Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kwana, doctor Bashir kenan likitan dabaya kyamar patients dinshi likita daya kware a Aikin shi, tunda yaga Maryam yaji harga Allah tayi mishi har cikin ranshi gashi kuma yaga mahaifin ta me cike da dattaku.






*JIDDA*





"Subhanallahi matar yaaya lafiya kike kuka daga shigowa amsa waya kuma se kuka iye meya faru" Shubai'a ta fad'a tana jijjiga Sarauta dake kuka Babu ji Babu gani, dasauri ta fita domin Kiran su Shuwaiba Aikuwa atare suka dawo tambayar duniyar nan Sunyi Mata ita amma Idan dutse ya tanka to itama tayi magana, ganin sunata bata hak'uri amma Kukan yak'i ci yak'i cinyewa yasa Neenah ta dafa ka fad'arta tace "maza goge hawayen nan kuka bedace dake ba, Sunan ki ba irin kuka bane tun asalin Sunan ba'ayi shi domin kuka ba me Sunan jaruma ce wacce ta had'u da k'alubale kalaΒ² amma batayi kuka ba sedai ta ambaci Allah, kidena kuka y'ata Sam Haka be dace ba kefa jaruma ce kamar Dai Neenah, yanzu maza share hawayen nan banason sake ganin su kinji" ta fad'a tana goge Mata hawayen fuskar ta, Shuwaiba na zama a gefen ta tace "ikon Allah kenan ke kuwa first lady miye Matsalar ki ne kodai abincin rana ne baki Ciba" har Sarauta seda tayi dariyar tambayar nan ta Shuwaiba kafin Neenah ta doke ta a kafad'a tace "Aike Aikin ki kenan" Shuwaiba tace "Naji iya abunda Allah ya rubuta zakaci aduniyar nan shi kawai kake ci" Shubai'a tace "sauwa sauwa dai deputy" kowa seda ya kuma yin dariya.








Aranar y'an uwan sarki sukaxo inda aka had'a ga garumar liyafa, kowa murna yake dan gane da ganin Shubai'a na magana Aiko har friends d'inta Seda ta gayyata, party ake yi sosai, inda ha hango Sarauta can gefen a tsaye saboda bata son hayaniya, gani tayi an mik'o Mata mango juice amsa tayi tayima kukan murmushi da godiya ya juya ya tafi, tana tsaye tana shan juice d'in taji mutum ta bayan ta, k'amshin turaren sa yasa ta gane shine ahankli ta furta "Sir Shureim" zagayowa yayi yace "meyasa baki shiga ciki ba" tace "just kawai Bana son hayaniya" yace "Nagode" ta kalleshi tace "Akan me fa" yace "Akan farin cikin da kika bani Ayau d'innan Ina cikin farin ciki duba kiga yanda take murna tana IHU da magana acikin k'awayenta duk ta dalilin ki Nagode sosai" tayi murmushi tana Kallon Shubai'a kafin tace "godema Allah, ammmm Yawwa ai inace zuwa yanzu na kusa kammala aikina ko" ta fad'a domin Jin meze ce, ya kalleta yace "Zaki iya tafiya kenan" ta kalleshi kasa magana ma tayi tsawon lokaci suna Kallon Juna ya zuwa yanzu kuwa ita kanta tasan tana cikin soyayyar Shureim, iska ya hura Mata yace "shikenan yanzu Muje can ki zauna" Kai ta d'aga Mai suka k'arasa gurin, wasu kayane yake nuna Mata a wayar wanda aka turo daga kamfanin su na glasses, Kallo suke suna tattaunawa akai.






Can gefe na hango su tsaye "kadai tabbatar cewa Tasha lemon d'in ko" Khaleesat ta fad'a tana Kallon kukun, ya d'aga Mata Kai, Juwaira tace "Yawwa ungo ka gama Aikin ka zaka iya tafiya" ta fad'a tana Mik'a masa bandir d'in y'an dubu dubu har uku, cike da murna ya juya ya tafi, kafin su kuma suka koma gurin zaman su inda kakan nin su suke, Sunyi murna sosai dajin abunda ya faru, ai koma miye yau seya zube.






