Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci sosai😄)





GURIN d'aurin auren ya cika sosai, y'an kasuwa, sarakuna, malaman Fawax na k'asashe daban daban, Kai mutane dai ba'a magana, Anan akai d'aurin auren ummah da Abba taheer, Shubai'a da Fawax, sannan akayi sanarwar auren Hisham da Maryam, ana gamawa kuma aka hau sallatar gawar Shuwaiba, angama sallar anata hada hadar kaita, Shureim shine yazo gaba domin kamawa asa a mota, Aiko kamar Ance kalli gefen ka.





Mamaki da tsoro ne suka hud'un mata lokaci d'aya, dasauri ta juya domin ganin ta k'arya ta tunanin ta, hango Shureim a gefen gawar tsaye yasa ta saki ajiyar zuciya, ta hanga ta hango Abba, ta hango Hisham, Fawax, Abba taheer, Khameel dadai kowa da kowa, kafin ta k'arasa gurin Shureim ya tare ta gaskiya Sam beso zuwan ta gurin nan ba yaso ace se ankai Shuwaiba makwancin ta sannan amma Kash, "waye ya rasu" girgiza Mata Kai yayi yana d'auke hawayen sa dasuka taho, Rass taji gabanta ya fad'i "Muje ciki" ta girgiza Kai wasu irin hawaye na zubar Mata tace "ka gayamin waye ya mutu" bece Mata komai ba ya jata cikin main falon, kowa na zaune har lokacin kuka kawai suke, kallon kowa Sarauta tayi kafin tace "Ummah waye ya mutu, dan Allah Ummee ku gayamin, HAJJA kukan me kikeyi ne duk jarumai ki, Maryam dan Allah duk ku dakata sa kukan nan ku sanar min abunda ke faruwa Shureim waye ne ya mutu" ta k'arashe tana fashewa da kuka, Shubai'a tace "Shuwaiba... Shuwaiba ce.... Itace.. Tamu....." bata k'arasa ba wani kukan ya k'ara kwace Mata Kai Sarauta ta soma girgizawa tana Kallon Shureim "ahahh Shuwaiba dai, Sam wannan k'arya ce nasani Shuwaiba tana nan kawai kuna b'oye min wanda ya mutu ne, Shureim dan Allah ka k'arya ta maganar Shubai'a kace min y'ar uwata bata mutu ba kace y'ar yayar ummah nanan bata mutu ba Ahah nasani tana nan tana nan ko Shureim" ta k'arashe tana kama hannun sa, zare hannun sa yayi tare da girgiza Mata Kai, wata uwar k'ara tayi kafin ta zube k'asa sumamma, Shureim har yayi kanta wani eacort ya shigo ya shaidamai dashi ake jira, nan yabi bayan escort d'in suka tafi, sukuma sukayi kanta dakyar aka samu ta farka amma ganin halin datake ciki yasa Doctor najwa tayi Mata allurar barci.





Shureim dakansa ya kama Kan Shuwaiba aka Sata acikin k'abarin ta, yayi kuka iya kuka Babu abunda yake tunawa face kalamanta "iya abincin da Allah ya tsaga maka zakaci aduniya kawai kake ci, Haba mana dan Allah kubar ni naci aduniya fa ake ci alahira sedai kaji ka k'oshi,..... Uhm Nidai na yafe ma kowa ma" irin wa'innan maganganun bata kuwa sukadai yake tunawa yayi kuka sosai kafin suka dawo gida.





