma ga Idan ta gano d'ayar gaskiyar Hhhhhh zaku sha mamaki" hajja Mubeena tace "daga ke har ita banzar a tafin hannun mu kuke acikin gidan nan se abunda muke so" Shubai'a ta kuma yin dariya tace "da kenan da Babu gimbiya acikin masarautar amma xuwa yanzu komai ze tsaya a matsayin shi wasuma kuma su koma banyi" hajja jumaima tace "ke MADINAT ki iya bakin ki" Shubai'a tayi murmushi tace "wow Sunan kuma yayi dad'i a bakin ki amma let me tell you Sarauta nanan Sarauta to dawo dan Haka" tayi Kwata ta nuna musu yatsa kafin ta juya tana fad'in "Akan mahaifiyata kuma bance ku fasa ba" daga Haka ta fice. Abakin part d'in ta had'u da Sarauta tana k'ok'arin shigowa, wani uban ihun murna sukayi suna rungume juna, murna sukeyi sosai dan Sarauta ba k'aramin farin ciki tayi ba.





"you are welcome dear" Shuwaiba ta fad'a tana rungume Shubai'a, Shubai'a cike da murna sekace amarya itama take d'okin ganinta, kafin tad'an d'aure face tace "since jiya Nike baza idon ganinki amma se yanzu ko" Shuwaiba na zama kusa da Sarauta tace "Eyyah sorry dear wallahi Mr billionaire ne be fad'a min bane se yau" ta fad'a kafin ta juya ta kalli Sarauta tace " *first lady* ya jikin naki kuma" Sarauta tayi murmushi tace "hmm lafiya qlau *deputy* ya gidan" Shuwaiba tace "gidanki nanan yanda kika barshi Babu wani cigaba" kafin Sarauta tayi magana Shubai'a tace "excuse me guys, yaushe ne kuka fara shirin nan" Sarauta tayi dariya suka tafa da Shuwaiba kafin Shuwaiba tace "to kekuwa y'ar kurma duniyar ma Duka nawa take balle kuma" Shubai'a tace "but wallahi I'm shocked about it" Sarauta tace "ke Malama Shuwaiba is my sister and also my friend my husband wife my deputy so duk miye na mamakin" Haka suka cigaba da tattaunawa atsakanin su ka rantse wani Abu be tab'a had'asu ba.





"waikuwa kinji abunda mutanen nan suke fad'a kuwa are they in there sense kuwa kodai tsufan nan ne yasoma tab'a lafiyar su" Khaleesat ta fad'a hankali a tashe, Juwaira taja dogon numfashi kafin ta mik'e tace "ni wallahi bak'in cikina ma shine da waccan kusakar itace silar komai koba komai yanzu ma zata k'ara samun matsayi a gurin shi hunm wallahi daga ita har Shubai'a ji nake kamar na kashe banzaye" Khaleesat tace "kinga d'auko mukullin motar ki Muje gidan can muga meke going" Juwaira ta tab'e baki ta mik'e kanan suka tafi.





"Kai Kai yaya masha Allah Naji dad'in labarin nan ashe kuma su Shubai'a se baki ya bud'e to Allah ya kare gaba, Amata Allah Sanya alkhairi kafin na iso" sarki yayi murmushi hak'ik'a Yana k'aunar y'an uwanshi musamman Sirayya wacce har yanzu matsayin ta be sauya ba a ranshi, yace "Eyyah y'ar k'annuwata Ni'imatu Babu komai wallahi ykk yasu jameel da jabeer" tayi dariya tace "lafiyar su klau jameel ma yasamu aiki anan bayan kula da company mahaifin su dayake" sarki yace "Kai masha Allah, Allah ya temaka yaron nawa ai akwai hazak'a sosai" nan suka gama wayar su inda faraa fuskar shi takasa d'aukewa, bayan lokaci kad'an Safiyatu ta kirashi itama Sunyi fira ba laifi, Jin wayar shina ringing ne Alamar wani Kiran na shigowa yasa yayi sallama da'ita ya d'aga Kiran *big sis* kuka tasa mishi tana cewa "Wai Dan Allah meyasa yaya yadena sona, nasan kana ganin kirana amma kak'i d'agawa ko saboda nariga nasan Banida mahimmancin dazakayi hakan ni shikenan ma dama zuwa zanyi yanzu kuma na fasa zuwan" sarki ya dafe Kansa yace "kinajina my Surry wallahi dole na yanke wayar danike kawai domin na d'aga naki, yanzu Dai kiyi hak'uri kinji y'ar k'anwas yaya is sorry" kamar tana gabansa tayi murmushi tace "dama nasan yayana baze so b'acin Raina ba, Yawwa inanan zuwa anjima ko gobe, ashe kuma daughter na ta samu lafiya Kai ai akwai kwaryaΒ²r walima Idan na iso" sarki yace "wace irin walima kuma Haba my k'anwas muyi addua kawai muyi farin ciki" ta had'e rai tace "Inna yarda..... Sefa Nayi kaima kasani wallahi Idan Nayi niyyar Abu ko jumaima uwata bazata hanani na hanu da Nidai kayi hak'uri amma senayi fa" yace "shikenan Rigima queen Allah ya kawomin ke lafiya sekin zo" daga Haka sukayi sallama.