"Mrs lafiya dai ko" yak'en dole tayi tace "banajin dad'in cikina zan koma ciki" yace "Eyyah sorry Muje na rakaki ko" ya fad'a Yana temaka Mata ta mik'e shiya rakata har d'akinta, seda yaga ta kwanta tayi luff kamar barci ya d'auke ta kafin ya tashi ya fita, Allah sarki jarumar mu ashe tayi me domin kawai karya d'aga hankalin shi, yana fita daga d'akin tasauko tare da dafe k'asan mararta da'ita kad'ai tasan yanda take ji, mamaki yagama Kamata ganin jini na fita ta k'asanta Duka ko 2 weeks ba'ayi ba da gama period d'inta kuma ita Bama tayin ciwon Mara, wasu zafafan hawaye ne suka wanke Mata fuska take tunanin anya lafiya kuwa, kuka takeyi sosai inda marar bata Dena murd'a Mata ba kuma Haka ma jini be Dena zuba ba.






*KATSINA*





"Sannu da Jiki Maryam" Doctor Bashir ya fad'a Yana Kallon ta, kanta a k'asa ta d'aga mishi Kai, yace "Yawwa to yah jikin naki yake" tace "Alhmdll" yace "masha Allah, Maryam dama so Nike na tambaye ki amma ki sanar min gaskiya" ta d'aga mishi Kai yace "good girl Maryam, jiya dawa kikayi waya before akawo ki asibitin nan" tana goge hawayen ta tace "k'awata" yace "k'awa kuma" ta d'aga mishi Kai, yace "kinason kice min saboda k'awa kika shiga wannan halin yanzu k'awa ce ta d'ora miki hawan jini" Maryam ta girgiza Mai kai tace "abunda yasani hawan jini is a personal issue" yace "Ohk to na jiya kuma fa" tace "mun d'an samu matsala ne da k'awata shysa amma zuwa gobe komai ze warware" Doctor na jinjina rayuwa irin ta Maryam yace "to why not ki Rabu da'ita tunda harta fara jefaki a irin wannan halin wata rana kashe ki zatayi" Maryam tayi murmushi tace "tabbas nafi kowa sanin halinta, ita kanta batasan halinta ba kamar yanda ni nasani, karka damu, tana matuk'ar k'auna ta tana kare ni daduk wani Abun cutarwa kuma ko yanzu nasan Ina ciki tunanin ta bata manta dani ba" Doctor Bashir yace "amma meya had'a ku Haka" tace "Doctor is a personal issue" kafin doctor yayi magana ya jiyo muryar malam na cewa "Humm likita daka tafi abunka Maryam bazata tab'a sanar maka da abunda ke faruwa ba" Doctor yayi dariya ya gaida malam cike da gurnanmawa kafin suka gaisa, mama ta Mik'a Mata wayar ta da duk ta tsage amsa tayi tana gaida su, cike da so da k'aunarta duk suka amsa, HAR su Naja ma sunzo duba ta.





