Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabuwa wannan kuma ko Wacece oho*





*karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labarine danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa dakuma tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)

...... 19th May, 2023


*Story & writing*
*By*

@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘





πŸ…Ώ....... *027 & 028*




...... Tace "zan koma na d'auko files ne, amma lafiya dai ko" Shureim yayi ajiyar zuciya yace "ki koma kawai driver zeje zan kawo miki ai kinji ko" Sarauta ta juya ta koma gidan tana tunanin meyasa ya hanata komawa company, afili Shureim ya furta "Nagode Allah" daga Haka ya biyo ta ya shiga gidan, part d'in shi kurum ya wuce abinshi, kamar dai da safe seda kowa taje tayi mishi Barka da dawowa.




At 2:00am



Garin yayi tsit, bakajin motsin komai, kowa yayi barci, a wannan lokacin Shureim ne zaune a Saman sallaya da Alama yagama sallah ne, mik'ewa yayi ya cire jallabiyar jikinshi yasaka kayan barci sannan ya fita, direct d'akin Juwaira ya wuce, Yana zuwa ya tura k'ofar yashiga, tana kwance Saman kujerar dake d'akin, cikin kayan barci jajaye Riga da wando, ajiyar zuciya yayi ya kalleta ya k'arasa tare da d'aukarta cak ya maida ta Kan gadon, addua yayi Mata sannan ya lullub'eta da blanket ya kashe Mata light ya fita, d'akin Khaleesat ya shiga, tana kwance Saman gado cikin doguwar rigar barci me hannun best, tayi d'aiΒ² a gadon se littafan dake gefen ta a ajiye da Alama tana karantawa barci ya d'auke ta, kwashe littafan yayi ya d'ora Saman drawer sannan ya gyara Mata kwanciya yayi Mata addua ya kashe light d'in sannan ya fita, ya nufi d'akin Shuwaiba tun daga nesa yake jiyo dariyarta harya k'araso d'akin, kwance take Saman gadon sanye da Riga best da wando iya gwiwa, chat d'inta kurum take tana dariya, Jin motsin mutum ne yasata juyawa ta kalleshi dasauri ta mik'e zaune dan batayi tunanin shi bane, zama tayi tana murmushi tace "my billionaire husband Kaine da Daren nan" zama yayi a side drawer yace "Mekike yi cikin Daren nan baki kwanta ba" ta nuna mishi wayarta tace "chat" ya maimaita "chat" sannan yace "bani wayar nan ki kwanta da safe Idan kika tashi Aise ki cigaba tunda ba wani kikeyima wani Abu ba" tadan zumb'uro baki tace "to zan kwanta amma sedai Idan Anan zaka Kwana" yad'an jima Yana kallonta kafin yace "Sam hakan be dace ba, kinga y'an uwana basu sani ba kuma bayason ji dad'i ba, ni banason hayaniya yanzu ki kwanta se zuwa gobe mayi magana" tayi ajiyar zuciya ta zame ta kwanta, rufe ta yayi da blanket sannan yayi Mata addua kamar Dai sauran kafin ya kashe Mata light ya fita"





Daidai k'ofar d'akin Sarauta ya tsaya Yana tunanin ya shiga ya dubata ko kuwa, zuwa can wata zuciyar tace ai itama matar kace kuma hakkinta ne kawai kaje ka duba ta, a jiyar zuciya yayi yana shiga d'akin, ko Ina na d'akin fes dashi har Saman gadon, tana kwance Saman sallaya da Alama sallah ta gama barci ya d'auke ta a gurin, yad'an jima Yana kallonta kafin yayi murmushi, shikanshi yasan Yana cika Mata aiki kuma hakan ba d'abi'ar shi bace betab'a yin P.A d'in dayake cikama aiki se ita kuma bata tab'a complain akai ba, a fili ya furta "tana da hak'uri" k'arasawa yayi yana tunanin d'aukarta zeyi ya kwantar Saman gadon ko kuwa, a gaskiya baze iya d'aukarta ba Bawai dan tafi k'arfin Shiba sedan yanajin kawai be dace ya tab'ata ba, filo ya d'auko ya gyara Mata kwanciyar ya d'aura kanta Saman filon sannan ya d'auko blanket ya rufeta, nanma tsayawa yayi yana Kallon ta kafin yayi Mata addua, yaje fita ya kashe Mata light d'in, ji yayi ta farka a firgice da sauri ya kunna light d'in zaune ya ganta tana kalleΒ², kusa da'ita ya k'araso yace "lafiya dai ko" dasauri ta mik'e tana cewa "sorry sir bansan lokaci ya k'ure haka ba na kwanta Inata barci Bari naje na shirya" a zahirin gaskiya ta bashi tausayi Wai duk AKAN KUD'I takeyin hakan, murmushi yayi yace "koma ki kwanta safiya batayi ba kinji, kawai na kashe miki light ne" Kallon shi tayi nad'an lokaci sannan tace "Banason duhu fa" ya kalleta yace "to kikwanta kinji gobe se 11am zamu fita" taji dadin hakan sosai tayi murmushi tace "Ohk Sir" daga Haka Shureim ya tashi ya fita, "y'allabai Shureim mutumin kirki ne sosai" ta fad'a tana gyara kwanciyar ta.