"ki kwantar da hankalin ki kinji my diamond bafa wani ciwo bane ne yawa tamaji sauk'i karki damu" Shureim ya fad'a hankalin shi ad'an tashe, hawayen ta ta goge kafin tace "shikenan, wallahi hankali na duk ya tashi amma tunda kace Haka na yarda, amma itakuma Shubai'a ya take," Shureim yaja kujera ya zauna yace "Yawwa ki kwantar da hankalin ki, Shubai'a kuma tana cikin farin ciki fiyeda yanda kike tunani inama ace kina nan hakan ta faru, please diamond kizo kidawo nan mana we missed you alot" ta kuma goge hawayen dake fuskarta kafin tace "da wane ido zan kalli yayana miye na aikata Haka a rayuwa ta, my golden boo banajin Inada kwarin gwiwar daya wuce Sarauta amma ashe itama WA rayuwar ta takeyin komai.... Wai yarinya tace ta aikata hakan" ta k'arashe tana fashewa da kuka Shureim ya mik'e Yana cewa "please my diamond Ummah kidena yin kuka wallahi kukan ki tashin hankali ne arayuwata inajin zubar hawaye ki tamkar na Ummee na, Ummah please ki dawo cikin ahalin ki duk y'an uwanki suna buk'atar ki Atlast Zaki gyara komai da kanki kizo kiyi musu bayani" Ummah ta goge hawayen ta tace "mah golden boo kenan yayana yayi fushi dani ne fa, nasan halin shi Sarai baze hak'ura da wuri bafa zan had'u da fushin shi sosai" Shureim yayi ajiyar zuciya yace "Yawwa to kin gani ai nasan kinfi kowa sanin halinsa baya iya fushi da abunda yake so dan haka kema baze iyayin fushi dake ba wallahi Abieyna Yana matuk'ar k'aunar ki my diamond yanda kika San yasan cewa Ammerh d'iyar kice bakiga yanda yake sonta ba" Ummah tayi ajiyar zuciya tace "kaga mubar wannan maganar yanxu dai akwai abunda Nike so dakai, kanaji" Sarai yasan so take abar maganar, yace "Tohm inajinki" tace "haryanzu baka iya shiga inda Mamu take" yayi shuru kafin yace "wallahi mah diamond nagwada da dama anma na kasa Koda zuwa bakin gurin amma Ammerh na shiga gurin zata dubamin komai zanyi Mata magana akai" Ummah tace "wallahi Idan Ina magana dakai kana sakamin waccan se ranka ya b'aci Aikin Banza" yayi murmushi yace "sorry my ummah na Dena to yanzu Dai Bari na koma ciki zuwa anjima zamuyi waya ki kulaamin da kanki kinji Ina qaunar ki" tace "shikenan Naji se anjima d'in ka kula bye" daga Haka duk suka ajiye wayar.






