Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Abun nan ya faru taga ta sauya, itama murmushi tayi tace "inanan gurin amarya" khairat tace "Aunty ga wannan Inji yaya" Maryam ta amsa ta ajiye Jakar da ya Aiko Mata da'ita, Sarauta ta kalli Maryam tace "Mrs Hisham nizan tafi se anjima" Kai kawai Maryam ta d'aga Mata, inda ta zauna suka cigaba da fira dasu Khaleesat, ita kuma Sarauta ta fita.






*3Days later*





Komai ya kusa k'arewa, ummah ta fiddo Mamu daga part d'innan kuma wani ikon Allah tunda ta fito kawai seta samu lafiya, yanzu lafiya klau take tafiya, kuma tun bayan hakan Abiey ya yafema ummah komai, haka itama ummah ta yafe ma Sarauta komai, amma kuma har yanzu Babu wani shiri tsakanin Sarauta da Maryam, a wannan Karon ummah dakanta tace tana son Abba taheer zata aure shi, Sarauta gata take samu sosai agurin kakarta Rookayya mahaifiyar Abba Shureim, domin gani take Shureim d'inta ne ya dawo, acikin wa'innan y'an kwanakin kuma aka had'a duk wata dukiyar Abba Shureim dake a JIDDA da Kuwait dama wasu k'asashen duniya aka Bama magajiyar sa, dakyar aka samu ta amsa domin cewa tayi Abiey ta rik'e agurin sa kawai, ganin bazata amsa ba yasa aka raba biyu aka bata Rabi wanda Koda rabin dukiyar ma bazasu fad'u ba balle kuma Duka a tak'aice Dai Sarauta tazama Mrs trillioneire.





"zaune take a gefen gadon tayi kyau sosai, duk da tad'an rame hakan seya k'ara fiddo Mata ainahin kyanta, kallon Shureim tayi dayake danna waya ta amshe wayar tana cewa" Nakiraka ne fa muyi magana amma kawani d'au waya se dannawa kake" ya kalleta yace "inajin ki you can go ahead" tayi murmushi ta sunkuyar dakai ta soma cewa "abaya Babu abunda Nike ganin shine rayuwa sama da kud'i, Babu abunda yafi amfani sama da kud'i, alokacin neman su Nike iya yina, amma tun bayan Dana had'u dakai komai ya sauya, brother Shureim tun Randa na fara ganin ka Naji araina cewa kud'i bashi da wani amfani a rayuwata Kaine, me amfani a rayuwa ta, se bayan shigowarka rayuwa ta na fahimci soyayya itace hasken komai da komai, tun bayan wannan lokacin na karkata hankalina Akan soyayya duk wani bincike dazan yi akanta Nayi na Riga da nagane cewa itafa itace ma silar da aka fara yin kisa akanta, Hum zaka ce nacika surutu ko, Nima abunda Nike tunani kenan amma se bayan had'uwa ta dakai ne nadawo hakan, inshort dai kawai *INA SONKA BROTHER SHUREIM BANAJIN ZAN IYA RAYUWA DAWANI WANDA BAKAI BA, SOYAYYAR KA ITACE ZATAYI AJALINA, ZAN IYA SADAUKAR DA KOMA NAWA NE AKANKA, AKAN SOYAYYAR KA BABU ABUNDA BAZAN IYA BA* (NIKO NACE AKAN KUD'I ya dawo AKAN SOYAYYA 🤣🤣😂), Shureim ya mik'e tsaye ya kalleta kafin wani irin murmushi ya kwace mishi yace "wait wait, WAI me kike nufi ne, kina nufin kina sona, Malam shut up, mak'aryaciya kawai, na zauna dake kike nufi angaya miki naci Kaine ko an gayamiki ni Banida hankali ne, Idanma na zauna dake what of my future child's sukuma ya maganar tarbiyyarsu waye ze basu kina nufin nakai su gidan horon tarbiyya ne domin Kedai Babu abunda Zaki iya koya musu, Hum Wai Akan soyayya ta, ni nazata ma Akan kud'in ki zakiyi min magana tunda Aikin ki ya k'are tare dani, kuma suma very soon zan baki kud'in ki da duk alkawarin da mukayi sannan mu rabu, ni Bana sonki kuma karki k'ara kirana Akan abu Mara mahimmanci kamar wannan, Shuwaiba najira na muyi dinner" daga Haka ya fizge wayarsa dake hannunta yayi hanyar fita, Sarauta da tunda ya fara magana take kuka ta mik'e cikin d'aga murya da k'unann zuciya tace "wallahi ni kuma inason ka koma mizakayi, Aishi so Hana ganin laifi ne, kuma indai Ina tare dakai Babu wacce zata rab'e ka Kai nawa ne ni kad'ai, Ina SONKA Shureim" ta k'arashe tana fashewa da kuka, Shureim yayi tsaki ya girgixa Kai yace "Allah ya baki lafiya" daga Haka ya fice.......






*NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN GA DUK WASU HEARTBREAKERS AKAN SOYAYYA ALLAH YA SAUYA MUKU MAFI ALKHAIRI* 🥰






*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'iraren labarine Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu*🥰🥰



Ina matuk'ar godiya da fatan alkhairi aduk rayuwar ki masoyiyata abar k'aunata, a duniyar marubuta bazan manta dakeba Nagode Nagode sosai madam tawa, Ina miki fatan alkhairi y'ar uwa *YA² ZAITUNA*




@07064706167

💵 💴 *AKAN KUD'I* 💴 💵

(A poor lady story)



..... 5th July, 2023



*Story & writing*


@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰





🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚





👑J. W. A👑





🅿......*069 & 070*






Yana fita ta fad'a Saman gado tare da fashewa da kuka cikin kukan take cewa "wallahi ko mutuwa zanyi bazan dena sonka ba kaima ai kana sona wulak'anci ne kurum, Haka ta dunga rizgar kukan ta Babu me lallashin ta.




Ta b'angare shi kuwa Yana fita ya jingina da kofar tare da lumshe idanun sa, duk iya kukan da take yi Akan kunnen sa, yakai almost 10mins agurin kafin ya bud'e idanun sa dahar Sunyi ja yabar gurin.





Yauma Maryam a fusace ta taho domin zuwa ta k'ara yima Sarauta kashedi na k'arshe Akan karta kuma turo Mata mijinta ko kuma takarda d'auke da sak'on ban hak'uri itafa bata Santa ba dan Haka ta rabu da'ita, a fusace ta tura k'ofar tana cewa "Babu ni ba....." ganin irin yanda Sarauta ke kuka kamar ummah ce ta mutu yasa Maryam tsayawa cak, ai tuni ta manta da abunda ke going tahau Saman gadon tare da kamo Sarauta jikinta tana cewa "Subhanallahi Sarauta Meya faru Haka waye yayi miki wani Abun ko mutuwa akayi" Sarauta na rungume Maryam tace "iya tsawon rayuwata ke kad'ai kika San sirrina kuma ke kad'ai kike bani shawara me amfani, Maryam wallahi Ina son Shureim, kuma soyayyar sa bak'aramin kamu tayi min ba Maryam shi kuma baya sona ko kad'an halina ya Jamin AKAN KUD'I gashi Ina neman rasa soyayya ta ta farko, Maryam wallahi mutuwa zanyi Idan Shureim be amshi soyayya ta ba, Maryam ki temakeni, a baya inaganin kamar bak'in ciki ne yasa bakyason shegen son kud'i na ashe ke sona kike, Maryam dana rik'e mutuncina, ban bar k'asata ba kuma banyi aure AKAN KUD'I ba danasan Shureim ze Soni kodan albarkacin ummah amma yanzu na lalata komai AKAN KUD'I Maryam ki temakamin" ta k'arashe tana fashewa da kuka, Maryam tayi ajiyar zuciya tana goge hawayen fuskarta ta d'ago Sarauta tace "kinaji k'awass Wai dama Akan wannan ne kike kukan nan, maza jeki wanke fuskar ki kizo na gayamiki yanda Zaki ai wannan duk me sauk'i ne Tunda ba Shureim d'in ne ya mutu ba, ni kinma bani tsoro nasha Shureim d'in ne ya mutu fa" Sarauta ta Mike taje ta wanko fuskarta, sun dade suna shawara da Maryam kamar basune suke rigima ba, dama Ance tsakanin mutum guda biyu se Allah, nanfa suka washe kamar ba suba.





