Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dazamu RAYU" ya kalleta yace "har abada kenan" ta tsaya tana Kallon shi kafin ta kama k'ugu, shima yanda tayi yayi harda wani kama k'ugu Aiko nan take dariya ta kwace musu su biyun, wayar shi datayi ringing ne ya katse musu dariyar, "Mrs d'an mik'o min wayar" kai ta d'aga tare da nufar wayar, seda tad'anyi tsaki kafin tace "Shuwaiba" seda ya kalli yanayin fuskarta kafin yace "bani" yana d'agawa Sarauta ta juya zata fita, hannu yasa ya jawota, ahaka ya Gama wayar kafin ya kalleta yace "inane zakije bayan baki sanar min ba" ta d'aure face tace "mexan sanar ma" yace "na had'u kuwa" ta girgiza Kai, yace "magana zakiyi" tace "ni Dallah sakarni Ina ka wani had'u kabar masu Mata d'aya dai su had'u" daga Haka ta fice.





Tana zuwa ta soma shiri domin aranar takeso taje ta dawo, banki ta biya inda ta ciri kud'i kimanin 2 millions naira.





*Mahuta*




Dakyar da kwatance suka gano inda Layla take, gidan kad'ai Abun Kallo ne, gidane irin na k'asarnan gaban shi duk ya zaizaye, d'akunan cikin gidan kuwa duk se a hankali, Layla tayi matuk'ar Jin dad'in ganin Sarauta, a d'an d'akinta ta sauketa wanda daga d'an k'aramin gadon kara se k'asa dake d'akin danko suminti Babu, itama tana Sanye da wata t-shirt kod'add'a se zanin atamfa, abunda ba'a magana.





Zaune take Akan tabar mar da ta shimfid'a Mata, ga ruwa da fura da'aka kawo Mata, sun d'an soma tab'a hira kafin Sarauta tace "Layla meke faruwa ne haka, ya'akayi haka kisanar min mana" Layla tayi murmushin dayafi kuka ciwo tace "Humm rayuwa kenan Wai yau ni Layla mk me bulawus ce a wannan halin, tunda na taso rayuwata bansan miye rashi ko Babu ba, amma a yanzu nasani, bansan suwaye dangi ko ahali ba amma yanzu na sani, bansan fari ko bak'i ba amma yanzu na sani, hak'ik'a Nayarda Idan kaga Allah ya hanaka Abu to kawai ka hak'ura da abunnan ba alkhairin ka bane Nima Nagani da kud'ina nasiyama kaina wannan bala'in, Sarauta tun bayan aurena komai ya canza min, mijina Yana nuna min tsantsar soyayya da kulawa, bayan wani d'an lokaci Sega ciki, daga nan kuma seya zugeni da dad'in bakin na ajiye Aikin gidan TV danike, Aiko alokacin soyayya ta rufemin ido na ajiye Aikin, cikina yanata girma kulawa Nike samu Kota Ina, iyayena dakuma mijina, ana Haka kwatsam se iyayena sukayi hatsari wanda duk wanda ya gani yasan shirya shi akayi hakane kuwa domin shirya shi akayi, mijina shams shine wanda ya aikata komai, bayan iyayena sun mutu Nayi kuka sosai inda mijina shine wanda yake lallashina, duk y'an uwana dasuka zo gaisuwa haka nayita wulaqantasu domin Ina musu Kallon k'azamai saboda bansan sud'in su waye ba Sam iyayena basu nunamin cewa su dangina bane harsuka mutu, bayan komai ya Lafa, aka bani gadona, nanfa wata sabuwar kulawa ta k'ara b'ullowa, Allah yasani a lokacin Banida kowa se mijina dakuma d'an cikina mijina ya nemi na bashi kud'in nan domin yayi kasuwa Haka na d'auka na bashi yaso muyi rubutu akai amma nace ah ah, bayan wani lokaci na Haifi d'ana na miji inda yaci Sunan mahaifina Al-musbahu (Abba), ko arba'in banyi ba asirin shams ya tonu saka makon wa'inda sukayi Aikin sun biyoshi kud'i kuma be basu ba, Aiko suka tona mishi asiri, yanzu Dai maganar da ake shams na prison d'aurin rai da rai, y'an uwan mahaifina babu wanda ya kulani a cikin su, dakyar yayar mahiafiyata ta amshe ni nan ma danike zaune gidan ta ne" ta k'arashe tana fashewa da kuka me tsuma zuciya, Sarauta ta goge hawayen ta tace "kenan AKAN KUD'I ya'aikata haka" Layla ta d'aga Kai, Sarauta taja dogon numfashi tace "yanzu to Ina gida dakuma motar daya Bari" Layla tace "ana binshi bashine me yawa shysa gaba d'aya aka amshe komai" Sarauta tayi ajiyar zuciya tana k'ara jinjina ma wannan cin Amanar dakuma buwaya irin ta ubangiji, sunanan zaune suna fira dattijuwar matar tashi go, Layla ta mik'e tana sauke Mata damin hatsin dake kanta tace "Sannu da dawowa iyalle, gashi kuma kin tafi da yaro nasan yau kin gaji sosai" dattijuwar tace "Yama yi barci ai, ah ah bakuwa mukayi sannunki da zuwa maraba" Sarauta tace "Ina wuni ya aiki" dattijuwar tace "lafiya klau ya mutanen gidan" Sarauta tace "Alhmdll" iyalle tace "Aiko maza Kira Manniru yazo ya Kai barzi ayima bakuwa dambu" Layla tace "Tohm" tana yunkurun fita Abba yaronta ya farka Yana sa kuka, iyalle tace "dawo ki ji dawannan fitinannen Bari inje inkira Mannirun ai Yana gonarsu yahaya" daga Haka ta fice, Sarauta tace "kinga Layla sauri nike wallahi gashi munyi da Ummah bazan jima ba kinga gwara na wuce" Layla dake shayar da d'anta tace "aw Wai dama ba Kwana zakiyi ba" Sarauta ta zare ido tace "Kwana Dai to wallahi Hakanma dakyar aka barni, kawo babyn nagani" ta k'arashe tana amsar yaron daketa Kalleยฒ, around 4, suka tafi inda tabarma Layla kud'i kimanin 1m sannan ta Bama iyalle 500k, Wayyo Allah Layla harda kukan murna, hakama iyalle.





