Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayomin tsaraba" Sarauta ta d'aga Kai ta fice.





"Mama unana inajin lokaci yayi da zamuyi Aikin da zamuyi dan wallahi na k'osa Naga k'arshen shegiyar nan" Hajja Mubeena ta fad'a tana Kallon bokanyar, mama unana tace "Uhm Uhm Ina rabaku da Aikin gaggawa, a yanxu akwai kariya ajikinta tako Ina, dan haka kubari se lokaci yayi Idan lokaci yayi tabbas da kaina zan Kira ku na sanar muku" Hajja Jumaima tace "to shikenan zamu k'ara hak'uri har zuwa lokacin.





" wallahi shegiyar yarinyar nan taci Amanar mu kuma sena nuna Mata k'arshen ta munafuka kawai ai Juwaira ta Gaya min komai" Khameel ya fad'a a fusace, Nabil ya rik'e shi yace "ka kwantar da hankalin ka kawai ni nasan yanda zamuyi da'ita" JABEER yace "wallahi kashe ta kurum zamuyi" Khameel yace "gaba kawai zamu saka Mata Tasha ta mutu a Banza" Nabil yace "hakan kawai za'ayi" jabber yace "Wai Ina wannan banzan yake ne" Khameel yace "Noo karku gayamai kunsan halin Fawax" duk suka d'ago Kai.






"Nani Waini za'ayi ma Haka to wallahi bazan tab'a yarda ba sena nuna Mai iyakar shi, shiwai a komai ya fini, yanzu yarinyar ma danaci burin aure ya aure ta to wallahi dashi da'ita duk senaga bayan su kashe su zanyi baki d'aya" Ali khan ya k'arashe maganar Yana Kallon matar dake gefen shi, dafa ka fad'arshi tayi tace "hakane yarona Nima banji dadin hakan ba kayi hakuri amma dukkan su ka kashe su kawai indai zakaji Sanyi a ranka" Ali khan yace "Nagode da goyon bayanki Nani"