Sakamakon rasuwar daakai yasa Babu wata Hidima da akeyi gidan yayi tsit ta ko'ina se y'an Sanda dasuke Aikin su, wanda zuwa wannan lokacin kowa dake cikin gidan Dpo yayi Mai tambayoyi



Yanzu ma kowa zaune yake afalon harsun gaji dayin kukan wasu sun hak'ura wasu kuma sun koma sharar kwalla Allah sarki rayuwa, wanda ya mutu fa shi akayi ma mutuwa allay yasa mu Dace, ajiyar zuciya Dpo yayi yace "a iya binciken da mukayi na gano wata madafa guda d'aya wanda acikin amsar Kowannen ku ya bayyana min irin yanda mariganyiya take neman Mrs Sarauta, wannan Abun tambaya ne akai, please koxan iya ganin Mrs Sarauta" Shureim ya girgiza Kai yace "tana barci" Dpo yayi dariya yace "nice, Wato aikinta yaci tayi nasara shine Har lokacin barci ta samu wow please Mr Sarauta ka tado mana ita inyaso taida barcin a magark'ama" Shureim yayi shuru domin zuwa yanzu yagama fahimtar wannan d'an sandan kodai turo sa akayi kokuma nufin wulak'anta Sarauta yakeyi, guri ya samu ya zauna, Dpo yace "magna Nike sir" Shureim yace "nagaya maka barci take ko ka'iya jira ta farka" daga Haka ya tashi ya nufi hanyar d'akin da take ciki.





Zaune ya tarar da'ita a Saman gadon kamar mahaukaciiya se uban kuka take, HAR yanzu ganin Abun take kamar imagination ne kawai, kusa da'ita ya zauna inda yasoma bata baki da nasihohi Akan dukkan merai mamaci ne, "Haba mana Sam hakan bata Dace ba, a yanzu Shuwaiba adduar ki kawai take buk'ata Ammerh, kidena kuka man, bazataji dad'i ba hasalima Idan kikayi Mata addua seyafi tunaki Akan kowa please Ammerh kiyi shuru kinji nasan daba Shuwaiba bace ta mutu da zuwa yanzu tasa kowa dariya agidan nan, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un " ya ka Yana dafe Kansa, hak'ik'a gaskiya Shureim ya fad'a, ajiyar zuciya tayi ta kalleshi, mik'ewa tayi ta shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta gyara gashinta ta fito ta kalleshi d'an murmushi tayi mai inda take Jin zuciyarta kamar zatayi tsalle ta fito waje, "Muje k'asa" shine kurum abunda ta furta murya a dusashe, mik'ewa yayi ya kama hannun ta suka fita,




Tambayoyin da Dpo yake Mata sun fara isar ta fa, "atak'aice dai kenan Mrs Sarauta, bayan kin had'u da'ita agurin mijinku shine kikaji kishinta ya taso miki, hakan ne yasa kika fita daga d'akin, ita kuma mamaciyar daneman zaman lafiya hakan ne yasa ta biyoki domin baki hak'uri ke kuma kikayi amfani da wannan damar gurin yimata bara ana Akan rayuwar ta, a iya tunani na alokacin dakikayi Mata barazanar Sam Abun be dame ta ba, se bayan Kwana biyun nan taji Abun ya dameta hakan ne yasa take neman ki ruwa a jallo domin ganin kun sasanta ta baki hak'uri, aduk inda ta duba bata same kiba hakan ne yasa tayo gida domin ganin ko kinanan, taci sa'ar iske ki, ke kuma se kikayi amfani da wannan damar gurin ganin bayanta" Sarauta ta mik'e tace "ya'isa, ya'isa Haka Dpo duk miye wannan ne, Akan meyasa zan kashe Shuwaiba, y'ar yayar ummah ce fa, mijin Banza zan iya barmata Shureim da naso, kuma Idan ni na kashe ta zan b'oye ne, karka manta I'm trillioneire zan iya rufema kowa baki kuma a rufe case d'in, kuma meyasa seni dakaina zan aikata hakan meyasa zan wahalar dakaina Akai, Sam baka Dace da Aikin d'an Sanda ba driver ya Dace dakai kodai road safety tirr da wannan tunanin naka" Dpo yace "kinyi amfani da damar kine akanta, Wato kinayin duk abunda kika ga dama kenan saboda kinada kud'i ne ko miye to Bari kiji Babu ruwana da kud'in ki ko matsayin ki Kece wacce Muke zargi dan Haka dole mutafi dake station" Sarauta tace "Akan wane dalilin, kun samu photo nane ko kuma zanan yatsuna" Dpo yace "kinsan za'ayi amfani dawannan hakan yasa kika goge duk wata sheda" nanfa aka fara ja'inja da Dpo da Sarauta.




