Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Harare ta yace "ganinki nazoyi koke bakiyi murna da ganina ba" ta kuma juyawa bata hangi Shureim ba tayi ajiyar zuciya tace "Ohh Nayi murnar ganinka mana takanas fa kazo daga hindi kawai dan kaganni ai Nayi murna" Ali khan yayi murmushin Jin dadin maganar ta, bata ankare ba kawai taji an kama Mata hannu anjata, dasauri ta juya ta kalli Shureim daya had'e rai, cikin motar yasata sannan ya rufe kofar tana son tayi magana amma tama kasa batasan Sanda kuka ya kwace Mata ba, kuka takeyi sosai, dakanshi yakeyin driving d'in fuskar nan tashi me cike da annuri da kwarjini yau cike take da b'acin rai da Jin haushi, kukan ta ba k'aramin tab'a shi yake ba, tsaki Yaja yace "KO kiyi shuru kona saki motar nan tayi duk inda zatayi se Inga In a lahira zakiyi soyayyar" rage sautin kukan tayi dan wallahi tana tsoron mutuwa kuma a yanayin shi tsaf ze iya sakin motar........





*INA MATUK'AR GODIYA GA ALLAH DAYA BANI IKON CIN INTERVIEW NA, HAK'IK'A YAU INA MURNA DA FARIN CIKI, INA MATUK'AR GODIYA AGAREKU MASOYANA SAKAMAKON ADDUAR DAKUKE MIN, NAGODE ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI*






*karku manta AKAN KUDI k'irk'irarren labarine danayi shi domin fad'akarwa nishad'antarwa tare da kuma tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *Sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)


...... 30th May, 2023


*Story & writing*
*By*


@ *sherntee Ghayu* 😍 😍




πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š




πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘




*Unforgettable day* πŸ˜‡πŸ˜‡πŸ˜




πŸ…Ώ...... *037 & 038*





Suna Isa gidan ta bud'e motar, dagudu tashiga gidan, shima a 360 yaja motar ya tafi, tana shiga falon ta fad'a Saman kujerar tare da fashewa da kuka, kuka takeyi sosai wanda ita kanta batasan miye dalilin yin kukan nata ba, Jin kamar ana kuka yasa Hajja Neenah k'arasowa falon, duk da batason yarinyar saboda abunda ya had'ata da jikarta, amma kuma tanajin yarinyar har cikin zuciyarta saboda Sarauta dama yarinya ce me shiga rai (Saura Inji kunce wani abu), k'arasowa gurin tayi tare da dafa Mata kafad'a, dasauri Sarauta ta d'ago ta kalleta tana goge hawayen ta, HAJJA Neenah tayi murmushi ta zauna gefen ta tana mik'a Mata ruwan dake hannun ta, amsa Sarauta tayi tana Jan hanci, seda tagama shan ruwan sannan Hajja Neenah tace "komai yayi wuya maganin shi Allah, yarinya ked'in zubin jarumai gareki Sam kuka be Dace dake ba, Humm akullum addua ta kenan cewa yarana ko kuma Dai jikokina su zama kamar dai ked'in nan, ma'ana kalar halin ki wanda jarumtar kima a fili take, duk y'an uwanki sun koma gidan mijin ku why not ke baki koma ba, yakammata ki koma nasan duk hakan Yana daga dalilin dayake sakaki kuka, kina son mijin ki Yana sonki dake kad'ai yayi auren soyayya amma meyasa kukema juna irin Haka" dafarko Sarauta taso sauke Mata shikashikan rashin M, amma kuma setaji zuciyarta tayi Sanyi, mik'ewa tayi ba tare da tace ma Hajja Neenah komai ba ta wuce upstairs d'in. Tana xuwa tad'auko Jakarta me amfani da mukullin wancan part d'in ta wuce can domin samun nutsuwa kuma dama yau zata koma.