*JIDDA*





Gaba d'aya hankalin shi yana Kanta, amma Shubai'a ta kama ta wani rik'e shi adole Wai pix akeyi shikuma baya son ya b'ata ma k'anwarshi rai Haka Dai ya tsaya har tsawon lokacin da aka gama taron, shiya tsaya sallamar manyan bak'i da kanshi saboda Abiey da Ummee sun fita outing yau, seda dare sosai kafin komai ya lafa, se asannan kuma ya samu damar zuwa gurin Mrs d'in tashi, ganin halin da take ciki ne yasashi saurin k'arasawa Yana fad'in "Ammerh" kwance take cikin jini yanda kasan gawa jikinta duk ya saki, hankali tashe Shureim ya d'auketa yasoma jijjigata, Yana kiran Sunan ta iya k'arfin shi amma ko motsi batayiba, wasu irin zafafan hawayene ke fita daga idonshi zuwa Saman fuskarta, kuka yake sosai kafin kuma ya tuna da asibiti, ahanzarce ya d'auketa Yana goge hawayen shi wanda jinin daya tab'a duk ya goge a fuskar, ihun dayayi ne yasa Shubai'a da Shuwaiba dake duba gift suna Cigiyar Sarauta suka ji Aiko ba k'aramin zabura sukayi ba ganin Jini sosai a jikin su, lokaci d'aya hawaye yasoma fita daga idanun su Aikuwa suka rufamishi baya suna tambayar lafiya, daidai fitar sa su Ummee suka dawo, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un iya tsananin tashin hankali Ayau wannan ahalin ya shige shi, su hajja's kuma dama abunda suke jira ya samu dama Duka su hud'un suna nan suna dakon abunda ze faru, Aikuwa kafin kace me kowa ya farka daga barcin daya fara, cikin hanzari suka Isa asibitin, kafin suje angama shirya komai Doctor Najwa itace amintacciyar likita a asibitin nashi wanda duk wani sirrin asibitin tasani, itace ta Hana shi shiga d'akin Aikin, su kad'ai suka shiga Aikuwa nan kowa yayi cirko cirko, shikuwa jikin shi duk Jini, kowa Yana son ya tambayi abunda ya faru amma ya kasa, ganin yanda Shureim ya zauna yayi shuru yasa Ummee ta k'arasa kusa dashi, hannunta ta d'aura Saman kafad'arshi Aikuwa kamar jira yake ya fashe da kuka, kuka yake sosai wanda hakan seda ya Bama kowa mamaki saboda a iya zaman su dashi duk irin wahalar da suka sha be tab'a zubda hawaye ba Koda yayi to ba'a gaban mutane irin Haka ba, Aikuwa nan kowa ya tsorata da Abun gaba d'aya idonshi ya kad'a yayi jajir, Babu wanda ya iya tanka mishi Haka dai wasu duk suka sab'e wasu kuma suna nan zaune, se gaban nin Asuba kafin Doctor Najwa ta fito itama idonta jawur, wata nurse ce ta fito tare da zare Mata hand gloves d'inta, tana goge Mata zufar fuskar ta seda ta d'ago Mata hannu kafin ta tafi, a hankali duk sauran likitocin suka dunga fitowa suna wuce WA, mik'ewa Shureim yayi yana Kallon ta kafin cikin wata irin murya da ba kowa ya tab'a Jin yayi amfani da itaba, a kausashe yace...........






*TO MARYAM TAMU BAIWAR ALLAH, ALLAH YA BAKI LAFIYA KINJI πŸ˜”πŸ˜”, KE KUMA MRS MS KOME YA FARU AKAN KUD'I KIKAYI AI, AMMADAI SABODA IRIN SU UMMEE TJ DA UWAR BABA SU MY HAJRA, MY, SU ANEESAT, DA DAI SAURAN Y'AN TEAM D'INKI ALLAH YA BAKI LPY πŸ™ƒπŸ˜‰*






*Karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*






@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°







@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)