Duk zaune suke a falon kowa ma yarasa abunda zece, Juwaira ce tayi tsaki had'e da tab'e baki, Neenah data sauko daga Saman benen ta kallesu tace "kukuma lafiya Naga Kunyi jugum jugum Haka" Hajja Mubeena ce ta Harare ta a kaikaice kafin Khaleesat tace "zaman makokin ki muke kafin ki mutu" Neenah ta d'aure face tanuna Mata Hajja jumaima tace "wannan ita kikewa zaman jiran mutuwa shegiya fits Ararat me halin uwar ta" Hajja jumaima tace "Uhm Uhm karki sake ki zagarmin ta gaban goshi Tam" Neenah tayi dariya tayi shewa tace "kwarai kuwa Nayi Sanyi yanzu jumaima har Kece kika samu kwarin gwiwar gayamin magana Haka agidannan Allah sarki mijina ban manta da maganar ka ba dakake cewa, Nid'in nan kura ce ga tsoro gaban tsoro, Humm to Bari kiji daga ke har d'iyar taki maraar kunya dawannan tijararrar jikar taki zan iya yin maganin ku wallahi ku kiyaye ni fa Tohm" kafin jumaima tayi magana Hajja Mubeena tace "kinga Neenah dan Allah Zoki wuce haba tun Muna yara ake Abu d'aya Zoki tafi kiyi hak'uri" wata uwar harara ta bankama Mata, karya murya tayi ta kuma cewa "kiyi hak'uri fa nace" Kwata Neenah tayi kafin ta fice a sashen, Khaleesat tace "miye kuma na wani bata hak'uri tsohuwar Banza kawai" Hajja Mubeena tace "hmm mumuka zauna da'ita har sarki shakkun ta yake balle kuma mu wallahi k'aramar hauka take dashi a kanta" Juwaira tace "Aini wallahi dakun barni da'ita" Hajja jumaima ce tace "kunga Mubar maganar nan kunji muyi maganar data had'a mu" Khaleesat tace "Yawwa yanzu ya kuke gani zamuyi dawannan munafukar yarinyar" Hajja Mubeena tace "yanzu Dai muhau tsari na farko, Sarauta tanada ciki hanyar zubar dashi zamu bi yanzu" lokaci d'aya Khaleesat da Juwaira suka maimaita ciki kafin Khaleesat ta Mik'e tana cewa "Inji wane tsinannan wallahi wannan k'arya ce wannan ai munafurci ne yaushe hakan ta faru" Hajja Mubeena tace "kinga ki kwantar da hankalin ki kinji, zauna ai inma da cikin zamuyi maganin shi kwanan nan" Khaleesat ta zauna tana cewa "wallahi mutuwa zanyi Idan hakan ta tabbata" Hajja Mubeena tace "mun tabbatar cewa tanada cikin saboda wacce ta sanar mana bazatayi mana k'arya ba yanzu kawai Abunda za'ayi kusaka tazauna gidan nan kona zuwa gobe ne kungane saboda Idan kuka koma gida kuma aka bata maganin za'ayi saurin gano gaskiya amma Anan Babu wanda ze zarge ku kunji amma kuma kuma ku zauna Anan d'in kafin gobe" duk sunyarda da jawabin nata, Haka sukayi ta k'ulleΒ²nsu.





Fira suke suna dariya sosai inda Hajja Neenah ita ke basu labarin yanda takeyi ne yake matuk'ar basu dariya, Sarauta dake zaune a gefen damanta tace "wallahi hajjarmu bakida dama" itama murmushin tayi kafin tace "humm ai wallahi ninan dakika ganni da ace yarana kokuma jikokina wasu sun biyo halina toda Babu wanda ya'isa ya nuna musu yatsa ya Kwana dashi" Shuwaiba tace "Uhmm toni Ina ruwana nifa indai da d'a'amun to Banida matsala ko kad'an, amma ai Ance kinada wata yarinyar ma bayan mammaana ko" Neenah tayi murmushi saboda itad'in mace ce me matuk'ar dakewa Arayuwar ta Sam zuciyar ta bata karyewa kamar dai Sarauta tace "tabbas ma kuwa yarinya ta danafi k'auna, saboda yanda Nike k'aunar ta yasa na d'auke ta nabama Mamu ita tamin rainon ta saboda nasani ahannun Mamu zata samu tarbiyya sosai fiye da agurina saboda Idan agurina ne se abunda take so zanyi saboda San da Nike Mata amma ta tafi tabarmu da soyayyar ta, fatana ace tana cikin farin ciki" Sarauta tad'an jima Hajja Neenah ba dad'i, kafin tace "kiyi Mata addua Hajja" Shubai'a tace "Uhmm Ance ma Abieyna Yana matuk'ar k'aunar ta, kuma saboda ita yakamu da ciwon zuciya amma duk da hakan behana ansamin Sunan ta ba gashi kuma uncle ma bashi da lafiya duk ta dalilin ta batayi ma kanta a dalci ba" Shuwaiba tace "sosaima kuwa data hak'ura ta zauna toda tasamu d'a'amun me kyau da inganci" kowa seda yayi dariyar maganar ta kafin Sarauta tace "deputy kenan inda d'a'amun...." kafin wani yayi magana wayar Sarauta tayi ringing murmushi tayi kafin tad'au ki excuse agurin su ta shiga d'aki domin amsa wayar.