*washe gari*




Tunda matan gidan suka fito sukaga basu ga fitowar Shureim ba kowa ta koma b'angaren ta, dan dama ranar da kishin juna suka tashi kowa na tunanin yanda Shureim yashiga d'akinta haka yashiga na d'ayar shysa Babu wacce tayi ma wata magana a cikin su, Sarauta kuwa tun almost 7:30am ta fita domin gama sauran ayyukan da bata gama ba, gashi kuma sunada meeting at 10am, bata sanar da Shureim bane kawai saboda taga kamar Yana buk'atar samun hutu shysa, tunda taje take aiki, taje nan taje nan, y'an k'asar Syria ne xasu zo meeting d'in shysa suketa shiryeΒ², komai yayi daidai Sunyi meeting lafiya inda suka samu damar amsar contract d'in, ita kanta Sarauta taji dad'i Ina kuma ga Shureim, kowa se San Barka yake Mata, har shugaban kamfanin yanemi kozatayi aiki dasu amma se cemishi tayi zan nemeka Idan buk'atar hakan ta tashi.





K'arfe 11:10am ya shirya, yayi kyau sosai cikin milk suit, dasauri yake saukowa daga stairs d'in dan yasan zuwa yanzu kome take ta shirya saboda sarai tasani beson African time, falon tsit Babu kowa aciki, tab'e baki yayi ya juya ya nufi d'akinta Abun mamaki bata ciki, juyawa yayi yafita, Yana fita yace ma drivers "cikinku akwai wanda ya d'auketa ya fita da'ita" Behar yace "Sir tun da safe na kaita company tana can" Shureim ya d'aga Kai ya shiga mota suka tafi.





Tana zaune a office yashigo, dasauri ta mik'e tsaye cike da nuna girmamawa tace "morning Sir" KO kallonta beyi ba ya wuce gaban teburin shi ya tsaya, tasowa tayi d'auke da files d'in ta k'araso inda yake tace "Sir munyi meeting d'in, and fine munyi nasara mu muka samu contract d'in and the happiest thing is that zamu shiga cikin jerin manyan company da ake alfahari dasu a duniya baki d'aya, kuma zamu samu riba sama da 1.5 billion dollars" yad'an kalleta kafin ya amshi files d'in yace "saboda wannan kika taho lokacin tahowar ki beyiba" tace "yes Sir of course, and na taho ne saboda Naga kaidin ango ne kana buk'atar hutu that's why" yace "Ina buk'atar hutu" tace "of course ma kuwa" ya jefamata files d'in yace "contract disaccepted" ta zaro ido tace "what contract cancel" yace "of course" tace "to amma sir why" yace "Ina buk'atar hutu daga yau har zuwa Randa zan aje hutun all the agreement, meeting or contract are canceled understood" daga haka ya juya ya fita daga office d'in.



Batasan Sanda hawaye suka cika Mata ido ba, dasauri ta goge hawayen taje ta ajiye file d'in Saman Table d'inta tana k'ara k'arfafama kanta gwiwa Akan su zasuyi contract d'in.