...... 21st June, 2023





*Story & writing*
*By*





@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°






πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS*πŸ“š




πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘






πŸ…Ώ...... *057 & 058*






Yace "meke damun ta" doctor Najwa ta lumshe idonta kafin ta bud'e tana saisaita kanta ta kalli mutanen wajan har Abiey Yana nan da uncle Yusuf sannan Aunty Rama, jameelerh, khairy, Fawax, su Shubai'a da Shuwaiba dadai sauran su Kallon shi tayi tace "zefi kyau Muje office sena Gaya maka" tana gama fad'in hakan ta juya zata tafi hannun ta ya rik'e Yana dawo da'ita yace "ki gayamin what's wrong with my Mrs" ta k'ara yin Sanyi da murya tace "kasan dai hakan dokar asibitin nan ce ko, ba'a sanar ma mutum abunda be dace ba a inda be dace ba" cikin tsawa yace "inace asibitin nawa ne ko, to daga yau ancire wannan tsarin maza fad'a....." kafin ya k'arasa ta katseshi da cewa "tayi abortion ne" ai gaba d'aya mutanen dake gurin mik'ewa sukayi atare suka maimaita kalmar abortion, Shureim yace "abortion" doctor Najwa tace "kwarai kuwa" yace "kuma tanada cikin" Doctor tace "abunda muke bincike akai kenan, saboda ta zubar da jini dayawa Idanma akwai nasan zuwa yanzu ya fita amma gaskiya tana buk'atar jini yanzu ya Kamata Muje a samo jinin dazeyi asamata" ai Shureim shi Yama kasa yin wani motsi ne kwari kalmar abortion d'in ta tsaya Mai har Ina tayi cikin dazata yi abortion d'in "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kurum ya tsinci kanshi da fad'a, doctor ta yunk'ura zata wuce yace "Ammm Doctor najwa nace dama Koda mutum bashi da ciki Idan yasha Magani ze iyayin bleeding" doctor tayi murmushin tambayar dayayi tace "Haba Doctor Kaifa Babban likita kasan komai amma Bari na tuna maka, tabbas Idan har ya shashi dayawa to ze iya sashi bleeding saboda ze iyayin affecting mahaifa wanda kuma hakan shine babbar Matsalar amma in sha Allah zanyi iya bakin k'ok'arina yanzu Bari Muje aduba jinin" Shureim ya d'aga Mata Kai ya koma ya zauna, kallon su Shubai'a Ummee tayi kafin tace su tafi gida, seda tayi musu Jan ido kafin suka tafi ya zamana daga shi se Aunty Rama, Ummee dasu Abiey, suma su Abiey d'in fita sukayi suka tafi.





Cikin d'an lokaci aka samo jinin aka Sanya Mata, a office d'in Shureim aka kwantar da'ita, inda doctor Najwa tayi musu bayanin Magani ne Tasha, amma batada cikin, kuma Tasha maganin dayawa ne wanda zuwa yanzu bamu San wace matsala ta Samu ba se zuwa nan gaba Idan Allah ya azurta ta da ciki, Koda Shureim ya tambaye ta shin zata iya aihuwa Dai ko, doctor tasanar mishi da basu da tabbas ciki na Allah ne, amma gsky kota samu cikin bazata iya aihuwa da kanta ba, Haka nan Dai yace zeyi bincike akai, ranar Anan ya Kwana shida Ummee.






*Washe Gari*





Tun around 12pm ta farka sedai bata iyayin tafiya dakanta sosai, se'an temaka Mata, yanzu ma zaune take tad'an k'ishingid'a, idonta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin abunda yake shirin faruwa da'ita take yi kuma duk AKAN KUD'I. Ummee data shigo takalleta tace "yarinya ta driver yazo d'aukata, amma zan turo Shubai'a yanzun nan" Sarauta tayi murmushi ta d'aga Mata Kai, Ummee ta fita, a main office d'in ta iske Shureim zaune ya d'an lumshe idonshi Yana tunani, Ummee ta kalleshi ta dafa shi tace "karka sama ranka damuwa kaji yarona, zata samu lafiya" ya bud'e idonshi ya kalleta, Ummee tace "ka tashi kaje kar a barta ita d'aya" ya d'aga Mata Kai ta juya ta tafi.