"Shubai'a munyi magana dake kuma har yanzu baki ce dani komai ba" Fawax ya fad'a Yana Kallon ta, d'agowa tayi ta kalleshi, kafin tayi magana taga shigowar motar yayanta, dasauri ta mik'e tana mishi nuni da "please ka tashi ka tafi ga yaya nan karyayi tunanin wani Abu kaje zan kiraka" ya kalleta yace "Dagaske Zaki nemeni" ta d'aga Mai kai tana nuna mishi hanya,mik'ewa yayi tare da tafiya, ita kuma ta gyara vail d'inta ta nufi motar fuskarta d'auke da murmushi, tana zuwa Sarauta na bud'e k'ofar ta fito, Shubai'a tayi nuni da "Kece Wai" ta fad'a tana rungumeta cike da murna, itama Sarauta ta rungumeta tace "Nayi mantuwa ne a b'angaren can Muje na d'auko" Shubai'a ta d'aga Mata Kai tana Mata nuni da "ya yayana yake" Sarauta tace "lafiya klau Yana gaida ke" Haka har suka kusa k'arasawa, Shubai'a ta dafe kanta tanajin jira na d'ibarta, Sarauta ta kalleta tayi murmushi tare da kama ta, tace "Sannu lafiya kuwa" Shubai'a tayi Mata nuni da "kanta kamar ze tsage" Sarauta tace "sorry Bari mu k'arasa seki huta" Sarauta ta Kamata suka cigaba da tafiya, ita kuma Shubai'a ji take kamar tana matsawa k'abarin ta ne zuciyar ta sewani suya take, zamewa k'asa tayi tana girgiza Kai bakin ta na motsi amma takasa furta abunda tayi niyya, da k'arfi Sarauta taja ta harsuka k'arasa ciki, suna k'arasawa falon Shubai'a taji kamar an zubama zuciyarta ruwan Sanyi, gaba d'aya zafin ya tafi, tsaya tayi tana Kallon falon, daidai lokacin Dalia da daniyah suka fito, suma tabisu da ido, Sarauta tace "Ina kwanan ku" dania tace "Humm jiya ko sallama bamuyi ba kika tafi" tace "sauri nike yine ana jirana shysa, Ina Mamu ne" daniyah tace "tana d'aki tasamu tad'an kwanta" Sarauta ta kama hannun Shubai'a tace "Muje ciki" Shubai'a ta fashe dawani irin matsanancin kuka cikin wata irin murya tace "dan Allah kiyi hak'uri ki rabu dani wallahi Idan Nashiga mutuwa zanyi Dan Allah ki rabu dani" nan take itama Sarauta ta juye kamar ba'ita ba ta daka Mata tsawar da ba'ita kad'ai ba harsu dania seda suka rud'e "wuce mu shiga Muna fiki kawai" ta fad'a tana fincikar ta suka hau Saman benen, Shubai'a tace "wallahi zan tafi kuma bazan k'ara dawowa ba ki temaka min ki rabu dani dan Allah wallahi nabiki Shugaba Nabi Allah kiyi hak'uri" wani Kallo da Sarauta tayi Mata yasa tayi tsitt bata kuma cewa komai ba, HAR suka shiga d'akin Mamu, suna shiga Shubai'a ta fasa k'ara anan gurin ta zube, Sarauta ta jata har bakin gadon, kafin ta kalli Mamu tace "kimata magana" Mamu ta kalli Sarauta tace "yarinya lafiya" Sarauta tace "d'iyar Zabvier ce kiyimata magana zamu tafi" Mamu taji tsoron yanayin dataga Sarauta shysa ta dafa Kan Shubai'a tare da cewa "yarinya ta yakike" wata k'ara Shubai'a tayi Wacce duk gidan seda ya amsa,itama Sarauta nan ta zube, Mamu ta fashe da kuka tare da kwala masu dania Kira tace "Nashiga ukuna y'an biyu kuzo ku temaka min kar jikokina su mutu Wayyo MI Maryam kaicona dabana da amfani" ta k'arashe tana fashewa da kuka, dasauri y'an biyu suka k'araso, makullin mota suka d'auka tare da d'aukar su Sarauta suka sasu a motar sukayi part d'insu Ummee wanda sukayi alkawarin sun Dena zuwa kenan.





A bakin part d'in suka iske me martaba, da sauri yayo kansu ganin halin dasu Shubai'a ke ciki yasashi Kiran Ummee, kafin d'an lokaci duk mutanen gidan sun fito, d'akin Shureim aka Kai Sarauta, ita kuma Shubai'a d'akin Abiey, inbanda ihu Babu abunda Sarauta keyi tana fad'in abarta taje ta kashe Shubai'a rayuwar shi bata da amfani su kowa cutarwa suke, iya k'arfi Neenah da Ummee suka rik'e ta amma duk da Hakan ihun take, Shubai'a kuwa kuka kurum take tana girgiza Kai Tama kasa magana.





"ko wane irin ihu zakuji kar kuyi kuskuren fita wallahi Idan Bahaka ba zaku mutu saboda, alamu sun nuna Shugaba tana cikin gidan nan kar wacce ta fita daga cikin ku Aidai kunji ni ko" Mama unana ta fad'a daga cikin wayar, hajja Mubeena tace "Wayyo to Yaza'ayi kenan mama" Mama unana tace "mafitar Dai itace kar kuyi kuskuren had'uwa da'ita sab'anin hakan kuma Tohm" daga Haka ta yanke wayar.





"Wayyoh Allah na yarona Nashiga ukuna ni Maryam na bani" Ummee ta fad'a tana fashewa da kuka, hankali tashe Shureim yace "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah karabani dajin kukan mahaifiyata Allah ubangiji kasa banine silar zubar hawayen ta ba, Ummee na lafiya dan Allah kidena kukan nan" Ummee tace "Muhammad kazo gida za'ayi kisa munyi iya k'ok'arin mu mun kasa hana faruwar hakan kayi sauri kazo" daga Haka ta yanke wayar tana cigaba da rik'e Sarauta, cak Shureim ya tsaya Yama kasa motsi tunanin shi Wacece za'a kashe kuma waye zeyi kisan, " *AMMERH* " ya fad'a Yana tunanin tabbas itace da'ita kad'ai za'ayi rigima a gidanan har a nemi kashe ta" dagudu ya d'auki key d'in motar shi yafita, a 90 ya figi motar, Shuwaiba dake tsaye jikin frish tana d'aukar lemu taga ya fita a Haka, kawai jikinta ya bata ba lafiya ba, itama tad'au key d'in motar ta tabishi.