Ko parking be gama ba ya fito daga motar, daka ganshi zaka fahimci ranshi a b'ace yake, Yana shiga parlorn ya iske su, duk su ukun suna fira kamar ba kishiyoyi ba, tsaki yaja yayi hanyar upstairs d'in, Khaleesat ma tsaki taja tace "kawai wata y'ar iska ta b'atama mutum rai a waje shikuma ya shigo gida yace ze sauke mana" Juwaira tace "kinsan ai tsoron ta yake y'ar shegiyar yarinyar nan wallahi ba haka ta barshi ba" dawowa yayi falon tare da nuna Khaleesat da hannu yace "tabbas ma kuwa ita batayi kalar matan da za'a dunga saukewa akansu ba Kece kikayi kama dasu" sannan ya juya ya kalli Juwaira yace "tabbas tsoron ta nikejin saboda Idan da soyayya Babu abunda ba'ayi ke meyasa banajin tsoron ki" yaja dogon tsaki ya wuce dama Abun shi, Shuwaiba ta tuntsire da dariya tace "Al'imsaku alal hikimatu (shuru ma hikima ne)" ta k'ara fashewa da dariya ta mik'e tayi hanyar dining tana cewa "ku taho muyi evening mana nifa na fara Jin yunwa" duk tsaki sukayi suka tashi suka bata guri, dariya ta kuma yi tana zama a dining d'in, seda taci ta k'oshi sannan ta koma falon kafin kuma na dare yashigo.





"Asslamu alaikum" ta shiga d'akin bakin ta d'auke da sallama, ko d'agowa beyi ba balle ya kalleta, k'arasowa tayi cikin d'akin tana kalleΒ² kafin ta k'araso gefen shi tazauna tana dafa kafad'arshi, tace "Wai duk miye hakan ne, kawani bi ka d'aure fuska kaida Sam baka irin Haka shine yau kakeyi, Uhm Matsalar dai bazata wuce sarautar gidanka ba to kaje ka dawo da'ita mana, Kai nifa indai bazaka hanani abinci ba agidannan to Nima Banida matsala da kowa Nidai ai Kai nikeyi bawani ba kuma Kai d'innan Allah ya bani, Toh Akan miyene zan takura kaina dan Allah ka dawo daidai anjima ko gobe kaje ka dawo da'ita kaji my Mr billionaire " Shuwaiba ta k'arashe maganar tana k'ara dafa kafad'arshi, d'agowa yayi ya kalleta cikin d'an lokaci kafin yace" in sha Allah, Nagode" tayi murmushi tace "that's my Mr billionaire" shima yad'an yi murmushi dan karya sage Mata gwiwa, harta mik'e zata fita sekuma ta juyo ta kalleshi fuska a d'aure tace "karkaji nace kadawo da'ita ba matsala, wallahiΒ³ Idan akayi kuskuren samun dokar abinci hummmnn kasan komai base nafad'a ba tunda kasan wace ni, abota muka fara kafin soyayya ka tuna wannan" besan Sanda yayi dariya ba tunawa da yanzu zakaga Shuwaiba ta had'e rai tana kumbureΒ² Idan tanajin yunwa, ita cikinta shine kawai Matsalar ta, itama dariya tayi kafin tace "ka cigaba da kasan cewa a hakan mijina kamafi kyau" d'an harararta yayi, tana dariya tace "kamar dodo fa Idan ka d'aure" pillow ya jefamata Aiko dagudu ta fice tana dariya shima dariyar yake.





Wani dogon tsaki taja kafin ta mik'e daga kwancen datake ta lek'a k'asan benen domin tanajin hayaniya, wasu Mata ta hango su uku, d'aya a kwance biyu a tsaye akanta kamar dai gyara Mata kwanciyar suke, tsaki taja ta sauko down stairs d'in.