Yana nan zaune Doctor Najwa ta shigo sakamakon Kiran da yayi Mata, kallonta yayi kafin yace "doctor najwa kina ganin kuwa tabbas tabbas bata da cikin" Doctor tayi murmushi tace "ranka shi dade ka yarda dani nasan aikina duk wani bincike dazamuyi munyi amma alamomin sun nuna bata da ciki kurum Tasha maganin ne" yayi ajiyar zuciya yace "wani temako Nike son kiyi min" ta kalleshi tace "Allah ya bani ikon yi aikai Shugaba na ne, zanyi maka duk wani temako in sha Allah" yace "Nagode, Yawwa please so Nike kiyimin checking d'inta kiga is she Virgin" tayi y'ar dariya tace "she's Virgin" yakalleta cike da mamaki yace "Taya kika sani" tace "kamar yanda na sanar maka duk wani binciken daya Dace Nayi seda Nayi shi, danaga Abun Yana son kawo rud'ani yasa Nayi Mata checking d'in, ganin ta a Virgin yasa na yarda bata zubar da ciki ba kawai dai maganin aka saka Mata" wani irin k'ayataccen murmushi ne ya kwance Mai tare da kallonta yace "thanks xaki iya tafiya, goron ki kuma semun had'u zuwa anjima" itama murmushin tayi, tayi mishi godiya tana tafiya.





Tashi yayi ya k'arasa inda take a zaune, hannun ta ya kama tare da zama a gefen ta, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta kalleshi, tabbas tana buk'atar kafad'ar dazata kwanta akai itama tayi kuka, wasu irin zafafan hawaye ne suka soma wanke Mata fuska, jawota yayi tare da rungume ta yasoma petting d'in bayanta, kuka takeyi sosai, ganin kukan nata bashi da matsaya yasa ya d'ago ta Yana share Mata hawayen yasoma girgiza Mata Kai har tayi shuru, murmushi yayi Mata kafin yace "kinajin ciwo ko" ta d'aga Mai Kai yace "Zaki samu lafiya in sha Allah kinji" ta kuma yin murmushi, hannun ta acikin nashi yace "jiya before ki kwanta kin sha wani abune" ta girgizamai Kai yace "Menene kika sha last" tad'an yi shuru kafin tace "mango juice" yace "a Ina" tace "a gurin taron nan wani ya kawo min Ina tsaye" kafin yayi magana yaji shigowar su Shubai'a, tashi yayi tare da gaisawa dasu kafin ya kalli Sarauta ya lumshe Mata ido yayi hanyar fita Yana fad'in "Shuwaiba Minti d'aya mana" Jakarta ta ajiye ta bishi, a main palon dake office d'in ya tsaya, kallonta yayi bayan sun gaisa yace "maganin zubar da ciki aka bata Tasha jiya" Shuwaiba tace "Subhanallah kuma bata da cikin ko" yace "Uhm, ko kinsan da maganar" tad'anyi shuru kafin tace "amma karka fad'i ma kowa, tabbas kwanaki Naji hajjas na cewa Wai Ance musu tanada ciki, amma kuma daga Haka ban kuma Jin komai ba" ya lumshe idon shi yace "jeki to ki kula da'ita kinji" ta d'aga Kai tanajin zuciyar ta Babu dad'i saboda a zahiri mijin Nasu yake nuna yafi k'aunar Sarauta, duk da yanayin datake ciki behanata cewa "yaya ka taho mana da abinci Idan zaka dawo" yayi murmushin da be shirya ba yafice.






*KATSINA*





Kwanan ta 2 a asibitin aka sallame su, HAR gida Doctor yake zuwa Yana kuma dubata tun basu fahimci komai ba har suka fahimta, doctor Yana matuk'ar so da k'aunar Maryam me irin Halinta ya dad'e Yana nema se gashi Allah ya bashi, sosai Malam Nasir yaji dad'in harkar saboda duk wanda zaka tambaya halin Doctor Bashir to ze Gaya maka kyaklyawane.