Ahankli komai yake tafiya, duk inda Shureim yake Sarauta nanan, komai tana wani shishshige Mai, koda yaushe tanayi domin burgeni amma kullum matsayin ta d'aya a gurin shi Ummee tayi mishi magana harta gaji, cikin wannan d'an lokacin kuma aka fara hidimar bikin Shubai'a, Shuwaiba itace take temaka Mata Akan komai duk da Kwana biyu bata wani Jin dad'in jikin ta.





Yanzu ma kwance take Saman cinyar Ni'imatu, hira sukeyi sosai dan sun Kwan biyu basu had'u ba, cikin firar ne ummah Ni'imatu take cewa "my daughter kina Jina ko dan Allah ki rage nuna zalama Akan abinci Haka ki duba fa kigani kowa camfa ki yakeyi Allah Sam banajin dad'in hakan" Shuwaiba tayi dariya tace "Ummah na kenan itafa rayuwar nan komai na lokaci ne, ta yiyu Allah y rubuta min abincin shekara 20 zanci ni kuma bazan Kai shekarun nan ba kinga kuwa ai dole ne nadunga cin abinci Babu dare Babu rana domin Nakai wannan limit d'in ko" Ni'imatu tace "gidanku waike Bana hanaki in ana hira ki dunga sawo maganar mutuwa ba" Ummah Nur ce tashi go fuskarta d'auke da faraa tace "ahahh Wai dama kina nan daughter" Shuwaiba tayi murmushi tace "yau fira zanyi da uwata ko partyn ma bamu zuwa ko ummah na" Ni'imatu ta ture kanta daga Kan cinyarta tace "dawa zakiyi wannan shiriritar taki, matsa bani guri ana bikin y'ar tawa zan zauna ne ki Bari Idan angama bikin mayi firar" harta tafi taji Shuwaiba ta rik'e Mata hannu, Ni'imatu na juyo WA Shuwaiba tace "to Aini Banida lokaci wannan ne kurum lokacina Haba ummah na mana dan Allah" duk da Ni'imatu taji jikinta yayi Sanyi amma se tace "sakarni kinji y'ar nan, Allah yayi miki albarka Bari Muje ai bazamu dad'e ba zamu dawo" Ummah tace "yauni Naga k'auna to ki hak'ura ki zauna mana" Ni'imatu tace "Muje kawai" Shuwaiba tace "kema Ina sonki ummah Nur sekun dawo zanyi kewar ku" duk sukayi murmushi suka juya suka tafi. Jiki a sanyaye ta mik'e tare da kashe wayar ta da take ta ringing wanda tun dazu Shubai'a take kiranta.