Almost 20mins segashi ya dawo, ko kallonta beyiba kamar yanda itama ko Kallon shi batayi ba, shuru office d'in ya d'auka kowa na Aikin gaban shi, ji sukayi an turo k'ofar anshigo, lokaci d'aya suka d'aga Kai suka kalli k'ofar, Shureim ya mik'e ya nufeshi fuska d'auke da murmushi yace "Hisham!!!" fuskar Hisham d'auke da murmushi ya k'araso ya rungume Shureim sannan ya bashi hannu suka gaisa, Hisham yace "the great the Muhammad Shureim Sarauta" Shureim yayi dariya suna zama Kan kujerar dake office d'in, yace "amfa kashe Sunan nan tsohon suna ne fa na kashe shi" Hisham yace "ni agurina a Raye yake be mutu ba" Shureim yace "ya kasuwancin naka" Hisham yace "se Alhmdll" kafin ya d'ora da "Yawwa Sarauta yanzu abunda ka aikata kana ganin shine daidai kenan" Shureim ya juya ya kalli Sarauta da tunda tai musu Kallon farko ta d'auke kanta ta cigaba da Aikin ta, yace "kije gurin M.D ze baki sak'o" ta mik'e tana fad'in "Ohk Sir" sannan ta kalli Hisham tace "you're welcome Sir" Hisham ya d'aga Kai Yana mamakin ashe da mutum a office d'in, sannan yace "thank you" tana fita tace "never mind" daga haka ta fice abunta. Hisham ya kalli Shureim yace "itace Maryam Sarauta?" Shureim ya d'aga mishi Kai, Hisham yace "wow but she's beautiful fa" Shureim yace "ai kyan iya na fuska ne" Hisham yace "yanzu Dai kayi aure har Mata hudu ko" Shureim yace "kwarai ma kuwa, sedai duk rabuwa zamuyi very soon" Hisham yace "rabuwa kuma, but suna sonka fa, gaskiya bana goyon bayan hakan, tunda Dai har Allah yasa anyi aure gaskiya karkiyi haka my friend" Shureim yace "dukkan su fa bani suke so ba, nikuma inason na auri matar da ni takeso ba wani abu ba" Hisham yace "to Idan ba Kai suke soba ni suke so" Shureim yace "kaga ita Khaleesat kyauna take so bani ba, kaga duk Randa kyan nan ya tafi shikenan zata rabu dani, ita kuma Shuwaiba kud'i take so bani ba, idonta yariga ya bud'e da kud'i, duk Randa na talauce ko awa d'aya bazata k'ara dani ba, ita kuma Juwaira kawai jarumin namiji take nema wanda ze Dunga biya Mata buk'ata a Koda yaushe kuma wanda zata dunga fita kunyar kawayenta dashi, Kai abarma wannan maganar dukkan su y'an iskane Babu me tarbiyya a cikin su a Haka kake son na zauna dasu, Idan ni Nayi hak'uri nazauna dasu what of my future childs, itama wannan maganar abarta cikin su Babu me ganin darajar mahaifiyata basu son k'anwata, tunda Nike bantaba ganin wata acikin su taje sun gaisa ba Kai ko Akan hanya basu gaisheta balle, nikuma kasani Banida abunda Nike dashi duniyar nan se Ummeena da k'anwata, Taya kake tunanin zan Zauna dasu Hisham" Hisham yayi ajiyar zuciya yace "gaskiyar Kam hakane, kana da gaskiya, but what do of Maryam Sarauta?!" Shureim yad'anyi shuru kafin yace "ita Aikin kud'i take" Hisham yace "duk da Hakan she's your wife" Shureim yace " hakane she's my wife" Hisham yace "kasa kowa ya yarda da auren soyayya kukayi da Maryam to why not bazaku cigaba da acting as that ba, kaje kasamu sauran matan ka ka gyara gidanka ka raba musu Kwana, bance kayi wani abinba amma kowa zata San matsayin ta sannan kasa itama Maryam taji itad'in matar kace" Shureim yace "waikai ka manta Sunan nan ko Sunan waye kake ta maimaitawa" da sauri Hisham ya rufe bakin shi yana fad'in "tofah wallahi Abun ya shigemin ashe sunan me darajar ne" Shureim yace "ohomma Kai kasani" Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.