"hak'urin ya k'are cutar tayi yawa dole yau nadauki mataki akai dan haka ku sakeni naje na kashe shi, shid'in Banza" Ummee tace "yarinya ta dan Allah kiyi hak'uri kibarmin y'ata ita Kad'ai ce mace danike da, please Idanma wani Abu tayi miki sena saka tabaki hak'uri amma dan Allah karki cutar da'ita" Sarauta tayi tsawa tace "wallahi Inada k'arfin dazan iya kwacewa kawai dai Ina tausayin halin dazan jefaku ne shysa amma ku sakeni" Neenah tace "ke bafa tsoron ki ake ba, dalla Malama ki tsaya, me tayi miki yarinyar dako magana batayi itace zakice Wai Zaki kashe kizo har gidan ubanta ki nemi kashe ta ked'in Banza" Sarauta ta kalleta tare da fashewa da dariya, da gudu tayi Kan Neenah Aiko Neenah k'afa me naci ban baki ba ta dan k'ara a guje, daidai stairs d'in ta zame, Sarauta ta tsaya tana Kallon ta, ta yunk'ura zata Kamata kawai ya rik'eta gam, ko motsin kirki ma takasa yi "dama nasani akwai abunda ze kawo ki gidannan shysa dama na hanaki zuwa da farko yanzu Neenah Zaki kashe iyaeh" Kallon shi kurum tayi batai magana ba ta amshe jikinta daga Nashi, idonta jawur ta kalleshi tace "matsa min a hanya" yad'an ji tsoro amma ya dake yace "na matsa Kije Ina" kafin tayi magana me martaba ya fito daga d'akin shi jikinshi a sanyaye ya kalli Shureim yace "Prince bata hanya ta wuce" lokaci d'aya kowa ya juya ya kalleshi, dasauri ya goge hawayen dasuka zubo mishi yace "kabata hanya nace maka" dasauri Shureim ya matsa Mata hanya, Aiko har tuntub'e take tashige d'akin, Ummee ta fad'i k'asa ta fashe da kuka "shikenan zata kashe ta nashiga ukuna"





Shuwaiba na shigowa taci Karo da kakarta a bakin k'ofa tanata juyaΒ², "Innalillahi hajjanmu lafiya Meya faru" ta fad'a tana maidata Kan kujera, hajja Neenah tace "wash bayana jeki ciki kawai ni barni Anan" ihun data jiyo ne yahanata yin tambayar datayi niyya ta Haye Saman benan da gudu, duk zaune ta gansu inbanda kuka Babu abunda Ummee keyi, Abiey kuwa ya dafe Kai Yama rasa mezeyi Haka shima Shureim tana hawowa ta kallesu tace "lafiya ihun su waye haka, wai meke faruwa" babu wanda yayi Mata magana tayi hanyar d'akin Shureim ya rik'e Mata hannu ya girgiza mata Kai, Aikuwa ta dawo gefen shi tana toshe kunnen ta, saboda ihun yayi yawa.






Almost 15mins, sannan sukaji shuru, dasauri suka tashi suka shiga d'akin dukkan su, a kwance suke a k'asa gaba d'ayan su inka kallesu zakaga kamar ba lakka ko jini a jikinsu duk jikin su ya saki, da sauri Shureim ya k'arasa Yana tab'a Shubai'a "ke tashi, Shubai'a ki tashi maana Kota kashe tanne da gaske" ya fad'a Yana Kallon Abiey, Abiey ya gurgiza Mai Kai, yace "Noo ka kyaleta Babu abunda ya faru kawai ka d'auki matar ka ka fita da'ita Koda d'akin Ummeen kane kaji" Shureim ya d'aga Kai Yana d'aukar Sarauta, d'akin Ummee ya kaita ya kwantar da'ita juyawar duniya yayi mata amma ko motsi batayi ba, Haka ya hak'ura ya kyaleta ya fita.