Zaune yake Saman 2seater Yana danna laptop Yana Jan tsaki, ita kuma tsaye take a gefen Kansa se faman zunb'ura baki take, wani tsakin ya k'ara ja ya d'ago ya kalleta yace "waike mayya ce nace miki Bana sonki Bana sonki amma ke kink'i fahimtar Hakan ko, ki matsa min aka kafin na mik'e" murya kamar zatayi kuka tace "to Nidai koma miye Ina sonka, kuma Allah Babu inda zani harse ka taso mun tafi partyn nan, bikin Shubai'a sukutum ace kana gida Haka zaune hankalin ka kwance" yace "Ohh so kike naje nayita yawo hankali na a tashe ko to ta Allah ba taki ba Muguwa" kafin wani ya kuma magana aka bud'e k'ofar aka shigo, kallon su tayi Duka tayi murmushi tare da cewa "Laaa first Lady ashe kina nan" Sarauta tayi yak'e tace "Uhm" Shuwaiba ta zauna kusa da Shureim tace "baza kuje partyn ba" Sarauta tace "ke Me ya hanaki zuwa" Shuwaiba tace "banajin dad'in jikina Kwana biyu" Sarauta tace "Allah y sauwake" Shureim yace "Subhanallah Mrs billionaire Mike damun ki" tayi murmushi tace "kawai dai jikin ne babu dad'i, Amm Yawwa my Mr billionaire yau Idan ba damuwa fira Nike son muyi please karka ce Ahah, dan Allah first Lady kisa baki mana karya ce Ahah" Sarauta ta kalleshi, ajiyar xuciya yayi yace "shikenan Tohm amma dai hope ba firar abinci bane" tayi dariya tace "Sam yau ta sauya zani" Sarauta tace "amm Ina zuwa" daga Haka ta fice, Shuwaiba tace "yaya da fatan dai bani na b'ata Mata raiba, Idanma nice Ina neman yafiya a rok'amin, kuma kaima na yafe maka duk komai na itama Haka Kai ni kowa ma na yafe mishi Allah ya yafe mana Duka" Shureim yace "yau kuma y'ar yafiya ce kenan, to Nima na yafe miki komai kinji" tayi murmushi tace "inason ka har bayan rayuwa ta" nan fa suka cigaba da firar kamar masoyan asali.






"Kundai gama shirya komai ko dan gobe Nike son ganin gawar Mr & Mrs M.S ai kunji" Ali khan ya fad'a Yana Kallon wanda ke gabansa, wanda yake tsayen yace "ai y'allabai Idan Nabi ta kansu gobe ki gawar su bazaa gani ba domin sena musu raga² Akan Titi" Ali khan yace "Yawwa mu2mina shikenan nizan wuce Ohk bye" daga Haka sukayi sallama.




Awannan rana dai Haka nan Sarauta take jinta, tana kishi da kowa Akan Shureim amma batayi da Shuwaiba maybe hakan ya samo asaline tunda jininta ce, sunsha fira ma da'ita sosai kafin sukayi sallama ranar dai duk wanda yayi ma Shuwaiba tayin abinci sedai tayi murmushi domin wani ikon Allah jinta take ak'oshe har mamaki ake ana zolayan ta kodai bata da lafiya ne a Kira doctor itadai sedai tayi dariya.





*WASHE GARI*





Yau ta kama ranar dinner partyn Shubai'a wanda bak'aramin shagali aka had'a ba kowa ya tafi except Sarauta da take jiran Shureim su tafi tare, shikuwa Bema San tanayi ba, duk yawan gidan Babu kowa se y'an tsirarrin escorts.




Shureim ne ya fito da sauri tare da bud'e mota yana shiga yayi Mata key amma kafin ya tada motar kawai yaji ta bud'e ta shigo, tayi bala'in kyau cikin red party gown kanta yasha gyara ta fito sak a balarabiyar ta se faman ajiyar zuciya take ya d'ago ya kalleta duk da yaso ya shagala Akan Kallon ta amma be hanasa cewa "ke get out" itama Sarauta ta d'aure tace "wallahi yau daka tafi ka barni...." tayi kwata ta juya, kad'an ya Hana murmushi be kwace Mai ba yace "saboda kina Bina bashi" ta GIRGIZA Kai tace "Sata dai kayi min" yace "nii" tace "Ehmana Kaine mana b'arawo kawai Ina zaman zamana lafiya kazo ka sace zuciyar ba komai, Nidai Muje dan Allah kar a tashi" yayi Mata wani irin Kallo Yana d'age tinted glass d'in yace "bakida hankali a hakan zan kaiki gurin can sekuma aka ce miki kowa ma besan ciwon Kansa ba, ni Bama gurin partyn zani ba" daga Haka ya tada motar ya tafi Aiko Sarauta fa nan ido ya Raina fata dan taci burin zuwa dinner amma firr Shureim ya rufe idonsa yace "Babu inda zata sak'o ma ze amso" Aiko Sega Sarauta harda hawaye amma ko Kallon ta beyi ba.