"k'awata Kwana biyu Ina kiranki amma shuru lafiya Dai ko" Sarauta tace "lafiya" Maryam tayi ajiyar zuciya dan har cikin ranta batason Sarauta ta shiga cikin wata damuwa tana matuk'ar k'aunar ta, tace "Tohm masha Allah, yakike kuma ya aiki" Sarauta tayi tsaki tanajin zuciyarta na Mata zafi Akan cin Amanar da Maryam tayi Mata tace "lafiya" Maryam tad'an lura dasauyin gurin Sarauta tayi tunanin ko Akan maganar auren tane yasa tace "lafiya kuwa besty ya mijin naki yake" Aiko kamar hakan Sarauta take jira ta mike a fusace kamar Maryam na gabana tasoma surfa jaraba tana cewa "......... .






*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'iraren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da koyaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)





...... 19th June, 2023





*Story & writing*
*By*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š






πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ....... *055 & 056*






...... "Hhhhhh Maryam Kenan, WAI bayan kina tare da mijin amma har kike tambaya ta Wai ya yake, to Bari kiji kinshani na warke zuwa yanzu nasan komai Maryam Nasir kenan ban tab'a tunanin kalar wannan cin Amanar daga gareki ba amma Babu komai, kuma Bari kiji Sarai nasani kud'irin d'aukar fansar abunda Nayi miki Akan shams ne yasa kikeyin hakan to Bari na gayamiki duk wani makirci dazakiyu kiyi iyayin ki amma wallahi Idan mahaifiya ta tasan da wannan maganar Maryam sena d'ed'eta rayuwar ki, kibar ganin Bana Nigeria wallahi da waya guda d'aya kawai sena juya ki daga sama xuwa k'asa, mayaudariya kawai" tunda Sarauta ta fara tijararta Maryam ke kuka,duk wanda yaji kukan zesan irin kukan nan ne nahar cikin zuciya take yin shi tace "Haba Sarauta miye haka kinsan Wacece kuwa Maryam Nasir cefa ah ahh miyene haka, Sarauta anya......" tsawar da Sarauta ta daka Mata ne yasata yin shuru, "munafuka kawai, dakenan da hawayen ki suke da tasiri agurin ba yanzu ba, to Bari na kuma gayamiki Nid'in nan wallahi nafi k'arfin ki Maryam Nasir karki yarda kikaini bango fa,zan wulaqantaki yanda bakya tunani annamimiya wallahi bantaba tunanin kalar wannan cin Amanar daga gurin ki ba Maryam kin bani kunya, kuma Bari kiji na rantse da Allah ko agabaan ka'aba na ganki Maryam karkiyi kuskuren yimin magana dan zan d'auki kwakkwaran mataki akai daga yau Babu ni Babu munafuka mtsww" ta yanke wayar batare data tsaya ta saurari abunda Maryam take cewa ba. Tana ajiye wayar wani kukan k'unci ya kwace Mata, dama ai dole tasan zatayi kukan rabuwar su, Maryam Nasir kawata ce tun ta yarinta da Maryam Nasir kawai ta saba, ita take samar ma duk wani sirrinta da damuwarta wanda Koda mahaifiyarta ma bata sanarwa, kuka take sosai kamar ranta ze fita (Niko nace rashin sani........)