*JIDDA*





"Sannu ko ai semu tafi gida tunda Naji jikin naki yayi sauk'i kar hankalin Ummee ya tashi" Fawax ya fad'ama Shubai'a dake kwance Saman gadon asibitin, saboda numfashin ta daya fara seizing, kallon shi tayi kafin tayi mishi nuni da "shikenan dama ya Dace Muje gida ai dare yayi" Kamata yayi ta mik'e suka tafi a motar ta sukaje har gida, Yana yin parking ya soma k'ok'arin fita ta kama hannun shi tayi nuni da "dan Allah karka gayawa yayana da Ummee" FAWAZ yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace "Babu wanda ze sani kinji" nan ya temaka Mata suka shiga gidan a falo ya barta inda shikuma ya juya ya tafi zuciyar shi cike da tunani kalaยฒ.





"kinsan yanda hankali na ya tashi kuwa my daughter, Ina kikaje tun safe se yanzu" Ummee ta fad'a tana Kallon Shubai'a da tun d'azu take wani shareta, yanzu ma hakane mik'ewa tayi tare dayin hanyar shiga toilet, kafin Ummee tayi magana Sega Abiey ya shigo, "Shubai'a Ina kikaje tun safe" ko Kallon shi batayi ba tacigaba da abunda takeyi, hannu yasa ya kamo Mata hannu yace "my daughter" a fusace ta amshe hannun ta tashige bedroom d'in ta kullo, ya juya ya kalli Ummee itama ta mik'e ta fice, ajiyar zuciya yayi kafin shima ya fita.