"wallahi mama Unana Abun harya fara bani tsoro yanzu yakike ganin za'ayi" Hajja jumaima ta k'arashe tana Kallon Hajja Mubeena, tsohuwar matar dake gaban su tace "komai laifin ku ne, tun farko meyasa kuka Bari akayi auren, wannan yarinyar itace mabud'in sirrin dakuka dad'e kuna kullewa, gashi kundau jikokin ku kunbashi balle ayi mishi wani Abun" Hajja Mubeena tace "amma Mama yanzu Babu wata hanya, mu ko kashe ta ne kiyi indai zamu samu abunda mukeso" bokanyar tace "ah ahfa bani kashe mutum Idan lokacin shi beyiba sedai zamu duba mugani abunda duk ya dace ayi Mata za'ayi" Hajja jumaima tace "waini yarinyar nan zata Mara kartaga kamar Nayi shuru jira Nike tazo hannu zata ga yanda zanyi da'ita" bokanyar tace "jumaima gwanda da baki Rama ba dan da kin Rama komai ze iya faruwa bugun bala'i zatayi miki Sam yarinyar bata da mutunci dama ai natab'a Gaya muku cewa Naga bak'i ya doso rayuwar ku ashe itace" Hajja Mubeena tace "ko haukama kisata tayi" bokanyar tace "zakuga yanda zanyi da'ita" Haka sukayi ta k'ullaΒ²rsu.





Almost 40mins segata ta dawo tana shigowa office d'in tace "y'allabai naje munyi magana harma Lissafin munyi" Shureim yace "Ohk good" ta d'aga Kai ta nufi mazauninta, Shureim yace "ammmm zonan" juyawa tayi taje Kiran da yake Mata, gani tayi ya Matsamata guri kusa dashi, tad'an kalleshi kafin ta zauna, yakalli Hisham yace "Hisham this my Mrs," ya juya ya kalli Sarauta yace "Mrs this my friend I mean my best friend Hisham Yusuf" Sarauta tayi murmushi tace..........





*karku manta AKAN KUDI kirkirarren labarine danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa dakuma tunatarwa nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)

...... 20th May, 2023


*Story & writing*
*By*


@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




πŸ…Ώ....... *029 & 030*





....... "Sannu Hisham" Hisham yayi murmushi yace "Barkanki dai ranki shidad'e" tayi murmushi tace "wane irin ranki shidad'e" Hisham yace "matar Mr billionaire ai dole Akira ta da hakan" tayi murmushi tace "amma ban tab'a ganinka ba fa" yace "Uhmm gaskiya bananan, saboda am business man" tace "business man" Shureim yace "kin ganshi nan tare mukayi karatu daga matakin primary har k'arashe daga ya fad'i jarabawar samun license d'in zama babban likita shine kawai ya ajiye be kuma nema ba kawai ya cigaba da business zuwa yanzu kuwa yayi nisa sosai a kasuwanci" Sarauta ta juya ta kalleshi tace "amma d'an uwa wannan babbar dama ce kasamu, meze Hana wannan shekarar kasake gwadawa kagani ai inaga zakayi nasara" Shureim yace "Nayi mishi wannan bayanin yafi sau d'ari amma yak'i ya fahimta" Hisham yace "Wato had'emin Kai zakuyi kenan ko" Sarauta tace "ah ah ba haka bane kawai Dai gaskiya ce" Hisham yace "to gawata gaskiyar, kowa fa da inda Allah yayi abincin shi nacan, Nima Allah be rubuta Inada abinci a Aikin bane shysa har yanzu bekuma bani damar yin ba, kaga tashi mujee na gaida Ummee tun kafin taji labarin na dawo" ya k'arashe maganar Yana Kallon Shureim, Shureim ya mik'e ya kalli Sarauta yace "taso semuyi dropping d'inki a gida" ta d'an shagwab'e fuska tace "toni baza'a gurin Ummeen dani ba" saurin kauda Kai Shureim yayi, be iya bata amsa ba ya juya yabi bayan Hisham, itama tasa after dress d'inta ta biyo su.




A gida sukayi dropping d'inta, duk da irin yanda take k'orafi Akan su tafi tare amma ko kallonta beyi ba balle ya kulata.



Tana shiga tasamu tayi wanka tad'an kwanta, hannu tasa ta jawo wayarta tahau online, nan messages suka fara shigowa, cikin sa'a kuwa taga Shubai'a online, sallama tayi Mata, Aiko kamar jira take ta maido Mata da, "Nayi fushi matar yaya Wato aure dad'i anyi anmanta dani ko" Sarauta tayi murmushi ta tura Mata da "Allah sarki wallahi laifin yayanki ne seda nace zan biyo shi yau amma seyace Wai bayason nazo Idan nazo Zaki wahalar mishi dani, se Randa bakinan zanzo na gaida ummeena 😎" da Shubai'a taga sak'on kuwa rasa ma mizatace tayi daga baya kuma se cewa tayi "lallai yayana ashe abunda yake aikatawa kenan to kibarni dashi ainasan yau zezo, amma kuma fa serious Nayi missing d'inki inason ganinki ya za'ayi" Sarauta ta tura Mata da "kizo gidana ki ganni man" Shubai'a tace "kut Wai dankinga kinyi aure shine kikemin irin Haka" Sarauta ta turamata da "ke Dallah wasa nikeyi wallahi Nima Nayi kewar ki over amma karki damu zan Kira Ummee nasa tayi mishi magana yabarni nazo ke kinma San yanda Nayi kewar ki kuwa" Shubai'a ta turomata da "yawwa y'ar gari ai gwara Haka, dakunyi magana da ita kisanar min Ohk" daga haka suka cigaba da fira gwanin ban sha'awa.





