Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kake ciki, rabonka da abinci fa yau Kwana uku meyasa kake son yima kanka horo irin Haka, kaga tashi ka ci abinci kaji" kallonta yayi, yayi murmushi yace "Ummee na kenan Taya zan iya cin wani Abu bayan keda Shubai'a kuna cikin k'unci wanda nine silar k'uncin naku, Ummee Dan Allah ku yafe min, kinsan irin Haka bata tab'a faruwa ba wallahi bazan...." da sauri ta rufe mishi baki tana fad'in "nasan waye Kai yarona bakason rigima kuma bakayi wannan ma kuskure ne amma ya wuce" Shureim yace "Nagode Ummee please muje kici abinci" kallonshi take batare datace komai ba, kallonta yayi yace "akwai matsala ne?" idonta na cikowa da kwalla tace "har yanzu Abieynka baya min magana fa" ajiyar zuciya yayi kafin yayi magana sukaji shigowar sarki, da sauri ya mik'e yana duk'ar dakai, murya can k'asa yace "sabahul lail ya Abiey" ko Kallon inda yake beyi ba yace "next two to three months P. A d'inka zata fara aiki, Dan Allah ka koreta Idan ka Isa, Ina jiranka seka koretan" ya k'arashe yana kwata, juyawa yayi da niyyar fita, dasauri Ummee tace "JARUMINA" cak ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "lafiya..." mik'ewa tayi tazo gaban shi, Kai a k'asa Shureim ya juya ya fita yanajin zuciyar shi namishi zafi, duk'awa tayi agabanshi tana rik'e hannun shi tace "Jarumina ka yafemin nayima alk'awarin bazan sake aikata makamancin abunda ya faru ba naji na amshi laifina dan Allah kadubeni ka yafemin kaji" ta k'arashe maganar tana hawaye, ajiyar zuciya yayi yace "amma meyasa kikayi hakan kinsan yaro bashi da da manta Abu ko" hawayen ta ta goge tanajin rad'ad'in sharrin da akayi Mata kuma dole ansata amsawa, "kayi hak'uri" shine kurum abunda ta fad'a, shima duk'awa yayi yace "karki kuma" Kai ta gyada tace "In sha Allah" yace " Idan kika kuma kin bani dama Nayi koma miye" Kai ta gyad'a tana hawaye, murmushi yayi ya goge Mata hawayen yace "Toh kuma miye na kukan eye Jarumata" murmushi tayi tare da rungumeshi.