*KATSINA*





"ke Maryam lafiyar ki kuwa anya kina cikin hayyacin ki kike irin wannan kukan, ki nutsu mana ki sanar min me akamiki Haka Maryam" Maman Maryam ta k'arasa fad'a tana jijjigata, Maryam kuwa wani irin kuka takeyi had'e da sheshsheka Me k'arfi, cikin kukan take cewa "wallahi mama Koda xuciyata ban tab'a fallasa sirrin Sarauta ba amma meyasa zata yanke hukunci Akan abunda bani Nayi ba, mama da zuciya d'aya Nike son Sarauta ban tab'a yin Abu domin ya cutar da'ita ba amma mama...."kukan dayaci k'arfin tane yahana ta k'arasawa seda takuma shan kukan ta kafin ta cigaba "Mama wallahi banci Amanar taba, ni Babu wanda na tab'a cima Amana, Allah mama banyi ba mamaah....." Mama bata ankare ba seganin Maryam tayi a k'asa kwance, hankali tashe mama tasoma jijjigata tana Kiran Sunan ta batasan Sanda kuka ya kwace Mata ba "Naja! Naja!! Maza ki kiramin Malam, Nashiga uku ke Maryam, Maryam ki tashi nace miki karkiyi min haka Maryam" duk irin yanda mama take jijjigata amma Abun yaci tura, ahaka Malam Nasir yazo ya iske su hankali tashe ya k'araso domin Kai koba'a fad'a ba zaka iya fahimtar irin yanda suke tsananin so da k'aunar ta, Maryam itace yarinyar su ta farko kuma duk wata uwa tana son y'ay'an ta amma sedai na farkon nan ya bambanta dasauran Koda kuwa bata nunaba, saboda ko wace mace ashayar warta ta farko setaji wannan rad'ad'in da azabar Koda sau d'aya ne wanda hakan na faruwa ne sakamakon tsotson ta da jinjirinta ze fara wannan rad'ad'in kuma Yana tafiya ne da zazzafar k'aunar yaron data soma shayarwa wanda daga shi kuma ko yara nawa zata kuma Haifa bazataji wannan rad'ad'in ba, Bawai nace yaran farko ake soba Abun had'uwar jini ce ai, kuma koba Haka ba Maryam yarinya ce me biyayya dasanin ya Kamata, akwai sirri Amana dakuma faraa, Maryam tasamu sheda me kyau a gurin iyayenta, hankali tashe Malam Nasir yad'au keta suka tafi asibitin.






Yanzu kusan 20mins kenan da aka shiga da maryam ER wanda har yanzu basu fito ba, mama kuwa tana zaune gefen tana rizgar kukan ta, a hankali Malam Nasir ya k'arasa kusa da'ita ya kama hannun ta yace "Haba Maman Maryam ki Dena kukan nan maana addua zamuyi Mata Allah ya bata lafiya kinji" malam Nasir mutum ne wayayye me addini sannan kuma me kula, yanada tsari Arayuwar sa sedai kuma komai dayake yi Yana yinsa ne domin kiyayewa da dokokin Allah, amma iyalan said nasamun kulawa sosai a gurin sa. Mama ta goge hawayen ta, yakuma cewa "meya faru" Mama na sheshsheka tace "Ina waje kawai Naji tayi jifa da wayar ta tana cewa ah ah ita bazatayi cin Amana ba ita ai bataci Amana ba da zuciya d'aya take zaune da Sarauta, tana cikin maganar ne kuma numfashin ta ya d'auke" ta k'arashe tana goge hawayen dasuka zobo Mata, malam Nasir yayi shuru bece komai ba kusan Minti 2 kafin Doctor ya fito, office dinsa suka nufa, seda ya tambaye su kosune iyayen Maryam Nasir, suka amsa masa da eh, yace "gaskiya yarinyar nan tana fama da damuwa aranta sosai, kuma dai Ina fatan kunsan tanada hawan jini wanda kuma ayanzu angaya Mata wani Abun ne nafirgitarwa kamar mutuwa haka ko hatsari wanda yayi sanadiyyar Dena Bama huhunta damar Jan iska, amma karku damu munyi iya bakin k'ok'arin mu akai zuwa anjima zata farka, kafinan seku dage domin Jin miye damuwar ta" Malam Nasir yace "to likita mun gode, amma Inada tabbacin Maryam Koda ta tashi bazata tab'a Gaya mana abunda ke faruwa da'ita ba tanada matuk'ar sirri ko Ince zurfin ciki seda ko ta b'angaren ku ku gwada" likita yayi dariya yace "Allah sarki, to babu matsala zaku gwada d'in, amma ku kuma zaku iya tafiya gida se zuwa gobe ku dawo Anan bama buk'atar y'an jinya akwai nurse dazata na jinyar ta karku damu" Haka su mama suka wuce gida inda suka cigaba da tattaunawa Akan yaushe Maryam ta samu damuwar daharta jininta ya hau, ta b'angaren likita kuwa nurses biyu yasa domin kulawa da'ita kuma shima Yana shiga domin ranar Anan ze

Please Login or Register in order to submit comment