*After some hours*





"ah ah gaskiya yaza'ayi na tafi na barku acikin wannan halin Nidai gaskiya ah ah" Shuwaiba ta fad'a tana Kallon shi, daka kalli fuskar shi zaka hango zallar damuwa akai, Kai ya girgiza Mata kafin yace "Kije kawai ba wata matsala itama data farka zamu dawo gida kinji tashi Kije" Shuwaiba tace "nifa ah ah" yace "kofa lunch bakiyi ba gashi har yamma tayi please Kije gida muma anjima zakiga mun dawo and nikadae nasan me zanyo miki tsaraba" ta mik'e tana cewa "fine to sekun dawo d'in amma Idan da matsala fa ka kirani" ya d'aga Mata Kai sukayi sallama har bakin motar ta ya rakata.





*Washe gari*





"Ummee wallahi hankali na atashe yake har yanzu fa cikin su Babu wacce ta farka kuma na dubasu duk lafiya suke kodai imamu Sheik zamu kirane" Ummee tace "wallahi Nima jiya ko barci ban ba hankali na yak'i kwanciya" Abiey yace "dan Allah kuyi hak'uri banason kuna fad'in irin haka kudena fad'a in sha Allah duk xasu farka cikin k'oshin lafiya" kafin wani yayi magana acikin su ta bud'e k'ofar ta shigo Fuskarta d'auke da dariya, kallonsu tayi kamar dai yanda suma suke kallonta, k'arasawa tayi tare da tattab'asu tace "ku gayamin gaskiya kunajin abunda Nike cewa Wayyo Allah na, Abieyna, Ummeena, yayana, WAI da gaske ba mafarki bane da gaske nice Nike magana, Anya kuwa nice ji nake kamar bani, WAI nice kuwa Ummee, Abieyna nice Wai Nike magana Wayyo Allah na, Alhamdulillah, Alhamdulillah".............





*Toh Shubai'a you are welcome back to duniyar masu magana* πŸ‘ŒπŸΌπŸ‘ŒπŸΌπŸ˜πŸ˜






*karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin nishad'antarwa, fad'akarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me Nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)



...... 8th June, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍






πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. AπŸ‘‘





πŸ…Ώ........ *051 & 052*





Baki bud'e Ummee ta mik'e tana nuna Shubai'a, tana Kallon Abiey tama kasa magana, zuwa can kuka ya kwace Mata, cikin kukan take cewa "Zabvier kaji kuwa abunda Naji, da gaske kuwa kaji muryar gimbiyata tana magana kodai yauma mafarkin ne kamar Koda yaushe, Shubai'a tayi magana Wayyo" Shubai'a ta rungume Ummee tace "wallahi Ummee nice, nice nan Nayi magana Wayyo xuciyata dad'i kamar ze kashe ni, yayana duba kagani kalli bakina magana fa nikeyi dawannan bakin fa Nike maganar" Shureim ya goge hawayen daya zubo mishi yayi saurin rungume ta domin duniya bayason aga kukan shi, murmushi yake yi sosai hak'oranshi sun kasa b'oyuwa yace "my sister magana kikeyi Naji da kunnena Naji kina magana shikenan kema yanzu kina magana kamar kowa kamar ni kamar Ummee kamar Abiey kamar dai kowa dake magana" Shubai'a ta kalli Abiey daya duk'ar dakai Yana hawaye tace "Abiey ka tabbatar min nice Nayi magana" Abiey ya d'aga Mata Kai domin Idan yayi magana kuka ze iya kwace Mai.