" Shubai'a! Shubai'a!! Shubai'a!!! Kizo ki bud'e k'ofarnan mana ko bakya Jina ne, Shubai'a!!!" duk da irin Kiran sunanta da yake yi amma kamar Babu mutum acikin d'akin, gajiya yayi da Kiran sunanta yasa iya k'arfinshi ya bud'e k'ofar, "Shubai'a" shine abunda ya furta da sauri ya k'arasa bakin gadon nata inda take a kwance, jijjigata yasomayi, a hankali yakai hannun shi Saman jijiyar hannun ta domin ya tabbatar ma da kanshi bata mutu ba, Aiko akwai rai a jikinta ajiyar zuciya yayi yanayin baya da gashin kanshi daya rufe mishi rabin fuska, d'aukar ta yayi, yafita da'ita a hanya ya had'u da Ummeenshi ta fito Aiko tare suka tafi asibitinshi, (wow asibiti fa yaji kayan duniya komai acancan ba'a magana, asibiti ce dataji glasses ta ko'ina, office d'in Shureim kuwa kusan ciki uku garai, na farko tank'ameme ne wanda yaji kujeru dawa su kayan buk'ata na likita daga bangon gabas kuma wani teburine had'e da kujeru a gurin gakuma takaddu a sama wanda ze tabbatar ma da akwai wanda ke zama a gurin, bangon kudu kuma wani glass ne dake d'auke da flowers da wani irin light blue d'in ruwa a ciki wanda da remote ake controlling dinshi ya fitar da Sanyi me k'amshi, se TV dake gurin dadai kayan buk'ata irin frish, ta bingon yamma kuwa glass ne wanda bakowa ke lura dashi ba se wanda yasan dashi, nand'in k'oface dazata sadaka da main office d'in shi wanda fad'in had'uwar shima b'ata lokacine se wani d'an b'angare da gadone da yake kwantar da specials agurin saboda shi bakowa yake dubawa ba bcos ya tara manyan likitoci aduk asibitin daya mallaka)
Suna Isa asibitin ya wuce office d'in shi da'ita RAMADAN dake zaune yake kula da office d'in Idan shugabanshi benan, direct yawuce da'ita main office d'in ya kwantar da'ita nan danan likitoci sukai kanta, almost 30mins suna Abu d'aya kafin suka gama. . " Ummee hankali na ya tashi bansan miye Matsalar ba kiduba kiga yanda Nike k'ok'ari Akan Shubai'a amma duk da Hakan....." takaici ya Hana shi k'arasawa, Ummee ta dafa ka fad'arshi tace"kiyimin bayanin meke faruwa "ba tare daya d'ago ba yace" Ummee akullum cikin bawa Shubai'a farin ciki muke kuma da saninki saboda in faranta Mata ne yasa Nike k'unta tama kaina, Ummee Shubai'a nada ciwon zuciya wanda tunani shine ya jefata acikin wannan halin, Ummee wallahi gwara mutuwa ta da rayuwata Banida amfani, Keda kanki kinsani Nima bawata cikakkar lafiya ce dani ba amma.... " dasauri Ummee ta rufe mishi baki tana hawaye tace" tabbas hakane d'ana amma ka auna dakaine a matsayin da take ciki a yanzu ya kenan, ai dole Shubai'a tayi tunani, yau tsawon shekara biyar kenan bata magana komai sedai ta nuna meyasa bazatayi tunani ba eyeh meyasa "ta k'arashe tana fashewa da kuka " Shureim d'ana meke damun ka bayan ciwon asthma danasan kanayi" duk suka d'ago Kai suka kalleshi, k'arasowa yayi yana shafa kyakyawan gashin Kan Shureim daya rufe rabin fuskar shi yanayin baya dashi yace "meke damun ka yarimana kaifa yarumine ban tab'a ganin gazawarka ko kukan ka ba haka ban tab'a ji ko ganin kayi k'arya ba kagayamin Mike damun ka" duk'ar dakai kurum yayi, Alamar baze yi magana ba kenan, wannan d'abi'arshi ce indai ba Ummee ko Shubai'a ba da matuk'ar wahala kaji yace uffan, a hankali ya tashi ya nufi inda aka kwantar da Shubai'a.


Kusa da Ummee ya dawo ya zauna Yana kama hannun ta yace "jarumata meke damun d'ana kuma farin cikina" ajiyar zuciya Ummee tayi tace "tsawon shekara bakwai yana fama da k'unci da ciwon zuciya wannan dalilin ne yasa ya dawo gida domin gudun abunda ka iya faruwa a Koda yaushe domin ciwon Nashi yakai mamakin k'arashe wanda rashin fad'in abunda ke damun shi shine ya jawo komai" cike da mamaki sarki yace "meke damun shi" "inama Idan ansanar dakai abunda ke faruwa acikin ahalinnan zaka yarda amma Kash bazaka yarda ba ko kad'an addua kurum zamuyi kuma itace zata fishe mu inaji a jikina komai yazo k'arashe Allah ze turomana da agaji very soon" ta k'arashe maganar zucin ta tana ajiyar zuciya a fili kuma tace "be fad'amin ba amma dai inaga kamar Matsalar k'anwarshi ce ke damun shi" tashi sarki yayi yaje gurin Shureim yace "my hero what's wrong" kallonshi Shureim yayi kafin yayi murmushi yamike Yana fad'in "kud'i basu yimin rana ba Babu abunda Banida shi na rayuwar duniya am not a millionaire but a billionaire sedai Kash na rasa kwanciyar hankali dama akwai wani wanda zan Bama duk duniyar da Allah yayimin shikuma ya barmin farin cikin shi Dana bayar amma Babu komai inaji ajikina komai yazo k'arashe Allah ze turo mana mafita " Ummee tace" in sha Allah " daga Haka ya fice, sarki ya kalleta yace" Wai what's going on" murmushi Ummee tayi tace "never mind yana son barin k'asar ne" sarki yace "God forbidden, a bashi da lafiyar is he Ohk" Kai kurum Ummee ta girgiza tana murmushi batace komai ba.