"ke lafiya kuwa bakusan da mutum a ciki bane ba kunbi kun isheni da surutu" ta k'arashe maganar tana Ida saukowa, lokaci d'aya matan duk biyu suka juyo suna Kallon ta, "lafiya kuwa why the look" D'ayar matar ta juya ta kalli D'ayar tace "DANIA yau Naga ikon Allah tsawon lokacin nan Babu wani d'an Adam daga cikin masarautar nan da yazo b'angaren nan amma yau gawata tazo wacce Alamu sun nuna itace mabud'in komai" wacce aka Kira da Dania tace "wannan Haka ne y'ar uwata DALIYAH" kafin Daliyah ta juya ta kalli Sarauta tace "Wacece ke yarinya kuma Meya kawo ki nan" fuskar Sarauta d'auke da tambaya tace "Kai ku dakata kud'in su waye kuma ita wannan Wacece, ku tsaya ma ni'ina kuka sanni" Daliyah tace "kizo ki zauna nan nizan gaya miki komai da komai" ta k'arashe tana zaunar da Sarauta gefen matar dake kwance, Dania tace "itad'in matar sarki marigayi ladteef ce Mamun sarki Zabvier, ciwone yasameta wanda ba'a San miye maganin shi ba bata iyayin komai da kanta sedai ayi Mata, mud'in nan y'an biyu ne tsawon shekara 15 Muna kulawa da'ita, shekarar ta 17 tana wannan ciwon shekaru biyun farko Zabvier da Maryama suke kulawa da'ita, amma zuwa wannan lokacin me tsawo babu wanda ya sake zuwa gurinta tun bayan shekarun nan, kullum tambayarta d'aya shin Zabvier ko Maryama sunzo ko kuma sun Aiko da sak'o a bata, kowace safiya da yamma tambayar ta kenan bata gajiya ma dayi, a bayan wa'incan shekarun Babu wanda yaxo se ayau ke kika zo" Sarauta ta cika da mamakin Abun mahaifiyar Abiey ce ahaka, kuma basa zuwa dubata duk yanda take ma mutanen nan Kallon na gari a yau taji basu da adalci a rayuwar su, kafin tayi magana, taji ankama hannunta, dasauri ta juya ta kalleta, murmushi Mamu tayi tace "ked'in Wacece Zabvier ne ya Aiko ki kiga lafiya ta ko, Aidama nasani y'an biyu kun gani ko, dama na Gaya muku yarona be manta dani ba aiki ne yayi mishi yawa amma ai gashi yau ya Aiko min da sak'o" ta k'arashe tana murmushi, Sarauta ta goge hawayen ta tace "Uhm shine ya Aiko ni yace a duba lafiyar ki," Mamu takuma yin murmushi har kyawunta na bayyana tace "Ina lafiya fatan suma suna lafiya Ina jikana Sarauta da uwar surutu MADINATUL MUNAWWARA, fatan Dai duk suna lafiya" kafin ta cigaba da cewa "kema ya mamar taki take" Sarauta tace "lafiya klau" Mamu tace "amma Ina Maman ki taje hartasa d'an uwanta yaji Babu dad'i, gashi kuma ta dawo yanzu" Sarauta tace "Uhm Wakenan" Mamu tace "ummahn ki mana Noor" Sarauta tace "gaskiya ban Santa ba Nid'in matar Sarauta ce" Mamu tace "k'arya zakiyimin bayan ga fuskar Noor nan k'arara a fuskar ki, kuma dama ai nasan auren ki da Sarauta za'ayi shi ko bayan Raina" Sarauta tace "wallahi bansan Wacece kike magana akai ba" Mamu ta had'e rai, Sarauta tace "Ohk tohm suna Lpy suma" Mamu tace "ai dama nasani DUK wanda ya ganki yasan ke d'iyar Noor ce kuma jikar Neenah" Sarauta tayi murmushi tabar shi ahakan, ranar yini sukayi fira Mamu taji dad'i sosai kamar tayi ihu, suma y'an biyu Sunyi murna sosai da sosai, da dare ma Mamu tare ta Kwana da Sarauta.