Babu zato Babu tsammani kawai sukaga wata mota daf tayo kansu kuma tsakanin ta da Allah kansu tayo, Sarauta ta zaro ido tare da kurma IHU shikuma Shureim duk ya rud'e Yama rasa yanda zeyi, gashi motar se k'ara gudu take, hannun sa d'aya yasa ya Kamata sannan ya runtse idonshi seda ya Bari Sunyi dab da motar kawai shikuma ya juyar da Kan motar su tayi gefe tare da bugar bishiya ta tsaya zuwa wannan lokacin kuma Sarauta ai hartayi sumar Riga mutuwa dan ta sadak'as Akan ta mutu, dasauri Shureim ya bud'e motar sa tare da fitowa, Aiko yaci sa'a mutanen nan suna nan basu Bar gurin ba, dukan tsiya yayi musu kafin yasasu kneeling a gabansa sannan ya d'aga waya ya Kira shugaban escorts dinshi, cikin d'an lokaci kuwa segasu, nan yabar case d'in a hannun su yace suyi bincike kuma a gano waye yasasu daganan akai su police station yaji da komai, daganan suka sauya Mai mota ya d'auko matar sa yasa a ciki yaja motar suka tafi.






Tunda aka fara dinner ta kasa zaune ta kasa tsaye se zagaye take yi, hajjas ta hango zaune se wasu mutane biyu sun juya baya se Khaleesat dake zaune itama da wata Mata, murmushi tayi ta k'arasa gurin sedai kuma cak ta tsaya Jin abunda suke tattaunawa akai, rass taji gabanta ya fad'i kenan Dai mutanen nan bazasu Bar Sarauta ba, to Wacece suke cewa xasu kashe Idan ba ita ba dole, ta nemi Sarauta ta bata kariya daga sharrin mutanen nan, dasauri ta juya ba tare dasun ganta ba, ta zagaye duk iya yawan Hall d'in amma bataga Sarauta, kowa ta samu tambayar sa take koya ga Sarauta, duk y'an uwanta maza ma seda ta kirasu ta tambaye su kosunga Sarauta amma Babu wanda ya iya bata amsa, dasauri ta fita tahau motar ta wanda y'an kad'an ne basuga fitar ta ba saboda irin gudun datake.





Ta b'angaren Shureim kuma, wani killataccen part dayake a rufe agidan ya bud'e yashiga da'ita, iya tsarawa part d'in ya tsaru, nan ya bata duk wani temakon daya dace, sannan ya temaka Mata ya rabata da rigar jikinta y sauya Mata da sleeping gown, yasa Mata drip domin ba k'aramin firgita tayi ba, sannan ya fita ya rufe ko'ina na part d'in kafin yaja motar sa ya tafi.





Shuwaiba kuwa direct gida ta nufa, tana shiga ta soma Kiran Sunan Sarauta amma shuru, ta duba ko'ina amma bata ganta ba, hanyar gate tayi domin tambayar escorts d'in kosunga fitar Sarauta, sedai Babu kowa agurin can ta hango su sun zagaye wata mota da mashin da suka samu accident, tsaki tayi ta kalli mutum guda daya rage tace "kaga fitar motar Mrs M.S Sarauta yau" Kai ya d'aga Mata yace "yanzu suka fita itada sir Shureim" tsaki tayi tare da dafe kanta ta koma cikin gidan tana ta dialing number Shureim amma shima baya picking, wasu hawaye taji sunzo Mata kafin tayi niyyar fitowa daga gidan.