Aiko da gudu ta fita daga d'akin tana fad'in "yeeeeeeh, Allah na gode maka dakasa Nayi magana, Wayyo Allah na dan Allah kowa yazo yagani Nayi magana da bakina, dawannan bakin Nayi magana Wayyo Allah" part d'in su Neenah ta nufa Kai tsaye, Neenah ce kawai a falo zaune, "Neenah duba ki gani yau kurma tayi magana wallahi nice nikeyin magana da bakina kalli bakin ki gani dakanshi yake motsi harshe nama motsawa yake Idan Ina magana kin gani" ta k'arashe tana fiddo harshen ta waje, Neenah kuwa mamaki ma yahana ta magana, kafin zuwa can itama ta nuna murnarta sosai da sosai Akan Abun yanzu shikenan kurma ta dawo tanayi magana Kai Alhamdulillah, sunanan zaune Sega hajja's sun fito, wani irin Kallo Shubai'a tayi musu, nan take taji zuciyarta ta buga, abunda taji yafara dawo Mata, suma tsayawa sukayi suka kalleta kafin Hajja jumaima tace "Ohhni Mubeena jimin ikon Allah gurin kurmar nan Wai ita harta samu damar hararar mu" Hajja Mubeena tace "ki barta rashin bugu ne" Shubai'a ta mik'e tace "Idan akwai tsinannar data Isa acikin ku to dan girman Allah tazo ta nunamin yatsa ma" wata irin razana sukayi kafin suka kalli juna, HAJJA MUBEENA tace "ke.. Kece kikayi magana" Shubai'a tayi dariya tace "kina mamakin mugun nufinku ya karye ne" dagudu suka koma upstairs d'in itama ta juya a fusace tabar part d'in, tana zuwa ta d'au wayarta tayi video sannan tasoma yad'awa a kafar sada zumunta, Aikuwa nan danan aka fara tayata murna.





"Ummee ki Dena kuka Allah zamu gode mawa kinji" Ummee ta goge hawayen ta tace "tabbas komai na Allah ne amma kuma komai yanada sila a rayuwar nan, Sarauta itace silar komai itace tayi silar abunda ya faru kuma sauran ma itace zatayi sila" Shureim yace "kwarai ma kuwa Ummee, acikin alk'awarin datayi min na bani farin ciki to tabani sama da 99% Ummee itad'in mutuniyar karkice tanada hak'uri sosai nizan gayar miki hakan" Abiey yace "ni wallahi nama rasa mexan ce, amma Dai yanzu Kai kaje ka duba lafiyar ta kaji karta farka Babu kowa akusa da'ita" Shureim ya d'aga Kai ya tashi ya fita.





"hello!!!" Shubai'a ta fad'a da cincin k'arfinta, ta cikin wayar akace "Nashiga uku Zaki fasa min dodon kunne Bama me wayar" Hisham ya fad'a Yana karkad'e kunnen shi, Shubai'a ta k'ara wage murya tace "Kai Malam ka tsaya ka saurareni dakyau, ai komai na Allah ne to yau Allah yasa Nayi magana, dan Haka Idan ka kuma kirana da y'ar kurma na rantse Nida Kaine kuma bazaka samu matar data kaini ba" Hisham da mamaki ya kusa kashe shi ya mik'e tsaye yace "what Shubai'a Kece kikayi magana da gaske" tayi dariya hawaye Nabin fuskar ta tace "wallahi nice nice Nike magana Nima har yanxu ban yarda da Hakan ba shysa Nike ta Kiran waya domin a tabbatar min" Hisham ya katse wayar Yana fad'in "Ina zuwa ganinan zuwa gidan" daga Haka ya yanke wayar ya fito a tamanin ya nufo gidan.