*Washe gari*




Da wuri ta shirya domin tana son ta biya ta gaida Ummee kafin ta wuce aiki, tana fitowa taga an shak'e dining da abinci kalaΒ², ko ba'a fad'a Mata ba tasan Aikin y'an biyu ne, Aiko harda Mamu aka Sata agaba seda taci abinci sosai irin wanda tunda tazo JIDDA bataci irin shi ba, seda ta sumbaci Mamu sannan ta tafi, ahakan ma seda tasa tayi Mata Alkawari Akan zata dawo.





"tunda kika zo Naga se wani fisgeΒ² kikemin konayi miki laifine" Sarauta ta tab'e baki tace "Uhm nizan wuce aiki Ummee sena dawo" ta k'arashe tana mik'ewa, Ummee tace "to yau kuma sarautar ce ta motsa to sekin dawo Adawo lafiya" Sarauta bata tanka Mata ba ta fice, yau d'an gaida Abiey d'inma da ake ba'ayi ba haka ta wuce office.





Acan ta iske shi, shima yau go gaisuwar be samu ba, Abun ya matuk'ar bashi mamaki amma beyi magana ba ya Danne, se wani y'an fisgeΒ² take, shidai be tanka Mata ba, suna nan zaune wayarta tayi ringing ta mik'e ta fita.




"hello Maryam yakike" Maryam tace "ban saniba y'ar rainin hankali tun yaushe Nike Kiran layinki Bana samu, ke kuma kinzama Mrs billionaire ko Kiran mutane bakya yi ko" Sarauta tace "ai Matsalar itace ka Kira a cika maka kunne da surutu, ni kinga very soon wani aiki ze kawoni 9ja Kota wace hanya sena zo gida ai kinjini" Maryam tayi ihun murna tace "Wayyo Allah nasani da kuwa munyi murna sosai dan Allah yaushe Zaki zo" Sarauta tace "ke Dallah tafiyar fa bata tabbata ba seta tabbata kinga Ina aiki zan kiraki anjima bye" daga Haka ta yanke wayar ta koma ciki.





"dan Allah ka d'aga wayar mana Haba ta dameni da ringing ga aiki inayi" Sarauta ta k'arashe tana Kallon wayar Shureim data isheta da ringing, shima Kallon wayar yayi kafin yakai hannu da niyyar d'agawa, dasauri Sarauta ta dakatar dashi ta hanyar cewa "sorry Sir but is not allowed kad'aga waya Anan is better gaje waje" tsaki yaja ya mik'e ya fice saboda hakan dokar shice kuma ma koba haka ba yau yaganta asama sama besani ba ko akwai makarai akanta yanzu su motsa dan wannan ba'ita kad'ai bace,wannan tunanin yake harya Kai waje.





"hello Diamond Kinata kirana Ina office" diamond tace "laaa Babu matsala ai nasani" Shureim yace "Tohm shikenan fatan kina lafiya" diamond tayi murmushi tace "lafiya klau gold fatan kana cikin farin ciki" yayi ajiyar zuciya batare daya ce komai ba, diamond tace "dama Akan maganar zuwan ku 9ja ne, kana ganin Babu matsala kuwa" Shureim yace "in sha Allah zanyi takatsantsan akai Babu abunda zata fahimta karki wani ji kin damu" diamond tace "to gold Allah ya temaka kuma ya kawo ku lafiya, yanzu yaushe zaku zo" yace "weekend domin na bata damar zuwa taga mahaifiyarta sannan semuyi Aikin dazamuyi mu taho amma karkiji komai zanzo gurin ki kuma mu Kwana Muna fira" dariya diamond tayi tace "Allah yasa, yanzu ka koma domin ka cigaba da Aikin ka kaji" yace "Laaa ai Babu komai my diamond zanyi komai domin ki" Haka sukayi sallama ya koma office





"ki shirya weekend d'innan zamuje 9ja domin yin aiki da company d'in coal dake ibadan sannan zamuje Abuja domin duba wasu Kaya a RADIUS GLOBAL DMCC COMPANY companyn wani chemical ne da y'an agro-chemical ke amfani dashi gurin had'a wasu daga cikin maganin shuka wanda akafi sani da ruwan Sanyi dan haka ki shirya" Kai kurum ta d'aga mishi domin shima haushin shi takeji Akan abunda take tunanin Sunyi wa Mamu ace ka wulak'anta kakarka tab wa'innan ahalin se ahankli............