"wash Allahna wallahi hankali na yagama kwanciya yanxu" Juwaira ta fad'a tana zama gefen su, su hud'une a falon, Hajjo Mubeena, hajja jumaima, Khaleesat se Juwaira, HAJJA MUBEENA tace "ai wallahi yarinyar nan datasan abunda zata iske Idan ta dawo da bazatayi marmarin dawowa ba" hajja jumaima tace "tabbas ma kuwa y'ar uwa seta gwammace bata San Shureim ba Arayuwar ta" Khaleesat tace "Yawwa my hajjos Haka Nike soo Allah ai harkarnan dole ma damu za'ayi koba Haka ba juwy" Juwaira tace " tabbas ma kuwa ai ni harna k'osama ta dawo wallahi" Haka suka cigaba da fira abunsu.





*KATSINA*






*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe*






@ *sherntee Ghayu* ๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜






@07064706167

๐Ÿ’ต ๐Ÿ’ด *AKAN KUD'I* ๐Ÿ’ด ๐Ÿ’ต

(A poor lady story)



....... 5th June, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* ๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜






๐Ÿ”” ๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* ๐Ÿ“š





๐Ÿ‘‘J. W. A๐Ÿ‘‘





๐Ÿ…ฟ...... *047 & 048*





*KATSINA*




*BAYAN SATI D'AYA*





Shiryeยฒn komawa kawai suke, yanzu ma zaune take itada ummah, ummah tace "wallahi gabana faduwa kawai yake" Sarauta tace "Nima Haka ummahna amma addua kawai zamuyi" Ummah tace "in sha Allah, amma yaushe Zaki kuma dawowa" Sarauta tayi murmushi tace "Nima bansaniba wallahi amma ummahna Aikin sani zan dawo Gare ki very soon" Ummah tayi murmushi tace "in sha Allah".




*washe gari*




"Ummah kiyi hak'uri kidena kuka kinji Wai miye na kukan" Shureim ya fad'a Yana kama hannun ta, ummah ta d'aga Kai tace "Allah ya tsareku ya kiyaye ku Allah ya bada sa'a" Shureim yayi murmushi Yana d'aga Kai yakama hannun Sarauta yace "Ummah mu zamu tafi" Ummah ta kuma binsu da addua har suka tafi, juyawa Shureim yayi ya kalli Maryam dake kuka ya girgiza Mata Kai sannan suka shiga motar suka tafi Airport.





"Wai kukan nan na miye ne Mrs dan Allah kiyi hak'uri mana kinji" tana sheshsheka tace "kawai ummah na" ya jawota jikinshi yace "shikenan to kiyi hak'uri, ai Zaki dunga zuwa kina ganin ta ko" Sarauta ta d'ago ta kalleshi tace "Dagaske" yayi murmushi ya d'aga Kai, tayi murmushi itama ta rungumeshi, a hankali barci ya soma d'aukar ta, seda yaga barcin nata yayi nisa sannan ya goge Mata hawayen fuskar ta, ya zura ma fuskarta ido kallonta yake sosai, kafin ya gyara Mata kwanciyar sannan ya fiddo wayar shi yasoma d'aukar su pix, kallon pix d'in yayi yanda yayi kyau sosai.





*JIDDA*





"Oyoyo Oyoyo gata gata" Sarauta ta fad'a tana rungume Shubai'a, itama rungumeta tayi tana murna sosai, Ummee ma tayi farin cikin dawowar su lafiya.





*At night*




"Ummee Bari inje b'angaren can zan d'auko kayana gobe zan koma gida" Ummee tace "Kai amma Naji dad'i, shikenan tashi Kije kinji" sarauta ta mik'e ta kama hannun Shubai'a tace "zomuje ki rakani" Shubai'a ta mik'e suka tafi.





"lafiya Dai" Sarauta ta tambayi Shubai'a dataga ta rik'e Kai, Shubai'a ta duk'a tana kama kanta, dasauri Sarauta ta tareta tare da cewa "Subhanallah Sannu tashi mu k'arasa ciki ki kwanta" shuru kuma tad'anyi tana tunanin ranar dataga Shureim ya taho amma kuma shima ya duk'e be iya tashi ba hasalima daga bisani juyawa yayi. Tunani take kalaยฒ kafin ta kama Shubai'a ta maidata part d'in su. Koda Ummee ta tambayeta lafiya cewa tayi lafiya klau amma zata Aika d'aya daga cikin maid's d'in gidan su amso Mata.