Tsaki Shureim yayi tare dayin hanyar waje, bayason yasa baki domin karya shigarmai aiki, Yana fita ya Kira shugaban masu tsoron sa, yace "kaje station ka shigar da k'ara Akan Dpo sannan azo atafi dashi kuma ka Gayama shugaban y'an Sanda ya turomin jajirtaccen d'an Sanda daze iyayin Aikin nan" escort d'i shi yace "Ohk sir, but laifin me Dpo yayi" Shureim yace "da Alama yasan wani Abu Akan kisan nan Idan an kulle sa kayi bailing d'in sa ka kaisa sabon company na da aka fara ginawa Idan kayi komai ka kirani kurum" daga Haka ya koma ciki,




Yana shiga ya samu guri ya zauna, HAR lokacin Abu d'aya ake, da Alama dai Dpo nasan dole Sarauta seta amsa laifin da tayi, suna cikin hakan wayar sa tayi ringing sak'on an dakatar dashine yafara isarmai, yana ajiye wayar kuma Sega y'an Sanda sun shigo tare dayin arresting d'in shi, Sarauta tayimai Kallon ka Raina kanka tace "wannan ba komai bane ba, sema nasa an koreka Aikin ba panshow ba graduty mtsww" bece Mata komai ba suka tafi dashi,kallon Shureim Sarauta tayi tana share hawayen ta tace "Nagode".





Cikin d'an lokaci Sega sabon sefeta ya k'araso, nan fa aka cigaba da binciken, yagama had'a duk wasu bayanai yanzu bayanin Sarauta yake d'auka, "Ammm sorry Mrs Sarauta zakiga Kamar na katse ki ko, dafarko kince rabon ki da'ita tunda kuka had'u a d'akin mijinku yanzu kuma kince taje d'akin ki, kafin ku had'u a d'akin mijin Naku ne tazo kokuwa bayan kun had'u" Sarauta tace "bayan mun had'u ne, na Gaya maka tana shiga ni nafita, kuma kawai senaga ta biyoni" Speter yace "koxan iya sanin abunda ya had'a ku a d'akin" Sarauta tace "cewa tayi dani Idanma dan Shureim ne aiseta barmin shi Duka amma na rik'e Mata shi Amana, kasantuwar banason hirar yasa kawai na sauya maganar da Muje muci abinci amma Abun mamakin seta cemin uhuhn ta k'oshi, wallahi bani na kashe ta ba Akan mene zan kashe y'ar uwata tun jiya fa Ina tare da Shureim ko sau d'aya bamu rabu ba Allah ne shedata ni ban kashe ta ba" ta k'arashe tana fashewa da kuka, Shureim ya rik'e ta yace "sorry Mrs kinji" Speter yace "to amma a bayanan sir Shureim ya bayyana mana cewa around 7:40 bayanan yabar gidan ke kuma kina ciki kina barci, awannan d'an lokacin kuma Shuwaiba ta dawo gida, kuma cikin wannan d'an lokacin ne aka kashe ta kuma masu gadin sun tabbatar mana da Babu wanda ya shigo masarautar nan bayan ita" Sarauta tace "to amma kuma be bayyana maka cewa mun samu accident bane wanda hakan yasa na fita a hayyacina kuma be bayyana maka cewa a inda yabar ni Anan ya sameni ba ko be bayyana maka cewa nisam banma San a inda Nike ba saboda totally ban tab'a shiga wancan building d'in ba, meyasa Wai seni za'a zarga" Speter yace "wannan gaskiya ne to amma ko kinsan da filo akasa aka danne ta harta mutu" tace "Taya za'ayi nasan hakan bayan bani na kashe ta ba, Idan dan kishi ne Aiga Khaleesat nan ko meyasa ita ban kashe ta ba seta kusa dani" Speter yace "may be kinyi amfani da damar kine na ganin ta yarda dake ko" Sarauta ta girgiza Kai tace "sakaran tunani Sam bazan iya kisan rai ba" wayar Shureim ce tayi ringing, yana d'agawa ya kalli Speter yace "Minti 2 please" Speter ya d'aga Mai Kai tare da tashi suka fita tare.