Yauma kamar kullum tana zaune tsakar gida da waya a hannun ta seta danna number Sarauta se kuma ta fita, a gaskiya tana son ta kirata taga ko zasu fahimci juna amma wata zuciyar na hanata, Jin Mama ta zauna kusa da'ita ne yasa ta ajiye wayar tare da cewa "Laaa mama Kece ai banji ma zaman ki ba" Mama tace "dama ya za'ayi kiji kinsa waya agaba, kinga Maryam ki raba kanki dawannan damuwar Sarauta fa bani bace kuma ba Malam bace ba kuma Naja bace dazaki d'orama kanki damuwa akanta yarinyar da tana k'asar arna karatu tana ganin wayayyu classic ke kuwa me zatayi dake, gani fa take wannan taren taku kamar kina cin arzikin tane, wallahi yarinyar duk ta fitamin Arai duk ta sauya Hali bansan miye damuwarta ba, amma kuma Maryam Idan ke kikayi Mata laifi ki gayamin" Maryam tayi ajiyar zuciya tace "Mama kenan cikin mu Babu me laifi kawai y'ar matsala ce muka samu" Mama tace "matsala kuma kamar wacce" tana mik'ewa domin gujema tambayoyin mama tace "kawai wani d'an misunderstanding ne muka samu" Mama tace "Aidama nasani koxan mutu baxaki fad'a ba" tayi murmushi tace "Mamana kenan ai Banga Zaki mutun bane" kafin mama tayi magana suka jiyo sallamar Ummah, mama ta mik'e tana cewa "ahahah maraba da manyan bak'i" Ummah ta Washe baki tace "Yawwa, Nidai ai gani naxo bikon y'ar gidana Inji konayi laifine Kwana biyu shuru" Mama tace "Allah sarki Maryam Wai, wallahi bata da lafiya Kwanan mu 2 a asibiti" Ummah tace "Subhanallah meya sameta" Mama tace "kinsan tanada hawan jini to dasuka d'an samu matsala da Sarauta kuma se Abun ya motsa" Mama tayi hakan ne ko zata samu Maryam ta Gaya musu abunda ya faru, Aikuwa kafin Ummah tayi magana Sega Maryam ta fito seda suka gaisa sukayi wasa da dariya kafin Ummah tace "Maryamu ta gayamin meya had'aki da k'awarki har kukayi fad'a" Maryam tace "Babu komai kawai y'ar rashin fahimta ce amma anjima zamu shirya" Ummah tace "to Allah ya kyauta dan Allah kiyi ta hak'uri kinji yarinya ta nasani tabbas kina hak'uri da Sarauta amma ki cigaba da hak'uri da'ita tabbas nasani Idan Sarauta ta rasa ki tofa ta rasa Aminiya, ni yanzu zan wuce asibiti k'irjin nan ya matsa min amma zan dawo Allah ya baki lafiya kinji" Maryam ta d'aga Kai tayi Mata rakiya kafin ta dawo ta zauna, tana nan zaune tana karatun littafi awaya wani yaro ya shigo tare da cewa "Wai Inji Doctor yace Maryam tazo" Maryam ta harari yaron tace "bata nan" harya juya mama tace "kace mishi tana zuwa" zumb'uro baki tayi tace "wallahi ni mama banason mutumin nan nifa na gayamiki akwai wanda nikeso kuma daya dawo zezo" Mama tace "Uhmm to komadai baki sonsa kowa ai lafiya akeson a rabu dashi ko, kuma maganar akwai wanda kike so ai bata taso ba Tukunna tunda mu wanda muka gani shi zamu aura miki kozamu aura miki aljani ne" Maryam tana Hijab d'inta tace "Bama aljani bane Yana nan zuwa" daga Haka ta fice





Tsaye ta gansa jikin motar sa fuskar sa d'auke da murmushi tana k'arasowa ta gaida shi cike da kulawa ya amsa kafin yace "patient ya Jiki" tace "Naji sauqi" yace "good Allah ya Karo sauki ya mutanen gidan" tace "Alhmdll" harya bud'e baki zeyi magana ta katse shi da cewa "akwai abunda nikeyi ne aciki zan koma nagode da kulawa se anjima" ta fad'a tana juyawa ta tafi, shifa komi zatayi bata bashi haushi saboda son da yake Mata, yaro ya Aika da ledojin dayayo Mata tsaraba sannan ya tafi.