At 1:30am




Se sannan Sarauta ta farka, duk a tunanin ta ta mutu har anyi jana'iza ganin Dagaske bata mutu ba yasata yin hamdala a fili, (Niko na kalleta nace, Mrs M.S Sarauta dama baki shirya mutuwa ba, tace "ke ko sherntee Ghayu wake son mutuwa), tashi tayi tare da fincike drip d'in ta jujjuya, nan kuma Ina ne haka, ta tambayi kanta tana kuma duba gurin, seda ta duba ko'ina gaskiya gurin so nice yayi kyau sosai, toilet ta shiga tayi wanka, tana fitowa tad'au ki wata sleeping gown d'in tasa, a hankali tasoma saukowa daga Kan stairs d'in falon ma ba k'aramin kyau yayi gashi sawwa sawwa beyi tarkace ba, tana zuwa dining taga abinci akai, zama tayi ta zuba d'an kad'an, amma dad'in abincin yasa batasan Sanda ta k'ara ba, tayi mamakin yanda abincin nan yayi dad'i, kamar Ance ta d'ago ta gansa ya shigo falon, dasauri ta mik'e, kallonta yayi yace "matsoraciya kawai" ta Harare shi ta juya, "Kai kayi girkin" ya tsinkayi muryar ta tana tambayar sa, murmushi yayi yace "dake kika yi ko an gayamiki ke kad'ai kika iya girki" tayi murmushi tace "yayi dad'i bara naje gurin ummah" Shureim ya Harare ta yace "kinsan k'arfe nawa ne is around 2am fa" ta kalli agogon d'akin tace "gaskiya banji dad'in hanani zuwa dinner nan dakayi ba amma Babu komai yanzu Dai bani Wayata" yace "Aida kin mutu dase kiyi k'orafin acan kuma wayarki da tawa Duka suna d'akin ki ajiye, Aw Yawwa na tuna masoyinki ne fa ya kawo mana Hari" ta zaro ido tace "WA kenan" yace "Ali khan mana" tace "to Akan me zeyi hakan" Shureim yace "Wai kawai dan Yana kishin ke Mata tace, shysa ya shirya kashemu mu Duka ni bemasan takura min kawai kike ba" Sarauta tace "Allah sarki Ali khan shi yayi ne dan yana sona kaiko takura maka ma kawai Nike ko to gobe da safe zanje Nayo bailing d'inshi dakoma nawa ne ai me sonka ka soshi" daga Haka ta wuce Sama a fusace, ajiyar zuciya yayi yanajin Babu dad'i gaskiya baze biyema ummah ba gurin cikar burinta shikuma ya rasa tasa soyayyar, binta yayi abaya, Yana shiga ta juyo ta kallesa tace "almost 29miss calls from Shuwaiba kun had'u yau ne" ya girgiza Mata Kai shima yad'au ki tasa wayar yace "Nima Haka fa Dubi miss calls Haka dayawa ko Lpy" ya fad'a yana dialing d'in number, tayi ringing harta gaji ba'a d'aga ba, Sarauta ma takira Amma bata d'aga ba, kallon ta Shureim yayi yace "Allah sarki d'a'amun tayi fushi bara naje na ganta" Sarauta ta mik'e tace "Muje tare ko" Kai ya girgiza Mata yace "zanje ni kad'ai Idan ban dawo ba akwai kayanki acikin wardrobe d'innan dazaki sa gobe ga key kuma, Allah karki fito da Daren nan" daga Haka ya juya ya tafi ya barta nan tsaye, Haka kurum taji batajin barci ta hau online, Aiko nan sak'on ni suka fara shigowa, kusan mutane 7suka tambaye ta Ina taje yau Shuwaiba nata neman ta, nanfa taji hankalin ta yasoma tashi da kalar neman da Shuwaiba take Mata, harta k'agu Shureim ya dawo Allah, gurin 4am barci ya d'auke ta.