"Hajja wallahi tsoro Nike ji karfa a gano gaskiya" Hajja jumaima dake zufa tace "karki damu Babu wanda ze gano wata gaskiya" Hajja Mubeena tace "yarinyar kirki maza jeki kar wani ya ankare kinji" Kai Khaleesat ta d'aga musu ta tafi, HAJJA MUBEENA ta kalli k'awar ta tace "karfa reshe ya juye da mujiya Muda mukayi Abun nan domin ya koma Kan Sarauta amma gaba d'aya Yana son ya juye" Hajja jumaima tace "Nima gaskiya nagama tsorata akai kin gane Nidai gaskiya tafiya zanyi koma me kenan ma had'u daga baya" Hajja Mubeena tace "ki tafi Ina, ai kafata k'afar ki wallahi gwara mu tafi tare" nan fa suka had'a kudaden su suka d'auki mota d'aya suka fita daga gidan, Babu wanda ya ankare da fitar su saboda halin da ake ciki.




"gayamin miye hadin ka da case d'innan kuma waye yasa ka Akan kayi bincike Akan Sarauta" Shureim ya tambaya Yana had'a lantarkin dake hannun sa, Kai Dpo ya girgiza yace "na rantse bansan komai ba, kud'i kawai aka bani akace Kota halin yayane na d'ora Mata wannan sharrin" Speter yace "waye ya baka kud'in" Dpo yace "dan Allah ka tsaya karka kashe ni zan fad'a, wata yarinya ce da wasu samari guda biyu" Shureim yace "kasan ta" Dpo yace "matar ka Khaleesat wallahi itace amma bansan su waye wannan mazan ba itama dan Nayi bincike agidan ne nagane ta dan Allah ku sake ni natuba wallahi, Inada yara sannan ga iyaye na ku temaka" Shureim ya saki wayo yin dake hannun sa tare da cewa "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Speter Bari naje naxo da'ita kafin na dawo, ku Kai wannan munafukin station ku shigar da rahoton abunda ya aikata" duk irin yanda Dpo ke rokon Shureim amma ko Kallon sa beyi ba, Haka suka tafi dashi shi kuma ya koma gida domin d'auko Khaleesat.





Hankalin Khaleesat ba k'aramin tashi yayi ba sakamakon ganin su Hajja basanan to Ina sukaje, ta Kira nombovin su amma switch off, hankalin ta duk ya tashi, my d'inta harta soma zargin ko akwai wani Abu, Khaleesat na zaune tana k'ara trying d'in number su Hajja taji anzauna kusa da'ita, dasauri ta juya ta kalleshi "Brother Shureim" murmushi yayi Mata yace "Muje na baki wata bazata" tace "bazata kuma awannan ranar" ya d'aga Mata gira ya kama hannun ta suka fita, shike driving d'in amma Khaleesat ita ke zufa hankalin ta ya matuk'ar tashi Dagaske,




*After some minutes*




Zuwa wannan lokacin kuwa Khaleesat harta sauya kamanni, gashin kanta Shureim ya kama yace "kinji haushin rayuwar ki Banza, yanzu zamuje gida kuma dole ki amsa wannan laifin naki aikinji ni ko" Khaleesat tace "wallahi ba laifina bane ka tsaya ka..." Speter yace "shuru munafuka tashi mu tafi" Shureim ya fice yayi gaba, itakuma aka samata hangup aka tafi da'ita.