Number FAWAZ tayi dialing Aiko bugu biyu ya d'auka Yana fad'in "tun jiya nake yi miki text amma Babu reply naxo kuma Ance min bakinan, please Shubai'a meyasa kike son ki wahalar dani har Haka, please Idan baki sona ki sanar min I promise yhu that zan hak'ura dake amma da shara d'in sonki shine zeyi ajalina, wallahi Shubai'a saboda ke na sauya ambition dina nazama soldier nakoma lawyer kawai saboda nasan shine burin ki amma sakamakon qaddararki data sauya shysa kika hak'ura, Shubai'a wallahi Ina sonki I promise you that zan baki duk wani farin ciki, ammm Ina zuwa gidan dai yanxu please ki fito mu had'u" yanata k'ok'arin yanke wayar tayi saurin cewa "brother Fawax" cak ya tsaya daga k'ok'arin mik'ewar dayake, mamaki ya daskarar dashi Anan "Shubai'a" shine kurum abunda ya'iya furtawa, tayi murmushi tana kuka ta cigaba da cewa "hak'ik'a nasan zakayi mamaki, to karkayi mamaki komai na Allah ne ayau shine ya k'addara zanyi magna kuma gashi Nayi, Kai d'in farin ciki ne kuma haske a rayuwata daga shigowar ka rayuwata Naga sauyi da dama, *Fawax Ina sonka Ina qaunar ka kuma Ina me farin cikin sanar dakai, dakai kad'ai zan RAYU duk runtsi duk wuya I love you more and more my nisful hayat* " daga Haka ta yanke wayar tana fadawa Saman gado tare da fashewa da kuka.





Yad'au tsawon lokaci a d'akin Yana jiran ta farka amma shuru, HAR duba ta yayi domin ganin lafiyarta amma lafiyarta klau shysa kawai bece sutafi asibiti ba, Haka har aka Kira sallah bata farka ba ya tashi ya fita domin yin sallah.





*After some hours*




Gidan ya cika sosai da y'an uwa da abokan arziki kowa Yana mamakin abunda ya faru masu murna sukayi masu bak'in ciki ma sukayi, Shubai'a kuwa yau farin ciki ba'a cewa komai, Haka ta zauna cikin y'an uwa akaita labari da'ita gani takeyi kamar har yanzu mafarki take kamar imagination takeyi amma har ruwa ta watsa ma kanta taga bata farka ba, tana cikin farin ciki, kowa kuma jira yake Sarauta ta farka, yau Dai har yayan Ummee yazo Wato uncle Yusuf bn raqiz da iyalan shi jameelerh da khairy da matar shi Aunty rama (rahama). Dukkan su jiran tashin Sarauta kawai suke.





"kaga Prince jeka duba yarinyar nan zuwa yanzu yaci ace ta farka Idan bata farka bakuma ka watsa Mata ruwa mugani shima Idan bata farka ba kaga semu San Nayi koba Haka" Aunty Rama ta fad'a tana Kallon Ummee, Ummee tace "ai tashi zamuyi mu shiga cikin Danni wallahi dama tun tuni Abun ke damu na" Shubai'a tayi caraf tace "Allah sarki matar yaya duk saboda ni tashi ga wannan halin gaskiya bazan tab'a mantawa da'ita ba a rayuwa ta" Hisham yace "Aifa kurame anyi baki surutu kuma se Allah" Shubai'a ta jefeshi da filow tace "anji d'in" jameelerh tace "Allah sarki d'an k'anina duk ya shiga damuwa matar sa rai a hannun Allah" Shureim ya wani watsa Mata harara yace "wane k'anin naki to Bari kiji ni nafi k'arfin ki kuma a yanzu banda lokacin ki ki jira zuwa Sanda noorul hayat d'ina zata farka zakiga yanda zanyi dake" duk dariya akayi a falon kafin sarki da Yusuf bn raqiz suka shigo domin zuwa su duba Sarauta, Aikuwa gaba d'ayansu suka nufi d'akin.