*washe gari*




"Sarauta inajin ki ajikina tamkar yarinyar Dana Haifa da cikina, please kiyi hak'uri ki zauna lafiya da mijin ki kinji banason Inji wata hayaniya, Kece Babba agidan, duk da kasan cewar Kece me k'ananan shekaru acikin su amma nasan kinfi su hankali dan Allah a kiyaye" Sarauta ta d'aga Kai tace "in sha Allah Ummee" lek'owa yayi tare da cewa "Inafa da abunyi" Sarauta tace "to katafi mana dama ai bakai ka kawoni ba ko konace maka bansan hanya bane" Shureim ya Ida shigowa yace "wallahi Ummee yarinyar nan bazata canza Hali ba inaji fa kina Mata fad'a amma Babu abunda ya sauya" Ummee ta Harare shi tace "ashe lab'e kuma ka koma yi" ya girgiza Kai saboda kunya ya juya Yana fad'in, "naxo shigowa ne Naji fa" Ummee ta girgiza Kai tace "tashi kuje kinji yarinya ta" Sarauta ta mik'e ta fita har bakin motar Ummee ta rakata kafin ita kuma ta koma ciki, to kamar dai yanda kuka sani a motar ma seda aka buga drama kafin aka k'arasa gidan, kaf cikin matan nashi Babu wadda taji dawowar Sarauta, itama bata damu dasu sani ba ta wuce ciki.




A ranar da dare yabi kowaccen su yace yanason ganin su a falo gobe da safe around 9:00am.