"sisyna sannu kinji" ya fad'a Yana bata tea a baki, amsa tayi tana murmushi wanda Koda yaushe Yana Kan fuskar ta "kina son na tafi na barki ko" dasauri ta girgiza Kai yace "to meyasa kike damuwa meyasa hakan harkika tadama kanki tsohon ciwon ki" Kai ta sunkuyar Alamar bazatayi magana ba wanda dama d'abi'arsu d'aya da Shureim indai bazasuyi magana ba su sunkuyar dakai, ajiyar zuciya yayi yace "alright, promise me that kin Dena d'orama kanki damuwa, Shubai'a komai fa nufi ne na Allah, yasan halin da muke ciki kuma ze kawo mana mafita in sha Allah kidena damuwa kinji Lil sis" murmushi tayi tace "in sha Allah" yace "Yawwa that's my sisy" Haka suka ci gaba da firar su gwanin burgewa, Haka su Ummee sukazo suka samesu sunji dadi sosai a ranar suka koma gida.



*KATSINA*


"yanzu me kike son Nayi" shams ya fad'a Yana goge zufar dake tsatstsafo Mai a fuska, gyara tsayuwarta tayi tana gyara vail d'in Turkish abayar dake jikinta wanda iya ganinta zaka iya yimata kud'i dakanka tace "zuwa zakayi kasameta kace ka fasa auren if not.." ta k'arashe tana cije leb'e, shams ya kuma goge gumi yace "wallahi Sarauta tsakanina da Allah Nike son Maryam kuma auren ta Nike son yi ki temakamin please" tana yamutsa face tace "kadai ji abunda nace" idonshi jawur yace "Sarauta Maryam fa aminiyarki ce meyasa zakiyi Mata haka meyasa kinsan fa tana sona nima ki temaka kibarmu mu rayu meyasa zakiwa k'awarki hakan" murmushi tayi tace "Haba shams sekace bakasan Maryam Sarauta ba AKAN KUDI Babu abunda bazatayi ba dan haka kayi yanda nace" juyawa yayi ya bud'e motar shi ze shiga tace "ammm Yawwa kafara biyawa gidansu Layla kasanar da'ita zaka aure ta kafin kaje gidan su Maryam d'in" Kai kurum ya d'aga Mata ya shiga motar dan ayanda yake ji ze iya sa kuka duniya Yana k'aunar Maryam, daga Haka ya wuce, itama ta juya cike da tak'ama da k'asaita ta wuce ciki tafiya take kamar y'ay'an Sarauta Haka tasoma hawa upstairs d'in, harta kama handle d'in k'ofar d'akinta tajiyo motsin ummah a kitchen "sannu da aiki ummah na" daga kitchen ummah tace "Yawwa y'ar albarka bak'on harya tafi" tana shigewa d'aki tace "Uhm ummah" d'akine daya amsa sunansa d'aki wanda ze isheka rayuwar Jin dad'i ta duniya (amma a gurina da bawani dogon buri gareni ba amma a gurin Sarauta kuwa tab ba'ayi komai ba).