*JIDDA*





Dukkan su zaune suke afalon gidan harda Abiey saboda y'an uwanshi dasuka zo yasa ya zauna domin basu lokacin shi kamar aradu ahaka ya shigo d'akin Babu ko d'igon walwala Akan fuskar shi, yana shigowa yanufi inda suke a zaune kowa seda yaji tsoron ganin shi ahakan, Yana k'arasowa cikin d'aga murya yasoma magana "kun tab'a uwata Nayi shuru, kun tab'a ubana Nayi shuru, kun tab'a k'anwata shima Nayi shuru, kun Nisantamu da kakarmu wannan ma bance komai ba to amma Idan kukayi kuskuren tab'a min matata farin cikina rayuwata gaba d'ayan ku nine zanyi silar rayuwar ku a kurkuku Kuzama bayi k'ask'antattu, inason kusani duk abunda kukeyi Akan idona ne Sarai kunbama Mata ta maganin zubar days ciki ko to congratulations na Tayaku murna, amma kuma inason ku sani hukuncin hakan yafi abunda kuka aikata min xafi "maganar da Ummeenshi keyi ne ta katseshi tana cewa" Haba Shureim Baka da hankali ne ko kafara shayeΒ² ne ban sani ba, wa'innan dinfa kakanninka ne sukuma wa'innan Goggon ninka baka da hankali ne komai ba mukaddari bane" Yana kawar dakai yace "Ummee hak'uri na fa ya k'are dole na d'au mataki" sarki ya mik'e tare da cewa "dama abunda zakayi mana kenan Shureim irin tarbiyyar da muka baka kenan, to dan Allah kad'auki matakin nace ka d'auki matakin seka nunamin ban isaba, to Bari kaji Koda gigin wasa ka kuma bud'ar baki a gurin nan kayi magana zaka ga abunda zanyi maka" Aiko sarki ko numfashi be gama maidawa ba Shureim yace "kayi haquri Abiey amma dole zan k'ara yin magana Koda sau d'aya ne" ya kalli Khaleesat da Juwaira dasuka rakub'e a jikin hajjas yace "Khaleesat da Juwaira kuje na sakeku saki d'aya".............





*yanzu Kai shureim Akan Sarauta ka saki y'an uwanka tab* πŸ€”






*karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)




...... 22nd June, 2023





*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°





πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ........ *059 & 060*





...... Be tsaya sauraren kowa ba ya fice, hankali tashe duk mutanen falon suke salati, Khaleesat na kuka tace "Wayyo Allah na shiga uku wallahi bazan iya rayuwa Babu Shiba duk kune kuka Jamin wallahi bazan zauna gidan nan ba" ita kuma Juwaira dama hakan take jira ya saketa ta amshi kud'in shi ta tafi tayi aure da masoyinta dama ai kakarta ce ta tilasta ta Akan tayi auren, duk mutanen falon Kallon su suke kafin Sirayya ta mik'e a fusace ta nuna su da yatsa tace "rufema mutane baki munafuka kawai, Baku da hankaline eye taya zakuyi irin wannan mummunan Aikin yaro tun bezo duniya ba zaku kashe shi to Bari kuji narantse da Allah Idan akace wani Abu ya faru da d'an cikin nan sena wulak'anta ku marasa hankali kawai wannan ai sakarci ne, muma ai Muna son ganin namu ko to wallahi zakuga yanda zanyi daku" Abiey ya rik'e hannun ta yace "calm down sister, kibar su suji da abunda ke damun su, kuma fa kinga hada hajjas aciki" Arayuwar Sirayya ta tsani taji Ance anyi kisa Koda kuwa na dabba ne balle kuma na d'an mutum, amshe hannun ta tayi

Please Login or Register in order to submit comment