Cikin gida kuwa hankalin kowa ya tashi neman Shuwaiba akeyi sosai amma shuru Babu ita Babu Alamar ta, nanfa hankalin kowa ya tashi gashi ana kiran wayarta tana shiga amma bata picking, tuni y'an Sanda suka cika gidan, sosai ake namanta har around 4 ba'a ganta ba, kowa zaune yake a falon Jiki a sanyaye, sukuma y'an Sanda se y'an bincike² sukeyi, cak Shureim ya mik'e tare da nufar hanyar d'akin da Shuwaiba take matuk'ar so, domin abaya before suyi aure datazo cewa take itadai Idan Sunyi aure sunzo nan gidan to nan d'akin xasu dunga zama, Yana zuwa ya tura d'akin cak ya tsaya ganinta kwance ga wayar ta ajiye a gefen bed drower,dasauri ya k'arasa harze d'ora hannun sa akanta dpo yace "wait Mr billionaire please kasa, handgloves karka b'ata mana aiki, Shureim kamar bejin abunda ake fad'a ya amshi gloves d'in yasa, ya k'arasa gabanta tare da zama a gefen ta yasa hannunsa ajijiyar bayan wuyanta wanda indai mutum ba mutuwa yayi ba to za'aji tana motsi, cak Shureim ya tsaya tare dayin baya yasoma girgiza Kai, wasu irin zafafan hawaye suka zubo Akan fuskar sa, kowa dake d'akin cak ya tsaya domin har yanzu Babu wanda ya tabbatar da abunda yake gani, Dpo ya k'arasa tare da dubata, yaja white blanket d'in dake d'akin ya rufeta sannan ya juyo ya kallesu yace "sorry to say she's gone" sannan ya kalli abokan aikinsa yace "Akira tawagar binciken gawa yanzu"............






*R.I.P SHUWAIBA, ALLAH YASA KIN HUTA, DAMA AI ITA RAYUWAR K'ALILAN CE, WANNAN PAGE D'IN SADAUKAR WANE GA DUK WA'INDA SUKA TAB'A YIN RASHIN MUTUM ME ABUN BAN DARIYA A FUNNIES PERSON, NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN AGARE KU ALLAH YAJI K'ANSU YASA SUN HUTA*







*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰






@07064706167

💵 💴 *AKAN KUD'I* 💴 💵

(A poor lady story)


..... 9th July, 2023



*Story & writing*
*By*



@ *sherntee Ghayu*🥰🥰





🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS*




👑J. W. A👑


🅿.... *071 & 072*


*5 hours later*




Angama shirya gawar Shuwaiba inda ake jiran lokacin d'aurin auren yayi, da an d'aura auren se akaita, rayuwa kenan su Shuwaiba kuma cin d'a'amun ya k'are Allah yaji k'anki.





Se around 8:30 ta farka, tayi mamaki sosai ganin har lokacin Shureim be dawo ba, kome ya tsaya yi Oho, toilet ta shiga tayi wanka, tana zaune Kan mirror tana y'an shafe², tunani kala² yake zuwar Mata Idan tayi wannan se tayi wannan "Hum ai wannan Shureim d'in banzan ma rabuwa zanyi dashi can ta matse Mai, inba rainin wayo ba ace sewani lallab'a shi Nike amma abanza toze gani kuma nasan duk saboda Shuwaiba yake min hakan, kuma ta Allah ba tasa ba, be Isa ya had'ani da y'ar uwata ba saboda Shuwaiba y'ar yayar ummah ce, Ohh y'ar baiwar Allah tun shekaran jiya Babu abunda taci to kodai bata da lafiya ne, Allah sarki k'ilama neman da take min kenan, Anya ma ba jikin nata bane yayi tsanani shysa Shureim be dawo ba Kai Bari Dai Nayi sauri naje koma miye Naji" ta k'arashe tana saka doguwar rigar da Shureim ya kawo Mata, ba k'aramin kyau tayi Mata ba, blue black in color shysa ta amshi farar fatar ta sosai, irin sosai d'innan, ko breakfast bata tsaya yiba ta fice (dama kunsan Idan gidan Ku ana Hidima ko abinci baka

Please Login or Register in order to submit comment