*Washe gari*




*At 9:00am*




Zaune yake a falon inda yasha adonshi cikin Riga t-shirt fara da bak'in wando se farin takalmi bawata shiga yayi ta azo agani baa amma ya had'u, yananan zaune Sega Juwaira da Khaleesat sun sauko Sanye cikin shigar su ta alfarma Ansha alkyabbar nan kamar y'ay'an sarakuna, Sunyi kyau sosai, Kan 3seater suka zauna su biyun kafin Khaleesat tace "morning my handsome" ya d'aga Kai yayi murmushi yace "morning my beautiful wife" tayi murmushi tace "what's amazing name, thanks babe" Juwaira taji wani k'ududun bak'in ciki ya tsaya Mata, kafin tace "morning my hero" yace "morning my queen" tayi dariya tace "thanks for the special name dear" kafin yayi magana Sega Shuwaiba ta sauko itama Sanye cikin shiga irin ta alfarma, 1seater ta zauna kafin ta kalleshi tace "morning my billionaire husband" ya kalleta itamma yace "morning Mrs billionaire" tayi dariya tace "and billionaires mother in sha Allah" ya d'aga Mata Kai, almost 10mins later suka soma Jin k'arar takun takalmi a nutse, kwass! kwass!!kwasss!!!, lokaci d'aya duk suka d'ago domin Kallon abunda ke tunkaro su, Aikuwa sungani saboda sunga uwar gida sarautar Mata Idan Babu ita Babu gida, Sanye take cikin wani leshi d'an ubansu, tayi simple makeup, sannan ta d'auki wata dank'areriyar alkyaba ke adon stones d'in diamond tasa, ba k'aramin kyau tayi ba, fad'in kyan jarumar nan baya misaltuwa, ba iya Shureim ba harta matan dake gurin kasa d'auke idonsu sukayi akanta, k'arasowa tayi fuskarta d'auke da annuri dakuma kwarjini na musamman akai, ayau shi kanshi Shureim ji yake Babu abunda zata Sanya shi beyiba balle kuma 3kishiyoyinta, a Kan kujerar dayake zaune taje ta zauna tare da d'ora hannun ta Saman Nashi tace "shine daga kace Nayi wanka zaka jirani kawai seka taho" ta fad'a cike da tsantsar shagwab'a, kallon ta yake cike da mamakin yaushe ma yaje d'akinta balle har sukayi hakan, ta kashe mishi ido tace "forget about it my life, morning my dear happiness my husband my everything and anything" yayi murmushi shima ya kama hannun ta yace "morning my happiness princess, and sorry for not waiting you" ya fad'a Yana d'an Kama kunnen shi, tayi murmushi tace "aiya wuce my Mr, just kawai Nayi kewar Kane kasan banason kana nesa dani" yayi murmushi dan ya lura Idan ya biyema Sarauta setasa y'an uwanshi su hadiyi zuciya duk su mutu, kallon su yayi kafin ya soma cewa "Asslamu alaikum, Shuwaiba, Khaleesat, Juwaira, dakuma ke, dukkan ku Mata nane, tabbas Inada arziki ba d'an k'arami ba amma maganar gaskiya Idan har zaku cigaba dawannan zaman to kuwa tabbas very soon zamu talauce, Sarai nasan kunsan banason rigima amma kuyi ta Abu hakan nan, wallahi ko kwanaki nama rasa mezanyi muku ne kawai da'ace Nayi magana a lokacin nan Toh da Babu wacce zan Bari acikin ku, dandai kawai akwai wacce bazan iya rayuwa Babu ita bane shysa ban aikata hakan ba amma please kundai ga rok'on ku nikeyi ko to dan Allah karku sake, kuhad'a kanku mana ku zauna lafiya Nima hankali na ya kwanta kuma Haka, kubi y'ar uwar ku tunda Dai itace Babba a gidannan please ku zauna lafiya" Yana kaiwa nan yayi shuru dukkan su Yana Kallon fuskar su kamar daga sama sukaji Shuwaiba tace "yaya kiyi hak'uri Akan abunda ya faru a baya, tabbas munada laifi saboda mune muka tsokane ki, Nidai AGASKIYA da ace arzikin Mr billionaire ya karye gwara kawai mu zauna lafiya" Sarauta tayi murmushi tace "Babu komai yaya Shuwaiba and Nima kiyi hak'uri Akan abunda ya faru bada niyya Nayi ba" Shureim ya kalli Shuwaiba fuskar shi d'auke da murmushi yace "that's my wife Shuwaiba thanks alot Mrs billionaire" tayi murmushi tace "anything for my billionaire husband" Juwaira ta juya suka had'a ido da Khaleesat kafin suka had'a baki gurin cewa "in sha Allah zamu kiyaye" suka k'arashe sunama Sarauta Kallon Banza, tayi murmushi azuciyarta tace "habawa zakuga yanda akeyi ne tsinannu marasa mutunci" Sarauta taja dogon numfashi kafin ta mik'e tsaye tana k'ara gyara alkyabbar jikinta tace "basena gabatar da kaina tunda Inada tabbacin kunsan Wacece ni, hakane ko, ta k'arashe tana Kallon Juwaira da Khaleesat," tab'e baki sukayi, taci gaba dacewa "anywere, kafin na fara sanar muku da abunda Nayi niyya Ina buk'atar na tambaye ku wani Abu, Ince dai kunacin abincin house maid ko?" duk suka kalli juna suka d'aga Kai, tace "good to acikin gidan nan akwai ranaku biyu da kowacce acikin mu zata dunga kulawa da gidan, acikin kwanaki na guda biyu Babu wata baiwa ko house maid dazata yi ma mijina aiki ba, akwai house maid guda biyu Dana d'auka sune zasu dunga yin Aikin gidan nan akwana biyuna Ina fatan kun fahimta" Juwaira ta mik'e ta buga tsaki kafin ta finciko hannun Khaleesat suka haura Sama, Sarauta tayi murmushi azuciyarta tace "dawannan bak'in halin Naku zan koreku matsiyata" afili kuma ta koma gefen Shureim tace "karka damu kanka kaji mijina" yayi murmushi yace "Aiga Shuwaiba nan am proud of her" Shuwaiba tayi dariya tace "sorry sir but yakamata fa Muje muci abinci ni wallahi yunwa nikeji" ( *itadai Shuwaibar nan na lura indai da girki toba matsala*) Shureim yasa filo ya jefata dagudu ta k'arasa dining area har angama breakfast ta zauna kuwa tahau ci.