*karku manta AKAN KUD'I k'irk'irarren labari ne Danayi shi domin fad'akarwa, nishad'antarwa tare kuma da tunatarwa, nice taku me nishad'antar daku akullum da ko yaushe*





@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





@07064706167

πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUD'I* πŸ’΄ πŸ’΅

(A poor lady story)


....... 31st May, 2023




*Story & writing*
*By*




@ *sherntee Ghayu* 😍 😍





πŸ”” πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š





πŸ‘‘J. W. A πŸ‘‘





πŸ…Ώ....... *039 & 040*





Yau da wuri ya dawo gida, seda yayi wanka ya kimtsa sannan ya lek'a kowaccen su yaga lafiyar ta, har sun gama gaisawa da Shuwaiba ze fita se kuma ya dawo ya amshe wayar hannun ta yace "kina wani Abu ne?" ta girgiza mishi Kai tana d'an kwab'e fuska tace "Babu abunda zanyi, amma ka bani wayar please" ya saka wayar a aljihu yace "ki d'auko mayafinki ki rakani unguwa" ta mik'e tana d'an turo bakin hanata wayarta da yayi ta d'auko mayafinta ta biyo shi ( *hak'ik'a Shuwaiba ta siyama kanta mutunci a gurin mijin su ta nuna mishi zata so abunda ze so, ita shi take so ba hayaniya ba ta kwantar ma kanta y'anci da kanta, dama Arayuwar d'a namiji Yana matuk'ar so kinuna masa ya'isa namijin gaskiya Sam bayason rigima, Ina fatan mu rage wannan masifaffen kishin namu muyi koyi da Shuwaiba, Nima amin addua Allah ya ragemin kishin nan*).





"yaya ina zamuje ne" batare da yakalleta ba yace "gida Zaki rakani ko baki zuwa" ta girgiza Kai tace "inaso mana Nima daga nan na gano y'ar hajjata tunda ummah na ta tafi gida" Shureim ya d'aga Mata Kai, ita keta labarin ta har suka k'arasa.




"Asslamu alaikum" ya shiga falon bakin shi d'auke da sallama, Ummee dake tsaye gefen dining tace "ah ah Wai harkun tashi Aikin" Shureim yace "tun d'azuma har gida naje Nayi wanka" Ummee tace "to ya'akayi banji d'uriyar Sarauta ba ko bata dawo bane" Shureim ya had'e rai yace "bata dawo ba kuma" Ummee ta juya ta kalli Shubai'a ta d'aga murya tace "kinga dawowar Sarauta" Shubai'a ta girgiza Kai tana nuni da "Koda safe banganta ba" Ummee tace "Bari na kirata Naji" tana k'arashe tana dialing number Sarauta, seda ta kusa yankewa sannan ta d'aga, Ummee tace "y'ata kina inane" Sarauta tace "ah ah Ina gida mana" Ummee tace "kin dawo kenan" Sarauta tace "tun d'azuma kuwa se anjima" ta k'arashe tana katse Kiran, Shureim yace "Ummee Wai yarinyar nan Anya ita d'aya ce kuwa bata da wasu makarai akanta, Dubi kiga yanda take cije ma kowa yau, nifa ko gaidani batayi ba" Ummee tace "Nima dai Haka amma alamu sun nuna kamar wani Abun mukayi Mata" Shureim yace yanzu Dai tana Ina "Ummee bataso gaya mishi ba amma ganin halin da Sarauta take ciki yasa tace" tana b'angaren can na k'arshe, amma dan Allah karka takura Mata kaji "ya d'aga Kai ya juya, ya mintsini Shubai'a daketa chat sannan ya fice.