At 8:30pm

Zaune suke suna fira cike da nishad'i gwanin burgewa ga kayan tab'awa nan kala² ummah tace "yanzu Idan kika tafi shikenan Banida abokin fira" Sarauta tayi murmushi tace "Ummahna kenan ai shekara biyu kamar yaune faka faka zanyi ingama fa sekiga harna dawo ki kwantar da hankalin ki" Ummah tace "Toh Allah yasa, Nidai Sarauta Allah yasani Nayi iya bakin k'ok'arina gurin baki tarbiyya dan Allah ki guji yi ko aikata duk wani Abu dakikasan ze cutar dawasu, kinga Dai cikin turawa Zaki ki kula da mutuncin ki ki guji Abun duniya duk k'ank'antar shi hakan shi ke Kai mutum ga halaka ki kula da kanki bazan dena sanar dake ki rik'e addininki a ko Ina kuma ako wane Hali kika samu kanki kinji " kamar Dagaske jikinta yayi Sanyi tace" in sha Allah Ummahna "Ummah tace" kwanan nan Naga kinyi sababbin k'awaye kuma kamar kin janye WA Maryam "Sarauta tace" laa ummah ba haka bane suma fa y'an makarantarmu ne kuma Maryam d'in ma tasansu, kinga ita kuma yanzu tanata Hidima saura sati uku bikinta wani Abu ma Nike son siyar Mata me mahimmanci sosai "Ummah tace" kwarai kuwa Nima akwai abunda zan siya Mata na daban" Sarauta tace "Ummah miye" Ummah tace "sirri ne" Sarauta tace "dan Allah" Ummah tace "ah ah" kafin wani yayi magana suka jiyo sallamar Maryam hankali tashe duk mik'ewa sukayi tana zuwa ta fad'a jikin ummah tare da fashewa da matsanancin kuka "Ummah!!!" kawai ta iya fad'i tana k'ara rushewa da kuka, ummah tace "Subhanallah, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Maryam lafiya meya faru" dafa ta Sarauta tayi tace "komai ya xafi maganin shi Allah kiyi hak'uri kimik'ama Allah lamarinki kawai kiyi ta nanata sunayenshi Zaki samu sauk'i da rangwami" cikin kuka Maryam ke cewa "Sarauta shams ya fasa aurena yace ya fasa..." ta k'arashe tana fashewa da kuka me tsuma zuciya, hankali a tashe ummah tace "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un to mikika yimishi wani Abu ya faru ne ko kuwa kawai iskanci ne da wulak'anci" Maryam na durk'ushewa tace "Wai y'ar uwar shi ze aura wallahi ummah Banida matsala da auren shi amma ya had'amu ya aura mana ummah zuciyata kamar ta fashe har yaje yabama Malam hak'uri yanzu maganar da ake Malam na gida jinin shi ya hau ummah wallahi shamsu ya fasa aurena..." ta k'arashe tana fashewa da kuka me tsuma zuciya, da dadin baki da nasiha suka samu tasoma rage kukan nata ranar Anan gidan ta Kwana duk da baccin ma rabi da rabi sukayi sakamakon zazzab'i me zafi daya kama ta.


*BAYAN KWANA BIYU*


Zaune suke a gefen tank'amemen gadon nata hankali kwance suke sipping juice d'in, Sarauta ta kalli Layla tace " Ina fatan Dai kinsan halin shi na fili Dana b'oye ko" Layla tayi murmushi tace "Babu Matsala nasani kuma Sarauta Nagode sosai, jiya har gurin 11pm Muna tare dashi wallahi Kai amma Naji dad'i yanzu ki fad'a min Mekike buk'ata" Sarauta tayi murmushi tace "ai kince ke AKAN SHAMS Babu abunda bazaki iyaba nikuma nace AKAN KUDI Babu abunda bazan iyaba" Layla tayi murmushi ta d'aga Mata Kai, Sarauta tace "aduk Sanda zakiyi show akwai wasu set na jewelry d'inki dakike sakawa sunikeso" Layla ta Zare ido tace "Kai wannan ba na diamond ne a Malaysia mom ta kawomin diamond jewelry ne fa" Sarauta tace "kwaraima kuwa na sani ki bani su ki auri shams ki hanani kuma k'awata ta aureshi kuma Bana son musu su kad'ai Nike so" ajiyar zuciya Layla tayi tana goge zufar data fara yanzu me zata ce da mom kenan an sace kokuma y'an fashi suka kwace komadai miye tasan yanda zatayi da'ita Bari ta rabu da wannan lafiya, kallon Sarauta tayi tace "Ohk tohm ba matsala yanzu muje gida na baki" tashi sukayi suka je, aranar Dai aka bata diamond jewelry d'in.

*BAYAN SATI D'AYA*


AKAN KUDI K'IRK'IRARREN LABARINE WANDA NAYI SHI DOMIN FAD'AKARWA, NISHAD'ANTARWA TARE DAKUMA TUNATARWA NICE TAKU ME NISHAD'ANTAR DAKU KULLUM DA KO YAUSHE


@ *SHERNTEE GHAYU*



07064706167

💵 💴 *AKAN KUDI* 💵 💴

(A poor lady story)