Nanfa Mrs tafara rarraba idanu mik'ewa tayi daniyyar barin wajen domin gudun tambayoyin dazeyi Mata, Aiko caraf ya rik'eta tare da jawota ta dawo ta zauna, "gayamin duk hakan miye sababbin tsareยฒ dawasu dokoki sannan kuma sabuwar d'abi'a" ya tambaya Yana fuskantar ta, kameยฒ ta fara kafin tace "to ai maganar gaskiya ake" ya d'aga Mata gira yace "kenan da gaske kina sona" Sarauta ta harare shi tace "kaga dan Allah ka Bari banaso miye haka" ya kalleta yace "wakike d'aure mawa" ba tace mishi komai ba, dakyar tasamu ta kubce mishi ta wuce d'aki domin raba kanta da kayan jikinta dan ba sabonta bane Jinta takeyi duk a takure.





*At night*





"nifa Bangane meke faruwa ba, wai ina abincin mu yake ne naga Babu komai Akan dining d'in" Khaleesat ta fad'a tana Kallon Juwaira dake kwance tana tunanin yanda zata bar gidan taje America gurin boss d'inta, itama mik'ewa tayi tace "Nima Abun yafara bani mamaki tun breakfast fa, Babu abunda aka kuma dafawa a gidan nan" Khaleesat tace "Aiko tashi zakiyi Muje muga wainar da'ake tonawa a gidannan" Juwaira ta mik'e tace "Aikuwa dai Muje to"





"nifa wallahi sekinyi hak'uri dani, nifa indai harkar cine to ba'a barni abaya ba" Shuwaiba ta fad'a tana d'and'ana girkin da Sarauta tayi, Sarauta tayi murmushi tana cigaba da had'a girkin ta, tace "Aikuwa, amma fa yakamata ki rage wannan yawan cin naki" Shuwaiba tace "Wa, inaa *sisyna* barni naci aduniya ake ci alahira sedai kiji kin k'oshi" Sarauta tayi dariya tace "kai yaya Shuwaiba alahirar" Shuwaiba tace "kwarai ma kuwa, ai alahira sedai kawai kiji kin k'oshi Babu wani harkar tauneยฒ, ko ciyeยฒ" Sarauta ta tuntsire da dariya kafin tayi magana sukaji shigowar su Khaleesat, Juwaira tace "ke Ina abincin mu" gaba d'aya Babu wacce ta tanka musu, Khaleesat tace "daku fa muke" Sarauta tayi tsaki tace "yayata Muje ko" Shuwaiba tayi gaba zata wuce, Juwaira ta rik'eta tace "ke Dallah bakuji ne" Shuwaiba tace "ke me k'irar b'akar kaza sakeni konayi k'asaยฒ dake Anan gurin Banza kawai mayya" Khaleesat tayi dariya tace "ke akwai ma wacce ta kaiki maita ne iyeh jaka kawai" Shuwaiba zatayi magana Sarauta ta rigata da cewa "tun d'azu maid's d'innan sukayi jiranku kuzo ku sanar musu da abinda zakuci su dafa muku amma Baku fito ba, dan haka nace musu su tafi ai Ina fatan kun gane, yayata Amatsayin ki name hankali dan Allah kidena biyema mental disorders" daga Haka ta kama hannun Shuwaiba dake dariya suka fice, Khaleesat tace "jakar ubancan kice yau akwai bura'uba" Juwaira tace "Mekike ci nabaka na falling down Kibarni dasu damu sukeyi Muje kawai" daga Haka suma suka wuce ciki.