Kowa a falon yayi jugum har yanzu mutuwar bata sake su ba, Sunanan zaune bame cema kowa komai, kawai seji sukayi an shigo, kowa yayi mamakin ganin Khaleesat da hangup gakuma jini a fuskarta, gakuma Shureim a gefe ga tawagar y'an Sanda, cike da mamaki kowa ya mik'e, Sirayya tace "Innalillahi mezan gani haka kuma y'ar marainiyar Allah kukayi ma Haka, me tayi muku kuma" Shureim ya kalli Khaleesat yace "yi bayani" cikin kuka take cewa "saboda yanda su Hajja suka tsani Sarauta ne yasa sukayo hayan y'an daba domin su kashe Shuwaiba kuma su d'ora mata laifi, sune kuma sukayi ma Abba Shureim kurciya yabar garin nan, sannan sune suka raba tsakanin Mamu da dangin ta baki d'aya, duk abunda ya faru sune sila sune ma suka Sanya ma Sarauta maganin abortion domin a tunanin su tanada cikine sune sukayi komai "Shureim yace" cigaba ko kinkai k'arshe ne" ta share hawayen ta tace "Nima Ina goya musu baya Akan komai saboda na tsani Sarauta, amma wallahi sharrin shed'an ne dan Allah ku yafe..." bata k'arasa ba taji anwanke ta da Mari sosai ummah Sirayya ke kuka tana bugun ta, "azzaluma kin cuceni Kinci Amana ta Hajja ta b'ata miki tarbiyya kamar yanda ta b'ata min tawa, Khaleesat yanzu rai kika kashe dama, ranma kuma na y'ar uwar ki kawai kuma domin ki d'aurama y'ar uwar ki laifin, kin bani kunya Allah ya'isa na bazan yafe muku ba azzalumai kawai mugaye" Ummah ta tashi ta rik'e ta, dakyar suka hanata dugun jakan da takema Khaleesat, wani d'an Sanda ne yashigo tare da cewa "Ranka shi dad'e ankamo su Duka" Speter ya d'aga Kai ya kalli Shureim yace "mungode sosai y'allabai, zamuje da wa'innan sukuma sauran mun baza jami'ai domin Nemo su, Allah yaji k'anta yasa ta huta sukuma wa'innan xasu amshi hukunci daidai da abunda suka aikata" daga haka aka sa Khaleesat gaba aka fita da'ita, nanfa gida ya k'ara rudewa kowa kuka yake Babu Me rarrashin wani acikin su.





*7days later*




Anyi neman su Hajja har angama amma Babu ko labarin su, itakuma Khaleesat anyanke Mata zaman yari na har abada, sukuma mazan dama y'an fashine hukunci kisa kawai aka yanke musu inda har lokacin aka baza jami'ai domin Nemo su





Sirayya kuwa ko 5 ba'ayi ba ta had'a kayan ta takoma gidan mijinta, zuwa wannan lokacin kuwa mutuwar ta soma bin jikin su, sedai kuma wani Abun burgewa y'an uwan sarki sun k'ara had'a Kai sosai musamman Sirayya da Safiyatu da Abun yafi tab'awa, duk da zaman makoki ake amma suna kulawa da junan su sosai, Sirayya har k'asa ta duk'a ta nemi alfarmar Ni'imatu, itama ta yafe Mata, zaman su yanzu gwanin burgewa.





Tana zaune a d'akin ya shigo, ya lura cikin y'an kwanakin nan se wani shashshare shi takeyi shikuma Sam bayajin dad'in hakan ko kad'an, yanzu ma sallamar dayayi kurum ta amsa ta yunkura zata tashi ya rik'e hannun ta "ki shirya anjima zamuje gidan Abu-nawwas" tace "Angelina ta haihu ne" yace "Zahra dai, ta haihu tunda dad'ewa kasantuwar Babu nutsuwa a wancan lokacin yasa ban sanar miki ba" Kai ta d'aga mishi kurum ta tafi gurin Maryam.