"Ummee tun d'azu banga y'ar kurma ba tana Ina" Hisham ya fad'a Yana cin cake d'in gaban shi, Shureim ya kalli Ummee Yana nuna Hisham d'in yace "wallahi Ummee zanyi mishi dukan daze rasa jinshi shima, Idan yakuma cema k'anwata kurma" Ummee ta rik'e shi tace "rabu dashi my son, aikuma kurmar tafi me idon, yanzu wannan abincin dayake ci, aisarai yasani tafi me jinma" Hisham yace "Aini matar dazan aura se kowa ya raina kanshi" Ummee tace "bazaka tab'a samun me halin y'ata ba" Hisham ya mik'e Yana goge hannun shi da tissue yace "halin madam d'ina nadaban ne se kowa ya Raina kanshi, Bari inje mu gaisa da kurma" Yana gama maganar ya ruga da gudu, Aiko Shureim ya bishi, Ummee tayi dariya ta girgiza Kai.





"kurma!!!" har cikin kwakwalwarta taji k'arar dasauri ta mik'e tana jefar da wayarta dariya yayi yana d'aga murya yace "me kikeyi a d'aki har nazo baki sani ba" hararar shi tayi tad'an yi tsaki sannan tayi nuni da, "danasan yau zakazo daban zauna gidannan ba wallahi" ta k'arashe tana d'aukar wayarta, Hisham yace "bala'i keni d'in Wai kike gayawa Haka Aiko zakiga yanda zanyi dake" ya k'arashe Yana Binta dagudu, key d'in motar ta tad'au ka tare da vail d'inta ta zuba dagudu, Ummee nata magana amma Ina Sunyi waje, tana zuwa tashi ga motar ta tafice gidan dagudu, Hisham yace "ai Zaki dawo ki sameni". Ita kad'ai a motar amma se dariya take b'abb'akawa, a bakin wani shopping mall ta tsaya domin yin siyayya, fitowa tayi fuskar ta d'auke da murmushi tayi hanyar Mall d'in tana tunanin mezata siyamin wancan hamagon.




Duk su hud'un tsaye suke a bakin mall d'in, Khameel ne yace "Wai me wannan banzan yake yi acikine har yanzu nifa Nagaji da jiran shi Allah" Nabil yace "kasan d'an wahalar Wai wasu littafai yake nema kasan wannan itace jarabawar k'arashe dazeyi ya fito a lawyern shi" jabeer yace "Uhmm koma Dai miye ai kud'i sune komai shima Aikin lawyer ai wahala ne" Khameel yace "Uhm shidai ya Sani...... Kai waccan kamar Shubai'a ko" Nabil yace "wallahi itace" Khameel yayi murmushi yace "Bari kugani" jabeer yace "Wai yanzu Khameel duk class d'inka da shekarunka amma ace ka tsaya akan kurma gaskiya kaji kunya" Khameel yace "dad'ina dakai jakine Kai baka fahinta, yanzu Idan na auri yarinyar nan, ai bata Isa ta hanani yin abunda Naga dama ba, kuma Babu abunda Shureim ya'isa yayimin indai Ina tare da'ita" Nabil yace "shege Khameel ashe abunda kake shiryawa kenan" Khameel ya d'aga murya yace "Shubai'a" seda ya Kira kusan sau hud'u sannan ta juyo, da hannu ya kirata, tana ganin shi taji wani mummunan fad'uwar gaba, da farko sotayi ta shareshi ta wuce amma sanin Abun Akan Ummeenta ze k'are yasa ta juya taje.