" Nidai kawai yaya Jameel ka rabu dani hakan shine yayi ma rayuwata kowa fa da rayuwar shi" jabeer dake waya da Jameel yake sanar mishi da Hakan, Jameel yace "Ohk to yayi nidama shawara zan baka Akan gwara ka nemi na kanka, wallahi dukiyar brother Shureim bazata tab'a ciwo muku ba saboda shine me gaskiya kuma ku in banda Baku da hankali, kun kawo yarinya kunsa ta aureshi, shuru kuma kukeji kuna ganin bata sanar dashi komai akai bane ko kuma kuna ganin baze iya yimata tayin kud'in dasuka fi Naku bane, to ka canza tunani ka dawo mucigaba da wannan Aikin da Nike wannan company ya ishemu rayuwar duniyar nan d'an uwana kayima kanka fad'a" jabber yad'anyi shuru Yana tunanin maganar d'an uwanshi kafin yace "Idan kuwa hakane wannan yarinyar semun Mata hukunci mafi girma a rayuwa, kuma kawai kayi shuru Shuwaiba y'ar uwata zata temaka min nasan zatayi iya bakin k'ok'arin ta" Jameel yayi dariya yace "amma Kaci wani Abu, to Bari kaji Shuwaiba bazata tab'a temaka maka ka cutar da mijin ta ba, eh Shuwaiba ta aureshi saboda he's billionaire, amma kasani ita ba kud'in take soba me kud'in take so, jabeer kayi tunani, ummah na gaishe ka tunda kayi girman da bazaka iya zuwa ka gaida ta ba" daga Haka jameel ya yanke wayar.






"Khameel Anya kuwa bakwa tunanin yarinyar nan Sarauta Amanar mu take ci" jabber yayi maganar wanda tunda yayi waya da d'an uwanshi take damun shi, Khameel ya gyara zaman sigarin shi yace "amma jabber meyasa kayi wannan tunanin" jabber yace "kaga tunda akayi auren nan Babu wani motsi a gurin yarinyar nan, nifa ina tunanin ta sanar Mai da komai ne, kuma yabiya ta kud'in dasuka finamu, yanzu da wuya Idan bashi takewa aiki ba, kuma Dai kun sani AKAN KUD'I Babu abunda bazatayi ba, gwara fa kusan matsaya" Nabil yace "tabbas ma kuwa saboda su dama kasan y'an Nigeria cin Amana agurin su k'aramin lamari ne, gaskiya akwai gaskiya a maganar d'an uwa jabber" Khameel yayi ajiyar zuciya yace "amma kuwa da yarinyar nan anyi tsinanna, bala'innan Aikuwa kukan ku kunsan da bak'aramin hukunci zamuyi Mata ba kaga shegiyar yarinya" kafin wani yayi magana Sega Fawax ya shigo fuskar shi d'auke da murmushi, yanda sukayi jugumΒ² ne yasa yatsaya Yana Kallon su, kafin yace "ah ah brothers lafiya" nan suka bashi labarin abunda yadace faru, shuru yayi yana tunanin wane me tunanin ne yasanar dasu hakan dan yasan sudai basu da wannan ilimin, amma kowaye wannan yayi musu wani Abu tab, ajiyar zuciya yayi yace "yanzu Idan maganar jabber ta tabbata ya kenan, waikai jabber tsaya ma ya'akayi kayi wannan tunanin" jabber yace "d'azu da mukayi waya da brother jameel shine yake sanar min Akan muyi tunani akai mudunga amfani da hankali, kuma kaga ai yayi mana tunani me kyau" murmushi Fawax yayi a zuciyar shi yace "ahaaf abunda nasani cikin ku Babu me kalar wannan baiwar" a fili kuma yace "tab lallai da kuwa yarinyar nan ta gane bata da wayo, amma kun gane Bari zan tambayi Juwaira Naji yanda ake ciki" Nabil yace "Nima zan tambayi sis Khaleesat ko xuwa gobe" Haka suka cigaba da sak'a da warwara.