*MAHUTA*




Layla taji dad'in kud'in da Sarauta ta bata sosai, cikin gari ta dawo inda ta nemi d'an k'aramin gida ta kama, tasan ya d'anta Abba a makaranta, ta kama sanaar hannu, Babu laifi sakamakon zumunci data rik'e yasa Allah yasama kasuwancin nata albarka, yaran y'an uwa sukanzo gidanta sannan itama akai² take zuwa ganin su, tanajin dad'in rayuwarta ahakan sosai, wani d'an lokaci kuma ta samu aiki da takaddun makarantar ta, tana Aikin radio kuma tana kasuwancin ta, ahakan Allah ya bata miji, managern station d'insu gaba d'aya yake sonta, Babu abunda ta b'oye Mai nadaga rayuwarta, ya tausaya Mata sosai wanda hakan yasa ya k'ara Jin k'aunarta a zuciyar sa, takaisa har gurin dangin ta na uwa Dana uba, kasancewar matar sa bata da wani zafin Kai yasa ba'a d'au lokaci ba akayi auren, zaman su suke lafiya itada abokiyar zaman ta hakama yaransu sun had'a Kai kamar Babansu d'aya, Layla sedai tace "Alhamdulillah" kawai.





*SEMI FINAL PAGE*





*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu*🥰🥰






@07064706167

💵 💴 *AKAN KUD'I*💴 💵

(A poor lady story)



.... 11th July, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* 🥰🥰





🔔 📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚





👑J. W. A👑


Last!Last!! Last!!!



🅿...... *073 & 074*





"Kai yaron kyakkyawan gaske, Zahra baki fad'a min Sunan sa ba" Sarauta ta fad'a tana Kallon Angelina, murmushi Angelina tayi tace "HERO MUHAMMAD SHUREIM" Sarauta tace "what a beautiful name, Allah sarki ashe Abbana ne" Abun-nawwas yace "y'allabai Shureim ya cancanci komai daga Garemu kinga itama iyayenta yanxu suna nan tare da iyayena kuma suma sun amshi musulunci tsakanin mu da y'allabai Shureim sedai addua" Angelina ta kalleshi tace "mun gode" yayi murmushi kurum suka fita shida Abun-nawwas, Angelina ta kalli Sarauta dake ma hero wasa tace "ma'am kinyi sa'ar miji sosai da sosai y'allabai Shureim Yana matuk'ar k'aunar ki fiye da yanda kikeyi, ko zuwanki gidannan na farko shine wanda ya Kira Abun-nawwas a waya yace ahad'a miki abincin da kika fi so Kwana biyu bakya son cin abinci" Sarauta tayi murmushi azuciyarta tana tunanin tafi kowa decen samun miji na gari, nan suka cigaba da firar su har su Abu-nawwas suka dawo, kallon Sarauta Shureim yayi yace "ma'am Muje ko" ta kalli hero dake hannun ta tace "Anan zamu barshi ko" yace "Ahah dashi zamu tafi tunda ke kika Aifa Mata shi" kowa yayi dariya Angelina tace "kema very soon ma'am your own baby is loading..." tana gama fad'a ta b'uya a bayan Abu-nawwas, nan suka basu d'ansu suka biya suka gaida iyayenta sannan suka d'au hanyar gida