"yayyafa Mata ruwan mana" sarki ya fad'a Yana Kallon Shureim daya rik'e ruwa a hannun shi, Kai ya d'aga kafin ya matsa kusa da'ita ya yayyafa Mata ruwan, arazane ta farka, Aiko shima dasauri ya ajiye ruwan Yana Kamata "Sannu yi hak'uri kinji" kanta take girgizawa tana fad'in "Ummahna kaina, kaina kamar ze fad'i ummah kaina" ta fad'a tana fashewa da kuka kuma tana rungume Shureim, shima mantawa yayi da mutanen dake d'akin ya rungume matar sa Yana fad'in "kiyi hak'uri kinji Bari Nayi miki addua Zaki samu sauk'i kinji babu abunda ze faru kiyi hak'uri kinji" Sarauta ta kuma rungume shi tanayin ajiyar zuciya, zuwa can ta d'ago ta soma Kallon su, hawayen fuskar ta ya goge Mata kafin yace "ya Kan naki yanzu" Kallon shi tayi kamar ranar ta fara ganin shi kafin kuma ta d'aga mishi Kai, Shubai'a ta zagayo tare da kama hannun ta tana murmushi tace "y'ar uwa ngd sosai Kece silar komai nasan kema zakiyi mamakin ganin Ina magana kamar Dai sauran ko to duk ta dalilin kine hakan Nagode sosai" abunda yaba kowa mamaki shine ganin yanda Sarauta batayi mamakin ganin Shubai'a na magana ba, ajiyar zuciya tayi kurum ta lumshe Mata ido, tana mik'ewa tsaye, duk Kallon mutanen falon tayi kafin ta kalli Shureim can k'asaΒ² tace "inason Nayi wanka" Kallon khairy yayi yace "help her" khairy ta d'aga Kai tana mik'ewa tana nufar inda Sarauta take, Aiko Sarauta ta kauce tana had'e gira, Shureim yace "barshi kawai khairy bata sanki bane, Shubai'a temaka Mata" Shubai'a ma tana mik'ewa Sarauta ta matsa tana d'aure fuska, ta kalli Shureim tace "inajin jira kuma inason Nayi wanka" Kallon mutanen d'akin yayi ya duk'ar dakai, Sarauta ta kuma Kallon shi tace "inajin jira fa" ahankli mutanen d'akin suka soma fita, ya rage daga shi se ita, mik'ewa yayi yana Kamata har bayin ya rakata, duk ta saura Mai kamar ba ita ba, ta Gama wankan ta fito Yana nan zaune ta soma shafa Mai kafin ta d'auko wata doguwar Riga tasa, kallon ta yayi kafin ya kama hannun ta yace "amma meyasa kikayi yima khairy Haka bazata ji dad'i ba fa" Sarauta ta k'ura Mai ido, batace Mai komai ba yakuma cewa "shikenan na fahimta, yanzu ya kike Jin jikin naki" ta d'aga Mai Kai, yace "to masha Allah, ahankli zakiji dad'in jikin kinji" ta kuma d'aga Mai Kai, mik'ewa yayi daniyyar yabar ta ta huta, harya Kai bak'in k'ofa seya juyo domin yimata magana kawai seya ganta abayan shi, murmushi yayi yace "Zaki iya fita ne" kawai ta d'aga mishi tana kama hannun shi, kallon hannun nata yayi kafin yayi Mata murmushi suka fita.





Suna fita falon, jameelerh tace "Sannu k'anwarshi ya jikin naki" bayan Shureim Sarauta ta koma tad'an b'uya kamar mejin tsoron mutane " khairy tayi murmushi tace" to kodai Auntyn Tamu batason mutane ne" Ummee tayi saurin cewa "ah ah wallahi khairy Bahaka bane inaga Kan abunda ya faru ne" Hisham yace "gaskiya Kam amma ai Mrs M.S ba haka take ba" Shubai'a tace "gaskiya Kam" Shureim ya d'an zame hannun shi daga nata ganin su Abiey na magana, kallon ta yayi ya lumshe Mata ido, ya wuce gefen Abiey, Aiko Yana zama yaga itama ta zauna Kallon ta yayi da niyyar yin magana, amma Abiey yace "no don't worry about it, ka barta kawai, yanzu zanje na Kira imamu yazo ya dubata" Shureim ya d'aga Kai yace "to shikenan sekun dawo" Ummee ta shafa Kan Sarauta tace "Sannu kinji y'ar nan" k'ara rik'e Shureim tayi tana b'oye face d'inta, Shureim ya yima su Aunty murmushin yak'e.





Yarasa yanda zeyi da'ita gaba d'aya yau duk inda zeje tana biye dashi gashi

Please Login or Register in order to submit comment