......1st may, 2023

*Story & writing*
*By*

@ *Sherntee Ghayu*

🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* 📚


👑J. W. A 👑


🅿.....013 & 014


*BAYAN SATI D'AYA*


"Asslamu alaikum" Layla tayi sallama tana hawa benen, "wa'alakis Salam" Ummah dake futowa daga d'akinta ta amsa, kallon wacce ta shigo tayi tace "ah ah sannu da zuwa bak'uwa mukayi sannunki da zuwa" Layla tad'uk'a har k'asa tace "Ummah Ina wuni" Ummah tace "lafiya klau ya mutanen gidan" Layla tace "suna lafiya suna gaisheki" Ummah tace "Ina amsawa agaishesu" Layla tace " zasu ji in sha Allah, ummah Sarauta nanan kuwa" Ummah tace "gaskiya Babu inda taje kuma banji motsinta ba baridai na duba miki" Layla tace "Tohm ummah" ta k'arashe tana hawa Saman kujera. Atare suka fito, tana sanye da doguwar riga ta material ta yafa kallabin akanta daga gani a kwance take, yamutsa fuska tayi tace "Wai Layla ce sannunki da zuwa" Layla ta kalleta tace "Aikuwa kince zakizo kuma shuru shine na biyo hanya" Sarauta na zama tace "ayyah ban samu zama bane Kwana biyu kuma kinga kaina ma yana ciwo shysa" (tabbas Sarauta nada son kud'i amma Sam bata k'arya kuma batason mutane su cika rab'arta shysa ita k'awaarta d'aya a rayuwa Maryam, ummah kad'ai take ma k'arya itama ta kare Kai), Layla tace "ayyah Allah ya baki Lpy" dakai ta amsa Mata, ganin yanda take amsa Mata ne yasa tace "Tohm dama na kawo miki engagement card d'ina ne next one month bikin" ba tare data kalleta ba tace "Eyyah Allah Sanya alkhairi sedai bananan" murmushin yak'e Layla tayi tace "to ki amsa mana ai Babu komai" amsa Sarauta tayi se sannan tayi murmushi tace "Allah ya kaimu" daga Haka taje ta kawo Mata ruwa, sun d'an tab'a hira da Layla kafin ta tafi, tsaki Sarauta tayi a zuciyarta tace "tunda nagama miki Aikin ki kuma miye na nacin mtswww", a bakin gate Maryam ta had'u da Layla tabbas ta ganeta domin duk wanda yake Kallon shirin perfumes show to yasan Layla m k me bulawus. Hankalin Maryam ya k'ara tashi ba kad'an ba da taganta a gidan su Sarauta, bata shiga gidanba ta juya ta tafi gida hankali tashe tana tunani kala².


"ah ah Ina kuma Zaki kike sauri Haka" Ummah dake zaune Saman kujera ta tambaya, Sarauta ta d'auki mukullin mota tace "Ummah gidansu Maryam zani kinsan batajin dad'i kuma gashi yau tsawon sati biyu bata zoba ai gwara naje na duba" Ummah tace "Aiko kin kyauta kiyi maza ki dawo kinji" Kai kurum ta d'aga ta fice dasauri.