"Mr dan Allah ka kaini na duba Shubai'a"yana cigaba da driving dinshi yace "Duka yaushe aka samu ta tare dahar Zaki ce Wai Nakai ki" ta Harare shi tace "to me k'anwa, aiseka kaini na duba Ummahna ko" yayi murmushi yace "yarinya kenan to wayo akayi miki jiya ummahnki ba'a JIDDA ta Kwana ba a Kuwait ta Kwana da dare suka tafi" Aiko nan Idan Sarauta ya kawo ruwa shikenan ba ummah ba Maryam, kuka take sosai Abu k'arami ya girmama, a hankali kukan nata yasoma tab'a ma Shureim zuciya parking yayi a bakin titin ya fuskanta ta Yana kama hannun ta yace "dan Allah kidena kukan nan mana ko Nima kinason Nayi ne" ta amshe hannun ta tace "tokai Ina ruwanka da kukana tunda ba sona kake ba, gashi kuma ummah ta tafi.." hannun ta ya k'ara kamowa yace "waye yace miki Bana sonki, nine na fad'i hakan to k'arya Nayi, Ammerh tun kafin kisan Zaki zo JIDDA Nike sonki ke nafara gani kafin diamond,tunda na ganki Naji Ina sonki kuma na tsara da yardar Allah Kece matata, kuma cikin ikon Allah komai ya tafi yanda na tsara, Ammerh wallahi Ina sonki Ina matuk'ar k'aunar ki ki yarda dani" kallonsa ta tsaya yi tana tunanin Anya da gaske ne kuwa, WAI Shureim Yana sonta, Wayyo Allah gaskiya se yanxu ta fahimci wani Abu Aduniyar farin cikin soyayya kud'i ba komai bane, Sam bazaka had'a kud'i da soyayya ba *AMFANIN KUD'I IDAN ANA DA BUK'ATA ITA KUMA SOYAYYA AMFANIN TA IDAN ANADA RATUWA* tabbas soyayya duniya ce AKAN KUD'I, maganar da Shureim yake ne ta katse Mata tunanin ta "Ammerh please ki yarda dani, Ina sonki fiye da komai da Nike dashi a duniyar nan, Ammerh bansan miye farin ciki ba seda kika shigo rayuwata bansan miye Jin dad'i ba seda kika shigo rayuwa ta Bana banbance wari da k'amshi amma Akan turaren ki na fara banbacewa, Ammerh Akan ki na fara nuna fushi na arayuwata Ina sonki fiye da yanda kike tunani soyayyar da kikemin 0.01 ce Akan wacce Nike miki please ki Dena min asarar hawayen ki kinji" Yana k'arashewa ya jawota ya rungume, cikin muryar kuka irin na farin ciki tace "Nima Ina k'aunar ka mijina Ina sonka banason abunda ze rabani dakai" sun Jima ahakan kafin ya saketa ya goge Mata hawayen ta ya sumbaci goshinta yayi murmushi, itama murmushin tayi Mai tana sadda Kai k'asa, Kai kurum ya GIRGIZA ya cigaba da driving dinshi gaskiya yanason kunyar nan ta y'an Nigeria (jinjina ga Mata masu kunya) driving yake cike da farin cikin da yake Jin rabon shi da irin shi tun Randa ya shak'i iskar duniya, a yau Sarauta ta k'ara sashi wani yanajin ze iya sadaukar da komai Akan sa, Bama komai daya mallaka ba harshi Kansa mamallakin, (Niko nace Uhm Uhm Shureim karka fad'a da yawa AKAN KUD'I Babu abunda bazatayi ba ranta ne kurum bazata iya bayar WA ba to better kasan nayu).





Suna k'arasawa ko Parking be gama ba tafice murmushi kurum yayi ya gyara parking d'in shi sannan ya fita, tana shiga direct d'akin Ummee tayi, Ummee na zaune tana duba wasu files da jaruminta ya bata jiya kurum seji tayi an turo k'ofar an shigo, ajikin ta ta zauna tana cewa "Ummee ashe Abba wayo yayi min jiya shine suka tafi suka barni" Ummee ta shafa kanta tace "ummahnki taje yin bautar Allah kinji kema seki dage kiyi naki Anan kinga mijin ki ma yace honeymoon Zaku tafi abunku" Sarauta ta mik'e zaune tace "honeymoon kuma Nida wa" Ummee ta Harare ta tace "Nida ke mana" Sarauta ta mik'e tana cewa "rufamin asiri karki Jamin kwanan prison yau, na taima sarki da sarauniyar sa" daga Haka ta fice, murmushi kurum Ummee tayi ta girgiza Kai tana tuna rabin ranta Shubai'a.





Direct b'angaren Shureim ta nufa, rasss taji gabanta ya fad'i sakamakon ganin Juwaira zaune a d'akin, hakanan ta dake ta wuce kusa dashi ta zauna, Juwaira ta kalleta tace "Ina Kwana Sarauta" Sarauta tayi yak'e tace "Ina Kwana" Juwaira ta juya ta

Please Login or Register in order to submit comment