*Kuwait*


"yanzu abunda ka zab'ama kanka kenan, taheer Nayi nasihar Nayi lallashin amma Abun Sam, a halin yanzu bansan in d'ana yake ba shin Yana Raye koya mutu yaci abinci kobe ciba, yayi aure kodai shima kamar Kai d'innan ne, wannan Abun kullum dashi Nike Kwana, Amatsayina na mahaifiya harna iya dannewa, mahaifin ku kuwa ya kasa aikata hakan wanda wannan bak'in cikin shine silar mutuwar sa, yanzu Kai kad'ai ne agaba wanda Nike gani da idona nikejin dad'i, Taheer meyasa bazaka Maye min gurbin Sarauta dakuma sarki Omar ba, meyasa bazakayi aure dan ka taramin jikoki ba, nasani tabbas da Sarautana yananan da Babu shakka zuwa yanzu nazama kaka, amma Kai d'innan kullum Abu d'aya, taheer meyasa kodai aljanu ne suka aurar mun Kai" mahiafiyar sarki taheer ta k'arashe maganar ta da tambayar shi, kanshi ya kuma duk'arwa yace "Sayyadarmu dan Allah kiyi hak'uri komai yayi farko zeyi k'arashe inajin ajikina Nur ta kusa dawowa kuma Haka zalika ma d'an uwana, in sha Allah Sayyadarmu ninan zan cika miki burin nan naki kinji dan Allah kidena damuwa dan banshirya WA rasaki ba a wannan lokacin" Sayyadarmu ta kalleshi tace "Allah yasa, harna gaji kuma da Jin cewa Nur zata dawo gareki Allah Dai ya kyauta kawai" sarki taheer yace "Sayyadarmu addua xakiyi min" tace "to Allah ya bayyana ta" yayi murmushi me kyau yace "Ameen Y hayyu y qayyum ngd Sayyadarmu" haka suka cigaba da fira.





*JIDDA*




Tunda ya d'auki hanyar part d'in yaji wani Jim, jikinshi duk Babu dad'i kamar bashiba, yakusa Isa part d'in kurum yaji kanshi ya Sara mishi Babu shiri yayo baya tare da samun guri ya zauna, d'an lokaci kad'an Yana zaune a gurin kafin kuma ya mik'e Yana tunanin mema ya kawo shi nan meyazo yi Anan, juyawa yayi ya nufi part d'in Neenah domin ya gaisheta kuma yasa Shuwaiba taje ta gaishe da Ummeenshi.





"sannun ka da zuwa Yarima" Neenah ta fad'a tana murmushi, seda suka gaisa sosai har sukayi fira sama sama sannan yace ma Shuwaiba "Shuwaiba ki tashi muje ki gaida Ummee daga can mu wuce gida" Shuwaiba ta mik'e tace "hajjarmu zamu tafi" Hajja Neenah tace "Tohm ai Nagode Allah ya tsare ku gaida mutanen gidan" suka amsa da "Xasuji" sannan suka tafi.





Ummee Tasha mamakin ganin Wai yau ita Shuwaiba tazo ta gaida, amma hakanan ta share har y'ar fira sukayi kafin su tafi.





Suna kaiwa gida Ummee ta Kira Shureim ta tambaye shi ya sukayi da Sarauta amma se yace Mata Bema jeba amma xasu had'u gobe.





*BAYAN Kwana uku*




"Mamu kenan ki kwantar da hankalin ki nifa bawani dad'ewa zanyi ba, kuma ma tare da Sarauta zamuje Idan muka dawo zamu zo tare ma ya gaida ke" Mamu tace "to kidai rik'e alkawari karki manta dani kema" Sarauta tayi dariya tace "Laaa ya za'ayi mutum ya manta da farin cikin shi" duk dariya sukayi kafin tayi sallama dasu Dania ta fito.





"Wai sarautar lafiya kuwa cikin y'an kwanakin nan senaga Kinata

Please Login or Register in order to submit comment