"Asslamu alaikum" ta shiga gidan da sallama, mama tace "lale marhaban da mutanen k'asar turawa" Sarauta tayi murmushi tana duk'awa tace "Kai Mama tun banje ba, Ina wuni" Mama tace "lafiya klau Sarauta yakuma ummahn taki" Sarauta tace "tana gaisheki, Maryam fa" Mama tace "tana bayan gida tana shanya wanki tayi" Sarauta ta mik'e tace "Tohm Bari in lek'ota" "ai kunfi kusa" shine kurum abunda mama tace, a bayan gidan ta tarar da Maryam na shanya, kallo d'aya zakai Mata kaga tsantsan ramar da tayi ga uban haske kamar Mara jini, "Maryam kuma ba fad'a meya kawo gaba" Maryam na k'ara had'e fuska tace "me kika gani" Sarauta tace "Inata kiranki baki d'aga wayata, ke tsayama Wai ubanwa kike ma wannan d'aure²n" Maryam ta d'aga Mata hannu tace "dakata karkiyi kuskuren zagin ubana kuma" Sarauta tace "Toh fa Allah ya kyauta yau kuma kome kika sha oho" Maryam ta aje zanin hannun ta ta kalli Sarauta tace "Sarauta ko rantsuwa Nayi bazan yi kaffara ba kina da hannu a fasawar arena ki sanar min gaskiyar me kika sani akai" Sarauta tayi ajiyar zuciya tace "Maryam Bana yin k'arya, kawai mu Bar maganan" Maryam taci kwalarta tace "ki gayamin gaskiya tun kafin a Jimu" Sarauta tace "sakarni Maryam banaso ki sakeni nace miki" Maryam ta saketa tana huci, Sarauta tace "kinga Maryam Mubar maganar nan" Maryam ta rik'e k'ugu tace "Sarauta nagaji² da rayuwa dake ki sanar min abunda ya faru" ran Sarauta ya b'aci, itama cikin fad'a tace " Maryam shams Sam ba mutumin kirki bane bashi da d'abi'a...." "ke awa...nace ke awa, wanine yasaki yin bincike Akan shi,iya binciken da Malam yayi ya Isa ke miye naki a ciki" Maryam ta katse ta a tsawace, Sarauta tayi ajiyar zuciya tace "Layla ta buk'aci da Hakan shysa Nayi tabani diamond jewelry d'inta da take amfani dashi a show d'inta, maganar danike miki har I.V ta kawomin na bikin saura sati uku ma, kinga Maryam ki kwantar da hankalin ki dama Allah ya rubuta shams ba mijin ki bane kuma nice silar rabuwar ku wannan duk tsarin Allah ne " Maryam na zubar da hawaye Tace " yanzu siyar da soyayya ta ki kayi " Sarauta tace" Maryam ki ts..." hannu Maryam ta d'aga b'ata tace "dan Allah ki fita daga gidannan Bana buk'atar ganinki, wata rana nizaki siyar tarayya ta dake bata da amfani ki fita ki bani guri nasan Allah zemin sakayya bakisan miye so ba amma namiki uzuri, ya hayyu ya qayyum ya rahamanu ya Raheem ka jarabci wannan baiwar taka da SOYAYYAR DA KUD'I BASA SIYE daga nan zata fahimci irin abunda tayi min, Sarauta fita daga gidannan dan Allah Kije kawai... " ta k'arashe tana fashewa da kuka tana durk'ushewa k'asa, a d'an fusace Sarauta ta juya ta fita daga gidan, tun Akan hanya mama ta had'u da Sarauta ta tambaye ta amma sallama kurum tayi Mata ta tafi, jiyo kukan Maryam ne yasa taje bayan gidan," ah ah Wai Maryam lafiya kuwa taso nan gayamin meya faru " dagudu Maryam taje ta rungume ta tana k'ara fashewa da kuka, mama tace" Subhanallah meya faru kuma meya had'a ku kidena kuka mana banaso " Maryam na goge hawayen fuskarta tace " Mama fad'a mukayi "Mama tace" meya had'a ku " Maryam tace" Akan wata magana ne kuma wallahi mama bani Nayi ba "Mama tace" to shikenan kidena kuka tashi ki Tai d'aki Bari na Ida miki shanyar kinji jeki " Maryam tace" ah ah mama Bari na Ida kawai ki barshi " Mama tace" keni bani son sakarci wuce kitafi d'aki ".


Tana driving tana sak'e² a zuciyarta, ringing d'in da wayar ta keyine yasa ta dawo daga tunanin da take, FAWAZ ta gani, seda tayi tsaki sannan ta d'aga wayar, da turanci suke magana, bayan sun gaisa ne yace " tafiyar ki yanzu saura sati biyu, fatan duk abunda muka saki zuwa yanzu kin gama" Sarauta tace "Uhm dan yaren larabci da turanci bani da matsala dasu na iya, sannan zuwa yanzu Babu kalar iPad da laptop d'in da ban iyaba, sannan signature d'in MS Babu wanda ban iya ba, komai is ready karkaji kawani damu" fawaz yace "good Allah ya bamu sa'a zuwa gobe zakiyi magana da Khameel kinji" tace "Tohm shikenan seya Kira d'in Nagode se anjima" ta yanke wayar.



*JIDDA*



Duk su ukun dariya suke inka cire Shureim daya sa hannu ya rufe bakin shi yana murmushi me k'ayatarwa, Abiey ne yace "serious hakan take faruwa fa Aikai Prince kasan komai ko ka gaya musu" Shubai'a da take tayin dariya ta tab'o Ummee tana Mata nuni da cewa "amma Abiey ma bashi da dama" Haka suke firar cike da ban sha'awa. Kafin aka Kira Abiey a waya, Yana gama wayar ya kalli Shureim yace "Prince next two week P.A d'inka zatazo, banason matsala wannan shine na k'arashe karka rabu da yarinyar nan kadai ji na gaya maka ko" kanshi a k'asa yace "in sha Allah Abiey" Kallon Ummee Abiey yayi yace "jarumata bari inje Ina

Please Login or Register in order to submit comment