Kwance Sarauta take Saman gadon ta lumshe idonta, seka rantse barci take amma idonta biyu, tunani kurum take wannan na koraar wannan, "meyasa sir Shureim yakasa shiga b'angaren nan, meyasa Shubai'a ta kasa k'arasawa, meyasa Ummee batason maganar da anfara se kanta yasoma ciwo, ya'ilahi duk miye hakan, yaza'ayi d'a ya manta da uwarshi na wannan tsawon lokacin, shin ko Mamu tayi musu wani Abune Kai Ina, nasani Babu abunda Mamu zatayi musu Kodama tayi itad'in ai uwace bekammata Suyi hakaba, duk miye wannan ne daga Ina Matsalar ta b'ullo ne" ta k'arashe tunanin tana mik'ewa zaune, "Aikin asiri ko tsafi" zuciyarta ta bata amsa "Aikin asiri kuma, Aiko to indai hakane kenan itama Shubai'a asiri ne akayi Mata bata magana, kenan itama Mamu asirin akayi Mata, to waye ya aikata hakan, Aikuwa indai Dagaske ne asirin ne to kuwa shigar Shubai'a gurin nan ze karya Mata nata asirin, tabbas hakane Idan harta shiga zata koma tanayin magana kenan kamar kowa" wani murmushi ne ya kwacewa Sarauta tace "Wai Wayaga madam Shubai'a ana magana zabira kenan" tayi dariya tare da saukowa tashi ga toilet ta d'auro alwala ta kabbara sallah, inda gaba d'aya rok'onta Akan Allah ya yarda Shubai'a tayi magana ne Aikuwa dataji dad'i sosai.





*Washe gari*





*karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labarine danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* ๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜






@ 07064706167

๐Ÿ’ต ๐Ÿ’ด *AKAN KUD'I* ๐Ÿ’ด ๐Ÿ’ต

(A poor lady story)


...... 6th June, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* ๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜






๐Ÿ”” ๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* ๐Ÿ“š





๐Ÿ‘‘J. W. A๐Ÿ‘‘





๐Ÿ…ฟ....... *049 & 050*





*washe gari*




Yau Sarauta ta tashi cike da farin ciki da murnar abunda ta Kwana dashi jiya, a yau taci niyyar Kota halin k'aka' se Shubai'a ta shiga b'angaren Mamu.





"Barka da safiya" Sarauta ta fad'a tana k'ok'arin zama a falon, Shureim yace "Barka da safiya, kin tashi lafiya" ta d'aga Mai Kai tace "Alhmdll" kafin tace "yaya Shureim alfarma Nike son nema" Shureim ya kalleta yayi murmushi yace "Ina kuma kike son zuwa" ta zare ido tace "Kai ya'akayi kasani" Shureim ya ajiye mujallar hannunshi ya fuskanceta yace "ai indai Naji kin wani kwantar dakai to nasan buk'atar ki" ta duk'ar dakai tace "Uhm dama dan Allah akwai abunda na manta a gida inason na koma na d'auko dan Allah anjima naje" Shureim ya girgiza Kai yace "ah ah ki Kira Ummee ko kiyima Shubai'a text se abama driver ya kawo miki" ta girgiza Kai tace "ah ah sirrine fa" yace toni zan amso miki ai kinjini" Sarauta ta Harare shi kafin tace "Yawwa dama a b'angaren nan na ajiye kuma Babu wanda yasan inda na ajiye sedai Idan zaka rakani se Muje" yad'an kalleta yace "shikenan sekin dawo amma Idan kika Jima" yayi kwata ya jefa Mata key d'in motar shi, tsalle tayi ta mik'e tana Mai godiya, d'akinta ta wuce ta shirya Yana nan zaune ta fito hannun ta rik'e da key d'in motar, Shuwaiba ta hango kitchen tana zuba sanwa, tayi dariya ta k'arasa kitchen d'in tana cewa "madam ci kenan" Shuwaiba ta juyo tayi dariya tace "iya abunda Allah ya rubuta maka zaka ci Anan duniya Aiko kinga gwara naci ko" Sarauta tace "to Naji Ina Kwana" Shuwaiba tace "mun tashi lafiya, Ina zuwa ne bayan Naga yau ba'a aiki" Sarauta tace "Abu na manta gida zan d'auko" Shuwaiba tace "adawo lafiya,

Please Login or Register in order to submit comment