"me kikazo yinan" ya tambaya kamar wani ubanta " jikinta na rawa tayi mishi nuni da" nazo shopping ne "ya k'ara had'e rai yace" shine baki sanar min ba, ke meyasa jahila ce bayan rashin ji harda rashin kwakwalwa gareki, ubanki kika tambaya kika fito "Kai kurum take girgizawa idonta ya cika da hawaye, harya fara zuba, Nabil yace" Ohhni jimun munafuka uban me mukayi miki" jabeer yace "sharri mana, ai Idan batayi Haka ba bata cika y'ar gidan Maryamu bint Raqiz ba" Khameel yace "Bari inmiki me dalili sekiyi kukan" ya k'arashe yana d'aga hannunshi da niyyar marinta, jiyayi an rik'e mishi hannu juyawa yayi yaga wane d'an mara kunyar ne, Fawax ya had'e rai yace "common guys, miye haka kukeyi ne, itad'in fa mace ce" Khameel yace "yanzu fawaz Saboda karna Mari wannan dump d'in shine karik'emin hannu Haka" Fawax ya shafa gashin kanshi yana k'ok'arin yin controlling d'in kanshi yace "but nan cikin mutane ne, meyasa zaka aikata hakan Aise mutane su fara yimana wani irin kallo" ya juya ya kalli Shubai'a dake kuka yace "disappear" Kallon shi tayi Jin yanda yayi maganar kamar yayanta, seda yakuma maimaitawa sannan ta juya ta tafi, shopping d'in dabatayi ba kenan ta tafi.




"amma Fawax miye haka ka aikata" Fawax yace "Khameel Idan kana yimata irin Haka kasan Sarai yayanta ze iya Hana auren, kaduba kagani Dai" jabeer yace "amma daka Bari ya mareta" Khameel yace "ah ah jabber maganar Fawax gaskiya ce, kana ganin Shureim kamar bayason fitina ko, to munafuki ne, guri d'aya na rayu dashi Duka shekara biyu ya bani" Fawax yace "nasani muma ai duk Haka ne, kawai Dai Allah ya rubuta shine me arzik'in amma koni yanda Nike da zafin neman ilimi Aida tuni Nayi arzik'i, amma yanzu ka kwantar da hankalin ka ai komai yazo k'arashe badai the great Sarauta na cikin gidan shi atare dashi ba aikarka damu" Haka suka cigaba da fira a tsakanin su.





Shubai'a kuwa direct gida ta wuce, zuciyar ta da tunani kalaΒ², Sam bata fad'ama kowa yanda akayi ba ko abunda ya faru amma daga ganin yanayin ta zaka fahimci wani Abu ya faru, Hisham ne ya mintsineta a kafad'a yace "y'ar kurma lafiya dai ko" Kai ta d'aga mishi tana mishi nuni da "anyi accident never" Hisham yace "ashe kurma nada tsoron Allah" tad'an harare shi kafin ta wuce d'aki, Sarai Shureim na lura da'ita, shifa babban likita har karatun nazartar halayyar d'an Adam yayi, tabbas ya gane akwai abunda ya faru kuma maganar data fad'a k'arya takeyi, amma bece da'ita komai ba.






"Asslamu alaikum" Sarauta ta shigo falon bakin ta d'auke da sallama, babu wacce ta kalleta a cikin su balle ta tanka Mata, itama tab'e baki tayi ta wuce tad'au ki remote ta sauya channel, ad'an zabure Khaleesat ta Mik'e tace "how to dear you Ina Kallo Zaki wucemin" Sarauta ta kalleta tace "ohp ai bansaniba Naga kamar chat kukeyi" Juwaira tace "and so, Idan chat d'in muke Aidai da kud'in ubanmu aka siya ko, ko ubanwa ta ya kawo" Shuwaiba tace "to ai se Idan akwai father shine zakuyi wannan maganar" Sarauta ta juya ta kalli Shuwaiba tace "what..." Juwaira tace "kinada uban ne" lokaci d'aya Sarauta taji wani dumm, bata tab'a tunanin akwai ranar da wani zeyi Mata gorin uba ba, to tsaya waye ma uban nata, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, shine abunda take maimaitawa, Khaleesat tace "please Malama Idan ba ubanki ya kawo kayannan ba kid'an kama kanki" Shuwaiba tace "Kash Kash Khaleesat waike yakike Haka ne me uba ba ake fad'a ma hakan" tasssss kakeji Sarauta ta d'auketa da Mari idonta yayi jawur tsabar b'acin rai, tasssss kakeji Khaleesat ta

Please Login or Register in order to submit comment